Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
Ko ita kanta Hajiya Iya bata ƙaunar taga Habiba ta haifama Ladan ɗa namiji a gidan, ita ko Habiba ba tasan wainar da suke toyawa ba, illah ta maida kanta ga kula da kanta da abunda ke cikinta, da kuma kai kukanta ga Allah, don ita mace ce mai yawan ibada, haka dai har cikinta ya kai wata tara, rana tsaka ta tashi da naƙuda Alhaji Ladan ya kwasheta shi da su Hajiya Iya zuwa wani private Hospital inda aka shigar da ita labour room. Ko awa ɗaya ba'ayi ba sai ga wata nurse ta fito da dariyarta tana faɗin Habiba ta sauka, cike da tsantsar farin ciki Alhaji Ladan ke faɗin Masha Allah, Hajiya Iya ko da Ummah haɗa baki sukayi wajen tambayar me Habiban ta haifa cikin fara'a nurse ɗin ke sanar dasu ta samu ɗiya mace, washe baki sukayi suna hamdala a tare, shiko Alhaji Ladan yaji mamakin abunda sukayi amma sai bai kawo komai a ransa ba, duk da bai samu abunda yakeso ba, bai nuna damuwarsa ba,.sai washegari aka sallami Habiba suka dawo gida aka shiga kiran dangi ana sanar dasu labarin haihuwar.... Ranar bakwai na zagayowa akayi suna inda yarinya taci sunan *Asma'ul Husna..* Alhaji Ladan yayi bajinta sosai a haihuwar Asma'u wanda baima Hajiya Iya daɗi ba sam, haka dai suka ɓoye abunda ke ransu basu nuna ba, amma tsanar da sukema Habiba sun kasa boyeta, haka dai take zaune dasu tana haƙuri tunda mijinta bai chanza mata ba, tana cigaba da rainon 'yarta Asma'u. Asma'u nada shekara biyu da haihuwa, Ummah ta sake haihuwa kuma itama mace ta haifa, aka sa mata suna *Fa'iza* bayan Fa'iza ta ƙarayin *Rabi'atu* lokacin Asma'u nada wajen shekara bakwai kenan a duniya, har an sakata a makaranta inda su Aunty Bilki ke zuwa wato *Dutse Capital School*, lokacin ne kuma Hajiya Iya ta matsama Alhaji Ladan akan tana so ya ƙara aure bai so ba gaskiya domin shi bashi da ra'ayin auren mata fiye da biyu, amma Hajiya Iya taga yana mata wasa da kanta ta nemo mai auren Mama wato Salamatu kenan itama 'yar Dutse ce, Mama mace ce mai halin ko in kula bata shiga abunda babu ruwanta, kuma mace ce da bata bayyana abunda ke cikin zuciyarta akan fuskarta, baka isa ka gane ina ta dosa ba. Da yake ita bamai shiga harkan kowa bane, shiyasa Ummah bata mata abunda takema Habiba, itama watanta tara ta haifo 'yarta mace wacce taci sunan *Kursum* bayan kursum tayi *Fati* bayan Fati tayi *Maryam* itace ta ƙarshe da yake haihuwan nata kusa kusa takeyi, itama dai bata haifi ɗa namijin ba, shiyasa Ummah abun yayi mata daɗi sosai domin bata ƙaunar ita bata haifi namiji ba wata tazo daga baya tace zata haifa. A lokacin zama yaƙi daɗi tsakanin Habiba da Ummah wacce ta kasa haƙuri har ta fara tanka mata, ganin haka yasa Ummah ta fara fitowa da makirci kala-kala tana haɗama Habiba a wajen Hajiya Iya da Alhaji Ladan na wai tana ware Asma'u dasu Fa'iza bata barinta tana shiga cikin ƴan'uwanta, abunda ya sa saida Alhaji Ladan ya tanka bayan ya tsawata ma Habiba, bayan wannan anyi wasu abubuwa da dama waɗanda suka wuce misali, har ranar dai akayi na ƙarshe wanda yayi sanadiyar rabuwar auren Habiba gaba ɗaya wanda Ummah ta mareta akan ta bangajeta