an buk’aci hukuma ta shigo ciki shi Kuma baya son lamarin ya kai ga hukuma har sai ya san silar afkuwar abin tukun. Doctor Saif ya d’ago kai yana kallon Faruk “Wuk’ar fa ta shiga sosai Allah ne ya kiyaye Amma sai an masa d’inki, ko waye ya masa wannan aikin gaskiya ransa ya so karb’a.” Faruk ya ja ajiyar zuciya ya ce “Matsala aka samu zan maka bayani daga baya, ba kowa ba ce illa matarsa illar auren dole kenan.” Doctor Saif ya jinjina lamarin yana saka masa drip ya ce “Ya zama wajibi ka fa’da a gida gaskiya a raba auren nan don duk wanda zai nemi kasheka da gaske mak’iyinka ne na gaske.” Hankalinsu ya kwanta ganin Jaheed ya samu barci bayan ya sha allurai na kashe zafi da ra’dad’in ciwo. Sai a lokacin Faruk ya kira Umma a wayarsa ya sanar mata don bai san ta inda zai fara yi wa Baffa bayani ba. Jikin Umma na b’ari ta juya tana kallon Baffa da ya kafa mata ido yana neman k’arin bayani. Ba ta da dalilin b’oye masa tunda fuskarsa ta nuna ya ji komai. “Kashe shi ta yi?” Ya fa’da cikin rashin nutsuwa. Umma ta girgiza kai “Bata kai ga kisan ba amma an kusa suna asibitin Saif clinic.” Baffa ya mik’e yana zura doguwar rigar jallabiyarsa hankalinsa a tashe da jin mummunan labarin nan, ashe rashin Imanin Najwa har ya kai nan.” Umma ma hankalinta a tashe ta bi Bayansa tana sake hijab d’inta.
A asibiti fuskarsa Cikin b’acin rai ya Zubawa Jaheed ido. Faruq sai k’ok’arin Kwantar masa da hankali Yake amma ina Baffa kamar tura lamarinsa ake burinsa kawai ganin Najma ya sauke mata b’acin ran da zuciyarsa take ciki.
Har safiya Jaheed bai farka ba, kamar yarda suma su Baffan ba su samu sun rintsaba. Sai shidda na safe sannan ya motsa ya bu’de idanunsa da suka masa nauyi. Ganin Baffa da Umma a zaune yasa shi saurin bu’de idanunsa ya yi k’ok’arin mik’ewa da sauri Faruk ya taimaka masa. Ya d’an harari Faruk yana furta “Shine sai da ka gaya musu me yasa Faruk?” Shi d’inma gintse fuska ya yi ya ce “Saboda ya kamata su sani, kai a tunaninka wannan maganar abin a barta ne?” Baffa kuwa wani yawun b’acin rai ya ha’diye kafin ya ce “Maza Faruk kama shi ya shiga toilet ya yi alwala.” Faruk ya aikata abinda Baffan ya ce. Sai da ya idar da sallah da Azkar sannan Baffa ya amsa gaisuwarsa yana furta “Ya aka yi wannan abin ya faru Mujaheed? Kuma bana son ka min k’arya.” Jaheed ya d’an saki ajiyar zuciya bai son gayawa Baffan ta’asar da y’arsa ta masa, sai dai Baffan ya Riga ya d’aure shi da jijiyoyin jikinsa don haka murya a raunane ya ce “Tsautsayi ne Baffa da kuma sharrin yarinta” Baffa ya yi tsit cikin tsananin b’acin rai jijjiga kansa kawai yake. Ba tare da ya furta komai ba har zuwa sanda Doctor Saif ya shigo duk sun kasa katab’us a d’akin kowa da tunanin da yake cikin ransa. Jikin da sauk’i” Doctor ya fa’da a hankali yana kallon Baffa. “Ko yanzu zai iya tafiya gida idan har zai iya kula da kansa baa son ruwa dai ya tab’a ciwon.” Baffa ya d’aga kai yana yiwa Saif godiya Faruk ne ya kama shi suka mik’e suka fita.
