Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma ta neme shi ta rasa don tsoron ya danne shi. K’amshin turaren da ta ji wanda ya banbanta da wanda ta saba ji ne ya sake d’aga mata hankali da tunanin wanene kuma? Taku ake cikin isa da tak’ama ta ji ana nufota gadan gadan bayan an haska hasken torch light ya hasko inda take. Duhu bai bata damar ganin kowanene ba sai dai koma waye ya banbanta da wa’dancan mutanen da suke zuwa. Murya a kaurare ta ji an bada Umarnin kunna fitila ta hanyar cewa “Kunna haske.” Kafin k’iftawar ido kuwa sai ga hasken ya gwauraye d’akin. Mai tahowar bai fasa iso wa inda take ba, har ya iso ya zauna a gefen gado duk da bata banbance mace ce ko namiji saboda yarda kayan da suke jikinsa suka b’oye duk wata sura da za’a tantance jinsin Namiji ne ko Mace. Ji ta yi cikin raunin muryar da ta kasa tantance tausayi ne yasa ta fita a sirrance ko kuma asalin muryar ce ta so fallasa kanta saboda firgicin ganin halin da take ciki. “Hasbunallah labor take” a ka fa’da a ru’de kafin kace me ta ga an mik’a hannu wanda yake tsaye daga gefe ya mik’o brief case cikin zafin nama aka ce “Fita ka tsaya a waje ka tabbatar kuma ba wanda hankalinsa zai yi yo nan d’in, dama ce muka samu sai mu gode wa Allah.” Aka fa’da cikin murya mai kauri da bayar da umarni kai tsaye. Da sauri mutumin da aka wa Umarnin ya fita zaro kayan aiki aka fara a gaggauce mai kayan basajan ya ko ta fara taimaka mata. Ta sha wuya sosai kafin cikin k’arfin ikon Allah ta haifo d’a namiji. Hamdala ta ji an yi, aka kuma d’aga jaririn ana kallonsa murya cike da rauni ta ce “Alhamdulillah Muhammad Murad ya iso duniya.” Aka fa’da ana sakin ajiyar zuciya had’e da sanya Babyn a k’irji aka ba shi kyakykyawan runguma. Ba tare da kyankyamin jinin da ke jikinsa ba. Ciwon ya lafa mata sosai tana kallon yaronta a hannun mutumin da bata san waye ba? Ko ganinsa bata da ikon yi. Tsaf aka goge shi da turaruka na alfarma kafin a mik’o mata shi cikin kaurin murya aka ce “Ki masa kallon k’arshe ki kuma k’addara a zuciyarki ko cikinsa baki tab’a d’auka ba balle ki haifeshi kin gama aikin ki, ni ba zan d’au ranki ba kamar yarda wad’ancan sakarkarun suke son d’auka burina samun yaron don haka zan miki sallama a yanzu zan kuma nuna miki hanyar da kai tsaye zata rabautar da ke daga mummuman kisan da za su miki, ki nesanta kan ki da masarautar gabas da duk abinda zai danganta ki da masarautar idan kina son zaman lafiyar ki kenan idan ba haka ba masu farautar ranki zasu iya yi miki kisan wulak’anci. Ki yi sallama da gidan jininki kisa masa albarka don ko bakomai ke kika haifeshi duk da ba zaki amsa sunan Uwarsa ba har abada!” Karb’ar yaron ta yi hannunta na rawa ta sumbaci goshinsa kafin ta furta “Allah ya yi maka albarka Muraad!” Wasu hawaye na zuba daga kwarmin idonta tana kallo aka karb’e d’an sannan aka umarceta ta shiga band’aki ta tsaftace kanta. Kaya masu kyau aka bata ta saka sannan aka bata wasu zinare masu tarin yawa. Daga haka ta ji an yi fito sai shigowar Basamuden mutumin ta gani. “Ka fita da ita