Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
Fadin"Asma"u kinga Baffa na ko..? yau Abdallah ya Dawo garemu." mirmishi Asma"u ta Saki kafin tace"Nagani Hajiya,sai mu godema Allah,don hakika babu Abunda ya gagari Allah.."gyada kai Hajiya kafin tace"Gaskiya ne Ma"u Shiyasa kike burgeni har nakeji araina Dama dama ace Yau nice na Haifeki dana Fi kowacce Uwa sa"ar samu yata gari.."Maman Fati ce tace"Aiko yanzu Hajiya Asma"u ba ya'ta bace Wlh Har Abada tana Mtsayin yarki ce..."Jin haka yasa Hajiya tace"Na sani Habba kuma nagode da wannan kyautar taki.."Dariya Su Anty Nafi Suka sakama Hajiya,suna mata Tsiyan Ciwo ya kare Tunda Baffa ya dawo,dakuwa ta aika musu tana Dariya mai Cike da Nishadi. Suna sallar La"asar basu Zauna Suka Shiga kichen yau Hatta da Maman Fati Cewa Sukayi ta Huta,su zasu Dafa abinci,Da Asma"u da Anty Nafi da Anty Safina,Hajiya ko Da maman Fati Suna tare da Mallam da Baffa Ashashensa,Mallam na karamai Fadan ya Dage da addu"a kuma yadaina Sakaci da ibada,ya amsa da Insha Allahu zai kokarta,Yana Falon Mallam din wayarsa keta bugawa tana Neman Dauki,Daya Duba yaga mai kiran sai ya kashe,Sai daga baya ya Turamata Text sai kirata later baya gari ne yana Bauchi. Polina Taga Sakon Abdallah sai Hankalinta ya kwanta Don ta Zata wannan Shegiyar matar tashi ce,mai kama da Tarwada ce ta tsareshi ammh yana Bauchi sai hankalinta ya kwanta,Buh ammh tayi mamaki Duk da Abdallah yataba Fadamata Shi haifaffan bauchi ne,iyayensa da yan"uwansa na chan,ammh Ita dai Tunda take dashi bata taba ganin yaje ba,ko kuma Yayi waya da wani Nashi Sai Yusuf Shima ba Sosai ba,Ta taba mai Tambayan meyasa baya Zuwa ganin iyayensa sai yake cemata baisan Dalili ba,ammh koda yana son Zuwa baisan meke hanashi ba. Jin haka yasa polina ta saka aka Mata Bincike kan Abdallah da Abunda ya Shafeshi,Dayake Duk wani Iskanci sun sakanshi,wani Boka ne A lagos Arne ma baiga Ruwan musulunci ba,Shi ya sanar da ita kaf Sirrin Wasila game da Abdallah,Abun yabata mamaki taji Takaichin Wasila da Tsanarta Sun kama,Kuma ta tabbata ba Son gaskiya takema Abdallah ba,Tunda Zata iya Cutar dashi Ta rabashi da iyayensa,anan ne ma Bokan ke Fadamata akwai wata yarinya zata Shigo Rayuwar Abdallah,Itace Zata Ceceshi daga hannun Wasila ammh kuma akwai Duhu sosai acikin al"amari daga Dukkan Alamu Zata Sha Wahala. Jin haka yasa Polina ta kudiri Niyyar Ita kuma Zata bada dukkan gudummuwarta Wajen Kwato Abdallah daga Hannun Wasila,bata kuma Taba Nuna ma Abdallah komai ba,Don Wasila ta Riga ta zama wata masifa gareta don ko laifinta baya kaunar yaji,Tayi murna Sosai da Zuwanshi Bauchi tasan ko ba komai Aikin Wasila ya Fara lalacewa. ***** Wasila ko Tun wajen 6pm ta iso gida Dayake Samuel yayi Gudu Sosai,tana Shigowa Su Jamila basu gida Sun Tafi yawon iskancinsu, ta koma Shuga bedroom dinsu Ta iske Abdallah baya gida,kuma Tun tana Hanya take Kiransa bai Daga ba,Hankalinta duk ya tashi,koda Suka kariso gida bata Cikin Natsuwarta,Ranta ya baci Wayarta ta Daga ta kirasu Hafsat ce ta Daga kiran,Fada