cikin masarauta duk wanda aka sake samu da laifi irin wannan tabbas hukuncin sa kisa ne, ba zamu yarda da zalunci da keta haddin d’iyoyin mu mata ba, abu na gaba Mata mun sabunta musu suturarsu ina nufin y’an mata da suke yawo ba mayafi daga cikin bayin mu, a yanzu masarauta Zata raba su kayan da zai rufe jikinsu sink’if ba tare da an ga ko da yatsan k’afarsu ba madadin wancan kayan da suke sakawa da yake bayyana surar jikinsu yake kuma banbanta su da iyayensu, a yanzu masarauta zata mayar da suturarsu irin ta iyayensu don gujewa ya’duwar Fasadi a cikin Masarautar Gabas. Duk Macen da aka sake samu an mata fyad’e kai tsaye zamu jingina laifin ne kan Iyayenta akwai kuma mummunan hukunci da zai biyo kanta da iyayenta gaba ‘daya, don haka ya zama dole gareku Iyaye ku saka ido akan d’iyoyin ku mata, ba mu amince da sake ganin Mace bayan sallar Magriba ba ko cikin dare a waje dafatan zaku kiyaye.” Hukuncin sosai ya yiwa iyayen da’di don duk masu y’ay’a mata a masarautar zuk’atansu a cikin fargaba da taraddadi suke, don haka suka dinga godewa Sarki Mukhtar dafatan gamawarsa lafiya tare da samun Magaji mai albarka. Wannan addu’ar ita ta bak’anta ran wasu daga cikin mutanen wajen musamman y’an Uwansa da suke Uba d’aya a zuciya suka dinga amsa Ba Ameen ba, In sha Allah har gaban Abada Sarkin Gabas ba shi da Magaji. Haka taro ya tashi zuk’atan Iyayen yara cike da farin ciki a gefe guda kuma masu aikata laifin suka k’ullaci Sarki tare da ji a zuciyarsu ba ta yarda za’ayi su fasa aikata hakan tunda shima yana daga cikin shara’din da Bokansu ya gindaya musu in dai suna son wani daga cikinsu ya zama sarki ko shi ko ahalinsa to dole sai sun bi wannan hanyar ta keta wa y’an Mata mutuncin su, sun kuma ji suka bi kuma suka sakankance da maganar Boka GAKSIYA ce!
_______\____
Wannan shine ya d’aga hankalin iyayena.
Tunda suka koma gida Inno da Babani suka fito da ni da suka b’oye a d’aki can bayan Gadonsu na k’arfe, Inno ta saki ajiyar zuciya tana dubana hankalinta a tashe,Tun bayan hauhawar lamarin fya’den suke killaceni a ‘daki basa barina na je ko ina. Tsoro suke ji sosai basa son wani abu ya same ni. Inno ta shafa kaina tana fa’din “Ya Allah ka kare min Fatu daga wa’dannan Azzaluman.” “Idan kin tsaya tsayin daka akan tarbiyyarta tabbas Allah zai kare miki ita.” Babani ya fa’da Idanunsa a cikin na matarsa Inno “Ban amince da fitar Bayan Magariba kamar yarda Sarkin Gabas ya ce kin ji ko Fatu? Don ya rantse duk wanda aka sake samun an yi wa y’arsa fya’de to hukuncin kisa ne a kansa da y’ar tasa.” Wani irin bugu k’irjina ya yi na d’ago a tsorace ina kallon su da suma suke kallona. Inno ta d’ebo bak’ak’en kayan da aka basu a fadar ta ce “Daga yau wad’annan su ne kayan sawarki Umarnin Sarkin Gabas akan duk wata Mace data balaga a cikin masarautar nan, ba a amince da cire koda nik’ab d’in fuskarta ba ne.” da sauri na karb’i kayan ina jin da’di jin tsorona na yawaita ta yarda har hakan ya kasa b’oyuwa a cikin idanuwana da fuskata. Tun bayan da aka wa k’awata fya’de da ya yi sanadiyyar rasa raina nake cikin wannan yanayin na tsoro da firgicin, ko muryar namiji na ji na y’an gidanmu samun kaina nake da rawar jiki da na zuciya, saboda ni Yarinya ce da ban wuce shekaru sha bakwai ba ina da kamala da nagartacciyar Tarbiyya da Inno bata min wasa da ita, nutsuwata ta samo asali ne ta yarda Inno take Jana a jiki take nuna min abu mai kyau da marar kyau, tun kuma a k’ananun shekaru na Inno ta tsoratar da zuciyata ta hanyar nuna min kada na yarda namiji ya rik’e min hannu da zarar na amince ciki zan samu na haihuwa duk wacce kuma ta sake ta yi cikin shege a Masarautar Gabas hukuncinta kisa ne ta hanyar d’aurin rai da rai. Don haka da wad’annan abubuwa suka faru na fi kowa shiga tashin hankali.
