bata samu Hutu da barci da kuma Kaucema hayaniya,Toh bazata rabu da Wannan Azababbar Ciwon kan ba.."Jinjina kai Maman Fati ta Cigaba Dayayi alamun gamsuwa kafin tace"Hakane Kam,Allah yayi Miki albarka kema Allah ya jikanki ya baki mai miki Asma"u.."Ta amsa da Ameen Cikin Farinciki kafin tace"Me zan Tayaki Dashi Mama..?
Maman Fati tace"Na kammallah komai Saura kadan na Karisa,Ammh Sai dai ki Shigarmin wajensu Mahamud yanzu haka Suna chan Wajen Tsiyansu na Fama,Shida Fati basu Shirya ba.."Kada kai Asma"u tayi tana Fadin"Toh mama,...Tafada tana Kokarin Ficewa Daga kichen din,Ta sa baki ta kirata.
Asma"u...!Ta fada da kakkausan Murya alamun ba wasa kafin ta juyo tana maida hankalinta kan Asma"u Data waigo tana Fadin"Na"am Mama,.."Ajiyar Zuciya Maman Fati ta Sauke tana dafa hannunta ajikin Cabenet din dake kichen din kafin tace"Ya zaman gidan mahaifinki ta chanza zani koko har yanzu yana nan ayadda na Sanshi..."? Tafada tana Tsurama Asma"u ido,Saurin Sadda kanta Ma"u tayi kafin tace"Bai wani Chanza ba Mama,Kawai kinsan yau da gobe sai Allah,Nida ba Wuni ma nake agidan ba ina zasu ganni,.."Tafada tana kokarin boye Damuwarta.
Girgiza kai Maman Fati tayi kafin tace"Haka dai kika ce Asma"u ammh ni na Haifeki nafi kowa sanin Zurfin Cikinki,Abunda nake So dake ki kara hakuri akan Nada,Insha Allahu Jinkirinki ya kusa Zama alheri.."Kan Asma"u na kasa ta amsa da Allah yasa acikin Ranta,Maman Fati na kallonta sai ma ta kada kai Ta juya tana kokarin Juya Dankalin Dake Cikin Mai take Fadin"Shikenan Dama,Jeki Dubamun Su Fatin in Sun Shirya.."Bata yi musu ba ta juya jikinta asanyaye ta Fita Daga kichen din,Maman Fati ta bi bayanta da kallo Cike da Tsausayi kafin Ta Kada kai Tana Fadin"Allah gamu gareka..."
Koda Asma"u ta Shiga Falon Maman Fati babu kowa,cikin bedroom taji hayaniyar Su Fati,koda ta Shiga ta Iskesu Sun sarke da Rigima kan Wandon mkrantansu Na hadda,dayake iri daya Ne,Karisawa tayi garesu Tana Musu Yar dariya,suna ganinta gabadayansu Suka tafi gareta Suka Fada mata Suka Rumgumeta suna gaisheta da kwana,amsawa tayi tana Shafa kawunansu,Cike da Farinciki da Annuri.
Ita ta Raba Rigimar bayan ta Fidda ma kowa wandonshi kuma ta Taimaka musu Suka Shirya,Kafin 7:30am Sun Fito Falo,lokacin kuma Maman Fati Tagama Hada musu Breafsat,ta kuma Zuba musu Cikin Luch box dinsu,Karyawan ma Sama sama Sukayi Ruwan Tea kadai Suka Sha,Fati ne ma taci buredi ammh Shi Mahamud irin Mallam ne bayacin Buredi dayake ma takwaranshi ne,kuma Mallam din da kanshi ya hana Kowa ya sakaya Sunan Yace kowa ya Kirashi da Mahamud dinsa.
Sai da Suka Biya Shashen Proff.Suka gaisheshi da kwana zasu Shiga wajen Hajiya Asma"u ta hana tace ta kwanta,Dole Suka Hakura, haraba gidan Suka Fita da gudu kowanne da jakarsa,hanuun kowanne Rige da basket dinsu,Tunda Hadda mai Hade da Islamiya ce sai yammah Zasu Dawo,Koda Suka Fita har Mamman yazo,Shiga mota kadai Sukayi yajasu Suka Fice Daga gidan Zuwa mkrantar Nasu.
