Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamata ganin yarda yake da tarin followers fin million d’aya. Ashe Jaheed celebrity ne bata sani ba? Ta shiga comments d’insa inda ya yi posting wani pic d’insa da ya yi masifar kyau ba zata manta ba pic d’in da sallah ya yi shi don ta tuna sanda ya saka shaddar, gani ta yi y’an mata suna ta furta wow! Wow! A comment majority sun kasa hak’uri har da masu cewa check your dm sir. Da sauri ta wurgar da wayar ta kifa kanta a pillow ta saki kuka mai ratsa zuciya. ****** Jaheed kuwa zan iya cewa farin ciki da yake ciki a ranar ji yake ba na biyunsa, don haka cikin fara’a da yalwar murmushi yake amsa gaisuwar abokansa. Haka aka gama hotuna abokan su ka watse bayan Faruk ya sanar musu gobe akwai kai amarya Suna buk’atar su zo su musu kara. Sai sannan suka samu damar shiga cikin gida shi da Faruk. Najwa da take tsaye a parlourn ta k’i d’ago da kanta balle ta kalleshi don wani irin haushinsa take ji da kishi mai zafin gaske. Nene kanta ba wani fara’a take ba don ta ita da ba’a fara d’aura wannan auren ba. Umma ce kawai ta tareshi da fara’a tana fa’din “Ma sha Allah Jaheed ango.” Ya d’an sunne kai yana murmushi, ta gefen ido ya ke hangen Najee da ta k’i juyowa ta kalleshi. Bai mata magana ba, Umma ta masa fatan alheri kafin ta kalli Nene ta ce “Saura ke Nene ban ji kin ce komai ba?” “Allah ya yi albarka shine kawai abidna zan ce.” Umma ta saki murmushi tana fa’din “A haka ma mu ne da godiya.” “Najee” Jaheed ya fa’da a hankali ta d’ago da k’yar tana kallonsa kafin ta ha’diye abinda take ji a ranta da k’yar ta furta “Congratulations Ya. Jaheed.” Ya lumshe idonsa yana furta “Thanks Najee, Allah ya nuna mana namu.” Ta d’auke kanta ba tare da ta amsa ba, sai Nene ce ta masa da saurinta tana fa’din “Ameen, ranar kuwa da na yi rawa da juyi.” Dariya sosai Umma da Jaheed har ma da Faruk suka yi. Haka suka zauna ana ta hira har Baffa ma ya shigo aka cigaba da hirar da shi. Yana sake jaddadawa Jaheed hakkokin da suka rataya a kansa a matsayin sa na Miji, idan kuma ya zalunci matarsa ya sani tabbas sai Allah ya saka mata. Jaheed ya amsa kansa a k’asa idan bai manta ba irin waccan nasihar da Baffa ya masa ce wancan satin da za’a kai masa Najma sai ga shi still yana maimaita masa tabbas Baffa ya ci ya amsa sunan Nagartaccen Mutum dattijon k’warai. ****** Bayan sati guda….. Jaheed da amaryar sa suka d’aga Qatar bayan sun yiwa y’an uwa sallama cike da kewar juna suka bar ahalinsu zuwa wata k’asar. Najma hankalinta ya tashi sosai da sosai ta rasa nutsuwarta sosai take son Jaheed a yanzu da ta tabbatar ya mata nasiha. Lokacin ana saura sati guda azimi. Baffa ya fara shirin tafiya Umara da yake duk shekara yawanci a can yake aziminsa, kowace shekara kuma akwai matar da yake tafiya da ita. Wannan zuwan sai ya fa’da kan Mahmeey. Don haka a daren da zai yi tafiya ya tara duka ahalinsa kamar yarda ya saba. Ya musu nasiha da su ji tsoron Allah musamman idan baya nan, su tuna duk abidna za su yi Allah na kallonsu. Kowa ya amsa a