yace"Eh Mana Wato Hajara Kowa yagama Lura dake In Ana Son ganin Hakoranki awaje toh Ayi Miki Zencen Abdallah,Ciwo ya Kare ko Tunda yanzu Baffan Na Kula da Uwarsa Dakyau Dakyau.."Yafada Yana Yar Dariya.
Kunya Takama Hajiya ta D'an Dara Tana Rike Baki,Dariya Mallam Ke Mata Cike Da Farinciki yace"Kina Rike Baki,ko nayi Karya Tsakaninki ga Allah Zaki Fada.."Bakinta Awashe Tace"Ni bance kayi Karya ba Mallam ammh.."Dakatar Da ita yayi Yana Fadin"A"a bar Mganar Maman Nafisa Tunda Dai Kin San Gaskiya.."Yafada Yana Kallonta Lokaci Daya Yana Mata Dariya.
Gyara Zama Hajiya Tayi kafin Tace"Mallam wajenka Nazo Fa.."karkato Da Hankalinsa yayi Kanta Bayan ya saka Hannu ya rage Karan Karatun Da Remote din Dake kusa Dashi ya Maido da Hankalinsa Kanta Yana Fadin"Inna jinki Hajiya Allah sa Lafiya.."
Muskutawa Hajiya Tayi kafin Tace"Wani Tunani nayi Game Da Baffa Mallam.."Da Mamaki ya Kalleta kafin ya Maimata Sunan da Sigar Tambayan"Baffa Kuma..? Cike Da kwarin Gwiwa tace"Eh Mallam,Duk da yanzu Hankalinshi ya Dawo Jikinsa ya Fahimci Mune iyayensa Na har Abada Wanda Bai da kamarmu,Addu"armu Bata Fadi kasa Banza ba Mallam Tunda yanzu Zaka Ga Duk Safiya sai Baffa ya Kira mu Yana Tambayanmu lafiyanmu Wanda Abaya bamu Samu wannan Damar ba.."Ta Dakata tana Sauke Numfashi.
Mallam na Kallonta ya Kada Yana Fadin"Ina jinki hajara.."Cigaba da Mgana Tayi Da Cewa"Shine Na Zauna Nayi Tunanin Mai Zai Hana mu Samu Wani Abunda Zai Dawomana Da D'anmu gabadaya garemu Wanda Ko baizo Donmu ba Zai Zo Don Abunda Zamu Masa.."A Natse Mallam Ke Binta Da Kallo Kafin yace"Ban Tari Numfashinki ba Hajara Menene Wannan Abun Wanda Abdallah Ko baizo Donmu ba Zai Zo Don Shi..?"Cike da Kwarin Gwiwa Hajiya Tace" *MATA*..."
Da Kallon Mamaki Mallam ya Bita kafin yace"Mata Kuma..? Taya ya Hajara..? Hajiya Ta Numfasa Tana Fadin"Ma"Ana mu nema Masa Mata Daga barayinmu Mallam mu Aura Masa Koda bayaso,Kuma mu Ijiyeta Atare Damu Tilas Abdallah Zai Dinga waiwayan Gidan Ko badon mu Kodon Matarsa Dake Tare Damu.."
Mallam yayi Shuru Yana Nazarin Mganar Hajiya Kafin ya Kara gyara Zama,glass din idonsa ya Cire ya ijiye Kan Hannun kujeran Dayake Kai yace"Banki Taki ba Hajara Ammh Wani Hanzari ba Gudu ba Wata Yarinyace kike ganin Zata Dace da Yanayin Abdallah,Karka ki Manta Shedaniyar Matarsa Bata barsa Haka ba,Duk da Nasan Abdallah bazai Bijirema Umarninmu ba,ammh Fa kinsan yanayin Da"ake Ciki Hajara Azo Aneman ma yaron Nan Aure ,Daga Baya Ya Gudu ya barmu Da Jin Kunya,in mu munyi Hakuri Mun Nuna Juriya mu Iyayen Baffa ne baza mu Taba kin D'anmu ba Ammh Matar fa,da Yan"uwanta Watarana fa Zasu Gaza Hakuri Har Zuciyoyi Suzo Su baci,shi nake Gudu Hajara Tuntuni Shiyasa Kika ga Banta b'a Kawo Shawaran Mu Matsama Abdallah yakara Aure ba Tun Abunda ya Faru na Farko game da Aurensa da Matarsa daSuke Tare yanzu.."
