mahaifinsa. Ashe shi yasa koda wasa bai tab’a ganin hoton mahaifiyarsa ba a zahiri kamar yarda koda wasa bai tab’a jin sunanta daga bakin kowa ba, ashe ba a santa ba balle a kwatanta masa ita. Bai san inda yake takawa ba, saboda raunin da zuciyarsa ta yi ya isa cikin Fadar. Mamaki ya kama mutanen da suke cikin fadar ganin yarda ya shigo fuskarsa d’auke da tashin hankali ya zauna a gaban sarkin gwuiyoyinsa a k’asa, idanunsa da suka yi jajur ya zubawa Sarkin cikin nasa idanun ya ce “Ina son ganin hoton magaifiyata da kuma sunanta.” Wani irin shiru fadar ta d’auka sarki kuwa gabansa ne ya fa’di jin abinda ya fito daga bakinsa hankalinsa tashe ya zubawa Murad ido. Rashin nutsuwa da tashin hankalin da ya gani a idanun Murad shi ya tabbatar masa da ya ji wata magana da ta dangance shi. Ya d’an d’auke idanunsa irin wannan ranar yake tsoro yake kuma fargabar zuwanta ga shi tazo masa a lokacin da bai shirya mata ba. Ya zame masa dole a yau ya sanar da Murad ta hanyar da ya zo duniya ko da kuwa baya so. Mutanen da suke zube a fadar kuwa suma jikin su tsuma yake suna son su ji Mai Sarki Mukhtar zai ce da Murad tabbas ranar wanka ba’a b’oyen cibi. Murad idanun nasa ya cigaba da zubawa Sarki yana jin tsoron Sarkin ya fito ya sanar da shi ba shine ya haifeshi ba kamar yarda ya ji a yau. Bai san sanda ya fara datse leb’ensa ba a hankali yana furta “Ina jin ka, don Allah ka sanar da ni.” Ajiyar zuciya Sarki ya saki kafin ya dafa kafa’dar Murad d’in ya ce “Yau Zan sanar da kai duk abinda kake son ka sani Murad sai dai bana son ka min tambaya a kan abinda ba ni da masaniya a kansa.” Murad ya lumshe idanunsa yana d’aga kai.
Kunnuwansa suka fara jiyo masa labarin da Sarki Mukhtar Wanda ya d’auka a matsayin Mahaifi duk da kamaninsu sun zamo d’aya amma a yau zuciyarsa ta yi rauni yana tsoron Sarki ya zama ba shine mahaifinsa ba…..
—————-❤️🔥💫
Wata irin iska mai k’arfin gaske ce ta karad’e harabar gidan Sarkin, me tafe da wata guduwa da take barazanar d’auke duk wanda yake filin gidan sarkin. Hankali tashe mutane suka fara neman mafaka ganin yarda gari yake k’ara duhu kamar ba yanzu hasken alfijie ya Keto ba. Kowa neman inda zai tsira yake kafin narkakken hadarin ya zubo da ruwa wanda da alama ruwa za’a shek’a ba na wasa ba.
