Don haka zuciyarsa ta sake samun damar zurfafa da tunanin. Da k’yar ya mik’e ya shiga wanka don ya san a irin wannan lokacin Baffan baya amsar uzirin kowa na k’in zaman cikin parlournsa. Don haka ya daure ya fita daga part d’in samarin zuwa na Baffa sanye cikin doguwar rigar jallabiya fara sol data sake fito da fuskarsa data zama fayau alamun rashin lafiya kwance cikin kyakykyawar idaniyarsa.
A kuma lokacin Baffa da shi da ahalinsa su Haidar da k’annensa da ma hadiman gidan suka dawo gidan. Fuskarsu d’auke da murmushi mai bayyana asalin murnar da zuk’ata suke ciki, idan ka d’auke Haidar da tasa zuciyar take cike da raunin tausayawa Mujaheed na auren da aka aura masa ba tare da shirinsa ba, da ace Najma wata mutuniyar kirki ce da sai ya ce abokinsa ya yi dace k’warai da kyakykyawar mace ta nunawa da kerewa sa’a. Sai dai Najman Kyawun d’an miciji gareta.
A babban falon gidan Baffa ya zube inda anan duka ahalin gidan aka saba taruwa duk ranar juma’a a ci abinci a kuma yi wasa da dariya kasancewar Baffan mutum ne mai barkwanci a wasu lokutan idan yana jin nisha’di. Aka ta shigo da coolers na abinci masu kyau da inganci wad’anda daga ganinsu ka san an lashe mak’udan ku’di wajen siyensu.
Bata Abincin Baffa yake ba don haka hankalinsa gaba ‘d’aya bai kai kan abincin ba balle ya ga yarda Umma ta tsarashi Alkubus ne da Masa sai aka musu peppe soup na kaza dagargajajjiya sai zob’o da ya sha kayan k’amshi da fura mai sanyi a gefe da ta sha zuma. Burin Baffa ya tara su ya sanar da su abin alherin da yake ganin shi ya k’ulla. Don haka da k’yar ya hak’urcewa zuciyarsa aka gama cin abincin aka kwashe kwanukan tas kafin a yi addu’a aka shafa sannan Baffan ya yi gyaran murya ya yi sallamar data saka kowa da yake wajen ya tattaro hankalinsa da nutsuwarsa kan Baffan. Kowa ya ga yanayin fuskarsa ya san wani abu ne mai mahimmanci zai fa’da don haka suma suka sanya nutsuwa a zuk’atansu da kan fuskokinsu. Baffa ya kalli Najee ya ce “Maza ki kira min Nenne don abin ya shafe ta.” Gaban Jaheed ya fa’di jin abinda Baffan ya ce ya fara addu’ar Allah yasa ba wani lamari mai girma bane yasa Baffan ya buk’aci ganin Nennen a irin wannan lokacin don ba kasafai Nennen ta fiye son shiga taron mutane ba.
Nenne a zaune saman sallayar take hannunta d’auke da carbi tana ja. Sanin cewa ba wanda zai shigo a irin wannan lokacin yasa tana cikin nutsuwarta. Najee ta tura k’ofar tana sakin sallama, sallamar ta tsaya mata a mak’oshi ganin Nennen zaune cikin nutsuwa akan Sajjada tana rik’e da carbi. Nennen ma a firgice ta kalli Najee ta rasa kuma yarda zata yi ta riki’de ta koma mahaukaciyarta a fuskar zahiri. Najee ta shigo cikin d’akin tana sake mutstsike idanun ta don tabbatar da zahirin abinda ta gani. Da sauri Nenne ta aro tunanin dole ta sanyawa zuciyarta da wani irin sauri ta fara jan Carbin tana nuna alamun hauka a tattare da ita. Najee ta dubeta kafin ta saki ajiyar zuciya ganin da alama Nenen bata san abinda take ba ba mamaki yanayin haukan yau da sallah yazo mata. Ta mik’a mata hannu tana furta “Mu je Baffa na son ganinki.” Nene ta maimaita kafin ta mik’e ta bi bayan Najeen tana sake waro idonta kamar mahaukaciyar gaske suka nufi Babban parlourn Baffan da yake harabar gidan sai dai yana da k’ofa ta cikin sashensa da yake cikin gidan.
