Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
lbr. Kada muyi shisshigi na tabbata mai kudi da talaka da mai sarauta duk Allah guda suke bautawa. Kuma ba wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoronsa. Zan tafi dashi don ya halarci bikin gudun faruwar wani abun zamansa anan zai iya zama wani tashin hnkln nizan bar wanda zai kula da kamar... Inna ta kalleta ISA bazamu kara kwana a nan ba yau zamu tafi gida. Da sauri ya dago kai gsky mama ba inda zanje gobe idan an kai amaryar da daddare na taho washe gari ayi budar kai amma dole in tsaya in kula da lfyrsu inna don nine musabbabin faruwar komai. Inna ta girgiza kai ko kadan bazakyi wann danyen aikin ba wllh mun yafe duniya da..... Ni inna ban yafe ba. Dakata to yanzu me kakeso ayi? Wane irin so ne mama ke masa batason bacin ransa kokari take tayi masa yanda yakeso. Ya bata fuska yace a kyaleni na zauna da inna gashi tfyta tasa zasu koma gida suma... Inna tayi murmushi na rantse da Allah ba wann ne yasa zamu tafi ba asibitin ne kawai bana son zama . Sadauki yace to ai ba'a gama dubaku ba ko inna? Tayi shiru bata tanka ba. Tace to zuwa yaushe za'a sallamemu? Ya langwabar da kai nan da kwana 4 da an kwance daurin. Ta kauda kai tace Allah ya kaimu suka amsa ameen. Mama ta mike zan bar mace 2 ta dinga kula daku zuwa sanda za'a sallameku zasu dinga siyo muku abnci da duk abnda kuke bukata, ta dora bandiran kudi akan gadon inna ga wann ko zaku bukaci wani abu, Allah ya bada lfy Har ta fito bai motsa ba Inna ta kalleshi tace tashi ka bita Allah ya bada sa'a. Saura kadan kwalla ta zubo masa ya kalleta yace inna banida lfy zuciyata na min zafi ga humaira tana fushi dani bata kaunar kallona tun jiya bata min maggana. Ya kara langwabar da kai inna laifi na ne? Cikin tausayawa tare da mmkin soyayyarr da yake min tace ba laifinka bane humaira kuma kada ka damu wann halinta ne nima tana min irin wann. Yace inna in bata waya? Tace a'a bazan taba amincewa ka bata waya ba kayi hkri kamr yanda nasha fada maka to yau ma kalmae ce. Ya sauka kasa ya durkusa. DonAllah inna ki taimakeni kinga gobe nisa zanyi daku. Tace kayi hkri wann sharadin mahaifinta ne idan ka aureta saika bata. Jin wann batun yasa ya mike kamr me koyon tfy haka yabar dakin. Wani dunkulallen abu ya tokare min wuyana shi bai wuce ba shi ba fito ba na runtse ido a cikin raina ina fadin Innalillahi wa'innalihirraji'uan. Motsin su Aisha yasa na bude idona na dauka ko shine ya dawo da sauri na maidasu na rufe ruf a yau na tabbatar yayi min nisa. Anya zai dawo gareni? Na dafe kaina cikin ikon Allah sai kwalla suka zuraromin makar famfo inna ta kauda kanta. na fara rokon Allah ya cire min tunanin yarima kuma Alhmdllh na fara ragewa sosai. Da marece bayan mun gama awara ina zaune inna taje gidan kawu auwalu su Aisha sunje islamiyya kamr daga sama naji sallamar amira da gudu na tarota muka rike juna cike da murna na kalleta a lokacn data zauna Inna bata fada miki inata zuwa ban iskeki ba? Ta dan bata fuska wllh humaira inajin sakonki matsalar bana zama kullum nayi dariya sannu agogo. Ta kai min duka na kauce ta mike dama lbr nazo na baki sannan nayi miki albishir kiyi min murnar abnd ya sameni safiyar nan kuma muyi bankwana amma tunda....... Haba kawata yi hkr, da kinjawa kanki yarnya ta kara gyara zama humaira yanayi miki wani irin so wanda bazan iya fassara shi ba domin abnd ya faru lokcn da za'a tafi da gimbiya motar mu daban amma ni ya hanani nabi cikinsi ya sanyani a motarsu. Nida shi ne a baya tunda muka tafi kansa yake a duke har muka