Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
Momy da Maimartaba ba su ce komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa maimartaba daka musu wata irin tsawa da kowa da ya yi mamaki. Nan da nan kowa ya na'abba. Wannan ai hauka ne! Ya fada, sannan ya ci gaba da cewa. Ba ku da bambanci da dabbobi, musamman kai. Ya nuna Yarima. Gabana ya yi wani mummunan faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai zan koma. A matsayinka na namiji yausha zaka biye wa mace musamman lokacin da kishi ya turniki zuciyarta? To kowa ya zauna zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan zan fara da abin da ya kawo mu. Ya kalli Yarima, Ya sunanta? Kansa duke ya ce, Humaira. Humaira zo daga nan. Ya nuna min kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni saboda na san kaina kawai zai sare da adda shi ne sakamakona. Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake. Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba. Na gode, Allah ya yi miki albarka. Wane ne mijinki kuma?.saboda har da wannan tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima ce min yake yi matar abokinsa. Wayyo duniya! Wayyo Iñna! Wani sab9n kuka ya zo na ji kamar na zura a guje. Ko ba kya iya magana? Na ce wane ne mijinki? Wane ne fa banda Yarima. Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta ke zaune. Cikin tsananin bacin rai maimartaba ya kalle ta.. Kada ki yarda na gane ba ki da da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani. Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni, abinda ya ba wa kowa mamaki. Ya kalle ni, Humaira ko zan san wane ne mijinki? Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na iya furta. YARIMA NE! Amma don Allah ka yi hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da son.......Dakata! Bari kukan kada ki sarke. Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi ya sa ni da Yarima saurin kallon juna. Ya mike tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na mike saboda an bar ni ni kadai a zaune. Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban taba shan riwan gidansa ba sai a nan. Sai ka tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai hada kan iyalanka. Yana fadar haka ya yi hanyar waje, saura kuma suka mara masa baya. Wani yayan Yarima ya banko mini harara wacce ta sa dole na yi kasa da kaina. Karaf! A kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu da ma. Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka shirya da ma don a ci mutuncinta. Yan baya suka ji abin da ta ke fada, amma shi maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota. Ta yunkura tare da shako wuyana ta makare ni jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta kwada min abin fulawa ta fasa min goshi. Da kyara ya kwace ni tana faman dukana da harbi, ni kuwa sai kuka nake. Hayaniyarta ta dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina gidan tana ta hauka. Jikina sai rawa yake yi saboda tsoro duk na firgice sai bari nake. Da kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya daure da bandeji. Wayarsa ta fara kara ya dauka tun bayan da ya yi sallama, ban da kalmar TO babu abinda yake fada har ya ajiye. Ya kalle ni asanyaye. Maimartaba ne ya ce kar k8 sake ki kara kwana nan gidan, na maida ki can gidana inda Zarina ta ke ku..... Wallahi Kano zan tafi, ba ni kara kwana nan