Baffa cikin nutsuwa ya nunawa Najwa kusa da Umma ya ce “Zaunar da ita.” Sannan ya gyara zama ya na furta “Dalili ne mai girman gaske yasa na taraku anan. Albishir d’in da zan muku ina kuma mai farin cikin furta muku a yau burin da na da’de da shi cikin zuciyata ya cika, zo nan Najma.” Najma da gabanta ya wani irin fa’duwa ba tare da ta san dalili ba ta mik’e jikinta na rawa ta isa gaban mahaifinta da ya ke kallonta kamar yau ya fara ganinta. Hannu yasa ya jata kusa da shi azuciyarsa yana fatan Allah yasa ta amince da k’addarar auren da ta k’ullu tsakaninta da Jaheed kada ta bujire masa. Dafa kanta ya yi yana fa’din “D’ago Najma ki gaya min wanene ni?” Tambayar ce ta mata banbarakwai don haka ta rasa amsar da zata ba shi illa ha’diye wani kakkauran yawu da ta yi, ta san koma wane lamari abin mai girma ne kuma ba mamaki ita ya shafa. “Ki yi magana ma.” Muryarta na rawa ta furta “Kai Babana ne?” “Kin amince da hakan?” Ta d’aga kanta wannan karan cikin rauni. Ya saki ajiyar zuciya yana furta “Ina da iko da ke ko bani da shi?” Kai tsaye ta furta “Kana da shi Baffa.” “Alhamdulillah ya fa’da yana sakin kanta ha’de da zura hannu a aljihunsa ya zaro ku’di bandir biyu yana mik’a mata, hannunta na rawa ta saka ta amshi ku’din hannu bibbiyu tana tunanin ku’din menene sai ta ji amsar daga bakin Baffa cikin kakkaurar murya yana furta “Alhamdulillah yau na cika umarnin Ubangiji na aurar da ke ga Mijin da ya dace wannan shine sadakinki, ki shirya wani watan In sha Allah zaki tare a gidansa zaki yi azimi na zab’a miki Jaheed a matsayin Mijin aurenki……” d’if ji da ganin wasu da dama daga cikin jama’ar parlourn ya d’auke na wuncin gadi. Jaheed ne farko sai Najma data kasa tantance abinda Baffan ya ce don tuni ta manta a duniyar da take da alama suman zaune ta yi. Sai Najwa da ta ji jikinta ya fara rawa jin a yau Wai Jaheed da take mafarki a matsayin Mijin aure shi ya auri Najma ba ita ba. Mahmeey kuwa tashin hankalinta ya fi k’arfin kwatance kamar yarda na Nene ya kasa b’oyuwa jin wai mara kunyar yarinyar data mugun tsanarta take kuma mata rashin kunya son ranta a gidan itace a matsayin Matar Jaheed sam ba irin matar da take masa Fata ba kenan. Umma kanta wannan ha’din bai mata ba da kuma Baffan ya yi shawara da ita da ta gaya masa Najee ce ta dace da Jaheed ba Najma ba. Mahmeey ta mik’e cikin tashin hankali tana kallon Baffa cikin gatsali ta ce “Amma dai Isma’il a mafarki ka d’aura auren nan ko? Don in dai ni na haifi Najma to sunan auren nan haramtacce a yanzu ba nan gaba ba wallahi sai ya sakar min y’a………..
A yi hak’uri ina busy biki ya sa kwana biyu ban yi typing ba yanzu ma daure wa na yi na muku….
JIKAR NASHE✍🏽
KUDIRAR ALLAH.
Page 6.