lokacin wata dabara ta fa’dowa Umma a zuciya da sauri ta kalli Baffan yana shirin raba musu ku’di kamar yarda ya saba, ta ce “Baffa ina neman alfarma don Allah.” Ya juyo yana maida hankalinsa gareta “Ina jin ki.” Ta gyara zamanta tana furta “Dama cewa zan yi tunda ana hutun makaranta don Allah Najma zata Bauchi wajen Hajiya Inna hutu ita da Nene zan aika saboda su d’ebe mata kewa ka san jikin tsufa.” Ya juya yana nazarinta baya jin shakkar tura Najma wajen Hajiya Inna don ya san Macece mai nagarta da sanin ya kamata, Yayar Umman ce amma kallon Uwa yake mata don ita ta rik’e Umman har ta ba shi aurenta. Har ta fitar da rai zai yarda sai kuma ta ji ya ce “Kwana nawa za su yi? Kin san ban fiye son y’a mace da barin gida ba, don Ma dai Hajja Inna ce da kai tsaye zan ce a’a” Cikin fara’a Umma ta ce “Ko ana gobe Sallah sai su dawo.” Ya girgiza kai yana furta “Kada su wuce haka, idan sun shirya sai Habu Driver ya kai su.” Umma ta shiga godiya cikin farin ciki. Kashegari kuwa da sassafe Baffa da Mahmeey suka wuce Makka, Bayan Baffan yasa su Najma da Nasma sun ha’de kayansu kaf sun koma b’angaren Umma don kula da tarbiyyarsu. Sai da ta gama komai sannan ta shiga d’akin Nenen. A saman sallaya ta sameta na azkar bayan ta idar da Sallahr walaha. Ta zauna a gefen gadon tana fa’din Allah ya amsa mana dai Nene.” Ameen” Nene ta ce tana nazarin fuskar Umman da alama akwai abinda yake tafe da ita. “Yaushe za mu tafi Bauchin da na ji kina gayawa Baffa?” Umma tana murmushi ta ce “Ba bauchi za ku ba Nene, GARIN GABAS za ku ke da Najee…” wani irin waro ido Nene ta yi tana kallonta murya na rawa ta ce “GARIN GABAS kuma?” Umma ta d’aga kai cike da gasgata wa ta ce “Yanzu nake son mu fara wannan yak’in na gano silar samuwar cikin Jaheed da d’an uwansa, Najee ba zata iya ita ka’dai ba, ni kuma shekaru Uku ina tunanin sun yi nisa don haka zaku tafi tare ki taimaka mata bayan kun yi Basajan Kamanninku.” Nene hankalinta tashe take kallon Umma Sam bata gano wasa a icon Umman ba, da gaske abinda yake zuciyarta kenan. Ta saki ajiyar zuciya a hankali muryarta a raunane ta ce “Ina jin tsoron Umman Yara, wallahi ina tsoron shiga masarautar nan.” Umma ta dubeta duk da tana jin tausayin yanayin da ta ganta bai hanata murtiske tsoron nata ba ta ce “Wannan shine lokacin da ya dace ku je Nene, zamanki anan d’in ba tare da kin san me can yake ciki ba ina ga sam ba mafita ba ce, ki je can ku yi fito na fito da koma waye ya yi silar shigar Ki cikin matsalar nan. Najwa tana da wayo kuma tana da kaifin basira da hankali fiye da ta wani babban don haka na tabbata zata taimaka miki, zan nuna muku abubuwan da zaku yi Basaja da su a jikin ku da fatarku ta yarda duk bala’in mutum ba zai gane ku ba In sha Allah har sai mun cimma mafita.” Nene ta saki ajiyar zuciya tana d’aga kanta a hankali duk da tana jin tsoron har a lokacin sai maganar Umma ta k’arfafa mata gwiwa, ita da kanta ta san zamanta a nan d’in bai da wata ma’ana zuwa can d’in ta fuskanci k’alubalen shine abinda ya kamaceta, don haka