Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kara’de duk wani lungu da sak’o na d’akinta, kamar dai a cikin mafarki mai tasiri a kwanya da zuk’ata. Sai dai ko kafin k’iftawar ido waccen maganar ta d’auke da kuma ta bu’de ido bata ga kowa ba, sai iska mai k’arfin gaske data kara’de d’akin. Da gaske ta firgita saboda yanayin da aka isar mata da sak’on ya sha banban da inda ta saba karb’ar sak’o a kowane lokaci. Ta ja baki ta yi shiru ta kuma manta da maganar sai yanzu da take gaban Sarki maganar ta fa’do mata, bata ji komai a ranta ba illa wannan auren da za’a yi shine ake mata ishara da shi a cikin mafarkinta, me hakan yake nufi? Idan banda haka me yasa ranar idi zata kasance rana Mafi mahimmanci ga al’ummar gabas! Ta d’auke numfashi tana gujewa dukkan wasu tunani da suke sanya ru’dani a zuciyarta ta ayyana waccan ranar ta idi da za’a d’aura auren Murad da Amra shine abu mai mahimmancin. To za dai mu gani! Mai martaba ya gyara zamansa yana kallonta “Sai a je a fara shirin duk abinda ya kamata don sati uku kamar yau ne.” Fulani Raheena ta saki murmushin jin da’di da cikar burinta ta ce “In Sha Allah komai zai tafi successfully cikin nasara.” Mai martaba ya jinjina kai yana furta “Haka muke fata!” Daga haka ya mik’e don isa makwancinta ita kuma ta fice daga d’akin zuciyarta wasai tana jin kamar yau ne za’a na’da Abdu d’inta a matsayin Sarkin gabas. Fulani Saddik’a kuwa koda ta koma d’aki kasa nutsuwa ta yi duk ranta ya gama b’aci ga wani irin bugu da zuciyarta take yi mai k’arfin gaske. Da gaske ta sare da duk al’amarin Raheena, a komai ita take zama mai nasara me yasa koda yaushe ita take zama koma baya? Har mutane suke mata kallon itace BORAR SARKI! Ta zauna turus a gefen gado idanunta na tsiyayar da k’walla da yake nuna gazawar zuciyarta a fannoni da dama. Me yasa idanun Mai martaba kullum a runtse suke ba ya hango aibu ko bak’in halin Raheena? Ko da yaushe sune masu laifi har gwara ita akan wad’ancan sauran matan nasa da ba’a san meye matsayin su a gidan ba, don ba ma ya shiga sabgarsu baa san Kuma wani laifi Suka aikata masa ba. Tana wannan halin su Nene suka fa’do mata sai dai ta ji ta samu sauk’in fargabar ta tana jin komai ma zai zo mata da sauk’i, tabbas zata b’ullowa Raheena ta inda zatonta ba zai tab’a zata ba. Haka kawai sai ta samu kanta da sakin k’ayataccen murmushi ha’de da sakin ajiyar zuciyar da ta tafiyar mata da duk wani b’acin ranta. A hankali ta dinga jin sanyi na shiga kafofin jikinta zuciyarta na hucewa daga turirin da take. TABBAS IDAN RAHINA TA SAN WATA BATA SAN WATA BA! Ta fa’da murya a fili cike da karsashi. Ta zame a wajen tana mayar da kai ta kwanta. Da a ce dama tana da tsarki kwana zata yi ta na fil fili tana kaiwa Allah kukanta. A hakan ma cikin rashin tsarki ta dinga tasbihi ga Jalla ha’de da tsarkake sunansa. Sai ta ji ta sake samun k’warin gwiwar tunkarar duk Matsalolin RAHEENA da suke fuskantota, tana jin kamar burinta ya cika, kamar wancan burin da ya dad’e zaune daram a zuciyarta daf yake da cika, burin ranar da Raheena zata tozarta a idanun