Suna Fita Asma"u ta koma Shashen Hajiya,Tunda Maman Fati ta Shigarma da Mallam Abun karinshi Shashenshi ta barmu Nata ita da Hajiya a kichen tace ta Dauka tatafi Dashi Chan Shashen Hajiyar,Tana komawa Ta Shiga gyaran Falon Hajiya dayake ma ba wani datti yayi ba Cikin lokaci ta gyara ko"ina,hatta Dayan bedroom din sai da ta Shiga ta gyarashi ta wanke Tiolet,Dakin Hajiya ta koma ta isketa Haryanzu Tana barci,Toilet din ta Shiga wanka ta wankeshi tas kafin ta Fito tana kauda wasu kayan Hajiya dake Bisa gado,Duk ta Ninke mata ta Bude Wardrope dinta ta Saka mata,ganin har Lokacin Hajiya bata tashi bane yasa ta Shiga wanka,bayan ta Fito ta Tsane jikinta ta Jawo jakarta ta Fito da Manta Olive ta hau mulkama jikinta,sai da ta gama tsab,Kana ta Fito da wani Less dinta Doguwar Riga mai Kalan Maruon,da Zanen ja,Dinkin A shape ya Dace da Surar jikinta,Dankwalinta ta Daura irin Daurin Zamani na Zahra Buhari,Bata yi ma Fuskarta kwalliya ba,illah Liptick data Shafama bakinta.
Tana gaban Madubi tana kallonta Kanta Cike da Sha"awa yadda Fuskarta ke Nuna Annurin datake Ciki Kwarmin Wuyanta tataba,Tana wani Mele baki,Yar dariya Tayi kafin ta Juyo Ta maida Sauran kayanta Cikin akwatinta Ta maidashi a ma"ajiyarsa,Fita tayi Daga dakin Cikin Natsuwa,Babban Falo ta koma na Ta iske Wata yar Dattijuwa Na Share Falon,bayan ta gama Gyarashi, tana ganin Asma"u ta Shiga Gaisheta Cikin Girmamawa,Ma'u ta amsa Tana kara gaisheta Duk da bata santa ba,Tana jin mai aikin ne Wacce ke tayasu Share Share ammh bata kwana ba,da zarar tagama ne kila take Tafiya gida,Don ko Jiya data Iso bata ganta ba.
Dakin Maman Fati ta koma,sai Ta iske batanan ,Tana Shashen Malam kenan,Fitowa tayi ta Fada kichen ta Iske Abun karinsu,Cikin Wani katon Faranti mai Fadi,Dauka tayi Ta fito ta Nufi Shashen Hajiya Cikin Tafiyarta Na natsuwa,da Kallo Yalwa ta Bita tana Tunanin ina kuma aka Samu Budurwa mai Kirki haka ganin bata da amsa yasa ta koma ta Cigaba da Abunda ke gabanta.
Afalon hajiya Asma"u ta ijiye Farantin kayan karyanwansu,bayan ta Ja Center Table din Tsakiyar Falon Ta Dora akai,Bedroom ta Shiga tana Fatan Allah yasa hajiya ta Farka,tana Shiga ko ta ganta Zaune,Mirmishi Asma"u ta Saki tana Fadin"Sannu Hajiya,ina kwana.."Hajiya na Hamma tace"Lafiya lau Ma"u,sannu da kokari Nagode Fa,Allah ya saka miki alheri.."Bata amsa ba ta Kama hanyar Tiolet tana Fadin"Hajiya bari na Hada miki Ruwanka mai Dan Dumi ki Shiga ki Watsa kizo ki karya Kisha magani Zaki karajin Dadin jikinki.."Tafada tana Tura Kofar Tiolet.
Da kallon Sha"awa Hajiya Ta bita dashi kafin tace"Toh ma"u Yanzu kuwa don Wlh Tun jiya Zuwa yau naketa jin Dadin jikina,Babu Abunda Zence dake sai godiya."Ma"u tana jinta ta cikin bayi ammh bata ce Komai sai dai kawai ta Murmusa.
Tana gama Hadama Hajiya Ruwan wanka ta Fito,da hajiya ma Zata tashi ita ta Taimakamata ta rakata har bakin Tiolet din kafin ta barta ta Shiga koda Hajiya ta Fito,har Asma"u ta Fito mata kayan data zata saka harda man da Zata Shafa,Hajiya bakinta ma ya kasa mgana Gyada kai kawai take Cike da Murna ta kuma kara Sakama Asma"u albarka acikin Zuciyarta Falo Asma"u ta koma bayan ta Sanar da Hajiya in ta Shirya ta Fito Su karya da Toh ta amsa tana Fadin"Allah yayi albarka Asma"ul Husna.."
Kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta yada Zango,wayarta dake hannunta wacce ta Dauko da Cikin dakin,Ta kunna sai ga haske ya bayyan,dan Kishingida tayi kafin ta latso Nombar Rabin Ranta,Ringin Uku tayi Aisha ta Daga tana Fadin "Nayi Fushi Rabin Raina,Shikenan kuma daga Zuwa Bauchi an samu Mama da Hajiya an Manta dani ko..? ta karishe Cike da Tabara,Yar dariya Asma"u ta saka kafin tace"Kedai bari Rabin Raina,Allah Bauchi Tafi Dutse dadi,.."Wata Dariya Aisha ta saka kafin tace"Da gaske,Kodai...Ko...Kodai....."Katseta Asma"u tayi tana Fadin"Kodai..Me...? tafada tana Hade rai,Shekewa Dadariya tayi,tana jin muryan Fahad,shima yana Tayata Dariyan,girgixa kai Asma"u tayi kafin tace"Allah ya Shiryeku daga ke Har Mai Daure Miki gindin.."Tafada tana Gyara Zama,Ameen AIsha tace kafin ta Shiga Tambayan Su hajiya Asma"u na Fadin Duk Suna lafiya basu gama,gama mgana ba Aisha ta yanke Kiran tana Fadin Rabin Raina ina Zuwa,daidai lokacin Hajiya Ta Fito Daga Bedroom din ta Shirya tayi Tsab da ita.
Da Hanzari Asma"u Ta mike ta taro Hajiya akasa ta Zaunar da ita bayan Ta kara mata Filullunkan Kujera guda biyu,tana kuma Jeramata sannu Farantin Abun karyawan Ta dauko Ta ijiye agaban Hajiya Tana Fadin"Hajiya me zan Hada miki ne,?gadai Soyayyen Arish,da kwai sai Ruwan Tea,sai Soyayyen Buredi.."Gyada kai Hajiya tayi kafin tace"Kafin tace Bani Soyayyen Buredi,sai ki Hadamin Ruwan Shayi.."Cikin Natsuwa Asma"u Ta hada mata komai Ta Tura mata gabanta tana Fadin"Gashi Hajiya,Ki cinye sai kisha mgani,Ko zaki koma barcin ne bayan kin gama.."Tafada tana yar Dariya.
Mirmishi Hajiya tayi Mata Kafin tace"Kina Shagwabani Asma"u,na Zama yar gata,..."Asma"u na Mirmishi tace"Toh Hajiya in bamu ji dake ba,wazai ji dake..? Kuma wannan barcin Dakikeyi, Shine kadai Zai kara Taimaka wajen Saukar Da jininki.."Jinjina kai Hajiya tayi kafin tace"Naga alama.."Tafada tana jan Filet din Soyayyen Buredin gabanta ta Gutsura ta Tura abaki Lokaci Daya Tana Kurban Shayi.
Gefe Asma"u Ta koma bayan ta Zuba Shayi awani karamin Kofi tana kurba,Kallonta Hajiya tayi tana Fadin"Ma"u bazaki ci Ko dankwalin ba naga Shayin kadai kika Zuba.."Yamutsa Fuska Asma"u tayi kafin tace"Wlh ya Isheni Hajiya,bani Son Cika Cikina da Safe me yanzu Duk Jikina Zai Mutu Wlh,sai Zuwa anjuma kila naci.."Hajiya bata ce komai ba Sai da Ta hadiye Abunda ke Bakinta kafin tace"Toh Shikenan,dama ku ma"aikatan lafiya Koda yaushe Ciki akida kuke,haka Dr,Nura yake Kullum Cikin Tsari.."Yar dariya Asma"u Tayi batayi mgana ba.
Sun Dade da Hajiya anan Falo,har bayan Sungama karyawa ta Maida Kayan da Suka bata kichen ta Iske yalwa na wanke wanke,sannu da aiki ta mata kafin ta koma wajen Hajiya,mganinta ta tambaya ta sanar Da ita Inda yake,ta Dauko ta Zo tana Dubawa kafin ta babbala ta bata tasha tasha kenan Sai wayar Hajiya ta Dauki Tsuwa,Daga cikin daki,Asma"u ta Shiga dakin ta Daukota yusuf ne ke kiranta tadaga Suka gaisa bayan ya Tambayeta jikinta tace da Sauki,Zainab ya bamawa Ta gaishe da Hajiya nan Hajiya ke Fadamata taji Sauki Sosai Asma"u tazo tana Kara Kula da ita,Zainab Taji Dadi nan take tace abama Asma"u Waya Su gaisa.