can bayan gari kafin wayewar garin asuba idan kuma har aka Kamaku kada ka sake sunana ya fito a bakinka.” D’aga kai ya yi yana kallonta ya nuna mata hanya. Nene na kuka ta bi bayansa bata da yarda zata yi amma zuciyarta ta yi rauni ganin zata bar gidan jininta dama iyayenta bari na har abada. Tunda suka fara tafiya ta fara jin ciwo na sake turnik’e ta sai dai ta daure ta kasa furtawa drivern ciwon da take ji. Tafiyar awa guda ya yi kafin ya ajiyeta a wani k’aramin k’auye yana furta “Daga nan ki k’ara gaba, don nan d’in ma yana cikin yankin masarautar gabas idan kuma kin k’i ba ruwana.” Ya mik’a mata ku’di masu yawa a enveloped ya fisgi motarsa da k’arfin gaske. Nene ta durk’ushe a wajen bayan wata Bishiya tana hawaye saboda azabar ciwon da yake cin ta mararta kamar zata rabe biyu saboda tsananin azabar ciwo. Murk’ususu kawai take kamar wata haihuwar zata sake yi. Tsawon lokaci tana wannan halin kafin Allah ya kawo wasu mata guda uku sun dawo daga d’ebo itace. Da sauri suka rufa a kanta suna mamakin kasancewarta a wajen don dai bata yi kama da y’an yankinsu ba tafi kama da k’abilar fulani su kuma barebari ne. Kamata suka yi suna tambayarta abinda ya sameta? Ko kafin ta basu amsa sai ji suka yi ta yi wani nishi sai ga yaro ya sumb’ulo da sauri suka cafe shi. Mamaki ya kama Nene ganin wata haihuwar ta sake yi. Tsoron kada asirinta ya tonu yasa nan take ta aro haukan dole ta k’ak’aba wa kanta. Tana kallo matan suka ruga wata bukka sai gasu sun sake fitowa aka yankewa yaro ci iya kafin su kamata su kai ya cikin gida. Duk da bata so bin su ba sai dai ba yarda zata yi dole ta bi su tana zaro ido don gudun kada su tambayeta daga inda take. Wanka suka bata ta yi da ruwa mai zafi kafin su tambayeta kayan jariri a sannan suka gane mahaukaciya ce. Cikin tausayi suke bin ta da kallo aka samo kaya a cikin kayan yaran da suke gidan aka zunduma masa aka na’deshi cikin zani. Itama suka bata kaya ta canja na jikinta. Tambayar duniya da suka mata ta k’i ba su amsa sai zare ido take har suka hak’ura suka k’yaleta so take kawai su bata jaririnta ta rungume shi a jikinta ta ji sanyin rad’ad’in da ke zuciyarta. Da kansu suka fahimci tana son ganin jaririn suka mik’a mata shi ita kuma nan take ta ba shi Nono tana sakin ajiyar zuciya da Hamdala ga Allah da ya mata wata kyautar d’an bayan rasa wancan da ta yi. Cikin dare zuciyarta ta kasa nutsuwa da zama a wannan k’auyen kasancewar ya mata kusa da garin Gabas hakan yasa ta d’au jaririnta ta Goya ta sulale ta fice daga cikin gidan ba tare da sanin masu gidan ba. Har duhun asuba ya washe tana gararamba daga wannan sak’o ta fa’da wannan sak’o ta yi dabarar zame d’ankwalin kanta wanda hakan ya bayyana zallar haukanta kamar mahaukaciya sabon kamu. A bakin titi ta tsaya saboda kukan da yaron ya fara ta zame shi a daidai kuma lokacin Baffa ya taho da motarsa da gudu saura k’iris ya bugeta. Da sauri ya ja burki yana mamakin kasancewarta a wajen bakin titin. Ta’ajibi da tsoro ne suka kama shi ganin mace mahaukaciya da jariri a hannunta. Cak