na Sanye cikin wani Takalmi mai Tsinin bala"i Idanuwanta ta kara musu gashin ido sunyi Zaro zaro,hakama Kumbunan Hannunta suke zako zako Sunsha penti,Fara ce Doguwa Duk da tana karawa Dana kanti ammh babu Laifi tana da kyanta Daidai gwargwardo.
*POLINA JOSAYA* Kenan Arniya ce Kuma tangararriyar karuwa wacce taga Duniya kala kala,Abokiyar Holewar M.A ne Suna Tare Tun Shekaru Uku da Suka Wuce,kuma yakasa Rabuwa da ita,Tun kafin motar ta gama parking ta Nufeshi cikin yanga da kwakwarsa Ita ta budemai Murfin Mota ya sawo kanshi waje,Tunkafin Yagama Daidaita Tsayuwarshi Ta cakumoshi Zuwa Jikinta Cikin Wata murya mai Cike da Shagwaba tace"U know i miss u *MY SUGAR*..."?Tafada tana Fito da Harshenta tana lasan Gefen Wuyanshi kamar Wata mayya.
Rumgumota yayi Sosai yana kissing gefen Wuyanta Suka Fara Tafiya Zuwa cikin gidan Yake Fadin"I know Babe buh Stop give me a call,juzt text me,U aleady know duk Ranar da My Noory ta ganoki Both of us We got into Trouble.."Batama Saurareshi ba Bakinta ta Hada Danashi lokaci Daya Tana Shafa Sassan jikinsa,shikuma cikin kwarewa ya cakumi Nononuwanta Ahaka suka Shiga Falon gidan Suna Tsotsen Bakin Juna kamar Wasu mayunwata,Dakyar Polina ta bari suka Shiga bedroom Saboda yadda idonta ya Rufe Ta kosa taji ya Shigeta,Cikin besdroom din Suka Shiga chan Suka Cigaba da lalacewarsu.
*****************
_BAUCHI_
*Area-Yakubu Wanka*
""Zaune Suke Dukkansu a kayatattacen Falon na Hajiya,wacce ke Zaune kan lallausan Cafet din daya Malale dakin,Ta jingina da kujera gefenta an saka mata kananan Filulluka Guda biyu,Daga yadda take Yamutsa fuska Daga gani Bata da lafiya ne.
Ya"yan nata Guda biyu mata Wato *ANTY NAFISA* da kuma *ANTY SAFINA* Sune Suka Tasata agaba Suna Faman mata Sannu,kai kadai tadaga musu Ta maida kanta ta Jingina da kujera tana Runtse ido,Anty Nafisa ce Ta kalli Hajiya ta Girgiza kai kafin ta Maida kallonta kan Anty Safina tana Fadin"Wai ni kan Anty Safina ba Wanda zai iya zuwa gidan Ya Baffan ya gano ko lafiyanshi kalau..? Wlh kina ganin Duk wannan Tashin Ciwon Na Hajiya Tunaninshi Ta Daurama kanta.."Anty Safina dake Bama karamar Diyarta Nono tace"Wazai je Nafisa,kema kinsan banda *YA YUSUF* ba wanda yasan Address din gidan ya baffa,to koma mun sani kinsan ko giyan wake mukasha Mallam bazai barmu muje ba,sanin Halin wannan Tsinanniyar Matar nashi wacce bata ganin kowa da gashi,karshenta ta Wulakantamu Ta hanamu Shiga.."Tafada Tana kwafa da alamun Abun na Cimata Tuwo kwarya.
Hajiya Datayi Shuru kamar batajin Me Suke Fada,tana jin Duk Abunda Suke Fadi,mirmishin gefen baki tayi batare ta ce komai ba,Anty Nafisa ko da Anty Safina suka cigaba ta tattaunawa har *MAMAN FATI* tayi sallama ta Shigo dakin,nan dukkansu suka gaisheta ta amsa cikin sakin Fuska tana Fadin"Ina wanka naji Shigowarku,Kunzo duba Hajiya ne..?
