Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Subul da baka 1 page 1 Posted by ANaM Dorayi on 08:41 AM, 20-May-15 Under: Subul da Baka Lungu ne mai dauke da komatsen duwatsu, robobi, leda da kuma fasassun kwalabe, kana ketare Wadannan zaka yi karo da katuwar bola mai dankaren wari, musamman a lkc irin wnn wato damuna. Gefe da bolar daga hnn dama Wani kwarmatsattsen gidan kasane mai ' yar guntuwar katanga yana dauke da daki daya tak! sai makewayin langa-langa, daga bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane da ' yar guntuwar katanga yana dauke da daki daya tak! sai makewayin langa- langa, daga bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane da. ' yar randar ruwa, sai igiyar shanya data raba gidan biyu. Daga nesa kana hango gwangwanayen alwala a jikin langa-langar makewayin. Karamin gadon kara ne a dakin, mai dauke da katifar Rimi, sai jikunan kaya na gana ( Ghana must go ). Daga bakin kofar akwai ' yar kujerar katako ta zama, Kasa kuma an shimfida tabarma. Gida ne na mabukata wnd rashi yayi wa ka tutu. katutu. Na yi saurin maida kwallar da ke zubo min, tare da kara gyara fuskata. mahaifina Allah ya karbi rayuwarsa tun muna kanana kwarai, danginsa kuma sun yi fatali da al'amuran mu, nice babba sai kannena biyu Aisha da Sumayya. Allah ya jarrabi mahaifiyar mu da ciwon asthma, shi yasa duk talaucin mu baka ganin kura a gidan mu, musamman kura. Kr2 na ya tsaya tun shkr 2 da suka wuce, wato lkcn da na gama aji uku. Da farko na fara talla sai muka Ga cewa, hakan ba zai fisshe mu ba, shi ne Wani aminin mahaifinmu ya samo min aiki a gidan sari a matsayin BAIWA cikin bayin da aka dauka sabbi. Insha Allahu kuma gobe nake sa ran farawa. karfe 9 na dare muna shan garin rogo da kuli a matsayin abincin darenmu kamar kullum, Ina ta kalle ni tare da fadin. "Abinda nake son ce miki shi ne, ki yi addu'a Allah ya tabbatar miki da alherin wnn aiki, sannan ya kawar miki da sharrinsa kmr ydd na dage da tawa addu'a ba dare ba rana. Kuma a dk inda kika shiga ki sanya tsoron Allah a zuciyarki, ki tuna matsayin ki dana iyayenki, banda daukar abinda ba a baki ba, wlh ki guji abin hnn mutane ki zauna Lfy. Ban yafe miki ba matukar ba a baki abu ba kika dauka, ko kika roka. Aiki ya Kai ki, shi za ki maida hnkl ki yi, banda yawan surutun banza idan ba tmbyr ki aka yi ba, do min yawan magana na haddasa karya. kada ki manta ko ke wace ce, lkcn da kike ckn gidan SARAUTA, to ki ringa hango yanayin gidanku. Yi na yi bari ya rabaki da kowa, wlh dk wulakancin mutum dk izgilancinsa, matukar zai ce ka yi ko ka bari kuma ka aikata hakan, to lallai sai dai Wani abun,amma ka wuce wulakancinsa. Da fatan kin ji abinda na fada miki? " Na daga kaina Ina fadin, " lnsha Allah inna zan kiyaye ". Tayi murmushi, " Allah ya yi miki albarka, je ki sha ruwa ki zo ki kwanta kada gobe ki makara. Na ji shi mal. barau yace karfe 7 ake son ganinku a fada. ". Na mike Ina fadin, " ko 6 ne inna Insha Allahu akan lkc zamu je".Ta yi 'yar dariya, " ja'ira na sanki da sammako, amma ai dole ki zo ki kwanta