Rayuwarta Tanajin Rayuwarta Zata Raunana matukar Babu Abdallah Shiyasa lokaci kadan Duk ta Fita Kamaninta kallo Daya Zakamata Ka Gane Bata Cikin Hayyacinta,Koda yaushe Cikin Kiran Momcy take tana Mata Kuka,Tun tana Bata Baki Har Ta daina Daga Kiranta Domin Bata Son Shigen Kulafuncin Wasila da Wutar Cikinta ya lalata musu aiki ya Dawo Dasu baya.
Hajiya Kudirat Ganin Abun na Wasila Yana gabane ba baya ba,yasa ya Ta Shirya tazo Nan Porthercourt,ta kwana Biyu Tana Kara Lallashin Wasila tana Kara Jadaddamata Duk Tsiyan Iyayen Abdallah Dole Su barshi ya Dawo Tunda aikinshi Yana Nan,Ta kyaleshi Zai Dawo ya Sameta ita Kuma bazatayi Jinkirin Zuwa wajen Boka ba Da Zarar ta Samu lbrin Dawowar Abdallah,da Haka ta Kashe bakin Wasila ta Daina Shigen Haukan Datakeyi ammh fa Bata Daina Nuna damuwarta ba Don Har Rama tayi Tsabar Ta sama kanta Bala"i.
*******. *******. *******
*DUTSE*
Asma"u Bata Kai ma Aisha Sakonta ba Sai Karshen Sati Ranar Lahadi Bata da Zuwa asibuti Ta Shirya tun Safe tatafi Gidan Aisha ta Wuni Suna ta Hira Bayan ta Bata Sakon Maman Fati,tsalle Aisha ta daka tana Murna Haka da Fahad ya Dawo Ta dauko tana Nunamai Tana Murna,shima Yana Nuna murnanshi Sosai Nan ta Wuni sai yammaah Fahad din da Aisha da Amir suka kawota gida kamar suce ta Zauna agidansu Saboda yadda Suke Sonta da Kuma Mutumtata Koda suka Kawota sun Dade Wajen Ammi kafin Su Tafi ita Kuma Asma"u Ta Koma gida.
Tunda Asma"u tadawo Gida Kullum da Safe Sai ta Kira Hajiya Sun gaisa sai Taji ya Jikinta,Nan Zasu Sha Hirarsu da Hajiya Abun na Mata Dadi Jin Hajiya jiki yayi Sauki Sosai Koda Maman Fati Suna Mgana kowani Lokaci Kuma Itama ta Tabbatarmata da Cewa Hajiya jiiki yayi Kyau Sosai,Wato Asma"u ta Lura Duka Farincikin Hajiya na wajen Baffa ne,Ji daga Zuwanshi Hajiya ta Samu Sauki,lalle Uwa uwace ammh ba Domin Haka ba Miye Abun kwallafara rai akan Wannan gayen Dan Wulakanci,Domin Tuni ita ta Sakashi Acikin Jerin Sahun Marasa kirkin Gidan Proff.
Awannan Satin Haihuwar Rabi"a ce ke Dawainiya da Umma Don ta Haihu ta Haifi yan biyu Duka Maza,Wanda Yasa Umma ke Kara bude Hanci ita adole ya"yanta sunyi Aure Kuma Suna hayayyafa har Wani Taku Zaka ga tanayi,wannan Haihuwar Tasha bambam Duk da Hauhuwarta na biyu kenan Dayake Mijinta Dan Boko ne Tsarin Iyali Sukeyi,Umma ta Saki bakin Jaka tayi Hidima Sosai Kuma ta Saka Hajiya ta matsama Abba Shima ya Bata kudade,na Hidimar Suna Domin Shagali na musamman Ta Shirya Nata,Bayan Wanda Za"a gudanar agidan,Bayan Kuma Wanda Za"a gudanar A Jigawa Gidan maijego.
Asma"u batayi Gigin Cewa Zata bi Su Anty Bilki Jigawa ba Wanda Sukatafi Tun ana jibi Suna Ita Dasu Anty Rukayyah da Fa"iza sai Maryam da kursum Sai Anty Amarya da Mama Gidan dai gabadaya Suka D'ade,Itama harda ita Abba yace Atafiyar ammh sai ta Zame da Cewa Ranar Tana da Zuwa Asibiti Duk da Ranar Bata Dashi ammh tasan In ta Sake taje toh karshenta Ta Dawo DUTSE Tana Kukan Bakinciki Domin Banda Fa'iza da Anty Amarya ba Wanda Zai Mata Kallon Sani balle Hartaji Dadin Zuwanta Sunan.
