Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko ta huta da ciwo da ra’da’din zuciya. Sarki da yake hankalce da ita bai mata magana ba, har sai da su Fulani Maimuna da Fulani Habiba suka fice sannan ya dawo da kallonsa gareta cikin muryar garga’di ya ce “Ki aikata abinda yake ranki, tabbas kina son ki bi sahun su Maimunatu don zan iya aikata komai game da tsare rayuwar Murad.” Daga haka ya Mik’e cike da taku mai nuna nagarta da k’arfin Mulki ya bi bayan Fulani Saddika. Wannan furucin nasa shi ya sake gigita Rahina ta rasa natsuwarta gaba d’aya ta san tunda ya furta tabbas yana nufin abinda yake cikin zuciyarsa ne kai tsaye. Ta ciji yatsa a hankali tana sake jin azababben ciwon na sake dawo mata k’ugunta kamar zai b’alle. (Ku cigaba da biya masoyana da’din Littafin na gaba wannan duk shimfi’da ne. Kamar yarda na fa’da In sha Allah. 500 zuwa asusun banki kamar haka 2118666253 UBA. Sai a tura shaidar biya ta numberr waya 08033748387. JIKAR NASHE.✍🏽 K’UDIRAR ALLAH. 11. NAZEEFAH SABO NASHE.✍🏽 08033748387. Yarda gumi ya jik’a Fulani Saddik’a zai tabbatar maka da nak’uda ce take yi mai azabar gaske. Runtse ido take yi kawai tana cije bakinta kukan ma ya k’i zuwa sai cizon leb’enta take. Hakan ya janyo hankalin Barorinta ba shiri suka yi yo kanta da sauri da k’ok’arin son su taimaka mata. Zafin ciwon da take ji ne yasa tana ji tana gani suka kamata zuwa cikin d’akin. Kafin su juya sanar da Jakadiya ta yi wani irin k’akkarfan nishin da yasa kan Babyn ya danno da K’arfin gaske. Ta saki hucin wahala a hankali tana duban abinda ta haifa, zuciyarta ce ta kusan bugawa ganin jaririyar yarinyar a gabanta. Da k’yar ta ha’diye yawun da ya tokare mata a mak’oshi ta janye hannunta ta d’au jaririyar a hannunta kamarsu guda da y’ar ba abinda ta d’auko na Ubanta. Hawaye ne ya so ya kece a idanunta sai dai ta yi k’ok’ari sosai ta danne abin a ranta ganin yardaddun barorinta a wajen. Labari ya kara’de masarautar gabas aka fara sanar da haihuwar Fulani Saddika kowa ya cika da al’ajabi gefe guda kuma ana tunanin a ina aka samo wancan jaririn da aka tsinta? Sanda Sarki ya samu labarin bai ji komai a ransa ba kamar yarda ya samu farin ciki da aka kawo masa Murad a matsayin d’ansa bai sani ba ko don Macece. Da kansa ya taso zuwa b’angaren Fulani Saddik’an don ganin lafiyar ta da ta jaririyar da ta haifa. Ido Fulani ta zuba masa lokaci guda kuma abinda yake ranta ya kasa b’oyuwa a zuciyarta sai da ta bayyana kuka ta saka sosai kukan da ya raunata zuciyar Sarkin gabas bai san sanda ya k’arasa wajenta ba da sauri ya fara tambayar ta lafiya?” Hawayen ne ya fara zubo mata ba kakkautawa kafin ta sanar masa damuwarta na rashin samun muradinta Magajin Sarkin Gabas. Shiru ya yi yana zuba mata idanunsa masu cike da kyau da Haiba kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Ki k’addara haka Allah ya so ki ma gode masa da ya baki d’iya macen ki kuma yi fatan ta rayu…” Ta ha’diye kukanta ta yi tunawa da budulcin da taso ta yiwa Allah da sauri ta ce “Astagfirullah.” Ta kuma sake rungume jaririyar a Jikinta cikin nutsuwa take sauke ajiyar zuciya. Sarkin