Cike da Fara"a Suka gaisa da Asma"u kafin Suyi sallama,Asma"u ta mikama Hajiya wayarta tana Fadin"Hajiya ki koma ki kwanta Zuwa anjuma kya Tashi.."Hajiya batayi gaddama ba ta yunkura ta Mike Asma"u na mata sannu,har dakin Ta Rakata bayan ta kwanta ta Lullebe kafafunta da blanket,kallonta Hajiye Keyi tana kara Yabawa da Kirki da Natsuwar Asma"u,Falo Ta koma hannunta rike da waya,ta Kwanta Bisa kujera tana Danne Danne Bisa wayarta.
****
Yau Tunda ya Tashi yakejin kanshi yana Saramai,bai damu ba haka kuma ya Shirya ya Fice Zuwa Office Cikin Wannan Halin,Yana wajen aikin wayar Wasila ta samai Inda take Sanar Dashi yau Zata Dawo,Abunda ya kara bata Tsoro Shine Bai Nuna wani Dokinta ba kamar abaya,wanda wani lokacin ma,sai dai kawai Ta ganshi Abida yazo daukanta ammj sabanin yau sama sama ya amsamata kafin ya yanke Kiran,Kuka ta Fashema momcy dashi sai da tayi ta lallashinta Kafin ta Hakuri,jikinta ba Laka Suka kamo Hanyar Portharcourt,Ita da Samuel bayan Momcy ta jaddadamata Ta Danne komai,Kawai da Zarar Abdallah ya Tafi Bauchi Tayi mata waya.
*****
Misalin 09:08am Na rana yana Zaune acikin Office dinsa,duk yau yakasa Tabuka komai,Kujerarsa ke Faman juyi dashi Shiko Hannayensa kan Kuncinsa kamar Wanda akace Wani Nasa ya Mutu.Sanye yake da American Suit,Masu Ruwan Toka,Farar Rigarce kadai ajikinsa ya Cire Coat din ya sagaleta jikin kujeran dayake kai,Wuyansa kuma yana Matse da Tie dinsa mai Ruwan Toka,kallon Farko zakamai ka Fahimci Fuskarsa na so ta bayyana Damurshi,Idanuwansa har Sun Chanza launi.
Yana Cikin Wannan Halin ne,wayars dake kan Tiburen gabanshi Ta Dauki ruru,Sai da ta kusa yankewa kana ya Dago da kansa ya Daukan wayan,ganin Sunan *POL* 2 yana yawo akan Screen din wayarshi Bai dagaba illah Maida kanshi da yayi ya kwantar yana kara juyaw kujeran,Har wayar Tagaji da Neman Dauki ta Kashe kanta..
Ko Minti biyar ba"ayi ba,Naga ya Zabura yana Dafe kansa kamar Wanda aka Dakeshi akanshi,Mikewa yayi da Hanzari jikinsa na rawa Sosai,wayarsa ya Dauka yana Duba lokaci 09:30pm,Kwakwalwar kanshi Banda Kiran Sunan garin Bauchi Babu Abunda Take,Yana jin kowani bangare na Zuciyarsa da Ganganar jikinsa tana Kara Izashi,bai tsaya Neman wata Shawara ba ya Zari Coat dinsa,Wayarsa ya Dauka kafin ya Fice Daga Office din da Sassarfa,Yana Fitowa masijansa ya Matso hannu kadai ya Dagamai kafin yace"Ka Rufe Office din,Zanyi Tafiya ne.."Daga haka ya Fito haraban Wajen,Emeka dake cikin Mota Zaune,Kawai sai ji yayi M.A Ya bude bayan Mota ya Shigo,cikin Hanzari ya gyara Zamanshi,ganin yadda Ogan nasa yake Arikice yasa bai Wani tsaya Tambayanshi ba ya Tada Motar Suka Fice daga Haraban wajen
Sai da Emeka ya Daidaita Motar a saman kwalta,kafin ya waigo,zaiyi mgana kenan M.A ya katseshi Cikin Numfarfarshi yana Fadin"Airport.." Ya fada yana Dafe Kanshi Saboda yadda yaji Zuciyarsa ke Gudu,Da Hanzari Emeka ya Tada Motar Suka Fice Daga Haraban Wajen,Cikin Lokaci Lokaci Suka isa portharcoaurt International Airport,Cikin ikon Allah kuma M.A Na Fita ya Shiga Cikin Airport,nan ya samu Jirgin da Zai Tashi Zuwa Bauchi nan da Minti arba"i,Mota ya Dawo ya Umarci da Emeka ya Fita yayi Mishi Buking din Jirgi da zai Tashi Zuwa Bauchi,Cikin lokaci kalilan Komai ya kammallah,Emeka bai Tafi ba sai da yaga Tashin Jirgin su M.A kafin ya Tada Motar ya Nufi hanyar komawa gida yana Cike da Mamaki yau yallabai Zashi Bauchi wanda kusan Shekaru biyar yana Tuka oga,Ammh zuwanshi Bauchi kiragage ne,Koda ga ganin yanayin M.A din akwai babban Abunda ke Damunsa.