garin, ban iya masifar Gimbiya ko kadan nan din ma kana ganin ga manya ba ta j8 kunyar raunata ni ba, ina ga nan ware daga ni sai ita? Aure ne na yi na Allah, amma ba zan kuma ba. Idan ita ba ta da hankali ke ma....... Kwarai ni ma haukan nake a kan komawa gidanka kam, kai auren gaba daya ke bana yi, ko dole ne? Na fashe da kuka. Da ma tun farko ni wannan masifar nake gudy wallahu. Ya langwabe kai. Allah ya baki hakuri. Na hayyako masa. Eh da man duk wanda ka ji ana ba hakuri ai an gama cutarsa. Haba Humaira 8na hankalin ki ne yau? Daga turu na fito karewar hauka. Na mike ina faman hada kaya a jaka. Ya karaso murya a raunane ya ce. Don Allah ki yi hakuri, mu gode wa Allah da matsalar ta tsaya gurin Zarina kadai, kin ga alherinki ne ya sanya mahaifina ya yafe mini kan rashin bin maganarsa, shu ya sa aka ce YADA ALHERI BAYA ka tsince shi gaba. Wallahi.na tabbatar da lallai ya ji dadi sosai a kan abinda kika aikata, domin ni ina tunanin fushi da wulakanci wanda zan fuskanta a lokacin da ya gano abin da nake boyewa, don ko mahaifiyata ba za ta tsira ba. Shi ya sa na nace wa aurenki don na san ke alheri ce a wurina. Wallahi ba ki ji yadda hankalina ya kwanta ba..... Dole ka sami kwanciyar hankali mana, ni tunda ka ti silar tada nawa. Xaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Subul da baka 3 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 05:17 PM, 21-May-15 Under: Subul da Baka Ya yi murmushi, "ya xa a yi na yi silar tada hankalinki?" "ban sani ba". Na fada lokacin da nake qoqarin rufe jakar. "Allah ya ba ki haquri, kin ga maimartaba ya yaba hankalinki kada ki yi abinda xai sanya ke ma ki fita ransa kamar xarina". "dole kuwa in yi, domin na tsira da raina da lafiata.. A gabanka ta fasa min jiki, to ina ga ba ka nan?". "nima ai bayan idonta gashi kina mini tsiwa mai ya hana ki rama? Ko kin san xarina ta gane kin tsorata da ita? To wallahi ni ba xan tare miki fada ba, domin akwai lokacin da dole ba na nan kinga kuwa dole ta ringa ba ki wahala, amma idan ta ga cewar ke din ba ki tsoronta, to lallai xa ta shafa miki lafia, don Xarina ba ta fi qarfinki ba ni a ganina. Abin mamaki kishiya...". "ka ga malam ni ba fitina na xo yi ba...". "nima bana son ki yi fitinar, amma ya kamata ki amsar wa kanki 'yanci, ki nuna ke ma fa MATA ce ba baiwa ba. Maganar gida kuma wallahi babu inda xa ki tafi yau a gidana xa ki kwana ke da axara'ilunki xarina ta qarasa ki". Na fashe da kuka, sai kawai ya shige bandaki. ***** ***** *****Tashin hankali ba a sa masa rana, kwana 2 da komawata gidan aka kawo mini dattawa guda 2 wadanda xa su ringa tayani aiki, sabanin gimbiya da nata yara-yara ne majiya qarfi, kuma aqalla xa su kai su 9 ko 10. Qaton gida ne da babban 'gate' sannan kowace bangarenta guda. Yau xan amshi girki don haka magariba na yi na fara kimtse-kimtse, 2n 6:pm na sallami su dagwayye ana gama sallar isha ya shigo. Na kawo masa abinci ya kalleni. "yo ina en aikin?". Ba tare da na yarda mun hada ido ba na ce, "sun tafi sashensu na sallame su". Murmushi ya yi, "to dauko abincin mu tafi sashena". Gabana ya fadi, amma ban yarda ya fahimta ba. A falonshi muka xauna mai tattare da kayan more rayuwa, kujerun kansu sun ishi mu2m kallo, ban iya tsayuwa fasalta falon amma ina iya cewa komai ya ji na more rayuwa, hmmm! Jin dadi sabo na fada a xuci. (kun ji mu2niyarku an kile an fara 2nanin jin