ta hau yi musu Tana Tambayan Suna ina..? Jamila ce ta amshi wayar tana Fadin"Suna Club ammh yanzu zasu dawo,Bata damu ba balle Tayi musu Fadan Zuwa Club dinsu da sukayi Tambayansu Ta Shiga yi Ina Dee,Jamila tace Su koda Suka tashi Da Safe ya Fice Daga gidan,Ammh kuma kafin Su Fito Sunga Emeka ya Dawo da Mota Shi kadai,jin haka yasa hanjin Cikin Wasila ya Kada,Katse wayar Tayi tana Zufa,haraban gidan Ta Fita da gudu kamar Zata kife,tana karema Pradon motar Abdallah kallo,Ashe Tun lokacin da Suka Shigo motar na wajen Rudewar datayi ne yasa bata Lura ba. Cak ta tsaya tana karema Motar kalllo kafin ta Shiga kwalama Emeka kira,Yana dakinsu yaji kiran Madam da Gudu ya Fito,Tunda nesa ta Fara jehomai Tambayan ina Oganshi,Durkushewa yayi gabanta Don baka isa kama Wasila Mgana Atsaye ba sai ta Mareka bayan taci Ubanka,Kuma daga Ranar kabar aikin agidan,kuma ta Zauna don Wasila ce Mijin Abdallah Kuma matar,sai Abunda takeso akeyi kuma sai Wanda Tagama Damar aiki dashi Zatayi Shi Abdallah Dan bi ne kawai kamar Rakumi da akala. Lokacin da Emeka ke Sanar da Wasila yakai Yallabai Airport ya Shiga jirgi Zuwa Bauchi,Hannu ta Dafe akirji kamar Zata kifa Saboda Tashin Hankali Cikin gidan ta Rumtuma har tana Turgudewa Saboda Tashin Hankali Emeka da Samuel har Suna kunshe Dariya,saboda Ganin yadda take Tafiya,Tana Komawa cikin bedroom dinsu ta Dauko wayarta Hannunta Bisa kai ta Shiga laluban Momcy, Momcy naganin kiran Wasila gabanta ya Fadi,tana dagawa Sai taji ta Fashe mata da kuka tana Sanar da ita"Shikenan Momcy Sun Cika burinsu,koda na Dawo Abdallah yatafi Bauchi Yau Momcy ya zanyi,Wlh Zuciyata tana Zafi da Zarar na Tuna yana wajen makiran Tsofafun iyayen nashi wanda basu kaunata da Abdallah.."Shuru Momcy tayi Takaichin Wasila na Cikata Ganin tana Neman lalata musu aiki ammh sai Ta Danne. Lallashinta tashigayi Tare da Kara Tunatar da Ita Mganar Boka da Abunda yace tare da Tabbarmata da Cewa kada ta damu da Zarar ya dawo ai ;ba"a achan zai Dauwama ba,Zata koma wajem Boka asake Sabon Zubi wannan karon zasu Sha mamaki,Da wadanan maganganun Ta kwantarma Wasila hankali Suka Rabu Zuciyoyi ba Dadi. Bata hakura ba Cigaba da kiran Abdallah tayi bai Daga ba,sai ga Wasila kamar zata Zauce,daga Falo Zuwa upstair Tayi safa da marwa kamar Sau Ashirin Saboda Bacin Rai,ta kasa Zaune ta kasa tsaye,sai Chan Taga Text dinshi na ban Hakuri Cewa zai kirata da Safe,sai lokacin Taji Sanyi,Su hafsat da Suka Dawo akansu Ta Wuce Takaichi da Masifa ta hau yi musu,wai meyasa basu Hana Abdallah Tafiya,Su Abun ma dariya ya basu Suka fara Tunann Kila Anty Wasila ta Fara Tabuwa Saboda Soyayyar Abdallah. ***** Iyalan gidan kaf yau ashashen Mallam Sukayi Dinner Dare,Don Daga Anty Nafi har Anty Safina kowacce Sai da Ta tambayi kwana aka Barta kana Tazo,Asma"u Duk ta Takura Saboda Data dago sai Sun Hada ido da Abdallah Ita gani take kamar Hararanta yake,Shikuma Tun ganin Farko dayayi mata Dazu Zuciyarsa ke Bugawa,Yarasa dalili Kuma Duk Sanda ya kalleta sai yaji Faduwar gaba,Ido kawai yake