Baffa umarni ya bawa Faruk akan su fara zuwa gidan Jaheed. Jaheed bai so haka ba amma haka ya yi shiru yana ji yana gani aka isa gidan nasa.
Tana zaune a parlourn zuciyarta a dugunzume da b’acin rai da ciwon jiki da ma na zuciya. Bata ji d’uriyarsa ba don haka ta kasa ta tsare a parlourn tana jiran fitowarsa su d’ora daga inda suka tsaya. Sai ta ji alamar mota ta tsaya ta gyara zamanta sosai tana kallon kwalbar acid d’in da ke hannunta. Ta windown parlourn ta lek’a sai ta ga Baffanta da Yaya Faruq. Da sauri ta b’oye kwalbar tana ji suka shigo ganin Jaheed da bandage a wuya ya d’aga hankalinta don ba mamaki Baffa ya ji labari kenan shine abinda ya kawo su da sassafe. Fuskar Baffa kawai ta kalla hankalinta ya ninka na baya tashi. Ta zauna a tsorace tana gaida Baffan da Umma da suka zuba mata ido cikin takaicinta da tarin jin haushinta. Ba wanda ya amsa gaisuwar a cikinsu. Baffa ya kalli Jaheed ya ce “In dai ina da iko da kai Mujaheed kuma kana kallo na a matsayin mahaifi ina so ka saki yarinyar nan yanzun nan.” Jaheed cikin sanyin jiki ba na komai ba sai na tausayin Baffan ya d’ago yana kallonsa murya a raunane ya ce “Ka yi hak’…..” Da sauri Baffa ya dakatar da shi murya ba wasa ya ce “Just obey my commands.” Jaheed ya d’ago yana kallon Najma da ta yi k’asa da kanta ya ce “Na saketa Baffa.” Baffa ya saki ajiyar zuciya ya ce “Hankalinki ya kwanta ko? Sai dai ina so ki sani daga rana irin ta yau na zare ki daga sahun y’ay’ana kai kuma Jaheed Allah ya yi maka albarka ya baka mata ta gari, albishir d’in da zan maka Na baka Najwa nan da shekara biyu idan ta gama makaranta za’a yi bikinku, abinda ta maka kuma ina mai baka hak’uri ni na jawo maka.” Jaheed ya lumshe ido wasu hawaye masu d’umi suna saukar masa bai san wace irin soyayya Baffa yake masa ba. Umma tana kallon Najma ta mik’e “Burinki ya cika sai ki fito na mayar da ke gida.” Jikinta a salub’e ta mik’e tana kallon Jaheed d’in gabanta na wani irin fa’duwa haka kawai sai ta samu kanta da ganin tsananin kyan Jaheed d’in a wajen. Kamar ba zata tafi ba sai kuma ta juya ta bi Umma cikin mutuwar jiki. Suka bar Jaheed da Faruk a zaune Faruk yana ta lallashinsa akan ya hak’ura ya koma Gida. Jaheed ya girgiza kai “Faruk ba na k’i ta taka bane, amma bana son na koma gida hijira zan yi daga Nigeria gaba d’aya ko zuciyatta da ruhina za su huta.”
Ya fa’da yana lumshe idonsa
Wasu hawaye na zubo masa, haka kawai yake jin ransa ba da’di.
