An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
E-Book by Bro Sardaunah
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
*Bismillahir rahamanir Rahim*
_*GARGADI:BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYAMIN LBRINA BA,WANNAN LBRIN MALLAKINA NE,BAN YARDA A SARRAFASHI TA KOWACCE SIGA BA,YIN HAKA ZAI SA A HADU DA FUSHIN HUKUMA*_๐โ
_I Dedicate Dis 1st page To u my Friends 4evrer...๐ซ๐ฌ *AHMED MUSA* ๐And u *JABIR ABUBAKAR* ๐ Tanque Dudes..Tanque For ur Advice_๐
*Free page* 0โฃ1โฃ
_DUTSE-Jigawa_
......."Misalin Karfe 2:30pm Na daren Ranar Monday,Litini kenan acikin anguwar Gida Sittin,Sautin karan Alamar din data Saitashi acikin wayarta Wanda ke Tashinta Duk Dare,shine yafara Bugawa Ajikin wayarta Dake Kan wata karamar Dirowa dake Gefen Katifarta
Cikin Natsuwa ta Farka Tare da mika,kafin Ta Zuro da duka kafafunta Waje,Wayar ta Fara Dauka ta kashe alamar din kafin tayi amfani da wayar wajen Haska dakin Sakamakon ko"ina ya dau Duhu Dumdim ,Nepa sun Dauke Wuta Tun kafin ta kwanta, gen kuma tana Tunanin Mai ya kare ya kashe kanshi,da Hasken Fitilan wayarta tayi amfani ta haska har ta Dangana da Tiolet din dake Dakin Tarki ta Farayi kafin ta Dauro alwala ta Fito tana Tsane Ruwan Fuskarta da hannunta,Kai tsaye Dirowan dake Manne da Katifarta ta Nufa inda ta Dauki Dardumanta ta Shmfidata agabas,hijabinta Shima dake Ninke awajen ta Dauka ta Saka Wanda yakai mata har kasa,daga gani ta ijiyeshi ne Domin ibadarta,wayar Hannunta ta ijiye a gefenta,Gabas ta kallah kafin Ta daidaita Natsuwarta Ta Tada Sallah.
Sai tayi Raka"a Goma,sai kuma tayi Shafa"i da Wuturi Raka"a Uku kafin ta Sallame,Cikin Natsuwa ta kalmashe kafarta Ta sanya yatsun Hannunta tana kirga dashi,Ba"a ganin Fuskarta Saboda Dakin yana Da Duhu sai dai ana iya ganin Inuwarta,Cikin hakane Ta Daga Hannayenta Sama tana Kwararoma Allah kirari _Ya Allah Don Girmanka da Isarka Don Mulkinka..Ya Allah Don Gudurinka Ya Mahaliccin Samai da kasa,Kaine kake Umartan Abu yafaru kuma ya Faru Nan take,Ya Allah kaine Gatan kowani Bawa kai ka Umarci kifi daya Hadiye Annabi Yunusa,kai kuma ka Umarci Wuta Data zama Salama ga Annabi Ibarahimu,Kai ne Shugaban Halittun Duniya,kai Ubangijin Annabinmu Muhammed Salallahu alaihi Wasallam,Yakai mai Sunaye Guda 99 Da Tara Nayi Tawasalli dasu ya Allah na sani kana sane dani baka kuma Manta dani,Kai ne kake bawa Wanda kaso arziki ko wani kawan Duniya ka kuma hana Wanda kaso ba don baka son Shi Ba sai don Jaraba imaninsa,Kai kuma kai Aurar da wanda kaso,ka hana wanda kaso,ka azurta wanda kaso ka Hana wanda kaso..Ya Allah na karbi Kadarrata hannu bibbiyu Allah ina Rokon ka Sanya Jinkirina ya Zama alheri Allah ka Bani Miji na gari wanda Zai Soni Tsakani ga Allah,wanda zaiji kaina ya Mutumtani dani da iyayena Gabadaya..Ya..Allah...Ya.Allah.."_
Take Fada kuka na cinta kafin Ta kife Fuskarta da Duka Hannayenta tana Sakin Shesshekan kuka mai Cin rai,sai da tayi ya Isheta kafin ta Dago Fuskarta Bayan ta Share Hawayenta,Wayarta ta Dauka ta Duba taga 5 Saura na asuba da Hanzari ta Mike Ta Cire Hijabin jikinta ta Ninkeshi tare da Sallayan ta Maidashi inda ta Daukoshi Tana Kokarin Fitowa Daga Dakin, Sai ga Nepa sun Dawo da Wuta kau kamar Rana,ajiyar Zuciya ta Sauke sai alokacin na dago ina kallonta Yar Matashiyar Budurwa Ce Wacce akallah zata kai Shekara 26 aduniya Fara ce Doguwa,mai Dauke da Dogon Hanci tana da Fadin Fuska ammh ba Sosai sai bakinta daya kasance yana da Fadi kadan,daga gefe da gefe kuma ya Tsuke kanshi,Akallon Farko in kayi mata zaka Fahimci Tana da Dirin Mata,domin kirjinta ne ya bayyana cikin kayan Barcin dake Jikinta Riga da Wando,Kanta na Sanye cikin Wata Hula mai Raga raga kamar ta Sakan Zare,wanda Har ana Iya Hango Kitson kalaban data Hadesu Waje Daya ta Dauresu da Band,Yanayin yadda kan natayi ne zai sa ka Fahimci tana da Yalwar Sumar gashin kai.
