da na Tsorata Domin Halittarsa ba Abun Sha"awa bane,Wani Wada na gani Kamar an kifeshi da kwarya kanshi kato yana Rinjayar gangar jikinsa,ga Katon ciki ga baki,bashi da kaya ajikinsa sai wani ganye da ya Rufe gabanshi dashi,Akidarshi da kin Shigo bazak yi mgana ba sai ya baki dama,cikin wata katsuwar Murya yace"Meke Tafe Daku..."
Momcy ta gyara Zama tana Fadin"Boka kan mganar yaron nan Dakake Mana aiki akanshi,..'"Katseta yayi da hannu yana Fadin" Kitafi Kai Tsaye Duk munsan da wannan Jawabin Naki.."Yafada yana Zuba mata jajayen idanuwansa kamar gawarshi Wuta,Wasila ta kalli Momcy tana Tabata Tsawa ya daka mata yana Fadin"Ke.."Kya kanki ba"a mana Munafunci anan,Duk Abunda kika aikata Aljanu Suna Lura dake Saboda haka Ki shiga Hankali ki barta tayi mgana da kanta.."Wasila ta Tsorata ammh haka ta dake,Momcy ne ta Rusuna tana Fadin"Amata afuwa Ran Boka ya Dade dama Yaron ne yanzu yakeson Zuwa garin iyayen nashi,toh Shine mukeso Don Allah Boka..."Wata Tsawar ya kara daka musu Wacce ta sakasu Tsorata cikin Wata Firgitattaciyar murya yace"Kul kika kara kiramana Don Allah anan,Don Ubanki kinsan Da Allahn kika zo Wajen mu,Maza ki Tafi kai Tsaye ga bayaninki in kuma kika kara yanzu aljani Tsidugu Zai Raba kanki da gangar jikinki.."Yafada yana Kecewa da Wata Mahaukaciyar Dariya...
Wasila da Momcy Suka Kamkame juna Suna rawan Jiki,Momcy cikin Rawan Murya take Fadin"Amin Afuwa Boka Subutar Harshe ne,.."Hannu ya Dagamata kafin yace"Mgana ta Farko gargadi ne daman,Ina jinki yanzu meku so asake yi mishi.."Jin haka yasa Wasila tace"Muna so ahanashi Zuwa garin gabadaya bayan an Ciremin Sha"awar DuK Abunda ya Danganci Garin.."Shuru yayi ya kura ma Waje Daya Ido kafin ya gyada kai yana Fadin"Wannan karon baza mu taba iya Hanashi Zuwa garin Mahaifansa,tabbas sai yaje.."Yafada yana Zare ido.
Wasila da Momcy Suka Zaro ido bakin Wasila na Rawa tace"Sai yaje kace Boka..? Tafada da Sigar Tambaya ammh da alamar Ficewar Hankali,kai ya gyada mata kafin ya sakarmata idanuwansa yana Fadin"Eh haka nace Tabbas wannan karon Sai Abdallah ya Danganta da Mahaifansa,Dole yaje..."Jin haka yasa Wasila ta Dora hannu akai tana Fadin"Na Shiga uku Boka Don Allah ka hanashi Zuwa,Wlh Zuwarshi Bauchi babban Matsala ce wajena..."...
Wata Dariya yakece dashi kafin yace"Baki Shiga uku ba Tunda kika Kawonana kukanki,Na sanar daku Tun abaya Iyayen yaron Suna tsaye akanshi ba Dare ba Rana,Ko alokacin Aurenku dana Turama mahaifin yaron Aljanu sai dawomin yayi Duk jikinsa Rauni bai samu Nasaran Rabanshi ba Saboda Mutum ne mai Riko da Ibada da kuma yawaita karatun alQur"ani ko Shima yaron mun samu Nasara akanshi ne Saboda yana da Sakaci da ibada kuma baya Addu"a..."Gyada kai Sukayi basu Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin.
"Aljanun dana Turama Abdallah wanda yake Nesantashi da Garin Bauchi da kuma Abunda ya Shafi ahalinsa yanzu haka yafara jigata,Domin addu'o'in da iyayensa Suke masa,yana Zuwa garesa,..Dama na Fada muku Afarkon Zuwanku zamu aiki akan Abdallah ammh kuma Zai dinga warwarewa Lokaci bayan Lokaci Saboda yana da Wasu Taurari Guda uku wanda Suke da Matukar Tasiri akanshi,Saboda Abdallah Zai Tafi Ga Mahaifansa Dole sai yaje..."Yafada cike da Tsaawa.