bata sani ba, shine kawai ta daga hannu ta kifa mata mari, ganin haka yasa itama Habiba ta daga nata hannun ta sharara mata mari, kawai sai Ummah ta zube ƙasa tana kwarara uban ihun Habiba ta daketa, koda Hajiya Iya da Mama suka fito nan suka iske Ummah kwance Habiba na gabanta tana kallon ikon Allah. Wannan dalilin yasa Hajiya Iya ta zabgama Habiba mari kuma ta saka Alhaji Ladan bayan ya dawo ya saki Habiba hukuncin da har abada yake nadamar aikatashi ranshi bai so ba, don yana son matarshi, amma haka ya rubuta mata saki ɗaya ya bata, Habiba tayi kuka amma ta barma Allah komai, tun a daren ta kira Bauchi ta sanar dasu su kuma washegari tun safe sai ga matar kawu Inna Jummai sun iso Dutse da katuwar motarsu ta kwashe kaya, aka kwashe kayanta tsaf, lokacin da Habiba taga tabbas tafiya zatayi sai hankalinta ya tashi na yarda zata bar rayuwar Asma'u a hannun muguwar kishiya, Mama kuma bata shiga shirginta saboda ita halinta kenan baka gane wani hali take ciki da kai. Hajiya Iya da kanta ta amshi Asma'u ahannun Habiba wacce ke kuka itama Asma'u na kuka wacce lokacin Asma'u nada shekaru 12 a duniya tana da wayau sisai lokacin tasan zafin rabuwa da uwa, tana ji tana gani aka kwashe kayan mamanta tas, kuma suka shiga mota suka koma Bauchi, ranar wuni tayi kuka haka Hajiya Iya ta sa bulala ta zaneta tas, wai karta damu mutane da kukan banza, ko Alhaji Ladan daya dawo yaga an kwashe kayan Habiba abun bai mai daɗi ba amma bashi da yanda zaiyi, dole ya ɗau haƙuri. Tun daga lokacin rayuwar Asma'u ta shiga garari da ƙunci, domin kamar yadda Ummah ta tsani Habiba haka ta maida akalar tsanarta akan Asma'u wacce take ganin bambamci ƙiri ƙiri ana nuna mata da ya'yan Ummah, kamar ba gidansu ɗaya ba, Mama kuwa bata da wata matsala da ita, sai dai bata shiga shirginta kuma bata hanata ta shigo ɗakinta har kwana tanayi a wajenta suyi wasa ita da ƙannenta amma kuma bata isa don tayi ma ya'yanta wani abu ta haɗa da ita ba, ina babu ruwan kowa da ita sai dai idan Alhaji Ladan ne ya dawo wajenshi kaɗai take samun salama, Hajiya Iya ko ɗakinta ta shiga yanzu zata koreta tana zaginta ita da uwarta. Tun daga lokacin Asma'u ta fara janye jikinta, lokacin ne kuma Allah ya haɗata da *AISHA WADA* wadda suka taso daga Jigawa suka dawo Dutse mahaifinta ma'aikacin Civil Defences ne, sai kuma akayi sa'a aka sanya Aisha a makarantarsu Asma'u kuma aji ɗaya, tunda ga lokacin shikenan shaƙuwa da ƙawance suka ƙullu tsakanin Aisha da Asma'u wanda ɗaya bai taɓa iya wuni in bai ga ɗaya ba, dalilin haka ne ma Aisha ta matsa sai da aka sata a makarantar Islamiyan su Asma'u, saboda su riƙa zuwa tare, suna dawowa tare. Mahaifiyar Aisha wacce suke kira da Ammi har gidansu Asma'u ta shiga suka gaisa dasu Hajiya Iya saboda dalilin ƙawancen Aisha da Asma'un, amma tunda su Ummah sukaji ance Asma'u kowacce ta shiga taɓe baki haka Ammi ta dawo gida jikinta a sanyaye, sai a lokacin take tambayar Asma'u ina mamanta take? tace bata nan ta kwashe kayanta ta koma Bauchi tsausayinta ya kama Ammi sosai, tun daga nan tayi alƙawarin kula da Asma'u inda ta haɗasu ita da Aisha tana kula dasu