bar garin nan zuwa can ya dago ido jajur don saida na tsorata. Inason kawarki amma son bayada amfani gareni. Na sunkuyar da kaina kawai ina wasa da yatsuna wanda ke tukin motar ya juyo kaidai akwai dan iska yaushe muna kan layin raka matarka gida amma kana zancen wata? Shiru yayi kamr bada shi yake ba kinsna miskilancin mutumin naki. Yaja guntun tsaki daga nan bai kara mgn ba har muka isa. Humaira naje karshen mulki a sarauta naga inda ake takama da sarauta ashe su gimbiya basu iya komai ba? Motarmu na tsayawa wasu gardawan sarki suka zo wani ya kwanta saman shi ya sauka biyun kuma sukayi sama dashi bisa wani dan gaka suka daukeshi sukayi ciki dashi daga nan ban kara ganinshi ba sai washe gari. Kwana akayi shagali washe gari da misalin 12 akazo nemana na gane hakan ta yadda akayi kwatancen wacce suka shigo mota 1 da yarima cikina ya dinga kadawa sbd tsoro kada ace ko cigiya sukeyi. Munyi tafiya sosai kafin muje inda suke ya nuna wata kofa ki shiga ba tare da bata tym ba na shiga mazane shakare a falon duk gimansa sun cikashi na duba amma nakasa gane kowa a cikinsu da alama basu damu da shigowata ba. Keni sai tsoro ya kamani nayi saurin juyawa kamar daga sama naji ya kira sunana ashe yana kishingide cikin kujera yana kallona Hmmm miskilanci da kasaitarsa yana ba mutane tsoro, a tsorace na karasa inda yake ko kallona bayyi ba ya miko min wata rantsattsiyar wayarsa, ungo kisamin lamabr da kike gani zan iya magana da kawarki nakasa karba sbd kinga banida lamabar kowa a kaina wllh kota sadan gidanmu ban rike ba. Murya na rawa nace wllh banida lambar kowa akaina Allah ya taimakeka. Kallon da yayi min na rantse saida guntun fitsari ya zubo min idanunsa sukayi wani irin ja har wani ruwa ruwa ya kwanta. Tunda ya dauke kao bai sake kallon inda nake ba saida na kusan 1hr a haka nagaji iyakar gajiya har kafafuna sukayi sanyi, dogarawan dake tsaye suna masa firfita sai kallona suke na raina kaina a wurin ranar naji na tsani abotarmu dake. Da Allah ya taimakeni saiga wani abokinsa ya kalleni yace wann fa? Naga bakuwar fuska, ya kalleni da wann yatsinar tasa yace ki tafi mana. Simi-simi nabar gun kamar na bude kasa na shige don kunya. Bansan wace amsa ya bashi ba. An gama shagulgula amarya ta tare a gidanta wann sashe daya kirani gida yasha kayan kwalliya dukiya tasha kuka. Abnd ya bani mmk har yanzu basu bar al'adar nuna kwanan amarya ba. Sbd washe gari gida ya rude da gimbiya bata cika budurwa ba Abun kunyar gimbiya ya nemi komawa fitina da tashin hnkl. Ga yarima an nemeshi an rasa tun safe gimbiya ko sai kuka take sharbawa kamr ranta zai fita tana rantsuwa tana sharbewa wai bai kwanta aure da ita ba. Magana har gaban sarki gida ya sake rudewa duk inda ake zatonsa an aika amma ba'a tadda shi ba, hnkln gimbiya ya kara tashi mai martaba ya kara fusata ita kuwa mahaifiyarsa ko gezau saima fada data kamayi ita bata ga amfanin auren dole ba shin tunda yace bayaso bayaso a kyaleshi ya auri wacce yakeso mana. Aiko magana ta komawa sarki, ta kalleni Humaira munga tashin hnkl bana fatan sake ganin fushin babba idan haka yake. Maganar na zuwa wajen sarki kuma sai aka sami wayar sarki yace duk inda yake wllh ya bashi 3mins ya gurfana agabansa sannan ya aika aka kira sauran matan gidan cikin yan dakikai falon me martaba ya cika da ahalin gidan gimbiya na tsakiya har lokacn bata daina kuka ba zuwansa kawai ake jira. Shigowarsa ke da wuya ga mmkin kowa sai mai martaba ya mike ya dinga kwada masa mari har sau uku hancinsa kuwa ya balle da jini amma wllh ko gezau baiyi ba. Ni zaka