Ashe Bata Tsira ba,Don Ranar Sunan da Ummah Tayi Nata taron agidan Ita da kawayenta da Yan'uwanta Sai da Asma"u ta Zubar da Hawaye,Ranar a Asibiti ta kwana wajen 8 na safe ta Shigo Gidan,Tana Rangaji kanta ke Saramata Sakamakon Jiya Bata Wani Samu Barci ba aiki yayi Musu yawa,Tunda ta Dawo Taga Gidan Cike Ta Shigo Dakinta ta Sakayo Ta kwanta,Sai Bayan Azahar ta leko Nan ta Iske Ana Hadar Hadar Arziki Baba lami ce ma ta Tuna da'ita ta Kawo Mata abinci Duk da bazaTaci ba ta Karba karta gwale Baba lami din.
Fitowarta yasa wasu Daga Cikin Dangin Umma Suka Fara yada Mata Habaici Suna Zaginta da Kuma Gulmar wai taki Aure tana Zaune agida tana yawon Iskanci Tanajin wata Na Fadin Aiko Taji Haushi gata ga Zaman Gidan Tunda Shi ta Zaba,wata Kuma Cewa tayi Bamai Aurenta ta Tsufa agida don Ance ta kusa Arba"in Domin ta girmi kowa agidan"Bata Gama jinsu ba ta Koma Daki tana Danne Kukanta kan Katifarta ta Fada tana Sakin Kukanta Lokaci daya kamar Wata karamar yarinyar,Aranta tana Jin kodai Tama Allah Wani Laifi ne dayake Horata ta wannan Hanyar,ammh Ba irin Kalan Addun"a da batayi ba akan Allah ya bata Miji na gari Wanda Zai Dauketa Daga wannan Zaman kunci Daya Fara isarta.
Har suka Gama Shagalinsu suka Watse Bata Kara Gigin Fitowa ba,
Da daddare Kuma Hajiya iya ta Shigo har Dakinta ta Dasa Nata Wai Bakinciki da Mugun Hali ya Hanata Bin Yan'uwanta Zuwa Jigawa Suna,hartana Cema Wai Sai dai Ta Mutu ammh Haihuwa Yanzu ya"yan Umma Suka Fara,Saboda Bakinciki ko Kulata Batayi ba,Illah Maida kanta Datayi kan Littafin Azkar din Dake Hannunta Gefe Daya tana Dauke Guntun Hawayen Daya Zubomata da karamin yatsar Hannunta.
_*Hurry And pay ur Register....Free page Ya Kusa Dauke Kafa Insha Allahu*_😘💝❤️💞
_Zaku samu Damar Karanta littafin *ZAMAN GIDANMU* Kan 200 kachal,ta wannan Account Nombar kamar Haka 0552179550 Jamila Umar Gtb,bayan An dauki Hoton Trancsation din an Turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Waya na Mtn bayan an Dauki Hoton katin sai a turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Yan Niger kuma zasu biya 300f...Ina maraba daku Masoyana masu Son Cigabana.._
*Anitha..*💞
*05/04/2020..*✍️
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*😘
1️⃣4️⃣
Sai da Baffa ya kwashe Sati biyu Cur a Garin Bauchi kana ya Koma portharcourt,Wanda Kafin yatafi sai da Mallam yakara Zuwa Wajen Mallam D'abarani ya karbo Mai Wasu Ruwan Addu"an,wanna Karan a kananan Goran Swan ne,Daya na Wanka Daya na Sha ne,sai wasu Addu'o'in da ya sake Rubutamai Kuma Alhamdulillah Sunga Chanji Sosai Shi kanshi Abdallah yafara Dawowa Cikin Hankalinshi.