ya tsaya yana son taimakon ta gefe guda kuma yana tsoron taimaka mata. Sai dai zuciyar musulunci ta sanya masa tausayinta ya matso kusa da ita. Tana ganinsa ta rungume jaririn tsam a k’irjinta fuskarsa da nuna alamun bata son ta rabata da shi. Murmushi ya saki kafin ya furta “Ba yaronki zan karb’e miki ba, amma zaman ki anan hatsari ne ga sanyi da zai iya yi wa jaririn illa ki zo na taimaka miki.” Ta nok’e kafa’da sai da ya dinga lallab’ata sannan ta yarda ta bi shi, bayan ya yi mata wayo da kayan wasa zai siyawa jaririn a zatonsa da gaske mahaukaciyar ce. Bai san ras take ba kuma ta ji da’din taimakon da zai yi matan duk da bata san a garin da yake ba. Ta shiga motar ta bi shi suka tafi. Wannan shine dalilin ha’duwarsu da Alhaji Ilu wanda ya zame mata majingina ita da d’anta. Sanda ya isa gidansa matansa kawai ganinsa suka yi sun shigo da ita. Turus Umma da Mahmeey suka yi a lokacin Umma na da tsohon cikin Haidar. Murmushi ya saki yana furta kun yi mamakin gani na da bak’uwa ne?” Umma ta d’aga kai ita kuwa Mahmeey tab’e baki ta yi fuskarta ta nuna zallar b’acin rai. Ya ce “Tausayi da taimako yasa na d’auko ta daga ganinta ban santa ba ban kuma tab’a ganinta ba, sai dai yanayinta ka’dai zaka kalla ka san mahaukaciya ce ga sabon jariri a hannunta sai na ji zuciyata tana son ta taimakawa wannan yaron saboda nima nan gaba Allah ya taimaki zuri’ata.” Umma ta saki ajiyar zuciya tana jin ta yarda da duk abinda Mijinta ya gaya mata zuciyarta ta gamsu da son kyautatawa Baiwar Allahn da zuri’arta don haka ba ko d’ar ta kama hannun Nene data tsaya ta turje tana nuna alamun hauka. “Zo mu je abincin zan baki ki ci ba cutar ki zan yi ba.” Umma ta furta tana kallon idanunta cike da tausayawa. Ji suka yi kawai itama ta maimaita maganar tana sakin y’ar dariya ta bi bayan Umma. Mahmeey kuwa tsaki ta zabga ta wuce ciki haka kawai ganin farko da ta yiwa matar ta ji ta tsaneta ba tare da wani dalili ba. Wannan shine dalilin zamanta gidan Alhaji Ilu a kuma daren Umma ta haifi Haidar sai ya Zamana Umma ke kula da Haidar da Mujaheed Alhaji Ilu shi ya saka masa Muhammad Mujaheed.da Haidar ya girma baya iya fa’din Mujaheed ya masa tsaho saboda rashin iya magana sai ya mayar da shi Jaheed har bakin kowa ya amsa, Umma ce tasa suke cewa Nene har kuma a lokacin ba su san sunanta na gaskiya ba. Makaranta guda suka yi. Asibitin duniya ba wanda ba a kai Nene ba in dai na k’wak’walwa ne kuma a Nigeria sai dai duk inda suka je ana sanar musu ba wata matsala hakan yasa Alhaji Ilu ya fara tunanin ko asiri ne yasa Malamai suka fara mata addu’a amma lamarin ba sauk’i sai na Allah. A wajen Mahmeey kawai suke samun matsala ita da yaranta idan banda haka sai ta ce zaman gidan Alhaji Ilu bata da wani matsalar komai. Tana kaiwa nan a tunanin ta ja ajiyar zuciya mai nauyin gaske idanunta na sake zubar da k’walla tunanin waccen rayuwar tata ya sake k’arfi a zuciyarta da tunanin ko a wane hali Murad yake? ___________ Kuka sosai Najma take tana jin wani irin zafi da ciwo a zuciyarta kafin ta mik’e da sauri