Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
ko Sun so sai ya Auri Wasila Domin itace Rayuwarsa,Wannan al"amarin daya Faru ya daga Hankalin kowa,gidan ya Hargitse hajiya kwana tayi kuka,Shima Mallam Abun ya tsayamai arai ammh bai taba kawoma kanshi Asiri akama Baffa ba, yafi barinshi a Duniya ce da kuma Rashin kunya irin ta Dan yau. Babban lbarin dayafi Tayarma Iyayen Abdallah da Hankali Shine Zuwan da Yusuf yayi har Gidan Baffa a Porthercourt,Yaje yayi mummunar gani,domin Wasila ta koma gidan Abdallah ta tare,suna zaman iskanci,Da yusuf yaga haka yanemi yama Abdallah mgana,wlh bai Saurareshi ba Daga karshe Wasila tace ya koreshi nan da nan ko ya sa Masu gadi suka yi waje dashi,wannan al"amari ya razana Yusuf har yakai Bauchi yana kuka,haka ya Fadi gaban Su Hajiya yana Fada musu Abunda ya Gudana,wannan lbrin Shine Sanadin da Hajiya ta yanke jiki ta Fadi,Lokacin ne Kuma ta kamu Da hawan Jini. Iyayen Abdallah basu taba tsintan kansu cikin bakincikin ba,sai lbrin da Yusuf yazo dashi na zaman Zina da Abdallah ke gudanarwa da Wasila yasa Mallam ya wanke kafanshi har Bida wajen Mahaifin Wasila ya kuma bukaci yanaso a daurama Abdallah da Wasila aure ,ammh sai ta dawo gida tayi Tsarki istibura"i Domin in ganta aurensu,da Farko yaso yayi gaddama ammh yana gayama Hajiya Kudirat ta Daga tsalle tace maza ya amince nan da nan ko ya amince ya kira yan"uwansa Duka duka ko Mutun goma basu kai ba aka gudanar da Neman Aure inda Mallam yace sai Wasila tayi tsarki kana zai Amince Abdallah ya Aureta saboda yanzu Aurensu ya Haramta,Ahaka suka amince bayan Hajiya Kudirat ta kira Wasila ta sanar da ita Abunda ke Faruwa kuma tabata Umarnin ta tattaro kayanta ta dawo gida. Har Mallam ya koma Bauchi Zuciyarsa Tana cike da bakinciki da kunci Halin Da Abdallah ke ciki tare da Tirr da irin gidan daya dauko Mata,kuma koda wasa bai sanar da kowa Abunda ke Faruwa ba saboda bayason Hankalinsu ya kara tashi Fiye da na da,domin haka su Anty Safina suka tasa hajiya suna ta mata kuka yusuf ne da Maman Fati keda kokarin basu baki tare da Shawartansu Su rika saka Abdallah acikin addu"insu. Duk Abunda ya Faru Wasila take Sanar da Abdallah daganan kuma ya Cigaba da Shiryen Shiryen Biki Batare daya kara bi ta kan iyayen nashi ba,Wasila ko kusan sati suna tare,sun daina Kusantan Juna Saboda tsarkaka Aurensu ammh Shafe Shafe kam basu Daina ba adaddafe Wata uku ya cika,Sai alokacin Mallam ya sanar dasu Hajiya Abunda Ke Faruwa,Ranar Hajiya ta kwana kuka da takaichin Halin da Baffa ke ciki Ranar Daurin Aure kuwa Mallam bai gayyaci kowa ba Dagashi sai Yusuf suka tafi Bida,Agida kuwa yan"uwanshi da Suka zo ,babu wanda suka Fadamawa balle Suyi gayyah ko Taron biki,ko zainab dake Kaduna Yusuf bai barta tazo ba,saboda kada su karama Hajiya damuwa,Ranar banda kuka babu Abunda Suka Dingayi Ranar ma Hajiya a asibiti ta kwana Saboda yadda jikinta ya Rikice Sosai... Awajen Daurin Auren Suka gamu da Abdallah dashi da tawagarsu Murna ta kama Abdallah bakinshi baya Rufuwa yau Burinshi ya Cika ya tabbata Wasila matarshi ce,Saboda bakinciki ma Su Mallam basu Tsaya ba Suka jiyo,shiko Abdallah