Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
kawo komai ba,sai Da Abba yace ta dawo ta kirasa ta Fadamai kuma yace gobe zai zo ya Dauketa,ammh sai me,har tagama Shirinta tana jiransa baizo ba kuma Tayi ta kiranshi awaya bai dauka ba,har Washe garin Ranar bai daga kiranta ba Hankalinta ya Tashi ta Shiga damuwa ta kuma Nuna tana son komawa Dutse ammh sai Mamanta ta hanata wacce Suke Kira Maman Fati,aShe Tun Ranar da Ishaq yace na jirasa,ya aika waliyansa suka karban mai kayan Aurensa tare da Sakon ya Fasa aurena,Ita ma Maman Fati Ammi ce ta kirata awaya tana Fadamata Abunda ke Faruwa tare da Shawartarta kada ta bari na dawo na Tsaya wajenta ta nemamin Taimakon don Tabbas al"amarin ba na lafiya bane,Ba Mamana kadai ba Duk masoyina Sai da Ya Shiga Tashin Hankali Da Abunda ya Faru Ganin na Tubure sai na Taho yasa Maman Fati ta saka Mallam ya kirani Falonsa ya Fadamin bayan yagamamin Nasiha karban kaddara hannun bibbiyu,Nayi kuka kamar Raina zai Fita wanda Shima sai da na kwanta ciwo harda su karin Ruwa agida,Tundaga lokacin Naji kila bani da Rabon Aure ne ni kaina ban Kara mganar komawa ba har akayi Bikin Rabi"a ina Bauchi Mamana da Hajiya da Su Anty Safina harda Shi Mallam din kanshi Suna kokarin Jana ajiki Domin Ciremin Duk damuwar dake damuna. Bayan Bikin Rabi"a Sai ga Aisha da Fahad sun sauka A bauchi Ranar Wuni mukayi kuka kamar Wasu yara,Aisha tana ta Fadamin Wlh Umma ce takemin Asiri domin Tasha Fadan cewa nafi ya"yanta Farinjinin Samari kuma gasu masu Hali bazata taba bari nayi Aure har naji dadi ba,ban Dauki mganarta ba illah na Bar Abun akan kila ni kuma Tawa kaddaran kenan Zaman gidanmu mai Cike da Kunci. Hajiya Iya ce ta matsama Abbana kan ya kira awaya maZa na dawo,ba yadda na iya haka na Hada kayana ina kuka Maman Fati na kuka,ammh bayan Mallam ya kirani yabani Wasu addu'o'i ya kuma yace Na zama mai Yawan Ibada,insha Allahu Allah na sane dani,Komawata Dutse sai da nayi Nadama Haka hajiya iya tatasani gaba da mganganun Son Ranta itako Umma wani kallo take bina dashi Cike da jin dadi Ranta fes Duka ya"yanta ta Aurar dasu A gidanmu bansa adadin kukan danayi ba,ko gidansu Aisha bana Son Shiga saboda bani so Ammi ta Fahimci Halin danike Ciki. Aisha ce tabani Shawaran mezai Hana na koma mkranta Tunda takarduna Sunyi kyau na yaba da Shawararta kuma kai Tsaye na samu Abbanmu mukayi mgana kuma ya amince nan na Sanar dashi School of Nursing nakeso yace zai saka A nemarmin,Nayi ta jiran Abbana ammh naji Shuru Koda na sakemai mgana sai ya nuna gwara na Hakura da karatun jin haka sai banji dadi ba na Kira Maman Fati na sanar da ita,ita kuma batare da Sanina ba tama Mallam mgana waya kawai yayi sai ga Sakon Maman Fati ta kira tace Na Shirya Duka takarduna Wani Mutumi zai zo ya karba,haka ko akayi yazo har kofar gidanmu ya karbi takarduna,ko Wata ba"ayi Ba Maman Fati ta kirani awaya ta Sanar dani na samu kurbin karatu a *SCHOOL OF NURSING BIRNIN KUDU..