Ta jirgi ya Koma Portharcourt Wanda Mallam da kanshi ya kaishi Har Filin jirgi na Abubakar Tafawa balewa Dake Bauchi Shida Mamman,Hajiya ko da Su Anty Nafi da Baffa Zai Tafi Rikesa Sukayi Suna Kuka,Domin gani suke in yatafi To sai Yafi da Da dadewa kafin yazo Gida,Hajiya ko Takasa Tsaida Hawayenta Saida Abdallah ya Duka Yana Share Mata Hawaye Yana Tabbatarmata da Cewa bazai Kara kwatatanta Abunda yafaru abaya ba,Insha Allahu Zai Dinga Zuwa Gida akai akai da Zarar Bukatar Hakan ya taso,da wanna Kalaman ya Taushi Zuciyar Hajiya Suka Rabu Cike da Kewa,haka ma Maman Fati da su Mahamud Suka Rike hannayensa kamar kar yatafi,sai da Mallam ya Ankarar Dasu Cewa Jirgin da Zai bi saura Lokaci Kadan ya Tashi kana Suka Sakeshi Yafada Mota Shida Mallam Mamman ya Fice Daga haraban Gidan Suna Daga Musu Hannu,shi kanshi Baffa Yana Jin Wani kwarin gwiwa acikin Ranshi Hawayen Hajiya Yafi Komai Dagamai Hankali,yanajin Shi kanshi baya kyautama kanshi Wanda baisan Dalili ba,ammh yayi alqawarin Gyara kurakuranshi na da Izinin lahi.
Su Mallam Basu Baro Airport ba sai da Jirgin su Abdallah ya Tashi ya Lula Sararin Samaniiya,shi kanshi Mallam kafin su Rabu sai da ya Dinga Jaddama Abdallah kada ya Sake yayi Wasa da Amfani da mgungunarshi,Kuma Kada ya Koma ya Shagala ya Manta da Addu"o'i tare da Azkar,Cike da ladabi Abdallah ke Fadama Mallam Cewa Insha Allahu Zai Kiyaye,Da haka suka Rabu Bayan Sun Rumgume juna,shi kanshi Mallam sai da ya Share kwallah,Yana Fatan Allah Yasa Karshen Wahalansu Kenan Akan Baffa.
Daganan Cikin Mkranta ya Wuce Zuciyarsa Duk ba Dadi,Gida kuwa duk Sai yazama Wani iri,Hajiya Dakinta taShige ta kwanta tana Tunanin Zucci,Aranta Tanajin Lokaci yayi da yakamata Itama ta Motsa Domin Tunda Har Baffa hankalinsa yafara Dawowa gida,to ya kamata Anemi wani Abu Wanda Zai Kara karkato Dashi na Har Abada,Wanda ko Matarsa Bata Isa tahanashi Zuwa garesu ba,tana wanna Tunanin Har barci ya kwasheta,su Anty Nafi Basu Dade ba kowacce taKoma Gidan Mijinta Hajiyama Bata Tashi ba lokacin,Maman Fati sukama Sallama da Zasu Tafi,haka Gidan ya Wuni Babu Wani Walwala,shi kanshi Mallam din har ya Dawo Bai da Wani karkarshi Hankalinsu Bai kwanta ba sai da Abdallah ya Kira wayoyinsu ya Sanar Dasu ya Sauka Gida lafiya,hatta Maman Fati Sai da ya Kira,shine Zuciyarsu ta Dan kwanta Suna Kuma ji Aransu Insha Allahu Sukeda Nasara.
*******. ********. *******
*PORTHARCOURT*
wasila Bata da masaniyar Dawowar Abdallah Domin Bai kirata ba,Wacce ke kwance bisa Daya daga Cikin kujerun Falon,kallo daya Zakamata ka zata Ta Shiga Haukane Saboda yarda Ta Dawo kamar Wata Mahaukaciya Sabon kamu Saboda Tashin Hankali,sanye take da Riga da wando,wandon mini ne Kuma ya kamata Sosai,sai Wata karamar Riga Mai Kama da Shimi,Iyakarta Cikinta Don ko Cibiyarta Bata rufe ba,kitson Attachement din ya Tsufa Duk ya Fara Tugewa Saboda Dadewa,Fuskarta Duk ta kode hartafara Wani Tambarin Baki baki,da wasu kananan kujera na kazanta,Idanuwanta sun Kada sunyi Jawur,da alamun Wuni Suke Suna Zubar kwallah.