sai da suka kwana biyu A bida ana Shagali kafin Su baro Bida Shida Wasila ajirgi suka yada zango A parthercourt,Suka cigaba daga inda Suka tsaya,Kafin bikin ma Sai da suka kara komawa gidan Boka suka kara bashi kudi yakara Karkatar da Zuciyar Abdallah garesu ya kuma Tusamai Tsanar iyayensa aranshi,Shiyasa har ya Auri Wasila da Wata goma bai zo Bauchi ba,kuma baya kiran Wayar kowa ko an kirasa ba!a samunshi Domin ko Sunan Bauchi yaji an ambata yanzu Ranshi zai Baci yaji Zuciyarsa na zafi. _Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 200kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 300cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._ *SHAKIRA...*💘 *17/03/2020*...✍ *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai cike da Kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)*  .....""Sai da Suka Shekara Daya Cur da Aure kana Wasila tace yakamata Suzo Bauchi Tunda kuma tace Shikenan mgana ta zauna,Zuwan da sukayi sai da kowa yayi Nadama mussaman Hajiya Don Zuciyarta ta kusa bugawa na ganin yadda Rayuwar Baffa Ta koma Bita zaizai,sai Abunda Wasila tace Shi yakeyi Wani karin Abunda takaichin ma ko gaida iyayen nasa ma Sai da Wasila tace ya gaida su kana Baffa ya Gaida Mallam da Hajiya. Tunda ga Zuwan nan bai kara taka kafarshi Bauchi ba,Su kuma basu Daina addu"a ba,Al"amarin akwai ban Tsoro aciki koda Abun yaso ya lalace Da Zarar Wasila Taji lbrin Baffa yana kiran Bauchi abakinshi Zata kira Hajiya Kudirat su koma Wajen Boka su Zube kudi asake sabon aiki,shikenan kuma sai Abu yakara komawa baya,Wasila ta zama itace Uwarshi da ubanshi sai Abunda tace Shi Baffa keyi,Ta mallakeshi dashi da Dukiyarsa gabadaya daga ita sai Yan"uwanta ke fantamawa da arzikinshi iyayenshi ko ya ma manta dasu kwata kwata mganar ibada ko Wasila duk ta kara Susutar dashi dama itama ba gwana ba,Wani lokacin baya sallah akan Lokaci Addu"a ma Baya samun yi balle har yayi ma kanshi ko wani mtsalan Nashi ya ragu. Saboda Samun waje Har Kannenta Tace su dawo gidan da Zama su Jamila suna tsoma biyar suna Fito da goma,babu Abunda Sukeyi sai dai Su ci su kwanta Suyi chart ko suyi wanka Direba ya Fita dasu yawo,mganar gyaran gida da girki kuma Tun kafin Aurensa da Wasila yana da kuku Josepen,shine ke kula mai da gidan,ko yanzu kuma Da ya Auri Wasilan Babu Abunda ya Chanza Zani. Tun Bayan Aurensu likitoci Suka tabbatarma da Wasila baza tataba haihuwa ba Har abada sakamakon Tun lokacin Datake kan ganiyar Watsewarta Tayi ta amfani da kwayoyin hana Daukan Ciki su sukayi Sanadiyar lalata mata mahaifa Yasa bazata iya Daukan ciki ba,Wasila bata wani damu ba,ta bar Abun Aranta tana ganin sai dai ita da Abdallah su Mutu basu ga Dan kansu ba,ammh Bazata taba bari Abdallah yaji wannan lbrin ba balle har ya kara aure Wata tazo ta Haihu dashi. Rayuwar Wasila ta chanza Fiye da Tunanin mai karatu,takara Fari da kiba da kyau Abdallah ya Siya mata Motar Kirar Vibe2019 sabuwal dal Ga Kudin daya ke Bata tana yarda taga Dama Babu Abunda ya Shafeta,Illah Soyayyar Abdallah Wanda takejin ko Uwar data Haifeshi bata Fita Son Shi ba shiyasa take bala"in kishinsa ko kallon Banza