*ASMA"U LADAN SHARIFF* Kenan Tana cikin Jerin ya"yana Na Uku acikin Jerin ya"yansa goma da Allah yabasa,ma"akaciyar asibitice waccce ke aiki ababban asibitin Jahar Dutse
Cikin Hanzari Ta koma cikin karamin Tiolet din dake Cikin dakin Ta Jona Kettle dinta bayan ta Cikashi da Ruwa,cikin daki ta Dawo ta Bude wani karamin Wardrope dinta mai kofa Biyu ta Dauki Wani Hijabi Fari mai Kwalliyan Leshi Daga kasa wanda ake Kira Breziya Hijab,Ta sanya shi Saman kayan Barci ta,batare data Tsaya komai ba ta Isa ga kofar Dakinta ta Zare sakata bayan ta Zura wani Takalminta mai soso ammh yana da Tudu kadan.
Koda ta Fito Tsakar gidan nasu yana da Duhu ita ta saka Hannu ta kunna makunnin Wutan Sai ga Haske ya gauraye Wajen,Bin katon Tsakar Gidan Nake da kallo Wanda yaji interlock ta ko"ina,Daga barayin Inda Jerin Dakinta yake Wasu Kofofine Guda uku wadanda Ke Jere da Juna,Na farkon Dakin Uwargida ce Wato Ummah,sai na biyun Dakin Mai Bi mata Wato Mama sai na Ukun Dakin Ta karshe ce Wacce Suke Kira Anty Amarya,Dukkansu kowacce tana da Makeken Falo ne da kuma 2 bedroom aciki bayan kowanne na Dauke da bayinsa,sai daga gabas kuma Wani Shashe mai girma Wanda nan ne Shashen Abba,sai daga Nesa yammah Shima wani daki ne Wanda nan ne Dakin Hajiya Iya kakarsu kenan,sai daga chan Nesa kuma Wani katon madafi ne ma"ana kichen, wanda kusa dashi Dakin masu aikinsu ne,Sai Kuma wani korido wanda zai Sada ka da Shashen Rijiya Daga baya kuma inda Bayinsu na waje yake,in kuma ka Mike zaka Fita ne Haraban Gidan inda yake kawace da Filawoyi masu ban Sha"awa Gefe kuma Parking Space ne inda ake Adana Motoci,gasunan ma Guda Uku suna Fake awajen,sai Daga chan kofar Wajen karamin Dakin Megadi ne da kuma katon Get din dayayi ma Gidansu Katanga
Daga Kallon Farko in kayi ma Gidan nasu Sai ka Rainasa kace bai da girma sai ka Shiga cikin Gidan zaka san Gidan yana da Girma Sosai.