* Murna ta kusa ta kasheni saboda Farinciki,lokacin danaje na sanarma Abbana Umma na Falonsa baiyi mgana ba ammh ita sai da tanka wai dama dalilin danaki Auren kenan zan tafi chan nayi ta yawon Iskanci da Sunan karatu Hakama Hajiya iya Ta inda take Shiga banan take Fita wai harda ikararin Mamata tayi asara wlh ba inda zani,wannan karon nayi musu bore don ko ta kansu ban bi ba,Tunda Abbana ya amince kuma har 20k ya bani da zanyi Siyayyaar tafiya Tunda Bording zanyi,Kafin sati biyu ta cika na gama Hada Dukkan kayana,mijin Maman Fati da kanshi yazo har kofar gidanmu Wato Prof.Abdallah Mahamud Azare,ya tafi dani har cikin mkranta aka karisa sauran cike cike kunga yadda ake karramani malamai jin yace musu ni yarsa ce,ko kafin ya Tafi har an kaini Hostel,nan ya tafi ya barni bayan ya cikani da kudin harda sakon Maman Fati da Hajiya. Shigata Sch of Nursing Birnin kudu Ta taimaka wajen Chanza Rayuwata daga kunci Zuwa Farinciki,Na maida hankalina wajen karatuna,ban yarda na karayin Wata kawa ba Aishata kadai ta Isheni saboda kada wata ta Shiga jikina watarana taji lbrina har tayi min gori,Gashi ina jin dadin karatuna,Shekarata ta farko a mkrantan ammh har Sunana ya Fita saboda hazaka ta uwa uba kuma ina amsan Suna ya' ce ga Prof Abdallah Muhamud Azare,Duk da Asma"u Ladan Sharif nake amfani. Arayuwata bana kaunarma ace zamu samu Hutu saboda zan koma Zaman gidanmu mai Cike da kunci kowata dabiba tana murna Zuwa hutu gida ammh ban da ni,ga kuma karatu ba Halin nace Zani Bauchi,Sai da na koma gida hakanan na zauna dakin da Fa"iza da Rabi"a Suka Tafi suka barni,Aisha ta yi bari sau biyu bata da lafiya Infection ke damunta Suna Zuwa asibiti Neman mgani Fa"iza kuwa har tayi Mace,Ina Shekara ta Biyu naji Lbrin Auren Kursum da Fati,ko daya ban damu har akayi bikin nasu banzo gida ba,ina Tunanin tafi tafi gashi har gida ya watse Dagani Sai Maryam,kuma ita karamace acikinmu. Haka aka Dinga Dauki Daidai agidanmu Aka wayi gari har Maryam din tayi Aure ammh ita kano aka kaita Wani dan"uwan Mahaifiyarta Ta Aura,lokacin da akayi bikinta Ina mkranta muna jarabawar Karshe ce ta gamawa ko da ace bamu jarabawa ba Abunda zai kawoni don Babu Abunda Zan Tsinta sai Bakinciki,mganar Samari kullun na Fita sai nayi Saurayi ammh kuma ni na yankema kaina Hukunci bani kara kula wani Namiji Tunda alamu ya nuna kila bani da Rabon Aure Aduniya. Mun gama Jarabawarmu Ta Fita kenan Bayan mun je Asibti munyi pratical kenan,wanda a babban Asibtin Dutse nayi nawa,lokacin ne kuma Aisha ta Haihu Namiji,yaro yaci Sunan Mahaifin Fahad,Aminu suna kiranshi Amir,Rayuwa haka ta cigaba da gangarawa har na Dawo gida ina jiran Fitowar sakamako koda Sakamako ya Fito ta hannun prof.Abdallah Azare yazo saboda yadda komai yayi kyau batare da sani na ba har ya neman min aiki a asibtin Jaharmu Wato General