kawowa raini? Ni zaka tozarta ka kunyata a idon dunia? Ka kwanta da matarka ko kuwa? Jinin dake zuba a hancinsa har ya fara bata gaban rigarsa fara, ya sunkuyar da kai a'a ban kwanta da ita ba. Ya fusata kayi hakane don ka nuna ban isa dakai ba? Ya kalli jakadiya saikije ki fada mutane yarinya bata kwanta aure ba Allah kuma zai saka mata bacin sunan dakayi mata. idan kuma nina haifeka wllh babu kai ba talaka komai ya dawo kunnena yau kuma na tabbtr da daurin gindin daka samu daga uwarka. Duk ranar da naji baka rabu da ita ba to wllh na yafeka dunia da lahira shashasha sakarai! Wann furucin na sarki ya haifar da zazzafar tsana da kiyayya tsakanin gimbiya da mahaifiyar yarima shima cin zarafin da akayi masa gaban jamaa ya kara sashi jin tsanarta fiye da baya. Sarki yayi musu kaca-kaca shida mahaifiyar sbd ina zargin ita ke goya masa baya. Sann yace da gimbiya dataga wani abu wanda baiyi daidai da tsarinta ba ta sanar dashi zaiyi maganin abun cikin gaggawa. Ana barin fada yaje ya zuba kankana akan habon jinin ya tsaya muna harabar gidan mukaji karar gimbiya sau daya. Muka razana kar dai ace shaketa yayi muka nemi shiga amma ya kulle kofar Ganin ya kullo kofar tsoro ya kamamu don munga shigarsa cikin tsananin fushi, karima ta kalleni gsky amira guduwa zanyi bana iya wan bala'in da gimbiya...uhm uhm wllh duk abnd yayi mata ita taja auren nan hadin iyayene, tun farko ya nuna mata bayaso shin idan ita mai wayo ce basaita lallabashi ba? Ga rashin so ga izgilanci da tsageranci mekike tunanin zai haifar? Kinga kuwa abnd tayiwa mahaifiyar humaira da ita kanta humairan? Wllh na tabbt gimbiya zata iyakisan kai, amma ke bakiga yanda ya shiga da fushi ba? Shin koma menene aiya riga ya faru ko kina iya balle kofar ki shiga? Ko dukansa yake kofa bude kina iya karbar gimbiya hannunsa ne? (Wannan rawar kan sai SIYYA) to wai humaira na sonsa da gaske? Kwarai saidai tsoro ya rinjayi son shiyasa ba kowa ke ganewa ba amma wllh humaira na sonsa matuka. Nayi saurin kai mata duka ni nace miki ina son sa? Kai-kai-kai ni kika doka? Baki sonsa kenan? To bari na tafi gida dama na dauka kina sonsa shiyasa na tsaya bata tym dina ina baki lbrnsa. Na marairaice yi hkri kawata dan karasa min wasa nake miki sorry, kina sonsa? Sosai ni kuwa ke sonsa zauna ki karsa min dukanta yayi? Wace irin fitina ce ya kara janyowa kansa? Na fakaiceta na mata gwalo, ta zauna idanunta sunyi ja kwalla ta taro mata taci gaba d acewa muna cikin wann magana humaira sai gashi ya fito ya sha kananan kaya yana ta uban kamshi hhar tym din acikin fushi yake. Dogarai suka rufa masa baya yayi hanyar shakatawa. Yana bacewa mukayi hanyar daki dake kallon nasa muna jiyo gunjin kukanta. A hamzarce muka nufeshi kwallan da take kokarin maidawa suka zubo gabana ya fadi na kosa naji abnd yayi mata ta kalleni kwallar na zuba wllh humaira duk irin isgilancinta saida ta bani tausayi, kwance take bisa gado yarima yayi mata kaca- kaca jini duk ya bata zanin gadon (wayyo Allah yarima ashe dai mugu ne kai?) Kukanta kawai kakeji har muryarta ta dashe amma bata iya ko motsawa hannu karima ta dora aka ta kurma ihu ni kuma na hau kyarma kukan yaki zuwa min hnklina ya bala'in tashi don ko a lbri wllh ban taba jin irin haka ba da gudu na fita zuwa sashen mama na sanar da ita abnd yake faruwa. Cikin halin ko in kula tace aje a sanar da jakadiya. Zuciata ta tsaya cak guri guda naji ya fita a raina sam, na sunkuyar da kaina na kassara abnd ke zuciaya wanda ya bakunceni yanzun nan. Abin haushi wai jakadiya na zuwa saita rangada guda wllh