Cikin mintuna da basu wuce biyu ba ruwan ya kece, ruwa mai yawan gaske ake kwararawa mai ha’de da tsawa walk’iya ga wani irin mamakon ruwa da yake shatata a harabar gidan Sarkin, kowa zama ya yi a cikin masallacin don gudun fita wani abu mummuna ya faru da shi, don idan ana irin wannan ruwan komai ma yana iya faruwa ga mutum. Lazimin dole suka fara yi, Sarki da yake zaune a kan daddumarsa daga can gefe shima lazimin yake, duk da wata irin mummunan fa’duwar gaba da yake mai tsananin gaske bai hana shi yin lazimin ba. A jikinsa yake jin akwai wani abu na farin ciki ko Bak’in ciki da zai same shi don a duk sanda ya yi irin wannan fa’duwar gaban ana samun hakan ko dai farin ciki ko kuma bak’in ciki ko kuma mutuwa mai girma daga ahalinsa jininsa. Ya ‘dan runtse idanunsa yana matsa hannunsa a hankali a zuciya kuma yana jan Hasbunallah cikin nutsuwa ya dafe k’irjin nasa da ya dameshi da matsanancin bugu. Zuciyarsa ta raunana kamar yarda idanunsa suka tare hawaye, tsoro yake ji wani irin tsoro da yake fatattakar dukkan nutsuwar zuciya da gangar jikinsa. Baya son mafarkinsa ya zama gaskiya, kamar yarda ya saba a duk sanda ya yi irin wannan mafarkin to ya sai ya rasa d’ansa wanda aka haifa ko wanda yake cikin mahaifiyarsa. Sau sha bakwai yana irin wannan mafarkin da fa’duwar gaba sau Sha Bakwai d’in kuma dai yana rasa jininsa. Bai tab’a samun d’an kansa rayayye ba tsawon shekaru Ashirin da aurensa da matansa hu’du sai dai a haifa masa sati na zagayowa su mutu wasu ma a ranar da aka haifesun suke mutuwa kamar yarda wasu suke mutuwa a cikin mahaifiyarsu, yanzu ne yake saka ran samun Tilon d’a daga Uwargidansa bayan shekaru Goma rabonta da d’aukan cikin, a kuma wannan watan ake saka ranar haihuwarta, Bayan addu’oi da duk wasu abinda ya kamata yana ji a jikinsa wannan lokacin zai samu d’an kansa kamar yarda aka nuna masa a mafarki. Sai dai yanayin da yake ji yanzu a jikinsa ya firgita shi ya kuma sanya masa tsoron rasa gudan jinin nasa a karo na barkatai.
A hankali Ruwan ya dinga d’aukewa kafin kaji tsit ruwan ya tsaya cak, Iskar da take ka’dawa ma cikin KUDIRAR ALLAH sai ta d’auke tsaf gari ya yi Ni’ima ya yi sanyi, daidai lokacin da a masallacin aka yi addu’a aka shafa. Aka bu’de k’ofa kowa ya yiwa Sarkin Gabas d’in Sallama dafatan saukar Magajinsa lafiya wannan karan. Ya dinga amsawa cike da farin ciki yana kuma damk’ar ku’din da baya sanin adadinsu yana rabawa miskinai da talakawan cikin fadawansa duk wanda aka bawa sai ya fice yana sake jaddada addu’arsa ta saukar YARIMA mai jiran gado lafiya ya iso duniya lafiya daga cikin mahaifiyarsa.
Cinicirindon jama’a ne suka taru a k’ofar masallacin cikin tashin hankali ana kallon Jaririn da aka ajiye a gefen Masallacin cikin shigar kayan sanyi da alama kuma ba’a dad’e da haihuwarsa ba. Salati da Salallamin jama’a shi ya ja hankalin Sarkin ya kalli wani bafadensa da sauri yana masa nuni da ya je ya duba masa abinda ke faruwa. Sarkin Fada Yana zuwa taron jama’ar Suka d’an dare suka bashi wuri. Ya is a wajen Jaririn da aka kwantar Yana Kallo cike da mamaki shima kafin ya saka hannu biyu ya d’auko shi. Ya zuba masa ido wani abu yana fusgar hankalinsa game da kamannin Jaririn da kai tsaye zai iya cewa tabbas jinin gidan sarautar SARKIN GABAS NE. Saboda a tsawon lokacin da ya d’auka yana aiki a k’ark’ashin masarautar tun lokacin Mahaifin Sarki Abdallah Mahaifi ne ga Sarki Mukhtar wanda shine Sarkin yanzu ya san ahalinsu ciki da bai d’in su, kuma a duk lokacin da aka yi haihuwar shi yake karb’ar yaro ya mik’awa Sarki ya gani ya masa addu’a, to tabbas kamanceceniyar Jaririn nan da Sarki Mukhtar kai tsaye zai iya cewa babu banbanci! Don kamar yarda ya d’aukeshi yanzu a hannu haka ya d’au Sarki Mukhtar yana yaro, hoton Sarki Mukhtar sanda aka haifeshi ya dawowa Sarkin fada a rai yaga tabbas wannan yaron da yake hannunsa ba shi da banbanci da Sarki Mukhtar hatta zubi da tsarin shan girarsu. Cire mamakinsa ya yi tunawa da ya yi Uwargidan Sarki tana da ciki ba mamaki ita ce ta haihu aka yi musu bazata da haka, ba mamaki ta haka zata sanarwa da Sarkin haihuwarta idan kuwa haka ne ya tabbata Sarki ba zai kyaleta ba yarda ta yi masa wasa da yaron da aka haifa masa a yau. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya juya cikin sauri tunawa da ya yi sarki ne yake jiransa.