Hospital Dutse,wanda Jin haka yasa na Shiga Farinciki ko banza zan Rage zaman gidanmu mai Cike da kunci. Inda Ace kudi na Siyan Miji toh da Aisha da Mamana Sun Siyamin gangariya ma kuwa,domin Sun Fi nuna damuwa ga Abunda ke Faruwa dani,niko na cire Abun Raina na maida al"amura ga Allah bana barci Sosai adare kullum cikin kai kukana nake ga Rabbil izziti kan yamin Zabin Alheri bana Wasa da azkar saboda kariya ce gareni,Kuncin gidanmu ya Riga yaxama acikin jikina,Ko Hajiya iya na Mganarta akaina bana tanka mata,balle kuma Umma wacce na Riga na gane Har Abada bata Sona,Anty Amarya ce kadai ta kwarai Acikinsu Balle Mama da ba shiga harkan kowa take ba daga ita sai ya"yanta. Abbana Yana jin zafin Abunda Ake man ammh kuma bashi da ikon Nuna wa,saboda kamar yana Shakkar Umma ne,ga kuma Hajiya iya Wacce bata kama Tsufanta kullum cikin Tsegumi take kamar wata yarinya,ba yadda basu kulla min Wajen Abbana akan ko waye yasamu ya Hadamu Aure dashi wai Tunda naki fito da miji,wai ko Samarin dake tafiya na baya ni nake Koransu da bakin Halina,Ammh meyasa su Sauran yan"uwa sukayi Aure..? ni na tsaya zabi da kuma jiran Mai kudi,duk Abbana bai bi ta kansu ba,domin Shi mutum ne daya san Hakkin Dan Adam,ammh Tabbas zamana babu Aure ahaka yana damunshi sai dai bai taba Furtama kowa ba,Domin kowa yasani Burin kowani Uba ya ga Duka ya"yansa Sun mallaki gidajen Aurensu. Aikina Shine Rufin Asirina da albashina nake ma kaina Hidima,in aka ga na Fita,toh gidan Ammi na Shiga ko kuma Naje gidan Aisha,sai ko Fa"iza wacce har yau bata yadani ba,Duka ya"yan gidanmu ba wacce bata haihu ba,daga mai Haihuwa daya sai me biyu,su Anty Rukayyah dai Sune masu garke,duk da suma bana Hulda dasu,wani lokacin sai mun hadu dasu Sunzo gida mu gaisa wani lokacin saboda gulma har cemin suke wai bana Zuwa gidansu Alhali ba wacce tataba Nemana,Mamanta ma takara Haihuwa inda samu Namji yaci Sunan Mahamud,,Shi kan ban samu zuwa ba Saboda Wajen aikina. Duk sadda naje gidan Aisha ita da Fahad da Amir sun dinga murna kenan Su rasa ina zasu sakani,in kuma zan dawo Fahad ya dauko ni amotarshi ya kawoni,wannan Dalilin ne,yasa Gulma ta Fito kuma Daga gidanmu ne,wai cewa ina Son Mijin Aisha Fahad wanda mgana ta Zagaye gari har gidansu Aisha,Ammi dataji sai tayi dariya tace Da haka zai Faru datafi kowa murna Yadda Asma"u da Aisha zasu zauna karkashin kulawar namiji daya jin haka yasa ba"a kara Kawo mata gulman ba,naji mganar Abun ya bani mamaki,Aisha ma dataji sai ta dinga Tusama Fahad ra"ayin Aurena,shi kuma yana Kaucewa daga karshe har Fada ta Faru tsakaninsu,Shi Fahad din ne ya kirani ya Fadamin Banje gidan ba ta waya na kirata ina mata Dariya bata da hankakli nan na Dinga lallashinta,Dakyar ta hakura ta bar mganar,Shine lbri har kunnan Abbana,kuma wannan ba aikin kowa bane sai na Umma itace Bata kaunar Taga ina Farinciki arayuwarta. Duk Da kuncin gidanmu