kamar wacce aka tsikara bata tsaya ko ina ba sai sashen da d’akunan su Jaheed suke. Da azama ta tura d’akinsa saboda tashin hankali kanta ko d’ankwali babu. Riga da wando ne a jikinta. Jaheed da yake zaune gefen gado ya yi nisa cikin tunaninsa ya d’ago yana zuba mata manyan idanunsa kafin ya lumshe su yana fa’din “Matsala, Baffa ya ha’da ni da wahala.” Ya furta hakan a zuciyarsa yana watso mata wani kallo da ya kusa yasa mata tsoronsa a zuciya. Sai dai ta matse tana dubansa cikin k’asan ido kallo mai nuna zallar bak’in cikin da zuciyarta take ciki. “D’an Mahaukaciya zuwa na yi ka sake ni….” Ya d’ago yana bata Wani irin kallo kafin ya ciji leb’ensa kawai yana jin zuciyarsa kamar ta fito daga k’irjinsa don azabar tsanarta da yake ji a zuciyarsa. Me zai yiwa yarinyar nan ta san shima ba wai sonta yake ba, yana son a yanzu ya goge rainin da yake tsakaninsu ya dasa mata bak’in ciki ita da mahaifiyarta a zuciyarsu wanda ba zasu tab’a mantawa da shi ba. Auren ne basa so suke kuma adawa da shi ya zama dole ya nuna musu shi kuma yanzu yake son auren. Don haka a zafafe ya fincikota ta fa’da jikinsa yana jin lokaci yazo da zai keta mata mutuncin ta na y’a mace abinda dai ya san da shi take tak’ama………… JIKAR NASHE✍🏽 Kin biya ko kuwa kina lak’ai lak’ai… haba Hajjaju kada 500 ta hanaki morar littafin nan yanzu fa aka fara.. shin Ina Murad? Su waye mutane biyun da suke jefar rayuwar Nene cikin tashin hankali kuma kowa da burinsa a kanta? Mhmmmn lamarin fa mai girma ne…. Ki biya 500 ta wannan account d’in 2118666253 UBA sai ki tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387. Special 1k. KUDIRAR ALLAH 8. NAZEEFAH SABO NASHE. 08033748387. ————— Jikinta ne ya fara rawa sosai tsoro mai tsanani ya bayyana akan fuskarta ganin abinda yake shirin aikatawa. Ta bu’de idonta sosai tana kallon yarda suka samu kusanci da shi. Runtse idonta ta yi hankali tashe ta ce “Me kake shirin yi?” Sai a lokacin ya dubeta fuskar mahaifinta ya gani a tata fuskar hakan yasa ya ji zuciyarsa ta karye har ya kasa aikata abinda ya yi niyya ya janye jikinsa yana zabga tsaki ya bita da wani wulak’antaccen kallo kafin ya nuna mata k’ofa yana furta “Get out Malama, ki sake kwatanta min abinda kika min sai na nuna miki akwai nisan banbanci a tsakaninmu da ke.” Bata yi magana ba don a lokacin hanyar tsira take nema. Mik’ewa ta yi da sauri tana gyara gashinta da ya yamutse ya mik’e tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu. Jaheed ya bita da kallo yana datse leb’ensa tsanarta tana sake kunnuwa a zuciyarsa da gaske ya tsaneta sosai da sosai mutunci da darajar Ubanta zai saka ya zauna da aurenta idan banda haka da tuni ya saketa tun a lokacin ma. Wayarsa da take k’ara ce ta dawo da shi cikin hankalinsa ya dubi wayar yana kallon numberr Khairi da ya haddace a kansa kamar karatu tana yawo akan screen d’in. Lumshe idonsa ya yi kafin a karo na farko tun bayan afku war abin ya ji yana son amsa wayar Khairin. Yana kara wayar a kunnensa ta rushe da kukan da dama shi take yi. Jaheed shiru ya yi