Kai Tsaye Madafi Ta nufa kan Windon Wajen ta Ciro key din Ta bude Kofar kichen din kafin Ta kunna Wutar Kichen din Wanda ya Taimakamata Wajen bayyana Hasken Wajen,Madafin yana da girma mai Dauke da ciki da Falo wanda da alamun cikin Wajen ijiye kayan abinci ne,shi kuma wajen Inda suke girki ne domin ka gas nan Ajera da Kuma jerin Abubuwan amfani batare da bata lokaci ba ta kunna babban Gas dinsu Mai Hudu kowanne ta aza Tukuya asama Citta ta Dauko ta Daka cikin Wani karamin Turmi ta watsa atukunyar Farko,kafin ta saka kafa ta Bude Wata Dirowa Doya naga ta jawo da Dankalin Turawa,Ta zubesu nan Tsakar kichen din,Wata yar Kujera ta Hau kafin tsawonta yakai Saman inda Wasu jerin Dirowowi suke nan ta Bude ta Dauko wasu Robobi da Wuka ta Sauko ta tara Kenan Jikon Famfon Dake Sink din kichen din tana Diban Ruwa, dayake daga Wajen Rijiyansu suna jawo Ruwa ta Tankinsu.
Motsin Shigowa taji tayi Saurin waigowa ganin Dattajiuwan mai aikinsu Baba Lami yasa ta saki ajiyar Zuciya,Tana Fadin"Ina kwana Baba lami.."Wacce aka kira da Baba Lami ta amsa tana karisowa daga kichen din"Lafiya lau Asma"ul Husna mai Tagwayen suna,sarkin Tsoro yanzu sai kice na baki Tsoro ko..? Ta fada cike da Tsokana,Dan mirmishi tayi kafin tace"Eh mana,Allah bakiji yadda gabana ya Fadi ba,na zata Shigen beran Nan ne dake Shigomana ta Rariya.."Dariya Baba Lami ta Saki kafin tace"Wai naga Tsiya wai Ma"u da Tsoron Bera,anya ke akwai Abunda zai baki Tsoro..? Ahaka dai kamar Jaruma,kullum fa ke ketashimu da asuba da Aikinki wanda bakya gajiya."Mirmishi ta Saki tana Fara Fera doyan tace"Kai kai Baba Wlh don nasan akwai Mutane ne,da ba kowa yaushe zan Fito wlh Tsoro nake ji.."Tafada ashagwaba,Kusa da ita Baba Lami ta karisa kafin tace"Nasani ai ke sarkin Tsoro ce, ko Farar kura ya Shafa miki lafiya kinga bani Wukar na cigaba da Firan Doya ,maza je ki Shirya yau ba kina da Zuwa asibiti ba.."Hanata Wukar tayi tana Fadin"Zanje Mana,Ki barshi zan karisa kinga fa ko sallah ba"ayi ba kiran Sallahr farko kadai akayi ina Da Sauran lokaci.."Ganin ta Hanata yasa ta Kyaleta sai ta Bude Dirowan kasa ta dauko Wata wukar taja kujera ta Zauna suna Ferewan Tare suna Hiransu ahaka Sauran masu kyau suka Fito suka Samesu,Dama su uku ne Baba Lami,Hassatu,da Zulai,wanda su Ba tsoffafi bane kamar Baba lami,Su suka mata chaa,sai da suka karbi wukar Hannunta,Itama tana Shirin atashi ne domin taji an Fara kiran Sallah na Biyu Fitowa tayi daga kichen din ta barsu Suna Hada hadan Faran Soyan Doya da Dankwalin Domin Duk Ranar Duniya Mutan gidan suna da List din Abunda zasu yi breakfast dashi da wanda zasuyi lunch da kuma Wanda zasuyi Dinner,wanann Duk Tsarin Umma ne.
Dakinta ta koma ta Fada Cikin Tiolet dinta Huncewa tayi,Kafin ta juye Ruwan Data sanya acikin kittle Tayi wanka dashi bata Fitoba sai da ta Dauro alwala,koda ta Fito har Wasu masallatai Sun Tada Sallah,saboda Saurin kada Lokacin sallah ya Wuce ko mai bata Shafa ba ta Zura wata Doguwar Rigarta baka tana kokarin Shimfida sallaya ne taji Fitowar Abbansu yana bugama Anty Amarya kofa Ita da Mama Yana kiran su Walid kan Su Fito su Tafi masallaci.
