Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi zafi ba, idan kuwa ya yi zafi ya gwammace ya tsallaka k’asar masu jajayen kunnuwa a duba shi tunda dama a can ya fi kauri. Lumshe idanunsa ya yi kafin ya girgiza kai a hankali yarda ita ka’dai zata ji ya ce “Na zo ne kawai na duba patient d’in ki.” Mamma ta ware ido tana furta “Are you sure?” Ya d’aga kai yana murmushi kafin ya fice da sassarfa yana d’aga mata hannu. Mamma ta bi bayansa da kallo tana mamakin abinda ya ce Lallai patient d’inta ta ci a kirata mai sa’a tunda har Murad ya tako ya zo dubata. Ta jinjina lamarin kafin ta saki ajiyar zuciya itama ta shiga d’akin don duba patient d’in. Idanunta a lumshe ta tarar da ita duk ba barci take ba sai son bawa zuciya nutsuwa daga zuzzurfan tunanin da yake damalmala kwanyarta. Sallamar da ta ji ne yasa ta ta bu’de idanunta tana kallon Fulani Saddik’a gabanta ya fa’di don ko a maye take kamannin Fulanin ba zai b’ace mata ba, Mace Adala kenan mai nagartattun halaye da ake kira ta fisu kaf ta fi matan sarki. Da ace bata b’atar da nata kamannin ba ta hanyar Basaja da tsaf Fulanin zata shaida ta don sun yi zaman mutunci da ita kusan itace nagartacciyar baiwarta wacce ta amince ta san duk wani sirrinta. Sai dai a yanzu kam ba zata shaida ta ba ba don nata kamannin sun canja ba sai don canjin da aka musu na dole don gudun kada a ganesu. Fulani ta zuba mata ido kafin murya da sanyi ta ce “Sannu da jiki baiwar Allah, dafatan dai kina samun sauk’i.” Nene ta d’aga kai tana k’ak’alo nata murmushin da kai tsaye za’a kira na dole. “Yi magana mana baiwar Allah ba dai matsala ko?” Murya a sanyaye ta furta “Alhamdulillah na samu sauk’i.” Fulani ta saki murmushi tana furta “Ma sha Allah, haka ake so. Sai magana ta gaba a ina za’a samu danginku a sanar musu don naga kamar k’aramar y’ar taki ba zata iya jinyarki ba, tunda an ce jininki ya hau kina buk’atar hutu sosai.” Najwa gabanta ne ya fa’di su ka ha’da ido da Nene da itama take kallonta da sauri ta d’an girgizawa Nene kai. Murya a sanyaye Nene ta ce “Garin mu da nisa Hajiya, Kuma ko Anje can d’in ba mu da kowa bamu da wanda zai iya jinyata ki bar ni da yarinyata zata iya komai.” Fulani ta juya tana kallon Najwa kafin ta jijjiga kai ta ce “Ya sunanki?” Da sauri Najee ta furta “Sunana Ladidi.” Fulani ta ‘d’aga kai tana furta “Ladidi Ai ba sunan gaskiya bane, sunanki na gaskiya nake son ji.” Najwa ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce “Hadiza nake.” Fulani ta d’aga kai tana furta “Ai kuwa sunanki yafi k’arfin furtawa ga duk wani mazaunin Fadar nan sai dai mu dinga kiranki Ladidin. Sabida sunan mai Babban d’aki ne Mahaifiyar Sarkin Gabas.” Najwa ta saki murmushi kawai wanda gatsonta ya sake bayyana. A zuciyar Fulani ta jaddada munin Najwa ga bak’i kamar mutanen South Africa. “Shikkenan ko mu zamu tafi, zan saka a dinga kawo muku abinci idan an kawo muku abincin sai ku dinga fa’da musu idan kuna son wani abu kafin a sallameku mu ga abinda Allah zai yi.” Nene ta d’aga kai tana furta “Mun gode Allah ya k’ara girma da d’aukaka ya tsare