dadi). Allah sarki su inna qwalla suka kwanta suka kwanta a idona da na tuno inda na baro su. Na duqa xan fara xuba masa abincin kenan naji an ingijeni nayi baya- baya na fada qasa da qarfi, kafin na yi wani motsi ta biyo ni da qafa tana harbi, a rude ya taso tare da ture ta wuri guda ita ma. "ke wace irin dabba marar 2nani ce fareeda?". "wallahi wannan munafukar sai na hallakata a gidannan, don uban...". fas! fas!! tasst!!! ya wanka mata kyawawan mari guda 3 a jere. "kar ki dauke ni sakarai, shashasha mana, ke me ya sa kike da fitina da rashin son xaman lafia ne? ko don kin ga ina tausaya miki saboda abinda ke jikinki?". ta harxuqo masa kamar ta rama marin da ya yi mata. "mene kai din in ba sakarai shashashan ba?". ya qara wanka mata wani marin guda 2 qwarara, ya juya xai dauko kebul (cable) ta ko dauki wani abin fulawa ta kwada min a goshi. "bari in kashe ta don ubanta in ga abin da xa ka yi". Tana qoqarin qara rusa min shi ya riqe da sauri. 2ni jini ya balle yana son dauko tsumma yana tsoron kada ta qara min wani dukan. Ya fige ta ya 2ra waje kafin ya rufe qofa ta banko da qarfi. Ganin idan ya biye mata ni kuma xan rasa jini da yawa ya sanya shi qyale ta, ya nufo gurina da sauri. Cak! Ya dauke ni xuwa bandaki sai kyarma nake ina kuka, tsoro da fargaba sun fi yawa a gabana. Muka fito, ya janyo wani akwati sai ga kayan dressing ya ci gaba da gyarawa. Ta xo kanmu, "aikin banxa aikin wofi, an asirce ka, an magance ka er talakaka ke wa wannan kyarmar kuma don ubanki yau na ga yadda xa ki kwana dakinnan. Na rantse da Allah ko gawarki ba a yi mata wanka nan dakin domin ba na hada daki da ke, banxa talaka". Ya kalleta a wulaqance saboda yau da fareeda ba ta da ciki, da Allah kadai ya san illar da xai mata, ya ce "ga ki nan talaka wacce ba gaji arxiki ba, maimartaba da ya tilasta ya sa na aure ki Yau saboda munanan dabi'unki na tsiya yana dana sanin aurena da ke, 'yar talakar da ki ke qyama ki ka raina kuma a yau ita ake alfahari da ita a matsayin suruka". Bai rufe baki ba ta hargitso masa qa2war talabijin da ke manne a bango, ta fado bisa sauran tarkacen kallon da abubuwar glass ji kake ratsatsatsa!!! Ya dauki waya kamar mahaukaci. "hello sahabi kana ina? Don Allah idan kana iya fitowa yi sauri ka xo gidana yanxu". Ni kam ina can rakube jikin bango kaina kamar ya bare, ga wata masassara da ta taso mini, ko tashin hankali ne ya hana ya yi min allura, ko ya bani magani? Oho! Shi ya fada ita ta fada, da ya matsa kusa da ita ta nuno shi da kwalbar glass ya rasa inda xai billowa tashin hankalin, iyakar qarshe ya kai. Sallamar sahabi ya sa duk suka yi shiru daga ita har shi din "Subhanallahi, innalillahi, Hameed mene haka ya faru? "mtsew! Shigo idanunka su gane maka barna da asarar da yarinyar nan tayi min, duk goshin er mutane, marainiyar Allah...". "shegiya dai! Domin mun dade da sanin shegiya ce ba ubanta ya mutu ba..." "haba gimbiya don...". "yi min shiru munafuki, ina ce da kai aka hada baki duk abin da aka qulla. Ni xa a yi wa makirci? ayi wa plan? xa a qirqira dafa abinci ana kaiwa sarki don munafunci, wallahi yau sai dai ayi wacce xa a yi". "Me fa xa a yi bayan na shirge ki kamar jaka, don ba xan tausaya miki ba 2nda na ga abin naki ya wuce 2nani...". "haba yarima har sau nawa xan fada maka ka daina biye wa mace?". "ka san Allah na dauka wa raina sai dai yau na kwana prison, amma