Sai dai kana taka Allah na tasa wata rana na dawo daga wajen matar sarki da ake kira Fulani Saddik’a kasancewar ni nake kula da kitchen d’inta don kam Inno ta min horo na girki ba na wasa ba babu girkin da ban iya ba. Cikin duhun Magriba nake tafe sanye sunk’uf da irin shigar da aka amince mu yi a masarautar, Da Suwaiba muke tafiya ranar kuma Suwaiba bata jin da’di bata zo ba daidai wajen duhuwar bishiya na ji an yi sama da ni, ina k’ok’arin kurma ihu na ji an shak’a min wani abu a hancina wanda daga nan ban sake sanin inda kai na yake ba, sai farka wa na yi na gan ni a wani d’aki mai tsananin duhu, a kuma lokacin na dinga jin maganganu k’asa k’asa da dariya mutane suna fa’din mun gama aikin mu saura jira da bayyanuwar cikin idan komai ya kankama zamu kasheta mu d’auki d’an da zai zama Sarkin Gabas ba tare da shi Sarkin ya san shine Ubansa ba mu za mu yi rainonsa zai kuma zama abin tunk’ahon mu! Suka saki shewa a tare.
Ba su sake bari na na sake lek’a waje ba, tun bayan da suka fahimci ina da shigar cikin da yake duk bayan wata guda suke aunani. A daren da za su min theatre su cire cikin ni Kuma su kasheni a daren na haihu bisa jagorancin wasu mutane da ban san ko su waye ba na haifi d’a namiji su kuma
Abinda na lura d’an suke buk’ata fiye da wad’ancan mutanen,su suka taimaka min suka fito da ni cikin gari suka umarceni da na gudu na ceci raina kafin mugayen su cimmani. Sai dai wani ikon Allah ina zuwa wani k’auye sai na fara wata nak’udar inda anan na haifi Jariri Mujaheed bisa taimakon wasu mutane a k’auye. Cikin dare kuma na gudu inda anan na ha’du da Baffa ya taimaka min.. wannan shine abinda na sani Wallahi ban san ya aka yi na samu cikin yaran nan ba…” Ta fa’da wani kuka na sake kece mata. Zuwa lokacin Umma da Najwa ma kukan suke suna tunanin girman lamarin da ya zarce tunaninsu. Sun da’de a haka kafin Umma ta d’ago ya share hawayenta ta ce “Yanzu Nenne ta yaya kike tunanin za’a gane Uban cikin nan?”
JIKAR NASHE✍🏽
Book 1 ne free Book 2 is 500 via 2118666253 UBA sai a tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387.
Tafiyar mai zurfi ce kuma an kusa gama na bati ki biya ki huta da takaici.
KUDIRAR ALLAH
13.
NAZEEFAH SABO NASHE.