******
Around 2pm jirginsu ya sauka Abubukar Tafawa Balewa international Airport,Bauchi Daganan bai Tsaya ba ya Nemi Taxi yayi Tashanta har Zuwa Federal Lowcost,Sai akofar gidan Makeken Get dinsu aka saukeshi,Fitowa yayi Cikin Wani yanayi yana bin gidan Nasu da kallo,kafin ya Fiddo Walet dinshi ya Biya Mai Taxi din kudinsa..
Jikinsa Duk asanyaye ya Nufi bakin Get yana Kwankwansaawa,Megadi daya Taso ya hau Tambayan Waye..? Bai amsa mai ba Domin kunya yakeji ma yace Shine jin anyi Shuru yasa Megadi ya Bude karamar Kofar yana Lego da kansa,daidai lokacin da M.A yadawo da kansa wajen,Zaro ido Megadi yayi yana Rawan Jiki da Baki yace"Ya..Yallabai...Barka da Zuwa..."Yafada Cike da Farinciki ya Bude masa kofar,Yake kawai yamai bayan ya Shigo gidan,hannun ya mikamai Sukayi musabaha,Shiko megadi kallonsa yake yana Fadin"Ikon Allah,wai da gaske Yallabai kaine.."Yafada Cike Da mamaki.
Dan Murmusawa Abdallah yayi ya juya ya Fara Tafiya Zuwa Cikin gida,hannunsa Rike da Coat dinsa da wayarsa,Ko"ina na gidan yake da Kallo Cikin Wani yanayi ya iya Shekarun daya kwashe bai Zo gida ba,Babu Abunda ya Chanza sai ma Wasu gyaran da baisan dasu ba,Shiko Megadi har ya Kule yana kallonsa Don har Kulle idonsa yayi ya sake Budewa wai ya Tabbatar gaske ne ko Mafarki.
Cikin Takunsa na Isa,da jarumta ya Saka kanshi Afalon,sai dai kuma babu kowa,sai Talabijin dayake tayi Shi kadai Atashar Sunna Tv inda Suka sanya karatun alQur"ani Cikin Suratul Maryam Cikin kira"ar Sheik sudes,Ganin haka yasa ya Tsaya yayi Shuru yana bin ko"ina da Kallo,wata kewa na Tasomai,Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Dumfaru Hanyar da Sai da Shi da Sashen Hajiyarsa Domin ayanzu idanuwansa Sun Kewar ganinta Fiye da kowa.
Asma"u na kan sallah Tana Addu"a bayan ta Idar da sallah,barci ne ya kwasheta kan kujeran nan bata sani ba,har wajen 2 na rana ganin Shuru ya Sanya Maman Fati ta Shigo,ganinta tana Barci ne yasa tatasheta tace Tatashi tayi sallah Taci abinci, Tashi tayi Tana Mika lokacin data Duba lokaci acikin agogon wayarta tayi Mamakin barcin data Sha,wanda Tadade batayi Irinshi ba.
A kasalance ta Shiga bedroom din Hajiya nan ta tarar Da ita tana barci bata Tashi ba,AC dakin ta Rage mata kadan Duk taga iskar tayi yawa Tiolet ta Fada ta Dauro alwala tana Fitowa sai ta Dauki sallaya da Hijabinta ta Fito Falo ta Shimfida ta Tada sallarta Saboda bataso Tatashi Hajiya tafiso ta Tashi da Kanta.