komai zata siya biyu take siya, hakama mahaifin Aisha shima komai zai ma Aisha bata karɓa sai an siyama Asma'u, dalilin hakama har zumunci ya ƙullu tsakanin Alhaji Wada da Alhaji Ladan. Tun da Ummah ta ƙyalla ido taga rayuwar Asma'u ta fara in ganta tana samun kula da gata wani lokacin ma ba a gidan take kwana ba, wani ƙarin baƙin ciki ma Asma'u role model ce, domin Allah ya bata kwanya sosai na ƙoƙari ko lokacin da ta gama primary sch ɗinta haka ta amshi kyaututtuka ba adadi, wanda ko su Aunty Bilki dake gabanta basu karɓa ba, ita da Aisha su sukayi ta karɓan kowani kyauta abun sai wanda ya gani, haƙiƙa abun yayiwa Abbana daɗi kuma tun daga lokacin yayi alƙawarin zai iya kashe min ko nawane don inyi karatu, in karanci fannin lafiya. Tun bayan tafiyar Mamana bata ƙara zuwa ba, sai dai ta kanyo min saƙo ta hannu Ammi in ta samu mai zuwa ko ta turo direba dashi, wannan ƙoƙarin nawa shike ƙara wutar tsanata a zuciyar 'yan gidanmu duk cikin ya'yan Ummah mutum daya ce muke shiri da ita Fa'iza domin ita yarinyace mai fara'a da son yan'uwa kuma gata sakona amma kuma muna jituwa sosai, su Maryam ko sama sama suma basu cika zhiga harkata ba, nima sai nake baya baya dasu, in ka ganni ina dariya nida rabin raina ne Aisha wacce ta zama tamkar yar'uwa ta jini agareni. Anan Dutse Capital School ɗin muka ɗora Jss1 ɗinmu nida Aisha hakama sauran 'yan gidanmu don nan mukeyi gaba dayanmu, muna Jss3 Abbanmu ya ƙara aure ya auro Halima wato Aunty Amarya wacce ta zama tamkar uwata agidan, don Aunty Amarya macece mai kirki da kawaici, tunda tazo gidan nan ta kamani ta riƙe hannu bibbiyu bata taɓa ƙyamata ko nuna min bambamci ba, shiyasa nima nake bata girmanta, kuma hatta da Abbanmu yana jin daɗin haka domin duk abunda ke faruwa yana sane bashi da yanda zaiyi ne kawai saboda Ummah ta samu ɗaurin gindin Hajiya Iya. Haihuwar farko da Aunty Amarya tayi ta haifi namji murna wajen Abbanmu ba'a magana Ummah ko kamar tayi hauka saboda baƙin ciki, amma bata da yarda zatayi domin Allah ke badawa ba mutum ba, ranar suna yaci sunan Kakanmu Lukman suna kiranshi da Walid, hakama haihuwarta na biyu ta ƙara samun ɗa namiji wanda yaci sunan mahaifin Aunty Amarya Shehu suna kiranshi da Abba. Muna SS1 bikin su Aunty Bilki da Aunty Ruƙayyah ya taso wanda za'a haɗa rana ɗaya, wai feleƙe wajen Ummah ba'a magana ita mai ya'ya zasu yi aure ko ankon bikin ma Ammi ta mana nida Aisha, Abba kuma ya bamu kuɗi muka ƙara da kala ɗaya, nima na fito nayi sharr, duk da ba haka Ummah taso ba, akayi biki lafiya amare suka tare agidajensu duka anan cikin garin Dutse. Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'aje ba duk wani ƙunci na gidamu da nake fuskanta yanzu ya ragu ganin na girma na zama budurwa, duk wani kyau da cika da ake nema a wajen mace na gama mallakanshi ko mutanen uguwa na faɗa, duk gidanmu ba mai kyawuna, tun muna SS2 samari suka fara mana chaa nida Aisha duk inda mukaje muka dawo sai an biyoni musamman ma ni Asma'u haka Allah yayi ni da farin jinin samari, a kuma lokacin ne akayi mana walimar sauka nida Aisha a makarantar haddarmu, wannan saukan ta izama Ummah ƙara