NAZEEFAH SABO NASHE.
Baffa shiru ya yi duk da yarda yake jin zuciyarsa na matuk’ar zafafa da jin rad’ad’in furucin Mahmeey idan har ya ce zai yi wata maganar ba zata zamo mai kyau ba, don haka ya rufe idonsa kawai yana sauraran kausasan kalaman da suke sake tafasa masa zuciya. Bata fasa fa’dar duk kalmar da tazo bakinta ba, game da Nene da Jaheed. “Ka rasa wanda zaka aurawa y’ata sai b’aragurbi wanda baa san asali da tushensa d’an mahaukaciyar da ka tsinto a hanya, d’an da tabbas ba shi da suna da ya wuce shege to wallahil azeem sai ya sakar min y’ata koda hakan na nufin komai ma.” Baffa sai a lokacin ya d’ago yana kallonta idanunsa suna bayyana wutar masifar da zuciyarsa take ciki. “Kika sake wani abin ya samu auren nan ki k’addara a bakin naki auren….” Daga haka ya mik’e ya kewayeta ya wuce don idan har ya cigaba da zama zata k’arasa kunyata shi a gaban jama’ar da suke ganin kima da mutuncinsa. Duk da dai a yanzun ma ba abinda ya yi saura. Tana ganin ya wuce ta juyo a fusace tana kallon Jaheed “Na fa’da maka ka sakar min y’a tun kafin ka yi aikin da ka sani don Wallahi ba ta yarda zan yarda na amince na ha’da jini da d’an mahaukaciya ba.” Runtse idanunsa Jaheed ya yi yana saurarar dafin kalamanta da suke kamar za su huda masa zuciya saboda tsananin zafinsu. Ganin lamarin Mahmeeyn k’ara ta’azzara yasa Umma mik’ewa cikin b’acin rai ta ja hannun Nene da take zaune kamar mutum mutumi tsananin tafasar da zuciyarta take ciki kuwa Allah ne ka’dai ya sani a wannan lokacin ji take kamar ta fasa musu sirrin da take aikin kudundunewa shekaru da shekaru. Umma tana jin sanda ta saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske sai dai bata cikin yanayin da zata gane mai ya janyowa Nenen ajiyar zuciyar. Jaheed ma ganin sun fita ya mik’e yana jin kamar ya kifa don jirin da yake d’ibarsa. Lura da haka yasa Haidar saurin mik’ewa ya rungumeshi ta gefe don kada ya fa’di. Mahmeey ta bi su da wani mugun kallo kafin ta isa wajen Najma da take zaune kamar mutum mutumi da alama mutuwar zaune ta yi ko nace suman zaune. Don Mahmeey tana tab’a ta ta yi baya ta fa’di Mahmeey ta saka salati da kuka lokaci guda tana furta Shikkenan Isma’il Ka kashe min y’a burinka ya cika dama duk gidan nan y’ay’a na ka sakawa ido.” Bai ma san me take ba don yana can cikin d’akinsa zuciyarsa da ransa a jagule ji yake kamar ya fito ya zabga mata saki uku. Ruwa ta d’ebo ta watsa mata sosai a fuska sai a lokacin ta kawo wani gwauran Numfashi tana kallon Mahmeey ta ce “Allah yasa mafarki nake Mahmeey ba gaske ba, idan gaske ne wallahi zan iya kashe kai na…” Mahmeey ta yi saurin rufe mata baki kafin ta ja hannunta tana furta “Mu je Najwa ki k’addara mafarkin ki ke don wannan auren sunansa wasa Wallahi ko zan yi yawo tsirara ba zan bar auren nan ba sai na lallata shi.” Kuka Najma ta fashe da shi sosai sanin cewa ba mafarkin take ba wato ta tabbata dai an d’aura mata aure da mutumin da tafi tsana tab’ akwai tashin hankali kenan.