yazamarmin jiki,ammh Wani lokacin Abun na kaini bango,na koma daki nayi ta kuka kamar Raina Zai Fita,shiyasa bana kaunar ace yau bani da Zuwa Asibiti duk saina Wuni cikin kunci ko ban Fito ba Daga waje zakaji Umma da Hajiya iya Suna yada min habaici wai naji kunya muna kwana daki daya da kannena har Sun Yin Aure sun barmin dakin niko naga wajen zama harda gyara daki Tunda Banda niyyar Aure,saboda Sunga na Siya karamar katifa da karamin Wardrope,niko ban bi ta kansu ba,Acikin Raina ina Fatan ko banyi Aure ba Insha Allah bayan na mutu ina Fatan Rabauta ranar gobe kiyama. Lokacin dana Fara aiki,Umma da hajiya sukayi Borin Hauka saboda Sunga ina Zuwa aikin kwana,har cema Abbana Sukayi ba Asibiti nake Zuwa ba Yawon iskanci nake zuwa,Duk da haka bai bi ta kansu ba,sai ranar kwatsam,Walid ya tashi cikin Dare yana ta amai,nan suka daukosa Zuwa Asibtinmu,Lokacin muna babban Falo,nida Sister bahijja mu muka karbeshi muka bashi Taimakon gaggawa kafin likita yazo,Abbana yana ta kallona nasan ko bai Fada ba Aransa yaji dadi,Inaga Tunda lokacin ya Toshe kafar kawo Wata mgana Domin da yawon iskanci nake zuwa da bai ganni ba. Fahad ya hadani da abokansa Dadama bana bashi hadin kai,sai da naga Aisha ta damu,kana na yarda na Fara kula wani ja"afar sama sama,shima tafiyarmu bata yi nisa ba Ranar na kirashi Matarshi ta Dauka tamin Zagin kare dangi,Tundaga Ranar na goge Nombarshi na kama kaina,bai kirani ba nima ban kara kira ba,shima yabi Sawun Sauran kenan,ban damu ba Domin daman ban sakashi araina ba,Na riga na Fidda rai da Aure kwata kwata arayuwa ta maida kaina ga bautar ubangiji ina Fatan mutuwa ta Riskeni ina cikin Bautar Ubangiji. _____________________ *Portharcourt* Wasila ta Fito daga Dakin Afusace Fuskarta sam Babu Fara"a ko kadan,Ko barayin su Jamila bata kalla ba Wadanda Suka baro Saman Dinning Suka Dawo kan Lumtsum lumtsumar kujerun Falon Sukayi Dai dai,Bata musu mgana ba illah jefama Jamila wayar datayi ita kuma ta Cafe,Cikin Fushi da Takaichi ta Haura sama kamar zata kife . Tana Shiga Bedroom din Ta Iske Abdallah yayi kwance Rigingine ya kurama Rufin dakin Ido Hannayensa Suna Harde akirjinsa da alamu ya Shiga kogon Tunani,Wasila ta Dade Tsaye akanshi tana Nazarinshi Gabadaya Ranta ya gama baci,Hayowa gadon tayi,hannu ta sanya ta Cire hannuwanshi dake saman kirjinsa ta Maida kanta awajen,Ajiyar Zuciya ya sauke yana Bin Wasila da kallo asanyaye kamar Wanda bashi da lafiya. Cike da makirci Take Shafa Kirjin nashi tana Fadin"Dee wai meke Damunka ne,Tun bayan da kayi waya da Yusuf mood dinka ya chanza,Meya Fadamaka ne Wanda ya Tadamaka Hankali haka Dee..? Bai mata mgana ba,kuma bai taba ta ba,Ganin yayi mata Shuru yasaa ta Dago kanta tana kallonshi Ganin idonshi biyu yasa Abun ya Fara bata Tsoro Cikin Wani yanayi Tace,"Dee..."Lum yayi da ido kafin ya Diresu akanta yana kallonta. Hannunshi ta Riko tana Fadin"Wai