Zubewa ya yi a gabansa yana mik’a masa yaron. Da sauri Sarkin Gabas ya mik’e bakinsa fal fara’a ya amshi yaron yana masa kallon k’urilla shima dai nasa kamannin ya hango tattare da yaron, a hankali ya furta “Alhamdulillah! Allah nagode maka Allah yasa rayayye ne, Ubangiji kasa magajina ne.” Sai da ya yiwa yaron addu’oi sosai kafin ya d’ago ya kalli Sarkin Fada ya ce “Yanzu fulanin ta sauka kenan? Dafatan tana cikin k’oshin lafiya mu je na ganta, Fulani ta samar min da farin cikin da ban tab’a tsintar kaina a cikinsa ba ta hanyar haifa min yaro mai kama da ni kwabo da kwabo. Wanda tunda ake haihuwa ba’a tab’a samun mai tsananin kama da ni har haka ba.” Ya mik’e da yaron a jikinsa ya yi hanyar da zata sada shi da cikin gida wajen Matansa kai tsaye. Sarkin Fada ma da murmushi ya bi shi yana mamakin yarda yau ‘daya fuskar Mai martaban ta washe da fara’a har haka kuma yana hira da magana sosai kamar ba shi ba. Bai yi k’asa a gwiwa ba ya bi shi da sauri, don duk wani masoyin Sarki tilas ne yau ya taya shi murna.
Harabar wajen Matan nasa shiru sai kai kawon Bayi da suke yi jefi-jefi. Kowa ya ga Maimartaba Sarkin Gabas da jariri sai a yi saurin kai gaisuwa su kuma matsa gefe suna magana k’asa-k’asa don dai a kaf masarautar ba wanda yake da labarin haihuwar Fulanin an san dai tana da tsohon ciki, tun bayan bayyanuwar cikin nata kuma aka saka matakan tsaro sosai a b’angaren nata.
Kansa tsaye ya nufi sashen Fulanin, fadawansa suka fara gyaran murya Alamar kowa ya kintsa Mai martaba na nan tafe. Duka bayin Fulanin suka dare zuciyoyinsu da mamakin halartar Maimartaba sashen Fulanin abinda za su ce sabon abu a wajensu don dai ba su tab’a gani ba.
A Babban Falon Fulanin Sarkin Gida da Amintattun Fadawansa biyu suka ja tunga suka tsaya. Shi kuma mai martaba kansa tsaye ya shiga Parlour na Biyu kafin ya kai Parlour na Uku inda a nan D’akunan Barcin Fulanin suke. Sassanyan k’amshi da sanyin Ac na ratsa ko ina kamar yarda k’amshin k’asa ya mamaye hancinan mutanen GARIN GABAS. Gyaran murya ya yi kafin ya mur’da d’akin hannunsa d’aya d’auke da kyakykyawan jaririn da ya bayyana kamanninsa tun yana yaro. Shiru d’akin Fulanin ba komai sai k’arar A.c da alama wanka take don haka kansa tsaye ya zauna a gefen gadon yana sake k’arewa jaririn kallo wata irin k’auna da soyayyar jaririn na sake fusgar ransa ji yake kamar ya mayar da shi ciki don tsananin so da begen yaron. Ya saka tattausan leb’ensa ya ba shi sumba sosai yaron kuwa ya d’an bu’de ido yana kallonsa kamar ya san waye shi a wajensa ya yi k’uri yana kallonsa. Mai martaba ya sake k’ura masa ido Kafin a hankali ya furta Allah ya raya min kai Muhammad Murad. Sai kuma ya sake kai bakinsa ya sumbaci goshinsa. Yana murmushi ya sake cewa “Murad Mukhtar Abdallah In sha Allah kai