Wasila da Ta fara hawaye tace"Boka ta min Rai kahana Abdallah Zuwa,wlh in yaje rabani dashi zasuyi.."Wata Shegiyar Dariya ya saka yana Fadin"Ai indai kin yarda da aikinmu Dole zai Dawo gareki bazai taba iya Rayuwa baki ba,Mune fa muka Sanya yake zaune Dake haryanzu ammh Abdallah baitaba Sonki ba,Mace irinki ma bataba Burgeki ba,Mune muke Dauke da Duka Gundin zaman Atare da Abdallah,Kuma Tunda kikaji nace Sai yaje Toh Zuwanshi Shine Mafita.."
Wasila da jikinta kaf ya jike da Zufa,ta kalli Momcy tana Neman saka mata kuka,ganin haka yasa Momcy tace"Boka kadai Taimaka mana,Yanzu ba wata hanya da za hanashi Zuwa.."Cike da Jin Haushi ya Daki Kwaryar dake gabanshi sai da Ta Fashe cikin karaji da Tsawa yace"Nace bazai Yuyu ba ko..? Indan kuka matsa Toh komai naku zai lalace,in nace lalacewa ina Nufin Abdallah zai sakeki kuma ya koreki daga gidanshi bayan kuma ya Wulakantaki ya Tozartaki aidon Duniya Daga karshe Ki Haukace Saboda Abunda kikayi ya koma kanki..."Yafada yana Sakarmusu jajayen idanuwansu.
Zaro ido sukayi atare Kafin su Samu Zarafin mgana ya Daga musu hannu yana Fadin"ku tashi ku Tafi..Kada ku Dawo sai bayan ya Dawo daga Bauchi lokacin ne zamu sake sabon aiki..Ku tashi ku Fita Lokacinku ya kare..."Yafada yana Nuna musu Hanya,da hanzari Suka Mike Momcy ce kema Boka godiya kafin Wasila ta damko Kudi acikin jakarta Ta Zubesu anan Suka Fita Jikinsu na Rawa da jin Abunda Boka Dandugaji yace.
Akwai Tafiya tsakanin inda Sukayi parking da inda Bukar boka suke Saboda Halin da Suke ciki ba wanda yama Dan"uwansa mgana,Wasila ko Tafe Take,kamar wacce Akace tarasa Uwa da uba,koda ganin yadda Fuskarta ya bayyana tashin Hankali kara kara,Har Suka isa wajen Motarsu Wasila ta Wurgama momcy key din ta na Fadin"Ban iya janmu Momcy kaina Saramin yake..",
Batayi mgana ta chabe Key din ta Shiga bangaren Direba ta Tada motar Suka Fara Fita daga Dajin sai da Suka Fita kwalta, kana Momcy ta kalli Wasila wacce ta jingina kanta ajikin Cussion din Kujeran motan Hannunta na Dafe da kanta,Cikin wani yanayi Momcy tace"Plz Wasila cool down...,kada ki Tada hankali kindai ji Abunda Boka yace ko? Toh gaggawa ga banamu bane.."Ido Wasila ta Bude wadanda Suka Kada sukayi jajir tace"Ya zanyi momcy... ?Bazan iya juran Rasa Abdallah ba inajin Tsoron Shegun iyayen nashi,kada su Rabashi dashi har Abada.."Momcy tace"Basu isa ba Wasila,Da zarar ya dawo Ki Zo mu koma wajen Boka Mu ji Abunda zai cema,kinji yace zai sake Sabon aiki akanshi.."Runtse ido Wasila tayi Tana Furzan Da Numfashi take Fadin"Zuciyata Zafi take,Ni Bauchin ne da naji an ambata sai yanayi na ya Chanza,Allah na gani bana Kaunar naga Abdallah yarabi wani bayan ni da Abunda na yarda dashi.."Tsaki Momcy taja tana Fadin"Owk Kenan kin Shirya Abdallah ya koreki kenan ko? Ko kuma kin Shirya tababbata cikin Hauka na har abada Bisamillah.."Jin haka yasa Wasila tayi Saurin Cewa"A"a Momcy Na bari Wlh..."Kai ta gyada tana Fadin"Better...'kafin ta Maida hankalinta Bisa kwalta Daidai lokacin Datake Duba agogon Fatan dake Hannunta Taga karfe 3:24pm na yammah.