Nene ajiyar zuciya kawai ta saki idanunta cikin na Umma tana sake share hawayen da yake zubo mata ba kakkautawa ta ce “Allahu a’alamu Umma Wallahi ba zan ce ba, abu d’aya nake so ku min ku rufa min asiri kada Baffa ko Jaheed ya san wannan maganar.” Umma ta girgiza kai tana fa’din “Ai hakan ba zai yiwu ba Nene ta yaya kike tunanin za’a samu mafita idan su Baffan ba su sani ba? Saninsu Ai ina ga shine abinda ya dace.” Nene kuka ta saka sosai hankalinta ya tashi ba ka’dan ba don ta san idan har Baffa ya sani to kai tsaye za’a tafi masarautar wanda hakan yake nufin da kai tsaye magautan za su iya k’aryata abinda ta ce kuma kisa shine makomarta. Ganin tashin hankalin da ta shiga ne yasa Najwa sakin ajiyar zuciya tana kallon Umma ta ce “Umma mu rufa mata asirin zuwa sanda Allah zai yi hukuncinsa.” Umma ta yi shiru a zuciyarta tana son rufa wa Nenen asiri sai dai wata zuciyar tana tunanin tona asirin shine abinda ya dace. Ta jijjiga kai tana kallon Najwa yarinyar da ta gasgata da lamarinta tun yarintarta ta san tana da wata baiwa mai girman gaske wanda Allah ne ka’dai ya barwa kansa sani a ranta ta dinga tunanin da ace Najwan wata k’atuwar budurwa ce da kai tsaye zata turata masarautar wajen binciken asalin yarda aka samar da cikin sai dai a yanzu ta yi yarinta ta saki ajiyar zuciya tana furta “Zan amince da abinda kika ce, sai dai daga yau Najwa ina son ki saka a ranki kina gama secondary zaki tafi Garin gabas yin karatun Jami’arki a can daga nan ne zamu san yarda kika yi kika shiga masarautar gabas kai tsaye koda da niyyar aikatau ne ba don komai ba sai don ki binciko mana asalin lamarin ta hanyar baiwar da Allah ya baki, na san zaki iya In sha Allahu, a yanzu dai zan rufa asirin zuwa lokacin da zan banka’da shi da kai na.” Gaba d’ayansu suka amince da shawarar Umma a wajen Nene shekaru uku kamar yau ne ta shafe shekaru sama da ashirin da biyar saka ye da sirrin a ranta balle wannan y’an shekarun ita kanta a zuciyarta tana jin Najwa zata iya tana da yak’i ni da fata a kanta. Umma ce ta mik’e ta fara fita kafin Najee ta bi bayanta suka bar Nene a zaune tana jin wani sanyi a zuciyarta duk nauyin da zuciyarta ta yi ya tafi kamar d’auke war iska, fitar sirrin ya jawo mata samun nutsuwar zuciya da sauk’in ciwon kan da yake addabarta kullum. Sai dai zuciyarta ta koma tunanin yaronta Murad ko a wani hali yake yanzu ina suka kai shi shine abinda ya tsaya mata a cikin ranta. Ta d’an lumshe ido hawayenta na zuba tana tunanin ranar da ta d’au Murad a cikin showel kamaninsa har a lokacin ba su b’ace mata ba Suna nan zaune ra’dam a k’wak’walwarta kamar ma yanzu abubuwan suke faruwa. Mutane na biyu da take son gani sune Mahaifinta Inno da Babani suna raye ko basa raye suma bata sani ba, abu d’aya ta sani ta san suna cikin tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya tun bayan b’atanta, tunda ba su sake ganinta ba tun sanda mutanen suka d’auketa.