Raka"atanul Fajar ta farayi kafin tayi Sallar Asuba sai da ta zauna ta gabatar da azkar din Safen daya Riga ya zaman mata jiki,lokacin data gama Karfe 7 Saura da hanzari Ta mike ta Kwabe Hijabin jikinta,sai da tasha fa Man Shafawarta na OLIVE kana ta Cire Rigar Jikinta cikin Wardrope dinta ta Bude ta Dauko goggun Fararen kayanta Ta saka Riga da wando,wanda Rigar ta kawo mata Gwiwa,Kalaban dake kanta ta Fara tattarata waje daya ta saka Band ta Hadeta waje Daya,Farin dankwalinta ta Daura kafin ta Zura wani karamin Farin Hijab dinta,Wajen ma"adanan Takalmanta ta Nufa ta Ciro wani Toms,baki mai Wani kwalliya asama tana gogeshi da wani kyalle,ta dauko kenan Ta zauna Gefen katifarta tana kokarin Sanya Farar Safarta taji sallaman Hassatu amsa mata tayi tana Cigaba da Abunda takeyi don bata son ta makara ko Kadan.
Hassatu ta Shigo Dauke da Wani karamin Faranti mai Dauke da Wani karamin Fulas,da Kula wanda Soyayyen Dankali da kwai ke ciki sai Kofuna Guda biyu,Saurin tashi tayi ta karbeta tana Fadin"Sannu Hassatu,Da kin barshi ma nazo kichen na ci kafin na Wuce.."Hassatu na Dariya tana Fadin"Baba Lami ce ta matsa akawo miki ai batasan kina karin nan naki atsaye tasanki sarkin ujila ne.."Yar Dariya Asma"u tayi tana Saka takalminta take Fadin"Allah Sarki Baba lami,Toh na gode Hassatu.."itama mirmishin Tayi mata kafin Ta Fice tana Fadin"Afito lafiya.."
Adakin ma atsaye tasha Ruwan Tea din Kwan kadai taci kadan don tana Son Soyayyen kwai sosai,Koda ta Duba karamin agogon Fatan dake Daure atsitsiyan hannunta Karfe 7:20am Daidai Da Sauri ta Zari Wani Blue hijabin data Fito dashi ta Zura asaman Uniform dinta wanda yakai mata Gwiwa karamar bakar Jakarta ta baya,wanda yan matan yanzu ke yayi ta Dauka ta Rataya kafin ta Suri wayarta ta Tura cikin aljihun wandonta Tiren kayan karyawanta ta Dauka ta Fito da Hanzari saboda ta Makara.
Kichen ta Shiga ta Mikama Hassatu tana Fadin"Bari na leka na gaida Su Abba yau na makara.."Bata jira Cewarsu ba ta Fada dakin Abbanta inda taji hayaniyar su Walid,yana kan kujera acikin kayataccen Falonsa gefensa kuma Uwargida ce Umma ta hakimce,sai Su Walid da ke Tsalle tsalle atsakar dakin,daga chan gefe ta Duke tana Fadin"Ina kwana Abba,Ina kwana Ummi.."Abba ne ya amsa Cikin sakin Fuska yayinda Umma ta amsa cikin Wani yanayi Fuskarta ba Annuri,Tashi Asma"u tayi tana Fadin"Zan tafi wajen aiki Abba,sai yammah zan dawo.."Gyada kai yayi kafin yayi Mgana Umma ta rigashi ta tabe baki tana Fadin"UmH...Aikin kenan Yawon zuwa asibiti da sunan aiki,ana Bigewa da gantali wlh Abban Walid kai ne ka mata sanya Dole sai ka Tsaya ta kawo maka wanda takeso ai kowaye ka samu ka Hadata dashi, da dai wannan Yawon kan ta zubar din Datakeyi agari ana yi Dakai ."Tafada tana Hararan Asma"u wacce ta sadda kai kasa,Hawaye sun cika mata ido,ammh inda ana Sabo da mgana yaci ace ta saba da Mganganun da Umma take jifanta dashi akullum.
Abba bai Tanka mata ba illah Dagama Asma"u Hannu dayayi yana Fadin"Sai kin dawo yau abini bashin kudin Mota,sai kin dawo zan baki yau ban kwana da kudi ba *MA'U*.." Tana jin haka tayi Saurin Cewa"Bakomai Abba ina da kudi atare dani Allah yakara girma da tsawon kwana.."Da Ameen ya amsa kafin ta Fice da Sauri tana jin Sadda Umma ta rakata da wani uban Dogon Tsaki.