ne magajina….” Daidai lokacin Fulani ta fito daga wanka jikinta sanye da rigar wanka tana tsane gashin kanta da towel d’in da yake hannunta. Turus ta yi baki bu’de tana kallon Maimartaba da mamakin ganinsa kai tsaye a cikin d’akin barcinta. Idanunta ya sauka a kan jaririn hannunsa. Yarda take kallonsa da mamaki shima haka yake kallonta da tsananin mamakin da yafi nata ganin turtsetsen ciki a jikinta haihuwa ko yau ko gobe…. Ta nuna jaririn hannunsa tana iso wa bakin gadon ta ce “Ranka ya da’de jaririn wa muka samu?” Dubansa ya sake kai wa kan jaririn da yake hannunsa kafin ya sake sauke idanunsa kan cikin da yake jikin Fulani ya ce “Ba ke kika haihu ba?” Cikin mamaki ta dubi cikin jikinta ta ce “Ni kuma? Ban gane ba ni na haihu ba shi kuma wannan cikin na jikina fa?” Hannun Maimartaba na rawa ya d’aga yaron yana mamakin al’amarin ya ce “Kada ki min wasa da hankali Rahina d’an waye?” Ta saki murmushi ka’dan ta ce “Banda kada ka ce na maka rashin kunya da sai na ce kai tsaye kai kake min wasa da hankalin, ni dai nan haihu ba kuma idanunka sun gane
Maka hakan, ga cikina nan a jikina don haka kai zan tambaya d’an waye?” Ya sake d’aga yaron yana nuna mata ya ce “Bari na je wajen Sarkin Fada na ji a ina aka samo yaron idan ba naki bane?” Da sauri itama ta zura zundumemen hijabinta ta bi bayansa da yaron a hannunsa. Tuni mutane sun cika sassan Fulanin da tunanin itace ta haihu ciki kuwa har da kishiyoyinta da kuma matan k’annen Sarki Mukhtar da mazajensu kowa bakinsa d’auke da fara’a ana murnar Fulani ta haihu. Mai martaba aka gani hakan yasa aka yi saurin yin shiru wad’anda kuma basu da hurumi a tsayuwar tuni suka watse. Mai martaba ya zauna idanunsa cikin na Sarkin Fada da yake tsaye shima bakinsa ya kasa rufuwa. Ya yi gyaran murya ya ce “Sarkin Fada a ina aka samo yaron nan don Fulani ta tabbatar min ba ita ta haihu ba, ga kuma cikinta nan a jikinta.” Cike da mamaki Kowa ya zubawa Fulani ido kafin Sarkin Fada ya fara fa’dar inda ya aka tsinci yaron… kafin ya gama bada labari kowa ya d’ago a zafafe yana kallonsa Maimartaba ma cikin mamakin yake kallonsa “A bakin Masallaci ku ka gan shi bayan d’auke ruwa fa ka ce?” Sarkin Fada ya d’aga kai cike da tabbatarwa. Shiru wajen ya yi kowa da abinda yake tunani a ransa, kafin Mai martaba ya sake karb’ar yaron yana sake ganin zahirin kamanninsa da yaron, ya mayar da kallonsa kan k’annensa da suke Uba d’aya kuma yawanci suna kama da juna. “A matayenku ba wacce take da ciki?” Da sauri suka girgiza kai suka tabbatar ba Mai ciki. Idanun Mai martaba ya fa’da kan wata takarda da take jikin showel d’in da aka nad’e jaririn da shi. Da sauri ya zaro takardar ya mik’awa Sarkin Fada yana umartarsa ya karanta kowa ya ji. Jiki na rawa Sarkin fada ya bu’de takardar ya fara karantawa.