mutanen Gabas…. A d’akinsu Nene kuwa zaune suke bayan sun gama Cin abinci suna tattauna duk ta inda bincikensu zai kama, duk da Saddik’a ta ce su bar komai a wajenta, sai zuciyar Nene ta kasa amincewa da hakan ta fara tunanin hanyar da zata kai su ga b’ullewa ba tare da sanin Saddik’an ba, don sam bata hango sanayyar Saddik’an a cikin wad’annan caku’daddun al’amuran masu kama da almara ba. Ta saki ajiyar zuciya tana duban Najwa. “Je ki parlour kiga Fulani tana nan? So nake mu zame na fita na duba ainahin tsohon gidan mu ko iyayena suna nan daga nan zan fara.” Najee ta d’aga kai. Ta mik’e tana gyara k’ullin zanin da ta yi shi mai suna d’age gwanjo. Ta mudubin d’akin ta kalli kanta haka kawai ita da kanta sai ta bawa kanta dariya har hak’oran gatson na shirin cirewa, ta yi saurin mayar da su. Nene ma dariya ta yi tana fa’din “Ladidi Uwar muni, maza je ki ki dawo ki kira mana Umma mu gaisa jiya da yau duk ba mu gaisa ba.” Najwa ta fice tana fa’din “Yanzu kuwa.” Ba kowa a parlourn da alama duk sun yi barci kasancewr dare ne lokacin goman dare ta yi kuma gajiyar azimi yasa duk sun kwanta. Najee ta juyo da sauri ta sanar da Nene ba kowa. Nene ta saki ajiyar zuciya ta mik’a mata bak’ar doguwar rigar tana furta “Mu je to. Ta k’ofar kitchen da nasa kika sato mukullin za mu bi. Ko da Fulani ta kama mu Kuma a take a wajen ki fara murk’ususun ciwon cikin k’arya sai na ce magani na je samo miki, ai kin gane ko?” Najee ta d’aga kai, tana cigaba da saka doguwar zulumbuwar rigar wacce ta Hadiman Fulani ce suka sato. Tas suka fito kamar Hadiman b’angaren fulanin, don haka da wuya ka gane su. Suka fita parlourn a hankali bayan sun gark’amawa nasu d’akin D’an mukulli. Shiru harabar gidan ba kowa sai fadawa da suke wucewa jefi jefi. Ba ka jin komai sai kukan tsintsaye. Wajen duk ya canja don haka Nene taso ta rikice, sai dai cikin hikima da buwayar Allah sai ga shi ta je hanyar gidajen Fadawan. Kamar wasa kuma sai ta gane gidansu duk da an d’an canja fasalin ginin amma hakan bai hanata gane k’ofar zaurensu ba. Ta saki ajiyar zuciya hawaye na shirin zubo mata tunanin waccen rayuwar ya dinga dawo mata, rayuwa ce mai cike da jin da’di da k’uruciya ba komai a cikin zuciyarta a lokacin banda shirme da wasa sai ga shi Lokaci guda an jirkita tunaninta aka kuma aza mata babban tunani irin na manya a lokacin aka mayar da ita cikakkar mace mai juna biyu a cikin shekara sha shidda kacal! Ta d’auke k’wallar idonta tana fatan ta je taga iyayenta da rai cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali, ba kamar yarda zuciyarta take d’imauta ta da cewa iyayen nata tuni sun da’de cikin kushewarsu tsoron hakan Yasa ta tsayawa a zauren gidan tana ajiyar zuciya. Bata son shiga ta tarar da wasu sab’anin iyayenta. Najee ta dafata cike da rarrashi ta ce “Mu shiga Nene, in sha Allah alheri za Mu tarar.” Nene ta ce “Allah yasa Najee Allah yasa na tarar da su cikin lafiya, Allah Yasa ina da rabon ganawa da su.” Najee ta amsa da ameen cike da tausayi. Kafin ta saka hannu ta k’wank’wasa gidan, sai dai alamu sun nuna saya gidan