***************
*Dutse*
Yau ta kama Alhamis ne,Aikin dare gareta,karfe 6 na yamah tayi Shirin Tafiya,kuma ayau din take so ta ma Abba mgana kan mganar Tafiyarta Bauchi gobe takoson Tafiya Tun Har Ranar Sunday bata da Duty,Sai da ta Shirya zata Tafi Asibtin ta Shiga Falon Abba yau din tayi Sa"a Umma batanan taje biki kuma bata Dawo da Wuri ba.
Har kasa ta Duka tana Gaida Abba kafin ya amsa cikin Sakin Fuska,Kanta na kasa take Fadin"Dama Abba ina so naje Bauchi gobe ne,Shine nace bari na Sanar dakai.."Shuru yayi yana kallonta kafin yace"Bauchi..? Anyi Wani Abu ne..?Kai ta girgiza kafin tace"Hajiya ce batajin dadi zan Je na Duba.."Kai ya gyada kafin yace"Aikin ki fa,Kindai san ko ma"aikatan lafiya Koda yaushe Cikin Taimako kuke.."Kanta na kasa tace"Nasani Abba,Ai Ranar Lahadi zan dawo monday ina da aiki.."Jinjina kai yayi yana Fadin"Toh Shikenan Allah ya kaimu ya kuma kaiki lafiya.."Da Ameen ta amsa cike da jin dadi Kafin tamai sallama ta Fito Cike da Murna,Tayi waje Ranta Fari tas Da murnan Gobe sai Bauchin yakubu.
Wajen Ammi ta biya ta Fadamata kafin ta Wuce wajen aiki,har Ammi na Fadin da domin gobe zatayi sammako Zuwa jigawa ba wajen kanwarta data Haihuwa ba da Sun Tafi tare,ko a Asibiti Kowa yaga Asma"u yasan tana cikin Farinciki Saboda yadda Abun yakasa boyuwa bisa kyayawan Fuskarta.
*Janafty...*
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
Sai around 8am ta baro asibitin dayake sai da Suka tsaya Sukayi Round din safe,Cike da Farinciki ma"u sukayi sallama da Sister Bahijjah,Banki ta fara biyawa ta cire kudi daganan kasuwa ta Wuce Ta siyanma Su Fati tsaraba,ko Bauchin bata kira ba so take ta basu Suprise,Tana Adaidaita zata koma gida ta kira Aisha awaya tana Fadamata Yanzu zata tafi Bauchi.
Bata Fuska Aisha tayi tana fadin Asma"u bata kyauta mata ba,Da bata fadamata Tunda Wuri ba,data Shirya Sun Tafi tare,Cike da Dariya Asma"u ke Fadin kibarma wa mijin naki da kuma my Son..? cike da Shagwaba Aisha tace Su zauna Su kadai mana Rabin Raina,Jin haka yasa Asma"u yin dariya sanin wacece Aisha,kafin suyi sallama sai da Aisha tayi ta jaddama Asma"u ta isar da gaisuwanta wajen Mama,da su Hajiya.
Koda ta Shiga gidansu bata iske kowa atsakar gidan ba,Dakin su Baba lami ta leka suka gaisa,Nan take sanar da ita yanzu zata tafi Bauchi baki Baba lami ta washe tana Fadin"Ehe yau ma"u sai kwananan dakin Mama ko.."Asma"u na dariya tace"Sosai ma Baba lami,bari naje na Shirya kada nayi dare ahanya ba,da dadewa zanyi ba Ranar Sunday zan dawo.."
Gyada kai Baba lami tayi tana Fadin"Gaskiya kam,hanzarta kada Rana tayi.."Kofar dakinta ta isa bayan tasa makulli ta bude,ta Shiga da sallama tana kwabe hijabin gidan dake jikinta,Tiolet dinta ta Fada bata ma tsaya neman Ruwan zafi ba ta tara Ruwa afomfon dake Bayin ta Cikashi da Ruwa kafin ta Tube tayi wanka agurguje ta Fito Fuskarta kadai in ka kallah zaka san Asma"u na cikin Farinciki.