“K’udirar Allah shi za’a kira samuwar yaron nan, yau aka haifeshi kuma wallahil azeem d’an sarki ne, Sai dai shi kansa Sarkin bai san Uwar yaron ba a zahirance bai tab’a ganinta ba Amma kuma tabbas wannan d’ansa ne jininsa Magajinsa In sha Allah, kuna da damar zuwa asibiti don tabbatar da hakan. Jinin Sarki Mukhtar Bn Abdallah ne……D’ansa na Halak ba shege ba…..Kuma ina rok’on ku saka masa Muhammad Murad” Da sauri Sarkin Gabas ya zaro ido cikin mamaki da jin sunan da irinsa dama ya sanyawa yaron, Wacece wannan ko wanene wannan da yake hangen irin abinda zuciyarsa take Muradi, kamar zuciyar tasu ma a tare
Take, A yanzu da ya sakawa yaron sunan Murad sunan ne kawai ya fa’do masa a zuciya duk da ya da’de yana da burin idan aka haifa masa Namiji Murad d’in zai saka, amma ba ya jin ya furta hakan ga kowa…
Tun kafin Sarkin Fada ya gama karantawa duk mutanen da suke wajen suka d’ago suka zubawa Sarkin Gabas ido. Daga kallon da Suke masa ya tabbatar k’arin bayani suke nema a wajensa, sai dai ya ce musu me? Ko Kur’ani za’a ba shi bai tab’a kusantar wata mace ba,bayan Matansa guda hu’du ko k’wark’wara ba shi da ita, amma ga yaro kuma an tabbatar masa nasa ne, alhali a takardar ma an sanar bai san Uwar Yaron ba… Ba shakka yaron sai dai idan D’an Aljannu ne… Tashin hankali ya bayyana akan fuskarsa yana kallon Muhammad Murad da yake hannunsa……
Jikar Nashe ✍🏽
(kada 500 kacal ta gagareki baiwar Allah wannan littafin ba free bane kuma saura 1pg free pages su k’are. Ki biya ku’dinki ta wannan account kamar haka 2118666253 UBA sai ki turo shaidar biya ta wannan number kamar haka:08033748387.
Special people 1K kacal. Allah ya baku ikon biya.
JIKAR NASHE CE✍🏽
K’UDIRAR ALLAH……..
Page 10.
NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.
_____________
Kowa a parlourn ya yi tsit aka
Zubawa Sarkin Gabas ido ana jiran jin abinda zai fito bakinsa, Ga shi dai magana ta bayyana jariri jininsa amma ta wace hanya aka samar da shi? Shine abinda mutanen Fadar suke son sani, tunda dai cikin Matan Sarkin ba wacce ta haihu balle a ce nasa ne, Ba shi kuma da kuyanga ko k’wark’wara tunda ba tsarin masarautarsu ba ne. Mata hu’du aka amincewa Sarkin ya yi shi kuma Matansa Hud’u a idon duniya tunda biyu daga cikinsu su sun san tsakaninsu da shi ba aure alfarma kawai suke nema ya b’oye hakan saboda wani gagarumin laifi da suka masa, shima kuma ya rufa musu asiri ne saboda ba ya son a sake cewa ya yi wani auren ba tsarin sa bane auren Mata da yawa.
Da k’yar ya saki ajiyar zuciya ya sake d’agowa yana zubawa Murad da yake hannunsa ido, kamanninsa da yaron yana sake k’arfafa irin kamannin nan da Hausawa sukewa Lak’abi da kwabo da kwabo. Idanunsa a raunane ya d’ago ya kalli jama’ar Falon wanda duk jininsa ne da suke Uba d’aya, shi ka’dai ne bare a cikinsu y’ar uwarsa d’aya ce Mace kuma ta rasu shekara d’aya da ta wuce a hatsarin Mota. Ya yi gyaran murya yana so ya fa’di abinda yake ransa Amma yana nazarin fuskar y’an uwansa da kai tsaye dama burinsu kenan su samu mummunan abu da zai zama bak’in tabo gareshi su ya’da shi a duniya don mutane su yi Allah wadarai da shi, so suke a dole sai mutane sun k’i shi, Haushinsa suke ji sosai da ya zamo shine Sarkin gabas ba d’aya daga cikinsu ba, duk da girman da ya bawa Yayansu bai wuce kwana ashirin da takwas ba, amma a tsari na Masarautar Gabas ko da kwana d’aya ya girme shi shi zai gaji sarautar Ubansa don haka sarautar kai tsaye ta fa’da kansa. Duk da Uwarsa itace ta uku a matan Sarkin Gabas Mai rasuwa Amma ita ta fara haihuwa don haka dole shine ya zama Sarki wannan ya d’arsa tsana mai girma a zuk’atan zuriyar Mahaifinsa Sarkin Gabas Abdallah.