Yana zama kiran Khairi na shigowa cikin wayarsa runtse ido ya yi yana tuno da kyautar da Baffa ya masa duk da bai tab’a kwatanta Najwa a matsayin matar aure ba sai ya ji abin ya masa banbarakwai da yanzu yake tunaninta a matsayin matar da aka wa alk’awarin aurenta. Ya lumshe ido Najee fa! Najee da yake mata kallon k’anwa ta ina zai fara rayuwar aure da ita? Jikinsa ba karsashi ya d’aga wayar duk da baya so don ya san kukan da ta saba dai zata saka masa. Wannan karan madadin kukan ajiyar zuciya ya ji ta saki mai k’arfin gaske. “Habibi shikkenan ka rabu da ni? Na ji ance matarka ta tare jiya.” Shiru ya mata tausayinta na sake rub’anya a zuciyarsa “Yes ta tare amma mun rabu yau da safe.” Da sauri Khaireey ta saka Uban ihu tana furta “Alhamdulillah Habibi na gaya maka kai nawa ne ni ka’dai In sha Allah, ka zo mu gudu mu yi aure.” Shiru ya mata yana jin ta tana fa’dar duk abinda yazo bakinta ya yi k’asa da wayar ya sab’uleta daga kunnensa yana lumshe idonsa tunanin dramar jiya na sake zuwa ransa. Da k’yar ya ya kice tunanin ya rasa me yasa ya kasa mantawa da
Lamarin ko don sabon shiga ne a waccan harkar bai sani ba. Da k’yar ya yakice tunanin ta hanyar jan wayarsa ya shiga binciken k’asar da ya kamata ya gudu ya bar Nigeria da tashin hankalin da yake cikinta. QATAR ya ji hankalinsa ya tsaya a kanta don haka ya shiga binciken yanayin k’asar da ma makarantunsu gaba d’aya.
Baffa kuwa yana isa gidansa ya shige sashensa baya buk’atar hayaniya kamar yarda baya son a sake masa wata magana da ta danganci lamarin Najma tabbas ya yarda Y’ay’an yau daf suke da fin k’arfin iyayensu ya yi mamaki k’warai da gaske da Najma ta zama mai kunnen k’ashi ta kasa yin biyayya ga abinda yake so, duk da k’ok’arin sa k’warai da gaske wajen ganin ya kyautata rayuwarsu da abubuwan jin da’di ya inganta iliminsu bai san ta inda ya kuskure ba da har take tunanin ta saka masa ta hanyar bijirewa muradinsa. Bai k’i yiwa iyayensa biyayya ba ga yarda y’arsa ta masa ina ga wad’anda suka bijirewa iyayensu? Allah yasa mu dace kawai.
Umma da b’acin ran ta shiga b’angarenta inda ta samu Najee da Nene suna ta gyaran babban parlourn ta, tun d’azu suke zancen rashin ganinta a kitchen da sassafe kamar yarda suka saba, nan suka dinga addu’a da taraddadin Allah yasa lafiya. Nene na ganinta ta san ba k’alau ba don haka bata san sanda tray d’in hannunta ya fa’di ba, mummunan mafarkin da ta yi da Jaheed take ya dawo mata a sukwane cikin tashin hankali ta ce “Umman su Jaheed Allah yasa lafiya me ya faru?” Daidai lokacin da Baffa ya tura k’ofar parlourn ya shiga idanunsa akan Nene da take furucin……..
JIKAR NASHE. ✍🏽
KUDIRAR ALLAH.
15.
NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
________________
Cak numfashin jama’ar parlourn ya d’auke na wani d’an lokaci ganin yarda idanun Baffan suka nuna ya ji abinda Nene take cewa. Magana ce mai bayyana wanda ya fa’deta yana cikin nutsuwa da hankali ba alamun rashin hankali tattare da ita. Don haka Nene bata da ikon mayar da maganar cikinta. Baffa ya cigaba da taku zuwa cikin parlourn duk takun da zai yi kamar yana taku ne da bugun zuciyar Umma, Nene da Najee. Saboda tsoro da fargaba da zuciyarsu take ciki. Bai d’auke idanunsa daga kan su ba cigaba yayi da kallonsu d’aya bayan d’aya yana nazarin yarda fuskokinsu suke bayyana tsantsar rashin nutsuwa da zuk’atansu ke ciki. “Yaushe hankalinta ya dawo?” Ya furta idanunsa akan na Umma ba alamun wasa tattare da shi. Umma ji ta yi k’afafunta suna neman gagarar d’aukarta. Ta waske cikin son b’atar da tunaninsa ta ce “Ni kaina yanzu tambayar da nake shirin yi mata kenan ka shigo, maganarta kawai na ji a sama cikin nutsuwa da kamala mai nuni da cikar hankalin kwanyar d’an Adam.” Ta fa’da da k’yar tana k’ok’arin kawar da waccan fuskar firgicin zuwa fuskar kamala da zata bayyana ainahin gaskiyar da zuciyarta ke ciki. Kallo ya mata irin dogon kallon nan da yake ratsa cikin ido mai sanya mutum ko yana da gaskiya ya daburce. “Ke Nene wacece ke? Zuwa yanzu na tabbatar da kina cikin hankalinki.” Bakinta ne ya fara rawa kafin ta dafe kanta da take jin yana sara mata tana tsoron zuwan wannan ranar ga shi tazo mata a lokacin da bata shirya ba, me zata cewa mutumin da ya mata halacci a rayuwa? Sam bai kamata ta sake k’irk’irar k’arya ta gaya masa a wannan lokacin ba da tasirin idanunsa ka’dai zai iya jijjiga zuk’ata. Umma ce ta dafa ta cike da k’arfin hali ta ce “Baffa kamar bata gama dawowa daidai ba, ka bari idan ta samu nutsuwar zuciyarta na san da kanta zata maka bayani.” Baffa ya yi shiru maganar Umma na masa yawo a kai ya yarda da kaso tamanin cikin zancenta sai dai wata zuciyar na k’aryata duk abinda ta ce. Sai kawai ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya furta komai ba ya fice daga sashen gaba d’aya yana ji a ransa ko ba yau ba zai yi bincike da kansa. Umma ta saki ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo kafin ta nunawa Najee k’ofar d’akin Nene ta mata alamar su wuce don ita kanta yanzu hutun take buk’ata hutun zuciya da na kwanya gaba d’aya. Najee ta ja hannun Nenen da sauri suka shige sashenta.
****
Najma kuwa jikinta a sanyaye ta shiga d’akin Mahmeey da take kwance tana barci hankalinta kwance. Najma ta ja k’afafunta da suke Mata ciwo ta zauna da k’yar a gefen gadon tana kiran Sunan Mahmeey a hankali. Mahmeey ta bu’de idonta da kyar jin an kira sunanta daga sama. Da sauri ta tashi idanunta a bu’de tana kallon Najma cikin mamaki “Ke kuma daga ina haka da sassafe?” Najma ta sauke idanunta a hankali tana ji k’una da rad’ad’in zuciyarta na sake hauhawa da gaske lamarin ya mata ciwo ga keta mutunci ga sakin aure da ma bai karb’e budurcinta bane da sauk’i amma yanzu duk wanda zata aura a matsayin bazawara zai aureta. Ta runtse ido tana sake jin haushin kanta da Jaheed duk lokaci guda. “Ki min magan Malama kin tasa ni gaba kina kuka.” Mahmeey ta fa’da cikin b’acin rai. Najma ta saki ajiyar zuciya ta ce “Ya sakeni Mahmeey bayan ya cuceni ya k’wace budurcina.” What! Mahmeey ta fa’da tana ware ido “Wani banzan zance nake ji daga bakin ki? Yanzu zuwa kika yi ya yaudareki ya k’wace budurcin sannan don rashin mutunci ya sako min ke.” Najma kuka ta saka mai k’arfin gaske tana fa’dawa jikin Mahmeeyn. Kukanta ya sake harzik’a zuciyar Mahmeey ta dinga jin itama kamar ta saka kukan saboda tsananin bak’in cikin da zuciyarta take ciki. Tsanar Jaheed ta sake k’arfi a zuciyarta. Mik’ewa ta yi da azama tana zura hijabinta wajen Baffa zata je ta gaya masa rashin mutuncin da d’an gaban goshinsa ya aikata, bata san tuni Baffa ya san zancen ba.