wata mace bata isa tayima Abdallah ba yanzu Wasila zata Fara hauka,shiyasa yake kiyayewa kirarin Da wasila take ma kanta itace kwara daya jallin tal matar Abdallah da ita zai Rayu kuma da ita zai Mutu. Abunda bata sani ba Bayan Auresu Da Wata goma Tafiya ta kama Abdallah Zuwa Lagos wajen Saminar daga wajen aikinsu ada yaso Ya taho da Wasila ammh sai taki,tace mai ya Tafi kawai ashe lokacin tana son taje Bida zasu koma wajen Boka,akan mganar iyayen Abdallah Tana so ayi musu Farraqu har abada atsakaninshi da wannan Shegen mijin Kanwar nashi Yusuf... Wannan Zuwan Shine Sanadiyar Haduwarshi da *POLINA* Wacce ta kasance Ba musulma ba kuma Karuwa ce Sosai wacce tasan Duniya sosai,A Hotel din da Abdallah ya Sauka anan ya kyallah ido yaga polina kawai yaji ta burgeshi Don shi akwai Son mace Doguwa Fara mai jikin Mata,ammh Duk da haka bai mgana ba,Saboda ajinsa,sai itane data hangeshi sanda yake kallonta ta kariso gareshi tana mai kwakwarsa,Da farko tashi yayi ya bata waje,Ya nufi dakin daya sauka ganin haka yasa tatashi ta bishi,yadda taga ya bar mata dakin Abude yasa ta tabbatar da yana Ra"ayinta. Da farko tasha Wahalanshi don yayi mata jinkanshi ammh sai ta nunamai ita yar Duniya ce tayi amfani da barikinta ta hilace Suka kwana aikata masha"a,Abdallah yasha mamakin yadda yaji ya Fita daga hankalinshi akan polina Duk da Tun dayake bayan Wasila bai taba kusanta Wata mace ma,ammh yaji polina tasha bambam da Wasila nesa ba kusa,ta tafiyar dashi yadda ya kamata,ga Ta da Ni"ima Sosai sai gashi Wasa wasa Shakuwa ta Shiga tsakaninsu Suna tare har yayi kwana hudun da zaiyi yayi Shirin komawa nan Fa hankalin Polina yatashi Domin ita ta kamu da Son Abdallah gaye ga kyau ga kudi ga iya Sarrafa mace,dakyar ya lallasheta akan zai dawo ya bata kudi masu yawa bayan sun karbi Nombar wayar Juna... Baisan Wasila Lami ce ba sai da ya Dawo Suka Kunsanci Juna,Daganan ya tabbatar da bambamci mai yawa tsakaninta da Polina,ai A daddafe yayi Sati biyu ya koma lagos aboye yayi kwana biyu daya tashi dawowa sai ya Dawo Tare da polina Farko guess hause Dinshi yafara ijeta sai daga baya ya Siya mata gida a Elelewo,ta koma chan bayan ya Siya mata mota yana kuma Dauke da Nauyinta,Duk sanda ya Fita da niyyar Zuwa wajen aiki sai ya biya gidan polina sun Sheke ayarsu da ita kafin ya Wuce ya Riga ya saba da dadinta bazai iya Rabuwa da ita,ammh fa yana takatsan takatsan kada Watarana Wasila ta ritsashi Shiyasa aduka Nombobin polina ya sanyamata pol1 pol2 Saboda Gudun Wata rana,kuma akwai amana Tsakaninshi da Emeka Direbanshi Duk Abunda ya gani Nuna yake Baiga Komai ba,balle ma Kowa Haushin Wasila yakeyi Saboda tana Abunda ko yallabai baya yinshi.. Farida tazo Haihuwa aka samu mtsala Jini ya yanke mata Ta haihu Yaron data Haifa bai Fito da Rai ba,ko awa daya ba"ayi ba itama Farida Tace ga garinku nan,Mutuwar Data girgiza Mijinta da iyayenta da yan"uwanta Lokacin da Mallam ya kira yusuf yana gayamai lbrin Rasuwar Farida daya samu yanzu abakin Mijinta Baffa ya fara kira ya sanar mawa,,Kuma ya tabbatarmai da gobe zai Hau Jirgi yazo ammh sai me,har Farida tayi bakwai da Rasuwa ba Baffa