tsanata tana ganin a komai sai na fi ya'yanta da taji labarin Fa'iza taje sai da ta kamata tama ta dukan tsiya, a gidanmu Abbana ne kaɗai yaje sai Aunty Amarya ko Mama bata samu zuwa ba hakama su Maryam wai sun tafi gidan kakanninsu, kuma suna sane da ranar walimar. Abunda yafi min daɗi shine zuwan Mamata walimar saukata wanda shine haɗuwata da ita ta farko tun bayan barinta gidanmu, a gidansu Aisha ta sauka nayi murna sosai da zuwanta haka muka rumgume juna muna murnar ganin juna mamata tana mamakin girmana da wayau na, ta kawo min kaya da abubuwa sosai harda kuɗi, tamana ɗinkuna nida rabin raina Aisha, sai awajen walima suka haɗu da Abba kuma sun gaisa cikin mutumci, anyi walima lafiya an watse bayan mun karɓi tarin kyauttuka. Washegari mamata ta koma Bauchi bayan ta sanar damu cewa ta kusa aure, nan muka buga ihu nida Aisha mukace wlh sai munje Bauchi, tana Dariya tace in lokacin yayi zata kira Ammi ta waya ta sanar da ita. Duk tarin samarin dani keyi basa gabana, burina kawai shine nayi karatu, Aisha ce ma ke man faɗa ya kamata na fara kulasu don mun kusa yin Candy kuma gidanmu nasan Abba baya barin wata ta cigaban mai da karatu agida sai agidan mijinta toh da wannan shawarar nata na fara kula wani Najib anan ƙasan layinmu yake ma'aikaci ne a Mtn office, mun fara soyayyah dashi ina sonshi yana sona, har magana takai wajen Babansu Aisha shi kuma yama Abbana magana nan suka samu Najib suka mai maganar ya turo iyayenshi ayi magana, da na gama zana jarabawar fita ayi aurenmu, Najib ya amsa cikin murna amma sai me? Tunda ga lokacin Najib ya ɗauke ƙafa daga gidanmu ya daina kirana a wayar daya diyamin, tun ban damu ba har na damu na sanar da Aisha, muka kirasa a waya yana ɗauka sai tambayata yayi wacece..? Tunda mukaji haka sai jikin mu yayi sanyi sosai da al'amarin, tun muna ɓoyewa har muka sanar da Ammi itama taji ba daɗi amma sai ta bani haƙuri ta lallasheni ta kwantar min da hankali. Shikenan ƙarshen rabuwa na da Najib, lokacin bikin Mamata ya ƙarato ta kira waya ta sanar da Ammi ita kuma ta shirya mana tafiya bayan Babansu Aisha ya tambayarmun izini a wajen Abbana kuma ya barni, cike da farin ciki muka ɗaga Bauchi ni da Aisha da Ammi, mamata da danginta sunyi murna sosai da ganina, sai da mukayi kwana huɗu kana muka dawo saboda makaranta, Mamata tayi aure a gidan manyan mutane kai da gani basai an faɗa maka ba, ta auri wani Proffessor Abdallah Mahamud Azare wanda ke aiki a jami'ar ATBU BAUCHI, kowa sai taya Mamata murna yake domin ta dace da samun gwarzo miji wanda kowa ke yabonsa yana da mata ɗaya da ya'ya biyar mata huɗu namji ɗaya shine babba kuma da yake duka sun girma babu yara a cikinsu. Ko a Bauchi da muka dawo sai da wani ya biyo ni mai suna Sagir, da farko banso na kulashi ba Aisha ce ta matsamin har na fara sauraran Sagir, shima dai kamar dai na Najib ɗin sanda aka mai maganar turo mgabatanshi shikenan alaƙarmu ta yanke, wannan karon abun ya dakeni don na shaƙu da Sagir fiye da Najib, amma rana tsaka ya barni ga magana ta gama yaɗa dangi har Bauchi mamata tana ta murnan zanyi aure akusa da ita. Rabuwata da Sagir tasa