ta amince da shawarar Umma d’ari bisa d’ari ta kuma samu k’warin gwiwa a tattare da ita. “Yaushe za mu tafi?” Ta ce tana kallon Umma. Umma ta saki ajiyar zuciya tana jin murnar nasarar da ta samu a kan Nene ta amincewarta ta ce “Jibi In sha Allah, sai dai ina so ki kiyaye kin san dai ban gayawa Baffa inda za ku ba, ita kanta Hajja yanzu sai na kirata na rok’eta kada ta sanar da Baffa inda kuka je, Nene bana son a samu matsala don ke da kan ki kin san Baffa mutum ne mai kafaffen ra’ayi don haka ki kiyaye.” Nene ta d’aga kai tana furta “In sha Allah.” Umma ta mik’e ta fice daga d’akin. A d’akinta ta zaunar da Najee ta gaya mata dukkan shirinsu. Haka kawai sai Najee ta ji gabanta na matsanancin bugu. Da sauri ta kalli Umma ta ce “Umma da ni kuma za’a?” Umma ta d’aga kai tana nazarin y’ar tata da ta bayyana dukkan tsoronta ga lamarin. Don son ta k’arfafeta sai ta ce “Da ke za’a je Najwa ina ji a jikina zaki iya don kina da kaifin basira da hangen nesa, In sha Allah kuma ba abinda zai faru.” Najwa ta d’an lumshe idonta tana amsawa a hankali. Tana kallon Umman ta fice daga d’akinta ta barta cikin yanayi na bugun zuciya da ma rauninta gaba d’aya da ba zata iya cewa ga sababinsu ba. Shirye shirye suka kankama Umma ta musu duk wani tanadi da za su buk’ata a can. Kafin ta samo wani abu da za su shafa a jikinsu kalar jikinsu ta dawo bak’a na lokaci ka’dan idan kuma suka wanke shikkenan. Hak’oran roba aka sakawa Najwa da zai b’oye duk wani kamanninta sai ta zama irin mutanen nan masu Gatso yanayin shigarsu ya yi kama da na mutanen nan da ake kira bararoji. Sun dai nuna alamun suna cikin wahala matuk’a ainun. Da Asussuba suka yi wannan shirin Umma ta kira Faruk ta sanar da shi komai. Ta kuma umarceshi ya kai su har cikin garin Gabas d’in ya tabbata sun shiga cikin masarautar kafin barowarsa garin. Duk da Faruk ya ji tsoro shima a farko amma da Umma ta bayyana masa dalilinta sai ya ji tsoron ya kau, ya samu k’warin gwiwa suka tafi ya saka location na sunan garin a wayarsa abinka da Zamani nan da nan waya ta nuna masa hanyar da zata sada shi da Babban garin Gabas d’in. Umma ta musu fatan alheri ta juya gida don bata amince Driver ya kai su ba, zuciyatta ta fi aminta da Faruk ta san idan Faruk ne bata yarda za’a yi Baffa ya san inda suka je sab’anin Driver da zai iya gayawa wani k’arshe har sirrin da ba sa so ya bayyana a zo a sani ta shiga uku wajen Baffa. _________MASARAUTAR GABAS…… Tunda suka iso cikin garin gaban Nene da na Najwa bai daina fa’duwa ba. Shi kansa Faruk haka kawai ya ji nasa gaban yana fa’duwa. Ya dai yi addu’a ya bar abin a ransa. Yana kallon Nene ta mudubi ya ce “Yanzu ya za’ayi ku samu shiga gidan Sarautar nan, don daga gani akwai matakan tsaro a gidan.” Nene ta bi gidan da kallo gaba d’aya fasalin da ta san shi ya canja, banda ma an rubuta Masarautar Gabas bai zama lallai ta amince shi ba ne. Saboda yarda ginin ya zama na Zamani mai matuk’ar kyau da burge mai kallonsa. Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Shine abin tambaya Faruk, ni kai na ban san ta yarda za mu shiga gidan sarautar nan ba, asalima Wallahi tsoro nake ji…” JIKAR NASHE✍🏽 To fa! ko wa ya san ta inda za su shiga gidan sarautar nan? Ga dai bikin zuwa babu zani. KUDIRAR ALLAH.. 19. NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. Faruk ya saki ajiyar zuciya a hankali Kafin ya furta Ina zuwa. Ya fita daga motar cikin takun nutsuwarsa ya isa bakin babbar k’ofar mai tambarin sarauta. Babban gate ne mai girman gaske kalar ruwan gold. Tun daga nesa zaka hango tsaruwarsa da girmansa kamar Anan aka dasa shi. Daga ganinsa mutanen da suke bakin gate d’in suka taso suna masa wani duba. Faruk ya samo nutsuwar dole ya sakawa fuskarsa duk da k’ok’arin zuciyarsa na son tona masa asiri. Hannu ya mik’a wa wanda ya fara zuwa wajensa d’in. Bak’in mutum ne dogo sosai mai siffar samudawa. Sai da ya ‘dan yi Jim kafin ya mik’awa Faruk hannu yana furta “Bawan Allah me ke tafe da kai? In dai Sarki kake son gani gwara ma ka juya yau bai sanar mana zai ga kowa ba, don shirye shirye na’din Yarima wanda zai gaji sarki bayan mutuwar sa ake saboda haka bai da damar ganin kowa.” Faruk ya saki ajiyar zuciya yana furta “Kamar ka san abinda ya kawo ni kenan, yanzu idan zan ga Sarkin ta ya Zan samu appointment.” Basamuden ya sake masa wani kallo kafin ya ce “Yaushe kuke tunanin Sarkin Gabas ya zama sarki mai araha da za’a iya ganinsa a koda wani lokaci, bana jin duk Nigeria akwai Sarki mai martabarsa don haka ganinsa yake da matuk’ar wahala.” “Ko da wa’dannan?” Faruk ya fa’da yana nuna masa damin ku’din da ke hannunsa da shi kansa bai san yawansu ba. Da sauri Bafaden ya ware ido yana kallonsa kafin ya furta “Afuwa Yallaba’ai Ai tun farko sai ka min bayani. In dai haka ne zan baka appointment zuwa Nan da jibi kazo zaka ga Sarki.” Murmushi Faruk ya yi, yana jinjina lamarin mutanen k’asar mu inda basa abu don Allah sai don Naira yanzu dubi yanda ya mayar da shi Yallab’ai don kawai ya ga Naira. Ganin ya samu kansa yarda yake so sai kawai ya saki murmushi yana furta “To godiya nake, sai dai ba Sarkin nake buk’atar gani ba, ina son ka bani numberrka nima zan baka tawa a duk sanda aka shirya taron ka sanar da ni.” Ya fa’da yana mik’a masa ku’din da suka doshi Naira dubu d’ari biyu abinda Bafaden nan bai tab’a rik’ewa ba kenan, don koda Sarkin Gabas zai bada Zakkar kamarsu to fa kafin tazo kansu an zabtare kaso mafi tsoka. Jikinsa na rawa ya dinga hangen mutanen da suke gefe ya yi saurin tura ku’din cikin Babbar rigarsa yana furta “An gama ranka ya da’de saka min numberr.” Faruk ya karb’i wayar tasa mai k’irar Nokia ya saka masa numberrsa shi kuma ya kira layinsa inda kiran ya shigo wayarsa sai ya yi saving yana murmushi ya kalli Bafaden ya masa godiya yana furta “A duk sanda na shirya ganin Sarkin ina fatan zaka shige min gaba.” Da sauri ya d’aga kai yana futta “Mai zai hana, ko kai abokin Yarima ne?” Faruk ya ‘d’aga masa kai kawai yana tafiya da sauri. Ya tsallaka can gefen titi inda ya yi parking motarsa. Sai da ya mata key sannan