ma aka yi. Don haka tana saka hannunta sai k’ofar ta bu’de, nan suka Hango filin tsakargidan da hasken fitila ya haske shi tarwai. K’asa ce malale a tsakargidan a share tas! Suka fara sallama daga cikin d’akin aka amsa musu kafin a fito ana furta Maraba lale wa muka samu da daddare?” Nene ta yi cak zuciyarta na bugu da k’arfin gaske ganin matar ba mahaifiyarta ba ce, wannan da take tsaye ba zata zarta sa’arta ba. Shikkenan ta faru ta k’are ta furta a hankali don in dai su Babi suna nan ba abinda zai saka a canja musu gida anan zasu rayu har su mutu matsayin su na gadaddun bayi. Matar ta dallaresu da fitila mai charging tana furta “Bayin Allah ban waye da ku ba?” Nene ta saki ajiyar zuciya kafin ta sake rufe fuskarta suka gaisa da matar sannan ta ce “Ainahin mutanen gidan muke nema” wani kallo matar ta bita da shi, duk da bata ganin fuskarta ta ce “Wane irin ainahin mutanen gidan sai dai idan b’atan kai kuka yi, ai nice a gidan nan tun bayan b’acewar mutanen gidan bayan b’atar y’arsu suma aka nemesu sama ko k’asa aka rasa, baa sani ba sace su aka yi ko guduwa suka yi oho! Sarki dai ya bada Umarnin ni da Mijina Sarkin Aska mu dawo nan shekaru talatin kenan kuma ba wanda yazo nemansu sai ku? Ku ‘din su waye?” Nene ta saki ajiyar zuciya kafin ta girgiza kai cike da k’arfin hali ta juya tana furta “Yi hak’uri baiwar Allah ina ji b’atan kai muka yi.” Ta ja hannun Najee da sauri suka bar gidan. Ko a hanya zuciyarta bugu take da tunanin ina iyayenta suke, a ina zata fara nemansu idan ma suna raye? Kuka sosai take sai dai mara sauti ba mai ji sai Najee da take jin yarda jikin Nenen yake rawa.Daidai k’erarren gidan nasa suka zo wucewa shi kuma ya fito kenan don shiga cikin gidan nasa ya ce karo da Najee da jikinsu ya ha’du, take ya ji wani irin shock ga shi ta buga masa kanta a k’irjinsa, cak numfashin Najee yaso tsayawa ta dinga kokawa da muryarta wajen ba shi hak’uri, sai dai yanayin tsoron da take ciki bai bar shi ya ji abinda ta ce ba. Ya zaro wayarsa cikin b’acin rai yana dallareta da fitila. A fili ya furta “What? You? Uban me kike da daddaren nan har kika zo kika bugeni kina ha’da wannan k’azamin jikin naki da nawa?” Yanayin yarda yake furucin a tsawace a kyamace ne yasa Najee zuba masa wani kallo ta cikin hasken fitilar ba tare da shirinta ba ta zabga masa harara ha’de da murgu’da baki…. Murad ya dinga jin wata wutar masifa tana juya rayuwarsa a zafafe ya fisgota da k’arfin gaske yama manta da batun k’azanta yasa hannu ya murje bakinta inda hak’oran roban suka tusge gaba d’aya……. JIKAR NASHE✍🏽 Da alama dai daf ake da barinki a baya, don kuwa part one ne free kuma daf yake da k’arewa ga shi kin tsaya son ku’di kin kasa biyan d’ari biyar kacal ko dubu d’aya ana jiran na bati! 🫣🤣 bana JIKAR Nashe ta murd’a kambunta book two ko kyallinsa ba zaku gani a whatsapp ba. Tura ku’dinki kai tsaye don gujewa barci kina tunanin ya aka yi aka samar da cikin y’an biyun? Kuma shin Nenen da Sarkin su ne iyayensu a gaske ko y’ay’an aljannu ne? 2118666253 UBA. Sai a tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387. JIKAR NASHE✍🏽 mai tak’ama da ikon subhana🤗 KUDIRAR ALLAH… 27. NAZEEFAH SABO NASHE.