Mukhtar ya saki murmushi a Hankali shima. Yana cigaba da nazarin Saddik’ar da bata iya b’oye abinda yake ranta. Da kansa ya amshi yarinyar ya kuma yi mata hu’duba Da Fateema. Daga lokacin da visar su ta fito ya ha’da Murad da Uwar rainonsa zuwa k’asar England inda a can ya fara karatu ba kuma ya zuwa ko ina sai idan an yi hutu yake zuwa Nigeria, don haka mutane da yawa ba su san shi ba saboda rashin son hayaniyar sa da shiga mutane. Sanda Sarki ya gama ba shi labarin tuni jijiyar kansa ta tashi ta yi ra’da ra’da, idanunsa sun sake girma kamar yarda suke kasancewa idan yana cikin b’acin rai. Hannu kawai ya saka yana murza goshinsa da yake sara masa kamar zai dare. Ya Lumshe idanunsa so yake Hawayen su zuba sai dai juriyarsa da izzar sarauta ga allurar sojojinsa mai saka zuciyarsu dakiya sun hana shi zubar da hawayen. Ya mik’e yana furzar da huci a hankali, Sarki yana ji yana gani ya fice daga fadar duk da yanayin da yake ya ci a dakatar da shi sai dai ya san a wannan lokacin ba wanda ya isa ya dakatar da Murad. Nutsuwa yake so ya samarwa kansa kafin zafin zuciya ya saka shi ya Jirge fushinsa a kan duk wanda ya yi nufin shiga gonarsa. Har ya isa b’angarensa hucin yake furzarwa, jin alamun Hadimansa suna binsa ba tare da ya juyo ba ya dakatar da Su ta hanyar d’aga musu hannu. Yana shiga ya rufe k’ofar da saurin gaske hannayensa duka biyun ya dinga dukan bangon d’akin da su, tunani ne fal ya cika zuciyarsa so yake ya hango wacece mahaifiyarsa shin shi d’in d’an Sunna ne ko d’an haram, dole ba zai zama d’an Sunna ba tunda dai sarki da kansa ya san bai tab’a kusantar wata mace ba sai Matansa hu’du idan haka ne ya zama dole ya gano ta hanyar da aka samar da shi wacece kuma Uwarsa? ______________________ A gefen Baffa Jaheed yake zaune kansa a k’asa zuciyarsa a raunace take sosai jin zantukan da Baffan yake yi. “Gobe zata tare a gidanta ba wata bidi’a da za’a yi don na ga Uwarta bata neman zaman lafiya da ni.” Zuciyar Jaheed ta shiga wani irin bugu da da hali da kansa zai dakatar da Baffa daga wannan zancen don bai hango ta yarda zamansu da Najma zai yi tsawo ba. Amma kima da martabar Baffan ta hana shi furta komai illa ha’diyar yawu mai kauri da ya yi ya d’agawa Baffan kai murya can k’asa Kuma ya yi furucin godiyar da ya san tabbas ba ta kai har zuciyarsa ba. Baffa ya d’aga kai ya ce “Ni zan gode maka Mujaheed da aka amince da auren mara kunyar yarinya irin Najma sai dai ina son ka yi hak’uri da duk abinda zai faru wata rana sai labari wata rana kuma da Kan ka zaka gode min.” Jaheed ya d’aga kai duk da bai hango sanda ranar zata zo ba in dai har da Najma yake tare yarinyar da ta tashi da tsanarsa a zuciyarta tun k’uriuciyatta. Jaheed yana fita Baffa ya mik’e zuwa cikin gidan. Fuskarsa a d’aure ya shiga sashen Mahmeey a parlour ya zauna kafin ya saka Nasma ta kira masa Najma. Fuskarta a ko’de ta fito daga d’akin da alama ranar ma yini ta yi tana kukan. A gaban Baffan ta zube idanunta suka cigaba da zubar hawayen da suke. Baffa ya bita da kallo mai cike da nuni da zallar jin haushi kafin cikin takaici ya kira sunanta murya a kaurare. Najma