Anty Nafisa ce tace"Eh Maman Fati,Hajiya dai jiki yaki Dadi,wai anya Mama Fati baza'a yi Wani abu akan Abunda ke Damun Hajiya ba.."Wacce aka kira da Maman Fati ta Nemi gefen Hajiya ta Zauna tana Fadin"Toh Nafisa me za"ayi,damuwarta bai Wuce Baffa,ba kuma Mallam yahana kowa mganarsa agidan nan nikaina Abun na damuna,ace ka Rataye iyayenka Fiye da Shekara daya,ammh ko waiwaiyansu bakayi ba,Anya Ba lauje cikin Nadi acikin wannan al"amarin.."Anty Safina tace"Wlh Maman Fati matarnan ta Asirce Ya Baffa,kiga fa ko su Hajiya baya gani da gashi daga ita sai yan"uwanta Sune Mutane awajensu,mu yanzu haka ya Rataye Nombobinmu ko ka kirashi baka samunshi.."
Anty Nafisa zatayi mgana kenan Sukaji gyaran Muryan Prof.Abdallah Mahamud Azare,Mahaifinsu wanda kowa yake kiranshi da Mallam,da Sallama ya Shigo Falon na Hajiya Bayansa Dr Nura ne Likitansu ne,shike Zuwa Dubasu in wani matsala tataso,dukkansu suka Shiga gaisheshi ya amsa cikin sakin Fuska,Tsohon Dattijo ne mai Haiba da kwarjini,Akallah ashekaru zai kai 69 aduniya,Dogo ne Fari ammh Farin gashi ya baibaye kanshi Da kuma Farin gemunshi,kallon Farko zakamai ka Fahimci ilimin addini dana boko ya Ratsashi Duba da yarda Fuskarsa ke sanye da Wani Farin gilashi mai kara karfin gani,Akallon Farko in akayimai Zaka Fahinci Tsantsan Kama da Suke yi da Abdallah,domin Hatta dogon Karan Hancinsu iri daya ne,Mutun ne wanda yasan kimar Dan Adam da kuma sanin yakamata ba kowa ke Fahintar damuwar Mallam,ba bai cika bama Fuskarsa damar bayyanar Abunda ke Cikin Ransa ba,yana da kyakyawan alaqa da mutane,uwa uba Matansa da ya"yansa wandanda suke Tamkar wasu Bangare na jinin jikinsa.
Maida gaisuwansu sukayi kan Mallam,Amal yar wajen Nafisa ya dauka yana Fadin"Saukar yaushe ya"yan Hajiya..?Anty Safina na Dariya tace"Bamu Dade da Zuwa ba Mallam.."
Yana kallon Hajiya tace"Kunzo Duba Mamarku ce,Kurika yi mata Fada,ta cire Tunani acikin Ranta saboda jninta yahau sosai yanzuma mganar da Muke da Dr.Nura kenan.."Anty Nafi ce tace"Mganar da mukeyi kenan Fa,Hajiya bazata daina Tunanin ya Baffa ba mallam me zai hana ayi masa waya asanar dashi batajin dadi kila in Matartasa taga dama ta barshi yazo ko ta ganshi taji Dadi.."
Mallam bai yi mgana ba,illah mirmishi kadai dayayi yana Kallon Dr Nura wanda ke gwada Bp Din Hajiya,sai da yagama Dubata kana ya kalleta yana Fadin"Hajiya gaskiya jininki baya kasa,bakya Taimakonmu wajen Ragema kanki damuwa,Ga kuma Shekaru Don Allah Hajiya ki Rage zama Shuru da kuma Shiga Tunani mai Girma..."Shuru tayi batayi mgana ba sai chan tace"Insha Allahu Dr za"a rage.."Tafada cikin muryan Ciwo,Gyada kai yayi kafin yace"Yauwa hajiya naji dadi yanzu zan Wuce asibiti sai zuwa anjuma in nadawo zan biyo na kawo miki sauran mgungunarki,Allah yakara lafiya.."