✍🏽 08033748387. (🤗 Wanda ya gane ya gane.) _________________ Cikin azama don gudun fallasuwar sirrinsu Nene ta janyeta ta tura a bayanta, tana kallon Murad d’in da b’acin ransa ya gama bayyana akan fuskarsa saura k’iris ya saukewa Najeen yatsunsa a kan fuskarta. Sai kawai ya saki guntsun tsaki yana furzar da wani huci ya cije leb’en k’asansa. Banda yana ganin girma da mutuncin Uwar yarinyar nan da yau ba abinda zai hana shi b’allata, idan kuma ya b’allata ya b’alla banza. Idanu Nene ta sauke masa hakan ya saka shi rusunar da nasa k’wayar idanun yana jin wani sanyi yana ratsa jiki da zuciyarsa wanda bai san dalilinsa ba. Ya dai samu kansa da dunk’ule hannu waje d’aya sai kuma ya juya da sauri cikin takunsu na sojoji ya bar wajen a zafafe kamar walk’iya. Nene ta saki ajiyar zuciya tana janyo Najwa da ta b’uya a bayanta jikinta na b’ari sosai al’amarin Murad ya bata tsoro, wato banda Nene ta janyeta so ya yi ya kifa mata mari. Nene dariya ce ta k’wace mata duk da bata cikin yanayin dariyar amma ganin yarda Najee ta tsorata idanunta suka firfito waje shi ya sata sakin murmushin da bata shirya ba. Najee ta lumshe ido tana fa’din “Wallahi Nene na fa zata mari na zai yi. Ga hak’oran bogin sun cire yau da asirin mu ya tonu.” “Banda na janyeki tabbas da marinki zai yi, ban san me yasa sam kurwarku bata jituwa ba, wuce mu je ki kira min Umman yara ina son magana da ita.” Najee ta bi bayanta da sauri suka koma cikin gidan Fulanin, cikin ikon Allah ba wanda ya fito don haka ba’a san har sun koma d’aki ba. A bakin gado suka zauna suna sakin ajiyar zuciya. Nene ta ce “Allah ya rufa mana asiri har muka je muka dawo ba wanda ya san mun fita.” “Ai kuwa da ba mu san ke za muce wa Fulani ba” “Yanzun ma ba abinda zaku ce min, tunda har kuna da wani sirri da zaku iya b’oye min.” Fulani ta fa’da tana. Fitowa daga wata k’ofa inda balconyn d’akin take. Jikinsu ne ta fara rawa a tsorace suka fara kallonta da mamakin furucin ta. Tana tsaye idanunta a kansu tana sakin murmushi ta ce “Ba ku same su ba ko? Baa san kuma inda suke ba?” Hantar cikin Nene da Najee ce ta ka’da suka dinga kallon Fulani a tsorace jin furucin ta daga sama, sai kace mai aiki da jinnu, wa ke sanar da ita sirrinsu ne?” Nene ta tambayi kanta sai dai kamar amsa da furucinta Fulani ta ce “Na san inda kuka je, kuma da kin gaya min can d’in zaku je zan sanar da ke ba zaki samu abinda kika je nema ba.” Shiru Nene ta yi idanunta Suka kawo ruwa tana duban Fulani ta ce “Kin san sun mutu ko? Don Allah sanar da ni labarin rasuwar iyayena.” “Ban san sun mutu ba, ba kuma zan ce miki suna raye ba. Addu’a ce kawai tsakaninki da su.” Nene ta sunkuyar da kanta tana jin harbawar zuciyatta yana tsananta. Fulani ta d’an bubbuga bayanta kafin ta fice daga d’akin cikin tafiyar rangaji tana furta “Asuba ta gari, just pray for them, Khairan In sha Allah.” Kukan Nene ta ha’diye tana bin bayan Fulani da kallo, kamanninta da yanayinta yana bata tsoro tabbas Fulani na aiki da