din. WASHEGARI A GIDANSARAUTA Muka bi layi ana bamu kayan sawa, wdnd zamu ringa amfani da su a cikin gidan a matsayin " uniform". Yadi ne mai Dan Karen kyau, Ga taushi ruwan sararin samaniya (sky blue) dinkin riga da siket mai kyau iri daya kuma kowacce za a bata dai- dai ita, kowa kala bibiyu ya samu har aka yi saura, don mu 26 ne sabbin dauka amma duka babu wdd ta hour a shkr 22. Mafi akasari sauran iyayensu a nan suke aiki gidan sarauta, sai mu uku ne kawai wdnd muka shigo ta hanyar ALFARMA! Abin mamaki har 'yan kunne da sarkar wuya da ta kafa tare da awarwaronsu aka rarraba mana, irin kalar kayan, amman na duwatsu mai haske. Musamman Wani fankacecen daki aka bamu domin shiga, wai mu sanya kayan da aka bamu yanzu. Duk wnn bidirin a Wani bangare muke cikin gidan ba mu isa inda ake son mu isan ba hr ynz. "Allahumma arzukuna" kawai nake nanatawa lkcn da nake zura kayan a jikina, dk na rude sai kyarma nake yi. Mutum kusan 6 suka hada baki wajen fadamin cewa, NA YI KYAU!! Ni kaina nasan kayan dole su yi min kyau, sbd klr ita ce wdd na Fi so ckn kaloli, ba don komai ba sai don kyan da kalar ke yiwa fatar jikina dk lkc da ta rabu da ni. Muka biyo layi, dogarai sun saka mu a tsakiya wasu gaba, wasu gefenmu, wasu kuma a bayanmu. Inda dk muka wuce bayi ne ke kara-kaina mana da mata, haka na dinga raba ido Ina kallon aljannar duniya a wnn masarauta, wuce wnn tsuntsu, ruwa, filawowi babu abinda ba mu gani ba har Allah ya Kai mu Wani katafaren muhalli. A nan ne naga abin mamaki, mata ce kyakkyawa kishingide bisa Wani hadadden gado, bayi kusan 12 gewaye da ita, wasu na firfita, wasu matsar kafa, wasu na ba ta lbr mai dadi don 'NISHADI' banda wdnd ke bakin kofa da tsakar dakin suna kara- kaina. Aka gaba tar da mu cikin wani irin yanayi na girmamawa dk Ina lura da ydd suke yi. Ta kalle mu ckn Dan murmushi kadan, ta ce. "karasa da su wurin GIMBIYAR " Nan da nan al'amarin ya daina bani mamaki da fargaba gami da tsoro. Wani bangare muka nufa, sashen da ya firgitani fiye da ckn inda muka shiga, naji tmkr ba a duniya nake ba. Can ma wasu bayin ne bila adadin suna bauta. Mun fi mintuna 20 a tsaye ba tare da wani ya kula da mu ba, dogarawan na tsaye su ma kmr gani suka ba ni tausayi (neman halak da wuya). Zuwa can muka hng ' yanmata biyu da ' yan kwanduna a hnn cake da filawoyi masu kyau ga kamshi suna zubdawa a Kasa. Mamakina ya karu ganin wasu nayin shara, wasu na ba tawa. Ai ban karasa mamakin ba na hng hadaddiyar budurwa ta biyo sawun filawoyin ta sha kaya irin na alfarma, Ga wata hadaddiyar alkyabba tana faman jan Kasa, kanta cikin hular alkyabbar wdd bazar kwaliyar ta boye rabin fuskarta, amma kana iya hango kyallin zinaren da ke falauniya a wuyanta da kunnenta. Har ta zauna saman wata rantsattsiyar kujera ba a bar zubda filawar nan ba. "GIMBIYA! !" Na maimaita sunanan ta a ckn raina, Ina kara yi mata kallo. kusan mintuna 15 da zamanta amman ko kallon inda muke ba ta yi ba. Tuni kuguna ya soma rikewa sbd ni kam Allah ya sani ba ni da jimirin tsayuwa. kafin na Kai ga sarewa Allah