Gabadaya Dakin suka amsa da Ameen,mikewa Dr Nura yayi bayan ya Ramkwafa Yana ma Mallam sallama,Hannu Mallam din ya mika masa hannu sukayi masabaha kafin yayi sallama dasu ya Fita Mallam yabu bayanshi,Bai dade ba ya Dawo dakin ya mika ma Anty Nafi Amal yana kallon Hajiya kai Tsaye yace"Hajara kinji dai Abunda Dr Nura yace Ko..? Bata dago ba ta gyada kai Gyara tsayuwa yayi yana Fadin"Toh ya rage Naki ki Rage ma kanki saka Tunani da damuwa kan yaron da baisan kinayi ba,saunawa zan gayamiki Hajara Baffa ba damuwarki yakeso ba addu"anki yake Bukata,Muna fa ba bamu sonshi bane da kika ga Bamu Nuna damuwa akan Halin daya ke ciki..? Wlh munfi ki damuwa Hajara kawai muna boyewa ne saboda kada muba damuwa dama tazo tayima illah,Don Allah Hajara kicire Komai aranki Mu dage da yima Baffan addu"an Allah ya warware masa Duk Abunda ya Shige masa Duhu.."
Hajiya tayi Shuru tana Share Siririyar kwallar Data Zubomata Cikin sanyin Murya tace"Haba Mallam mganar Nadai damuwa fa Duk bata taso ba,kaduba ka gani Yaushe Rabon Baffa da garin nan Har Ciwo nayi na kwanta asibiti ba sau daya ba,bai zo ba,,Kanwarsa Tazo ta Rasu wajen Haihuwa Shima bai zo ba,Kuma yusuf ya sanar dani da bakinsa ya Fadamai ammh bai zo ba,kuma bai kira waya ba,Tun ina kiran wayarshi baya dauka Karahema na daina samunshi,haka zamu Zurama Baffa ido ya lalace a gindin wannan Tambadaddiyar matar tashi da yan"uwanta.."Tafada Hawaye suna Zubomata Cikin tsausayi Maman Fati da Dafa kafadanta tana bata baki
Mirmishin yake Mallam yayi kafin yace"Hajara kenan,Ai shi yana ganin Duk Abunda yayi Daidai ne kuma da kike kiran matarshi Tabadaddiya toh ai gashi ya zabeta fiye dake,shiyasa nake kara Sanar dake mu dage da addu"a ammh babban Abun Takaichn Shine Baffa bashi da kokarin ibada balle addu"an tsari,shiyasa koma miye za"ayi mai bazai yi Wahalan kamashi,Bance karki damu ba,ammh ki Rage kodon samuwar Lafiyanki Don Allah Hajara..."
Jin Haka yasa ta gyada kai Tana Fadin"Naji zan kiyaye insha Allahu..."Yaji Dadin Haka kai tsaye yace"Alhamdullilah Allah ya kara lafiya,shikuma Allah ya warwarwaremai Abunda ke damunshi.."Gabadayansu suka amsa da Ameen kafin ya Fice Daga dakin,bayan Fitan nashi Ma Su Anty Nafi hirarsu suka Dasa,da hajiya ta gaji daji tashi tayi ta Shige cikin bedroom dinta cike damuwa ya!yan nata Suka bita da kallo,Sunfi kowa sanin yadda Yaya Baffa yake awajen Hajiya bata iya Hadasa da kowa duk acikinsu tafi sonshi Don ma tana mai kawaichin dan Fari,Kuma dama Hausawa sunce Duk wanda kafi so,shike Wahalar dakai.