nan da nan mata suka cika dakin a ka ciccibi gimbiya wasu sukayi toilet da ita tana uban ihun zafi wasu kuma suka yaye zanin gadon sukayi fada dashi. In takaice kiki har dinki akayi mata yaji mata ciwo sosai saida tayi jinyar sati w tun daga ranar ina kula ko kallon arziki bata samu daga gurinsa. Bayan 2wks yana zaune falo mun kawo masa b/ fast yana rike da waya a hannunsa kullum haka yakeyi a she pic dinki ne ajiki yake kallo kwatsam saiga gimbiya wllh humaira idan ni yayiwa wann wulakancin ko shine autan maza na hakura dashi. Amma don rashin zuciya irin na gimbiya daga fitowarta ko kunyar mu bata ji ta ta haye kan cinyarsa tana wani kissa aiko karaf idon ta ya kai akan wayar shi tayi sama da wayar tana surfa uwar ashar tana zazzaga bala'I wai me kake nufi dani ne ko an gaya maka abinci kawai nazo ci? Kin ji fa wato ita bata ji haushin abunda ya mata ba har wani neman shi take yi Wannan yar iskan kenan bata kyale ka ba har yanzu. To wlh ga mai marta ba zan kai ka kuma shi zan ba wayar ai bata karasa ba yayi kukan kura ya amshe wayar shi ta harziko sai kawai ta fara zagin sa banza dan talaka wanda bai gaji arziki ba wanda suka yiwa sarauta haye ai da bamu san asalin angulu ba duk abunda kayi babu mamaki tunda sarautar BORE ce kuma hakkina da kake tauye man Allah ya isa..... Bata karasa ba ya juyo ya kalle mu yace duk mu fita wlh a. Falo ya. Kara yi mata wani wulakancin ya barta nan kwance yayi tafiyan shi ranar nida karima muka taimaka mata ta gasa jikin ta kamarna bata shawarar ita ma ta kyale shi mana sai kuma nayyi shuru a tunani na a tunda an kara na 2 bata bari a kara na 3 ba Bayan kwana 2 ya kira ni yace na kawo mashi tea ba madara da dankali. Na ttafi zan kai masa na ga gimbiya tace na bata wannan na hada mai wani (kiji neman. Dalili da rashin zuciya) ina cikin hada masa kashi na 2 ya shigo kicin din ganin ina aikin yasa bai yi magana ba amma da ganin shi ranshi ya baci kinsan halin mutumen naki. Da KASAITA Har ya juya zai tafi na yi sauri na duka nace *llah ya taimaka kayi mini gafara na hada maka zan kawo gimbiya ta amsa tace na hada maka wani ya yatsina fuska kamar yadda ya saba kafin yayi magana Kina iya bari na fasa maza kije ki shirya zamu je garin ku ki raka ni wurin kawar ki watakila dalilim zuwa dake ta saurareni wlh wlj humaira daga ni har shi bamu san gimbiya ta fito ba ashe jakadiya ta aika aka kira mata ta tura ta gun sarki a shaida masa abinda yake shirin yi Tayi shigewarta daki na fiti a shirye yana zaune a falo yana shirin mikewa kenan aka turo kiransa a fada nazauna a saman kujera dogari ya kalle ni ya ce harda ke ma yar rakiyan yake kira gabana ya fadi ashe tunmi ya fahimci abunda ke faruwa Muna isa mai marta ba ya fara bala'I inda yake shiga bata nan yake fita ba duk yaddake sin kare kansa amma abu ya faskara ya dinga yi masa muna nan kalamai wadanda zasu bi shi matukar bai rabu da ke ba in takaice maki magana mafarin ya ce zasu bar kasar kenan da zama don ya manta dake shi da sarki ya mutu ya zo a bashi sarauta idan kuma ya saba ko da gigi yazo naija to babu shi har abada duk wanda yake son gani yayo waya zaa tura mashi shi ni kuma aka gargade ni akan duk randana sake biye masa muka aikata hakkan to zanyi zaman bursuna na shekara 20 a gidan sarauta kwalla suka zubo mata ina kallon ta ta ce humaira wlh muna fitowa fada wuri ya smau ya zauna kawai naga ya fashe da kuka nima sai na taya shi ya kalle ni bani da saa dunia ni kuma kaddarar da Allah ya nufe ni da ita kenan to shine fa aka bamu butu kafin cikin mu a zabi wacce zaa