Yafada Yana Sauke Numfashi,Hajiya Tace"Duk naji batunka Mallam kuma na yarda Dakai ammah Da yardan Allah Muna Kai kukanmu gareshi Bazai karabama Wannan Shedaniyar Matar Tashi Dama Akanshi ba,Mganar Yarinya Kuma kwantar Da Hankalinka ta Gida ce,Kuma Kaima Nasan Zaka Yaba da Zabina zakuma Ka yabama Hasashena Mallam.."Kai Tsaye yace"Wacece..?
Sai da Hajiya ta Murmusa kafin Tace" *ASMA"U...CE..*.." Tafada Fuskarta na bayyanar Da Annuri,cike da Mamaki Mallam Ke Kallonta kafin yace"Wata Asma"un..? Kai Tsaye Tace"Asma'u Dai daka sani Mallam Yar Wajen Habiba..."Tsam Mallam yayi Yana Bin Hajiya da kallo ganin Haka yasa Hajiya Tayi Saurin Cewa"Don Allah Mallam karkace A"a Wlh kafin na Tare Ka Da Mganar sai Da nayi Addu"a sosai Alan lamarin Kuma naji Zuciyata ta Natsu da Mganar,Mganar Gaskiya Asma"u yarinyace Burin kowani Namiji Mai kima ga Tarbiya ga Natsuwa ga Hankali Uwa Uba ga Addinina na Tabbatarmaka Alheri ne Matukar Baffa ya samu Dacen Samun Asma"u a matsayin Matarsa..."Tafada Cike da Tabbatarwa.
Ajiyar Zuciya Mallam ya Sauke Kafin yace"Hakane Duk Abunda Kika Fada Akan Asma"u Gaskiya ne Ni kaina Shaida ne Tunda Ga Mahaifiyarta Nan Muna tare Da ita Shekara da Shekaru Kuma bamu Taba samun Wata Mtsala ba sai Abunda ba"a rasa ba,Shin Hajara kina ganin Babu Matsala,ta bangaren Ita Asma"un ..? Bangaren Habiba Dai Babu Shakka Nasan Ba Mtsala."..
Baki Hajiya Ta Washe kafin Tace"Babu Mtsala Sam Mallam Asma"u Yarinyar Kirki ce,Bazata ki Abunda Muka Zo Mata Dashi ba,yanzu Dai Kafara yin isthikara Akan all"amarin In kaima Zuciyarka Ta Natsu kamar Nawa sai Mu Tuntubi Habibar Duk Da Nasan Bazata ce Komai ba,sai Asan Abunyi Banaso Abun ya Dau dogon Lokaci...
Gyada Kai yayi Kafin yace"To Shikenan Ba Mtsala Zanyi Zuwa Gobe ko Jibi Sai na Kira Habiban Mu Tattauna Allah Ka Shigemana Gaba.."Hajiya Ta Karba Da Ameen kafin Su Cigaba Da Tattauna Mganar Hajiya Nata Kara Karfafa Mganar Don Dai Mallam ya Amince 100%ai ko Tayi Nasara Domin Shawaran Hajiya Ta Zauna Sosai Acikin Ransa.
******
Hajiya Kudirat Tana Cikin Tashin Hankali sosai Sakamakon Washegarin Ranar Da Sukayi Mgana da Wasila Ta Nufi Kauyen Bamuzagi Wajen Boka D'andugaji Cikin Motarta Sai Dai kuma Kash Tayi Rashin Sa"a Domin Koda Taje Bukar Boka Tana Rufe Masu Tsaron Wajen ne Suka Sanar Da ita Boka D'andugaji Yana Cikin Bukarsa ya Shiga wani Aiki ne Dake Bukatar Shiri Sosai Bazai Fito ba Sai Yayi Wata Daya Cur Saboda Haka Duk Mai Bukatar Ganinshi Sai ya jira har Zuwa Lokacin da Zai Gama Aikinshi Ya Fito Daga Cikin Bukar Tukunnah..