Good 1hr Yabata ta kamallah Duka Shirye Shiryenta,Ta Zuba kayanta akaramar akwatinta Kala Uku,sai kayan barcinta da Dan Abunda zata bukata ita kuma ta Shirya Cikin wata Doguwar Rigar Atamfa wanda Ammi ta dinka musu sanda Aisha ta Haihuwa mai kalan orange da Brown,Mayafinta ta sanya brown babba,Fuskarta ba wani makeup dama ita ba ma"abociyar kwalliya bace.
Jakar hannu ta Dauka baka ta kuma sanya Wani Flat Shoe dinta baki,Sai da ta Kauda komai ta kashe Wutar dakin kana ta Jawo karamar Trolley dinta da hannun hagu,hannun damarta kuwa tana dauke da karamar Jakarta da kuma wayarta Ta Fito Fuskarta na bayyanar da Annuri.
Umma ce da Mama ke Tsarkan gidan,Umma ce ke kofar dakin Hajiya iya atsaye da alama suna mgana ita kuma Mama ta coge akofar dakinta Tana kallon Umma kamar dai wata mgana ce ta hadasu,cike da mamaki Suke bin Ma"u da kallo ganin ta Ijiye akwatin tana kulle Kofar dakinta da makulli,Galala suke kallonta musamman ma Umma,don ita mama Sau daya ta kalleta ta kauda kai,ita ko Umma kallon Kurillah tabi Asma"un dashi ganinta yau Cikin walwalwarta.
Basu samu zarafin mgana ba Asma"u tagama kulle dakinta ta waigo tana Riko akwatinta gefe daya tana gyara zaman mayafin kanta,Hakoranta duka Suna waje take Fadin"Umma,Mama zan tafi Bauchi...'
Mama ce tace!"Ayyah Allah ya kiyaye hanya.."Fuskarta bata Nuna Me Zuciyarta ke Ciki ba,Umma ko ido ta kwalalo tana fadn"Bauchi kuma..? Asma"u bata bi ta kanta ba tace"Eh,Anty amarya batanan ne.."Bata samu amsa ba Hajiya iya Ta Fito daga dakinta tana Fadin"Waye nake jin ana zai Tafi Bauchi kuma...?Umma tace"Wai Asma"u gatanan ta Fito ma..."
Kallonta Hajiya iya tayi Shekeke kafin tace"Bauchi kuma.. ? Toh da izinin wa zaki Tafi..."Abba da Shigowarshi kenan yace"Da izinina Iya,Jiya take Sanar dani tana So taje akwai wanda ba lafiya ne,ba dadewa zatayi ba Ranar Lahadi zata dawo.."Yafada yana kallon Hajiya iya wacce ta wani mele baki tana Fadin"Sai ta dawo Tunda kai ka Daure mata gindin gantali Agari,Mutum bazai ma kanshi Fada,Sa'o'inshi da kannenshi Sun gama kammaluwa agidan Aure,Allah dai ya Sauwake Wlh..."Tafada tana komawa daki .
Mirmishin yake Asma"u ta saki aranta tana jin bazata bari Hajiya iya Ta bata mata Mood dinta na Farinciki ba,Kallo Abba tayi tana Fadin"Abba zan Wuce bana son nayi dare ahanya.."Gyada kai yana Fadin"Gaskiya ne Ma"u Duk inda zakaje katafi ido na ganin ido,karbi kiyi na mota,kinji dai yadda mukayi dake kidawo Ranar lahadi na barki ne Saboda kin Dade bakije ba.."
Girgiza kai tayi tana Fadin"Toh Abba,ammh kabar kudinka ina da Mota.."Kallonta yayi yana Fadin"Karbi mana,.."Jin haka yasa ta sa hannu bibbiyu ta karba tana mai godiya,Wucewa yayi yana Fadin"Allah ya kaiki lafiya ki dai Habiban.."da Toh ta amsa kafin ta Dauki akwatinta ta kama hanyar Waje,saboda Su Baba lami basu nan Sun Tafi garinsu,hassatu ce kadai,kuma kamar Mama ta aiketa,Umma dake Binta da kallo haka kurum takejin gabanta na Faduwa ta rasa Dalili yanzu Asma"u kwarjini take mata Sosai.