Ya d’inke fuskarsa tsaf ba ragowar d’igon rahma so yake sai ya cirewa zuciyarsa Shakkarsu da tsoron cutarwarsa gare su. “Ba ni da wani abu da zance, sai dai ina ji a jikina koma daga ina wannan yaron yake na amince Jini na ne, zan kuma kira likitoci su zo su tabbatar da hakan, idan komai ya kasance kuma kuna da ikon zartar da hukuncin duk da ya dace gane da Mulki na, abu d’aya na sani Ina son sa! So mai tsanani da zan iya rasa komai da kowa a duniya ciki kuwa har da Sarautar da ku kan ku, zan zab’i kasancewata da shi na rabu da kowa saboda shi.” Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke yana jin hukuncin da ya zartar a zuciyarsa shine daidai su suka damu da Mulki suke kuma d’okinsa. Shi a yanzu Son da yake wa jaririn hannunsa ya fatattaki son da ya kewa Mulki dama shi ba ma’abocin son Mulkin ba ne don dai jama’ar Gabas sun nace sai shine, Business d’in da yake yi a k’asashe daban-daban ya ishe shi rayuwa don yana da ku’di ba na wasa ba.
Gunguni da k’ananan surutai ne suka dinga tashi a Babban Falon Fulanin kowa yana furta abinda yaga dama akan wannan maganar, Abu d’aya fuskokinsu suke nunawa duk da basa son bayyanuwar hakan sai dai kallo d’aya Sarki Mukhtar yake musu ya tabbatar da Burinsu ya cika! Haka dama suke so idan Jama’a suka ji abin kunyar da ya aikata su masa tawaye su kuma yi tur da Allah wadarai da Mulkin nasa. Don zina A masarautar Gabas Babban laifi ne a zamanin da yake sawa har su jefe mutum ko kuma a masa d’aurin talala. Balle Sarki da kansa? Da d’an da suke tunanin d’an shege ne a hannunsa. Fulani dai tana zaune tana jin zuciyarta ta yi wani irin nauyi sam maganar da Mijin nata ya yi bata mata da da’di ba, sai dai ta san ko giyar wake ta sha ba yarda za’a yi ta fuskanci Mukhtar da wannan zancen, duk da yake mutum mai sauk’in hali gefe guda kuma yana da zafin zuciya a lokuta da dama kuma mutum ne shi Mai zurfin ciki. Ta ja bakinta ta tsuke ga wani irin ciwon baya da na mara da ya zo mata lokaci guda.
Da k’yar k’ananan maganganun suka lafa kafin kowa ya mik’e suka fice d’aya bayan d’aya zuk’atansu d’auke da madaukakin farin ciki da ya kasa b’oyuwa a saman fuskokin su, duk da k’ok’arin da suka yi wajen b’oye hakan.