ya taimakeni ta dago Kai a hnkl kmr mai fama da ciwon sankarau, ta wurgawa dogarawan nan wani mugun kallo, nan da nan naga suna durkusawa suna godiya tare da ficewa da sauri. Ta kalle mu, tare da fadin. "ku zauna". Nan da nan muka ciki umarni. " kafin na raba muku aiki zan barku anan ku taimakawa sauran domin ku ga ydd ake ya cikin kwana uku, daga safe zuwa kr2 6 na marece. Jidda! " Ta kwada kira a hnkl. Da gudu ta karaso dattijuwa ta yi kusan kanwa ta 4 da ita, ko kallonta ba ta yi ba, ta ce. "A kaisu ciki suna bukatar horo na kwana 3 kafin a raba musu aiki". Ta rusuna tare da fadin. "An gama Gimbiya. Ku taso ku biyo ni". Da sauri muka bita riii. .. ****"Inna mutane na wahala a duniyar nan, kuma mutane na jin dadi. Na ga mulki ni HUMAIRA inna, a zage ka, a ci maka mutunci snn kayi gdy, Kai SARAUTA wata aba ce! Wlh inna kwana 2 nan ba ki ji ydd jikina ke yi min ciwo ba." Tayi murmushi tace dama ai sai a hankali zaki saba kuma ai gobe ne kawai ya rage da an raba muku aikin bashi ke nan ba tunda kince akwai na safe akwai kuma na rana dana dare kinga idan na safe Allah yaci da ke karfe 7 kina can 2 kin dawo gida idan na rana ne kuma 2 kina can 6 kin dawo idan kuwa na dare ne 7 idan kika tafi sai safe bashi ke nan ba? Ke dai ki sanya tsoran Allah a duk inda kike ki kuma tuna yana ganinki a kowanne hali kika sami kanki aikin nan mi wahala ne mutuka domin shi ba wani share share ko goge goge ke gajiyar da bayi agidan sarauta ba aa cin fuska da izgilanci ke ba kowa wahala don haka sai an daure mai nema yana tare da samu ki tuna idan baki daure kika hakura ba ina zamu samu abincin da zamu ci?ruwan sha har gagararmu yake yi a gidan nan sai mu roko a makota ga karatun 'yan uwanki tundda ke baki samu halin yiba sannan uwa uba aurenki idan ya tasi wazai bamu?daga dangina har na mahaifinki kin dai san yadda ake saboda haka kiyi hakuri wata rana sai lbari" Baku Murmushi kawai nayi domin a ganina kamar nafi inna sanin wadannan abubuwan kamar kullum muka isa gidan cikin lokaci ni da Amira wacce muke tafiya tare kwana 2 sakamakon gidansu na bayan namu babu nisa kuma nice ke biya mata safiya idan muka dawo zata rako ni har kofar gida kafin ta koma nasu muna cikin wankin gimbiya misalin karfe 12 na rana ina ta alajabin wai har da wandunanta da rigunan nono shin ita bata jin kunya mata bada wadannan wurin wanki nawan haukan nake ganin kamar wani sirrinta ne wanda ya kamata ace ita ke kula da abinta kai wani abin sai gidan sarauta HUMAIRA nayi saurin waigawa na'am bar musu wankin kizo gimbiya na son ganinku ina kyarma na dauraye hannaye na cikin gudu gudu sauri sauri na karasa saboda na lura latti na saurin hasala gimbiya duk abinda ta umarta lallai tana son ayi mata shi da sauri acikin gaggawa ,Na iske su Amira a layi kamar ranar farko ni mana bi sahu ta yatsina fuska tana kallonmu daya bayan daya kamar mai kallon tsohon ciwo a jikin kazamin mutum ku kasu gida 3 ta fada a wahale ciki 'yan mintuna da basu wuce 2 ba muka rabu kamar hanya abin haushi Amira bata kusa dani don haka ya kasance