Hajiya Kudirat Ta Dora Hannu akai kamar Ta kurma Ihu Saboda Takaichi Da Bakinciki,yanzu Ya Zatayi da Wasila..? Wacce Tun Safe Take Dokamata Kiran Tana so Taji tatafin ko A"a..?Gashi A Ka"idar Aikin Boka D'andugaji kafin ya Fara Yi Miki Aiki Sai ya Kafa Miki Dokokinsa Ciki Harda Da Zarar Kin Fara Dogara Dashi Toh Har Abada bazaki Guje Aikinsa ba Kijema Wani ba,In Hakan Tafaru Duk Abunda ya Faru Da Mutum Shi yaja Kana Uwa Uba Aikinshi Baya Bukatar garaje,Ko Wutar Ciki Baya Son gaddama In yace Ga yadda Abu Zai Tafi Kada Ki Nuna Taurin Kai,kawai ki Amsa Ki Koma Gida kijira Sakamako,Kuma sai Ka Amince kafin yafara Maka Aiki.
Wannan Dalilin Shi yahana Hajiya Kudirat Zuwa Wajen Wani Bokan taKoma Gida Cike da alhiini Tare Da Tararradin Abunda Zata Fadama Wasila Tasan ko giyan Wake Tasha Bazata Fadama Wasila Cewa Bata ga Boka ba,Don yadda Wasila TaHaukace Tsab zata Nemi Wani Bokan Ka,Kuma yin Hakan Tamkar Rugujewar Rayuwartane Da Rayuwar Wasila Gabadaya,Shiyasa tana Komawa Gida Kafin Wasila Ta kirata ta Kirata ta Shararamata karyan Taga Boka yace Su Jira Nan da Sati Daya Abdallah ko Garin Bauchi yaji an ambata Sai ya Suma Balle har Ace zashi,Hartana Fadin ya Tabbatarmata ko gawan Abdallah ba Wanda Zai iya Kaita Bauchi..
Jin wannan Lbrin yasa Wasila Taji kamar An Tsumdumata Acikin aljannah ne,Ada Tafara Sarewa ammh Jin Haka Sai karkarshinta ya Dawo Tana kuma Lura da Abdallah yadda yadda Chanza yanzu Ibada akan Lokaci Kana Baya Wasa Da Ruwan Addu"an shi Dama na Sati Dayane ya Kusa karewa Kuma Koda Wasa Baya Barin Wardrope dinshi Abude Indai Zai Fita,Wanda kamar ya sani Don Wasila ta Kudiri Niyyar Zubar Dasu Sai Dai Bata samu Dama ba,Bai Daina Sonta ba,sai da Kuma ya Chanza ya Daina Tsoronta ba wannan biyayyah ba Wannan Sadda Kan,yanzu In Yana Mata Mganar har Faduwar Gaba Takeji,ga Wani Tattali Dataga Yana bama Iyayenshi Koda yaushe Cikin kiransu yake,Hadda Shegun kannennan nashi Suma Suna kiranshi Suna Wani iyayi Abun Baya Damun Wasila Dariya Take Cikin Ranta Tana Fadin"Tabasu Lokaci ne,kwana Kadan ya Rage Abdallah ya Kara Zama Nata akaro Na biyu.,sakaryar Batasan Cewa wannan Karon Abun Na so ya Gagareta ba
Ko Polina Taga ya Chanza So Ammh Bata Damu ba, Domin Ta Fahimci alkadarin Wasila ya Fara karyewa bata Nunamai Komai ba Suka Cigaba da Sheke ayarsu Son Ransu Don Kullum Suna Nanike Da Juna,Domin Polina Tana Daraja Abdallah, Zuciyarta na Sonshi Gashi Dai ba Addininsu Daya Ammh Tafi kowa Sanin kyawawan Dabi"un Abdallah Da Kowacce Mace Zatayi Fatan Ya Zama Nata Har Abada,yayi Mata Komai Arayuwa yazama Uwarta ya Zama ubanta ya mayemata gurbin Yan"Uwa Kuma ya Zama Wani Ginshiki Gareta,Shiyasa Take Fatan Itama ta Samu Dama ko yayane Ta sakamai Da Abunda Yayi Mata duk Da Tasan Har Abada Abdallah bazai Taba Aurenta ba,Itama Kuma Bazata Aureshi ba Saboda Ba lalle bane Suka Kara Maimaita Shekarun Da Sukayi Abaya ba.