Haka dai Suka cigaba Da tattaunawa Mtsalan yaya Baffa,har zuwa lokacin da!a aka kira sallar la"asar,suka mike suka gabatar da sallah,suka Fita waje Suka taya Maman Fati hada hadar Dora abincin Dare,suna gidan kananan kanensu suka dawo daga mkrantan Boko,Fati da Mahamud,da Suka kuma yi Shirin Zuwa islamiya,Mallam ko yana Cikin dakinsa bai kara lekowa ba,shima ko bai Fada ba,Mtsalan ya Baffa tana damunshi bayason Nunawa Saboda kada ya karama Hajiya Wata damuwa,ammh ko su da suke kannenshi suna cikin damuwa da Wannan Halin da Yaya Baffa ke ciki,ammh gaskiyan Mallam ne,babu Abunda yake Bukata sai addu"a Tunda Allah ya Hadashi da Shedaniyar Mata mara Tsoron Allah.
Tare sukayi girkin Dare Su da Maman Fati suna yi suna Hirar Duniya babu Ruwansu in ka gansu bazaka ce Maman Fati abokiyar Zaman Hajiya Bace,saboda yadda take Tafiyar dasu kamar yaran data Haifa da cikinta,Sai Wajen 8 na dare kowacce Mijinta yazo ya Dauketa suka Nufi gida,dayake Duk anan garin Bauchin suke aure,ammh sai da suka Shiga wajen Hajiya suna kara Rokonta ta Cire Dukkan Wani Tunani aranta in har Takamar Wasila boka da Mallam,su kuma zasu Nuna mata Babu Abunda yafi karfin Allah,Hajiya taji dadin mganarsu Tayi ta saka musu albarka dama ita Abunda bataso Su Rika ganin laifin Baffa,wanda tasan da gangan Baffa bazai ki Zuwa wajensu ba,sai dai in da wani Dalili mai girma.
*************
Tana Shirin Baro Wajen aikinta Suna Baban Falo ita da Sister bahijja bayan Sungama Round din bada mganin karfe 6 na yammah,suna Zaune bisa wasu Fararen Kujeru suna hira ita da Sister bahijja,taji wayarta dake cikin karamar jakarta dake kan Teburin dake wajen ta dau Tsuwa,Ringing Tone din Dataji ne yasa ta saki mirmishin Mai kayatarwa sanin kowaye ke kiranta.
Cikin Azama ta jawo jakarta ta ciro wayarta inda taga Sunan mai kira Baro baro kamar Haka *RABIN RAINA* Cikin Doki ta daga kiran Tana Fadin"Rabin Raina kina Lafiya..? .Dagachan bangaren Aisha tace"Ina fa lafiya Rabin Raina,kwana nawa ban ganki ba na zata zaki zo cikin weeked din nan ammh naji ki Shuru.."Tafada cike da Shagwaba.
Dariya Asma"u tayi kafin tace"Yi hakuri Rabin Raina kinsan dai Halin da"ake cikin in ba Ranar aiki ba bana samun Fita,ki bari gobe in na Fito sai na biyo kafin nazo asibiti.."Tura baki Aisha tayi tana Fadin"wlh ban yarda ba,Nidai kizo yanzu in kintashi aiki,gama Da"nki nan yana ta Fama da zazzabi.."Zaro ido Asma"u tayi tana Fadin"Na Shiga uku meya Faru dashi Rabin Raina..? .
Aisha na gintse dariyarta tace"Zazzabi ne ke damunsa Wlh,ammh na bashi mgani.."Asma"u najin haka tayi Tsaki tana Fadin"Baki kaishi asibiti ba,Gaskiya kinada sakaci Rabin Raina yaro baida lafiya ku barshi agida kuna Zencen wai kin bashi mgani,Allah daga ke Har Fahad din sai ahankali zan biyo yanzu in natashi Daga wajen aiki.."..
Tana Fadar haka ta yanke kiran,Aisha dake kusa da Fahad ta saki Dariyar Jin dadi tana Fadamai Bisa kafada take Fadin"Allah sarki Rabin Raina,Bata wasa da Abunda ya Shafi Amir dinta,kaga yadda ta fara fadanta na Fama gatanan zuwa yanzu.."Kanta ya Shafa yana Fadin"Baki da dama yanzu zaki sa in tazo taga karyane ta hadani dani dake tayi ta Mana Fada ko. "Dariya Aisha ta saki batare datayi mgana Ranta yayi mata Dadi Jin Rabin Ranta zata Zo yanzu.