Ita kadai ce Afalon,su Jamila Suna dakinsu Domin yanzu Indai Anty Wasila na Falo suka Fito Sun bani da Masifa Duk sai Ta nemi Hucewa akansu,yanzu ba Halin Su Shiryawa su Fita club in Suka Dawo takama Bala"I Sai Sun Raina kansu,Gabadaya ta takura Musu ta damesu Kuma so ko Tsausayamata basa yi,Sudai Kawai Suji Dadi su Hole Tunda ita ta sakarmusu ammh yanzu ta Fara chanza Musu ko Kudi bata Basu balle Su Fita su Ji Dadin Rayuwarsu,shiyasa Suma suke banza da ita Suyi Shigewarsu daki Ko zata Shekara Tana Kuka ko a haban Zaninsu,toh ko su emeka da Josepen Basu Tsira ba kuskure kadan Mutum Zaiyi Sai ya Raina kanshi Ranar Har Sai da ta Shararama Josepen mari,Wai takan ya Kawo mata lemon Fanta ita Kuma Maltina tace,shine Kawai ta kasheshi da Mari,Toh ya ya iya Banda Hakuri Domin ba karamin Aikinta bane ta Bashi Red Card.
Emeka na Zaune Cikin dakinsu inda Suke kwana Shida Samuel, wayar Abdallah ta Sameshi Cikin Rawan jiki yadaga Kiran Ko kafin yayi mgana Abdallah ya Rigashi da Fadin"Come and pick me,am in Airport Now.."Bai jira cewarsa ba ya datse Kiran,da hanzari Emeka ya Mike Saboda Rawan jikin Dawowar oga ko tsayawa baiyi ba ya Zari key din Motar Abdallah Wanda ke hannunshi ya Fice da Sauri,sai da ya Shiga motan ya Tada ita kana ya Lura da Samuel Dake Mai mgana,Hannu kadai yadagamai kafin ya zuba Hon megadi ya wangalemai get ya Fita da gudu Cikin Motar M.A Wato Bakar prado.
Wasila Dake Zaune Taji Karan Hon da Bude Get,da hanzari ta Mike ta Isa ta Window Falon,ta Bude Labulen wajen ta leka sai dai Bata gakowa ba sai Kyallin Ficewar Emeka,Kai ta girgiza tana mamakin Yadda Ina Emeka zashi da Motar Dee,lalle Zai ci Kaniyarsa komawa tayi tazauna tana Jijjiga jiki da kafa kamar wata basarakiya.
Emeka Yana Zuwa Airport Yaga Abdallah Yana Tsaye Yana Jiransa ,Yana sanye Cikin Shadda Fara Riga da wando Dinki Muhammed kansa dauke da Hulan Zanna bukar,iren iren kayansa ne Dake Gida,Wanda Tunda Wasila ta tarwatsa Rayuwarsa bayama Zuwa Gidan balle Suyimai amfani,sai Hannunsa dauke da Wata karamar Jakar matafiya Wanda Mallam ya Zubamai Gorunan Ruwan Addu"an ciki,da Kuma Littafan Addu'o'in Tsarin Daya Siyo Domin Abdallah.
Tundaga Nesa Kwarjinn Abdallah ya Daki Emeka azahirin gaskiya ko Suit Abdallah ya sakar Yana Da Baiwar Haiba ta Kamala Atare Dashi,balle Daya saka manyan Kaya ai sai Emeka Yaga yakara Mai Wani girma a idanuwansa jikinsa na Rawa ya Nufeshi Yana Fadin"Welcome Oga.."Hannu kadai ya Dagamai Batare Dayayi mgana ba,illah Tafiya daya farayi Da hanzari Emeka na binsa Yana Kokarin karban Jakan Dake Hannunsa ammh sai yahanasa Lokaci Daya Yana Fadin"Tanque..."Dole Emeka ya kyaleshi Sai da ya kwashi Gudu ya Isa Wajen Mota ya budemai Gidan Baya ya Shiga shikuma ya Zagaya Gidan gaba Ya bude ya Shiga Suka Fice Daga Airport din da Hanzari.
Basu Wuce Gida Direct ba Abdallah yace yafara kaishi Office,sai da Sukace je ya Iske tarin Aiyuka Da fayel fayels,Bai iya Taba Komai ba,Saboda Aikin yayi yawa,Sai dai Zuwa gobe gaisawa Kawai Sukayi da Sauran ma"aikatan Dake kasanshi Suna Mai barka Da Dawowa,Daganan Gida yace Emeka yawuce Dashi Bayan ya Turama Polina Sakon ya Dawo gari yanzu.