Tana murza k’ofar bedroom d’in ta sameta a bu’de don haka kai tsaye ta danna kanta cikin d’akin, ba sabon abu bane wajen Baffa tuni ya banbance halayyar matansa ya san halin kowacce don haka ko da ya ji an danno d’akin bai bu’de idonsa ba don ya san Mahmeey ce. Tsaye ta yi a gaban gadon tana k’arewa fuskarsa mai bayyana kasala da tashin hankali kallo. “Sai ka tashi ai, ka ji tozarcin da d’an gaban goshin naka ya maka, bayan ya kusanci y’ar ka sannan da safe ya aikota da saki.” Wani irin murmushi na gefen baki Baffa ya saki idanunsa a lumshe ba tare da ya bu’de su ba ya fara magana “Ni na saka ya saketa.” Da sauri Mahmeey ta waro ido jin abinda Baffan ya ce “Kai fa kace ka saka ya saketa? To saboda me?” “Saboda sakin shi ya dace da mara tarbiyyar y’ar ki wacce zata iya saka wuk’a a wuyan mutum da niyyar hallaka shi, kin ci sa’a ma da baki tai Cesar a police station ba.” Gaban Mahmeey ya fa’di bata san sanda ta zauna a gefen gadon ba tana dafe k’irji ta ce “Kisa fa ka ce? Me zai saka ta kashe shi? Sai dai idan hawan k’awara ya mata ta ji zafi zata hallaka shi, amma ni ban yi mata hu’dubar ta kashe shi ba.” “Kin bata acid Ai ta watsa masa idan ba ki ce ta kashe shi ba kin ce ta nakastashi Wallahi Zainabu ki bi duniya a hankali.” K’irjinta ne ya shiga bugu ta mik’e jikinta a kasalance ta fice daga bedroom d’in tana jinjina k’arfin hali irin na Najma idan ta kashe shi bata san itama kasheta za’a yi ba? Hakanan ta koma b’angarenta ta tasa Najma a gaba da masifa, har sai da Najman ta fa’da jikinta cikin tashin hankali ta furta “To na tsane shi ne Mahmeey shi yasa.” “Hakan ne ya baki Lasisin kashe shi saboda wauta, kin san idan da ya mutu kema mutuwa za ki yi ko?” Rungume Mahmeeyn ta yi kawai don dole ta ja bakinta ta yi shiru jin jikin Najman ya d’au zafi sosai.
______
Najee jikinta a sanyaye ta fito daga kitchen ta koma bedroom d’in Umma. Haka kawai yau take jin wata irin fa’duwar gaba. Umma da take zaune d’auke da waya a hannunta tana neman wayar Faruk ta ji ko ya koma wajen Jaheed ta d’ago tana kallonta. Jikinta a sanyaye ta zauna gefen Umman ta zauna a bakin resting chair da take kujerar Umma ta d’ora hannunta akan goshinta tana furta “Me ya samu autata na ganki haka?” Murmushi Najee ta yi tana lumshe idonta ta ce “My heart beats faster Umma.” Shiru Umma ta yi sai yanzu maganar da Baffa ya yi ta fa’do mata na aurawa Jaheed Najee da sauri ta d’an janye Najee daga jikinta tana furta “Tashi Auta mu yi magana.” Bugun zuciyar Najee ya sake k’arfafa jin abinda Umma ta ce, a idanunta kuma ta hango ba wasa a duk abinda zai fito daga bakin ta. “Baffanki ya bada aurenki da zarar kin gama makaranta don haka ba ke ba kula kowane Namiji.” Najee ji ta yi zuciyarta ta daina aiki na wuncin gadi, zufa ta fara karyo mata da k’yar ta ce “Umma wa aka bawa aure na?” “Jaheed” Umman ta fa’da idanunta na zagaye fuskar Najee ta hango wani tsantsar farin ciki da ya kasa b’oyuwa a idanunta sai kuma ta ga ta runtse ido tana warasu a cikin na Umman ta ce “Me zai saka Yaya Jaheed ya aure ni bayan yana aurar Yayata.” “Allah ne ya halatta masa aurenki in dai basa tare da Yayar taki, abin buk’ata ki yi addu’a Allah yasa hakan shine alheri a rayuwarki.” Mamaki ne ya kashe Umma ganin Najee ba tayi wani bak’in ciki ba sai ma tarin walwala da jin da’di da ta gani tattare da ita, kamar dama jiran irin wannan ranar take. Umma murmushi kawai ta saki don ko da Najee bata fito ta fayyace sirrin zuciyarta ba a yanzu ta san da soyayyar Jaheed a zuciyarta a hankali ta furta “Allah yasa ku zamewa junanku Alheri.” Najee idanunta a lumshe kawai ta amsa a zuciyarta da ameen tana sakin ajiyar zuciya wanda Umman ta ji shi har cikin ranta.