lallai gab na ke da na lalata rayuwar wannan...". In taqaice muku, haka muka kwana a tsaye ana abu guda 1, ko sallar asuba sai da yarima ya fara yo wa sannan sahabi ya tafi gudun kada ta qara ji min wani raunin. Suka dauke ni muka bar gidan, amma sai da yarima ya tare ta sannan sahabi ya fidda ni dakin, saboda yunquran da take yi sai ta caka min gilashi a ciki. Iyakar firgita da kaduwa nayi, 2n ina kuka har na koma xare idanu, ni kadai na fige kamar wacce tayi ciwon shekara. Gidan sahabi muka je, na yi wanka na yi sallah, na nemi ciwon kai da masassara na rasa, har qara kan da ya yi min wani jummm! Allah ka raba bawa da tashin hankali da fitina. Da qyar na sha rabin kofin tea shi ma don Hafsat ta matsa min matar sahabi. Ina kwallonta tana goge qwalla, ta tausaya min. Xuwa can wajen 12 sai ga su sun dawo. Ban san me suka tattauna ba, tayi juyin duniya ta fita na qi fita, saboda sam bana son ganin yarima, don a ganina shine musabbabin haddasa min wannan fitinar, 2n farko da bai dawo rayuwata ba kamar yadda muka haqura da juna da farko, da hakan ba ta faru a gare ni ba. Ganin ba ni da niyyar fita ya sa ta ce, ya shigo dakinta ya same ni. Baqin cikin shigowarsa ya sanya ni kuka. Ya yi shiru kusan mintuna aqalla 8-10, kafin ya fara magana cikin sarqewar numfashi. "kiyi haquri humaira, na san cewa ke ba mai son magana ba ce, ballantana tashin hankali irin wannan, amma komai ya xo qarshe, mai martaba ya amince da na raba muku gida. Yanxu haka har ya bamu wani a lowcost cikin estate din da ya yi. Don haka ya sa kika ga mun dade sai da muka kammala komai, yanxu haka ana can ana sauran gyare- gyaren da ba a qarasa ba". Ke dai da ke kara2 idan na tanka kin tanka, ya matso kusa da ni, "ko sai xuwa dare idan kin qara hutawa nan? Na ga can din ma ba hayaniya, sannan babu aikin da xa ki yi, saboda su malama dagwayye na can 2n daxun". Ko motsi ban yi ba. Ya matso tare da xama bakin gadon. .....Farko da kuma kullum lallai tana kan hanya, 2nda a duk lokacin da muka hadu sai ta nemi xubda jinina. Ka sallame ni na tafi gida don girman Allah, bana sha'awar xama da kai ko da da qwayar xarra ne, domin wannan fitinar somin tabi ce yanxu aka tsoma hannu, ma2qar ina tare da kai". "kar ki so kanki mana humaira! Yanxu wannan baraxanar ce xa ta sanya ki bijire min? Ki iya 2na cewa, so da qaunar da nake yi miki ya sa na take dokar mahaifina na aure ki saboda Allah, na xabe ki fiye da tsinuwar mahaifina da fushinsa. Duk wannan baraxanar fareeda ta sami qwarin gwiwa ne daga wurinki, don ta fahimci kin kamu da matsanancin tsoronta. Ina qara fada miki, ki tashi tsaye ki qwatar wa kanki 'yanci, na tabbatar fareeda ba ta fi qarfinki ba, kawai kin sa wa ranki tsoro ne. Ga babban takaici ni din da take yi domin ni, saboda ta fahimci irin son da nake yi miki baki nuna damuwa a gare ni ba, babu wata kulawa. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ke ma ki nuna mata lallai ke ma mace ce, saboda duk wannan haukan da cin mu2ncinta ni ba xan sake ta ba domin al'adata ba ce sakin mace, duk da ba ni sonta, kuma ba xan sake ta ba ballantana ga dana ko diyata da ke jikinta". Ya miqe "xan jira ki a waje ki kimtsa mu tafi". Yana fita na koma na kwanta wajen mintuna 5 sai ga hafsat ta shigo, salati ta kama yi tana tafa hannaye. "kai jama'a, wai humaira kwanciya ki kayi? To wallahi tashi ki bi mijinki". Na miqe ganin ta