meke Faruwa ne..? kasani cikin Duhu ko wani Abun ya samu Hajiyar..?"Ta Fada Cike da Wani Salo,Bai mata mgana illah Hannunta daya Raba danashi kafin yace"Babu komai Noory plz Ina bukatar Kadaici.."Yafada yana juya mata baya. Zaro ido Wasila tayi Zuciyarta na Rawa,Kan bala"i Yaushe Abdallah ya Fara mata haka ita da ko Tari tayi Abdallah sai yaji Dalili,in tayi mai mgana jikinsa na Rawa yake amsamata ba,Bata jira komai ba ta Diro daga kan gadon ta Fada Tiolet da Sauri bayan ta Kalli Agogon bangon dake bangon Bedroom din nasu 12 ta kusa,Agurguje tayi Wanka ta Fito,koda ta Fito yana inda ta barshi ammh wannan karon ya Runtse Duka idanuwansa kamar mai barci bata bi ta kansa ba Ta Shafe jikinta da Lotion dinta Wardrope dinta Na nufa ta Fito da Wani less dinta Dinkin Doguwar Riga ne,Attachement din dake kanta ta gyara ta Daure da Band kafin ta Yafa wani karamin gyale bisa kanta ma"ajiyar Takalmanta ta Nufa ta jawo Wani baki mai Tudu ta sanya,daganan bangaren Jakunkunanta ta Nufi ta Dauko wata karama baka,Wata Drower naga Ta bude sai ga Kudi da yawa basu da iyaka,bata tsaya kirgawa ba ta sanya hannu ta Diba iya Dibanta ta Maida ta Rufe,ganin har yanzu yana yarda ta barshi yasa ta karisa gaban Dressing Mirrior din ta Dauki key din motarta Tana Fadin"Dee zani Bida Sai gobe zan Dawo in na gama Abun nakeyi in kuma Ban gama ba sai jibi.." Dakyar ya bude Idanuwansa da Suka chanza Launi,yana kallonta Bai iya mata Wani dogon mgana ba Don lokacin kanshi ke Saramai Cikin Siririyar murya yace"Wazai kaiki,baki ganin Rana tayi.."Far tayi da ido kafin tace"Dont Wrry Samuel zai kaini ba da kaina zanyi Driving ba.."Kai ya gyada maka kafin yace"Safe landeed Noory.."Mirmishi ta saki kafin ta Duka ta Sumbaci Kuncinsa,ta Fice da hanzari,Da kallo ya bita har ta Fice Daga dakin,maida idanuwansa yayi ya kulle yana jin gabadaya yanayinsa Babu dadi kamar Wanda akama Dukan Tsiya.. _Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 300kachalšŸ‘Œta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 500cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._ *Shakira..* *21/03/2020*...šŸ“ *ZAMAN GIDANMU..!* _(Mai cike da Kunci)_ *Jamila Umar(Janafty)*  Nan inda ta barsu nan ta iskesu ganinta cikin Shirin Fita yasa Duk Suka tashi Zaune,Jamila ce tace"Anty Fita zakiyi..? Kai ta gyada musu kafin tace"Eh Bida zani kuma sai jibi zan dawo,so u better take good of ur Self Abi.."Gabadayansu suka gyada kai kafin Su mike Suyi hugging dinta Suna Fadin"Safe trip Anty our grant To Momcy..."Suka Fada atare,kumatunsu ta Shafa kafin tace"Alright,in kuna bukatar kudi juz ku Tambayi Dee,kunji ko.." kai Suka Daga mata,alamun Sunji,Wucewa tayi da Sauri Suka bi bayanta har Farfajiyan gidan inda morarta Kirar prado take,Samauel ta Shiga kwalama kira sai gashi ya Fito da Gudu yana Fadin"Yes Madam.."Key din hannunta ta Wurgamai kafin ta Bude bayan motan