__________________
Baffa da Magribar fari ya shiga gidan, b’angaren Umma ya fara shiga tana zaune da ita da Nene da ta kasa sakewa balle ta bayyana a yanzu bata cikin haukan, duk da shi Baffan bai sani ba, sai dai gaba d’aya siffofinta sun canja zuwa sanyin hali k’warai da gaske. Gefe kuma Najee ce take ta gyara dinning inda suka ci abinci. Baffan ya amsa gaisuwar da suka masa kafin ya zaro waya a aljihnsa ya kira Inna Sa’a k’anwarsa da take bin sa tana d’agawa ya ce “Sa’a kin zo ne?” Sa’a ta sanar masa tana harabar gidan. Ya kalli Umma yana furta “Tashi ki je ga Sa’a can tazo za ku kai Najma gidan aurenta.” Umma ta d’ago da sauri tana kallonsa sai dai bata hango alamar wasa a tattare da shi ba, asali ma fuskar tasa a ha’de take sosai alamar baya son musu ko gaddama a cikin abinda ya ce. Umma ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa idanunta akan Nene da itama tashin hankalin da take ciki ya kasa b’oyuwa akan ta ta fuskar. Baffa yana fita Umma ta kalli Nene ta ce “Addu’a zaki musu Nenne da fatan alheri tunda dai Baffa a wannan gab’ar ba zai ji bari ba, idan banda haka sam ban hango ta inda lamarin nan ya dace ba Wallahi.” Nene ta saki ajiyar rai a fili ta furta “Allah ya ka’de fitina Umma sai dai ki jawa d’an naki kunne duk abinda zata yi don Allah kada ya kulata ta ci darajar Baffa.” Umma ta ‘d’aga kai kawai tana ficewa sanye da hijabinta. Najee ta bi bayanta don son ganin artavun da za’a yi wajen fita da Najma daga gidan don tsanar da ta yiwa Jaheed abu ne da kowa ya sani.
Umma cikin sakakkiyar murya ta yi sallama, suka amsa mata a ciki idanunsu a kanta don jin abinda ya kawota. Mamaki ya kama Umma ganin Najman zaune ba alamun ma ta san za’a kai ta gidan Mijin don kaya ne na barci a jikinta gashinta ko gyaran arziki bai samu ba. Ganin ba zasu tanka ta ba don Mahmeey sai cika take tana batsewa yasa Umman zama tana furta “Ashe amaryar bata shirya ba? Amma Baffa ya jajib’o ni nazo na tafi da ita?” Da sauri suka d’ago suna kallonta Mahmeey data kasa hak’urin turirin sa zuciyatta ke yi ta ce “Ki tafi da ita gidan Uwar wa?” Umma ta d’ago cikin mamaki tana kallonta sai dai ta kawar da b’acin ranta ta ce “A tafi da ita gidan Mijinta mana.” Mahmeey ta zabga mata harara tana sakin tsaki ta ce “Ki je ki gayawa Mijin naki ba inda zata je wallahi, na shiryawa duk abinda ya shiryawa amma y’ata ba zata gidan wani matsiyaci d’an mahaukaciya ba.” Umma ta ha’diye yawu mai d’acin da ya tarar mata ta ce “Sai dai ki d’aga waya ki sanar masa.” “Yanzu kuwa” Mahmeey ta furta tana zaro wayar ta “Idan banda munafunci me yasa baki aura masa taki y’ar ba?” Umma ta saki murmushi a zuciyarta tana tausaya musu wannan fa shine abinda hausawa ke kira rashin sani ya fi dare duhu. Da sun san waye Jaheed ta tabbata sai sun fi kowa Farin ciki da auren. Baffa na d’agawa Mahmeey ta fara masifar da ta saka shi katse wayar ya kuma nufo sashen ransa a b’ace. Yana jin a wannan gab’ar zai iya sakin Mahmeey idan bata bi umarninsa ba.