bata cikin namu gungun ma'ana nasu daban ta nuna su Amira da baki daga yau zaku shiga cikin 'yan aikin rana gabana ya fadi nan da nan na hau addu'ar zuci kada Allah ya hadani da aikin dare saboda inna bana tunanin zan iya barinta ta ringa kwana ita kadai sai su sumayya saboda cikin dare asmarta na iya tashi ta juyo garemu cikina ya bada wani kugi kulululu kune masu aikin safe wadannan kuma su shiga cikin masu kwana. A hankali na furta alhamdulillah saboda haka ku nadare kuna iya tafiya sai shida kwazo tare da yan kwana na safe kuma kuyi sauri ku karasa na ku 'yan rana su kar6a xa'a dinga biyan kowacce dubu ashirin awata tana gama fadan haka ta kalli masu bata abinci akawo mun kalaci na anan mukai ta tsalle nida amira,saboda kwanan aikin ne daman muke gudu,ga kuma makudan kudin da muka ji ta ambata fan ni ko rabunsusu wllhy bansa rai ba.ina ta faman sauri babu ko waiwaye shiga wancan lungun kurda wancan hanyar saboda muna da dan nisa da gidan sarkin ban ta6a kawo wa raina abin hawa ba saboda rashin kudin biya.da zafina na isa gida ina dokin yiwa inna albishir,tunda ga tsakar gida na fara jiwo nishinta da kakari alamar ciwanta ya tashi na wancakalar da takalman na karasa a guje tare da tallabo ta a rude nake fadin ina kika ajiye inhelar? Sai neman san karewa take ta faman yi na ga wawtata dana tsaya tambayarta,alhalin nadade da sanin cewa ta kare. ,Haba a guje na fice gidan kamar mahaukaciya,nayi hayin kwalta kyamis din dayyabu ,sai zufa nakeyi na fada shagon ina ta haki, nace."Dayyabu ka dubi girman Allah kaba ni bashin inhela,wallahi na sami aiki gidan sarki da an biyamu zan kawo maka kudinka, bazan sa6a ba insha Allah" kin tabbbatar?yafada yana gargadina da hannu.na durkusa, wallahi dayyabu zan kawo kaji na zantse"yadda ya miko min maganin nace na gode"sai na kwasa a guje. Da zuwa na isketa ta kai kasa warwas na shiga shaka mata ina dan fesawa cikin mintuna 3 zuwa 4 komai ya tsaya.nayi ajiyar zuciya, Allah mai yadda yaso yanzu da aikin rana nake fa? Nadaga hannu sama nace, Allah na gode maka,Ubangiji ka kara rufa mana asiri". A hankali naji tace Ameen na kalleta nace sannu inna"tace yauwa Ahankali,ya aka yi kika dawo da wuri haka?na labarta mata yadda aka tsara sai na ga tana murmushi, ni kuma na mike zuwa tsakar gida na ga wacce dabara zan yi mana a matsayin abincin rana. **** Ina mamakin mutane,gabanka faram faram,amma bayan idonka arinka zaginka ana gulmarka.su yanzu idan gimbiya tajisu yazasuyi ko basu tunanin cewa tunda naji zan iya kwarmata mata?naci gaba da sauraransu "kinsan duk abin nan wlh ganin ita ce bababba kuma sarki duk yafi ji da ita,sannan kowa gidan tarairayarta yake yi ana lallashinta".kware kuwa saboda ko wani abu ake son mai martaba yayi,idan ta kife ciki wlh ba yayi sai da ra'ayinta". "mts! Ni ina ganin harda da rashin 'ya'ya dayawa ga sarkin,kinga fasu duka shiddane a gidan ita kadai ce wurin uwargida su ta sallah kowa na da biyu biyu,sai Amarya da ke da daya namiji shi yasa duk suka tsane ta sai kace ba Allah ne ya bata ba"ke kuwa sun