ba dalilinshi da Yusuf ya kara kiranshi Wasila ce Ta dauka ta zageshi tas tace Kuma Abdallah su dashi har Abada wannan kalaman nata ya bashi Tsoro har ya sanar ma Hajiya ita kuma jin haka ga Rasuwar Farida sai jininta ya hau har ta kara komawa Asibiti nan ma Yusuf bai Dandara ba ya kara kiran Abdallah yana Sanar mai yazo yaga Hajiya hakikanin gaskiya Lokacin Abun yafara sakinshi yaso yazo Bauchi ammh sai Wasila ta ki bada damar haka Ta kira Momcy tace ta koma wajen Boka,koda taje wannan karon ya mata gargadi na karshen kan Duk Abunda zasuyi Toh Su Tsaya kan Abdallah Sudaina kokarin Son Taba iyayenshi Da kuma rabasu ,Abdallah dai zata sameshi ammh har abada iyayensa da yan"uwanshi suna tsaye kanshi kuma bazai taba Rabuwa dasu ba Har abada ko an Rabasu na dan lokaci ne Abun zai sakeshi karshe Reshe ya juye da Mujiya,jin haka yasa Suka Dakata da sun yunkuri yi musu Farraku na har Abada suka koma bangaren Maida Abdallah tamkar bawansu kuma Sun samu,domin Tunda ga Ranar Abdallah bai kara mganar Zuwa bauchi ba balle Ya Tuna da Wata Hajiya.. Mallam ya Umarci kowa da ya Daina damuwa akoma ga Allah,shiyasa Duka yan"uwanshi kowacce ta daina barcin Dare,suka dage da ma dan"uwansu, addu"a kan Allah ya kwatoshi,hakama Yusuf bai zauna ba,Shima yanayi kuma yana sakawa ana ma Abdallah saukan Qur"ani,shiyasa lamarin yafara lalacewa gashi yana son yaje ammh kuma Abun yana so yafi karfinshi,Kuma ya rasa ya zaiyi baida Tunanin yayi addu"a sam da kila Abun yazo mai da Sauki. Tun Bayan Haka sai Yusuf ya daukema Dukkan Su Hajiya Wani Nauyi inda zai zo wajensu zai zo da kayan abinci Niki Niki,kuma in Zai tafi ya basu Kudi Tun suna kin karba yana matsa musu har suka koma Suna karba tare da sakamai albarka,Ko bakomai yana Goge Wani kewar Baffan agaresu. Wannan kenan.. ----------------------------- _DUTSE_ …………"Yau din takama Weekend ne,Lahadin karshen Mako kenan,Yau Tunda gari ya waye Asma"u bata Fito ba sakamakon tatashi bata jin Dadi bakonta ne yazo,kuma indai zaizo mata sai tayi Ciwon mara,Dayake tana da mganinta na Rage Radadin Ciwon sai ta balla tasha Ta koma ta Kwanta bayan ta gyara jikinta. Bata tashi ba sai Wajen 10 na Dafe Hayaniya take Jiyowa daga Tsakar gidansu tana jin Muryoyinsu Su Umma da Anty Amarya Harda Hajiya,Zaune tayi Gefen gado tana Kallon kafafunta da suka dan haye Dama haka Suke mata da zarar Tana Period jikinta kumbura yake,Wayarta kirar Tecno spark 4 ta jawo nan ta Cikaro da 2missed clls din *MAMAN FATI* Mirmishi ya Subuce mata da Hanzari ta bi bayan kiran. Da Sallama Maman Fati ta Dauka cikin Fara"a Asma"u ke Gaisheta Cike da ladabi sai bayan Sun gama gaisawa ne Maman Fati ke Fadin"Ina kika Shiga ne,Na kira wayarki baki daga ba.."?Asma"u tace"Wlh banji dadi ne sai nasha mgani na kwanta tashi na kenan naga kiranki Shine na kira,yasu Hajiya..? Ina su Fati..? Ina Tsohon Megidan nan nawa.."