Daga yanayin fuskarsa Mahmeey ta san ba shi da niyyyar saurara mata kamar yarda itama bata da niyyar sarara masa. Ya kalli Najma a zafafe ya ce “Ke! Mik’e Ki wuce mu je, idan kuma kin k’i a bakin auren uwarki.” Najma ta d’ora hannu a kai zata zunduma ihu Mahmeey ta dakatar da ita “Tashi ki je Najma, amma ba wai na amince da hakan bane Saboda ina tsoron saki akwai dalili na Wallahi ka saka a ranka sai ka yi kuka da idonka a kan wannan auren kuma ban amince ki ragwa d’an mahaukaciya ba kin ji na gaya miki?” Ina Najma ta saurara kuka kawai take cikin tashin hankali tana jin zata iya aikatawa Jaheed komai a cikin daren nan ciki kuwa har da kisa idan ta kama. Don haka ba abinda take sai aikin ajiyar rai saboda yarda zuciyarta ta cunkushe da bak’in ciki matsananci.
Ta shige gaba ko mayafi babu a jikinta sai hular kayan da suke jikinta na barci. Nasma ce ta yi saurin binta da hijab ta zura mata itama kukan take taya y’ar uwarta.
Baffa ya bi bayanta da kallo yana fatan abinda ya k’ulla d’in ya zama alheri gareta da su ma
Gaba d’aya a rayuwa, so yake ya nuna mata shi d’an Adam ko yaya yake ba abin wulak’anta wa da tozarta wa ba ne, mutum
Yana da kima da mutuncin da Ubangiji da kansa ya ce ya karrama shi idan banda haka shi da kansa bai hango dacewar Najma da Jaheed ba. A zuciyarsa ya bita da addu’ar saka albarka da samun hak’uri da juriya a zuciyarsa yana ji a ransa gatan da zai mata kenan na aura mata nagartaccen mutum irin Jaheed.
Motar tsit daga Umma har Inna Sa’an babu mai magana sai kukan Najma da ya cika musu kai. Aka tsaye a babban gidan Jaheed da ya gina don zaman aurensa da Khaireey ashe ba ita ce zab’in da Allah ya masa ba. Najma da k’yar ta fito daga cikin motar idanunta akan gidan duk da kyansa da tsaruwar sa ya burgeta matuk’a ainun sai dai k’iyayyar mamallakin gidan ta shafi gidan ta inda shima ta ji tana masa k’iyayyar. Ta runtse idonta tana sake damk’e hannunta da k’arfin gaske kafin ta sake runtuma ihu.
Su Umma suka yi yo kanta da sauri suna tambayar lafiya? Bata amsa ba illa bin su da ta yi da kallo mai cike da nuni da zallar raini. Ba su bi ta kanta ba suka shige parlourn suna yaba kyau da tsaruwarsa komai a kam male tsaf da shi ba wani tarin hayaniya kamar yarda Jaheed d’in ma ya zama mutum mara hayaniya. Suka gama zage gidan kafin su saka k’afa su fice suna mata fatan alheri. Harara ta bi su da ita a zuciyarta tana jinjina lamarin gulma da kinibibinsu. Kamar wacce aka tsikara ta mik’e ta shige kitchen wuk’a ta fito da ita k’arama mai kaifin gaske ta soke a jikin aljihun wandonta sannan ta koma ta zauna tana sake risgar kuka tana ji a zuciyarta abinda zata aikata shine daidai.