gabanki da bayanki.” “Ameen” Fulani ta fa’da a hankali ta juya tana kallon Najwa ta ce “Ladidi Zan aiko da kaya don Allah ki cire na jikinki ki yi wanka ko kya yi kyan gani.” Najwa ta d’aga kai tana sakin murmushin da ko ka’dan bai mata kyau ba, sai ma muni da ya k’ara mata. Sai da suka fita sannan ta kalli Nene Suka saki dariya a tare. Najwa ta ce “Wai Nenne muni na yi ne sosai?” Nene dariya ta yi sosai ta ce “Ai Najwa don baki ga yarda kika koma ba ki je ki ga mudubi a toilet.” Da sauri Najwa ta mik’e ta shiga toilet d’in. Ware ido ta yi kafin ta saki dariya ganin yarda fuskarta ta yi dole duk wanda ya kalleta ya ji bata burge shi ba ashe shi yasa Murad ya ce mata Witch. Ta ha’diye yawu da k’yar saboda haushin Sunan da ya kirata da shi sai yanzu ta tuna ma’anar Witch Mayya! Haushin Murad ta ji sosai a ranta kafin ta fito daga toilet d’in tana sakin dariya tace “Cab Nene haka na koma Blacky!” Nene ta saki murmushi tana furta “Kamar ba Kyakykyawar Najee d’in Jaheed ba.” Kunya ce ta kama Najee tana hasasota matsayin matar Jaheed sai kuma nan da nan kishi da jin haushin matarsa ya rufeta, ko sai yaushe za’a kirata da Matar Jaheed? Ta tambayi kanta, sam bata san maganar ta fito fili ba Nene ta saki dariya tana furta “In sha Allah shekara I war haka kin amsa wannan sunan haka za’a yi auren ko baki gama makaranta ba.” Da sauri Najwa ta rufe fuskarta fahimtar da ta yi Nene ta ji zancen da take da zuciyarta. Nene ta saki murmushi kawai tana jin a ranta kamar itama ta janyo wannan lokacin tana burin ha’da jini da Baffa da Umma salihar mace mai nagartuwar halayya. _____________ Cikin toilet d’in take tsaye tana aman da ya k’i tsaya mata, ya zame mata jiki duk safiya sai ta yi shi kamar masifa ga shi kore sharr. Jiri ne yake d’iban ta da k’yar ta fara k’ok’arin dafa bango don fitowa daga bathroom d’in. Sai ga Umman Najee nan ta shigo da d’an hanzari idanunta akan Najma da ta wani d’ashe ta yi fari tas ga rama ta yi ba ta wasa ba. Bata mata magana ba ta kamata suka fita zuwa d’aki, a bakin gadon ta zaunar da ita tana furta “Yau kam duk kafiyarki sai mun je asibiti, wannan ciwon ya isheni ina dalili? Kin ga yarda kika dawo kuwa kamar mai yaron ciki?” Daga ita har Umma sai da zuciyarsu ta buga da k’arfin gaske suka zubawa juna ido kowa da tunanin da yake cin ransa. Umma nata fargabar kada dai magana Najma ta d’auko musu, don ita bata san Jaheed ya kusanceta ba, ita kuwa Najma addu’a take dafatan Allah yasa cikin Jaheed ne a jikin ta ko wannan ya yi dalilin da zai saka ya dawo ya saurareta. Ido Umma ta zuba mata duk da ba likita bace ita amma yawan shekarun da ta yi tana rainon ciki da haifeshi ya ci ace ta fuskanci ciki. Ta sake ajiyar zuciya kafin ta mik’e ta zaro hijab tana mik’a mata “Tashi mu tafi tun yanzu.” Najma ba yarda ta iya ta mik’e jikinta ba k’wari ta bi bayan Umman suka fita falo Umman na rik’e da hannunta zuciyarta na bugun jin tsoron tabbatuwar tunaninta. ____ Fulani Raheena kuwa tun bayan komawarta gida zuciyarta ta kasa nutsuwa da maganganun Baffan Gwandu da suke hasasho mata