tafi da ita a matsayyin mai aiki ranar da zamu taho ya bani takardar nan ya ce na kawo maki amma dom Allah kada kiyi kuka sbd haka zai tafi ki kawo rply na kai masa kuma zamu rinka waya da yaya zan ce ya rinka kawo maki muna gaisawa nace to tayi juyin duniya nace wlh bani da wata amsa ta gaida shi dole ta kyale. Ni Lbrn da amira tazo man dashi shi ya sa komai ta koma mini sabo nayi kuka har kaina yafara ciwo Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Subul da baka 2 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 07:12 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka kuma akace damu za a tafi wallahi yau yau dinnan na dawo wanka kawai nayi don na cika alkawarin dana daukarwa.. Da sauri na kalleta' se kuma na sunkuyar da kaina kasa. Ta fiddo doguwar takarda tace: "Gashi yace dan Allah kada kiyi kuka' kiyi masa wannan alkawarin" Murmushi kawai nayi idona ya ciko da kwallo' tayi saurin kawar da fuskarta'sannan ta kara mikomin takarda ambulan doguwa. Ta mike' zan tafi akwai labari' amma se zuwa jibi idan na dawo' gobe zanje Karkasara shi yasa. Nayi murmushi tare da mikewa na rakata' rakiya mai nisa har kusan lungun gidansu sannan na koma. inna nacan tana wanke waken awarar gobe' su Aisha na taya ta na shiga dakia kagare inji takardar abinda ta kunsa' haka kawai jikina ya ba ni maganace mai dauke da kwanciyar hankali domin na tabbatar yana sane da halin da na shiga. Tun kafin na fara karantawa na qurawa rubutun ido, yadda yayi shi wara wara yaddazan fahimta, nace "Bismillla" "Gimbiya Humaira" Na runtse ido ina sauraton yanayin furtakalmar acan baya da yayi' wanda ya kasancemasa tamkar" SUBUL DA BAKA" "ina roqonki da girman Allah ki daure ki cije kada kiyi ma rubutunnan kuka, kiyi mini wannan alfarmar please! Humaira ba se na fada miki ba na tabbata kin fahinci kaunar da nake miki, na da de ina mafarkin samun macen da nake muradi kafin Allah ya hadani dake, amma rashin sa'a se muka sami banbancin ra'ayi damahaifina. Nayi duk iya kokarina in tallabomatsalar amma abu ya faskaradomin yayimini FURUCIN dana tsorata da shi, furucin daya tsoratani kuma ya firgitani. Don haka ina rokonki kiyi hakuri mu dauki abin nan kaddara duk da na fahimci cewa ni ban kwanta maki arai ba humaira bana son farida bana kaunarta wannan cutar kadai xata galabaitar dani soyayyarki kuma takaini lahira mu yafewa juna domin gobe xamu bar kasar nan xuwa australia a can xamu xauna dindindin inji sarki harsai bayan ransa in dawo in karbi sarauta ga cheque dina nan na banki duk nayi signing ki rinka fidda kudi kuma ki koma makaranta idan xakiyi aure ayi miki kayan daki insha Allahu xan kawo maki xiyara anytime. Kuka y hananani karasawa nayi nayi kamar raina xai fita inna ta shigo da sauri tana salati dakyar na bayyana mata wani abun shiru tayi tare da ficewa waje amma a zihiri na ga ranta ya baci bata yi mini maganar ba sai da daddare ina zaune saman abin sallah na hade kaina da guiwa cikin wani yanayi idanuna ina jin su tamkar garwashin wuta kirjina kuwa kamar an dora man dutsen dala Humaira inna ta kira sunana Na amsa naam murya ta kasa kasa Yanzu kinfi son ganin tunon asirin rayuwan mu akan rufuwan sa Nayi shuru ban amsa ba Ashe ba zaki hkr ba? Kwalla suka zubo mani nace wlh inna ba wannan ne damuwa ta Na bata lbrn takardar da aka kawo mun da abunda amira tazo man dashi ta harzuka to ina abunda ya dame ki dasu bance ki manta ba kuma nima ba zan taba mantawa dashi ba amma wlh ki cire maganar soyayya Yafi karifin ki humaira ba mijinki bane kiyi nesa da soyayyar wahala