*****. ******. *******
Bayan Kwana biyu Dayin Mganar Hajiya Da Mallam,Proff. Da kanshi ya Kira Hajiya Da Habiba Falonshi bayan Shima yabi Shawaran Hajiya Yayi Isthikara Akan Al"amarin Kuma Alhamdulillah Zuciyarsa Ta Natsu Da Abun,ajiya ya kira Yusuf away Yana Sanar Dashi Abunda Hajiya Tazo Dashi Nuna Irin Farincikin Da Yusuf ya Shiga ya kasa Boyuwa Duk Da baitaba Ganin Asma'un ba Ammh yanajin Zainab Tana yabon kyakyawan Halin Yarinyar,Kuma ko Bama Haka ba In har kasan Wacece Maman Fati zaka So Hada Iri Da ita Sakamako Mace ce Mai Kyawawan Hallaya Da Dabi"u masu Kyau Duk Da Wani Lokacin Albasa Bata Halin Ruwa,
Sun Dade Suna Tattaunawa Da Mallam Inda Suka Tsaida Mgana Kan Gobe Yusuf Zai Dako Sammako yazo Nan Bauchi Jibi In Allah kaimu Sai Su Tafi DUTSE Wajen Mahaifin Asma"u Domin Nemama Baffa Aure Akaro Na biyu Tunda Dai An Tsaida Mgana So Bai Kamata A tsaya Wani Bata Lokaci ba Duk Wani Lokacin Gaggawa Aikin Shedan ne,ammh Kuma Shima Wani Lokacin Abari ya Huce Yana Kawo Rabon Wani.
Mallam ne ya Korama Maman Fati Da Shawaran Hajiya Da Abunda Suka yanke,Daga sama Maman Fati Taji Mganar Ta Dinga Maimata Sunan Asma"u Da Baffa Acikin Ranta Lokaci Daya Zuciyarta Na Tsinkewa Bata Da Abunda Zatace Kila Dama Shine Mijinta Tuntuni Duk Wannan badakalan Da"akeyi,Kallon Mallam Tayi Da Hajiya kafin Ta Murmusa Tana Fadin"Haba Mallam,Menene Nawa Aciki ai kaida Hajiya Kunfi iko Da Asma"u yarku ce Ta Har Abada Kuna da Ikon Zartar Da Duk Abunda Kuka ga ya Dace Da Ita, Hakika Kowacce Mace Zatayi Fatan Baffa yazama Mijinta Duba da Tarin Nagartar Da Allah Yayimai Naji Dadin yadda Kuka Nuna Sha"awarku Kan Kara Hada Zuru"a Dani Badamuwa Allah ya Tabbatar da Alheri Ni meye Nawa Aciki Sai Abunda Mahaifinta yace Ni Uwar Baffa ce ga Uwar Asma"u Nan Kusa Dakai Mallam Saboda Haka Kada ma Wani Abu yataso Asake kirana ko Asakani Aciki."Tafada Kai Tsaye kafin Tatashi Ta Fice Daga Falon Hajiya Da Mallam Suka Bita da Kallon Sha"awa Akullum kawaichin Habiba na Burgesu Bata da Kwaramiya ko Hayaniya Bata Kuma Nuna ya"yanta Nata ne Tafi Kokarin Jan Su Anty Nafi ajiiki Fiye Da Su Fati Ita Haka Allah ya Halliceta.,Bayan Fitarta Mgana Suka Cigaba da yi na yadda Komai Zai Tafi Daidai Mallam ya Tsaida Mganar Sai Sun Dawo Daga DUTSE kana Zai Kira Abdallah ya Sanar Dashi,Cike Da Fara"a Hajiya ke Fadin Sai Wannan Karon Tasan Baffa Zaiyi Aure Domin Shagali za"ayi kamar Ba gobe,Mallam baice Komai Ba illah ya Murmusa Yana Kallon Hajiyar.