?Maman Fati tace"Kowa lafiya Ma"u,Hajiya ce dai jiki yaki Dadi dama in ce ne in kin samu lokaci in kuma Baban naki ya bari kizo ki Dubata.." Cike da jimami Asma"u tace"Subhannallah..Meya sameta...? Cikin Rashin jin Dadi Maman Fati tace"Wlh Hawan jininta ne ke tashi,ta riga ta Sanya Baffa acikin Ranta Shike Wahalar da ita.."Cikin Tsausayawa Asma"u tace"Ashha Allah ya bata lafiya,Toh wai Shi har yanzu bai Dawo gida ba..?Maman Fati ce"Wlh kuwa Har Rasuwar Farida bai zo ba,duk ciwon da Hajiya takeyi bai Tako kafarsa ba kuma,bai yi aike ba.." Jikin Asma"u yakara yin sanyi Cikin Wani yanayi tace"Allah ya bata lafiya,shi kuma Allah ya Dawo dashi Wajen iyayensa lafiya.."Da Ameen ta amsa kafin su cigaba da mgana,Nan Asma"u tace Zuwa Sati mai Zuwa in ta Nemi Excuse a Wajen aiki,Zata zo In Abba ya barta da haka Sukayi sallama,. Bayan Asma"u ta yanke Kiran Tayi Zuru bayan ta zabga Tagumi taji Tsausayin Hajiya ya kamata,Matar nan tana da kirki sosai kai kaf iyalanta ma Suna da kirki Duka ya"yanta Mutum daya ne bata taba gani ba Baffa,wanda takejin lbrinshi na Matarshi ta mallakeshi Shine damuwar Mahaifiyarsa,Allah sarki mata mai kirki da kawaici Daga ita har Mallam din wanda Sau Biyu tataba zuwa Bauchi ammh yadda suke mata ko yar gida sai haka in ko zata tafi harta su Anty Safina basa barinta haka,Dawainiya sai ta kasa godiya,tana Tsintar kanta cikin Farincikin in taje Bauchi ammh ta lura kamar Abba bayason Zuwanta,uwa uba kuma Wajen aikinta in an bata dama bai Wuce kwana uku ba... Ajiyar Zuciya ta Sauke aranta tana Fadin zata cigaba da Taya Hajiya Addu"an Allah ya karkatomata da Hankalin Danta gareta,ammh wannan ai Zalunci ne Ka raba Mutun da uwar data kawoshi Duniya in da bata Haifeshi ba taya zaga ganshi har ka Aureshi da wannan Tunanin Asma"u ta Dauki lokaci mai Tsawo adaki tana sake sake,bata Fito ba sai dataji Ihun yan gidan ya karu ana Zencen Fa"iza Ta haihu jin haka yasa ta Fito daga daki da Sauri Tana Fadin"Masha Allah Fa"iza an sauka me aka samu ne Ummah...? Umma ne da Anty Amarya atsakar gidan Sai Hajiya Iya wacce ke zaune kan Wata Farar kujera akofar dakinta tana Shan Fura,daga ita har Ummi kallon banza suka Watsa mata,sai Asma"u taji ta muzanta idonta ya cika da kwallah tana Shirin Juya ne Anty Amarya tace"Aiko dai Fa"iza an sauka Ta samu mace,Su ma"u girma ya sake kamaku fa.." Tafada cikin Zolaya da Dariya,jin haka yasa Asma!u ta dawo da baya Tana Fadin"Allah ya raya..Masha Allah girma ya kamamu,gobe in natashi daga wajen aiki zan biya na Dubata insha Allahu.."wani Dogon Tsaki Hajiya iya taja kafin tace"Kai Tirr Wlh da Halinki Asma"u Yanzu ke ko Kunya bakiji ba,ki Fito kina washe baki kanwarki Ta haihuwa,haihuwan ma bana Farko ba bana Biyu ba ta uku..? Ammh ke kina Zaune agida kina gasan juya Duwaiwuka da matan Ubanki Shine Burinki Wlh anyi asara kuma bana ganin laifinki laifin Ladan nafi gani da ya barki kin gansamemai agida..".. Tafada tana jifan Asma"u da Wani banzan kallo... Asma"u da kalaman Hajiya iya Suka saka Kafafunta suka Fara rawa,Idanuwanta Sun cika da Ruwa,Anty Amarya zatayi mgana kenan Umma ta karbe da cewa"Nima Shi na gani Iya,kuma Abun ban Haushi bafa ba samarin Bane..,A"a an tsaya zabin mai kudi,koda yake an ce Mijin kawarta Aisha take so.."Da Sauri Hajiya iya tace"Wata Aishan...? Tafada cike da mamaki. Tabe baki Umma tayi kafin tace"Aminiyarta Aisha ta gidan Wada mana..."Ai