Daga haka Umma zameta ta yi a jikinta ta nufi b’angaren Nene da take zaune cikin tunani da firgicin zuciya bata san wani kallo Baffa zai yiwa abin ba, shin zai mata uziri ko kuma zai k’ullaceta akan b’oye masa da ta yi. Turo k’ofar ya sake razanata a firgice ta d’ago da kanta da idanunta da Suka jigata take kallon Idanun Umma.
A k’asan leb’enta ta amsa sallamar wanda hakan yasa Umma bata ji ba. Ta zauna a gefen gadon tana kallon Nenen ta fara fa’din “Kada ki ce zaki nunawa Baffa gaskiyar lamari a yanzu, b’oye masa shine abu mafi alheri a wajena da ke baki d’aya. A yanzu ki nuna masa kin dawo cikin hayyacinki amma ba zaki iya tuna rayuwarki ta baya ba, duk rintsi ki nuna masa kin manta komai, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa, musamman a yanzu da yake cikin bak’in cikin abinda Najma ta yiwa Jaheed….” Da sauri Nenne cikin fa’duwar gaba ta d’ago tana duban Umma. Umman ta d’aga kai “Allah ya kiyaye amma da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, ta yi attempting soka masa wuk’a shine dalilin fitar mu cikin dare afujajan amma dai da sauk’i kuma Baffa a take ya d’au hukunci ya raba auren don idan aka bar su nan gaba ba a san ne zata yi ba….” Da Umma ta san a wani yanayi Nene take da bata cigaba da bayani ba, idanunta ne a waje ta dafe k’irjinta da yake mata matsanancin bugu, tana kallon Umman. Umma ta dafata tana furta “Bakomai fa ya samu lafiya cikin hukuncin Ubangiji bari na kira miki shi ki ji muryarsa bai san kuma kin dawo hankalinki ba ban san ya za’a yi ba yanzu.” Nene ta ha’diye yawu da k’yar tana furta tunda dai ya samu lafiya bar shi ba sai kin kira shi ba Umman Jaheed ina son in ga wani farin ciki zai yi idan ya fuskanci a yanzu ina cikin hankali na.” Umma ta d’aga kai tana furta “Shikkenan.”
————
Bayan kwana biyu Jaheed ya ji jikinsa da sauk’i duk wata azaba da yake ji ta kau daga zuciya da k’irjinsa. A yanzu abu guda ke damunsa masifaffiyar sha’awar da ya jangalowa kansa, bai sani ba ko don farin shiga a lamarin abinda bai tab’a aikatawa bane. Da zarar ya rufe ido ba abinda yake gani sai surar Najma shi dai ya san ba sonta yake ba sai dai ya ta’allak’a abin da sha’awa. Yau ma da sassafe ya yi wanka yana zaune ya dinga ganin kiran Khaireey a wayarsa a hankali ya kai hannu kan wayar ya d’aga muryar Khaireey a d’ashe sai dai ta nuna zallar farin cikin da take ciki ta ce “Jaheed ka zo Babana ya amince da auren mu, ka zo za ku yi magana da shi…….”