da sauri ta d’ago kafin ta rusunar da k’wayar idanunta tana jin ko kasheta Baffa zai yi ba zata amince ta zauna da d’an mahaukaciya ba, da ta zauna da shi gwara ta gudu ta bar gidan. “Dole ne ki zauna da Jaheed in dai kina amsa sunana a matsayin mahaifi idan kuwa kin shirya goge sunana daga matsayin mahaifin Ki sai na ce Bissalam.” Ya furta mata kai tsaye kamar ya san abinda yake ranta. K’irjinta ne ya buga sosai murya a sark’e ta ce “Baffa bana son shi na tsane shi kamar yarda na tsani mutuwata Wallahi zan iya kashe shi na kashe kai na a duk sanda ya amsa sunan Mijina…” wani irin Mari Baffa ya bata, kamar an cillo Mahmeey cikin tashin hankali ta janye ta tana furta “Kada ka sake dukar min y’a akan wancan banzan shashashan…” Baffa ya d’ago ransa a b’ace yana kallonta ya furta “Idan kin ga bata amsa sunan Matar Jaheed ba sai dai idan na daina amsa sunan Ubanta……” wani irin jan burki Mahmeey ta yi kafin ta ce “Akan d’an mahaukaciyar?” Baffa ya d’aga mata kai cike da tabbatarwa. Mahmeey ta saki dariya kafin ta ce “Ai dama ni na san ba banza ka ke zaune da matar nan ba akwai wata a k’asa…” wani kallo Baffan ya mata wanda ya sata shiru ba shiri shi kuma ya mik’e yana nuna Najma ya ce “Ki shirya gobe kamar yanzu Mijinki zai d’auke ki zuwa gidansa.” Ba Najma ba harta Mahmeey sai da k’afafunta suka kasa d’aukarta suka zauna a k’asa cikin tashin hankali Baffa kuwa bai bi ta kan su ba ya fice daga sashen yana jin hakan da ya yi shine daidai idan har ya bar Najma bai aurar da ita ba tabbas Mahmeey zata iya b’ata masa tarbiyyarta. Mahmeey shiru ta yi kafin ta jawo wayarta ta fara kiran waya tana magana cikin tashin hankali. “A yi koma me ye akan lamarin nan, bana son a yi tariyar nan Don Allah Malam.” Shiru daga d’aya gefen kafin Mahmeey ta ce “Na yarda Malam koma me ye a yi masa idan ma haukata shi za’a yi a yi, ko kuma a birkita shi ya saketa dole.” Ta kashe wayar tana kallon Najma da ta kwanta a jikinta tana kuka. “Ki rufe min baki komai Malam ya ce zai zo da sauk’i abu guda muke so ki ba mu ha’din kai.” Najma ta d’aga kanta tana sakin ajiyar zuciya a hankali. Jaheed kuwa da jan k’afa ya shiga sashen Umma. Umma tana ganinsa ta san ba lafiya ba. Ajiyar zuciya ta saki a fili ta furta “Ka yi hak’uri Jaheed taka k’addarar kenan.” Ya saki ajiyar zuciya a hankali kafin ya d’aga kai ya kalli Najee da ta yi zuru zuru idan ba kallon tsoro ya mata ba sai yaga kamar har rama ta yi. Ya lumshe idonsa kawai kafin ya ce “Najwa kawo min Lipton tea, amma Honey zaki yi using ba Sugar ba.” Najwa da sauri ta mik’e don cika umarninsa. Tea d’in ya sha mai zafin gaske kafin ya sauke cup d’in yana sakin ajiyar zuciya yarda tea d’in yake da zafi haka yake jin zafi a zuciyarsa. Tsawon mintuna kafin a hankali idanunsa a lumshe ya ce “Baffa ya ce zata tare gobe.” Umma ta d’aga kai ta ce “Allah ya nuna mana yasa a ce gara da aka yi.” Bai amsa ba don ya san da k’yar hakan zata faru. Tsawon 1 hour ba mai iya magana a cikinsu kafin ya mik’e cikin rashin sukuni ya yi hanyar sashen mahaifiyarsa. Can yake so ya je ya yi kuka a jikinta ko ya ji sanyi a zuciyarsa. Jin