fallasuwar nata sirrin data tone ta zuba shi a cikin k’asa sai dai a yau tana tunanin akwai wanda ya kusa tono shi. Ya aka yi matsalar da take ciki ta yi kamanceceniya da ta Baffan Gwandu? Su waye wa’dannan mutanen da suke wasa da hankalinsu a da ta zata nata hankalin ita ka’dai ake watangaririya da shi ashe har da na jama’a da yawa a cikin a masarautar nan? Ya zama dole ta gano su waye idan ma Jinnu ne su dole su bayyana don wannan karan komai zai faru sai dai ya faru akan tonuwar b’aragurbin k’wan da zai addabi jama’ar da ke ciki da wajen masarautar Gabas. Bata da hannu a cikin samuwar cikin Murad tata matsalar ta daban ce ta kuma zarce matsalar da Sarki yake ciki ta samuwar cikin Murad da rashin sanin wacece mahaifiyarsa duka wannan mai sauk’i ce akan tata. Ta zauna a gefen gado dab’as bayan ta lalubo sirrintaccen layin wayarta ta saka a wata k’aramar waya ta daban. Bugu biyu numberr ya shiga kamar yarda ta tsammata waccan kaurararriyar muryarce ta yi magana bayan sakin dariyar da ta kusa saka Fulani yin fitsari a wando. “Tunanin ki ya baki daidai mowar sarki, b’aragurbin k’wanki ya kusa fashewa idan kuma ya fashe zai addabi masarautar gabas, hanya d’aya ce ki gaggauta saka Murad ya auri y’arki kamar yarda muka gaya miki itace zata mana ajalinsa shi kuma Mukhtar ki bar mu da shi ya kusa barin duniya ma gaba d’aya.” “Me yasa zaku ce sai ya auri k’anwata alhali kun san sarai a matsayin y kuma ina son na san ko ku su waye? Me yasa kuka saka ni a cikin wancan gagarumar matsalar?” “Saboda kin cancanci shiga matsalar sakamakon zalamarki da kika nuna na son haihuwar Magajin sarki wannan shine hujja mun baki abinda kike so kema ya zama dole ki mana abinda muke so daga gobe muke so ki fara aiwatar da k’udirinki na ha’da Murad aure da k’anwarki sanin ko mu su waye Kuma ba zai amfaneki da komai ba, idan lokacin sani ya yi da kan ki zaki sani.” Daga haka suka kashe wayar. Fulani ta bi wayar da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya hawayen nadama na sauka a idanunta da alama dai ta kusa tashi a tutar babu idan kuwa haka ne ya zama dole ta saka Murad ya auri K’anwarta in dai hakan shi zai saka ta samu cikar burinta. ———————- Nene ta mik’e tana kallon Najwa har zata ambaci sunanta sai kuma ta yi murmushi ta furta “Ladidi burin mu ya cika na shigowa masarautar Gabas abu guda ya rage mana samun hanyar da zamu shiga ainahin cikin masarautar don samo wancan rufaffen sirrin, ina jin tsoro Najwa bana son a sheganta min y’ay’a banda haka da tuni na bayyana kai na a matsayin Mahaifiyar Muraad…….” Turo k’ofar da aka yi da k’arfi ne yasa Nene yin shiru da zancen tana d’aga idonta tana kallon mai tahowar k’amshin turaren sa yana dukar hancinsu idanunsa ya zube a kan Nene fuskarsa na nuna alamun duk ya gama jin abinda suka ce, hantar cikin Najwa ta juya har kana iya juyo k’ararta ita kuwa Nene suman zaune ta yi tana k’ok’arin saita numfashinta da ya kusa d’aukewa…….. ya cigaba da shiga cikin d’akin cikin takun isa Fulani Saddik’a na bayansa…….. Ku min afuwa ciwon kai ne ya tasa ni gaba kwana biyu amma dai da sauk’i sosai Alhamdulillah KUDIRAR ALLAH. 