JIKAR NASHE✍🏽
KUDIRAR ALLAH
16.
NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
Talla! Talla!! Talla!!!
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.
*************
Wani irin duuuum Jaheed ya ji a kunnensa ya kuma kasa gasgata abinda Khairyn ta ce da shi har sai da ta sake maimaitawa. “Kana ji na? Nace Abba ya amince mu auri juna Yayyansa sun shiga cikin lamarin.” Sakin ajiyar zuciya ya yi ba tare da ya amsa mata ba saboda maganar zai iya cewa ta masa dirar mikiya ta ina zai fara sanar da Khairi abinda Baffa ya ce zai ha’da shi aure da y’arsa? Ta ina kuma a yanzu zai fara sanar da Baffa maganar auren Khairyn? Me Baffan zai d’auka akan hakan? Baya son y’arsa shi yasa ya kafe zai auri Khairi. Tabbas yana cikin TSAKA MAI WUYA LITTAFIN JANAFTY. Rashin amsar da zai bawa Khairi yasa ya zame wayar daga kunnensa bayan ya furta “Okay” cikin sanyin muryar da Khairi bata gasgata ta Jaheed ba ce,a irin soyayyar da suke wa Juna ta zata Jaheed da zarar ya ji amincewar Abbanta zai k’walla ihu da murna na tsananin farin ciki madadin haka Jaheed katse kiran ya yi yama kashe wayar gaba d’aya yana sakin ajiyar zuciya. Zuciyarsa hutu take buk’ata da dogon tunanin yarda zai rabu da kowa lafiya ba tare da ya sab’a musu ba.
Tsawon mintuna yana kwnace ya kasa aiwatar da komai kowace shawara ya yi sai yaga bata dace a wannan gab’ar ba. Don haka ba shiri ya kira wayar Faruk don shine abokinsa abokin shawararsa kuma wanda baya iya b’oyewa damuwarsa a yanzu d’in ma yana ganin duk shawarar da Faruk ya bashi da ita zai yi aiki tunda dai tasa zuciyar ta kasa aikin da ya kamata.
Ringing biyu ta yi Faruk ya d’aga wayar kamar dama jiran kiran yake. Jaheed ya saki ajiyar zuciya ya ce “Kana ji na Faruk?” Faruk ya amsa da “Yes ina jin ka.” Jaheed rasa ta inda zai fara ya yi saboda shi kansa Faruk d’in bai san fassarar da zai yiwa lamarin ba. Don haka kawai sai ya ce “Idan ba abinda kake don Allah ina son ganinka.” Faruk ya amsa da “Ba abinda nake, on my way to your house dama right now.” Daga haka ya kashe wayar.
Mintuna biyar ne suka kawo shi gidan Jaheed d’in. A zaune ya same shi ya zuba hannayensa biyu a k’ucninsa cikin dogon tunanin da yasa ko bu’de k’ofarsa bai ji ba balle shigowarsa, har sai da ya dafa kafa’darsa sannan ya d’ago da sauri yana sakin ajiyar zuciya. Faruk ya saki tsaki yana furta “Ban san sau nawa zan gaya maka dogon tunani illa ne ga lafiyar zuciyar ka ba.” Jaheed murmushi ya sakar masa yana furta “Tunani dole ne Faruk ga wanda tunanin ya kama, ni sai na dinga ganin kamar ni ka’dai duniya yake juyin waina da ni, kamar na fi kowa matsala a rayuwa.” Faruk ya zauna cike da tausayin Jaheed yana furta “Kai kake ganin haka, wani yana can gefe yana sha’awar taka rayuwar dafatan cewa dama shine kai. Yanzu kuma me ya faru?” Wayarsa Jaheed ya d’aga yana dialling numberr Khaireey. Bugu biyu ta d’aga muryarta na nuna kamar fushi take da shi. Ya saka wayar a hands free yana fa’din “D’azu Khaireey
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 16