sai da na kwanta ciwo Aisha da Ammi suka shiga damuwa sosai gashi muna gabda fara zana jarabawar fita ne, ganin na sa tunani araina ga kuma jarabawar dake gabana yasa na watsar da komai muka kama karatu nida Aisha inda muka zana jarabawarmu cikin aminci da nasara, ranar da mukayi Candy aranar Aisha ta haɗu da Fahad ni kuma Allah ya haɗani da wani Sulaiman ɗan Sanda ne. Wannan ma karon na tuɓure nace bazan ƙara kula wani namiji ba, amma Aisha da Fahad suka riƙa tausata har na sassauto na fara kula Sulaiman, shi magana har tayi nisa domin ana tunanin rana ɗaya za'a mana aure da Aisha amma sai me, har danginshi sun kawo kuɗin nagani ina so, shima su Fahad sun kawo, sai kuma magana ta taɓarɓare, domin kwata-kwata Sulaiman ya ɗauke ƙafa ko na kirashi awaya baya ɗauka da manya suka kira waliyanshi sai suka ce ai yaro yace ya bar wannan maganar... Labarin da ya sameni nayi kuka kamar zan zauce, tun daga lokacin sai dangin mamata suka fara zargin ko Ummah tamin wani abu ne duba da irin yarda bata ƙaunata muraran ta nuna, amma sai ban ɗauki abun da serious ba, na barma Allah komai, nan ko Ammi ta dage da nemamin taimako domin kariya, kuma duk abunda ke faruwa Ummah nada labari in muka haɗu ta dinga tintsira min dariya kenan, tun daga nan nasha jinin jikina da ita amma ban taɓa faɗama kowa ba na bar abun a cikin zuciyata. An saka ranar auren Aisha da Fahad wanda ta dinga kuka tana faɗin ita ba zatayi aure ba sai tare dani, shikanshi Fahad ɗin yasan ƙaunarmu daga Allah take, ni ce abun na Aisha ya bani dariya yaushe ake haka ni Fahad ya kawoma ƙararta nako mata faɗa sosai sai dai kawai ta rungumeni tana kuka, duka duka wata goma aka sanya bikin Fahad da Aisha tun kuma daga lokacin muka fara shiryen shiryen biki. _Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 300kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 500cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._ *Shakira..* *20/03/2020....*✍ *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai cike da Kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)* _Alhamdullillah ya Allah..Ina godiya ga Ni"imarka gareni...Akullum Bakina bazai Daina Mika godiyata ga ALLAH (SWA) da kuma Masoyana na Hakika,..Sau Tari Wasu mutanenan Basu da ganewa Dauka Suke Yadda Tunaninsu yake haka na kowa yake,Sun Manta Cewa ko yatsun hannuwanmu ba Daya Suke ba,Wasu kuma Suna Amfani da kalmar Hausawa da suke cewa Duk Abunda Na keyi Shina ke Tunanin wasu Na aikatawa,Rayuwa Babu Abunda yafi Haduwa da masoyan gaskiya Dadi,Duk da gane masoyanka na gaskiyan,Nada Wuyar Sha"ani mussaman awannan Duniyar Tamu mai Cike da Abun Mamaki na Social media,Kada wani yayi Tunanin Don yayi Butulci gareka Ko kuma ya Nemi ya Tozarta ka,ya koma yana Tunanin Rayuwarka ta yanke kenan ,Ko daya Matukar Ki ka Dogara da Allah kika kuma kasance Mai Taimako don Allah bawai Don Duba da Hallayan Mutanen Duniya ba,Toh sakayyarki na wajen Allah ne,Har Abada Ni *JANAFTY* zuciyata bata Janye Daga Taimakon Wanda Ya nemi Taimakona ba koda ba Harkan Rubutu bane Koda aharkan Rayuwa ce,Zan Taimaka Saboda da ALLAH da Monzonsa da Kuma Duba da Nima wata ta Taimakamin har Nakawo wannan Mtsayin Danike kai,Sai dai Zakayi gaggawan Daukan Darasin Rayuwa Daga mabambamtan Mutane,Ni *Jamila Janafty* Nasani ta kowa ce, Naga Soyayya Ta Zahiri Data bad'ini, Dalilin Rubutu📝 Wanda ba Dabarata bace,Ba kuma wayau na bane,Hakika Dukkan godiya tana Wajen Allah ne,Domin *INDAN RANA💥 TA FITO...TAFIN HANNU✋ BAISA YA KARETA BA* ...