Wasila na Zaune Taji Hon da Kuma Karan Bude Get,Da hanzari Ta Mike,Saboda Yadda Takejin kanta ko Suturta Jikinta batayi Tunanin yi ba Takama Hanyar Fita daga Falon,ta Kunno kanta Kenan Sai suka kwashi karo da Abdallah,Har Saida Suka kume Goshin Juna,Baya Sukaja da Sauri Kowa na Dade goshinsa Yana Kuma bin Dan"uwansa Da kallo,Wasila data ga Abdallah kamar Daga sama,Ta Waro ido Tana Binsa da kallo bakinta da Jikinta na Rawa take Fadin"Dee...is u...? Take Fada Tana Nunashi...
Mirmishi ya Saki Kawai Yana binta da kallo Cike da mamaki,baisamu Zarafin mgana ba Tayo Rumi Ta afkamai tana Sakin Ihu kamar zararriya,Karfinsa ne Ke jikinsa Shiyasa ya Tari Wasila da Hanzari Bata kadasu ba,Ihunta Shi ya Fito da Josepen da Su Jamila Hankali tashe,ammh Kuma sai Sukayi Turus ganin Abdallah.
Wasila bakinta yakasa Rufuwa Ta kalli Su Jamila tana Fadin"Kun ganshi ko? My Dee ya Dawo gareni dama I already Tell u Abdallah bazai Taba juyamin Baya ba Wayyo Allah.."Take Fada Tana Hawayen Farincikin,Jamila da hafsart Suka Saki ajiyar Zuciya Suna ma Abdallah Sannu da Zuwa Jospen kuwa bakinsa yaki Rufuwa,Riko Wasila yayi Yana kallonta Banda Mirmishi Babu Abunda yake Mata,Jakar Hannunsa take Son Karba ammh ya Hanata,Kallonsa take Tana Kara Shafa Fuskarshi,Hannunta ya Riko da Karfi Yana Fadin"Noory U are not in dream fa Nine.."Yafada Yana Kara girman idanuwansa.
Fadawa tayi Gefen Kafadansa tana Fadin"Wlh Dee na Fidda Rai Dazaka sake Dawowa gareni Na Dauka Su Hajiya Sun Rabani dakai Kenan har Abada.."Tafada lokacin da Suke Haura Steps zuwa Cikin Master Bedroom dinsu...
Mirmishi ya sakarmata kafin yace"Why..? Ko Shiyasa Duk Kika Rame Ki kwantar da Hankali Bamai Rabamu sai Allah,Kuma me Kika masu Hajiya da Zasu Rabamu ba Wanda ma ya damu Dake gaskiya.."Ya Fada Yana Kara kallonta Cike da kyamar Kanta Dake tashin Wari .
Gabanta ya Fadi tayi Cak tana kallonshi Daidai lokacin da Suka Shiga Bedroom dinsu,Cikin karyewar Murya tace"Hakane,ammh bazaka sake barina ba ko Dee..? Tafada tana Wani Narke Murya,Yana Ijiye jakar Hannunsa bisa Gado yace"Dama ba barinki Nayi ba,naje Duba iyayena ne,Wanda Na Dade banje ba,Suna da hakki akaina Wanda in ban Sauke ba Allah Zai iya kamani,nasan Kuma kema Zaki so Mijinki yazama Mai Sauke Nauyin Iyayensa ko..? Karki damu in Zan Koma sai mu Koma Tare Gudun Kar na barki ki Kara Shiga Wata damuwar.."
Tsurewa Wasila tayi Atsaye Tana bin Abdallah da Kallo Yana Tube kayan Jikinsa Cikin Rawan Murya tace"Bauchin Zaka Koma Dee...? Bai ba mganarta Muhimmanci ba yace"Eh mana ai Daga yanzu Insha Allahu Duk Bayan 2 weeks Zan Dinga Zuwa Chan,banson na Kara sakasu adamuwar Dana sakasu Afarko Noory.."Yafada Yana Jan Towel din Dake Rataye Akofar Tiolet ya Daura Kai Tsaye Kuma ya Shiga Tiolet din ya Rufo.
Baya Wasila taja Hannunta Dafe da kirjinta Idanuwanta Sun Fito waje,Wayyo tashiga uku Wani irin Abu ne yake Shirin Faruwa da ita..? Kalli Yadda Abdallah yake Fadamata mgana Babu wannan tsoron Da Jin Mganarta da Tsananin Son da yake Mata..? Lalle Tayi Kuskuren Babba Data bama wadanann Tsofaffun Dama Har Suka Samu Damar Kusa Rabata da Abdallah yazama Dole Ta Mike Tsaye Ta Nuna Musu Wacece Wasila,wlh ko Zatayi Yawo tsirara Sai Ta Kara Mallakar Abdallah Atafin Hannunta kamar yadda ta Sameshi Da Farko.