sakamata ammh Duk sai taji ta tsargu,Haka dazu lokacin Suna jera abinci a babban Dardumar da aka Shimfida atsakar Falon Mallam ita da Anty Nafi da Anty Safina,sun Sun Fita ita kuma ta kawo Jug din Zobo sai gashi ya Shigo Sun Dawo masallaci da Mallam,Da ta ganshi sai da ta Rude a daburce ta Gaisheshi Sai da ya wani kallon akaikace Kana ya amsa da Lafiya,daganan ya Zauna bisa kujera yana Latsa wayarsa Da Sauri ta ijiye Abunda ke Hannunta ta Fice Zuciyarta na Gudu Aranta tana Fadin"Wannan ya cika mugun Hali,goben nan Zan tafi.." Babu Wanda ya Fahimci Halin data ke ciki,tana dai Zaune tana Tsakuran abinci kanta na kasa tana jin Su Anty Safina suna ta waya da Anty Zainab da Yusuf Nan taji Suna Fadin Suma gobe suna hanya,Ta kosa tatashi Don Gabanta Fadi yake,Kuma suna Saitin Juna ita dashi data dago zasu Hada ido,kuma ita Fuskarshi Tsoro yake bata Baya Fara"a ko kadan. Cikin ikon Allah sai wayar Aisha ya Ceceta da hanzari Ta daga kiran tana mai Tashi ta Fice Daga Falon,afakaice ya bita da kallo Cikin Ransa yana yaba Tsarin Halitrarta don Tana Da duk Abunda yake so ajikin Mace,Shashen Maman Fati ta koma bayan Sungama waya da Aisha Sallar Issha'i tayi Ta koma ta kwanta batasan Sadda Hiran Falon Mallam ya Tashi ba,Barci tasha Sosai sai Around 4 ta Farka,Yau ta makara tatashi Tayi ta Fada Tiolet Ta dauro alwala tazo Ta tada Sallah,ita kadai ce Adakin kenan Maman Fati adayan bedroom din ta kwana Don Taji Shigowarta da Asuba tagani ko tatashi. Hajiya ko da ya"yanta kunsan kwanan Zaune Sukayi wajen 12 mallam ya tara kowa zuwa Barci,akabar Abdallah anan AShashen Mallam din ya kwana,dama aleady Tun tuni Dakin kwanansa na Shashen mallam din ne,Shashen Hajiya Suka koma suka dasa hirar,ammh Suma basu barci ba don Sai da dukkansu Suka dauro alwala Sukayi Nafilfilun godiya ga Allah,harda ita Hajiya sai bayan sallar Asuba kana kowacce Takoma barci Tana Ramuwa. *Shakira..* *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai cike da Kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)*  Duk da Asma"u batayi Wani barcin kirki ba bai hanata tashi akan Lokaci ba,Ko data idar da Asubama Bayan Tagama Azkar din Safe,Bata koma ba Fita tayi Zuwa babban Falon gidan inda ta tarar Da Maman Fati nata aikin Hada Abun kari a kichen. Gaisheta Tayi Cike da kulawa kafin ta tambayeta Dame Zata Taimakamata,Firan Dankalin Datakeyi ta Sakarmata ita kuma Ta koma wajen Dama garin kunun da Zata dama ma Mallam suna cigaba da Hira jefi jefi,Inda take son Mamanta kenan bata da yarda wata yar aiki tayima mijinta abinci ba,Tunda hajiya bats da lafiya ita keyin girki kullum sai dai indan Yalwa tazo ta taimakamata da Wasu ayyukan kamar Su wanke wanke da Gyara gyaren Waje Tagama Fere Dankalin kenan Ta dora Koskon Suya ta Kalli Maman Fati tana Fadin"Mama yau fa zan koma..."Dakatawa tayi ta Zuba Ruwan Zafi acikin Fulas Tana Fadin"Yau kuma Ma"u nasha sai gobe.."Girgiza kai Asma"u tayi kafin tace"A"a dama yau Abba ya bani kuma ko ba Haka ba gobe ina da Zuwa asibiti.."Shuru Maman Fati tayi kafin