👐 Dalilin Alkami✏Na zama Mummys din Wasu,Nazama Antie"s dinsu,wasu nazama Uwar dakin Wasu,wasu na zama Abun koyinsu,Nima kuma na Zama ya"ga wasu Dadama wanda Suke Daraja kimata acikin idanuwansu koda basu Taba ganina ba,Toh meya fi wannan Farinciki...,😅Babu Wlh ko Yau na bar Rubutu na tabbata Kimata a idon wasu al"ummah bazata taba goguwa ba,kuma alherina garesu bazai Taba Shafewa akwakwalwarsu ba,...Ko Ahaka aka Tsaya An Ci Riba,Annabinmu Muhammed (SAW) ya Horemu da in zamu So mutum Toh mu soshi Don Allah,kuma in Zamu ki Mutum Shima mu kishi Don Allah, Ba Daga yanayin Mutum ake gane Shi dan wani gida bane ,Anfi gane hakan Ta Furuci ko yanayin mganar Mutum Alkalamina wani jigo ne na Rayuwata Rubutu✏ da karatu 📝Suna Da matukar amfani arayuwata...Nafara Rubutu da Ra"ayin kaina,Kuma Zan Cigaba da Dora alkamina Har Sai Ranar Dani kaina naji na gaji na ijiye da Ra"ayin kaina,....., *ALKALAMINA*✏ Shine Abun *ALFAHARINA*_💕💞😘  Bikin Aisha da Fahad ya rage Saura Wata Hudu aka sanyama Fa"iza Rana wata bakwai Wanda lokacin yayi Daidai da tagama Candy Dinta,wannan karon Ban hana kaina kuka ba,Domin inaji ina gani agidanmu sai karewa ake ana barina,Dama mu uku ne muke kwana adaki daya Ni da Fa"iza da Rabia,su Maryam dakin Mama Suke kwana don daga ita har ya"Yanta basu Cika Shirgin yan gidanmu ba yadda kasan Suma ba ya"yan gidan bane. Ba laifi Fahad yana da Rufin ASirin Domin ma'akaicine A Hukumar Nepa,shiyasa akayi komai Cikin Wadata,Lokacin da bikin ya kariso Duk sai Aisha ta zabge ta rame kamar ba ita ba,haka itama Asma"u Suna jimanin Rabuwa da juna Saboda sanin yadda Suka Shaku,ammh babu yarda zasuyi Tunda haka Allah ya kaddara. Tun ana Saura Sati daya biki Na nesa dana kusa suka Fara Cika gida,Mamana Tazo Ana gobe biki tazo da Tsohon cikinta Haihuwa ko yau ko Gobe,Murna wajen Asma"u ba"a mgana ganin yadda Mamanta tayi kyau Sosai dagani ta samu kwanciyar Hankali ita kuma ganin yarta ta Sai Tsausayin Ta yakamata sosai,na ganin yadda zatasha kewa in Aisha Tatafi ta barta. Ranar biki komai Tare Suka sanya Aisha da Asma"u Domin hatta ita Sai Da Fahad yama kaya kamar wacce zai aura saboda sanyayama Aisha Zuciya,Tun da Suka ga yammah tayi suka Fara kuka kar Aisha taji lbri koda motocin Daukan amarya Suka zo Aisha bata yarda hannunta ya Rabu Dana Asma"u ba har aka kaita Dan madaidaicin gidanta dake GRA. Kuka da Tashin hankali bai Faru ba sai da Asma"u zata bi yan kawo amarya Aisha ta kamkameta tana kuka,duk yadda Asma"u taso Daurewa Abun ya gagara itama kukan Ta Fashe dashi,Ganin Sunki rabuwa da juna yasa aka bar Asma"un anan Sai da angwaye suka zo suka Siya baki kana Suka Wuce da Asma"`u Suka Sauketa agida,shi kanshi Sai da Asma"un tama Aishan Dubaran Zata Shiga Bayi ne ta Fito