23. 08033748387. NAZEEFAH SABO NASHE.✍🏽 _________________ Alhamdulillah na ji sauk’i ina godiya Anty Hadiza Sodangi abisa kulawarki gareni, na yi addu’a kuma an dace, Rabbi ya saka miki da mafificiyar Aljanna ya raya miki zuri’a akan tafarkin shiriya. ______________ Nene wani irin ha’diyar yawu take wanda bata shiryawa zuwansa a wannan lokacin ba, zufa ta gama jik’a ta ta ko ina duk da sanyin a.c d’in da take cikin d’akin. Kallo d’aya zaka musu ka tabbatar da rashin gaskiya a tare da su musamman Najwa da ta kasa kallonsu. Fulani Saddik’a wani murmushi ta saki bayan ta kalli Murad ta tabbatar shi bai ji abinda ta ji ba saboda airpods d’in da ke kunnensa yana amsa waya. Ta juya tana kallon Nene kallo mai bayyana tuhuma sai dai ta danne abin a ranta ta ce “Ya jikin naki?” Nene da ta kusa sakin fitsari a wando ta d’aga mata kai cikin raunin murya ta ce “Alhamdulillah” Fulanin ta ce “Ma sha Allah Ai daga gani jiki ya yi kyau shi yasa ma likitocin suka sanar min sun baki sallama, to sakamakon maganar da na ji kuna yi jiya na rashin wajen zama sai na yanke shawarar tafiya da ku can wajena kafin a samu mahallin saka ku.” Murad ya bu’de ido yana kallonta “Wajenki Mamma?” Ta d’aga kai cike da gamsarwa ta ce “Ba su da inda ya kamata su zauna fiye da wajen nawa, zan saka a cigita gida idan komai ya lafa sai su koma can a yanzu dai kam can ne ya kama ce su.” Shiru ya yi banda yana tausayin Uwar ba yarda za’a yi ya yarda Mamma ta d’auki wannan mummunar yarinyar ta kai gidanta, amma haka kawai yake da feeling na tausayi akan Babarta don haka sai ya share ya d’an tab’e baki ha’de da ware hannu yana furta “As you wished Mamma Allah ya bada lada.” Daga haka ya juya ya bar d’akin dama sam bai san me yasa ya biyo Mamman ma. Suka bi bayansa da kallo har Mamman kafin ta juyo da kanta tana kallon Nene irin kallon k’urilla mai cike da son tabbatar da zarginta, sai dai a ilimi irin nata ta yi k’ok’ari k’warai da gaske ta b’oye mamakin jin maganar ta nuna musu gaba d’aya ma bata ji abinda suka ce ba. “Ku taso mu tafi amma bana buk’atar komai kawai ku taho zallar ku ka’dai nake buk’ata.” Nene ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa jikinta cike da kasala zuciyarta na sake sanar da ita tabbas Fulani ta ji maganar nan kawai sharewa ta yi ta nuna bata ji, sai itama ta daure kawai ta ha’diye nata k’udirin. Suka bi Fulanin inda hadimanta suke bakin k’ofa suna jiranta. A sashen Fulanin motoci biyun Suka yi Parkin Fulani ta fita kafin ta umarcesu su ma su fito. Jikinsu na rawa suka fito Nene tana bin wajen da kallo, wajen dai fulanin ne dai da ta sani sai dai an yi renovating d’insa ya zama wani irin gini mai kyawun gaske. Ta dinga bin wajen da kallo tana tunano zamanin baya Lokacin k’uruciyarta kafin k’addara mai girma ta yi facali da wancan farin cikin da take ciki. Hanyar sassan bayi take bi da ido zuciyarsa na bugu da k’arfi tsoro take ji sosai bata son a ce ta rasa iyayenta kamar yarda zuciyarta take hasasho mata. Fulani Saddik’a ta juyo