Ta shafa Addu"ar kenan ta mike Kafarta Ya sawo kanshi Falon,inda Wani Siririn kamshi ya Biyi ta Kofar Hancinta na Turarenshi na Azzaro Visit,Lumshe ido tayi batare data bama Ina kamshin Ke Fitowa Muhimmanci ba,Shiko yana Shigowa da karamar Sallama jin ba"a amsa ba,sai yayi Tunanin Kila Hajiya na Ciki,kuma Shi harga Allah bai Lura da Asma"u dake Zaune Tsakar Falon ba,kawai Sai ya Fara taku Zuwa dakin Hajiya,Asma"u na Zaune sai ganin Mutum Tayi Tinkis Tinkis ya Wuce ta gabanta
Gabanta ya Fadi Ras"!ga Asma"u da Tsoro ammh haka Tamike tana Dafe da kirji take Fadin"Kai waye...? mallam lafiya zaka Shigoma mutane gida haka kurum kuma ka Wuto dakin Mutune ba Neman Izini.."Tafada tanabin Bayansa da Kallo Cike da Tsoro.
Cak ya tsaya kafin ya Waiwaiyo kadan Suka Hada 4 eyes da Asma"u yadda ya Zubamata ido ne yasa gabanta ya kara Fadi,Shiko ganin Farko dayayi mata Shima sai da gabansa ya amsa,basarwa yayi kawai Bai mata mgana Illah kallon Sama da kasa da yayi mata,Ya wani tabe baki kawai ya Juya Ya Shiga Dakin Hajiya.
Asma"u Tayi Wuri Wuri Cike da Tsoro saboda yadda ta Firgita ne yasa bata ga Tsantsanar kamar Baffa da proff.Ba cike da Tsoro ta kwashi Gudu Zuwa Shashen Maman Fati,bata Falo tana bedroom dinta tana Ninke kaya kafin Su Fati Su dawo Daga mkranta shi kuma Mallam ya Shiga mkranta Sunada Taro,,ji kiran da Asma"u ke Mata ne Tundaga Falo yasa gabanta ya Fadi,ta yarda kayan dake Hannunta ta Fito da Sauri sai gashi Sun Ci karo.
Cikin Mamaki Maman Fati ke Fadin"Lafiya Asma"u meya Faru..? Ma'u na haki ta Rike hannun Maman Fati Tana Fadin"Mama..Mama..Taho ki gani wani ne,Ya Shigo Har Falon Hajiya mama,kuma ya Shiga bedroom dinta ina ta tambayan waye yayi banza dani.."Cike Da Mamaki Maman Fati Tace"Wani kuma..?Kai Asma"u ta Daga har tafara kwallah Saboda Tsoro,Maman Fati bata Saurareta ba ta Kwashi Sauri Zuwa Shashen Hajiya Itama Asma"u ta Rufamata baya ammh Zuciyarta kamar ta Fito Saboda Tsoro Ita Duk Atunaninta Barawo ne.
*Shakira..*
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
Da karkarshinsa ya Tura Kofar Dakin Hajiya ya Shiga da sallama,ammh a ciki,dakin Shuru sai dai Wani Ni"imantattacen kamshi Turaren Wuta Daya Daki Hancinsa,Lumshe ido yayi kafin ya Bude su Fes yana bin Dakin da kallo har idonshi ya Sauka kan Hajiya Dake kwance kan gado Tana barci.
Cikin Sanyi Jiki ya karisa gabanta yana Kare Mata kallo,gabansa ne ya Fadi,ganin irin Ramar da Hajiya Tayi Duk ta Zabge Ba wannan kibar Nata,da Cikar Fuska mai Cike da karamci,Tsaye yayi yana kallonta idanuwansa Sun kala Sun karaja,yana ji kamar ya Durkushe Bisa kafafunsa. ya saka kuka,Hajiya ko dake barci dayake Duk Nisan barci Hayaniya kadan ko Mutum ya matso kusa da ita Zataji yanzu Zata Farka.
Ahankali ta Bude idanuwanta Da Suka Shige Saboda Barci,Abunda tagani yasata Saurin Maida idanuwanta ta Rintse kafin Wasu Siraran Hawaye Su Zubomata ta Gefen Fuska,gyara kwanciya tayi Kafin ta Murmusa tana Fadin',Har Sai Yaushe ne Baffa Zaka zo gareni,Akullum bani da wani mafarki sai na ganka Tsaye agaba.."Take Fada idanuwanta na Runtse tana kuma Share Hawayen da Suka ta gefen Kunnenta.