tabbatar ta haifo MAGAJI.duk suka kyalkyale dariya harda tafawa."Wai ni ya maganar auren gimbiya?"Uhum!shu'umin mijin ne yaki zuwa har yau,kin san idan sarauta ta hadu da sarauta dole a baza MULKI.Amma naji an ce ya kusa zuwa nan gidan zai yi wata 2 sannan iyayen su zo maganar sanya rana"wannan wace irin al'ada ce haka? "Ke ma kin gani,gidan nan ai sun yi bin da yafi haka kawai tsabar ISA ce".kinsan abinda yafi bani mamaki tace A'a". ,Wallahi kullum idan muna tare da gimbiya ita ce mai nemansa a waya,bai ta6a bugo mata ba".suka kara dariya tace,"YARIMA!!! Wlh yarima na wahalar da gimbiya,ina tunanin sarautarsu tafi wannan zafi".ko? Kware kuwa,ki ga fa mulki irin na gimbiya da giman kai,amma wlh cikin kunnena naji tana kwantar da murya tana rokonsa kada ya ajiye mata waya". To ko bai sonta? Cikin sauri ta kai mata duka."Yi shiru ban ce ba,domin ba a jimutuwar sarki a bakina ba".yaushe zai zo? "An ce talatar nan".kin san da maimartaba da babanshi wasu irin abokai ne na kud-da-kud,kara tu ma tare suka yi a kasar waje". ,ke a Ina kika ji?""ya za ki tambaye ni bayan kakar innarmu a nan ta yi aiki?""Uhm lallai, tashi ki tayani kwaso wnk guga zan yi na zannuwan gado".Na biyu da kallo a kaikaice Ina kara luliya hirarsu ckn kwakwalwata, kafin daga bisani na wancakalar da shi. Na dage ckn bada himma Ina aiki na baji ba gani kmr daga sama naga Gimbiya da tawagarta sun zagaye ni. ' Yarbaba Wacce ke hnn damanta ta ce. " Allah ya ja da ran Gimbiya, shin ko wnn kike magana? " Kafin ta yi yunkurin magana tuni ' yan ' yan cikina sun kada, nan da nan gudawa ta kusa kubuce min ckn wando, tunani na ko laifi na yi. Ta kalle ni sama da Kasa kafin tace, " a zo da ita daki ". suka juya. ' Yarbaba ta daka mini tsawa. " Saki wnn aikin maza ki zo Kiran Gimbiya ". kwalla suka cika min idona, muna tafe Ina addu'ar Allah ya tserar da ni. Da shigarmu ta sallami kowa suka fice aka barni da ita.Ta kalle ni a yatsune, "Me ye sunanki? " Na ce,"Humaira".Ta rausayar da Kai, "Na yaba da hnkl lki, Nutsuwa da kuma kawaicinki. Kina da kyakkyawar trby kwarai da gaske, sbd hk na daukeki a matsayin Wacce Zata dinga kula da yarima idan yazo da safe kawai, ckn masu aikin rana ma zan sami guda domin ba zai so 'yan aikin dare ba sai dai wadanda ba a rasa ba. In son da safe da kin zo ki Kai masa ruwa a tasa kmr ydd al'adar gidan nan take, zai wanke kafarsa kafin ya sakko daga gado ma'ana bayan sallar asuba. Ke ce Zaki dinga wnke masa kewaye da gyaran dakinsa tare da bashi kalaci., sa sauran kulawa har zuwa karfe 2 rana, kafin ta ranar ta karba".Dadi ya kume ni na rusuna ckn girmamawa na ce."Godiya nake Gimbiya". Ta kawar da Kai, "Na sallame ki" ,Ta fada ba tare da ta kallo inda nake din ba. Na kara russunawa karo na 2 tare da fadin, "Godiya nake Gimbiya ". snn na mike tsaye shima kafin na Kai ga tafiya sai da na dan rusuna mata alamar girmamawa. Snn nayi gaba abina. Washegari mun dukufa gyaran sashen da yarima zai sauka, an kawata wurin komai an saka sabo wai har da sutura aka saka zuba mishi ckn sif, shin dama tsinken