idanunta cikin na Nene tana sake nazarin fuskarta duk zarginta yana son tabbata daga ganin yanayin idanuwan Nenen ta san abinda duk take tunani zai iya zama gaskiya. Bata mata magana ba illa wucewa da ta yi tana nawa hadimanta umarnin su kai su Nenen wani keb’antaccen d’aki inda take ajiye manyan bak’in da bata son su yi nisa da ita. A sashenta d’akin yake cikin babban parlourn ta. Hadimanta suka bita da kallo suna mamakin abinda ta ce don ko su suna iya k’irga sau nawa k’afafunsu suka shiga cikin d’akin balle a kai wa’dannan yamutsatstsun mutanen da ko kyan kama ba su da ita. Sai dai basu da hurumi ba kuma su isa su tambayi Fulanin dalilinta ba don haka suka ja baki suka shiru tare da bin umarnin Fulanin kai tsaye, bayan sun wurgi su Nenen da wani kallon banza na raini. Nene ta saki murmushi kawai don ta san hassada ce irin ta d’an Adam da ba ya iya b’oyewa. Babban d’aki ne mai girman gaske mai d’auke da wani faffa’dan gado da ya sha filillika irin dai shimfi’da gidan sarauta. Sai zabga wani irin k’amshi yake na turaren wuta da na Humrar d’aki. K’asansa malale yake da carpet mai taushin gaske. “Nan ne d’akin sai a kiyaye banda k’auyanci, ni Wallahi ban san me ya sa Fulani tayi shawarar kawo ku nan ba.” “Me yasa ba zaki je ki tambayi Fulanin dalili ba?” Najwa ta fa’da fuskarta a ha’de cikin jin haushi da tsanar halayyar wasu mutanen masu wulak’anta mutum tun basu san irin girman da Allah ya masa ba, ji fa a rashin sani bata san Nene b’ace Uwar Murad amma ji abinda take gaya mata. “Kada ki min rashin kunya yarinya ji da munin da Allah ya baki da Uban hak’oranki.” Ta fa’da tana hararar Najwan. Najwa ta bu’de baki zata yi magana Nene ta dakatar da ita. “Barta Najwa akwai ranar mayar da magana ba yanzu ba.” Sai da ta harari Nenen sannan suka yi tsaki suka fita bak’in cikinsu guda basa son Fulanin ta kawo wanda zai maye gurbinsu tunda sun saba yi mata almundahana da hainci akan duk wasu abubuwanta. Suna fita Najwa ta ce “Amma Nene me yasa kika dakatar da ni baki bar ni na ci Ubansu ba.” Nene ta saki murmushi tana furta ba yanzu ba Najee akwai lokaci.” Suka mayar da kansu kan sake kallon d’akin duk da arziki ba bak’on su bane amma d’akin nan ya tafi da duk hankalinsu. Najee ta ‘Dane gadon har da tsalle tana murmushi ta ce “Na d’ane gadon Uwar Sarkin Gabas, Nene Allah ya nuna mana ranar da zasu san ke ce Mahaifiyar Sarkin Gabas daga kan wad’annan barorin zan fara rashin mutunci, Nene har shi fa Murad d’in ba zan k’yaleshi ba sai na rama kallon hadarin kajin da yake min.” Nene murmushi kawai ta saki kafin ta furta “Ai dole Najeen Nene ni kaina sai na tayaki rama wa don ina kallon idanunsa da hararar da yake zabga miki, don yaga an canja miki kamanni Bai san Najee na ko larabawa albarka ba wajen kyau sai dai a nuna mata hasken fata don ko gashi ba su fiki ba, tun yanzu ma kenan ina ga nan gaba mak’erin y’an mata ya k’ere min ke za’a ga cikakkiyar mace mai cikakkiyar sura ta nunawa a jarida.” Najee murmushi ta saki tana sunkuyar da kai. Kafin ta ce “Da gaske Nene ni kyakykyawa ce? Amma ana cewa