Bata tafi ba sai da Ta Shiga wajen Ammi ta Mata sallama,ita kuma ta bada Sakon Fulawa da garin Danwake Akaima Mama,har kofar gida ta rako Asma"u ta mata Allah ya kiyaye,Tana Zuwa bakin Titi ta samu Adaidaita ta Shiga sai Tasha,tana zuwa ta samu Motar Bauchi Diret sau ra Mutun Hudu ta cika,Ansa Akwatinta abayan Mota kenan Aisha ta kirata awaya tana Tambayanta tana ina,tace tana Tasha yanzu zata Wuce,Tace ta dan Jira ga Fahad nan Zuwa zai kawo mata Sako zata kaima Su Mama,Mirmishi tayi Aranta tana yaba Kyan Hali irin na Uwa da yarta.
Minti Ashirin sai ga Fahad yazo Tashan Dambum Nama ne Dayawa anyi Raping dinshi Cikin wata Leda kafin ta sanyashi Cikin wani karamin Botiki kuma Bai barta haka ba Sai da ya bata 4k yace ta kara Na mota tasan ko tace bazata karba ba bata baki ne ta karba tana mai Godiya Suna wajen aka samun Cikon Mutum ukun Sai da Motarsu tatashi kana Fahad ya Shiga motarshi ya Juyo Zuwa gida.
Suna Fita daga garin Dutse Asma"u ta kalli agogon Fatan dake hannunta taga 11:06Am daidai Mai da kanta tayi kan Littafin Azkar din dake hannunta tana karantawa cikin Ranta tana Fatan Allah ya kaisu lafiya,ammh yau da Ta Tuna sai kwanan Bauchi sai taji Farinciki yaki Barinta,Allah na gani Duk sanda ta Shiga mota Zata Bauchi tana Tsintar kanta Cikin Farinciki ammh kuma wannan karon Sai Murnanta yafi na ko yaushe kodon Ta dade bata je ba ne.
****************.
Wasila kuwa Tunda suka dawo daga Gidan boka take kwance Adaki Zuciyarta kamar zata buga Saboda bakinciki Data Tuna Cewa Buga yace sai Abdallah yaje Bauchi Zataji kamar Tayi Bindiga ita kadai,Arayuwarta bata kaunar taga wani ya Rabi Abdallah Saboda Son datakema Abdallah Wlh Zata iya kashe Rai Saboda Shi,Tun momcy na bata baki hartazo ta Fita batunta,Har Washegaru Wasila Sukuku take Abunda ma ya sanyayamata Rai Suna waya da Abadallah ammh bai Nuna mata alamun Zaije Bauchi ba,Su kuma Su Jamila Sun Fadamata Tun Safe yake Fita baya dawowa sai Tsakar dare Wani lokacin.
Ita kuma data Tambayeshi sai yace mata Wlh busy yake zama a office Saboda kwananan Akwai cases dayawa ne,Toh Wasila dama Tafi yarda Da Abdallah shiyasa ta watsar da Batunsu Jamila,ta yarda Dana Abdallah,Shiko Tun safe in ya Fita zai biya wajen Polina su Sheke ayarsu a office din ma ba Sosai yake zama yana gidanta chan yake Raba dare,Dalilin dayasa yake Dawowa ma Saboda Su Jamila ne,ya Lura yaran Munafukai tsab zasuyi kaima Wasila lbri,in ko Wasila taji lbri baya kwana agida Sai ya Raina kanshi.
Itako Polina sai tayi ta Ribanta da salo kala kala Sabida karya tafi dayace zai Tafi sai tafaramai kuka tana Makaleshi dakyar yake samun Damar tahowa itako Polina Duk burinta bai Wuce ta Raba Abdallah da matarsa Wasila ba,Domin Ta lura yana Sonta Sosai komai kaji yace My Wasi ko Noory,ko ita baya Sonta haka,Shine ta tattara Duka burinta na sai ta Rabasu Wlh Domin itama Abdallah ita kadai takeson Mallakanshi Saboda Shi ta daina bariki,Saboda ya mayeta gurbin iyaye da yan"uwa Shi amatsayin Zaratan goma ne,Ta yardan ma kanta Abdallah 1 in Town Ne.