murya a hankali ya ce “Ba ta hanyar da zaku samu shiga gidan Sarkin nan a yanzu, sai dai mai gadin ya sanar da ni akwai taron da za’a yi zai kira ni ya gaya min to ina ga ta hanyar nan ne ka’dai zaku iya shiga gidan, don haka yanzu sai dai na kai ku hotel idan ranar taron ta yi zan sanar da ku ta waya sai ku shiga kafin nan mun samo dabarar da zata sadaku da shiga cikin ahalin Sarkin sosai, amma fa dole ku yi takatsantsan Nene.” Ya fa’da idanunsa akan Nene. Ta saki ajiyar zuciya tana d’aga kai. Shi Kuma ya je ya samar musu masauk’i mai kyau inda zasu zauna kafin ranar taron ta zo, tunda dai Nene bata da wasu y’an uwa da ta sani duk rayuwarsu a gidan Sarkin yake anan ta girma anan ta tashi. Kuma ba halin zuwa wajen iyayenta bata sani ba suna raye ko sun mutu ma? Wannan ka’dai idan ta tuna yana d’aga mata hankali sosai. __________________ A zafafe Fulani Raheena ta zubawa Jakadiya ido bayan ta gama isar mata da sak’on Sarkin Gabas. “Me kike fa’da min Jakadiya?” Jakadiya ta rusunar da kanta ka’dan tana sake maimaita abinda ta ce “Sarki ya ce a sanar da ku ku fara shirin gangamin taron bikin na’din Yareema kamar yarda shari’a ta tanadar za’a yi nan da kwana bakwai.” Fulani Raheena ta sake ware idonta akanta ta ce “Bayan shi fa? Akwai abinda kika fa’da bayan wannan.” Jakadiya shiru ta yi bata so aka ji mutuwar sarki a bakin ta ba, shaf ta manta da Raheena take magana ba da Saddik’a Uwar goyon Murad ba shi yasa da farko ta ambaci Murad a matsayin wanda za’a na’da Yareema. “Ba zaki maimaita bane Jakadiya?” K’wayar idanunta a k’asa ta furta “Allah ya huci ran Gimbeeya Sarki ya zartar da Umarnin na’da Yareema Murad a matsayin Magajin…..” Kallon da ta wurga mata ne yasa ta datse zancenta tana ha’diyar yawu da k’yar. Tsoron idanun Fulani Raheena ya kamata. Sai ta ga Fulanin ta saki dariya ta ce “Shine ya zartar da na’da Murad d’in ko mutanen gari?” Jakadiya turus ta yi ta kasa amsa mata. “Ki koma ki sanar da shi yana buk’atar ganinsa yanzu ina neman iso.” Jikin Jakadiya na rawa ta juya da sauri don isar da sak’on Fulani Raheenan, ta sani sarai ba a b’ata mata rai bata k’i ta ci mutuncin mutum komai girmansa ba inda suka sha banban da sauran matan sarki kenan, musamman Fulani Saddik’a. Jakadiya na isar da sak’on Mai martaba ya saki murmushi shi da kansa ya san an zo wajen Raheena rigima zata yi ta gasken gaske shi kuma ya shiryawa duk abinda tazo da shi. “Aje a ce muna mata maraba.” Ya fa’da murya a nutse. Da sauri Jakadiya ta koma ta k’ofar da zata sadaka b’angaren Raheenan. Tun kafin ta gama isar mata da sak’on ta mik’e a fusace ta bu’de wata k’ofa da zata sadaka da b’angaren Sarkin ta sashenta kenan su matansa ka’dai suke da alhakin bi ta wannan k’ofar. A ciki ta yi sallama. Shi kuma ya yi gyaran murya yana amsa mata sallamar cikin kamalalliyar muryarsa mai kwarjini. Ta zauna idanunta akan hoton Yareema Murad da yake kafe a jikin bangon d’akin kamar ka kira shi ya amsa maka. Da k’yar ta ha’diye wani yawu da ya tsaya mata a mak’oshi tana jin haushin Murad da tsanar masa ma gaba d’aya wato ita baya ta nata y’ay’an sai ta Murad d’an gold duk nata ma a yanzu sun kai munzali banda ma ta farkon macece itace sa’ar Murad shi kuma na biyun shekarunsa ashirin da uku, don bayan haihuwar macen shikkenan sai haihuwa ta bu’de mata, y’ay’anta hu’du biyu maza biyu mata. “Sak’o ya isar min.” Ta furta muryarta a cunkushe. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ta ji ya ce “Alhamdulillah, haka ake so dafatan zaku nutsu ku shirya abinda ya dace, ki k’addara Muraad d’an cikin ki ne don haka yarda zaki tsyaa akan harkar y’ay’an cikin ki haka nake nema ki tsaya akan na Murad.” “Me yasa za’a na’dashi Yareema alhali kowa ya san ba halastaccen d’anka bane?” Wata irin d’au kewar wuta SARKI ya yi yana mamakin jin furucinta. Murya a sark’e ya ce “Ke kika haramta shi?” A zafafe ta d’ago tana kallonsa “Wacece Uwarsa a cikin mu matanka hu’du da musulunci ya halatta maka ka kusance mu? Ko kuma kana da k’wark’wara ne?” Zuwa lokacin zuciyar Maimartaba ta fara hassala wani irin tarnak’i yake ji a zuciyarsa sai dai ya daure abinda yake ji d’in ya bita da kallo kawai. “Don haka Murad ko mutuwa ya yi ba shi da gadon ka in dai duka babu d’aya a cikinmu da aka yiwa cikinsa ya haife kuma kowa ya san a tsari irin ta sarautar Yankin Gabas basu amince da k’wark’wara ba don haka Muraad ba shi da ikon gadar mulkinka koda baka da wasu y’ay’an balle kana da su. Abdulhakeem shine yake da wannan damar.” Murmushi Sarki ya sakar mata ya ce “Idan kuma ba haka ba fa? Tashi Raheena ki fice min daga d’aki mara tsoron Allah kawai, idan baki yi wasa ba….” Ya fa’da yana cizon leb’ensa kawai ba tare da ya k’arasa abinda yake son fa’da d’in ba. Ta mik’e a fusace ta fice daga d’akin tana jin zuciyarta na sake fusata da wani irin bugu mai k’arfin gaske, ta yaya komai yake shirin Kwab’e mata ne? Duk shekarun da ta kwashe tana jiran amsa sunan MAI BABBAN D’AKI yana shirin tafiya a banza kenan? Tunda ta shiga d’akinta zagaye d’akin kawai take cike da neman mafita tunani iri-iri ya shiga zuwan mata sai dai ta rasa tudun dafawa. Da tsauri kamar wacce aka tsikara ta d’au wayarta ta shiga danna wasu numbers bugu uku wayar ta shiga. Daga can gefe cikin murya mai kaushi aka amsa mata. “Komai yana shirin kwab’ewa ya kamata mu san abin yi, idan ba haka ba duk shirin mu ya zama a banza, kuna da labarin MURAD yake shirin nad’awa a matsayin magajinsa?” Daga can gefen aka tuntsire da wata bahaguwar dariya kafin cikin kaurara murya a ce “Lokaci ya zo kenan? Lokacin bankad’uwar sirrika da dama? Ciki kuwa har da lokacin bayyanuwar naki sirrin da kika da’de kina k’udundunewa, ko kin zata bamu son komai ba akan naki sirrin?” K’it ta kashe wayar jikinta na mak’yark’yata jin abinda mutumin ya ce, ta ware ido tana sake kallo da nazarin numberr ko ta yi wani kuskure ne wajen saka numberr tunda ta san number biyu ce banbancin numberr da ta wancan wanda ya san d’ayan sirrin nata. Abin mamaki numberr dai da take nema ce, amma me yasa? Ya aka yi ya san abinda bata son ya