motsi yasa Nene komawa ainahin suffarta ta mahaukaciya duk da rashin sukunin zuciya da ta tashi da shi hakan yasa idanunta suke cike jingim da hawaye. Jaheed ya zauna a gabanta jikinsa a sanyaye ganin kamar bata jin da’di ya d’ora hannunsa akan goshinta ya ji ba d’umi, sai sannan hankalinsa ya kwanta. Hannunsa cikin nata ya ce “Nene gobe zata tare.” Idanu kawai ta bi shi da shi, bai damu ba don sau tari tana kasancewa cikin wannan yanayin. Ya d’auke idanunsa a kanta. Suka zauna jigum jigum Nenne a Lokacin zuciyarta ta tafi tunanin irin rayuwar auren da Jaheed zai yi da matar da bata son sa bata k’aunarta. Ya da’de a zaune kansa a kan cinyarta yana zubar da hawaye addu’a yake Allah ya dawo da ita cikin hankalinta ta sanar da shi ko shi waye. Tsawon lokaci yana kwance kafin ya mik’e yana d’auke hawayen idanunsa ya fice daga d’akin. Kuka Nene ta saki sosai tana furta “YA Allah ka kai mu lokacin da zan sanar da Jaheed asalinsa….” Turo k’ofar aka yi idanunta ya fa’da cikin na Najwa da take kallonta cikin mamakin jin abinda ta fa’da don duk abinda ta fa’da a cikin kunnuwanta……… JIKAR NASHE CE. ✍🏽 Kin biya ko kuwa? Book 1 ne free Book 2&3 paid ne akan 500 kacal via 2118666253 UBA Sai a tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387. Na gode masu min waya min yi biki lafiya mun gama lafiya sai fatan Allah ya basu zaman lafiya. Na gode sosai K’UDIRAR ALLAH 12. NAZEEFAH SABO NASHE. 08033748387. Runtse idanunta ta yi gam sanin cewa Najwa ta gama jin abinda ta fa’da d’in, ga shi bata da ikon mayar da maganar cikinta da ta mayar. Najwa kuwa cikin mabayyanin mamaki ta k’arasa Wajenta jikinta a kasalance ta zauna daf da ita tana jan hannayenta ta ce “Nene na ji kin yi magana kada ki min pretending da gaske kin san asalin Jaheed duk shekarun nan ki ke walagigi da rayuwarsa sannan kika d’orawa kan ki cutar hauka na k’arya, me yasa kika aikata haka Nene?” Idanunta ta bu’de cikin na Najwa da itama ta kafe ta da nata idanun ko k’iftawa bata yi. Hawaye ne kawai yake sauka daga idanun Nene ta rasa yarda zata yi ta mayar da su a yanzu dai kam ta san ba zata iya k’arya ta Najwa ba don yarinyar tana da kaifin tunani da k’wak’walwa irin ta manya. Najwa ta sake jan hannunta tana matsawa a hankali ta ce “Ki sanar da ni Nene.” Nenen ta saki ajiyar zuciya a karo na farko bayan shekaru da dama ta yi magana da wani cikin hankali ba cikin pretending d’in hauka ba. “Ki yi alk’awari idan na gaya miki zai zama sirri tsakanin ni da ke ko Jaheed ba zaki fa’dawa ba?” Najee shiru ta yi tana tunanin d’aukan alk’awarin tana tunanin girmansa da raunin da zuciyarta take da shi wajen b’oyewa Ummanta abu don itace aminiyarta don haka ta tafi tunani. Son jin labarin yasa ta d’ago tana kallon Nenen ta ce “Zan d’aukar miki alk’awarin ba zan gaywa kowa ba sai dai bani da juriyar da zan iya d’aukar miki alk’awarin ba zan gaywa Umma ba.” Nene ta yi shiru don bata son Umman ma ta ji maganar sai dai kuma tana tunanin sanin Umman ba zai zama Aibu ba idan har ba Jaheed za su gaywa ba ita Kuwa bata son Jaheed ya san maganar har sai ta san sanadin yarda ta samu Mijinta. “Na