Itako hankalinta Duk ya tashi,Karfe 6:30pm suka tashi daga aiki Ko tsayawa Signing din Tashi batayi ba Sister Bahijja ta barmawa ta Fito da Sauri rataye da jakarta,Adaidaita ta tara ta ce ya kaita G9,Bai Direta ako"ina ba sai akofar wani dan Madaidaicin gida,Kudinshi ta bashi kafin ta karisa bakin Get din ta Shiga kwankwasa,Aisha dake Jikin Fahad ta Saki dariya kafin ta kwalama Amir kira dake Haraban gidan yana Buga kwallo,Cikin daga murya tace"MAza Son Ruga ka budema Mom dinka get.."
Yana jin tace Mom dinshi ya Kwashi Gudu yaje ya Bude mata sakatar get din,dayake Wajen sakatar bata da Tsawo yana dage zai kamota,Yana bude mata ya Tafi ya Fada jikinta yana Fadin"oyoyo Momy na,Sannu da Zuwa.."Cike da mamaki ta Hau Shafa kanshi bayan ta Rikoshi sun Shigo gidan Cikin Mamaki take Fadin"My Son ya jikinka,naji dadin ganinka kaji Sauki yarona.."..
Yana Rike da Hannunta yace"Ni lafiyata lau Momy,yanzu na dawo Daga islamiya ma Mommy.."Kura mai ido tayi tana kallonsa aranta tana Fatan Allah ya Shirya Aisha,hannunsa taja suka Fada Falon da sallama,da gudu Aisha ta bar jikin Fahad ta isa ga Asma"u ta Fada jikinta suka kamkame Juna,Rumgumeta Asma"u tayi Tana Fadin"Uwar banza,mai Sama Danta ciwo ko.."Dariya ta kama Aisha ta saketa tana Fadin"Nasan in ba haka nace miki ba bazaki zo ba,gashi ni kuma nayi missing dinki over Rabin Raina.."Tafada tana Wani Shagwabe Fuska.
Tsaki Asma"u taja kafin tace"Allah ya Shiryeki bansan yaushe zaki Girma ba.."Tafada suna karisawa cikin Falon sai lokacin taga Fahad yana zaune kan Kujera yana musu Dariya,baki Asma"u ta Rike tana Fadin"Au kaima kana nan daman,Wlh wani Abun kai kake Daurema Rabin Rai tana Abunda taga dama,Allah ya Shiryeku.."Atare suka amsa da Ameen suna mata dariya,A tsaye Suka gaisa da Fahad,ita kuma Aisha taje kichen kawo mata Ruwa,Amir ko na wajenta,ta fiddomai Tsarabarsa data Siyamai akofar asibtin,Dakyar ta tsaya tasha Ruwa,kafin tayi musu sallama ta Wuce basu barta hakaba Sai da Fahad ya matsa zai kaita gida data Nuna bataso,sai Aisha taji Haushi Dole ta Fito,ya Fito da motarsa kirar 306 Aisha da Amir na daga musu hannu suka bar Haraban gidan.
_Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 300kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 500cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._
*Shakira....*🖐
*14/03/2020*✍
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
*Free Page*
.....Suna tafe a cikin motan Fahad ya kalli Asma'u yana faɗin "Wai ni rabin ranmu ya maganar abokina ne Ja'afar? Har yanzu banji wata magana mai ƙarfi ba..."
Kallonshi tayi kafin ta ɗan murmusa tace "Kai zan tambaya abokinka ne, ni ai banda labarinsa yanzu.." ta faɗa kai tsaye tana maida hankalinta ta gefen window tana bin motocin dake wucewa da kallo, furzar da numfashi yayi kafin yace "Kinsan Allah Ma'u? Na daɗe rabona da waya da Ja'afar, sai jiya rabin ranki tasa na laluboshi, ina fara mai maganarki naji ya fara min zille zille bai bari munyi maganar ba ya yanke kiran."