dauki abin da xafi. Ta biyo tana fadin "wallahi ba ki da wayo yadda kika dace da mai qaunarki haka, duk wannan fitinar bai girgixa shi ba, amma kike ja baya da shi? Wallahi da ni ce wani sabon salon shafin soyayyar xan bude, kuma sai a gaban gimbiya xan nuna don ta ji haushi". Nayi mata banxa saboda na fahimci bata gane irin salon masifar gimbiya ba. Xaune yake cikin motarsa anaconda sahabi na tsaye jikin taga ban san abinda suke tattaunawa ba. Yana ajiye ni ya juya wai xai je gida, umma na son ganinsa. Kai daure har lokacin da bandeji a goshina, su dagwayye suka tarbe ni suna masu jajantawa, tausayina fal a fuskarsu. Nayi murmushi lokacin da na sami kujera na xauna. "ashe duk kuna jin wannan fitinar?". "qwarai kuwa ranki ya dade, wannan tashin hankalin ai babu dadi yau kam na kusa da ita ya shiga 3 saboda yarinyar nan ba ta da kirki ko alama, rashin ragowa a ba ya da dadi a rayuwa". "hmmm" kawai na ce. Wayata ce ta dauki kuka, nayi saurin dubawa don idan yarima ne wallahi ba xan dauka ba. Sunan inna na gani, wani irin dadi na ji har cikin raina, na kalli dagwayye. "ina ne dakina?". Ta nuna min da hannu. "ga shi can". Na miqe tare da daga wayar saboda bana son maganar gabansu duk da sun santa. "Assalamu alaikum, inna kashe in bugo miki kar a cinye miki kudi". "a'a barshi ina da isassun kudi, yarima ya turo min kati sosai, da ma wancan bai ko yi rabi ba... Duk kuna lafia ko?" "da sauqi dai inna". Na fada a hankali cikin muryar damuwa. Hankali tashe ta ce "me ya faru ne? Ko mahaifin nasa ya gano matsalar ne?". "a'a inna ko daya, shi mun daidaita". Na fada mata duk yadda aka yi "to me aka yi yanxu kuma?". "gimbiya ce inna wallahi bana iya masifar wannan matar". "haquri xakiyi, watarana sai labari". "inna ita fa har gabansa yi min take yi, ga shi tana iqirarin sai ta hallaka ni". "duk kishi ne babu abinda xata yi miki wanda Allah bai miki ba". Kamar in yi kuka, wai me yasa inna ba ta ganewa kullum idan ina kwatanta mata, ga shi ba na son fada mata raunin da ta ji min kada hankalinta har asmarta ta taso. "xata daina kiyi haquri dama xama ya qunshi haka ga masu sabon aure, kuma na hore ki da kai qararta ma2qar abinda ya faru tsakaninku bayanan. Yana fada miki baya sonta a baki, wallahi ba ki san xuciyarsa ba musamman yanxu da take dauke da ajiyarsa, duk yadda yake sonki yake kuma dokinki da kin kai masa qorafin matarsa xai ji kin fara sure masa. Ko 2nkararsa kika yi da muhimmiyar magana ba xai wani baki kyakkyawar kulawa ba, domin xai yi 2nanin qorafinta xa ki kawo masa. Rayuwar aure humaira haquri ake yi, kowace mace baki san irin xaman da take yi ba nata abokan xaman, amma tayi xamanta... Haka ki rike sirrin mijinki kuma ki kyautata zamantakewar zamanki da mijinki.munanan lafia kalau muke kuma muna cikin kwanciyar hankali dajin dadi alhmdllh kiyita godewa Allah ga mansura can yar uwarki mijin dukanta yake watanni nawa da aure amnan hr ya saketa saki 3 wanda Allah ya haramta..yarima ne tsaye bakin kofa ya kuramin ido cikib tuhuma na da dauke fuska..Allah ya kyauta inna zan kiyayae insha Allah inyi yadda kikace..yawwa toh Allah yayi miki Albarka ki dage da addu'a kada yi sanya da ibadarki,nace toh a gaushe da mutanan gidan nace zasuji a gaida su sumayya..ke kika buga mata ko ita ta bugo miki ya tambayeni lokacin da na ajiye wayar idonsa kyam a kaina wallahi na tsani kallo, na fada a