***** ***** ******
*BAUCHI*
Misalin karfe 4 na yammah Suka iso tashar Bauchi Tunda Asma"u ta Shaki iskar bauchi walwalarta ya karu daga Tasha,Mai adaidaita Ta dauka daganan sai gidan kakanininta,dayake Irin Family house,kowa ya tashi sai dai yaja barayinsa yayi gini.Duk da iyayensu sun Rasu ammh kawu wanda ya Rike Mamanta yana nan da Ranshi,sai dai Suka ganta kwatsam ta Shigo haka Suka zagayeta matan kannen mama,da yaransu suna mata barka da Zuwa,kowa sai mamakin ganinta yake da yarda ta zama,Sallah kawai tayi adakin Jummai matar kawu,ko abinci ta kasa ci ta kosa isa gidan Mamanta tsaraban yaran gidan ta Diban musu,ta mike tace zata karisa Federal Lowcost,Jummai tayi tayi ta tsaya ta jira kawun ya dawo tace Sai dai ta dawo gobe,Dole ta kyaleta tatafi,Wani mai Adaidaitan ta samu ya Dauketa Direct sai Federal lowcost bai Direta ko"ina ba sai abakin katon gidan Proff,wanda ya kawatau da wani Tamgamemen get mai kyau dana Tsari.
Cike da Farinciki ta biya mai ADaidaitan Kudinshi ta Dumfari get din gidan tana Rike da akwatinta,Get din ta buga kafin mai gadi ya leko yana Tambayan wacece tace Asma"u ce,bai ganeta ba Don Duk ta chanza tsaya yayi yana kallonta Mirmishi tamai tana Fadin Asma"u ta Dutse ne,ware ido yayi yana dariya kafin ya Bude mata kofar ta Shigo yana mata barka da Zuwa dayake Tun wanchan Zuwa Sun saba dashi sosai.
Tashigo Haraban gidan kenan taci karo da Fati da Mahamud,sun Fito Da Kayan islamiyansu ajikinsu,Mamam Direba yashiga mota Zai kaisu,Fati ce ta fara ganinta ta Zaro ido ta yarda jakarta ta Rugo da gudu tana Fadin"Anty Asma,"u OyoyO Oyoyo,..."Take Fada tana Kamkameta har jakar hannunta na Fadi Rikota Asma"u tayi tana dariya Shima mahamud Gudun ya kwaso yazo ya Rumgumeta suna ihun murna ga Anty Asma"u tazo,Tana dariya Fatinciki yaki Barin Fuskarta,Akwatinta Fati taja Shi kuma mahamud ya karbi jakar hannunta Sukayi Cikin gida da Gudu,Tabisu da kallo tana Dariya,Mamman ne yake gaisheta ta waiga Tana amswa Shima harda Zolayanta wai lalle Bauchi nada manyan baki,Dariya kawai tamai Ta Nufi koridon da sadata da Cikin Babban Falon gidan.
Anty Safina da Anty Nafi ce ke Zaune a babban Falo Suna hira sai ga Fati da Mahamud Sun Shigo Suna ihu murnan ga Anty Asma"u nan,Anty Nafu ce tace"Wata Asma"u kuma..? Fati yar Shekara Tara tace"Anty ma"un jigawa.."Anty Safina zatayi mgana kenan sai ga Maman Fati ta Fito daga kichen tana Fadin"Wai hayaniyar me nake ji ne.."?,Da gudu Mahamud yatafi wajenta yana Nuna mata jakar Asma"u yana Fadin"Mama Anty Asma"u ce tazo..",Kallonsa tayi Cike da mamaki tana Fadin"Wata Asma"un karya ne.."Asma"u data Sawo kanta Falo tana Fadin"Ba karya bane Mama.."Tafada tana Dariya Zaro ido Anty Nafi da Anty Safina sukayi suka kuma hada baki wajen Fadin"Asma"u...Ikon Allah wlh Ma'u maman Fati.."Suka fada Suna dariya,Dukkansu suka taso Suka Rumgumeta suna Murnan Zuwanta.