Ajiyar zuciya ta sauke tayi shiru tana kallon gabanta kafin tace cikin sanyin muryanta "Nima nafi sati biyu rabona da jinsa awaya, tun ranar da yazo na gaya masa saƙon Abba, da yace ya fito inda gaske yake, wlhi tun daga ranar bai kara kirana ba har yau, sai ni ne da naji shirun yayi yawa na kirasa sai kuma akayi rashin sa'a matarsa ta ɗauka. Kaji irin zagin rashin mutuncin data min? Tun daga ranar na goge nombarsa acikin wayata, na ganeshi shima yana cikin layin sauran ne, da sunji maganar su fito ayi maganar aure sai su gudu.." ta ƙarashe faɗa muryanta na sarƙewa kamar zatayi kuka..
Ran Fahad ya sosu ya kalleta cikin tsantsar tsausayawa yace "Ita matar tashi..? Kuma bai kiraki daga baya ba..?" Gyaɗa mai kai tayi kafin tace "Tun daga wannan ranar bai ƙara kirana ba, ni kuma sai na rabu dashi, inaga nidai kawai bani da rabon aure ne a duniya Fahad.." tana faɗa wasu ƙwallah masu zafi suna zubo mata...
Yana karya kwanar gidansu yace "Assha! Haba Asma'u ya zaki ce haka, ashe kin ma fidda rai da rahamar ubangiji kenan? Ki kwantar da hankalinki keep on praying Asma'u muma masoyanki muna tayaki insha Allahu mijinki na tafe wanda kowa sai ya yi mamaki da ikon Rabbi.." maganarsa ta sanyaya mata rai, duk da koda yaushe shida matarshi kalamansu kenan agareta, kuma bakomai bane yasa suke faɗar hakan ba, sai don kawai suga ta kwantar da hankalinta, tayi ta saka farin ciki da walwala a zuciyarta kamar kowa, shiyasa duk duniya bayan mahaifiyarta bata da kamar Aisha da mijinta.
Bata samu zarafin sake magana ba, ya faka motarsa a ƙofar gidansu daidai lokacin da ake ta fitowa daga masallaci gashi a ƙofar gidansu hasken ƙwai ya gauraye wajen babu wuta amma an tada gen, gabanta ne ya faɗi ganin Abba shida su Walid sun fito daga masallacin dake gefen gidansu tana sallama da Fahad suka haɗa ido, gabanta ya faɗi ras! Da sauri ta ɓalle murfin motar ta fito tana ɗagama Fahad hannu, baima lura dasu Abba ba shiyasa bai fito sun gaisa ba yaja motarsa yayi kwana ya fice daga layin.
Jikinta asanyaye tazo zata shiga gida taji muryan Abbanta yana kiranta.."Asma'u..." Muryarsa a kausashe, da rawan jiki ta juyo tana faɗin "Na'am Abba...ina yini..?" Bai amsa mata ba illah binta da wani irin kallo da yayi kafin yace "Mu shiga gidan tukunnah.." ya faɗa yana yin gaba, shi ya fara shiga cikin gidan, hannunshi riƙe da na Walid, dayan kuma yana riƙe dana Khalipa, bayanshi tabi jikinta ba inda baya rawa don Asma'u akwaita da tsoro sosai.
Suna shiga harabar gidan ya waigo yana kallonta cikin muryar dattako yace "Meke tsakaninki da Fahad ne Asma'u..?" Cikin wani yanayi ta ɗago tana kallon Abban nata cikin mamaki tace "Wane Fahad ɗin kuma Abba..?" Fuska ya ɗaure tamau kafin yace "Wane Fahad kika sani ke? Fahad dai mijin kawarki Aishan gidan Mallam Wada nake nufi.." jin haka yasa jikinta ya ƙara yin sanyi kanta na duƙe tace "Laaaa Abba wlhi babu komai, na biya ta gidan ne da muka tashi aiki na duba Amir baya jin daɗi, shine ya matsa sai ya kawo ni gida, tunda yammah tayi..." ta faɗa tana sadda kanta ƙasa, ya daɗe yana kallonta kafin yace "Yayi kyau, amma ki kiyaye.." daga haka bai ƙara cewa komai ba ya sakai ya shige cikin gida.