****
Umma kuwa Suna fita direct sashenta ta wuce hannunta rik’e da Nene da take ta kakkarwa Umman tana jin yarda jikinta yake b’ari bata kawo komai a ranta ba sai tunanin ko hayaniyar da aka yi ne ya tsorata ta.
Ta shige da ita d’akinta zaunar da ita ta yi gefen gado kafin ta rufa mata bargo tana furta “Ki yi barci Nenne In sha Allah bakomai.” Da zata lura Nenne wannan karan bata amsa mata maganar ba ba ta maimaita kamar yarda ta saba ba lumshe idanunta kawai ta yi don da gaske tana buk’atar hutun itama ba kuma ta buk’atar a hanata nutsuwa zuciyarta take buk’ata da aiwatar da shegen tunanin da ya zame mata jiki ta Yaya cikin d’an Sarkin gabas ya shiga jikinta ba tare da ita ko Sarkin sun tab’a ganin juna a zahiri ba? Me ya faru ne? Ta fara tunano sanda lamarin ya faru kamar Majigi haka ya fara yawo a kwakwalwarta……..
************
Shekaru 29 da suka wuce…..
__________________________
Wani d’aki ne mai matuk’ar duhu da rashin wadatacciyar iska, a cikin d’akin Nene ce a zaune da k’aton cikin haihuwa ko yau ko gobe, tsawon watanninta takwas a cikin d’akin tun bayan bayyanar cikin jikinta da kai tsaye zata kira shi CIKIN KADDARA KO CIKIN KUDIRAR ALLAH. Tuni ta saba da zaman d’akin don ta tabbatarwa kanta zamanta cikin d’akin shine kwanciyar hankalinta fiye da bayyanar ta cikin mutane. Bata san dalili ba a duk sanda ta kalli cikin sai wani tsoro da firgici sun shiga zuciyarta, tsoro take ji irin tsoron da yake jijjiga k’wakwalwa gani take a duk sanda ta haihu a masarautar sunan kanta fillalle don ga duk wanda ya ji labarin jinin sarki ta haifa D’an Sarki na fari ne a jikinta wanda ita da kanta tana tsoron bayyana hakan ga mutane duk da ta san Cikinta halastaccen ciki ne da ko shi kansa Sarkin bai san da shi ba, ta yaya ma zai san da shi alhali bai san da ita kanta Uwar cikin a doron k’asa ba, bai tab’a ganinta ido da ido ba a zahiri bata sani ba ko a cikin mafarki, kamar yarda ita ma lamarin yake gareta kamar almara ko kai tsaye ta kira shi Mafarkin. Da wani baki zata gayawa Sarkin d’ansa Halastaccen d’a ne ba shege ba kamar yarda ta san mutane da dama za su yi hasashe. Ta yaya ma zai yarda da halaccinsa tunda ba wanda ya d’aura mata aure da shi? Me ya kaita? Tabbas ta san idan ta bayyana kanta ,tabbas shi zai zama tsanin tafiyar ta lahira. Duk da ita kanta dole ce ta saka ta aikata hakan da kuma barazanar d’aukar ranta.
Ta runste ido tana sakin wata zafaffiyar ajiyar zuciya ita gata k’addara ta kaita ga samun cikin d’an Sarkin bisa tursasawar Mutum guda da kai tsaye za’a iya kiransa mai son zuciyarsa ko kuma mai son zuciyarta, don takamaimai ta rasa a wani jinsi zata saka mahaluk’in da ya jefata cikin wannan sark’ak’iyar da babu mai fitar da ita sai Allah, Mace ce ko Namiji waye kuma a cikin masarautar? Abinda har kullum take wa kanta tambaya kenan tun bayan samuwar cikin nata, ba tare da sanin shi Kansa mai martaban ba, ta yaya ma cikin ya shiga shine abinda ta kasa sani ta hanyar ha’da shimfid’a ma’ana kusanta tsakanin Miji da Mata ko kuma ta wani lamarin can daban da Allah ne ka’dai ya barwa kansa sani, bata sani ba ba kuma ta san hanyar da zata bi ta sani d’in ba.