Janta Sukayi kan Kujera cike da Murna Maman Fati ko baki yaki Rufuwa cikin Murna tace"Ma"u yanzu kike tafe,baki yi ko waya kin sanar kina hanya ba.."Mirmishi tayi kafin tace"Mamaki nakeson Baku Mama.."Anty Nafi tace"Aiko kin bamu mugun mamaki ma Ma"u wai yaushe Rabonki da gidannan,kinsan jiya muke zencenki Nida Hajiya.."Asma"U tace"Allah sarki Hajiya,Ita nazo Dubawa wlh Tunda mukayi waya da mama take sanar dani jiki yaki dadi,na kudurirta insha Allahu karshen Sati zan zo In Dubata,ya jikin Nata.."?
Basu zarafin mgana ba Hajiya ta Fito daga Falonta tana Fadin"Nafi hayaniyar suwa nakeji haka ne,Su fati basu Wuce mktanta bane..? Tafada tana Tsaye akofar Shashenta kallo daya zakamata ka fahimci Ciwo na Cinta Saboda yadda Duk Ta rame,ido ta Zaro tana bin Asma"U da kallo batayi mgana ba Anty Safina tace"Wlh Hajiya hayaniyar Murna Zuwan Asma"u muke gatanan yanzu take tafe.."Hajiya ta kariso tana Fadin"Ikon Allah Ma"u...Taho taho diyar albarka jiya nake zencenki ashe kina Tafe.."Da hanzari Ma"U ta mike Ta fada Jikin hajiya Suka Rumgume juna,Asma"u ta dago tana kallon Hajiya tana Fadin"Sannu hajiya ya jikin ki? meke damunki yanzu."Hajiya ta Dafa kafadan Asma"u tace"Naji sauki Ma"u kawai Ciwon kai ne ke Damuna yanzu.."
Kwabe Fuska Asma"u tayi alamar Damuwa tana Fadin"Hajiya jinin ke ne ke kara sama,shiyasa kike Fama da Ciwon kai,Da zarar kin Rage Shiga damuwa da Tunanin mai Zurfi jininki zai yi kasaa yakoma Normal har Ciwon kan yatafi kina Shan mgani kuwa..? Mirmishin dayafi kuka Ciwo Hajiya Tayi kafin tace"Hakane Ma"U ina Sha,Allah dai ya nuna mana iyakar Abun,ammh dai sai kinyi Wata zaki koma ko.."
Dariya Asma"u tayi kafin tace"Naso haka hajiya,ammj Saboda aikina Ranar Lahadi zan Tafi.."Bata Fuska hajiya tayi kan tace"Kai wai meyasa Mallam bai Neman ma Ma"u aiki anan garin bane.."Gabadaya Falon Suka saka mata dariya,itama dariyan tayi tama kamo Hannu Ma!u suka karisa ga kujera suka Zauna tana Fadin"Fati da mahamud maza ku Shigarma da Ma"u kayanta Shashena Duk inda akaje ko Jikoki Ma"u masaukinta na dakiNa.."Nan ma Dariya Suka sakamata Su AntY Safina na jin Dadin yadda Zuwan Asma"u ya saka hajiya ta saki jiki.
Fati ko da Mahamud da Hanzari Suka ja kayan Asma"`u zuwa Shashen Hajiya har Suna Fada,Su hajiya suka bisu da Dariya nan Mama ta kawo mata abinci tana ci Suna hira nan take Tambayan Mallam,Hajiya tace ya Shiga mkranta,Sai da tagama cin abinci ta natsa kana ta Shiga Shashen Hajiya ta Bude jakarta ta Fito da Sakon Ammi dana Aisha tabama su Hajiya Suka karba Suna godiya nan aka Bude Dambun Naman ana ci ana Hira,babban Abun Farinciki Shine Zuwan Asma"u yazo da Farinciki dadama Tunda ga Hajiya ta warware ta Shiga cikinsu anata Hirar Duniya,ko Su Fati basu samu Zuwa islamiyan ba Tunda Suka ga Ma"u.
Gabda mangariba sai ga Mallam yadawo,yayi mamaki jiyo hirarrakinsu Tunda Ga haraban gidan,sanin dayayi Tunda Hajiya ta Farama sama kanta damuwa gidan yazama wani Shiri,Cikin mamaki ya sawo kanshi Falon yana sallama sai dai Tambayanshi ta Tsaya da ganin Asma"u Shima yayi mamakin ganinta,nan Suka gaisa yana mata barka da Zuwa haryanama Hajiya Tsiyan Taga Yarta ta warware ko,shima Daga ganin Walwalwar Hajiya yafi komai Yimai Dadi koda bai Furta ba,Shashensa ya Wuce Mama ta bi bayanshi ta bar Su hajiya anan Falon.