yana sauraran kukan da yake sake karya masa gwiwa gwara ita idan ta yi tana da madafa ta kuma ji da’di ta tana da Uban da zai share mata hawaye, Shi fa? Ya saki ajiyar zuciya yana furta “Habibteey, am sorry please.” Kukan ta sake saki kafin cikin muryar kukan mai bayyana gazawa da rauninta ta ce “Dole na yi kuka Jaheed, bana son ka gaya min ka rabu da ni zuciyata ba zata d’auka ba.” Shiru ya yi tunda a zahiri ba shi da amsar bata. “Talk to me Jaheed.” “Me Zan ce miki Khairi? Abbanki ya datse alak’a mai k’arfin da take tsakaninmu…..” “Bai datse ba Jaheed zamu iya aure..” Murmushi ya saki irin murmushin da kai tsaye za’a kira na karayar zuciya ya ce “Ta yaya? Kin tab’a ganin auren da ba yardar iyaye a cikinsa ya yi inganci am sorry to say Baffa na ya d’aura min aure yau…” Ji ya yi ta saki wani irin gigitaccen ihu kafin ya ji shiru, maganar duniya kuma bata amsa ba. Hankalinsa ba k’aramin tashi ya yi ba yana tsoron kada ya rasa Khairin a duniya gaba d’aya. Ya dinga kiran wayar amma wayar nata ringing ba a d’aga ba. A hankali ya furta Ya Allah! Yana jin zuciyarsa na sake rauni. Hankalinta a tashe ta fa’da parlourn Mahmeey jikinta na rawa ta shiga kiran Mahmeeyn. Da sauri ta fito daga kitchen itama nata hankalin a tashe ta zuba mata ido. “Me ya faru?” Jikin Mahmeeyn ta fa’da a zafafe tana sakin kuka. “Ya cuceni Mahmeey.” Mahmeey ta saka hannu tana d’ago ya a razane ta furta “Me ya miki? Kada ki ce min ya kusanceki?” Girgiza kai ta yi kafin murya a d’ashe ta ce “Ya kusa dai Mahmeey don Allah ki san yarda kika yi kika raba auren nan.” Mahmeey ta saki ajiyar zuciya tana jin zuciyarta na d’acin masifa kafin ta ciji bakinta ta ce “Dole ma ya sake ki Wallahi ko ya k’i ko ya so.” Najma ta saki ajiyar zuciya a jikin Mahmeeyn tana fatan hakan ya tabbata da tafi kowa murna a duniya ta ina zata fara nuna Jaheed a matsayin Mijinta a wajen k’awayenta masu k’aryar tsiya da girman kai, a duk sanda suka san Jaheed Mijinta ne tabbas ranar duk wani ajinta ya zube. Baffa kuwa yana gama jin zuciyarsa ta sauka daga fushin da take ya kira Umma a waya. Umma bata yi k’asa a gwiwa ba ta je sashensa. A zaune ta gan shi da takarda da biro a hannunsa. Ta yi sallama ya amsa mata ba tare da ya dawo da annurin fuskarsa da ya yi k’aura tun d’azu ba. Ita dai Umma zama ta yi a gefensa zuciyarta tana addu’ar Allah ya kawo sassauci a cikin lamarin. Don kam bata hango ta yarda Najma da Jaheed za su yi zaman auren da har nan gaba za’a yi alfahari da shi ba. Baffa ya d’ago kai yana kallonta kafin ya mik’a mata takarda da biron ya ce “Rubuta min duk wani abu da ake buk’ata na kayan d’akin amarya kitchen da toilet parlour da komai ma.” Umma ta karb’i takardar tana son ba shi shawara tsoron yanayin fuskarsa yasa ta kasa bayyanawa don haka ta shiga rubuta duk wani abu da ta san shi zai dace da y’ar gata irin Najma ta rubuta tas sannan ta mik’a masa tana furta Allah ya tabbatar mana da alheri ya amsa da Ameen kafin ya sake mik’a mata wata takardar ya ce “Rubuta min list d’in kayan lefe.” Ta amsa nan ma ta