jinnu ko wani k’asurgumin Bokan, idan banda haka ta yaya aka yi ta san sun fita tunda ba bin bayan su ta yi ba, sannan yanzu ta zo tana mata wasu zantattuka masu kama da harshen damo. Kuka sosai suka sha ita da Najee, kafin su kira Umma. Bugu d’aya ta d’auka kamar dama jiransu take. “Kuna lafiya ko?” Suka d’aga kai da yake vedio call su ke. Umma ta jinjina kai “Hope kun fara samun abinda muke nema?” Nene ta girgiza kai “Ba abinda muka samu Umma, komai a rufe yake ban san ta inda zan fara ba wallahi.” Umma ta d’an yi jim kafin ta saki ajiyar zuciya “Alright, idan baku samu ba zuwa Ranar Sallah sai ku dawo, as you all know ranar d’aya Ga Sallah Baffa yake dawowa daga Umara bana son ya dawo yaga ba kwa nan.” Nene ta d’aga kai haka suka cigaba da hira cikin nutsuwa Umma tana sake ba su shawarwarin da za su bi don a samu a cimma manufa. ************* Tuni shirye shiryen biki ya fara kankama a cikin masarautar zancen Auren Murad ya kara’de lungu da sak’o, kowa burinsa da fatansa ganin wannan ranar mai d’imbin tarihi a masarautar Gabas auren Yareema d’an Sarkin da baa san ta yarda aka samar da cikinsa ba. Fulani Raheena fitar da ku’di take kamar bata so, ta kuma rufe bakin Sarkin ruf ta yarda yake sakar mata dukiya kamar baya so burinsa kawai a fita kunyar jama’a duka k’asa ma ba iya yankinsa kawai ba. Akwatin lefe da wasu irin gwalagwalai ba a magana akwatinan kansu a bin kallo ne. Shi dai ango Murad bai san ma wainar da ake Toyawa ba, bai san wacece amaryar ba sai dai waccan yarinyar da suka ha’du rana guda ta tsaya masa. A k’ahon zuciya, sau tari sai ya nufi cewa a fasa auren sai ya ji kamar an nanna’de harshensa ya kasa magana, haka yana ji yana gani ya zubawa sarautar Allah ido. Fulani Raheena bata damu su ha’du da amaryar tasa ba, don an umarceta kada su sake su ha’du har sai an gama sihirtaccen aikin da akewa amaryar don haka ta dage tuk’uru wajen ganin tasa Amra ta aikata duk wani tsubbu da aka saka ta ta yi. Gefen Fulani Saddik’a ma, tsaye ta tashi da nata shirin kamar dai ba ita ke adawa da auren ba ta dinga shirya k’ayataccen biki da nata aljihun da na y’an uwanta aka fara shirin gagarumin bikin da ba’a tab’a yi ba a masarautar Gabas. Ranar da aka umarceta ta ha’da amarya da angon don saka soyayya mai zafi a zuciyarta. A ranar ta bata wasu magunguna ta yi wanka da su, sannan aka tsumata sa sihirtaccen turaren da ya kama jikinta sosai. Idanunta ya sha sihirtaccen kwalli. A d’akinta ta zaunar da ita kafin ta kira Murad a waya ta ce ya zo sashenta yanzun nan zai ga matar da zai aura. Ji ya yi kansa ya yi wata irin sarawar da bai tab’a yi ba ya zauna a gefen gado yana rik’e kan nasa har a lokacin wayar na kare a kunnensa murya can k’asa kamar mai mura Fulani Raheena ta ce “Dafatan Murad ya ji mu, kuma zai bi umarnin mu.” Da sauri ya mik’e yana ha’da murya wajen fa’din “Yanzu kuwa.” Ta kashe wayar tana shek’a dariyar da sai da Uwarta ta d’ago tana kallonta, itama da tata dariyar a fuskarta ita da kanta da ta haifi Raheena sau tari tana tsoron shu’umancinta. “Da alamu aiki ya ci d’an banzan