zuciya amma a fili sai nace ita ce ta kira ni, wai me? kokwanto na me ni da uwata? ni ma ai uwata ce ko? na zaro ido ashe ba a zuciya nayi maganar ba,na lura ta yi masa zafi sai na hau kame- kame yayi saurin tarata cikin kunar rai "don me zaki fada mata rikicin da ake ciki,ko duk salon rashin kwanciyar hankalinta ne kike bukata? rainin hankali duk duniya akwai wanda ya kaini tattalin kwanciyar hankalin inna. "mst" ya buga tsaki wallahi humaira kina da matsala yasa kai ya fice rai a bace mamaki ya kamani ni na bishi da ido. kamar abin jira wayata ta kara kuka nayi saurin ridota na ga sunan amira a hanzarce na daga domin ina da bukatar nemanta ni kaina. hello kira ni don allah kiran gwandala daya ce ba kudi tuni ta mutu alamar kwandala dayar data ambata an cinye ta babu bata lokaci na kira ta. kaji manya ta yarima bada kanki a sare. nayi murmushi nace ke ni bana son iya shege da man wallahi ni ma ina da niyar kiranki a yau dinnan. dan allah? nima tun dazu nake neman ki bata shiga ba daman na fada maki an sanya rana nan da wata shida bikin yayi. a'a toh allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna mana lokacin lafiya. safwan kuma ya sami addmission saudi arabia zai cigaba da karatu yace shi da nigeria har a bada . nace allah sarki, amira baki tambayata ya zamana ba ? nayi mata tambayar dan na kau da wanchan zancen. hmm ai ko ranar juma'ar nan da abin ya tuko ni har zan kira ki sai na ga cewa ke fa har yau baki ce min komai ba toh ni kuma binciken me zanyi? nayi murmushi, hmmm ke dai bari na kwashe duk labarin kaf na fada mata sanna na cigaba da cewa "wai amma duk wanna fitinar ni yarima yake gani da laifi shin amira ina ni in fada da gimbiya lillahi warasuluhu? "tabdi" ta fada da karfi. nace maccen da kemin wannan illar har yaushe zan biye mata ranar da ta kunso wuka ta luma min fa? lallai kam ta kara fada "yanzu haka fushi yake yi da ni,wai na ki sakin jikina da shi yana ganina da wani gaggarumin laifi."ikon allah ta fada tana kara jinjina maganar. "ba ma kisan ina cikin matsala ba sai na fada maki cewa ,yanzu ya gama min fadan don me zan sanar wa inna,kuma wallahi amira ni ban ma fada mata gimbiya ta ji min rauni ba shine yayi fushi ya fita, kiji faa? "ke kam bone ta ciki humaira. wallahi kuwa na fada a marairaice. to iya gimbiya ta san inda ka maida ke ni yanzu? ni ban sani ba amma kema kin tabbata komai daren dadewa sai ta gano ni matukar ba baruwa nayi da yarima ba. ta ja dogon tsaki tace " ke wallahi bnaza ce saboda wata banza sai ki rabu da mijinki maimkaunar ki haka humaira? wannan furuncin naki fa zai sanya matsala ta afku tsakaninki da yarima. wai inna ta baki labarin yadda ya mayar da gidan ku? gabana ya fadi nace " kamar ya fa? tace "wai baki sani ba? ko daya ni dai na rabe da kullum mukan yi waya da inna sai ta ce kada na gaji da yiwa yarima godia" "lallai to wallahi kin san gidan honorable? na hanga nace kwarai, saboda duk shiyyar unguwarmu babu gidan daya kama kafar gidan honorable nura nasimat." to ko kofar gidan ku be kai ba a yanzu wurin kyau da tsari ke yan aikin inna biyu fa da me mata abinci da me mata shara da goge goge. " tsakanin ki da allah amira"? " na rantse da allah ta fada tana yar dariya. shiyasa nace maki wlh ki daina wannan furucin , yarima baya taba iya rabuwa da ke. da yayi maki fada yanzu har yai fushi ai da sai kiyi tunanin cewa inna