tace"Toh Shikenan ki karya sai kiyi Haraman Tafiya kada kiyi Dare,ai mun gode.."Dakai ta amsa mata kafin ta Cigaba da Abunda takeyi Ita kuma Maman Fati Ta dauki Fulas din Ruwan Zafin Ta Fice Daga kichen. Kafin Wani lokaci Asma"u ta kammallah komai,tana Kokarin gyara kichen din sai ga yalwa tazo,suka gaisa ita ta karbeta ita kuma ta Koma daki tayi Wanka ta Iske har Maman Fati ta Shirya su Fati Cikin kayan Haddarsu Ita da Mahamud,sai Tura baki Suke suna fadin bazasu ba,Maman Fati tace Dolensu kuwa,Dariya Abun yabama Asma"u aranta tana Fadim"Kuruci Dangin Hauka.." Koda ta Fito wankan Maman Fati bata a shashen,kayan jikinta Ta maida Tunda Jakar kayanta gabadaya yana Shashen Hajiya,hijabinta ta Maida kafin Ta Fito daga Shashen Maman Fati Zuwa Shashen Hajiya,Tana Shiga da sallama dashi tafara Hada ido yana Zaune akasa kusa da kafafun Hajiya,yana sanye da Jallabiya mai Ruwan Toka,Fuskarsa ta Fayau ammh kuma ta bayyana Rama Kadan,gabanta ne ya fadi Duk sai ta Daburce sanda Hajiya Dasu Anty Safina ke amsan Sallamanta. Cogewa tayi abakin kofar takasa Shigowa kanta na kasa,hajiya ce tace"A"a Asma"u kariso mana,jiya kuma sai aka min Yaji ko..? Tafada Tana yar Dariya,Jikin Asma"u Asanyaye ta kariso chan nesa da Hajiya ta Durkusa tana gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska tana kara Fadin",Haba Ma"u kuma Shikenan jiya sai kika gudu wajen Habiba ko..? Kanta na kasa tace"Ba haka bane Hajiya,barci ne ya kwasheni bansani ba.."Hajiya ta Kada kai tace",oho koda Naji,kin tashi lafiya.."Ta amsa da lafiya lau kafin ta juya barayin Su Anty Nafi ta gaishesu,Amal yar wajen Nafi ce ta rarrafo wajenta sai ta yunkura ta dauketa tana Satar kallonshi. Kanshi na kasa yana Latsa wayarsa dakyar tace"Ina kwana..."Yana jinta ammh ya basar kamar bada Shi take ba,ya Lura yarinyar Tana da jin kanta sai da Hajiya tace Baffa bakaji Ma"u na gaisheka bane,kana ya Dago yana amsawa da lafiya kawai Daga haka ya Maida kanshi ga latsa wayarsa,Asma"u ko kanta na kasa tana Wasa da Amal ammh duk Sai taji ta takura,gashi tana Son tashi ta Shiga dakin Hajiya ta Dauki kayanta,kuma ta kasa Don sai ta Wuce ta gabanshi,shiyasa tayi Zamanta Kanta na saka tana wasa da Amal dake hannunta. Maman Fati ne ta Shigo dakin Dauke da wani babban Farantin kayan karyawansu bayanta yalwa ce itama da Wani Farantin Anty Nafi ce tatashi da Sauri ta karbeta tana gaisheta,amsawa tayi Cikin Fuska kafin su gaisa da Anty Safina ta juya suna gaisawa da Hajiya,Tana jinsa yana gaida Mamanta ta amsa tana mai Tsiyar Wanda ya bar gida,Ganin Asma"u Zaune yasa tace"A"a Asma"u baki Shirya ba,Kada fa kiyi Dare Bisa hanya Baida amfani.." Da Mamaki Hajiya ta kalleta tana Fadin"Ta Shirya Zuwa ina...? Maman Fati tace"Dutse Zata koma Hajiya,dazu take Fadamin Babanta yau yace Ta dawo kuma gobe tana da aiki.."Hajiya tace"Kai da Wuri haka Ma"u,Gaskiya banji Dadi ba,Da kin bari Zuwa gobe.."Kanta na kasa tace"Hajiya Nima na So haka,ammh ina da Aiki ne gobe Da Safe Shiyasa..".. Jin haka yasa Hajiya tace!Toh Shikenan Ba