Jaheed kuwa tun bayan da ya fito daga wanka ya rasa nutsuwar zuciyarsa. Zama ya yi kawai a gefen gado jikinsa bakomai sai rigar wanka wani irin alhini ne a ransa na rabuwa da gida ya je ya komawa rayuwar da bai san makomarta ba. A idanun Najma yake hango muguwar tsanar da ta masa. Ya saki ajiyar zuciya yana tuno Khaireey da burin da suka ci a duk sanda daren aurensu ya zo, ashe ba zai tabbata ba ashe duk abinda suke mafarki zai zama shafe labari shuni. Ya lumshe idonsa sai ga saukar zazzafan hawaye akan fuskar sa. Knocking d’in da Faruk ya yi ne ya dawo da shi cikin nutsuwa da hankalinsa murya a raunane ya ce “Am coming Faruk.” Faruk daga waje ya amsa “Okay ka yi azama dare yana yi ga friends duk suna jiranka.” To kawai ya ce ya cigaba da shafa mai a jikinsa kamar baya so. Kafin ya samu sassauk’an yadi ya saka ya fice da d’an sauri. Faruk ya shigo ya ja masa akwatinsa zuwa waje. Sai dai suna isa harabar da yaga dandazon abokansu bai san sanda ya ja hannun Faruk da sauri ba suka yi baya. Kallo guda Faruk ya masa ya gane akwai matsala. “Wad’annan mutanen Faruk bai kamata mu tafi da su ba, ka san dai yanayin amarayar tawa sai a hankali so ina ga har kai ma na sawwak’e maka zan je da kai na kawai.” Faruk ya d’aga kai shi da kansa ya gamsu da abinda Jaheed ya ce don haka ya juya suka isa gurin abokan cikin azancin harshe suka sallamesu, sannan Faruk ya ja hannunsa wajen Baffa da yake zaune a gefen gidan wajen garden yana ganinsu ya saki murmushin dole ha’de da nuna musu gefensa suka zauna. Jaheed zai fara magana Baffa ya d’aga masa hannu. “Kada ka ce komai Jaheed, nima na zan ce ba Allah ya yi miki albarka ya ka’de dukkan fitina.” Jaheed ya amsa a hankali zuciyarsa na sake k’arfafa mutunci da girman Baffan a idanunsa. Jikinsa a sanyaye ya yiwa Faruk sallama sai dai bai iya ya shiga cikin gidan ba yarda zuciyarsa ta yi rauni baya jin zai iya ganin mahaifiyarsa da Umma ya san k’ara masa wani nauyin za su yi. Suka yi sallama da Faruk ya shiga motarsa zuwa gidan da kai tsaye zai kira gidan Khaireey don komai na cikinsa ita ta tsara ashe ba zai zama mallakinta ba.
Yana parking zuciyarsa na sake k’arfafa bugu mai k’arfin gaske, da k’yar ya sarrafa kansa zuwa cikin gidan. Bakinsa d’auke da addu’a ya murd’a key d’in babbar k’ofar da zata sada shi da cikin gidan. A yarda su Umma suka barta ya sameta fuskarta jik’a da hawaye. Tana ganinsa ta mik’e a zafafe tana masa wani kallo da kai tsaye zai kira na raini. “Kai d’an mahaukaciya idan ka cika kai d’an ta ne na gaske ka sake ni yanzu.” Ya juya ransa a b’ace yana sauke idanunsa a kanta da suka canja colour saboda tsananin b’acin rai. “Kalleni da kyau k’arya na yi ba d’an mahaukaciyar ba ne?” Wani irin taku ya yi ya isa gabanta cikin b’acin rai ya jawota da k’arfin gaske ya cillata saman kujera kafin ya bita a zafafe ya danne a hakan yake son keta mata mutuncinta don ya nuna mata ba kowa ba ce ita, ji ta yi kawai ya ja rigarta da k’arfin gaske hakan ya bata damar zaro wuk’ar da ta tana da a jikinta ta d’agata ta maka masa a wuya…..
JIKAR NASHE✍🏽
KUDIRAR ALLAH..
14.