Bata jira komai ba Ta Fito Daga D'akin da Hanzarin Bibbiyu Take Hada Step kamar zata Kife Falo ta Isa ta Rarumi wayarta Dake Kan Kujera ta Lalubo Momcy Wacce Ringing Uku TaDaga Cike da Masifa Wasila ke Fadin"Momcy Abdallah ya Dawo Daga Bauchi yanzunan,ammah Kuma Sun Gama lalatamana komai Yanzuma gayamin yake Zai Dinga Zuwa Duk Bayan Sati biyu,Momcy Kada ki Bari Shegun iyayen Nan nasa su sake Nasara akaina,in Boka D'andugaji bazai Iya ba Ki Nemi Wani ma,So Nake Arabasu Rabuwa Ta har Abada Zasu San Da wa Suke Zencen..."Takarishe Fada Tana Huci kamar Wata macen Zakanya.
Dariya Momcy ta Kece Dashi kafin tace"Yaro Yaro ne Baisan Wuta ba sai ya Taka..ki kwantar da Hankalinki Tunkafin kizo Duniya Boka D'andugaji keman Aiki Kan Mahaifinku Kuma Bantaba ganin Nakasu ba Sai Nasara,Kema kisa aranki Bazaki Taba ganin Nakasu A Al"amarinki ba Wasila Barni dasu Zan Nuna Musu Basu Isa ba Wlh Gobe in Allah ya kaimu zanyi Sammako Naje na Samu Boka,Kidai ki kwantar Da Hankali Abdallah Naki ne,Kuma Zai Cigaba da Zama na ki Har Abada.."
Mirmishi Wasila Tayi kafin tace"I Trust u Momcy...sai najiki.."Daga haka ta yanke Kiran Kafin ta Tsaya Tayi Shuru Kada Kai Tayi Kafin ta Haura Steps da Sauri Tana Komawa Bedroom din Ta Iske Abdallah ya Fito Daga Wanka Yana gaban dressing Mirror Yana Tsane kanshi Da karamin Towel din Dake Hannunsa,Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin tafara takawa Zuwa gareshi Ta Baya yaji Ta Rumgumeshi Tana Fadin"I miss u Dee..."
Bai Mata mgana ba illah Waigowa Dayayi ya Bambareta Daga Jikinsa Yana Fadin"I know,ki Shiga kiyi Wanka Noory ."Tsam tayi Tana Kallonsa Jakar dayazo Da ita ya Dauka kafin ya ijiyeta Saman stool din gadon Da Kallo Wasila ta Bishi Sanda yake karisawa gaban Wardrope din D'akin,Bata tare Data Kara mgana ta Nufi jakar Tana Budewa Hannu ta saka ta Fito da Gorunan Rubutun Tare da Farar Takardan Mai Dauke da Addu"o'in Gabanta yafadi Da Sauri Ta waiwaya tana Fadin"Dee menene wannan..? Tafada tana Raba ido..
Waigowa yayi Yana Kallonta Da Sauri yabar Abunda yake ya kariso Gareta yakarba Duka Abubuwa ya maidasu Cikin karamar Jakar Yana Fadin"Mgunguna ne,Karki Kara Tabasu Ba Abun Wasa bane..."Yafada Yana Daukan Jakan Cikin Wardrope ya bude ya Turata,Wasila Dake Tsaye Taji Wani Jiri na Dibanta in Tagani Daidai Addu"o'i ne Tagani Arubuce Toh Ruwan Fa Namene ne..? Bata Gama mamaki ba Taga Abdallah ya Shirya Cikin Riga da wando na kamfanin Armani Agaban Idanuwanta ya Shimfida Sallaya ya Tada sallaar Azahar din Data kubcemai Bata Gama mamaki ba Sai da taga ya idar Taga ya Daga Hannu yadade Yana Addu"a kafin ya Shafa,Tana Tsaye Ammh Ji takeyi Jikinta kamar ba Nata ba,Ninke sallayan yayi ya waigo Yana Kallonta Cike Da mamaki ganin yadda Ta Wani Chanza gabadaya ga A.c ammh Tana Zufa,Bai Kai ga mgana ba Tayi Wuf Tafada Tiolet tana Rawan Kafa,mele Baki yayi kafin ya Dauki wayarsa ya Fice Daga d'akin yana Lalubo Nombar Polina Domin Kewarta ne Yafi Damunshi ba Na Wasila ba,Kuma Yaga alamar Duk Dabaran Da Zaiyi Mata Bazata barshi Yafita ba balle Haryaje Wajen Polina.