ta Shiga batare da yayi mgana ba ya Shiga mazaunin Direba Ya Tada motar,bayan ya Zuba hon,megadi ya wangale musu kofar Makeken gidan Suka Sulala waje,Su Jamila na Daga musu hannu har Suka Karisa Ficewa daga gidan. Falon Suka dawo suka sake Daidai kowacce nata Faman Danne dannen A faska faskan wayarsu,Motsin Saukowan Abdallah Sukaji duk suka waiga yana sanye da Riga da wando Blak and White,Kayan na kamfanin Armani ne,Fuskarsa ta bayyana alamun kamar yana cikin damuwa,wayarsa ke hannunsa sai key din motarsa,Bai ko kalli barayin da Su Jamila Suke ba,ya Fice yana Taku cikin Sanyi da Rashin kuzari,Da kallo Jamila da Hafsat suka bisa kafin su koma Su kalli juna,suna tabe baki,dama ko da chan bai Cika Shiga Shirginsu ba koda yaushe Fuskarsa adaure in dai ba yana tare da Anty Wasila bane,ba wacce Ta damu sai ma kara Lafewa da Sukayi bisa kujerun Falon,yayinda Jamila ta shiga kwalama Josepen kira,jiki na rawa ya Fito daga kichen jikinsa daure da Rigar Girki,Yamutsa Fuska Jamila tayi tana bashi odar ya kawo musu lemo ita da Hafsart,jikinsa na rawa ya amsa kafin ya Fice daga Falon da hanzari,Hafsat ta rakashi da Wani Dogon Tsaki tana Fadin"Arnen banza dan Wahala..." yana Fita haraban gidan,Emeka ya taso da hanzari yana gaisheshi,hannu kawai ya Dagamai,bai mai mgana ya Nufi motarsa matrix,Emeka yayi hanzarin budemai bayan mota,ammh sai ya Daga mai hannu kafin yace"No i will drive my Self.."Yafada kafin ya bude bangaren Direba ya Fada,cikin kwarewa yayi mata motar key,kafin ya saki Hon,baya Emeka yaja lokacin da Abdallah yayi kwana da Motar ya Fice da Sauri kamar Zai tashi sama,yanayin yadda Emeka ya ga Ogan nashi yasan Sometins is happen. Elelewo yanufa,Bakin Get din gidan ya Saki Hon,Polina dake kwance kan Daya daga cikin kujerun da Suka ma Falonta kwanya Kewar Abdallah Duk ya cika yau Wajen kwana biyu kenan bataji shi ba,kuma tana ta kiran wayarsa baya dagawa sai dai ya yi mata Text dacewa zai Kirata ammh har yau Shuru,Tafara damuwa kuma gashi yau Sunday balle tace zata sameshi A office,kamar amafarki taji Hon din mota,cikin Fitan hayyaci ta tashi ta Fito da gudu wanda daga ita sai Wata kamarar yaloliyar Riga wacce Bata boye komai na Surar jikinta ba,bata bude get din ba,sai da ta leka ta karamar kofar taga Abdallah ne kana Tafara jan get din gidan cikin Farinciki da Zumudi. Yana kallonta ta cikin motan ya sakarmata mirmishin nasa mai Saka mata dadama Farinciki,cikin Hanzari ya Sulala da motar cikin dan karamin Haraban gidan nata,bai gama ba Daidaita parking ba Polina ta Rugo da Gudu ta Budemai Kofar mota ta sa hannu ta jawoshi waje Ta fada jikinsa Cike da Farinciki ta kamkamesa,ajiyar Zuciya ya saki lokaci daya yana kara Riketa cikin Wani yanayi take Furta"I Realy Miss u my Sugar..."Take Fada tana kara Tusa kanta acikin Kirjinsa cikin Wani yanayi,Shima kara Riketa yayi yana Shafa Bayanta Zuwa Tudun Hips dinta