Jin Abunda Hajiya ke Fadi ne yasa baisan Sadda ya Durkushe gaban Hajiya yana kamo Hannunta ba,Cikin karaya Da Nadama ya Furta.."Gani Agabanki Hajiyata ki Bude idanuwanki Da gaske wannan Karon Baffanki ne agabanki ba Mafarki kike ba.."Jin Muryan Baffa da kuma Hannunta daya Riko yasa Hajiya Bude idanuwanta Fes akanshi,Kuramai ido tayi kafin ta wani Zabura Kamar Zata Fadi,sai gata Diro kasa da Mugun karfi har kafarta ta Turgude Yayi Saurin Rikota yana kallonta.
Kafadunshi Ta damka tana Girgiza Shi Take Fadin"Da gaske Baffa na ne,Agabana..? Abdallah kai ne kuwa Kodai haryanzu Ban Farka daga mafarkin dana sabayi bane na Kazo gareni.."Tafada Hawaye Suna kwaranyomata Kana Duka hannuwanta Biyu tana Shafa Fuskarshi,Shima kukan yake son Saki ammh kuma Idanuwansa Sun bushe Zuciyarsa ne kadai ke iya Fassara Hadin Bakin Cikin Dayake Ciki
Ganin haka kawai yasa ya Fada Jikin Hajiya yana Sauke ajiyar Zuciya yana Fadin"Ni ne Hajiyata Abdallah ki ne,Don Allah ki yafemin bansan meya Sameni ba.."Yafada yana Runtse Ido Saboda yarda Kansa yake Saramai,Ai da hanzari Hajiya ta Kamkame Shi tana Dariya Hade da Kuka tana Fadin"Alhamdulliah Allah Mun gode Maka daka amsa addu"armu ka dawo Mama Na Abdallah garemu.."Take Fada tana kamkame Dashi tana Dariya da Kuka lokaci daya,yau Hajiya Duk ta Cire wannan alkunya ta Dan Fari ta na murna Zuwan Abdallah.
Daidai Lokacin Maman Fati ta Shigo dakin Hankalinta tashe,Asma"u na Biye da ita abayanta,Ganin hajiya Rumgume da Wani Saurayi ta kuka yasa Suka yi Turus,Maman Fati bata samu Zarafin mgana Hajiya ta ankare Dasu,Da hanzari ta Saki Abdallah tana Riko Hannunshi take Fadin"Maman Fati mu gode ma Allah,yau dai ga Abdallah yazo garemu.."Sai alokacin Maman Fati taga Fuskarshi,Ware ido tayi kafin itama ta karisa tana Damko hannunshi take Fadin"Hajiya Da gaske,Abdallah nake gaani ko kuwa Idona Keman Gizo.."Tafada tana Shafa Fuskarshi Kai ya girgiza kafin kawai ya Durkushe gabanta yana Rike da Hannunta yace"Maman Fati,Ku min aikin gafara,ku yafemin Wlh bansan meya Sameni ba,har nayi wannan Tsawon Lokacin banzo gareku ba.."Yafada yana Sakin Nishi Sama sama.
Kamosa Maman Fati tayi Tana Fadin"Ai mu ba Laifi tsakannmu Baffa,sai godiya Ga Allah daya Sa kadawo kana Cikin Hayyacinka."Tafada Tana Dagosa,Hajiya Dake gefe banda Sharan Kwallah Babu Abunda Takeyi,kallon Maman Fati tayi tana Fadin"Kamar amafarki na ganshi Habiba,Waya gaya miki Zuwanshi...?
Maman Fati tace"Asma"u ce Tazo Da gudu tana Haki take Cemin ga wani Chan ya Shigo gidan,wai ya Shiga Har Dakin Hajiya,Ganinta atsorace yasa Na boyota nazo na gani.."Tafada tana waigawa bayan Inda Asma"u ke Tsaye sai dai Suka ga wayam,Bata adakin ita ko Asma"u Tunda Daga Hajiya Rumgume da Baffa tana Kuka Abun yayi Mata wani iri baya taja kawai Ta Fito daga dakin Tadawo Falo a zuciyarta Tana taya wannan Ahali Murna Dawowar Wanda Suka Dade Suna Nema.
Tsakanin Maman Fati da Hajiya Aka rasa wane yafi Rawan jiki,haka Suka Taso Shi Zuwa Falo suka Zaunar dashi kan kujera Suka jeru akasa Suna kallonshi Sun ma kasa gasgata idanuwansu na Yau Baffa ne agabanshi,Hajiya ko da kanta ta daga waya ta kira Mallam Tana Shaidamin ga Baffa yazo gida,Da farko ya zata Wasanta ne ya Tashi Sai da Maman Fati ta karbi wayar ta Rantse mai kana ya yarda,Hamdala yake tayi Acikin Zuciyarsa Tare da yima Allah Kirari Domin Shine Ke amsa Dukkan Rokon bayinsa...