Amince ki gayawa Umma.” Ta fa’da cikin sanyin murya da taruwar k’walla a k’asan idonta tsoro take ji sosai idan abu ya fasu a duniya har ya isa inda bata son ya je ta tabbata wad’ancan mutanen da suke harin rayuwarta za su iya kasheta. Gefe guda kuma nauyi da kunyar idanun Abba ne yake shirin mama ye tunaninta, da wani ido zata kare kanta da tsawon lokacin da ta d’auka tana jinginawa kanta hauka lamarin da girma da kuma Kunya. Najwa cike da zakwa’din son jin labarin ta dafata tana furta “Bari na kira Umma ki bamu labarin nan a gabanta.” Kasa hanata ta yi duk da k’ok’arin hakan da ta yi tana kallo ta fice cike da karsashi. Nene ta lumshe idonta a ranta tana furta shikkenan yau dai ta faru ta k’are komai zai bayyana kansa sai fatan Allah yasa su fahimceni su fahimci abinda yasa na aikata hakan. Daga yanayin fuskarta Umma Ta gane tana cikin wani tsananin farin ciki da har ya kasa b’oyuwa a cikin idanunta. Hannun Umman kawai ta kama tana furta “Umma zo ki ga.” Umman tana tambayar ta amma ba amsa jan ta kawai take zuwa sashen Nenen. A zaune suka samu Nenen, idanunta na zubar da k’walla. Najwa ta ce “Nene ga Umman yi magana.” Nene ta kasa magana illa ha’diyar zuciya kawai da take yi tana danne zuciyarta da take jin b’acin rai kamar yanzu komai ma ya faru. Umma kuwa cike da al’ajabi take kallon Najwa ta ce “Wai me ya faru kin bar ni a cikin duhu?” Najee ta saki ajiyar zuciya tana furta “Umma Nene tana cikin hankalinta yanzu zata miki magana.” Umma ta ware ido tana furta “Alhamdulillah bari na kira Baffanku na gaya masa da Mujaheed.” Da sauri Najee ta ja hannunta tana girgiza mata kai “Ki zauna Umma bana son ki kira kowa Nene bata son a san tana cikin hankalinta, duk tsawon shekarun nan Ashe ba hauka take ba….” Kallon da Umma ta yiwa Najwa ne ya sata ha’diye sauran abinda ta yi niyyar fa’da don idanun Umma sun nuna zallar mamaki da Jin abinda ta ce d’in. “Najwa bana son shirmen banza ta yaya zata jinginawa kanta hauka….” Da gaske ne Umman Jaheed ba mahaukaciya ba ce ni, amma ina son ki min afuwa ki kuma rufa min asiri a yau Zan sanar da ku asalina da abinda ya baro ni daga gida Amma don Allah ya zama sirri bana son ko Jaheed ya sani…” Turus Umma ta zauna a gefen gadon k’irjinta yana matsanancin bugu Baffa kawai take tsoron ya san labarin nan don idan har ya sani ba zai yafewa Nenne ba, ya tsani mutum mak’aryaci balle ita abin nata ya yi yawa ma sosai ta yarda ta yaudaresu tsawon shekaru ta musu wasa da hankali a zuwan mahaukaciya ce ya dinga kashe ku’dinsa a kanta a banza tabbas ba zai sake yarda da lamarinta ba. “Ki yi hak’uri ki yafe min dalili mai k’arfi ne ya saka ni aikata haka ba son raina ba.” Umma ta ja ajiyar zuciya tana ha’diyar yawun da bata shirya wucewarsa ba. “Shikkenan ina jin ki, me ya rabo ki da gida kuma wacece ke? sannan Ina son ki gaya min gaskiyar zance bana son k’umbiya k’umbiya..” Umma ta fa’da zuciyatta na sake rauni tana fatan Allah yasa Jaheed ba shege bane ta yi cikinsa ta gudu daga gida ta jinginawa kanta haukan dole. Nene shiru ta yi zuciyarta rawa take da matsanancin bugu, duk da a ranta tana son furta