shiga rubutawa yarda aka san ana lefen duk wata y’ar gata. Baffa ya amsa ya ce “Kin gama na ki je ki Allah miki albarka.” Umma ta amsa tana ganin wautar Mahmeey da Allah ya bawa d’and’asheshen suriki amma ta raina kyautar da ya yi mata Saboda wani banzan dalili nata ina ma Najwa ce ta dace da Miji irin Jaheed da sai ta fi kowa murna. ———MASARAUTAR GABAS…. Duk wanda ya kwana ya wuni a wannan masarautar ya san akwai wani babban taro da zai faru a masarautar, saboda yanayin yarda ake ta sake k’awata masarautar da abubuwan ado iriiri masu bayyana ana shirin yin wani gagarumin taro. Ciki da wajen masarautar an shafe tas da sabon paint fari tas da ya sake k’awata masarautar. Sarki Mukhtar yana zaune a fadarsa fuskarsa a washe tas da fara’a yana kallon jama’ar cikin Fadar ya furta “Alhamdulillah Allah ya kawo mu lokacin da a yau Murad ya gama karatu zai dawo gida, kamar yarda na d’aukar wa Jama’a alk’awari a duk sanda ya kai munzali ma’ana shekarunsa sun kai inda zai iya amsar duk k’addarar da ta same shi a lokacin ne zan sanar da shi wanene shi? To In sha Allah a yau Zan aikata hakan, duk da zuciyata na jin nauyin sanar da shi amma ya zama dole don sauke nauyin alk’awarin da na d’auka.” Masarautar ta d’au Kabbara ana kaiwa Sarki jinjina zuk’atan wasu da dama daga ciki sun zama fari k’al don sun da’de suna jiran wannan ranar. Ranar da za su san asalin Murad da yarda aka samar da shi, tunda abu ne sananne har yanzu ba a san Uwar da ta yi cikinsa ta kuma haifeshi ba, abu d’aya suka sani ranar da aka tsinceshi a bakin fadar cikin shiga ta alfarma a cikin showel na jarirai sai zabga k’amshin turare mai k’amshin gaske ya ke. Sai dai ba Uwarsa ba kuma alamunta, lamarin da ya tunzira jama’ar masarautar suka so yi wa sarki tawaye sai dai Sarkin y nemi alfarma yana rok’onsu su bari Murad ya girma zai sanar da shi ko shi wanene duk da likita ya tabbatar Murad d’in jininsa ne ta hanyar gwaji na DNA. Surutai suka fara tashi a fadar kowa yana fa’dar albarkacin bakinsa jama’a da dama sun d’auki maganar sarki a wani ma’auni na rainin hankali idan banda haka ta yaya zai ce Murad ba d’ansa ba ne duk da tsananin kama ta kwabo da kwabo da suka yi. Yaron da ko makaho ya shafa ya san Jinin sarki ne don ba ta inda ya bar shi. Suna jira dai su ji wannan karan ko da me Sarkin ya zo. Abu guda da suke so ya faru shine a ce Murad ta hanyar zina aka samar da shi to tabbas wannan dama ce suka samu ta tsige sarki don a dokar masarautar su ba su amince da Mulkin Mazainaci ba za’a ciresa daga sarautar sannan kuma ya bar garin ko da ta k’arfin tuwo ne. To fa! Shigowar manyan jeeps d’in da ake kira motoci masu numfashi ne da jini ya yasa ahalin masarautar suka san MURAD ya iso masarautar gabas, bayan shekaru Ashirin da barinsa masarautar zuwa k’asar England karatu. Koda motocin suka tsaya bai fito daga motar ba, baya ya yi da seat d’in ya jingina da kujera yana jin ciwon kai yana dawo masa. Ransa ya sake b’aci sam bai so dawowa masarautar ba da Bahba ya sani barinsa yai a can k’asashen jajayen kunnuwa