******
Asma"u Ta sanya Abun Aranta Na irin Cin Zarafin da Yan"uwan Umma da Hajiya iya Sukayi mata,Tunda ga Ranar Walwalarta Ta ragu ko a Asibiti sai da Sister bahijja tayi ta Tambayanta ko Bata da lafiya ne..? Tace lafiyanta kalau,ganin batason Mganar ne yasa Ta Rabu da ita ammh yadda Ta karanci Asma"u ladan Tasan Akwai Abunda Ke Damunta,Kuma sanin Halinta na Zurfin Ciki sai Bata mtsamata na Sai Taji Kome ke Damunta baa.
Tundaga Lokacin Ta rage Fitowa Tsakar Gidan kamar Da da zata Fito suyi Hira da Anty Amarya ko Su Baba lami,ammh yanzu Ta dinke in Ta Dawo Daga Asibiti tana Daki kwance ko Tana karatu ko Tana Danna waya,in ko Bata da Aiki in tagaji da Zama Gidan Ammi take Tafiyarta sai yammah Tadawo,kosu Anty Amarya da Suka Dawo Ta Fahimci Wani Abu na damun Ma"u ammh sai Bata yi karambanin Tambayanta ba Sanin Halinta na Shigen Zurfin Cikin ammh A Cikin Ranta Tana Addu"ar Allah ya Kawo ma Asma"u Dauki Da gaggawa.
Itako Asma"u Duk da damuwar Mafarkan datake yawan yi Kwana biyun Nan da Zarar ta kwanta barci na wani bawan Allah Wanda ba"a Bayyana Mata Fuskarshi ba,Yana Cikin Wani katon Rami Mai Dauke da Kunamu da macizai da Wasu Ababen Marasa kyan gani,Ta Cikin Rami yake Miko Mata Hannu alamun Ta taimakeshi Sai ta rasa yadda Zatayi Dankwalin kanta take cirewa ta Yayyaga ta kullah Ta wurgamai ya Kama Kenan tana Kokarin jawoshi har ya Kusa Fitowa,sai ga Wata Mata ta bayyana Itama bataga Fuskarta ba Tayi Wurgi Da ita ta Fadi gefe Kuma taTura Mutumin ya Koma Cikin Ramin Tana wani Dariya Mai ban Tsoro,adaidai lokacin Asma'u ke Farkawa a firgice Tun Ranar Data Fara wannan Mafarkin Abun yake Damunta Data Farka Bata komawa Barci Zata Dauro alwala tazo Tafara sallah Tana Rokon Allah ya kareta Duk da Bata da ilimin Fassaran Mafarki Abun Yana Damunta ganin Ba sau Daya ba Tataba Mafarkin Ba Koma miye Toh tabbas Yana Bukatar Taimakonta ne,Abun mamaki Kuma Mafarkin Datayi Na karshe Taji Ana Kiran Sunanta Da Karfi Daga Cikin Ramin,ko Tayi Niyyar Zuwa gaban Ramin Don Taimakonshi Wannan Muguwar Matan Bata barinta,Abun Duk ya bi ya Dameta kafin Wani Lokaci Ramarta da Damuwarta Sun bayyana Ajikinta da Kuma Fuskarta.