su Yaya Nasma sun fi ni kyau.” Nene ta girgiza kai “Ko ka’dan sun dai fi ki hasken fata amma zallar kyau da dirin jiki Ai Najee na ba baya bace•” farin ciki ya lullub’e Najwa kafin ta mik’e ta shiga toilet don yin wanka sai kuma gata ta fito a guje Nene ta kalleta tace “Lafiya?” A hankali don kada kowa ya ji ta ce “Nene idan na yi wankan abinda zan shafa kamar fa mun bar shi a asibiti.” Nene ta saka hannu a aljihunta ta zaro robar mai d’auke da bak’in abin ta mik’a mata “Ban manta ba Najee, ta ya zan manta da abinda shine rufin asirin mu.” Suka saka dariya gaba d’aya. Najee ta ce “Wallahi Nene d’azu na tsorata na fa zata Sun ji abinda muke fa’da.” Nene ta saki murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba. Najee ta sake cewa “Yanzu da sun je abinda muka ce me za mu ce da su?” “Ba abinda za ku ce sai dai Zan yi murna sosai idan har ya tabbata hasashen da nake haka yake.” Suka tsinkayi muryarta daga sama tana shigowa cikin k’asaitacciyar shigar da take bayyana kasancewarta Fulanin Sarki ta yi kyau sosai kamar ba yanzu suka rabu da ita ba har ta sake fesa wani wankan sai zabga k’amshi take. Fuskarta d’auke da murmushi ta shigo cikin taku d’aid’aya. Ita ka’dai ce ba hadiman nata, hannunta janye da wata babbar trolley. Sak suka yi suna kallonta fusakrsu d’auke da tsoro da razani har ma da firgita gaba d’aya. Murmushin bai bar saman fuskarta ba ta samu waje daf da Nene a bakin gadon ta zauna. “Tun asibiti na ji duk abinda kuke fa’da.” Ta sake tsunduma su cikin mamaki “Mafarki na ya tabbatar na bayyanuwar Mahaifiyar Murad burin da na da’de ina son cika shi a rayuwata sai ga shi yazo min a lokacin da ban tsammata ba, wata zuciyar na ce min k’arya kuke amma wata zuciyar na k’arfafa ni akan tabbas ke d’in ke ce Mahaifiyar Murad da ta d’au cikinsa ta kuma haife shi.” Ta fa’da tana nuna Nene da ta yi mutuwar zaune don yanzu lamarin ya zarce suman zaune gaba d’aya bata fahimtar komai, razanar da zuciyarta take ciki ta zarce dukkan tunanin mai karatu, bata san a wata fuska Fulani zata dubeta ba, shin zata taimaketa ne ko kuwa itama da nata burin? Idan har taimakonta zata yi me yasa tun a lokacin bata sanar da Murad abinda kunnuwanta suka jiye mata ba? Me yasa ta zab’i ta b’oye masa? Alhali abin murna ne da farin ciki yau a ce yaga mahaifiyarsa? “Na san zaki yi mamakin dalilin da yasa na b’oyewa Murad kasantuwarki mahaifiyarsa, Ina da nawa Burin da kuma shara’din da sai kin min alk’awarin zaki cika shi sannan zan taimaka miki cika naki burin, kafin nan ina so ku yi wanka ku ci abinci ku huta sosai zan zo mu yi magana, idan kin fahimci ki d’ora kan ki akan turbar zaman lafiya, rashin fahimta ta kuwa yana nufin abubuwa da dama…” Daga haka ta mik’e har a lokacin dai idanunta akan Nene tana sakar mata murmushin da Nenen ta kasa fassara shi, bata san a matsayin da zata ajiye k’ayataccen murmushin nata ba, Me fulani take nufi? Shine tambayar da ta cika zuciyarta har ta hanata katab’us tana kallo Fulanin ta fice daga d’akin bayan ta d’aga mata hannu tana furta “Na baku Awanni hu’du zan dawo, kafin