abinda yake ran nata wanda ya hanata sukuni shekara da shekaru sai dai wata zuciyar tana kwab’arta ga barin aikata hakan. “Yi magana mana.” Umma ta fa’da idanunta akan Nenen da ta ga hannunta yana rawa kamar ma jikinta b’ari yake. Don ta kwantar mata da hankali sai ta kama hannayenta “Ki yi magana In sha Allah Zan rufa miki asiri in dai Baffa ne ba kya so ya sani ko wani nasa ba zan bari ya sani ba balle shi, yanzu dai abinda na fi buk’ata sanin asalinki da yarda kika samu cikin Jaheed saboda ina jin tsoro a zuciyata ina fatan Jaheed ya zamo tsarkakken d’a ba kamar yarda zuciyata take tararrabi ba.” Sai sannan Nene ta saki ajiyar zuciya ta d’ago raunannun idanunta da suke zubar da k’walla ta zubawa Umman kafin ta lumshe su cikin muryarta mai sanyi ta fara ba su labarin rayuwarta…… ___________ Sunana Fatima wacce aka fi kira da Fatu a can garin mu na Gabas. A cikin masarautar aka haifeni a ciki kuma na taso na girma tunda iyayena bayi ne a masarautar. Tun bayan taso wa ta ban tab’a ganin sanda Iyayena suka zauna suka huta ba kullum a cikin wahala suke da har ta bayyana a jikkunansu ta hanyar rashin wadatuwar lafiya tattare da su. Sunan Mahaifiyata Inno mahaifina Kuma Babani, mutanene da suka nuna mana asalin soyayya da kulawa musamman ni da na zamo mace a cikin yaransu maza guda biyar. __________________ ~SHEKARU TALATIN DA SUKA WUCE.~ MASARAUTAR GABAS… Masarauta ce mai tsohon tarihi da girman gaske ha’de da k’arfin mulki da kuma gamammen arziki. Duk wanda ya san Masarautar gabas ya santa da wadatar arziki game da k’ak’karfan ikon mulki da ake gudanar da shi bisa son rai da zallar mugunta. Duk da Sarkin sarki ne mai adalci da kuma son kyautatawa al’ummar sa, sai aka yi rashin dace da wa’danda suke kewaye da shi su kuma mutane ne Mugaye da ba abinda suka sani sai zalunci da son bak’antawa talakawa kamar yarda tarihi ya nuna. Mahaifinsu Sarki Abdallah kafin rasuwar sa mutum ne shi mai nagartattun halaye wanda ya sanya mutane suke son sa musamman talakawa da ya zamo Katanga abin jinginarsu, basu tab’a kuka da shi ba kamar yarda a zamanin sa aka samu wadatuwar arziki aka rabauta daga talauci don kuwa ya d’agawa talakawa k’afa sosai ya kuma bu’de musu hanyoyin samun ku’di a sauk’ak’e ta yarda kowa yake washshalawa cikin farin ciki da ginuwar arziki. Y’ay’ansa Ashirin da takwas sai dai Babban d’ansa su biyu kacal mahaifiyarsu da ake kira Fulani ta haifa da shi da y’ar uwarsa mace guda Fatume, Shi Kuma sunansa Mukhtar da mahaifinsa yake kira abin zab’i. Soyayyar mahaifinsu ga Mukhtar soyayya ce mai girman gaske da baya iya b’oyeta a idanunsa kowa ya sani yana son Mukhtar ne saboda rauninsa da tsananin son addininsa da mahaifiyarsa ta d’ora shi a kai. Ya yi farin ciki sosai da samun Mukhtar a matsayin Babban d’ansa da zai gaji sarautar gabas saboda yarda halaye da d’abiunsa suka barranta da na y’an uwansa. Su Mutane ne masu zuciya mara alheri a cikinta sai gungumen Sharri burinsu kullum cusgunawa talaka da Kuma bak’anta musu kamar yarda suke d’aukan duk wani talaka wulak’antacce kuma k’ask’antacce. Sosai yake jan Mukhtar a jikinsa tun