kenan?” Uwar ta fa’da tana kallonta. Raheena ta sake dariyar sosai tana tura kuttun hannunta k’ark’ashin gado ta ce “Tun yaushe, yanzu zaki ga d’an banzan, ko nace gawar wata guda na bashi Zan shek’a shi lahira. Ko ciki ba zan bari ta samu ba, ko da yake ko ta samun d’an ba zai gaji Sarautar gabas ba tunda Ubansa ba ya raye kuma Abdul yana raye.” Uwarta ta saki murmushi tana fa’din “Allah ya ida mana nufi, ace Jikana ne yake sarautar Gabas da na fi kowa sa’a.” “Ki k’addara hakan a matsayin an gama.” Ta fa’da cike da tabbatarwa. Daidai lokacin da amintacciyar baiwarta ta shigo don isar da sak’on zuwan Murad. Ta amsa mata tana kallon Amra ta ce “Zo nan.” Amra ta bita suka shiga wani d’aki wani powder ta sake fesa mata a fuska sannan ta ce “Wuce ki je.” Amra ta juya jikinta a sanyaye suka fita da hadimar da take tsaye tana jiran ta, ita ta kama k’asan doguwar alkyabbar da take jikinta. Suka fita zuwa babban parlourn da Fulanin take saukar bak’i. Tun daga corrodor suke jiyo k’amshin turarensa da ya mamaye wajen. Amra ta lumshe ido a hankali tana jin wani farin ciki na ratsata da gaske Murad ya kusa zama mallakinta, ha’dadden namijin da duk garin gabas ake zancen ha’duwarsa, ga ku’di ga mulki ga kuma jarumtaka ta Soja. Idanunsa a k’asa suke don haka bai san da zuwanta ba. Har sai da ta yi sallama. Ya amsa a ciki sai kuma haka kawai ya samu kansa da ‘dago idanunsa take idanunsa suka sark’e cikin nata, wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya murza idonsa sosai don tabbatar da cewa itace ba gizon da idanunsa suka saba masa ba ne. Murmushi ta sakar masa tana tafiya a hankali zuwa inda yake ta zauna daf da shi cikin tausashshiyar murya ta ce “Ina yini?” Ido kawai ya zuba mata ya kasa amsa gaisuwar tata. Har ta gaji da kallon ta d’ago tana kallonsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce “Ke ce?” Dariya ta yi tana d’aga mata kai ciki son tabbatar masa da itace. Ya saki ajiyar zuciya ha’de da lumshe ido yana jin duk wata damuwa da ta tattare ya cushe a k’irjinsa ta kau. Farin ciki ya maye gurbin wancan bak’in ciki. Murna yake sosai da ya zamo itace zata zama mallakinsa matarsa nan da lokaci ka’dan, hak’ik’a shi mutum ne mai sa’a tunda ya auri matar da ta dace da rayuwarsa irin matar da yake buri da muradin aure mai shekaru da hankali wacce ta san kanta ba k’waila ba. A hankali ya furta Alhamdulillah. Shikkenan sai hira ta kaure tsakaninsu ya saki jiki suka fara tsara yarda rayuwar auren su zata kasance da ma shirin bikin gaba d’aya. Wannan shine babin da ya bu’de zafaffiyar soyayya a tsakaninsu yana jin itace maha’din rayuwarsa a yarda yake jin zafin soyayyarta a zuciya baya jin akwai wani abu da zai saka ya rabu da ita. _____\ Yarda Azimi yake gudu haka kwanaki suke tafiya kamar k’iftawar ido, da gaske rayuwar duniya k’arewa take, ba tare da bawa ya sani ba. A kullum kwanan duniya tafiya suke da ajalinka wasu su mutu wasu su rayu rayuwa mai kyau, wasu su rayu cikin cuta da rashin jin da’din rayuwar haka Allah yake so ba wai don baya son bawa ba sai don jarraba Imanin