sani… wannan karan tsoron da take ciki ya fi na gaya mata da aka yi Murad ne Magajin sarki. Ta yaya zata yi maganin Matsalolin da suke tunkarota. K’arar da wayarta ta yi ne ya sake razanata a tsoroce jikinta na b’ari ta kai dubanta kan wayar tsoronta ya sake bayyana ganin sune dai suka sake kiranta. Bata damar k’in d’agawa don ita da kanta ta san bata isa ba. Duk mulkinta da isarta a idanun wa’dannan mutanen banza suke, don sun san abin da duk take k’ullawa. A zuciyatta ta shiga tsinewa wanda ya samar da cikin Murad duk da bata shiga cikin wa’dannan matsalolinba. Hannunta na rawa ta sake dank’ar wayar ta kara a kunnenta. “Ki nutsu ki saurari abinda za mu ce miki, idan kina son komai ya tafi cikin sa’a da nasara sai kin san yarda aka yi kika ha’da auren Murad da k’anwarki, ta haka ne zamu samu cimma burinmu a kansa, za mu kashe shi ba tare da an san mu ne sila ba, abu na gaba daga yanzu zuwa ko yaushe kada ki sake ki sake nunawa Mijinki ba kya son na’da Murad da zai yi a matsayin magajinsa.” Jikinta na rawa ta amsa musu bayan nan kafin ta ce komai sun kashe wayar. Itama ta zare layin da sauri ta mayar da shi inda take adanashi don bata amfani da shi sai matsala irin haka ta taso. Daga ranar ta k’udirce a ranta ba zata sake magana akan na’din da za’a yiwa Murad ba, duk da ta san mawuyacin Abu ne al’ummar garin mahakuntan sarautar su yarda da na’din wanda ba a san ta yarda aka samar da cikinsa ba. Da ita aka fara shirin duk wani abu da za’a buk’ata a gidan sarautar Sarki ya ji da’din abinda ta yi don haka ba jin fargabar komai ya sakar mata dukka ragama duk da wani gefe na zuciyarsa na son nuna masa kuskurensa a cikin aikata hakan. _________ Ranar Na’din Sarauta……. Tun safiyar ranar yake jin zuciyarsa ba da’di, har hakan ya bayyana akan fuskarsa, duk da dama Miskili ne bai fiye sakin fuska ba, sai dai na yau ya bayyana matuk’a ainun. Da k’yar ya mik’e ya fara shirin wanka, shima hakan bai samu ba har sai bayan da Fulani Raheena da yake kira Mamma ta shigo sashen nasa har sau biyu tana sanar da shi mutane sun fara hallara kada a zo ana jiransa. Da Rangaji ya isa tafkeken toilet d’in nasa yana kallon ruwan wankan da hadiminsa ya cika masa. Kamar koda yaushe kuma an jera komai yarda ya kamata. A kasalance ya fara wankan. Kafin ya fito ya fara shiri duk da k’ok’arin sa na son aikata sauri sai dai kasalar da zuciayrsa take ciki ya kasa aikata hakan sosai yake jin rauni a zuciayrsa da gangar jikinsa. Sam mai martaba ya kasa ganewa ne amma baya son sarautar nan ko ka’dan balle har a ce wai an na’dashi Yareema mai jiran gado. Himilin kayan da aka ajiye akan gado da ake son duk ya saka su a jikinsa ya dinga bi da kallo yana yamutse fuksa. Sam baya son saka kayan sarauta nauyi suke masa sosai su hana shi sakat, ai kuwa yana sakawa yana mita don ya san idan bai saka bama Mamma ba k’yaleshi zata yi ba. Rawanin ne dai bai na’da ba don bai iya ba ma kuma ya san ko ya na’da idan ya je wajen kunce shi za’a yi a sake na’da masa wani. Don haka yana

Chapter 11 of 16