inda ya fi wayo. Ya d’an rik’e kansa yana murzawa a hankali. Ta cikin tinted glass d’insa yake hango dandazon mutanen da suke baibaye bakin motocin. Ya d’an saki ajiyar zuciya a hankali kafin ya kalli driver ya ce “Open.” Iya abinda ya ce kenan ya ja bakinsa ya tsuke bayan ya cilla wata alawa mai dad’i bakinsa. Ya hau tsotsa a hankali yana fatan miskilancin kansa ya ragu ko ya ji da’din zama da mutane lafiya kafin a fara kiransa mai girman kai. Murmushin dole ya dinga lalubo wa a fuskarsa yana jifan mutanen da shi. Su kuma suna d’aga masa hannu. Kai tsaye Fada aka nufa da shi duk da baya son hayaniya amma sau tari yana son kasancewa da mahaifinsa da yake jin k’aunarsa har tsakiyar ransa, Ya sani tun haihuwarsa mahaifiyarsa ta mutu kamar yarda Bahba ya gaya masa ya sanar da kowa kuma ya gaya masa haka idan ya tambaya. Sallama k’asa k’asa ya yi kafin ya shiga cikin Fadar Sarki Mukhtar ya mik’e da sauri yana bu’de masa hannu shi Kuma ya fad’a ciki Sarki ya rungumeshi yana sakin ajiyar zuciya ha’de da hawaye masu bayyana tsananin Farin cikin ganin Murad d’insa sanye da kayan sojoji kamar yarda ya jima yana buri. “Alhamdulillah” ya furta a hankali yana shafa kansa da ya d’an durk’usa kasancewar ya fi mahaifin nasa tsaho a yanzu. Sha’awa suka bawa jama’a da dama a wurin wasu kuma tab’e baki suka yi suna jiran cikar alk’awarin sarki da ya sanar da su a yau zai sanar da Murad waye shi? So suke wani hali Murad zai shiga idan ya samu labarin don haka suka hau gyara zama suna jiran ji daga bakin Sarki Mukhtar. Murad ya d’an rusuna a gabansu ya kai gaisuwa kafin ya koma gefe ya zauna yana rik’e kansa da yake damunsa ciwo. Sarki ya dube shi ya ga alamar gajiya a tare da shi cikin kulawa da taushin murya ya ce “Ka je ka samu ka yi wanka ka ware gajiyar da ke jikinka idan ka huta ka fito akwai taron da aka shirya don kai a waje…” Murad d’aga kansa ya yi kafin ya mik’e da taku mai nuna k’arfi ya bi ta wata k’ofa da Hadimansa suka nuna masa zuwa cikin gidan inda anan sashensa yake. Yana dosar hanyar da zata kai shi sashensa ya ji wata magana da ta fisgi hankalinsa. “Yau dai Ai dole ya sanar da shi wannene shi da yarda ya samar da cikinsa tunda har yanzu ba wanda ya san Uwar da ta haifeshi? Asirinsa zai tonu yau tabbas zina ya yi ya samar da shi idan banda haka wacece Uwar Murad d’in da yake b’oyewa? Wani irin jiri ne ya fara d’iban Murad da sauri ya juya inda yake jiyo zancen da azama ya isa wajen….. JIKAR Nashe ✍🏽 Biya naki 500 ko kin huta da jiran typing kullum…. Saura shafi biyu free pages ya k’are….. 2118666253 UBA ki tura shaidar biya kai tsaye zuwa ga 08033748387 KUDIRAR ALLAH 9. NAZEEFAH SABO NASHE. 08033748387. Fuskarsa na nuna zallar damuwa ya dinga duban sashen da ya ji maganar sai dai bai ga kowa ba, kamar wanda Aljannu suka d’ebo zancen suka saka a kunnuwansa. Hankalinsa a tashe ya juya zuciyarsa na wani irin bugu na tashin hankali ya koma hanyar da zata mayar da shi Fada a yau yake son sanin ko shi wanene daga bakin mutumin da yake tunanin shine

Chapter 5 of 16