Dakin Hajiya iya ta Shiga inda ta isketa zaune Baje akan Cafet tana Karyawa gefe Daya kuma cinyar kaza ne ahannunta tana yaga tana korawa da Ruwan Shayin dake hannunta,Hajiya iya kenan Tsohuwa mai Ran karfe,Abba na bala"in sonta da ji da ita,Bata wani Tsufa ba,saboda tana Samun jin dadi,don a akidar karinta bata karyawa da Safe sai da kaza,Komai nata classic ne kamar wata yar Boko nan ko,ko kofar aji bata taba Zuwa ba.
Daga gefenta ta Tsugguna tana Fadin"Ina kwana iya.."Banza da ita tayi har ma ta cire rai da zata amsa,tana Shirin mikewa taji ta tana Fadin"Lafiya.."Daga haka ta Maida kanta ta cigaba da karyawanta Asma"u bata damu ba,illah dan murmuwa datayi tana Shirin Fita iya ta dago tana Fadin"Hmmm,lalle Aikin kenan Kullum da Safe ashirya afita aiki,ba"a da Burin Aure kwata kwata Allah dai ya sauwake.."Tafada cike da jin Haushi,Wani kallo Asma"u ta makama iya Kafin tace"Ikon Allah Wai ni Iya Don Allah in Tambayeki shin Mijin nan Ana siyoshi akasuwa ne..? Haba kin dameni da mgana Daya wlh da ana Saida Miji a kasuwa na Tabbata da Uwata ta Siyan min koda mafi Kaskascin daraja ne kodon na Wuce gori da Takaichin da Ake kunsamin acikin gidanan Musamman ma ke.."Ta Fada cike da jin Zafin Abun lokaci Daya idanuwanta suna kawo Ruwa,Tana gama Fadin haka ta Fito afusace tana jin Iya na Zaginta tana Hadawa da uwarta tana Fadin duk ita da Daure mata gindi to bazata sabu ba,Tana jinta ammh ta mata banza kofar Dakinta ta jawo ta Rufe da makulli saboda bacin rai ko Baba lami bata leka tama sallama ba,balle ta leka dakin Anty Amarya wanda ya zaman mata jiki Duk safe sai ta Shiga sun gaisa kafin ta Fita zuwa wajen aiki.
Ko Baba megadi sama sama suka gaisa ta Fito tana Sauri domin takwas ta kusa kuma 7:30 Masu cold ke tafiya bayan sun ma masu aikin safe Handing over,Tafiya kadan tayi ta isa bakin Titi,tana zuwa ta samu mai adaidaita ta Shiga tana fadamai inda zai kaita *GENERAL HOSPITAL DUTSE*...Sun kusa isane taji wayarta ta Neman dauki tana Fiddota taga Sister Bahijjja ce ke kiranta bata Daga ba,Saboda sun kusa kawowa babban Get din asibitin.
*****************
*Portharcourt*
_Eleme_
Kokarin Daura Tektie dinsa yake agaban Makeken Dressing mirror din dake cikin Bedroom din, Inda yake Sanye cikin American Suit Ruwan Toka,Na Samfarin DKNY,kafarsa sanye cikin Rufaffen Takalmi na Fatar damisa,hakama hanunsa yana Daure da agogon Fata na Kamfanin Rado,gabadaya dakin ya Bude da kamshin Turaren sa,na Azzaro Visit.
Yana juyowa nace Woww,Masha Allah Saboda yadda kyau Tare da Zati suka Dakeni lokaci daya,Dogon Namiji ne kakkarfa mai cikar Zati da Haiba Ba Fari bane,baki ne ammh yanayin Fatarsa ta samu Hutu da jin Dadi,Shiyasa Fatanshi ta Murje ta bada Wani Hot colour mai ban Sha"awa,doguwar Fuskarsa ita ke Rudan Mutane dashi,saboda yadda Dogon Hancin dan Madaidaicin Hancinsa ya Dace da Dan karamin bakinsa wanda Wani Siririn bakin Saje yayi ma kwanya,Daga kasa kuma wajen gemunsa yana Tsire da wasu munafukan gemu,wanda daga gani zaka Fahimci Gemun na gayu ne๐น,Sai Idanuwansa,Wadanda suke Matsaikata,Gasu Farare masu Dauke da Wani Sirrin Wanda ke Rikita duk wata Diya macen daya sakar masu,Gashin idonsa zara zara ne,sai Gashin giransa mai cika da baki,haka gashin kansa yake baki Sidif a nannade kamar na Fulani yasha gyara da mayuka masu Tsada yana walkiya,Yana da Fadi daga samansa,Bashi da kiban jiki sai dai Ta murjewa da Hutu.