idan kika kuskure sai gimbiya tafiki kwanciyar hankali nayi saurin kai kaina kasa ina sujjada "Ya Allah kana ji Allah ka yi mini maganin matsala ta Allah kai ka haifar soyayya a zukatan mu Allah kayi magana maganin ta bayan kwana 2 inna tace gaskiya nima na goyi bayan ki koma makaranta amma baxamu taba kudinsa ba Sbd haka saimu shirya gobe muje Govt college muji idan zasu mai daki. Hakan kuw akayi ga mmkina aka sakani SS3 kuma saura 3mnths suyi exams na dage da karatu wanda rabinsa tunani ne. Dr ibrhm kuwa tun ina shareshi harna fara sakin jiki dashi sbd fadan inna kada nayi saki na dafe a dinga nunani nayi kwantai har an fara min shaidar me kudi nakeso, Inna ta buga tsaki sannan kiyi kaffa kaffa da masu zuwa wurin ki domin iyayen ki sunyi mugun kudiri akan ki maganar karatu kuma sun ce basu amince ba matukar kika ci. Gaba da zuwa wlh komai suka yi miki don kanki Ko don ina cikin damuwa? Sai maganar bata wani dame ni ba idan Allah ya nufe ni da ilimin bokon nan na tabbatar da kudin da ya bamu zasu ishe mu har zuwa wani lokaci ko da bamu sanaa balle ma muna awara ga cek bayan sati 2 na dayaye dr ibrahim yaci gaba da zuwa kusan kullun kwatsam rannan yazo ya ce zai tafi karo karatu an tura shi singapore kuma shekaru 4 zai yi inna ta nisa ta ce to Allah ya tabbatar da alkhairi amin ya fidda sabuwan waya mai kyau da tsada ya bani yace inna ga wannan zamu rinka gaisawa kusan kullun don Allah tace to bata angode kawai raina ya baci watau ya tabbata inna bata son tunda kiri kiri ta hana ya bani waya ya miko mani dalleliyar blackberry sabuwa dal na amsa fuskata babu yabo ba fallasa, Inna ta hararoni nayi kmr ban gani ba yana fiata ta jefoni da murfin kwano zaki bishi kuyi bankwana ko kuwa? Na mike idanuna cike da kwalla na bishi yana tsaye jikin katanga ya hada kaida bango mostina kawai yaji da alama ni din yake bukatar gani yayi saurin dagowa idanunsa sun dan yi ja abnd ban taba gani ba nayi saurin kauda kaina sbd wani abu da naji yana bakuntar zuciata ya dubeni yace humaira zan tafi amma bakin cikina bansami wata kwakkwarar amsa daga wurinki ba. Jikina yayi sanyi zuciata tayi kunci haka kawai nakasa fahimtar abnd ke damuna. Ya kara kwantar da murya na kasance ma'abocin son zama da mace kwaya 1 a rayuwata amma burina ya rushe lokacin da nayi katari da matar da muka sami babbancin akida. Wllh humaira ba don ina kaunarki nake kushe matata ba na rantse miki banajin dadinta ko alama. Kadan daga cikin abnd tayi min kuma shine mafi karanci data mari mahaifiyata agabana...... Da sauri na kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace kuma ta hanani na saketa, ki taimakeni ki sanar dani matsayina a wurinki wllh humaira bazan taba wulakantaki ba magnrki taje ko ina a danginmu mamana kullum sai tayi zancenki babana kuma ya rasu. Kuma nayi promise bazan hadaku gida 1 ko unguwa 1 ba believe me humaira pls. Tunani yazo min idan nayiwa ibrhm wulakanci koban amsa masa ba banyiwa kaina ba kuwa? Wa nake jira wa kuma nake dashi a hannu? Idan har abnd yake fada gsky ne ai nayi dace amma matsalr nayita jira har 4yrs? Kamr ya karanci zuciata naji yace kada kiji nace 4yrs ki dauka ko zaki ta zaman zuwana ne a'a ISA duk year zan dinga zuwa inaso ki tabbtr min da mgnta ne ni kuma a yau din nan zan gabatar da maganata zan bar komai in yaso da nazo hutu ayi biki idan da hali mu tafi tare if nt saina barwa broda na komai daga baya sai ki bini idan kuma kina ganin akwai matsala donAllah ki sanar dani. Nayi shiru ina nazari shin idan nace baiyi min ba wa zai min a dunia? Ko