Itako Maman Fati Daki Ta Koma Ta Zauna Gefen Gado Tana Tunanin Makomar Asma"u Matukar Ta Auri Baffa Ba Tsoron kowa Takeji ba Sai Tsoron Shedaniyar Matar Baffa Wasila Bata da Imani ko kadan yadda Bata Kaunar iyayensa Su Rabeshi Ta Tabbata Bazata Bari Wata Mace Ta Rabeshi ba,Duk Da Tana da kawaichi Akan Asma"u Ammh Fa Mganar Gaskiya Ita Mahaifiyarta Ne Ita Ta Haifeta Tafi kowa Sonta Da Sanin Zafinta Bata So yadda Asma"u Ta Dade Batayi Aure ba,ga Kuma Wahalhalun Rayuwa Data Fuskarta Tana Mata Fatan Samun Dacewa Da Gidan Miji Inda Zata Samu Kwanciyar Hankali Wanda Zai Yayemata Kuncin Zaman Gidan Mahaifinta,ammh Duk Da haka Bazata Ja da Hukuncin Allah Kamar yadda Annabin mu ya Sanar Damu Komai Zamuyi Toh Mu Nemi Zabin Allah Toh Itama Zata Gayama Allah batasan Me Allah ya Boye Game da Auren Baffan Da Asma"un.
Da wannan Shawaran Da Watsar Da Mganar Ammah bawai Bata Aranta bane A"a Tadai Kauda Tunanin Hakan ne Aranta Kada Mallam ko Hajiya Su Fahimci Halin Datake Ciki Wanda Ta Tabbata Indai Ta Nuna Bata son Wannan Hadin Koda Mallam da Hajiya Sun Kai Yayane Ason Abun Zasu Hakura ne,Ita Kuma Bazata So Haka Ta Faru Ba Domin Babu Abunda Zatace Mallam Da Hajiya Sai Fatan Sugama Da Duniya Lafiya.
Washegari Sai ga Yusuf ya Diro Bauchi Da yammah,Nan aka Zauna aka Kara Tattaunawa yadda Tafiyarsu Zuwa DUTSE Gobe,Yusuf ne ya Kawo Shawaran Suje da Sadakinsu da Kudin Nagani inaso Hade Da Goro da kwalayen Mintina da Tabarmunsu Wanda Da Zarar An Amince An Basu Auren Asma"u To ba Bata Lokaci Atsaida Ranar bikin Saboda Nisa Da Kuma Karancin Lokaci,Hakika Daga Mallam har Hajiya Sunyi Na"am Da Shawaran Yusuf din Nan da Nan ko Yusuf ya Fita Zuwa kasuwa ya Siyo Komai Da za"a Bukata Bakin Hajiya ko yaki Rufuwa Saboda Murna Ita Dai Maman Fati Yar Kallo ce Don Tace Ita uwar ango ce,Domin Har Kawu Ta Kira awaya Tamai Mganar Abunda Ke Faruwa Shima Shawaran Daya Bata Shine Ta Mika lamarin Ga Allah Insha Allahu Babu Komai,Kuma Alhamdulillah Itama Zuciyarta Ta Natsu Da Abun Addu"a take Dare Rana Kan Allah yasa Wannan Karon Wahalan Asma"un ya kare.