Da kallon mamaki Asma'u ta bishi kafin ta riƙe kai tana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu kenan har Abba sai da aka kaima wannan gulmar da aketa yawo da ita agari? kuma wlhi tasan daga gidansu maganar ta fita waje har ta kai gidansu Aisha, wai ita Asma'u wacce suka taso tun suna yara ita da Aisha tare sukayi yarinta suka girma makarantan islamiya tare boko ma tare su wuni tare wata rana ma tare suke kwana, amma ace wai awayi gari itace zata so mijinta ta aureshi, wanda duk duniya bayan iyayenta suna cikin jerin mutane masu matuƙar muhimmanci arayuwarta, tayi tirr ga duk munafukin da yake ƙulla wannan abin har ya zama ana zarginta, har abada koda yau Aisha zata faɗi ta mutu ta bar duniya sai dai ta mutu ba miji, amma bazata taɓa auren Fahad ba, cike da wannan takaichin ta shiga cikin gidansu, su Baba Lami kaɗai ta gani atsakar gida suka gaisa suna mata barka da dawowa, ɗakin Umma cike da hayaniya, nan taji muryarsu Anty Ruƙayyah da Anty Bilki suna ta hiransu da dararraku bata leƙa ɗakin ba kawai ta wuce ɗakin Anty Amarya ta leƙa suka gaisa kafin ta wuce zuwa ɗakinta makulli tasa ta buɗe ƙofar ɗakin kafin ta tura ta shiga, ranta duk a cunkushe saboda ɓacin rai, takalmin ƙafarta kaɗai ta cire da safa sai hijabin jikinta da jakar hannunta, ƙofar toilet ɗinta ta tura ta shiga domin ɗauro alwala don lokacin sallar Magrib har ya fita ana shiryen shiryen kiran sallar Issha'i ne.
__________________
_Bauchi_
*Area-Federal Lowcost*
..Zaune yake a gaban Hajiya inda ita kuma take zaune kan kujera, dogon matashin saurayi ne fari yana sanye da shadda mai ruwan toka ɗinkin tazarce kansa ɗauke da hular zanna bukar, daga yanayin fuskarsa zaka san yana cikin tsantsar damuwa, cikin wani yanayi yake faɗin "Wai Hajiya kina nufin Baffa ko awaya bai kiraki ya gaisheki ba..?"
Cikin damuwa Hajiya tace "Bai kirani ba Yusuf, wai anya ma kuwa Baffa yana lafiya..? Kodai bai da lafiya ne yana chan kwance rai ga hannun Allah.. ?" Kai ya girgiza yace "Lafiyarsa ƙalau Hajiya ko last week munyi waya dashi na sanar dashi baki jin daɗi, yana nuna min zai kiraki har na mai faɗan ya kamata yazo ya ganku keda Mallam ya roƙi gafararku, ni kafin mu rabu ya tabbatar min da yanason yazo abubuwa ne suka sha kanshi.."
Tagumi Hajiya ta zabga cike da damuwa tace "Oh ni Hajara, Ya Allah ina roƙonka ka dawo min da ɗana Baffa gareni..." Ta faɗa tana sharan ƙwallah kamar wata yarinya, Yusuf ya kalli hajiya cikin ɓacin rai yace "Don girman Allah hajiya ki daina zubarma da Baffa hawaye, kefa uwace agaresa wannan kukan naki wlh in baki yafemai ba Allah zai kamasa.." batayi magana ba illah share hawayen data keyi cikin yanayin damuwa.