sai Hajiya Iya ta kama baki kawai Tana kallon Asma"u cike Da mamaki itako Asma"u ba mamakin Furucin mganar bane ya sata kama baki Hawaye na Fitowa Daga idanuwanta ba,Yadda Ummah ta takarkare tana Fada ne Abun yabata mamaki kenan batayi karya ba dama daga bakinta mganar ya Fito,wani tukukin bakinciki ne ya Taso mata tama kasa mgana. Anty Amarya ce tace"Haba Umma kinbani mamaki ta yarda zaki yarda da wannan mganar inace Asma"u agabanki tatashi,Abunda zata aikata da Wanda bazata aikata ba zaki Fi kowa saninshi Wlh in nayi Rantsuwa na Tabbata bazan yi kaffara ba Asma"u bazata Taba cin amanar kowa ba balle Aisha yadda Suke da Juna tamkar yan"uwa.." Tsaki Umma taja kafin tace"In santa ni na Haifeta kajimin Halima da Wata mgana,Ai Tunda taga yana da maiko tasoshi nan fa akace ansha ganinsu tare ya daukota amotarshi,Kinga ko ai kam anfadi ba Nauyi."Asma"u da Abun ya Fara isarta ta kalli Umma tana Fadin"Haba Umma,yanzu da bakinki kike Fadar wannan mganar..? Ni yanzu na rasa wanda zance zan Aura sai Mijin Aishata wacce Nakejinta kamar wacce muka Fito ciki daya,Toh har abada babu aure tsakanina da Fahad ko da Aisha bata da rai,Kuna zargi ne kuma baku da tabbas akan hakan,kuma mganar Fa"iza ta haihu har na uku kuma ni ina zaune,Hajiya iya ai Aure da Haihuwa nake ga Duk na Allah ne,Allah da yabama Fa"iza miji tayi aure kuma yabata haihuwa nima yana Sane dani kuma bai manta dani ba,Kuma gareshi na ke kai kukana,Kuma da yardan Allah zai kuma Sharemin Hawayena na bar muku gidanku mai Cike da kunci.." Tafada cikin kuka kafin ta Ruga ta Shige Daki Umma da Hajiya iya keta tafa hannu suna Fadin"Lalle Asma"u Wuyanki ya isa yanka,yanzu mu kike Fadamana wannan mganar,.."Itako Anty Amarya Ranta bai mata Dadi ba ta girgiza kai acikin Ranta tana Fatan Allah ya Dubi Asma"u ya kawo mata miji tayi Aurenta ta bar Wannan gidan da babu komai cikinshi sai burin kunsa mata bakinciki da kunci. Itako Tana Shiga Dakinta ta Fada bisa katifarta tana gunjin kuka,Abunda yafi bata mata rai yadda ake mata kallon Maciya Amana wai zata auri Fahad mijin Aishanta,wacce Suka taso Tare Suna yara,tasan Aisha kamar yadda Aisha ta santa,Harda mata gorin Haihuwa,na aure Bai dameta ba inda sabo ya kamata ta saba da kalaman Hajiya iya da Umma gareta na Gayamata Taki aure ta Tsaya jiran Mai kudi,Kuka take kamar Ranta zai Fita ciikin kukan ne Take Fadin"Allah ka kawomin miji koda ma Wani iri ne,kai koda Dan Fashi ne... Da Sauri Wata Zuciyata ta kwabeta da Fadin"Haba Asma"u Dan Fashi kikema kanki Fata..? cikin kuka tace"Eh koda Shine indai zai yi nesa dani daga *ZAMAN GIDANMU* mai Cike da kunci ina so.."Take Afada abayyane tana kara Sautin kukanta Cikin Wannan yanayin Ta Zurama Waje daya ido kafin Tunanin Mafarin Wacece Ita ya Fara Dawomata Daki Daki kamar yanzu komai ke Faruwa abidiyon Majigin Bidiyo. _Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 200kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 300cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._ *ANITHA...💘* *19/03/2020*...