sa. Haka ne ya faru ga ahalin Masarautar gabas Sallah na k’aratowa ana sake shirye shiryen bikin Murad, har ya rage saura kwana d’aya kacal Sallah inda a ranar idine za’a d’aura auren Murad Mukhtar Mai gabas! Da amaryar sa Amra. Duk da azimi ne hakan bai hana bayyanar bak’i a ciki da wajen masarautar, duk wani hotel da ke garin Gabas na ya cika da mutane mak’il kowa burinsa a ce da shi aka d’aura auren d’an Sarkin gabas na farko. Tsananin yarda ake sanar da d’aurin auren ne yasa duka mutane da ake arewacin k’asar nan Suka samu labarin auren. Hidima ake kala kala ana yanka dabbobi iri iri da danginsu kaji da ma d’awisu. Fadar masarautar gabas a kacame take haka duk wani mai fa’da aji ya halarci wannan gagarumin d’aurin aure. Filin idi ya cika mak’il da jama’a ko ina motoci ne, da yake wajen Sallahr idin a cikin masarautar yake, mata manya da yara duk sun fito sallahr don haka Najee da Nene ma suna cikin tawagar Fulani da b’atacciyar shigarsu sun sha kyau cikin atamfa mai kyan gaske da Fulani ta d’inka musu. Suka kuma sake narka bak’in da ke saka su muni a fuska. Haka kawai Nene ta dinga jin wata irin fa’duwar gaba, don haka ta kalli Najee ta ce maza ki d’auko min waya a cikin gida. Sai dai kafin ta mik’e ta fara jin sanarwar za’a d’aura auren Yareema Murad da amaryarsa Amra. Itama Najeen nata gaban ne ya fa’di ta runtse idonta tana jan Hasbunallah! Kamar daga sama aka dinga jin magana a loud speaker “Kada a d’aura auren nan a matsayina na Uwar yaron na d’aura masa aure! D’if masarautar ta d’auka aka fara neman mai maganar don maganar zuwa tayi kamar daga iska. Can zuwa wani lokaci kowa yana cikin al’ajabi sai ga wasu irin manyan motoci suna bayyana a cikin masarautar. Kowa ya zuba ido gani wani babban bak’o ne wannan da yake tafe da jiniya ga motoci bak’ak’e wuluk da su. Tsawon mintuna biyu kafin mutane su fara fitowa daga cikin motocin suka kewaye mota d’aya suka zagaye ta kafin a bu’de tsaleliyar matar mai kama da larabawa saboda tsabagen kyau ya fito daga zabgegiyar motar. Idanunta sanye da wani bak’in glass. Da nik’ab. Kai tsaye babbar runfar da Sarkin Gabas yake zaune ta isa. Duk mutane suka zuba mata ido. Shi kansa Sarkin kallonta yake da mamakin wace mai k’arfin halin ce da har take kiran kanta da Uwar Murad! Gefe guda ma Nene mamakin take ta yarda tana zaune wata can daban take kiran kanta matsayin Uwar d’anta? A gaban Sarkin ta tsaya bata cire nik’ab d’in ba ta ce “Da gaske Ni ce Uwar Murad! Ko yanzu ka tsaga jikina zaka tarar da jininsa don haka na d’aura masa aure da zab’i na, ban amince ya auri yarinyar da kuke son ku aura masa ba. Yau ce ranar da ya kamata na bayyana kai na. Ta fa’da tana yaye fuskarta. Wani irin shock mutanen wajen suka shiga, musamman Nene da take zaune kusa da Fulani tsananin kamannin matar da su Murad ya bayyana Muraran ba mai sai ta furta ba, ko yanzu ta saka saje da gemu za’a iya cewa Murad ce ko Jaheed! Mutane da dama bayyanar fuskar matar ya girgiza tunaninsu hatta Sarki sai da ya yi suman zaune idanun sa cikin na matar da kai tsaye

Chapter 15 of 16