yake Fadin"Me too my Babe.."Yake Fada cikin Wani yanayi yadda taji muryansa ne,yasa tayi Saurin dagowa tana kallonshi Cikin Wani yanayi take Fadin"My Sugar,waht Wrong With u,u look so Cool..."Tafada tana Shafa Sajensa da hannunta tana kuma gangarowa zuwa Kasan Wuyanshi Lumshe ido yayi kafin ya Rike hannunta bai mata mgna ba,illah Janta dayayi Suka Fara tafiya Zuwa cikin gida,yana kankame da ita,Tun acikin Falon yafara Sumbatar polina cikin Wani yanayi ganin yadda yake aikamata Sakoninsa nasa cikin Zafi zafi Shiyasa ta gane Wani Abu na damunsa batayi Wasa ba itama ta tallafeshi Tana bashi dukkan Halin kai,basu samu isa Cikin bedroom ba sai da Sukayi Round na Farko,bayan Sun Dawo Natsuwarsu ne Ya dauketa Suka Shiga bedroom inda zasu Dora daga inda Suka Tsaya. ******** Karfe 4:30pm Motar Wasila ta Shiga haraban gidansu,Cikin Isa da takama Wasila ta Fito Ta nufi cikin gidansu Tubdaga Falon Farko take kwalama Hajiya kudirat kira,yan aikinsu kuwa Suna ganinta sai Duka mata Suke Suna mata barka da Zuwa,Ammh ko kallo ba wanda ya Isheta,tana kokarin Tusa kanta abedroom din Momcy dinta ne Ta Fito Suka cikaro da Juna,Cike da Mamaki Hajiya Kudirat ke kallon Wasila kafin tace"Wasila Kece Tafe yanzu..? Bata mata mgana Ba illah Fadawa datayi jikin Momcy ta Fashe da kuka tana Fadin"Momcy Zan Rasa Abdallah,Momcy Abdallah yanzu bayason Kallona,yadaina jin mganata..,Komai yana so ya Lalace Momcy.."Tafada kara Sautin kukanta Rikota Momcy tayi Suka Fada cikin Bedroom dinta gefen makeken gadonta ta Zaunar da ita tana Fadin"Wai meya Faru ne naganki da gaggawa haka,ba mun gama mgana sai gobe zaki Taho ba..". Wasila ta Yamutsa Fuska tana Share Hanci tace"Haba Momcy taya zan iya zama har nakai gobe,Zuciyata bazata jura rasa Abdallah ba Momcy Wlh Shegun Tsofaffun nan Suna neman yin Nasara akanmu.."Tafada cike da bakinciki kafadanta Momcy Dafa tana Fadin"Kalleni nan,Wasila..Matukar ina raye wlh Abdallah zai cigaba da tabbata naki Har Abada,ki kwantar da hankali in Sun sa wata basu san Wata ba,Gobe da Sassafe zamu ma Boka dangaju Sammako,Kisa ranki anuwa Abdallah haryanzu yana Tafin hannunki ne.." Wasila ta Riko hannun Momcy tana Fadin"Toh nidai muje yanzu Momcy plz.." Kusa da ita ta zauna kafin tace" Baki da Hankali ne,Yanzu fa yammah tayi so kike kafin mukai Dare yayi mana ahanya,kuma kin manta boka Dangaju,baya ganin mutane da Zarar 4 tayi,kibari gobe mana,kina Fa da Taurin kai Wani lokacin.." Tafada cike da Kufuluwa,Gyada kai Wasila tayi kafin ta Sadda kanta bisa kafadan Momcy tana sauke tawagen ajiyar Zuciya,ita kuma momcy ta Riko Gefen Cikinta Tana Bubbugawa alamun lallashi. Momcy da kanta ta Fita tama megadi mgana kan ya Shigar da Sumuel Dakinsa,bayan tasa an kawo mai Abinci,wasila ko Dakyar ta iya Shan Fressh Milk,Ta kwanta ko Babanta sai dai yaji lbrin Zuwanta abakin Momcy bai tsaya tambayan me ya kawota ba,saboda