bayan da ta fara rashin lafiya da yake ji a jikinsa kamar cutar ajali ce ta kama shi ya dinga nuna masa dabarun Mulki da yarda zai dinga samun nasara akan Mak’iya koda sun nufoshi da Sharri ba abinda zai same shi da izinin Allah da kuma kariyarsa. Tun kafin rasuwar Mahaifinsu bak’in cikinsu a kan Mukhtar ya bayyana muraran ta yarda suke son ganin bayansa. Sun kuma sha kai masa Farmaki Amma Allah yana kareshi. Kafin mutuwar mahaifinsa Mukhtar ya yi aure da d’aya daga cikin y’ay’an Sarkin Yamma wacce ya yaba da hankalinta. Watanninta bakwai Allah ya yiwa Sarki Abdallah rasuwa. A ranar da kuma ya rasun Mukhtar ya haye kujerarsa ta Mulki inda aka na’da shi SARKIN GABAS. Nan y’an uwansa suka shiga Hassada da bak’in ciki iri iri ta yarda Mukhtar d’in ya dinga tsallake sharrinsu da Makircinsu har ma da k’ok’arin kashe shi da suke son yi duk da komai suna aikata shi ne a b’oye a kuma sirrance. BAYAN SHEKARU DA HAWANSA KAN MULKI. Bai tab’a samun haihuwa ba hakan ya ‘daga hankalinsa da duk wani mai k’aunarsa duk kuma inda ya je za’a sanar da shi lafiya yake ko da yake tabbas da gaske lafiya yake tunda Sau kusan biyar matarsa tana haihuwa d’an yana rasuwa ko kuma tun cikin bai girma ba sai ta yi b’arinsa. Bisa tilas Mukhtar ya Amince da shawarar y’an uwansa akan ya k’ara aure. Aka aura masa mata Uku lokaci guda suma dai sun d’an jima babu haihuwar hakan yasa Mukhtar ya tattara lamarin haihuwa ya jingineshi a gefe, musamman da aka wayi gari k’anwarsa ta yi hatsari ta rasu motar ta k’one k’urmus ko gawarta ba a cire ba, sai d’anta da ta bar musu a wajen Mukhtar ta tafi ashe sallamar kenan shikkenan Mukhtar sai ya tattara duk soyayyar sa da kulawarsa ta koma kan Abdallah k’arami da ake kira Halifa. Ya saka a zuciyarsa tabbas ba shi da rabon ganin d’ansa ne a rayuwa don haka ko Abdallah ka’dai Allah ya bar masa ya gode masa. Wata irin guguwar tashin hankali ta fara faruwa a Masarautar ta yarda akewa y’an mata fya’de bisa son rai dana zuciya wanda kowa ya shaida ba wanda yake aikata musu hakan sai jinin Sarautar da suke gidan musamman yarda samarin y’ay’an y’an uwan Sarkin suka girma suka balaga to fa a duk sanda suka k’yallara ido suka ga budurwa basu da buri irin suga sun keta budurcinta ko da da k’arfin tuwo ne. Sarki Mukhtar bai san da wannan labari ba, ranar da ya ji kuma hankalinsa ba k’aramin tashi ya yi ba. Ba shiri ya saka aka tara masa taron Mata da Bayi da y’an matan da suke cikin masarautar. Aka cika a filin da yake harabar masarautar zuwa lokacin a k’idaye an ketawa y’an mata hamsin mutuncinsu wasu sun samu ciki wasu kuma sanadiyyar haka sun rasa ransu, wasu kuma sun samu motsuwar kwanya. Sarki Mukhtar Bn Abdallah, ya dinga sakin ajiyar zuciya ana iya juyo sautin ta ta cikin loud speaker da take hannunsa, kafin ya yi sallama cikin sakakkiyar muryarsa mai bayyana tarin nutsuwarsa da kamalarsa. “Mun yi tur mun yi Allah wadarai da wannan abin da yake faruwa a masarautar Gabas, bisa zalunci da son zuciya an wayi gari ana keta Mutuncin y’an mata, don haka mun zauna da mahukunta masarauta ta yarda zamu saka ido sosai a

Chapter 7 of 16