Kafin kace kwabo An buga su Anty Safina waya an sanar Dasu kowacce ta Cika Da mamaki,Nan da nan Suka ce gasunan Tafe ko yusuf dake Kaduna Sai da Hajiya ta kirashi,bayan Sun gama mgana da Hajiya Saboda ya Tabbatar Sai gashi ya kira Wayar M.A din,Yana dagawa yahau Tambayanshi Da gaske yana Bauchi..? mirmishi kadai yayi mai Batare Dayayi mgana ba,Saboda baida Abunda Zaice kalli yadda kowa ke Murna,Yana da Ranshi da Lafiyanshi Cikin kwanciyar Hankali ammh ya bar iyayensa da yan"uwansa Cikin kewarsa da Son ganinshi har na Tsawon Wasu Shekaru,Shiko mai ya Shiga kansa Ne...
Asma"u na gefe Tana kallon Abun Mamaki,tana jinjina girma da Tasirin da Abdallah keda Shi Wajen iyayensa da yan"uwansa,Bata gama Mamaki ba sai da Mallam ya dawo haka Abdallah ya Fada jikinsa Lokaci Daya kuma ya Saki kuka,Kamar wani karamin yaro yana Fadin Su yafemai Shida Hajiya ,Shikanshi Mallam din Saida ya Share kwallah saboda Tsausayin Abdallah,sai yanzu ya kara yarda an Shiga Tsakaninsu ko daga yadda Abdallah ke Fadin baisan meya Faru Dashi ba ammh kwata kwata Aka Ciremin Tunanin Bauchi aransa,dasu gabadaya yanzu ma Yana Zaune kawai yaji in bai Taho Bauchi kamar Zai Mutu haka yaji.
Ranar fa Ansha Koke koke,haka Suma da Su Anty Nafi suka zo Fadawa jikinsa Sukayi Suna kuka,nan fa Rasuwar Farida ta dawo musu Sabuwa,Abun gwanin ban Tsausayi,Shiko Abdallah Bayason kannensa Suga Rauninsa,ammh kam ya Zubda da kwallar Rashin Farida Sosai,Haka su Fati da Suka Dawo Suma Sunyi mamaki ganin Baffa,sai Suka fara Dari Dari dashi sai da ya mika musu hannu yana kiran Sunayensu kana Sukaje gareshi ya Daukesu yana Tambayansu Ajinsu Nawa a mkranta.
Ranar dai Ashashen Hajiya aka Ayada Zango Tsakanin Mallam da Hajiya da Maman Fati da Su Anty Nafi ba"asan wa yafi wani Rawan jiki da murna kan Baffa ba,Asma"u dai Shashen Mamn Fati ta koma ta kwanta Don itama Wani lokacin bata Shiri da Hayaniya,Balle kuma bata Son ganin kukan Babba,Sun hada ido da Abdallah Lokacin dayake ma Mallam kuka yana Rokonshi gafara,yanayin yadda ya kalleta sai Da taji jikinta yayi Sanyi,Shiyasa ta Fito Daga dakin Ta koma Shashen Maman Fati
Sai Zuwa chan ne,Hajiya ke Cigiyarta Maman Fati tace tana Shashenta ta kwanta,anan nema take Fadama Baffa Asma"u ce yar Wajen Habiba Yarta dake Dutse bai bama mganar Muhimmanci ba,dayake Tun Asali ma Shi bamai Yawaan mgana bane,ko yanzu ma Dayake Zagaye Cikin yan"uwashi kallon Farko zakamai ka fahimci Fuskar ta bayyana Farincikin daya ke Ciki,ammh kuma Fuskarsa bata Nunawa yana zaune yana kallonsu,sai sun sakoshi ya dan Saki Fuska yayi Mirmishi kadai..
Ranar Farinciki ga iyalan Proff.Domin atare da Mallam Sukayi abinci cike da kauna,Kuma tare Sukayi alwala Suka Fita Zuwa masallaci Su uku Shida mahamud,Sai la"asar Asma"u ta Fito,ta koma Shashen Hajiya su ka gaisa Dasu Anty Nafi don Lokacin da Suka zo idonsu ya Rufe da ganin Dan"uwansu,Rumgumeta Hajiya tayi Cike da Farinciki tana