fa mahaifiyarki ce amma ya nuna damuma fiye da taki, ke bama abin alfaharinki ne ma kina in a wanna zamanin akeyin fito na fito da surakai? to wallahi ki gaggauta zuwa ki bada hakuri sannan kada matsalar gimbiya ta sanya kiyi watsi da masoyinki, baraka ta shiga a sami rauni wannann shine babban burinta. nayi kasa da murya " amira nagode allah ya bar zumunci". Amin amin, na gode sai munyi magna. na dafe kaina tsananin tausayin yarinma ya mamaye zuciyata kmr kaina zai bare. a hankali na mike ,rabi na goge wasu zannuwan gado nace "ina yarima ne ko ya fita?" "A'a yana dakin chan" ta nuna min da hannu na bi sirdaden da ta nuna na sa hannu na murda gaa mamakina naji ta bude. na shiga sai na ga tankamemen falo ne daa yaji kayan gayu irin na zamani. na hango kofa daga yamma alama nan dakin yake na hanzarta isa tare da budewa. jin an bude kofar yasa shi dagowa da sauri na lura da idanunsa sun yi ja matuka, shi dai kam bacin rai na haddasa masa jan idanun, na fada a zuci saboda yadda na san idanunsa farare tar har wasu ruwa kake gani kwance saboda haske. ganin nice sai kawai ya maida kansa ya kifa kamar yadda yake kwance ruf da ciki.tausayinsa ya kamani ,naji kamar na dago shi na rumgume a yadda naji sonsa ya karu a raina. sai dai miskilancina bazai barni aikata hakan ba, na zauna bakin gadon gab da kafafuwansa ko motsawa bai yi ba. na rasa inda zan fara, toh me zan ce masa? daraba ta fado min. "amma yarima wannan kwanciyar ce fa aka haramta saboda ta yan wuta ce babu kyau yin ta" a hankali ya juya amma sai ya bani baya ya kalli can. raina ya bani fushi yake yi." allah ya baka hakuri" na fada a hankali. bai dai ce komai ba bai kuma motsa ba, nan da nan kunya ta baibaye ni naji duk na tsani kaina. na tuna irin dizgi da wulakanci sa da gimbiya ta sha, ba shi da wuyar dizgi ai sai na raina kaina. Na yunkura zan tashi gwiwa sake ina nadamar kawo kaina, sai kawai naji an ruko ni ta baya."ina zaki je kuma? haka ake lallashin maigida idan yayi fushi?" na sunkuyar da kaina, ya buga tsaki "ni di wanna kunyar wallahi tana kwarata....zo na koya maki yadda ake bawa maigida hakuri" ya shiga yimin cakullulo tun ina zillewa har na hau kyalkyata dariya sai kawai ya kura min ido, nayi saurin rufe idona shi kuma ya kai bakinsa ga nawa nan da nan yaren ya sauya.******** Cikin kwana uku ya bude min ido ya koya min son sa da tarairayarsa muka bude sabon shafin soyayya.na yi nadamar rashin sakin jikina da nayi tun farko na gane cewa lallai ba karamin so yarima ke min ba, ban da shagwaba babu abinda yake zuba min , duk yadda na wasance dole wani abun idan yayi min shi sai naji kunya, shi kuwa banda zagi babu abinda yake yiwa kunya, wai kunya na kwarar sa (mata a rike kunya domin ita ce adon mace, wallahi duk yadda kuka dade da miji ki rika nuna kina jin kunyar sa wasu lokutan musamman lokacin da kuke kebe kudai yana karawa mace martaba da kima a idonsa). Kullum cikin zabga karya yakeyi a asibiti cewar yayi tafiya ne maimartaba ya aike shi. Washe gari ya kama zai koma gidan gimbiya kamr kar ya tafi nice me kwarin gwiwar bashi magana, da kyar ta tafi wajan karfe biyar na yamma. kullum yana zuwa da safe mu gaisa da marece kuma ya dawo yi min sai da safe, ina lura dashi sam walwalarsa ta sauya amma sai kawai na share na san shi da mutuniyar ne ni dai allah ya min alamnashara. Rnar da zai dawo ina ta

Chapter 10 of 11