komai,mun gode Sosai sai Kuma yaushe kenan in kin Tafi Ma"u..? Dan Mirmishi tayi kafin tace"Insha Allahu zan Dawo Hajiya.."Kada kai Hajiya tayi kafin tace"Haka dai kika ce Ma"u ammh kila ai sai Wata Shekara Biyun.."Dariya Su Anty Nafi suka saka ma Hajiya,itama Asma"un sai da ta Dara,Dakyar ta mike tana mikama Anty Nafi Amal tana Fadin bari ta Shiga ciki Ta hada kayanta,ta gabanshi ta Wuce Kafarta na Rawa Zuciyarta kamar ta Fito saboda Tsoro,Kwata kwata mutum baida Rahama afuskarsa wannan Ai matarshi ta Shiga uku,ko acikin yan"uwa baida Fara"a. Anan Dakin Hajiyan ta Sauya kayan Jikinta ta Sanya Wata Atamfarta Riga da Sikat ne,wadanda suka mata Cas ajiki,Duka kayanta ta Hada waje Daya,Mayafin mahadin kayan ta Dauko ta yafoshi Bisa kanta kafin ta Dauki karamin akwatin babbar Jakar Na hannunta Ta Fito,inda Allah ya Taimaketa wannan karon bashi afalon Maman Fati ta tarar da Hajiya sai Su Anty Nafi Kila ya koma Shashen Mallam. Ranta yayi sanyi Har Saida ta Sauke ajiyar Zuciya,ganinta da kaya yasa Anty Safina tace"Wai ke Ma"u saurin me kikeyi Haka..? kin ma karya kuwa...? girgiza kai tayi kafin ta Zauna akasa tana Fadin"bani son nayi Dare ne Anty Nafi,Mganar Abun kari kuma ban cika sakama cikina komai ba in Zanyi Doguwar Tafiya.."Hajiya tace"A"a Ma"u Kefa Likita ce keke gayamin Illar Rashin Cin abinci don Allah matsa ki Zuba Abunda kikeso kici,Ina Mamman yake in ya dawo daga kai su Fati Daga mkranta yazo ya kai ki har chan Dutsen.." Ba Asma"u kadai ba Hatta Maman Fati taji dadi Sosai,Asma"u Tace"Ayi haka Hajiya wahalan Zatayi yawa daya Mikani Tasha na hau Ta haya.."Daure Fuska Hajiya kafin tace"Ammayi Ma"u ki karya kawai banison gaddama in kun gama Zaki Wuce ina Shashen Mallam.."Tafada tana tashi ta Fice Daga Falon. Ko karyawan Sama sama ta karya Ruwan Tea kadai tasha sai Soyayyen kwai don Mutumin ta ne,Tana gamawa ta koma dakin Hajiya ta wanke bakinta da Hannunta ta Fito,lokacin Maman Fati ta Fita inda tace ta Sameta adakinta,Akwatinta Anty Nafi ta dauka Zuwa Shashen Mallam ita kuma ta Shiga wajen Mamanta. Cikin bedroom dinta ta Sameta gefen gado,Dukawa tayi gefenta tana Fadin"Gani Mama..."Wata leda ta Bata da Turaman Zani guda hudu aciki tace "Gashinan ki Tafi dashi,Dikakken naki ne,keda Aisha sai Wanda ba"a Dinka ba daya ki mai Ammi daya muma Matar Babanki Halima,Ga wannan.."Tana Mika mata kudi,Hannu bibbiyu Asma"u tasa hannu ta karba tana godiya idonta Duk ya ciko da hawaye,mikewa Tayi tana Fadin"Ki gaida kowa da kowa,kada ki manta da Addu"a Asma"u Aduk Halin da kika Tsinci kanki Domin Ita addu"a takobin Mumine,Allah yayi miki albarka,zak biya wajen su Kawu ne kiyi musu sallama.."Kan Asma'u na kasa tana Share kwallar data taho mata tace"Eh zan biya,dama ranar dana zo bamu hadu da kawu Ba,Nagode Mama Allah ya saka miki da alheri.."Tafada kwallah na Zubomata. Tsausayinta ya kama Maman Fati ta Rumgumota tana lallashinta da Hannunta ta sanya ta Share mata hawaye,Afalon Mallam Suka tarar dasu dukkansu,ko Shima Mallam din baiji dadin Tafiyarta ammh kuma