nan ina son na jaddada miki bana son k’arya a duk zancen da zaki gaya min, sannan kuma bana son mutum mai sab’a alk’awari idan na sameki da d’aya daga cikin wa’dannan akwai hukunci mai tsananin gaske ciki kuwa har da b’atar da ke daga sararin duniyar nan……..” Daga haka ta fice da sauri bayan ta ja musu k’ofar da k’arfin gaske. Bugun k’ofar ya yi daidai da bugun zuciyar Nene da k’arfin gaske. Ta dafe wajen tana jan Hasbunallah a hankali, Ba abinda ta fahimta a zancen fulanin da ya zarce itama akwai nata b’oyayyen k’udirin… Ta kalli Najee da take tsaye itama kamar statue ta kafawa Nenen ido cike da nata tsoron da fargabar. “Zama bai gan mu ba Najee na lura itama da tata manufar ya zama dole mu bar gidan nan a yau d’in nan kafin komai ma ya faru.” Najee ta ware ido ita da kanta ta amince da abinda Nenen ta ce don haka ta fasa shiga wankan da ta yi niyya suka fara tunanin ta hanyar da zasu bi su tsere daga gidan nan ba tare da Fulani ta gan su ba. “Ki lek’a Parlour idan kin ga wa’dannan marasa mutuncin bayin ki kira min su.” Najee ta d’aga kai tana lek’a parlourn cikin sa’a kuwa sai ta gansu. Murya k’asa k’asa ta ce su je in ji Nene don Allah. Da dai kamar ba za su je ba, sai suka tuna mahimmancin su a wajen Fulani don haka suka bi bayanta. A tsaye suka ga Nenen tana ganinsu ta saki ajiyar zuciya. “Yauwa don Allah taimako zaku mana, ku nuna mana hanyar da zata fitar da mu mu kan mu bama son zaman gidan nan.” Kallon kallo Suka shiga yi wa juna kafin su saki murmushi su girgiza kai “Fulani ta ce ko Parlour kada a bar ku ku fita har sai idan ita ta bada izini.” Nene da Najee suka zaro ido….. Mhmmmmmmn! Baki biya ba ko har yanzu? Book one ya kusa zuwa k’arshe ki biya d’ari biyar kacal don samun kashi na biyu. Tura ta asusu kamar haka 2118666253 UBA sai ki tura shaidar biya ta number kamar haka 08033748387. Gundarin zak’in labarin cike da zazzafar k’iyayya da soyayya suna gaba. 🥰 JIKAR NASHE✍🏽 KUDIRAR ALLAH 24. 08033748387. NAZEEFAH SABO NASHE. ______________ Fargabar Nene ta sake k’aruwa jin abinda Hadiman Suka furta, da alama kuma ko mai za su ce musu ba zasu bar su su fita ba, umarnin mahaifiyarsu za su bi. Don haka ma bata rok’esu ba ta ja hannun Najwa kawai suka zauna suna kallo Hadiman Suka fita suna dariya k’asa k’asa, da alama sun hango mugunta Fulanin ta shirya musu. Najwa ta kalli Nene tana sakin ajiyar zuciya ta furta “Mun ga ta kan mu Nene wai me matar nan take shirya mana ne?” “Alheri In sha Allah.” Nene ta furta duk da zuciyarta tana taraddadi akan amsar da ta bawa Najeen. Tsawon sa’oi suna zaune a haka suka daure suka yi wanka suka kuma samu kaya a kayan da Fulanin ta kawo musu cike da akwati duka dogayen riguna ne free sizes don haka duk suka musu daidai. Fuskarsu suka sake shafa mata shuni. Abinci ka’dan suka tsakura saboda fargabar da zuciyarsu take ciki. Suna zaune shiru cikin taraddadi Fulani ta sake danno kai cikin d’akin, k’amshin dadda’adan turarenta ne ya sa suka san itace. A hankali ta sauke idanunta cikin nasu, wannan karan ba wannan yalwataccen

Chapter 13 of 16