NAZEEFAH SABO NASHE…
Wani irin runtse ido ya yi saboda zafin kartar wuk’ar, sai dai hakan bai saka ya fasa abinda ya yi niyya ba, ta wannan hanyar ka’dai zai hukuntata ya mata saduwar wulak’anci sai ta san akwai banbanci mai girman gaske tsakanin Mace da Namiji. A zafafe ya yaga ragowar sutirar da take jikinta bai bi ta kan albarkatun jikinta ba don ba so ne a gabansa ba. Da wani irin k’arfi ya shigeta ba tausayi bakomai. Duk da ihun da take bai sarara mata ba saboda idan tausayinta ma ya bijiro masa sai wa’dancan munanan maganganun su danne tausayinta a ransa.Son ransa ya yi mata duk da ya sameta a budurwa bai hanashi yi mata kusanta mugunta ba. Tun tana ihu har ta sume masa. Ya mik’e yana gyara jikinsa kafin ya d’ebo ruwa ya shek’a mata. Idanunta na bu’dewa suka sauka cikin nasa da yake mata kallon k’urilla tsanarsa mai girman gaske ta sake bijiro mata sai dai bakinta a wannan karan ya mutu murus ba zata iya masa rashin kunya ba. Jaheed ya saki murmushi yana murza yatsun hannunsa ya ce “Gobe ma ki sake maimaita raininki a kai na Wallahi sai na miki abinda ya fi wannan.” Daga haka ya wuce ya barta a kwance cikin azabar zafi da ra’dad’i mai shiga kwanya, kukan ma ta kasa yi ga shi ta kasa tashi saboda yarda take jin jikinta kamar ana zuba borkono da wani irin azabar zafi mai shiga kwanya. Kukan da take tuni ya d’auke wata irin tsanarsa ce take sake cin zuciyarta. Tsawon mintuna tana kwance ta kasa mik’ewa sai da k’yar ta dafa kujerar ta mik’e cikin tafiyar tata tata ta nufi wata k’ofa da take kyautata zaton bedroom ce. Sai da ta shiga ruwan zafin da ta tara sannan wani kuka ya zo mata mai k’arfin gaske da ta tuna shikkenan Jaheed ya amshi abinda take tak’ama da shi, abu guda da yake ci mata rai yarda ya mata saduwar rashin mutunci kamar wata dabba. Ga shi ya gama gane jikinta don fatafata ya yiwa kayan ta. Ji ta yi ba abinda ba zata iya aikata masa ba, yau dai ya yi escaping amma next target d’inta ba zata yi loosing ba In sha Allah.
Sai da ya shiga toilet sannan ya dinga jin jiri na d’ibarsa da sauri ya kalli gefen wuyansa a mudubi tsoro ne ya kama shi ganin yarda jini yake malala a wuyansa, idanunsa suka fara lumshewa da sauri ya fito tun kafin ya kai ga sumewa ya kira Faruk a waya. Faruk yana d’agawa ya sanar da shi yazo gida yanzu ba shi da lafiya. Gaban Faruk ya fa’di sosai da sauri ya fito daga gidan da yake ba su da nisa sosai ya shiga motarsa zuwa gidan Jaheed d’in. Ko kafin zuwan sa Jaheed ya galabaita iya galabaita ya dai samu ya d’aure wajen da yake zubar jinin. Yana ganin missed calls d’in Faruk ya d’aga murya da k’yar take fita ya ce “Faruk shigo ciki ba zan iya tafiya ba jiri nake ji.” Wani irin shock da fa’duwar gaba suka samu Faruk ko kashe wayar bai yi ba ya danna kansa cikin gidan. Direct Master bedroom ya shiga inda tun daga bakin k’ofar ya fara ganin jini. Zuciyarsa na bugu ya k’arasa cikin d’akin yana k’wala kiran “Jaheed Hasbunallah me ya faru?” Numfashinsa sama sama yake fita don haka ba zai iya amsa shi ba. Faruk ya kama shi da sauri ya Goya a bayansa suka fita bai bi ta kan Najma ba da bata san ma sun fita ba tana can cikin tafasa da d’acin zuciya ji take kamar ta kashe kanta don tsananin bak’in ciki da takaicin irin saduwar da Jaheed ya yi mata ga gane mata albarkatun jiki da ya yi.
Kai tsaye asibitin wani amininsu da suka yi makaranta tare ya kai shi bayan ya masa waya ya sanar da shi. Don ya san idan har ya kai shi wani asibitin sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 16