Abu d’aya ta sani a daren da komai ma ya farun ta tsinci kanta a wani killataccen d’aki mai kyawun gaske wanda zata iya cewa ba tab’a ganin irinsa ba ko da a cikin fina finai. Tana kwance ta ji kamar shigowar mutane suna magana k’asa k’asa da alamar farin ciki a cikin muryar tasu duk da ta kasa banbance muryar tasu tunda sun bu’da ta sun kuma kaurarata inda duk masifar ka ba zaka iya shaida mamallakin muryar ba ko da kuwa ka masa farin sani balle a ce baka san shi ba. Aka haske ta da fitila mai tsananin haske kafin cikin bu’dewar murya mai sanye da bak’ak’en kayan sink’if ya fara magana, “Burin mu ya cika mun gama namu aikin, abinda za mu jira yanzu shine bayyanar cikin a jikinta idan aka dace sai mu jira haihuwarta kafin mu k’wace jaririn ita kuma mu salwantar da rayuwarta. D’aya daga ciki ya ce “Wannan shine abinda ya dace da ita, an kuma umarcemu kada mu sake ta gudu kada mu barta a haske ma balle ta samu damar guduwa da zarar ta haihu kuma sunanta gawa don gudun tonuwar asirin mu.
Wannan shine abinda ya tayar mata da hankali tunda duk maganganun nasu sun yi su ne a cukurku’de ba kuma su bata wata k’ofa da zata gane dalilinsu na aikata hakan ba. Abu d’aya ta sani an tirsasa ta samun cikin ne aka kuma tsareta aka killace a wannan bak’in d’akin tun bayyanar cikin aka kuma saka manyan fadawa marasa Imani su tsareta su killaceta ba kuma za’a saketa ba har sai bayan ta haife abinda ke cikinta sannan a kuma k’wace d’an ita kuma a koreta bayan an haukatar da ita ko kuma a kasheta kamar yarda ta ji masu bak’ak’en kayan suna fa’da Hauka zata iya warkewa su Kuma basa son ta samu sauk’i ta tona musu asiri gwara kawai idan ta cika musu burinsu su kasheta, ta san za su iya tunda bata da wani gata iyayenta bayi ne da aka siyesu suke bauta shekara da shekaru bata san asalin su ba idan ma akwai zuwa yanzu ta san sun k’are tunda yak’i aka yi ya ci garin hakan yasa Iyayenta suka zama ganimar yak’i mamallakinsu kuma ya zo ya siyar da su a wannan masarauta mai cike da d’imbin tarihi.
Duk wannan maganganun ta ji su ne a daren da aka gark’ameta a d’akin. Bayan kwana biyu matar mai bak’in kaya ta kawo ziyara d’akin bata santa ba don bata bari taga fuskarta ba har ila yau ta kasa tantance muryarta don muryar tana fita a kaurare ne saboda bata san a san wacece ita, duka tana ji ta bada umarni. Abu d’aya ta sani koma wacece tana son cikin ne tana kuma muradinsa ba don ta cutar da shi ba sai don cika wani burinta a kansa, ta fuskanci haka ne ta hanyar abinci mai kyau da gina jiki da ake bata wanda ake son duk masu ciki sun ci, a duk kuma bayan satittika akwai likitan da ake sawa yazo ya duba lafiyarta da abinda yake cikin. D’akin ne dai a duk daren duniya ake kashe fitilun cikinsa daga waje switch d’in fitilun yake don haka idan suka gark’ameta bata da ikon sake ganin gaske sai kuma washegari ta inda suke da tabbacin ko Karen hauka ne ya cijeta ba zata fita da rana ba tunda ta san da zarar ta aikata hakan kai tsaye zata amsa sunan GAWA a cikin k’urataccen lokaci. Mutane na biyu kuwa da suke zuwa su ma ta lura suna buk’atar cikin sai dai ko misk’ala zarratin babu tausayi da imani a tare da su abinda ta lura kowa da abinda yake so game da ita ba kuma su san suna tarayya wajen son cikin su dukkansu ba kamar yarda alamu suka nuna Mutanen farko ba su san mutane na biyu sun san da ita ba kowa bulayi yake cikin duhu da kuma k’wak’war son cikin.