Shiru parlourn ya d’auka, ba kowa daga Sarki sai Matansa guda hu’du biyu ba gaske biyu kuma daga ciki sun san Matan Jabu ne, tunda ba aure a tsakaninsu. Sarki Mukhtar ya d’ago a hankali yana nazarin fuskokin Matan nasa da kai tsaye zai iya hango matsananciyar damuwa da take kwance akan fuskokinsu musamman biyun Fulani Rahina da Fulani Saddik’a su fi nuna matsanancin tashin hankali duk da na Rahina ka’dan akan na Saddik’a da bata ma da cikin ba kuma ta da alamar sa, gwara Rahina zata iya haihuwa nan kusa. Su kuwa sauran idan ya yi nazarin fuskokinsu zai iya d’orasu a mizanin Kadaran kadahan duk inda ta kwana sha ce, tunda su da kansu sun san igiyoyin auren nasa a wajen Sarki Mukhtar sun mutu murus ba ko d’aya. Ya saki sauk’akkar a zuciya kafin murya a dake mai sautin Amon rashin tsoro ta daki dodon kunnensu. “Ku saka a ranku Murad d’ana ne Jinina ne, kuma ina son kowa ta masa kallon hakan bana son wata magana bayan hakan, kuma ban ce kowa ta tambayeni dalili ba abu d’aya na sani da Kuma shi zan gaya muku ba wata mu’amalar banza da ta tab’a ha’da ni da wata Mace, ban san ta yarda aka samar da cikin ba kamar yarda ban san a yaushe na kusanci wata Macen na mata ciki ba, wanda ya aikata shi ya san ya ya samar da cikin ko shi ko Uwar yarinya, abu d’aya da zan fa’da idan likita ya tabbatar da Murad Jinina ne, zan rungumeshi zan nuna masa So ba Kuma zan laminci a nuna masa k’yama ba zan iya rabuwa da kowa saboda Murad, dafatan kun fahimta?” Ya fa’da yana ware idanunsa masu tsananin kyau da kwarjini a kansu. D’aga kai suka yi alamar sun gane sun kuma Fahimta. Ya dubi Fulani Saddik’a Mace mai hak’uri kawaici mara son tashin hankali sab’anin Fulani Rahina da ta zama Mace mai fa’da da masifa ga saurin fushi ya ce “Saddik’a zo nan.” Ta mik’e jikinta a sanyaye ta isa wajensa. “Daga yau na baki Amanar Murad, Ina son ki saka a ransa ke ce Uwarsa ke kuma kika haifesa kada ki bar wani abin cutarwa ya rab’esa zaki iya?” Cikin wani irin tsananin farin ciki Fulani Saddik’a ta d’aga kai tana jin duk wani bak’in cikinta ya yaye. Ta saka hannu biyu ta amshi Murad tana saka shi a jikinta ta rungume wata irin zazzafar k’aunarsa tana bin sassan duka jikinta. Da gaske Sarki Mukhtar ya gama mata komai. Fulani Rahina kuwa hankalinta ne ya tashi jin hukuncin da Sarki ya zartar lokaci guda, idan har tana fahimta daidai shikkenan Fulani Saddik’a ce zata zama Uwar Sarki mai jiran gado, duk da ta san Al’ummar Garin Gabas ba za su amince D’an Shege ya Mulkesu ba, duk da Haka bata so ba, bata so a bawa Saddika ba, me Yasa SARKI bai bata ba duk da Kowa a Gabas ya san itace MOWAR SARKI, ita Sarki ya fi so kamar yarda kowa ya shaida itace mai fa’da a ji a Fadar Garin Gabas. Cikin fushi mabayyani ta kalli Sarkin da ya d’auke fuskarsa tamau “Me yasa za’a bawa Saddika alhali ni ce Uwargida?” Sarki Mukhatr ya zuba mata ido kafin shima nasa ran a b’ace cikin zafin murya ya ce “Haka na yi niyya.” Ya juya ga Saddika da ta sake rungume shi tsam a jikinta ya ce “Ki je da shi Sassana a can na amince ki yi rainonsa saboda bana son a yi wasa da lafiyarsa idan komai ya kammala ma barin k’asar za ku yi ke da shi za ku koma England har sai Ya girma sannan zaku dawo ni da kai na Zan dinga zuwa muku ziyara, abu d’aya nake son sani yanzu likitoci su tabbatar Murad Jini na ne. Za’a siyo Madara da duk abinda yake buk’ata.” Fulani Saddik’a ta sake d’aga kai kafin ta mik’e rungume da Mukhtar a jikinta ta bi wata hanya da kai tsaye zata kai ta sassan Sarkin. Fulani Rahina ta bita da wani wulak’antaccen kallo tsanarta da kishinta yana sake kambaba a zuciyarta ji take kamar ta je
Ta mak’ureta da ita da Shegen jaririn su Mutu gaba d’aya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 16