✍ *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai cike da Kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)*  ......" *Alhaji Ladan Sharif Mai Auduga* Shine asalin sunan mahaifin Asma'u wanda haifaffen garin babban birnin jihar Jigawa ne, wato Dutse, ya samo asalin laƙabin Mai Auduga ne sakamakon tun yana matashi yake manominta, ya gada ne shima a wajen mahaifinshi, dan da ita aka sanshi har kawo yanzu, domin itace rufin asirinshi, Alhaji Ladan baiyi karatun boko ba sai na addini, sai daga baya ne kana suka shiga makarantar yaƙi da jahici. Mahaifinshi ya rasu sai mahaifiyarshi mai suna Hauwa'u wacce ake kira da Hajiya Iya, ya'yansu goma cur na da suka haifa kuma babu wanda ya koma duka suna nan da rayuwarsu, kai tsaye bazaka kirashi da mai kuɗi ba, amma za'a iya sakashi cikin sahun masu kuɗin dake zaune a unguwar Gida Sittin dake Dutse, matarsa ta farko mai suna Mandiya wacce ake kira Ummah auren zumunci akai musu, Mandiya irin matan nan ne masifaffu, ga son abun duniya ga ƙyashi, ba laifi itama mahaifinta ya mutu ya bar musu tarin dukiya, shiyasa Hajiya ta matsa kan sai mahaifinta ya aurota domin Hajiya Iya itama akwai son harka da masu dashi. Shekaransu biyar da aure har tayi haihuwa biyu 'yarta ta farko itace Aunty Ruƙayyah, sai mai bi mata Aunty Bilki, tun a lokacin yaso ƙaro aure, saboda yana ƙaunar Allah ya bashi ɗa namiji domin shine duka burinsa, sai Hajiya Iya ta hanashi, badan yaso ba ya bar maganar, kuma tun daga kan Aunty Bilki sai haihuwa ta tsayama Ummah cak bawai don ta gama ba sai don haka Allah ya tsara mata. Zuwanshi Bauchi wajen harkan sana'rsu ta Auduga achan ya haɗu da mahaifiyar Asma'u wato Habiba, kuma tunda ya ganta ALLAH ya ɗora mai sonta baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nemi gidansu kuma ya gana da mariƙinta wato wan mahaifinta, domin lokacin Allah yayi ma mahaifinta rasuwa ba tare da jin ta bakin Habiba ba aka bada aurenta ga Alhaji Ladan, duk da ko da taji ba taji daɗi ba, amma bata nuna ba sai ta sadda kai tayi biyayyah ga iyayenta aka sanya ranar aure akayi biki aka ɗauketa daga Bauchi zuwa Dutse. Lokacin da Alhaji Ladan yajema Hajiya Iya da maganar Habiba bataso ba, amma ganin shi ya dage ne yasa ta amince, amma bayan taja kunnansa kada ya sake ya wulaƙanta Mandiya wato Ummah, ya kuma mata alƙawarin hakan ba zata taɓa faruwa ba, tunda Ummah taji za'a auro Habiba shikenan hankalinta ya tashi ta fito da kishinta muraranta, har aka kawo Habiba gidan nan Ummah na cikin masifa da Alhaji Ladan, kawai baya biye mata ne, saboda yadda ta samu ɗaurin gindi a wajen Hajiya Iya. Da farko zamansu ya fara daɗi saboda Habiba mace ce mai tsananin hakuri da kawaici, koda Ummah tayi mata wani abu bata tankata, kuma tunda ta lura Hajiya Iya na nuna bambamci tsakaninta da Ummah tafi sonta akan ta, bata damu ba ta watsar da komai ta rumgumi mijinta hannu bibbiyu, watan Habiba biyu da zuwa gidan ciki ya ɓulla a jikinta, murna wajen Alhaji Ladan ba'a magana yana ta addu'ar Allah yasa wannan karon ya samu namiji, tunda Ummah taji haka shikenan hankalinta yaƙi kwanciya ta dinga shiga tana fita domin tayi alwashin bazata taɓa bari Habiba tazo daga baya ta haifi ɗa namji a gidan ba.

Chapter 4 of 11