A lissafin su a yanzu cikin nata ya isa haihuwa don haka aka sake tsaurara matakan tsaro a bakin d’akin, ba wanda ya san da ita a ciki saboda girman masarautar can a gefen masarautar aka killaceta. Ganin hasken da ya gauraye d’akin yasa ta san safiya ta yi idan kuma ba safiya ba ce ta yi tabbas masu kawo mata ziyara ne, gabanta ya fa’di duk da basu kasance masu cutarwa a gareta ba amma maganar kisan ta girgiza hankalinta shi yasa a duk sanda ta gansu take tsintar kanta cikin wani yanayi mai bayyana tsagwaron tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Aka turo jibgegiyar k’ofa mai tsawon gaske wacce aka d’aure ta tamau da jibegegiyar sark’a don ta itace ma da sun bar kayarsu a bu’de don ta san ko Karen hauka ne ya cijeta bata isa ta tsallake umarninsu ba idan ba so take su yi gunduwa gunduwa da namanta ba, don kowa ya san Tarihin masarautar Sarkin Gabas bai fiye Zafafawa rayuwa kamar yarda wad’anda suke kewaye da shi suka zama
Mugaye na gasken gaske, suka kuma mayar da ran bayi ba a bakin komai ba su kashe wanda suke so a lokacin da suka ga dama da son ran Sarkin ko ba son ransa don shi dai kawai zaune yake a kan kujerar mulki amma don ya ci gadonta kuma a k’aidar garin duk wanda ya ci gadon kujera daga Ubansa babban d’a shi ake bawa mulki, hakan yasa ake wata irin rayuwa a masarautar kowa ya zama mugun kansa. Shi yake mulki amma a b’angaren gudanarwa mulki ya zama d’an kallo don shakulatun b’angaro suke da mulkinnasa su ci zarafi da keta Haddin duk wanda suke so.
Aka turo k’ofar da k’arfi, hakan yasa da sauri ta yi k’asa da kanta don basu bata damar kallonsu ba, ko kuma don ta saba a haka dama suke a gidan sarautar wasu mutane ne su marasa galihu da basu isa su yi iko ko da da yatsansu ba sai abinda aka zartar a kansu.
Takun suka shiga yi mai cike da firgitarwa da razanarwa k’amshin turarensu mai k’arfin gaske da ko ba a fa’dawa mutum ya san mai tsada ne ya cigaba da samun muhalli a cikin d’akin a duk sanda suka shigo sai d’akin ya yi kwanaki yana zuba wannan mayataccen k’amshin.
Zama suka yi a saman kujera su biyu ne dai kamar yarda suka saba zuwa, sai wata likita da take sunk’ife cikin nata bak’in kayan baka ganin komai a jikinta har fuskarta. Cikin tausasawar kalami dkamar ba wad’anda suke son cutar da ita ba suka bata umarnin kwanciya a kan gado don likitan ta mata awo, saboda a cikin d’akin har Scanner machine na duba yaro akwai. Likitan ta fara aikinta su kuma suka kafawa scanner d’in ido ta inda tas suke hango jaririn a cikin mahaifiyarsa yana ta wutsilniya da alama mai lafiya ne kuma namijin da suke fata, gefe guda kuma wani dunk’ulallen abu suke gani a cikin nata da suka kasa gane menene. D’aya daga cikin mutanen suka ce “Abin da aka fata ya samu, burin Uwargijiya zai cika ga yaro Masha Allah kyakykyawa da shi.” Na kusa da shi ya kalli likitan yana furta “Zuwa wani lokaci za’a yi tiyatar a cire yaron ita kuma daga nan ka san yarda zaki mana da ita Uwargijiya dai ta gaya miki bata son ko yatsanta a bari so take ana zaro Babyn a aika da ita barzahu ta yarda ba wani balli da zai tashi daga baya.” Doctor ta saki murmushi tana fa’din “Ai haka za a aikata kamar yarda ta ce don har na tanadi Allurar da zan mata da zarar na gama mata theatre d’in, dole ne cika burin Uwargijiya.” Suka shek’e da dariya ba tare sun damu da ita ba duk da sun san tana ji sanin cewa baiwa ce ba abinda za ta iya yi yasa suka saki jiki suke fa’dar komai a gabanta.
Aka umarceta ta mik’e ta zauna sannan aka turo wani kwando gabanta mai cike da abin sha masu k’ara jini da kuzari. Tashin hankalin da take ciki bai hanata ci ba don ta san bata isa ta ce ba zata cin ba, ko da kuwa idan ta ci za tayi amansa bata da wannan damar. Ta ci sosai aka kuma bata tatacciyar madarar shanu mai d’umi ta sha kafin su fice su barta a d’akin cikin gigitaccen tashin hankali. A tsorace take a tsorace da kalaminsu da kai tsaye yake nuna kasheta za suyi bayan sun cire abinda suke buk’ata. Wani hawaye masu zafin gaske suka zubo mata tausayin kanta take yi na rashin madafa cikin kuka take furta “Ya Allah ka zama gata na kafin jibi.” Tunda a jibin aka ce za’a cire cikin ita kuma su kasheta…..
JIkar Nashe✍🏽
(Free pages sun kusa k’arewa, Kin biya kuwa? Idan baki biya ba daure ki biya ta wannan account d’in y’ar uwa. Tsagwaron labarin na gaba wannan duk tsakure ne. 2118666253 UBA. Sai ki tura shaidar biya ta number kamar haka: 08033748387.
KUDIRAR ALLAH.
Page 7.
NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
(Ina barar addu’arku an min mutuwa kada kwana biyu ku ji ni shiru. Nagode ku cigaba dai da biya In sha Allah nan da kwana biyu za mu d’ora.)
Ina godiya Aysher Adam (Ayshacool K’anwar maza)
And
Na’ima Sulaiman Sarauta (Nimcyluv)
Bisa k’ok’ari da suke wajen ganin littafin KUDIRAR ALLAH ya samu karb’uwa nagode sosai really appreciated. 🥰
————————
Tunda kashegari ta yi hankalinta ya sake tashi, tsoro da firgici ya sake shigarta ta sani sarai kwana d’aya ya rage mata a duniyar gaba d’aya idan har suka cire cikin za su aiwatar da kisan kamar yarda suka fa’da.
Shiru take zaune a cikin duhun, zuciyarta ma ta kasa aikinta yarda ya kamata, balle har k’wak’walwa ta karb’i sak’on itama ta yi aikin da take so. Hawaye ne kwance a idanunta hannunta ta d’ora saman cikin tana jin yarda yake watsalniya da harbawa da k’arfin gaske kamar mai shirin fitowa duniyar a lokacin. Wani irin ciwo ta fara ji na tashin hankali tun tana d’aukar lamarin wasa har ta tabbatar al’amarin ya wuce yarda take zato. Gumi ne ko ta ina yake zuba a jikinta. Cikin tashin hankali ta durk’ushe a k’asan carpet tana karanta addu’ar duk da tazo bakinta.
Ko ba a gaya mata ba, ta san nak’uda take ganin yarda wani ruwa yake bin k’afafunta ta sani da zarar ta haihu a yau ba sai gobe ba za su kasheta tunda abin da suke buk’ata ya samu.
Motsin da ta ji na bu’de k’ofar shi ya sake razanata ta dunk’ule waje d’aya ciwon nak’udar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 16