raginsa zai zo? Kai! wnn al'ada da wnn mulki da tsauri suke. Shi mulki, ita mulki, na ga wnn so yayya. Gulmar mutanena ta kara katsen tunani da hasashen da nake yi."Gimbiya na whlr da kowa a gidan nan".Inji Rabi Mamman. Ayyo ta amshe tana murmushi, "Baki ji abinda sarki ya fada wa matan gidan nan ba?" "Don yace ita ce sarautar sai a yi ta amfani da ra'ayinta, ga wuri a ce babu mai ra'ayin kansa sai abinda ta zartar? ""Mulki ke nan! ""Ni abinda ya fi damuna wlh da aka bar mu a haraba na so ace muna 'yan cki-cki don m u ga kwakwaf! Duk fa sabbin daukar nan ne ta raba a nan din, ashe daman sbd zuwansa ya sanya aka karo BAYI, ana yi da Kai ya fi ace ba a yi da kai".Ta yi dry,"wnn hk yake. sai mu jira jibin mu yi kallo, Allah ya taimake mu ya zo da irin na su bayin, watakila mu sami mazaje ciki ko kuwa?""In sami miji dai malama ke Ina sama'ila Tasawan? "Ta buga tsaki, wnn fa mayaudarine ba aurena zai yi ba sai shegen wayo kllm idan an bamu albashi sai ya kalallame ni ya amshi rabi ko da dada ba na fadawa, kllm ckn matsala yake kin ji fa wayo, ko ke kin ga mijin aure a nan?" "Ina! Wlh da sake ku yi mishi korar kare mai wayon tsiya". Ni dai a nan na barsu sbd na gama nawa aikin na nan bangaren, na koma bangaren Gimbiya, can ma na karasa wnd na baro. Idan kana duniya zaka ga abin mamaki kala-kala. Duk inda ka gitta kamshi ne, Gimbiya an ci kwalliya ta kin karawa. Motocinta ne a jere wdnd ke dauke da sunanta, GIMBIYA 1, GIMBIYA 2 har zuwa GIMBIYA 10, rantsattsun motoci na zama ni, ,Mu ne ckn sahun gaba zamu je taro Yrm, magana ba aiki na bace, don hk na tsuke bakina Ina kara mamakin wnn shagali. Lallai Gimbiya na matukar kaunar Yrm, hatta sarki da matansa ba a bar su a baya ba wajen tsara ydd za a tarbi wnn gagarumin baki. Inda za a hadu kmr ydd aka tsara nan muka tarar da su, don haka ba tare da bata lkc ba aka dungumo zuwa fadar Mai martaba don Kai gaisuwa. Mu kam tuni kowa ya kama tsagin da aka bashi don fara gudanar da aiki, ni kuwa inda Allah ya taimakeni a dai-dai wnn lkc na gama nawa a takaice 'yan rana Zasu karba, don hk tuni na harhada yanawa-yanawa na yi gida kafin kuma gobe da safe. Yau ma lbrn ya sha bambam da na klm, Inna ta dinga kyalkyala dariya, tana fadin, " lbrn gidan sarki bai karewa Humaira, ni dai hr na fara gajiya sbd tun da kika fara aikin nan klm da sabon lbr ake zo mini, babu maimaitawa. Kinga ni na manta wlh inhelar ta kusa karewa ki koma wurin Dayyabu ko Allah zai sanya ya kara baki wata kafin biyan ki" . Na ce, "to Inna, bari na yi sallar la'asar na je mu gani in zai bayar". Ckn yardar Ubangiji kuwa muka yi sa'a ya bayar, amman ckn kashedin lallai da an biyani na Kai masa kudinsa. Washegari na isa kan ka'ida kmr Klum, sashen Yrm na yiwa tsinke masu tsaron kofofin ko'ina na wuce suna tsaye ana gudanar da aikin tsaron. Masu dafa abinci na kicin sun dukufa. Na hanzarta zuwa falonshi na hau gyara ba tare da an sami wani wani kuskureba, snn na shiga dakin kwananshi. Abinka da rashin sabo, sai kawai na tsinci kaina da faduwar gaba, nan take na