Kosu Anty Nafisa Dare kowacce Mijinta yazo ya Daukesu suka koma gida,Rans kal na ganin Hajiya ta Fara Dawowa cikin walwalarta,Ranar Maman Fati keda Miji,shiyasa da Wuri Asma"u Suka Shige Daki ita da Hajiya,da Farko dayan bedroom din ta Shiga,dayske kowacce tana da babban Falo da Bedroom guda biyu kowanne kuma da Bayi,Kichen kadai Suke da guda daya wanda ke Babban Falon gidan Gabadaya.
Hajiya ta Hanata tace tadawo Dakinta Su Dinga kwana,Haka ko akayi,Ranar kusan 12 suka kai Suna hira da Hajiya da Asma"`u kafin barci ya kama Hajiya,Wajen 2pm na dare ta Farka nan ta Iske Asma"u na sallah ita ma bata koma ba ta mike ta Shiga Tiolet da Dauro alwala tazo ta Jera da Asma"u tada sallah,sai wajen 4 asuba kana Suka idar kowa ya Daga hannu sama yana Rokon Allah Bukatunsu,Hajiya ko kallo Asma"u take tana yabawa da Natsuwar yarinya tare da Hankali,da kanta ta karama Hajiya wajen kwanciya tace tataso in ta idar da addu"ar,Ta koma ta Kwanta Saboda lalurata,koda ta kwanata da kanta Ma"u ta Lullubeta da Bargo,kafin ta koma ta Zauna kan Darduma bayan Ta bude karatun alQur"anin dake Cikin wayarta Tafara karantawa Cikin Siririyar muryanta mai Cike da gardi da Dadi,
Kuramata ido Hajiya tayi Sha"awarta na kamata tare da Sha"awar Ina ma ace yau Asma"u yarta ce ta Cikinta datafi kowa murna gaskiya Duk Namijin daya samu Mace kamarta yagama Morewa,Haka kuma Duk Surukar data sameta amtsayin Suruka ta Godema Allah,Har aranta tana ji Da"ace tana da wani D'a bayan Baffa da sai ta nema mai Asma"u ko kuma Da"ace tana da wani kani ko wa,wlh bazata taba bari Ma"u ta Subuce musu ba.
Tun tana Sauraran Karatun Nata Har Barci ya Fara Daukanta batasan Sadda ta idar da karatun ba ita dai lokacin da Aka fara Sallar awasu masallatai ne Ta Farka ta iske Asma"`un tana Sallah,Jikinta asake ta Sauko daga kan gadon Tafada Tiolet tana kallon Asma"u Aranta tana Fadin"anya Wannan yarinyar Na barci kuwa.."Take Fada acikin Ranta kafin ta Yi tsarki ta Dauro alwala ta Fito tana jikinta yamata Dadi,ciwon kan ma ya Lafata Tunda ta Samu barci.
*Janafty..*
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
Koda Suka idar da Sallar Asuban Ma Matsama Hajiya tayi saida ta koma barci,ita kuma sai da ta gama Azkar Dinta kafin ta Tashi bayan ta Sanya karamin Hijabinta Datazo dashi acikin kayanta,Ta Fita Zuwa babban Falo,babu kowa sai dai taji motsi a kichen haka yasa ta gane Mamanta ne Ke aiki,da hanzari ta karisa kichen din tana Mai Maman Fati Sallama,wacce ke ta Faman Soya kwai,hade da Dankalin Turawa.
Waigowa tayi tana amsawa lokaci Daya Ta washe baki tace!A"a Ma"u,Harkun tashi,ya hajiya ta kwana da jikin..? Asma"u na karisawa gareta take Fadin"Ina kwana Mama,Hajiya taji Sauki Don ta matsa mata tayi barcI Sosai yanzu hakama na Sata ta koma.."Cike da Farinciki Maman Fati tace!Masha Allah naji Dadi Sosai Ma"u,.."
Asma"u Ta kada kai tana Fadin"Toh ai dama Mama koda Hajiya na Shan mganin Hawan Jini,matukar