_Zaku samu Damar Karanta littafin *ZAMAN GIDANMU* Kan 200 kachal,ta wannan Account Nombar kamar Haka 0552179550 Jamila Umar Gtb,bayan An dauki Hoton Trancsation din an Turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Waya na Mtn bayan an Dauki Hoton katin sai a turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Yan Niger kuma zasu biya 300f...Ina maraba daku Masoyana masu Son Cigabana.._
*Anitha..*❤️
*06/04/2020..*✍️
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*😘
_*Alhamdulillah Allah Ne Abun godiyata akoda yaushe,Tun kafin LABARIN ASMA"U Ko nace ZAMAN GIDANMU yayi Nisa Mutane Sun Fara Tsinta ko Nace gane inda Alkalamina ya Dosa,Naji Dadin hakan Sai Dai Tunda Nafara Rubuta Wannan Lbrin na Samu Text massages da Kiran waya Babu Adadi,Wato Yan Mata Da dama Suna Cikin Wata Rayuwa,Daga wacce Zatacemin kamar Lbrinta Nake Rubutawa sai Wacce Zatacemin Wlh Abunda Ke Faruwa Da Asma"u Yana Kan Faruwa Da ita!Ya illahi Wlh Tallafi na Zubarma da Sakonnin Wasu Hawaye Dadama,Shiyasa Nayi Amfani Da Wannan Damar Wajen Jawo Hankalin iyayen Mata Da Maza,Matar uba kike..?Antyn gida ne..? Uwa ce ke..? Toh ki Natsu Wlh Allah kadai ne Maiyi ,kuma ya Umarta yakuma faru a lokacin,Karmu Manta AURE na Allah ne,In kina Tunanin Ni ya"yana Sunyi Aure ko Kannena sun Samu Miji ko ya'yan Yayyena duka Sun Samu Miji shikenan sai Kifara zunden Wance,ita Bawani Lbrin ne..? Kuji Fa Wasu ma Cewa Suke Toh Wance Waye Kuma alayi.? Tun suna ganin Zabi ta tsayayi harda daga karshe Kiji ana Fadin Ta Tsaya jiran Mai Kudi,kuma iyayenta Na ganinta..! Plz my Sisters iyayenta Suna Da Ikon Aurar da Itane indan Allah bai yarda Ba,Wlh Aure da mutuwa lokaci ne,Ubangiji ke Dibanmusu,in Lokacinka Yayi Ko ka kashirya Ko baka Shirya ba,Wlh Zaka Mutu hakama In Lokacin Aurenka Yayi Ba Mutum ba Aljannah babu Wanda ya Isa ya Hana,Saboda karfin Lokaci Da Rabo Har Rasa Rai anayi,Kuma Haka Zalika In Lokacin mutum baiyi ba Wlh duk son Mutum da Aure Haka Zai Hakura Sai Ranar Da Allah yace,Shiyasa nake Kira Da Mu kama Allah Shine Majibincin Kowani Al"umura tare da Rokon Duk Wanda ya Karanta Wannan page din ya Daga Hannun ya Rokon Ma Duk yan'matan dasuke gaban iyayensu Babu Mijin Aure Allah ya basu Mafi alheri albarkacin Wannan Watan mai zuwa Mai albarka Wato RAMADHAN...AMEEN*_🤲👏😪
*LAST FREE PAGE*👐
1️⃣5️⃣
*BAUCHI*
Misalin karfe 4:30pm na yammah,Proof.Muhamud Abdallah Azare Yana Zaune Acikin Daya Daga Cikin Manyan Kujerun Falonshi Wani Littafin Azkar ne Ahannunshi Yana karantawa Yana Sanye da Wata Jallabiya Doguwa Mai Ruwan Toka Harda Wata Hula Mai Kama Da Tabani Kaji Hadisi,😂,Idanuwansa Sanye Da Wani Siririn Glass Wanda Ke Taikamai Wajen Karatu,Gefe Daya Kuma Kira"a ne ke Tashi Acikin Katon Talabijin Din Dayayima Falon kwanya tashar Manara TV ne Suka Sanya Karatun Alqur"ani Cikin Suratul Ankabut,Cikin Kira"ar munshawi.
Hajiya Tayi Sallama Ta Shigo Falon Cikin Kulawa ya Amsa Mata Sallaman Yana Kokarin gyara Zamanshi Lokaci Daya Yana Kallonta Kusa Dashi Ta Zauna Tana Fadin"Barka Da Hutuwa Mallam.."Bai Dago ba sai da Ida Karatun Dayake kafin ya Janye idanuwansa Lokaci Daya Yana Rufe Azkar din Dake Hannunsa.
Dubansa yakai Kan Hajiya kafin ya Saki Mirmishi Yana Fadin"Yauwa Hajiya Hajiya Uwar Abdallah bawan Allah.."Ya Fada Da Sigan Zolaya,Mirmishi Ta Saki Tana Fadin"Kai Mallam Baka rabo Da Zolaya yau Kuma kirari Akejin yi ne.."Mirmishi ya Saki Kafin