babu yarda ya iya,20k ya bata Hajiya ma 10k su Anty Nafi kowacce sai ta bata Turmin Zani,Anty Safina ta Hadamata da Turaren Jiki wato Humra mai kyau da kamshi Asma"u tarasa kalamar godiya Babu Abunda Zatacema wadanan mutanen Sai Godiya Abunda yabata mamaki Baffa na wajen Ammh ko Dago kai baiyi ba Daga karshe tashima yayi ya Shige wani Korido inda Zai sadashi da Dakunan barcin Shashen Mallam din Lokacidaya yana Kanga waya a kunne Da kallo ta Bishi asace Aranta tana Fadin"Kowa na gidan nada Mutumci ammh banda Shi.."Harda Mallam acikin masu mata rakiya Zuwa haraban gidan Inda Mamman Zai kaita,su Anty Nafi su suka sanya mata kaya amota,Da zata Shiga mota sai da kwallah ta Zubomata ta Rumgume hajiya da Su Anty Nafi Maman Fati ko na baya,Taki bari ma Su hada da Asma"u bata son Kawaichinta ya karene,Tashiga gidan gaba kenan Sukaji Hon koda megadi Ya bude get Motar yusuf ta sawo kai Shida Zainab da ya"yansu da Annie,nan fa waje ya Karade da murna Ita dai Asma"u bata Fito daga cikin Mota Zainab ta leko Suka gaisa ko Yusuf din Daga Nesa ta Hangeshi,Har Suka Fice daga harabaN gidan Suna dagama juna Hannu. ****** *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai Cike da kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)*😘 1️⃣3️⃣ *BAUCHI* ...... Zuwansu Yusuf yasa kewar Asma"u Bata taba su Hajiya ba Sosai ba Nan aka sake sabon Zaman Hira gida ya Gama Haduwa,Baffa ko da Yusuf suna gefe,suna Hira Jefi Jefi domin Baffa dama ba ma'aboci Mgana bane sai Ta Kama Ranar in kaga Ahalin sai kaji Sun burgeka Ganin yadda kowanne Fuskarsa ya cika da Annuri lalle Baffa Shine jigon Gidan Proff.Abdallah Azare. Mallam Bai Fita ba Aranar Sai Zuwa da yammaah Suka Fita Shi da Yusuf Wanda Hajiya ce Take da Labrin inda zasu,Ko Baffan Bai sani ba,yana dakin Hajiya kwance acikin Bedroom dinta Gajiya yayi da Hayaniyarsu Nafi yashiga ciki ya kwanta,Chan ma Bai samu Runtsawar ba Saboda Kiran Wasila kamar mayya sai lokacin ya samu Kiranta,Kuka Reras take sakin Mai Tana Fadin yayi Tafiyarsa Bai Sanar Da ita ba,Lallashinta yafarayi Yana Fadamata Tafiyarce Tazo ba Shirin Shiyasa,Nan Wasila Tace Ko ya gayamata Ranar Da Zai Dawo ko Itama gobe ta Biyoshi Bauchi,Jin Haka yasa hankalinshi yatashi Domin yasan yadda iyayensa da Yan"uwansa Suka Tsani Wasila Zuwanta bazai Hafar da Mai ido ba. Hakuri yadinga Bata Yana Tabbatarmata da Zuwa jibi Zai Dawo,Duk da Bata yarda ba ammh Taji dadin gane Haryanzu Abdallah Nata ne ita Kadai Sun Dade Suna Mgana a waya tana Narkemai kamar Wata yarinya Kafin su Rabu Shima Shigowar Hajiya yaji shiyasa ya Yankee Kiran,Hajiya Bata Kawo komai Ba don data Shigo Saurin Runtse ido yayi kamar Mai Barci so Bata gane Komai ba,lekasa tayi Kafin ta Dafa kanshi Cike da Tsausayawa kamar Wani karamin Yaro,blanket taja ta Rufemai Kafafu kafin ta Fice tana Rufemai kofar. Kofar ya Kurama ido Yana Sakin ajiyar Zuciya,Polina ya Lalubo itama din Kukan Shagwaban ta sakamai ammh ita na tayi kewarsa ne,ammh Bata Nuna damuwarta ba kamar yadda Wasila Ta Nuna Na Zuwanshi Bauchi