sai dai ta waiga taga batanan,Ranar Fahad yaga kuka,kuma yakara Jadaddama kaunar dake Tsakanin kawayen Biyu. Auren Aisha shi yakarama Asma"u da zaman kadaici da kuma zaman gidansu Tunda yanzu bata zuwa mkranta,kullun Cikin yada mata Habaici Umma keyi ita da Hajiya Iya ba wajen wanda take samun mgana mai Dadi sai Wajen Anty Amarya, sai Baba lami da hassatu sabbin masu aikinsu,dayake Suna da kirki Sisai,mama ko dama ban da gaisuwa babu Abunda ke Shiga Tsakaninsu daga ita har ya"yanta... Tun bayan Abunda ya Faru Ni Asma"u Nayi alqawarin bazan kara kula kowani Namiji ba,ammh kuma ya zatayi domin Zaman gidansu na neman ya Fita kanta,Kwatsam sai ga Ishaq ya Shigo cikin Rayuwata wanda kai Tsaye wajen Abbana yafara Zuwa Neman izini Shi Abban da kanshi ya kirani yana Fadamin,ban yi gardama na karbi ishaq tare da addu"ar Allah ya sanya Shine mijina,Shima yana da Abun hannunshi Domin ma"aikacin banki ne,haka nake Duka jinin samarina masu dashi ne,Aisha dataji lbri kamar ta Zuba Ruwa kasa tasha saboda Murna har gida na Kai musu Ishaq suka gaisa da Fahad. Tun ban saki jiki da ishaq ba Har nazo na Saki ganin mun kwarari Wata biyar Tare,har akayi bikin Fa"iza wanda ko ankonin bikin Shi ya dinkamin naci biki dashi,Ana gama bikin Fa"iza nasa Araina Insha Allahu nice alayi wannan karon,ashe Tsugunne bata kare ba,mganata da Ishaq tayi karfi wanda waliyansa Sun Hadu da Waliyaina,Wannan karon har an kai ga saka Ranar Aure na da ishaq wata goma masu Zuwa Baikon da ya sakani cikin Farinciiki har sai nayi Azumi bakwai Na nuna godiyata ga Allah,masoya aduk inda Suke sun Nuna jin dadinsu tare da Fatan Alheri kar Aisha taji lbri hakama Ammi mamata ko sai da tayi Sadaka,duk da lokacin tana jego ne Domin ta Haihu Abunda ta Haifa baizo da Rai ba. Bikina da Ishaq ya Rage Saura Wata biyar Aka sanya Ranar Auren Rabi"a Wanda Abbana yace zai hada Rana daya ne,ita ajigawa zatayi Auren ban Wani damu ba nidai ina ta Shiryen Shieyen biki na tare da murnan zan Wucema gorin Hajiya iya da Umma,Bikin na Saura wajen kwana 30 Na samu lbrin Haihuwar Mamata wanda ko nace sai naje,dakyar Abba ya barni Ranar ko Bauchi tayi baki,domin ishaq da kanshi ya kaini har gidan kakannina kuma ya Shiga Suka gaisa,daganan muka Wuce gidan Mamata,shima har Ciki ya Shiga ya gaida Mamata ya mata barka ta samu mace,ya gaida Hajiya abokiyar zamanta,Nan ya barni bayan mun Rabu akan Zai zo ya Daukeni.. Murna ta cikani ganin nayi kanwa ina nan har akayi Suna,Kanwata taci Sunan *FATIMA* Suna cemata Fati,gaskiyan gidan da mamata tayi Aure yayi ne,gidane mai Cike da tarbiya da Son Mutane haka Abokiyar Zamanta hajiya da ya!yanta ke Dawainiya dani kamar jininsu basu Nuna bambamci Tsakaninmu,hakama Shikanshi Prof,din Tun bata saki jiki har na saki jiki,su Anty Nafi da Anty Safina kowa na son Asma'u taje gidanshi ne,Tuni Farinciki ya sa na manta da zaman gidanmu na Share kafata,sai da Abba ya kira awaya yace Nadawo,Kana na Fara Shirin Dawowa. Wani Abunda na lura dashi Tun Zuwa na Bauchi da sati daya Ishaq ya rage kirana ta waya wani lokacin ma sai na kirasa sai yace aiki ne yamai yawa bata

Chapter 5 of 11