karanto, 'Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un". Barci yake sosai, daga shi sai gajeren wnd, ya kure na'urar sanyaya daki (A/C), dakin yayi karara don tsabar sanyi. Na kalle shi sosai, jin dadi sabo duk wnn uban sanyin amma bai rufa ba, na yi saurin fadawa makewayi na ci gaba da wankewa, tunanina ne ya tayar da shi, sbd lkcn da na gama na fito sai na tarar da shi zaune saman gadon. Da ma tuni na gama hada mishi ruwan wnk, da sassarfa na karaso wurinshi tare da durkusawa. "Barka da tashi Yrm, da fatan ka wayi gari ckn koshin lfy". Na fada kaina na Kasa. "Lfy, mai ya kawo ki dakina da sassafe kin hanani brc? "Na kara yin Kasa da kai."Allah ya huci zuciyar Yrm, tuba nake yi , wlh ban zo dakinka don na takura maka ba...""Ke!!"Ya daka min tsawar da sai da hanjin cikina suka kada."Ba ni amsar da na bukata".Ya fada ckn fada-fada kmr zai bugeni. Na yi sunkui da kai Ina fadin. "Ni ce mai kula da nan bangaren. .. Budewar kofar da aka yi ne ya sa nayi shiru. Gimbiya na gani ckn doguwar riga irin ta brc mai Karamin hnn. ya dalla mata wani rainannen kallo kafin ya ce da ita. "wnn yrnyr me Zata yi mini?" Maimakon ta ba shi amsa, sai ta dubeni. me ya rageGyaran gado da sharar nan". Na fada Ina nuna tsakar dakin."sai kuma kawo karin kumallo"."Da kyau,je ki hado kalacin ki kawo mishi, idan yayi wnk a gyara dakin".Inji ta. Na yi saurin cewa "an gama Gimbiya".snn na yi waje, ban San ydd suka kare ba. Tafe nake Ina al'ajabin wnn tsayayyen Yrm, shin ko gaskiyar 'yan gulma ne ba son Gimbiya yake yi ba? idan kuwa hkn ne lallai akwai MATSALA! Bisa kaina na doro tiren sbd ba ni iya dauka da hnn, akwai nauyi. Gimbiya ta tafi, amma shi yana inda ya ke, jallabiya kawai na ga ya saka. Na zuzzuba mishi komai, snn na hada mishi ruwan shayi (tea) kafin na zuba sukari na dube shi kadan. "wane adadi ne kake bukata? " "Au! Ni kike hadawa? "tmbyr tasa taso ta bani mamaki amma sai na sunkuyar da kai ckn girmamawa na ce. "Allah ya taimaka, duk kai nake hadawa karin kumallo"."To na koshi, dauke kayan ki ba na ce, ki ce wa Wacce ta aiko kin ba zan ci ba".A rasa new na dago Kai. "Allah ya taimakeka ba gardama zan yi maka ba, sai dai Ina rokonka don Allah ka rufa mini asiri ka amshi kalacin nan, lallai rashin amsarsa na iya haifar min da barin aikina a gidan nan". "So what? (sai me?)".Ya fada yana yarfe hannaye. Idona ya cika da kwalla na yi Kasa da murya. "Don Allah yallabai ka yi hkr kada ka yiwa kanka horon yunwa, ni matsalar Zata shafa". "Me Zata yi miki? "Ya tmby ni ."komai ma, ni dai kayi hkr ko na yi maka laifi? " Yanayin ydd na yi mishi tmbyr yasa na ga kmr ya dan tausayamin, sai yace. "Ba ni na hada Da kai na". Na yi saurin mika mishi kafin. Zaune nake har ya gama, sannan na kwashe kayan na fita. Lkcn da na dawo har ya shiga wnk, na yi hanzarin gyara gadon snn na share dakin. Na koma waje na ba shi mintuna 30, snn na koma. Har ya gama shiryawa, na yi turus! Jeans da T-shirt ya saka, maimakon Alkyabbar da na ga Gimbiya ta kawo mas. Na durkusa a gabansa. "Allah ya taimaki Yrm,

Chapter 1 of 11