Hirarsu Sukasha Cikin Romantic love kafin Suyi Sallama,Yana nan kwance Yana Tunanin Yadda abubuwa Suka Faru Dashi kamar amafarki Barci Mai Nauyi ya kwashe,dama Kuma ga Hayaniya tasa kanshi yayi Nauyi. Suko Mallam da Yusuf wajen Wani abokin Mallam sukaje Wato Mallam D'abarani Wanda ya kasance Malami ne na Boko Dana Addini ya Shahara Kuma yayi suna Wajen Bada mgungunar Musulunci Kama daga kowani Cuta har Zuwa na Sammu,To abokin Mallam din ne Sunyi karatun Addini tare Wajen Wani malaminsu Dake Azare,akwai kyawawan alaqa Sosai atsakaninsu ko lamarin Abadallah ma Yana Fadamai Yana sakasu Cikin addu"a toh adaren Jiya Sunyi Mgana da Mallam yamai bayanin Zuwan Abdallah da wasu Karin bayanai Shine yace gobe da Yammaah yazo ya Sameshi agidanshi Sukara Tattaunawa,shine ya nemi Rakiyar Yusuf Suka Tafi Tare. A D'anjuma goje Mallam D'abarani ke Zaune da iyalansa Nan Su Mallam sukaje dayake yasan da Zuwansu aka saukesu Cikin Babban Falon da yakan Sauke bakinsa masu Muhimmanci,Bayan ya Fito sun gaisa sai Kuma bayanai Suka biyo baya Sai da Mallam Da'barani yagama jin Komai kafin yayi gyara Murya yace"Masha Allah Naji Duka bayananka Mamuda,mganar gaskiya ayadda Duka abubuwa Suka Faru yaron naka Sihiri ke Dawainiya Dashi..." Gyada Kai Mallam yayi Yana Kallon Yusuf Wanda Shima ya Natsu Yana Sauraran Jawabin Mallam Da'baranin ,Ganin sun yi Shuru ne yasa Mallam din ya Cigaba da Fadin"Kuma kowa yasan Cewa Sihiri gaskiya ne Don ma Anuna mana gasgastan Hakan Sai da ya Kama Shugabanmu Annabi Muhammed (SAW)..."Suka Cike Salatin gabadayansu kafin ya Dora da Cewa"Toh mganar gaskiya itace Mu bamu Isa mu Yi abunda Allah Bai Tsara ba,Sai dai zamu Mika Al"muranmu ga Allah,akwai addu'o'in karya Sihiri Wanda Za'a Tofasu Aruwa,nasha ne Dana Wanka sai Kuma Garin magarya da Zan Hadamai da Wasu Karin magunguna da Zai Dinga Sha Yana Wanka Dashi da izinin Allah Duk Sihirin Dake jikinsa Zai Warware da yardan Allah.." Gabadaya daga Mallam Har Yusuf suka had Baki Wajen Fadin.."Allah Shi yarda..."Daganan Mallam D'abarani ya kalli Proff.yana Fadin"Karka damu Komai Zai Daidaita sai dai Kuma Adage da addu"a domin Ita Addu'a makamin Mumuni ne,Wannan ne yaron wajen Naka..? Yafada Yana Kallon Yusuf. Mallam yace"Bashi bane Akaramakallahu,Shima wannan din Duka na wajena,Abokin Abdallah Kuma Yana Aure da Yata,kaga ko Duk anzama Daya..."Mirmishi Mallam D'abarani yayi kafin yace"Hakane Masha Allah,toh Abunda za"ayi Yanzu KU bani Nan da Zuwa gobe da Yammaah Zan kiraka sai ka Turo a karbi Magungunan da Ruwan Addu"an tare Da bayannin Yadda Za'ayi Amfani Dashi,da yardan Allah indai yayi Amfani Dashi yadda yadda Dace Komai Zai Daidaita Da yardan Mai Duka.."Mallam yaji Dadi Nan yayi Ta ma Mallam D'abarani Godiya da Zasu Tafi ya Bashi 30k ammh yaki Karba 5k Kadai ya Cira Suma yace Kudin Siyan mganine ammh ko Sisinshi bazai Karba ba, don Abdallah Shima D'a yake gareshi,Haka suka Rabu Cike da Mutumta juna,har bakin Mota ya rakosu suna Kara Sallama da Mallam kafin ya Shiga Mota Yusuf yaja su bar anguwa