Banda Su Hajiya Da Suka San Mganar ba Wanda Aka Fadamawa Ko Su Anty Nafi ba Wacce Hajiya Ta Kira Ta sanarmawa Ko Yusuf Bai Fadama Zainab ba,da Zai Taho Ta Rika Tambayeshi Mai Zai Zo Yi Bauchi Harda Kwana,kawai sai yace Mata Zasuyi Wata Tafiya Da Mallam ne,Toh Sanin Yusuf da Mallam din Suna Tafiya Tare Shiyasa Bata Damu ba,Annie kadai ya Sanarmawa,Saboda Ita mahaifiya ce Kuma Uwa,tasama Abun albarka Kuma Itama Taji Dadi Takuma yi alqawarin Saka Al"amarin Acikin Addu"a.
******
Washegari Tun Misalin karfe 8:00am na Safe Su Mallam Suka Damki Hanyar Bauchi. Karyawa kadai Sukayi Shima Sama sama,Hajiya Da Maman Fati har Haraban Gidan Suka Rakosu Inda Mamman ya Gama Loda Kaya abayan Booth din Motar Yusuf 607 Kirar piogion,Mamman ya Taso Mallam ya Dakatar Dashi Yusuf Zai yi Driving da kanshi Yayinda Mallam ya Shiga Gidan Gaba Mazaunin Mai Zaman banza Dukkansu Cikin Shiga Ta alfarma Da Kamala Mallam Cikin Shadda Riga da Wando Har Da Babban Riga Kallon Farko Zakamai ka gane ilimi Tare Da Baiwar Zati Sun bayyana gareshi Dattakonsa Kuwa akallon Farko Ake Gane Hakan Atare Dasu.
Har Motar Ta Fice Daga Haraban Gidan Su Hajiya Suna Daga Musu Hannu,Hajiya Bakinta yaki Rufuwa Addu"a take Kwarorowa na Fatan Allah ya kaisu Lafiya ya kuma saka Su Dawo Da lbri Mai Dadi,Maman Fati Dariya Takema Hajiya Aranta Tana Jinjina Girman Kaunar Da Hajiya Kema Asma"u,Wanda Daga ita har Baffan ba Wanda Keda Lbrin Abunda Ke Faruwa.
Ko yau Da Safe Sunyi waya Da Asma"un Hartaji muryanta Tayi Laushi Nan take Tambayanta Ko Lafiya Tace batajin Dadi ne,Aran Mama Fati Taji Wani Iri Tace Kila Asma'un Taji Aranta ne,Bata Fadamata Komai ba,Suka gaisa Kafin Ta tambayi Su Fati Tace Suna Mkranta,Daganan Sukayi Sallama,Shima Baffa Tanaji Suna Waya Da Hajiya Bayan Tafiyarsu Mallam yana Tambayanta yanzu ya Kira Mallam ammh yace mishi Suna bisa hanya Shida Yusuf Zasuyi Wata Yar Tafiya ammh yau Zasu Dawo,Da eh Hajiya Ta amsamai Kafin Ta Share Zencen dayake Shima Baffan Bamai Son Jin Abunda Bai Shafeshi bane Sai ya basar Suka Cigaba da gaisawa kafin Suyi Sallama Su katse Wayar Aran Hajiya Tace"Tafiyarsu Takace Baffa Da Izinin Lahi Asma"u *HASKE CE RAYUWARKA*.."
_Zaku samu Damar Karanta littafin *ZAMAN GIDANMU* Kan 200 kachal,ta wannan Account Nombar kamar Haka 0552179550 Jamila Umar Gtb,bayan An dauki Hoton Trancsation din an Turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Waya na Mtn bayan an Dauki Hoton katin sai a turo kai Tsaye ta wannan Nombar 09069067488,Yan Niger kuma zasu biya 300f...Ina maraba daku Masoyana masu Son Cigabana.._
*Shakira..*💞
*08/04/2020...*✍️
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
_*KUDUBI GIRMAN ALLAH KURIKEMAN AMANA WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,KU KARANTASHI KU BARSHI ANAN,NAYI MUKU ADALCI KADA KU CI AMANATA*_👏
_Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 300kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 500cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels