ya fitar min aka ko waya na daga da niyyar kiransu sai wani abu yazo ya hanani kabama Hajiyata haƙuri, kace mata ta cigaba da min addu'a insha Allahu na kusa zuwa gareta da ikon Allah.."
Ya faɗa idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur, cike da rauni bai jira cewar Yusuf ɗin ba, kawai ya katse kiran yana jin wani irin abu ya tokare mai ƙirji, kwata-kwata baya ƙaunar yaji an ambaci garin Bauchi yanzun nan zaiji duk zuciyarsa ta ɓaci yaji baya ƙaunar zuwa garin, iyayensa kuwa gasu aranshi amma an ciremai duk wani tsausayinsu balle har ya tuna dasu yaji ƙansu yaje ya dubosu, gashi abun na damunsa amma ya rasa wazai faɗama damuwarsa ya tallafa masa yaji sanyi.
Wasila da ƙirjinta ke tsananta bugawa jin kalaman Abdallah ta matso kusa dashi cike da makirci tana faɗin "What wrong my Dee naga ka shiga cikin wannan halin plz...?" Bata ƙarasa ba ya tashi daga wajen ba tare daya kalleta ba, cikin wani irin yanayi ya haura sama kamar wanda bai da lafiya, da kallon mamaki ta bishi, ita da sauran ƙannenta.
Tana jin ƙarar buga ƙofarsa, miƙewa tayi ta riƙe kugunta da hannuwanta tana zagaye gurin take faɗin "Ni za'a batama aiki? Toh wlhi baku isa ba, nayi alƙawarin mallakar Abdallah ni kaɗai har abada, saboda haka bazan taɓa bari ya dawo gareku ba.." ta faɗa cike da tsantsar tashin hankali tana wani huci fuskarta a ɗinke babu wani annuri.
Jamila ce tace "Anty Wasila u have to wark hard fa, zuwan da mukayi wajen boka last nida Momcy dama ya faɗa mana komai na shirin lalacewa cuz Mamanshi da Babanshi basu zauna haka ba, kai hatta yan'uwanshi mata suma tsaye suke a kanshi da addu'o'i kuma wannan Yusuf ɗin ma shima har sakawa yake ana mai saukan Alqur'ani, duk don alalata miki aiki.." Wata uwar ashar ta danno ta lailalaya kafin tace "Ni zasu tozarta? Ni *WASILA* Wlhi basu isa ba! Ban fito ba sai da na shirya, ai wannan shegen tsohon nashi tun lokacin aurenmu sai da Dukaji ya sanar dani baya wasa, hakama uwar tashi, dukkansu ƙyalesu nayi sai na rabasu da abunda suka fiso, shi kuma wannan ƙaramin alhakin Yusuf so nake na mai zuwa ɗaya na gama dashi, wlhi matuƙar boka da Mallam na cikin duniyar nan sai nayi FARRAƘU a tsakanin Abdallah da iyayenshi da ƴan'uwanshi ba ƙara mallarshi ni ɗaya tal a hannuna.."
Ta faɗa tana ƙara jadadda kalamanta, Hafsat ce ta miƙe tana mata jinjina tace "We know u our sister, mun sanki in kikace zakiyi tohpa sai kinyi ne, ya kamata keda Momcy ku sake wani sabon shiri, tun kafin su karkatar da hankalinsa wata rana kiji labarin ya tafi Bauchi baki sani ba.." cikin murmushin nasara tace "Ina!...In su a tsaye suke toh wlhi ni Wasila a tafe na kwana, mu zuba dani dasu shege ka fasa, bani aron wayarki na kira Momcy tawa na barta a ɗaki.."
Da hanzari Jamila ta miƙa mata wayarta ita kuma ta latso nombar Momcy ta latsa wajen kira, ringing uku tayi naji wata ƙatuwar mace ta ɗauka da wata ƙatuwar murya take faɗin "Hello my Dota..." Wasila na tafiya zuwa cikin ɗakinsu Jamila tana faɗin "Momcy komai fa ya fara lalacewa, ki shirya zamu koma wajen boka na kan dutse, dan shegun tsofaffin nan sunƙi barina Momcy komai nayi sai sun lalata min.." ta faɗa cikin karyewar murya.
Cikin wata irin murya wacce aka kira da Momcy tace "Don't worry my Dota...Ai ni nayi miki alƙawarin har abada Abdallah naki ne ke kaɗai, in har bazasu gaji da lalataman aiki ba muma bazamu taɓa gajiya da lalata musu dukkan al'amuransu ba, kishiryo gobe mu tafi, a wannan karon zan nuna musu ni cikakkiyar banufiya ce gaba da baya...!"
******************
Hajiya data gama jin komai, sulalewa ƙasa tayi tana kiran sunan Allah, shima Yusuf ɗin shiru yayi ya sa hannu ya dafe kanshi kawai, Hajiya ta daɗe a haka kafin tace "Ba komai Yusuf, insha Allahu zamu cigaba da gayama Allah, shine zai mana maganin duk wani abunda bamu sani ba, Allah ya shiga sakanin nagari da mugu.
Da Ameen Yusuf ya amsa kafin ya ɗora da faɗin "Tabbas hakane Hajiya, wlhi Baffa baya cikin hayyacinsa, wannan shegiyar matar tasa ce ta bake komai itace ta juyar mai da kai, wlh tunda Baffa ya auri wannan watsatstsiyar yarinyar ya chanza gaba daya, amma ba komai zamu cigaba da gayama Allah, kuma insha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe.." ya faɗa yana miƙewa tsaye, kuɗi ya ijiye ma Hajiya agefenta yana faɗin
"Zan koma Hajiya, dama nazo dubaki ne, Allah ƙara lafiya Zainab na gaisheki may be sati mai zuwa direba ya kawosu ita da yara, ta matsa sai tazo ta ganki.." Hajiya na murmushi tace "Yusuf baka gajiya da ɗawainiya? Toh an gode Allah ya saka da alheri ya jiƙan magabata, ina amsawa daka ƙyaleta kawai tunda naji sauƙi sai dai ko in zata zo saboda sauran yan'uwanta don naji suna jajenta.."
'Yar dariya yayi kafin yace "Ba komai Hajiya, zata zo insha Allahu bari na leƙa nama Maman Fati sallama, sai na koma wajen Mallam faga chan zan wuce." kai ta gyaɗa ta mai fatan Allah ya kaishi lafiya, a kichen ya yadda Maman Fati yayi mata sallama itama bayan ya bata kuɗi alhalin kuma yazo musu da kayan abinci shaƙe da booth, kai Yusuf dai baya gajiya shiyasa wani lokacin su Hajiya ke kallonsa kamar Baffa, saboda yadda yake ɗawainiya dasu.
Falon Mallam ya koma suka ƙara tattauna maganar Baffa, shi dai Mallam baiyi magana ba, don in yaji ana asiri ya kama Baffa, sai dai kawai yayi dariya yace su daina cewa haka, kawai su dage da addu'a koma miye Allah zai warwareshi cikin sauƙi a haka suka rabu da Mallam bayan shima nan ya cikashi da kuɗi, Yusuf kenan baya gajiya ko kaɗan, addu'an gamawa da duniya lafiya yayi ta kwararamai, kafin su rabu cikin tsantsar farin ciki da fatan Allah ya kaishi lafiya.
*Assalamu Alaikum,Gaskiya korafin Wasu akan kudin buk din ya isheni Wlh,Bafa ni kadai bane na Fara Saka 300 akan Farashin kudin karatu ba,Marubuta dadama Sunyi haka,Buh ammh naga kamar nawane yayi Yawa ko? Ni janafty na tsani maimaita mgana Daya Damuna take Sosai,Ada ma Ni so nayi na Hakura da Rubuta lbrin sai Zuwa gaba,Buh sakamakon Alfarma wasu dayawa yasa zan Saussauto da Kudin karatu akan 200 ammh Don Allah Kada wacce ta karamin haka in kina Son mgana dani kibini private kiman mgana zan Saurareki,ammh banason Wata mgana acikin group din Masarautar Shakira Don Allah,kuma mgana ta karshe plz and plz kurikaman Uzuri komai DAn,adam baya gudanarshi Sai da Babban Dalili,ina da Dalilina na Sanyama wannan Buk din 300,meyasa na sanya ma Malika 200 shima inada Dalilina,agaskiya banji Dadi ba Sam,Yadda kuka kasa Daina Maimaita mgana daya kuma babu Wacce ta Bini Pc,sai mgana kuke Cikin group to dawa kuke..? in bangani ba fa..? plz mu zama manyama na Tunda dai kowaccenmu ta Mallaki hankalinta kanta,Bakomai Ayanzu zaman gidanmu ya koma 200,so Duk wadanda na karbi kudinsa 300 suman mgana na Maida musu Hakkinsu Nagode Sosai Fatana ban batama kowa rai abayanina ba.*
_Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 200kachal👌ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 300cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._
*Anitha..*👐
*15/03/2020*
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
_Ummina...💔Ummina...💔Ummina...💔...💚💙💛❤....U are So special *UMMINA*💔💘💕💞Tanque So Much Ummina Allah ya biyaki da gidan Aljannah Firdausi Can"t Love u Less Ummina *KHADIJA SALISU YUSUF*_🔐
*Free page*
*TUSHE MAFARI*
...." *PROFFESSOR MAHAMUD ABDALLAH AZARE* Shine Cikakken Sunan Mahaifin M.A,wanda ya kasance Haifaffan garin Azare ne, Local goverment ce Dake Jahar BAUCHIN YAKUBU.
Proffessor Mahamud Abdallah Azare,Yana da tarin ilimin Addini dana Boko wanda yayi gwagwarmaya a Jami"o'i dadama har Zuwa yanzu dayake Matsayin proff.a Abubakar Tafawa balewa Federal University Bauchi,abangaren Islamic Studie,kuma yana Zaune a agarin Bauchi,yana Da matan Aure Biyu *HAJIYA Hajara* ce Babba sai Matarshi ta Biyu *HABIBA*, Yana da ya"ya Guda Shida,Namiji biyu Mata Hudu,hajiya Hajara keda Biyar Mata Hudu Namiji Daya,sai Habiba data keda Biyu Mace daya Namiji daya.
Babban Da'nsa Shine *ABDALLAH* Wanda Shine Dansa na Fari,Wanda Hajiya Hajara ta Haifarmai bayan Shi sai tayi Safina,sai Nafisa,sai Zainab,sai Farida wacce Allah ya karbi Rayuwarta awajen Haihuwarta na Fari,ta rasu Duka daga ita har Abunda ta Haifa,Sai Habiba data ke da Biyu Fati,da mahamud,Wadanda sune Kanana,Dalilin dayasa kowa ke Kiranta Maman Fati kenan.
Gidan Proff. Muhamud Abdallah Gidane Babban gida ne,ginin zamani mai Cike da Wadata da Rufin Asiri,Suna zaune ne a Unguwar *FEDERAL LOWCOST* dake cikin garin Bauchi Gidane daya kunshi Tarbiya da girmama Manya,Ya"yansa suna da kyakyawan alaqa da girmama juna,bai Auro Maman Fati ba sai daga baya,ammh kuma sai zaman lafiya yakara wanzuwa agidanshi bayan Zuwanta Suka hada kansu da Hajiya suka zama tamkar yaya da kanwa,Ya"yansu ko suna Tafiyarsu dasu yadda ya dace,Tana Kokarin kyautata musu suma suna Bata girmanta amtsayinta na matar mahaifinsu Duk da ba aurenta na Farko ba kenan Tayi aure A dutse har ta Haifi yarta mace kafin Su Rabu da mijin Allah yasa kuma Tsakaninta da Proff. Abdallah akwai zama atsakani sai yazo ya aureta har ta Haifi ya"ya Biyu dashi.
Abdallah Dane Mafi Soyuwa awajen Iyayensa sakamakon yaci Sunan kakansa ne,wanda ya Haifi mahaifinsa wato Abdallah,Shiyasa suke Kiransa *BAFFA* Tun yana karaminsa Sunan Baffa ya bisa sakamakon Haka iyayensa suke kiransa,sai kannensa kowa ya Dauka Yaya Baffa yaya baffa,shikenan Sunansa Abadallah ya bace abakin kowa...
Hajiya Hajara Tana matukar Son Abdallah acikin Ranta,sai dai Tana mai kawaichin Dan fari bata cika Shiga Sha"aninsa ba,sai dai Mallam wanda baya mai Wannan alkunya jawosa yake ajikinsa Kamar wani kaninsa,Tun yana karaminsa yake da hazaka da wata baiwa mai Tarin yawa,shiyasa Mahaifinshi ya dauki Dukkan Buri ya Daura akanshi,sakamakon Shine Namiji kwara Daya da Allah ya basa,sai daga baya aka samu Muhamud.
International school yayi dake nan Bauchi anan yayi primary dinsa har Zuwa secondary Sch dinshi Bangaren Addini kuwa bayan islamiyan da suke Zuwa mallam bai barsu haka ba musamman ma Shi da yake ganin Namji ne,A internatinal Sch suka Hadu da Yusuf Tunda ga Primary ajinsu daya har Zuwa gama mkrantansu,wanda Shi Yusuf ya kasance Maraye ne,Allah yayi ma mahaifinshi Rasuwa mahaifiyar sa ne Kadai ce Wacce yake Kira Anne.
Dalilin Abokantanka Yusuf da Abdallah da kuma Shakuwarsu yasa Duka iyayen suka san juna,domin in Baka ga daya to yana tare agidan daya,Saboda Shakuwarsu ko makwannci basu iya rabawa suna tare yau su kwana gidansu Yusuf gobe kuma gidansu Abdallah Abunsu gwaninin ban, sha'awa gasu yarane masu Tarbiya da Sanin ya kamata...
Sai dai Tun Tasowarsu suna da Bambamcin Ra!ayi Wanda Shi Abdallah bai Da Yawan Fara"a da Sakin Fuska,Sabanin Shi Yusuf ne Mutum ne mai Raha da barkwanci koda kannen Abdallah ne haka zaka ganshi yana ta Hira dasu ana Dariya sabanin Abdallah da bako da yaushe yake Saka musu baki ba ko sakoshi akayi sai dai ya murmusa ba kasafai ya cika mgana ba,Wani lokacin Mallam na mai kirari da Miskili kafi mahaukaci ban Haushi,Ahaka suka samu nasarar samun Gurbin karatu ajami"ar Ahmadu bello dake zaria da Kokarin Proff.Muhamud Azare ammh kowanne da course din zai karanta,Shi Abdallah zai karanta Quantity Survey ne,ayayinda Shi Yusuf zai karanta Engenering ne.
Ko Amkaranta Duk da ba Department Dinsu Daya koda yaushe suna tare,Domin Hostel dinsu daya,kuma koda yaushe suna tare a laborary suna karatu,Domin basu da wasa ko kadan koda yaushe Cikin Maida kai Suke ga karatu Domin Cikar Burin Mahaifinsa...
Basu Rabu ba sai da Suka kammallah Digree dinsu na Farko,shi Yusuf Buk ya tafi ya Dora Masters dinshi ayayinda Shi Abdallah ya Zauna anan Abu din yana Cigaba da master dinshi,Tun Abdallah na matashin sa Zatinsa da kyansa suka Fara bayyana koda Suke mkranta ko Friendship bai yarda ya kulla da wata mace ba gwara ma Yusuf yakan dan kulasu ammh Shi Abdallah sam basa gabansa,Yan matan Jami"a dadama sun Sha Zuwa su kawo Tayin Soyayyarsu ammh baya karba daga karshe sai dai ya bar Yusuf da yar Murya yana basu Hakuri.
Bawai Baya son Mace bane,No Tun yana yaronsa yake da Burin irin macen dayake Muradin Aure,yana son Auren Doguwar mace,Fara kuma ta kasance tana da ilimin addini dana Zamani wacce zata mutumta iyayensa ta kuma kasance Wacce ke Tsoron Duniya,to yagama Auna yan matan wannan Zamanin Duk ya Fahimci Basu da kamun kai ballatana Mutumci ,ga Rashin aji,shi kuma ya Tsani mace mara Fasali da Rashin aji,Shiyasa har yagama Hada masters dinshi ba"a ce ga Buduwansa ba.
Cikin ikon Allah yana Gama Hada masters dinshi aka kawo Ma proff. Mahamud Tayi aikin Costome yana Tuntunbar Abdallah shi kuma ya Amince kafin Wani lokaci ya Shiga aikin Costome Wanda ko Shekara Uku baiyi ba yadinga samun Cigaba sosai Ada a lagas aka ijiyesa ammh da aka bashi matsayin DCG sai aka maidashi Porthercourt.
Duk da Proff.Mahamud Azare yayi karatun Boko soaai ammh bai sai ya bar ya"yansa mata saka saka, ba,da kin kammallah Secondry sch Dinki bai bari ki dora karatun Cigaba agidanshi da Zarar kin samu miji zai Miki Aure,ya Aurar da Safina da Nafisa,Duk anan garin Bauchin sukayi Auren,yanzu Farida ce tayi SSCE Dinta sai Zainab dake aji biyu amatakin karshen,Ita ma Faridan tana da mai Sonta,Zainah kuma yar gida za"ayi doMin Allah ya Hada Soyayyah mai karfi Tsakaninta da Yusuf wanda Tun tana karamarta ya Furta Anne ita kuma tazo tama Mallam mgana ya Amince.
Ba"ayi Auren Nasu ba Sai Da ya samu aiki A NNPC dake Kaduna tare dana Farida aka Hada,wacce ita kuma tayi aure a kano,lokacin da akayi biki da agidansu Tafara zama Wajen Anne,sai bayan Wata hudu kana Suka tattara suka Koma Kaduna NDC,achan ya Siya gida domin ragema kansa Zirga Zirga,ganin Yusuf yayi aure sai Mallam ya matsama Abdallah kan ya Fito da Mata yayi aure,ammh Abdallah yace amai Hakuri Har yau bai ga Wacce yakeso ba.
Ada Abdallah Mutum ne Nagari mai kokarin kyautatama iyayensa,ga kawaichi da Kuma Dattako,sai dai Tun yana yaro Mallam kemai Fadan yana Sakaci da addu"a Abdallah bai damu da ibada Sosai ba,Banda kamsin salawatun baya Wani ibada,ko yan Nafilfilin nan bai da kokarin,Balle akai ga Azkar din Safe dana Maraici da Anyi mgana yace Baida lokaci ne,Hajiya da Mallam suna iya bakin kokarin suna kuma Tsaye kanshi da addu'o'i Tunda shi ga Abunda ya zama.
Ada Duk Wata yake Zuwa Bauchi yayi Kudi ya sai gida da Mota,Koda wani Lokaci cikin kyautatama iyayensa yake da yan"Uwansa ,Rana tsaka komai ya Chanza daga Rayuwar Abdallah sakamakon Shigowar Wasila cikin Rayuwarsa.
*WASILA ARMAYA"U BIDA* Shine Cikakken Sunanta,Banufiya ce ta Uwa ta Uba,Haifaffiyar Niger State,Agarin Bida Dake Minna,Wasila Su uku ne awajen Iyayensu,Sunan Mahaifiyarsu Hajiya Kudirat,sai Mahaifinsu Alhaji Armaya"u,Rayuwarsu wata rayuwace babu kwaba balle gyara,Tun Suna kanana Sun Taso Sunga Mahaifiyarsu Tagama da Mahaifinsu domin Daga ita sai ya"yanta da yan"uwata yake gani da gashi,Hajiya Kudirat ta gama mallakeshi dashi da Dukiyarsa sai Abunda tace yakeyi,Shiyasa Tun Suna kananana Suka Taso da wannan Tarbiya,gashi Hajiya Kudirat tana Sonsu bata son Abunda zai bata musu Rai Shiyasa ta barsu Suke Abunda Suka ga dama,Shiyisa Dangin Ubansu Suka kawo Ido suka sanya musu,domin babu mai gaya musu,Suji Wasila ita ce Babba dai Jamila sai Hafsart Wanda tabasu Tsawon Shekara Shida,wasila ba mace bane mai kyau ammh akwaita da Son Mu"amala da abu mai kyau Tun tana karamarta Tana Son Mamanta na Shigen Shigen Malamai,Kuma Yadda take Gudanar da Mulkinta yake Bata Sha'awa itama tana Fatan in tayi Aure ta mallake Mijinta yazama yana Tafin Hannunta..
Wasila Tun Tana karamarta idonta Abude yake,Tun Suna Secondry schl Taasan Dadin Namiji ya Taba mace,Tunkafin Wasila ta gama Secondry Sch dinta tagama lalacewa da Harka da maza,sai kuma Tatafi Federal Universty Dutse achan gabadaya Rayuwarta ya kara Gurbacewa,Tazama Yar iskan karfi da yaji,kuma Mamanta ta sani ammh bata taba Cemata Abunda take aikatawa ba Daidai bane,Saboda yadda Rayuwar Bariki tayima Wasila kamun kuku taji bata ma bukatar Aure,domin ita haryanzu bata ga Wanda yayi Mata ba,Kuma bata iskanci Don Kudi No mahaifinta yana da Kudi Daidai gwargwardo Domin dan Siyasaa ne,kawai Tana yi ne Saboda Jin dadinta,Shiyasa suma kannenta Suka bi bayanta Suma ba irin lalacewar da basayi da Sunan Wayewa suyi Shigarsu yadda Suke so,Su kuma yi Abunda Suka ga Dama Mahaifinsu bashi da Abun Cewa Balle yan"uwanshi Wanda Dama Hajiya Kudirat tayi musu Farraqu atsakaninsu Sai dai kallo daga Nesa
Haduwar Wasila Da Abdallah ta samo Asali ne Bikin Wata course Mate Din Wasila,Sunanta Zubaida yar nan Garin Dutse ne,Zatayi Aure kuma Suna good Time da Wasilan,Duk da ita Zubaida Din ba yar Duniya bace irin Wasila,sai kuma akayi sa"a Wani ma"aikacin Costome zata aura kuma Wajen aikinsu Daya da Abdallah anan Portcourt,To Dukkansu sunzo mai Daurin Aure,Itama Wasila tazo,Ta ganshi ne Acikin Jerin abokan ango Sanda Suka Shigo gidan su Zubaida gaida iyayenta,Anan ta kyalla ido ta ganshi da Farko Wasila bata dauka Wani Serious bane,kawai ta Dauka burgeta yayi,sai kuma me Tunda ta koma mkranta takasa zaune da Tsaye akan Abdallah Wanda ko Sunanshi bata sani ba,Barci take Shi take gani Komai take Shi take gani karatun ma Tadaina ganewa,Cikin wannan Hali ta kira Kawarta Zubaida Wacce Aka kaita porthercourt,Tana tambayanta Abdallah ammh sakamakon bata Fadi Suna ba yasa daga Zubaidan har Mijinta suka kasa ganewa,ammh tana yin Misalinshi Nura Mijin Zubaida ya Gane Abdallah ne,domin Shi dabam ne awajen aikinsu,Nombar Wayarshi ya bata ammh bayan ya Sanar da ita Mata basa gaban Abdallah ammh Wasila bata damu.
Tafara kokarin kiranshi ta Waya ammh har Wajen Sati baya daukan Wayarta,Ranar daya amsa kuma Gaisawa kadai Sukayi ya Tambayeta Wacece ita,ta tsayamai Wani Dogon Turanci ya katse kiran bayan ya Bata Hakuri,Wannan Abun yama Wasila Ciwo Wasa,Wasa Ciwon son Abdallah ya kama Wasila mai Tsanani ganin irin Wulakamcin dayake Mata ne gashi yaki Sauraranta tasa Zubaida Ta Turo mata Full adreess Din wajen aikinsu Abdallah na porthercourt sai dai kawai Abdallah ya ganta kwatsam,Akaron Farkon ganinta yaji ya Tsaneta,kuma koda ma tana cikin Jerin irin macen dayake Son Aura bazai taba auran Mace mara aji ba Balle ma kwata kwata bata dace da Ra!ayinshi ba Fata Fata yayi mata bayan yamata koran kare,yasa Security suka Fita da ita,Wannan Abun shi yadasa ma Wasila Alqawarin ko ta Halin kaka sai ta Auri Abdallah ko ta Halin kaka ne,Daganan Bida ta koma Tajema Hajiya Kudirat tana kuka tana Sanar da ita Abunda Ke Faruwa,Ran Hajiya Kudirat ya baci Ta Dinga Huci ita kadai Tana Fadan Duk Duniya bata ga Wanda ya isa Ya Tozarta mata iyalai Ta bari ba ko Zatayi yawo Tsirara sai Ta mallakama Wasila Abdallah atafin Hannunta.
Washegari suka Shirya ita da Wasila suka Nufi acikin Wani kauye A Bida wajen Wani boka wanda ke Zaune awani Tsauni,Sunansa Boka Dandugaji,Aikinshi kamar yanka Wuka da zarar yayi miki aiki To Shikenan kawai,Tun Kafin su isa Aljanunsa sun karantamai komai,Suna Zuwa ya shiga karanta musu ya kuma Tabbatarmusu da su koma nan da Sati daya Abdallah Zai zo da kafarsshi nan yake Fada musu aikin zai bada Wahala saboda akwai Wasu Taurari Guda Uku da Suke Dabaibaye dashi,Masu matukar Hasken,Taurarin Guda biyu Kariyar Addu'an Mahaifinshi ne dana Mahaifiyarshi ke Tare dashi sai Dayan Taurarin da Allah bai bashi ikon ganin ko menene ba,ammh ga Duk alamun Taurarin yafi Haske ajikinshi kuma yayi mai Dabaibayi ne,Wani Al"amari ne Kuma ga Duk alamun Zane ne acikin kadarraransa,bai Fada musu Haka ba, saboda karsu ga gazawarshi,sai dai ya Tabbatar musu da zasu ci galaba akan Abdallah Domin baya Kokarin ibada yana da Sakaci da addu"a ta hakane zasu samu Nasaran yin aiki akanshi,Cike da Farin ciki suka baro Boka bayan Sun Cikashi da kudi.
Aikin Boka yaci Abdallah Domin Ba"a Rufe Sati daya ba,yaji Duk Duniya bashi da Wacce yakeson ganin Wacce ta Wuce Wasila yayi ta Nemanta har yagaji ammh bai Sameta ba,Wayarta kuma yayi ta bugawa bata Dauka ba,sai da ta bashi Wahala kana ta kirashi da kanta,Ranar kuwa ko Minti daya Abdallah bai kara a Porthercourt ba ya Iso Bida da kwatacen da Wasila tamai,sai ga Abdallah Durkushe afalon Su Wasila yana ma Wasila kukan magiyan tasoshi ta Aureshi itakuma tace bazata aureshi ba Tunda ya Wulakantata afarko,Hadda Hajiya kudirat ta Shigon Falon tana mai Tsawa kan yatashi ya Fita bazata tabama Wanda ya Wulakanta mata yarta ba,ammh aikin Asiri ko gizau Abdallah baiyi ba, saima kara Sadda kai dayayi yana ta Rokon Wasila datayimai Rai ta ceci Rayuwarsa,Tace zata aureshi in tana so yaji Dadin Rayuwrshi.
Awannan Ranar dai Wasila bata amsama Abdallah sai ba sai da yayi kwana biyu agarin Bida yana Rokonta kana ta amsamai Ranar kuwa kamar anshashi a ajannah,saboda Murna ganin sun Sameshi ahannu Shikenan kuma kakarsu ta yanke saka,Abdallah bai isa ya tsallake mganar Wasila ko Wuta tace ya taka zai taka,Uwa uba kuma bayason ganin bacin Ranta,yanzunan zai Fita daga cikin Natsuwarsa,Gabadaya Rayuwarsa ta Susuce ko wajen aiki bai cika zama ba,Duk sati yana kan Hanyar,Bida kamar wani Zazzautattace,Yasha kwana agidan Su Wasila bayan ta Ribace Shi Sun Fara aikata masha"a Tun awaje,Ai Wasila bata kara jin Tana son mallakar Abdallah ba Sai Ranar daya kusanceta bayan Ta Nuna bacin Ranta,shi kuma baya son ganin bacin Ran Wasila nan ya Biye mata ya Fara aikata Zina afarkon Tarihin Rayuwarshi,Tunda suka Fara Shikenan suka ji dadi koda yaushe Cikin kusantar Juna suke,Duk da Shi Abdallah yana biyemata ne Domin Baida yarda zai yi,Ga wani karin Abunda ke Damunshi Shine Wasila bata da dadi sex ko kadan bata da Wani Ni"ima,Gatanan dai kawai baisan awani babi zai sakata ba,Kuma bai Taba Nuna mata saboda Wasila ce Sanyin idanuwanshi.
Basu Rufe Wata Biyar da Haduwa ba Rayuwar Wasila ta chanza Domin Abdallah na kashe mata kudi daga Naira daya har Zuwa Miliyoyi,Tuni Wasila ta watsar da karatu ta kama cin Duniyarta da Tsinke,Shi kuma Abdallah gabadaya gida da wajen aikinshi aka ga ya chanza,koda wani lokaci yana wajen Wasila kamar Wani Mijin tace,Bauchi ko Tunda Wasila ta asirceshi bai kara marmarin Zuwa ba,yadaina kiransu akai akai sai dai in sune suka kira sai ya samu wata karya ya lailaya yace Baida lokaci ne ammh yana Tafe.
Wasila ce Tafara bijiro mai da mganar Aure,shi kuma sai bai Tunkari Mallam kai Tsaye ba sai yafara Tunkarar Yusuf da mganar,Yusuf bai kawo komai ba Yaje ma Mallam da mganar,shima baiyi gaddama ba ya kira Abdallah yana Tambayanshi Sunan Mahaifin Wasila,nan kuwa ya sanar dashi,Dayake Mallam yana da Mutane ako"ina ga kuma Tsofaffin dabi"ansa nan da nan Yasa ka akayi mai Binciken Gidansu Wasila sai dai lbrin da"aka Dawomai dashi bamai Dadi bane,Tun daganan Mallam yaji Ransa ya baci da Abdallah ya kirasa awaya yana Fadamai mai ya kaishi Neman Aure a Gidansu Wasila gidan da ba Tarbiya,to ahir dinshi maza yazo nan Bauchi ya Nemi yar Mutumci,Duk Abunda Mallam ya Fada sai da Abdallah ya sanar ma Wasila ita kuma ta sanar ma Hajiya,Ita kuma Washe gari nayi ta Tafi Wajen Boka ta sanar dashi komai,Dariya ya kece mata dashi yace tatashi tatafi za"ayi wannan Auren nan da Wata daya kuma yana bata albishir din Wasila zata mallaki Abadallah kamar Dan tsako atafin hannunta..
Aikuwa haka akayi Domin Abdallah yakara Haukacewa in ba Wasila ba zai iya Mutuwa,afujajan yaje Bauchi yana Sanar da Mallam har abada bazai iya Rabuwa da Wasila ba,har yakai yana tanka in tanka da Mallam,har sai da Hajiya ta Tsinkeshi da mari,Bai kuma sa yayi nadama ba,gabadaya kanshi ya juye haka ya Fita fuu yabar garin yana kara jadadda musu ko Sunki