Zukatansu Cike da Faricikin Nasara. Koda suka Koma Suka labartama Hajiya Da Maman Fati yadda Sukayi da Mallam D"abarani hakika Sunji Dadi sosai,har suka kasa boye Murnansu,Baffa dai baisan wainar Da"ake Toyawa ba,don Dakin Hajiya ya Wuni kwance,Sai Bayan la"asar ya tashi Bayan yaji kansa ya lafa,shashen Mallam ya Koma yayi Wanka,Yusuf ya matsa mishi Suka Fita Zaga gari amotarshi,Duk da Rabin Surutun na Yusuf ne ammh Bai damu ba,domin Yafi kowa sanin Baffa ba ma'aboci Mgana bane,Ammh duk da haka yaji Dadin Fitansu don Yana Tunamai da lokacin Kuruciyarsu Shida Yusuf,sunyi yawo Sosai sai After Issha"I suka Dawo Gida. Washegari Yusuf yaje ya karbo Sakon Wajen Mallam D'abarani,Bayan ya Kira Mallam awaya yace azo a Karba,bayanin Komai na Cikin Wata Farar Takarda Jakarne Guda na Ruwan Addu"an sai Wata jakar Kuma Cike da Haden Haden Magunguna,sai wasu Rubuttatun Addu"o'i na Tsari Wanda Annabin Tsira ya Koyar damu,Koda Yusuf ya Kawo Sakon Mallam ya Karba Da kanshi ya Kira Baffa har Shashensa Da daddare ya Damkamai Magunguna Bayan yamai Nasiha Mai Shiga jiki,Baffa baida ta Cewa illah saka Hannu ya Karba Hannu bibbiyu domin bayason ya Nuna gardama balle Shima Yana bukatar Wani abun da Zai Tallafeshi don Wani lokacin in yayi Wani Abu sai yafara Tunanin kamar Bashi ba. Hajiya ko Dataji lbrin An Damkama Baffa magungunar,Da kanta ta karbi Jarkunan Magungunar,ta Kai Dakinta ta Kuma Umarcesa Shashenta Zai Dinga Zuwa Yanasha in Lokacin yayi,Bai yi gardama ba ya amsa Mata da Toh,kowa yaji Dadin Haka Saboda Akula Da Shansa Ko zasu Samu Waraka kan Abunda ke Damunsu Shekara da Shekaru. Kwana uku Su yusuf Sukayi Suka Koma Saboda Wajen Aikinsa Suma Su Anty Nafi Bayan Tafiyarsu Yusuf Mallam ya Tarkatasu kowacce ta Hada kayanta ta Koma Gidan Mijinta Cike Da kewar gida,aka bar Baffa da iyayenshi Wadanda keji kamar su lasheshi,Hajiya da Maman Fati Harda Mallam ba"asan Wanda Yafi wani Kula da Shan mganin Baffa ba,Hajiya da kanta take Zubamai Wanda Zaiyi Wanka Dashi Bayan ya Fito Kuma ta ta sashi Har sai yasha nasha,Addu"o'in kuwa Yana Kokarin Karantawa Duk da Yana Da Rauni wajen Addu"a ammh wannan karon ya Dage Saboda idon iyayensa Dake kansa. Wajen Sati Daya Baffa ya kwashe agida Yana Amfani da mgungunarshi Kuma Alhamdulillah Sun ga Chanji Shi kanshi yanajin Chanje chanje ajikinsa,Lokacin dayayi Sati yaso komawa Porthercourt ammh Mallam yahana yace yabari yagama shanye mganinsa,Allah barshi in Zai Koma sai yatafi da Wani Tunda dama na Sati Dayane Duka Magungunar,Hakanan ya Hakura ya Zauna Bayan ya Kira Office dinsu yadauki Excuse. Wasila Ko takusa Haukacewa Da Rashin Abdallah,Bata Wanka balle Kwalliya Koda yaushe Cikin Kuka take da Rantsen Rantsen Cewa Sai Su Hajiya da Mallam Sun gane Kuransu,Saboda Tsabar Firgicin Da Wasila ke ciki ko Su Jamila Basu Sha,Abu kadan sai Tahau Zaginsu da Masifa,Ga dai Dukiya Abdallah ya barmata Don Duka ATM's dinsa suna Hannunta Bayan uban Kudin dayake ijiyewa agida,ammh Duk Basu da Wani Amfani awajenta,Abdallah shine Cikon

Chapter 9 of 11