Wayarsa ya zaro acikin aljihun wandonsa yana cewa "Bari na kirasa, ni zan gaya mai gaskiya in yaji ruwansa, in bai ji bama ya rage nasa, don baida kamarsu karya ga kamar don Mallam ya kawo ido ya sanyamai shikenan ya sallama shi ba, wlhi matukar bai zo ya roƙi gafaranku ba ya mutu cikin wannan halin wuta zai shiga.." ya faɗa yana manna wayar a kunnensa cikin ɓacin rai, amma haka wayar ta gaji da nemam ɗauki ta yanke ba'a ɗaga ba, bai haƙura ba ya ƙara kira a karo na biyu, nan ma ba'a ɗaga ba sai ana ukun ne aka ɗaga kiran.
*****************
Zaune suke su huɗu asaman wani makeken dining suna breakfast lokacin around 11 ne na safe, da yake yau ɗin takama weekend ne, Wasila na kusa da gogan nata ta chaɓa uba ado ana wani kwarkwasa, sai Jamila da Hafsa dake gefensu suma cikin tasu kwalliyar amma su dressing ɗinsu babu kyan gani kamar wasu ya'yan arna.
Karo na biyu kenan wayarsa na ɗaukan ruri sai ya daga yaga mai kiran sai ya share, ganin haka yasa Wasila jikinta bai bata ba, cike da kissa da makirci tace "My Dee wai wake kiranka ne kake ƙin ɗagawa..?"
Bai ba maganarta muhimmanci ba, sai da ya kai lomar chips ɗin daya ɗebo bakinshi kana yace "Yusuf ne..." ya fada cikin halin ko in kula, gaban Wasila ya faɗi amma sai ta basar cikin nuna wani yanayi tace "Wane Yusuf ɗin..?" Bai kalleta ba yace "Wanda dai kika sani, Yusuf ɗina mana..."
Wani abu taji mai girma ya tokare mata a maƙoshi jin ya ambaci Yusuf dina, kunu tasha tana wani faman zare idanu, kiran ya sake shigowa akaro na uku, M.A ya ɗaga kiran dai-dai lokacin da yake share bakinshi da tissue yace "Kai ɗan wutar ciki ne wlhi, ka kikkira kaji shiru baka ma mutum uzuri ko yana cikin wani laluri..?" ya faɗa kai tsaye daga chan ɓangaren Yusuf ya saki ajiyar zuciya jin Baffa ya ɗaga kiran, ganin yadda Hajiya ta saka mai ido ne yasa ya saka mata wayar a speaker tana jin muryan Baffan.
Cikin ƙuluwa Yusuf yace "Dallah Mallam gafara chan, wai ka manta abunda na kiraka last week na gaya maka ne..?" Ɗan shiru yayi kafin yace "Kamar name kenan, sorry na manta kasan yanayin aikin namu? muna yawan shiga busy ne sosai.." Kai Yusuf ya girgiza kafin yace "Na rashin lafiyar Hajiya Abdallah, Hajiya da Mallam suna buƙatarka ka duba ka gani kakusa shekara guda baka zo gida ba hatta da a waya ka daina nemansu ka manta sune iyayenka waɗanda baka da kamarsu? Hajiya kullum jininta cikin hawa yake saboda rashin ka Baffa, koda yaushe a cikin zubda maka hawaye take, kana tunanin in ka mutu cikin wannan halin Allah zai yafe maka..?" ya faɗa cikin sanyi da lallami ta sigar nasiha,
Gaba ɗaya kalaman Yusuf sun kashema M.A jiki, yayi shiru bayan ya saka hannu ya Dafe kanshi, Wasila dake gefenshi dayake ya ɗan saki karar wayar tana jin duk abunda Yusuf ɗin yake faɗi, tuni taji zuciyarta ta rine ta koma baƙinƙirin saboda tsantsar baƙin ciki da takaichi, waye yake neman ɓata mata aiki....? ai bata gama mamaki ba taji M.A yana faɗin "Am so sorry Yusuf, wlhi inaso nazo naga su Hajiya da sauran yan'uwana, buh duk sanda nayi niyyar tahowa sai naji kwata-kwata garin