indai Wasila bata wata sai Tazo Bida. Tun around 9 wasila keta kiran Nombar Abdallah tana Ringing baya dauka,Shiko Har lokacin yana gidan polina Suna Sheke ayarsu wayarma tana Falo baisan Wasila na kira ba,itako Duk inda hankalinta yake yakai Dubu tashi,Tafara safa da marwa tana Jijjigan jiki,Zuciyarta na hango mata Abdallah ya Tafi Bauchi ne bayan Tafiyarta,Wayar Jamila ta kira tana Tambayanta Abdallah,nan take Sanar da ita ta Fita ba Dadewa ya Tafi kuma haryanzu bai Shigo ba. Nan fa Wasila ta Tsure ta fara kuka tana Duren Duren Ashar tana Zagin Hajiya da Mallam tana kuma ikirarin har Abada Abdallah nata ne ita kadai cikin Wannan Halin Momcy ta tarar da ita cikin bacin Rai Ta Rikota tana Fadin"Are u mad..? kina Abu kamar Wata yarinya,Waya Fada miki Abdallah zai barki ehe...? Wlh in baki daina Wannan Wutar cikin naki ba Zaki lalata Duka aikinki da kanki kin Manta Sharadin Boka Dandugi ya jadaddamana banda gaggawa ya Fada ba Sau daya basau Biyu ammh kwata kwata Shigen Zuciyarki na neman Warware komai.."Tafada cike Da bacin Rai.. Kuka Wasila ta Fashe dashi tana Fadin"Momcy Sun Rabani da Abdallah,wlh SuN Rabi Da Dee,ina ta kiran wayarshi bai dauka ba na kira su Jamila sunce ina Fita ya Fita,ina zaije Momcy yau fa babu aiki,Kilama Bauchin ya Tafi. "Tafada tana Dora hannu akai Momcy bata samu Zarafin mgana ba wayar Wasila dake hannunta Ta dau kara,azabura ta Duba ganin Sunan my Dee ya Fito baro baro yasa ta Daka tsalle tana Fadin"Momcy Dee na kirana...' Tsaki Momcy taja kafin Ta fice Daga dakin Cike da Haushin Wasila,Ita ko Wasila kuka ta sakama Abdallah kuka,Tana Fadin ta kirashi yafi Sau nawa bai daga kiranta ba,Shiko lokacin ma ya baro gidan polina around 11pm na dare nan ya Shararamata karyan cewa waya ya samu Daga office kan wasu kaya da"aka Rike so tunda yaje yazama Busy bai samu kanshi ba sai yanzu,ma yake hanyar komawa gida,sai alokacin Hankalin Wasila ya kwanta Dataji ba Bauchi yaje ba Don ayadda take ganin Shegiyar Uwar Abdallah din komai Baffa yanzu Tunda ta samu Baffa Bazata barshi Ya dawo gareta ba,Shiyasa zatayi Duk iya bakin kokarinta na ganin tayi musu katangar karfe dashi Domin Abdallah Shine rayuwarta bazata taba bari Wata mace ta kusanci Abdallah ba bayan Ita. ******** Da Sassafe Su Wasila Suka Fita,Da kanta dake Driving din motar yayinda Momcy ke gefenta,kauyen Bazumagi Dake garin Bida Suka Dosa Chan cikin Daji Bukar Boka Dandugaje taje,Lokacin da Suka je wuraren goma ne,Don ma Sunyi Gudu ahanya Wajen akwai Nisa Sosai,sai da Suka jira Wata mata Ta Fito,don layi akemai Domin kowa yasan aikinshi kamar yankan uwa yake.. Suna Shiga Suka Zauna kan Wani Buzu dake gabanshi Takalminsu Rike a hannunwansu Domin ba"a Shigo mishi Bukar da Takalmi,ko kallonsu baiyi ba illah kansa dake Duke ya kurama Wata Kwarya dake gabanshi ido,yana kuma mgana kasa kasa,kallo daya nayi ma Bokan sai

Chapter 6 of 11