haka zan zauna ba wan ba kanin? Kirjina yayi min nauyi idanuna suka ciko da kwalla har yaushe zan manta da yarima a rayuwata? Ko in baki tym muyi magana a waya? Nayi saurin daga kai na alamar eh. Yayi murmushi to shikenn sai munyi magana. Na daure nace Allah ya kiyaye ya bada sa'a. Yanayinsa ya nuna min yaji dadi nagode humaira thank U so much for ur prayers, na yi murmushi na juya na shiga gida. Ko zama banyi ba inna ta hau fada wllh humaira banajin dadin halayenki da kika tsira har yaushe zaki daina tunanin yarima a rayuwarki? Wllh inna ni..... Zaki kaffara don kin isa yinta kibar rantsuawa. Wannan kunge-kungen da kikeyiwa wann bawan Allahn na menene? Kwata kwata kin daina sauraron kowa, wallahi kiyi nesa da kanki, iyayenki sun hanaki karatu saboda wata manufa tasu daban, shin auren kuma sai kihana kanki wanda shine mutumcin kowace ya mace? Humaira asirinmu kike son tonawa? Kin mance abinda mahaifinki ya fada akan soyayyarku? Gabana ya fadi saboda yanayin yadda naji inna tayi maganar kamar zatayi kuka. Kinyi dai dai, kuma Allah yabaki sa'ar kin sauraron ibrahim, yaron arziki bna ki tunanin Allah ne yakawo miki madadin....? Tunda shima gwargwado yanada kyawunsa? Ilimin nan yana dashi, sannan ga arzikinsa na rufin asiri? Anya ba maganar mutane bane Humaira kwadayi ke fizgarki ba? Haba inna..... Rufe mini baki mara kunya to me kike nufi in ba kwadayin SARAUTA ba? Ga babanki Auwalu can yadauki alwashin sai ya cusa mana bakin ciki ni da ke, bansan abinda yake nufi ba, yana korafin jin zafin yayansa na auren masu kudi, shiyasa kike wannan sakarcin, to yasan maganinmu. Ko dan wannan ma bakya yiwa kanki fada ba? Kiyi fatan Allah ya baki nagari mai kaunarki da danginki.. Ta kawar da fuska amma ba komai kije kiyi abinda kika ga dama.. Na sauko kasa, Inna kiyi hakuri, in sha Allah zan sanar da Ibrahim cewa na amince da shi... Da sauri ta kalleni to shikenan ya wuce Allah yamana jagora nace amin... Kwalla suka zubo min narasa na menene ni kuma haka Allah ya taaro mini rayuwa?? Baniga karaty baniga aure tunda shi Ibrahim......koda yake yace idan nayarda zai dawo a yi biki. Sallamar yaro muka ji inna tace ya shigo. Wai humaira ta zo anbugo mata waya daga kasar waje Ina jin haka na miqe zumbur na . gane ameera ce. Ya miqo man lokacin da muka isa nida aisha. Na koma gefen shagon kusada bedi na kanga a kunne 'Hello' amira kun isa lafia? Lafia qalau, baki lafia ne naji muranki kamar kinyi kuka? Na girgiza kaina kamar tana kallona, lafiata lau ina fama da mura ne. Nima kuwa nayi waya. Don Allah? Ta fada tana murna. Walhi kuwa zan sanya a turo maki lambar se mu dinga magana da tawa. Yauwa to yayi kyau nagode.nace nima nagode qawata se na kiraki. Haba yaya me ya hanaka qarasawa gdan? Yayi murmushi hakanan. Na miqa masa wayata turamata lambata nima ka sakaman tata. Yace to humaira manya wannan irin babbar waya? Nayi murmushi 'Ni don Allah gobema idan kanada lokaci zan zo gdan kadan gwagwada mani yadda take kasan sabon shiga, kuma ka turamani qur'ani da adu'o'i. Yayi dariya yayi ustaziya karfe nawa zaki shgo? Lokacin da kake nan, ni gobe ba inda zan je. Nace to zan shgo wajan goma zuwa sha daya. Muna bin hanya zamu koma gda wayar ta hau kuka nayi saurin latsawa na dauka a tunanina amira ce dan ko suna ban duba ba Assalamu Alaikun kinga lambar ta shigo? Yayi murmushi wacece har an fara rabawa qawaye lamba? Nayi jim, to me tafiya ne ya bugo yace maki gashi a cikin jirgi, nace au walhi ban duba bane kayi hakuri, Allah ya saukeku lafia. Amin ya Allah humaira

Chapter 6 of 11