*DEPUTY CONTROLLER GENERAL* Kenan Wato _DCG ABADALLAH MAHAMUD ABDALLAH AZARE_ Wanda Mutane Dadama Suka Fi sanin sa da M.A Azare,Matashi ne Dan kimanin Shekara 32 da Haihuwa ma"aikacin Costome ne,wanda ke aiki a affice dinsu dake Portharcourt,Onne port Federal Lighter Terminal,.
Matashi mai ji da Kudi da aji da Takama Wanda Allah yabama Sirrin kyau da zati Hade da Kwarjini mai cike da Haiba,Burin kowacce ya mace ne Taga ta mallakeshi amtsayin Saurayinta ko Mijinta,Duk takamar mace da ajinta komin Mulkinta da ji da kudinta in ta Kalleshi sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka.
D'ane ga *prof Mahamud Abdallah Azare* wanda Babban professor ne a jami'ar Abubakar Tafawa balewa Federal University Bauchi,Wanda ke Zaune da Iyalansa Garin Bauchi.,ba iya Mtsayin Malamin Jami"a ya tsaya ba Malami ne daya Shahara abangaren ilimin Addini da sanin Littafai Dadama,Mutum ne mai dattako da Girma a idon Wanda ya sanshi Da wanda bai taba ganinshi ba da Wanda kuma iya lbrinshi ya Tsira dashi sai yaji Sha"awar samun koda kwatankwacin Hallaya da ilimi irinta Prof Mahamud Abdallah Azare.
------------------------
Agogon Hannunsa ya Duba yaga Har pass 8 Kada kai yayi ya Nufi bakin Wani Makeken Royal bed,Wanda yake awani Dunkule kamar alkaki,,gefen gadon ya zauna tare da jan Wani makeken bargo mai Taushi,yana Fadin "My *NOORY* plz wake up hakanan,kinsa fa yanzu pass 8 kuma ko sallar Asuba bakiyi ba.."Yafada yana Yaye mata bargon data Dunkule aciki kamar ma Mutum bai Shiga ba Saboda Girma da Fadinsa.
Mika ta farayi tana Mutseke ido take Fadin"Plz *My DEE* Bari na koma After 9 Zan tashi nayi sallar Allah yanzu barci ne a idona.."Tafada ta Kura mai kananun idanuwanta Wadanda suka kara Shigewa saboda barci,Kallonta yayi kai Tsaye kafin yace"No ki tashi kiyi yanzu,Rana fa ta Fito,ba kyau wasa da Sallah my Wasi ina miki Fada Kullum.."Dan Mirmishin Makirci tayi kafin ta Mike tana Fadin"Yes my Dee,.."
Ta fada tana Riko hannunsa,Shi kuma yayi Saurin Mikewa yana Dora duka hannuwansa bisa Kafadunta,Da kallo na bita ganin yadda Saboda Rashin Tsawo Bata ma kai ga Kafadarsa ba,tana da kiba kadan,sannan kuma Farinta na kanti ne,Domin Faffadadiyar Fuskarta ta Yi Dodar da ita๐น,kanta kuma yana Daure da kitson Attachement,wanda akayi Shi kanana ya zubo mata har gadon baya duka kumbunan hannayenta Suna Sanye da Karin Kumbuna ba kyan gani,Mummuna ce ta karshe Kawai Kwalliya ce da Shafe Shafe ya maidata haka,girarta bata da gashi Sosai,kamar yadda gashin kanta yake,Hancinta sanye da Hudin hancin,Wanda yakara Fadada kofar Hancinta,tana Sanye da Wata Karamar Rigar barci pick colour Wacce Ta bayyana Duka Suran jikinta,domin Rigan Shara Shara ne bata Rufe komai ba.
Kiss ya sakarmata Atsakiyar kanta yana Fadin"Zan Fita my Noory.."Lum Tayi da ido kafin tace"Kayi breakfast kuwa...?"Girgiza mata kai yayi yana Fadin!"Zan karya office.."Kai ta gyada mai kafin ta sakeshi shikuma ya Fice da Sassarfa yana Kokarin Fiddo wayarsa dake Ruri acikin aljihun wandonsa yana kallon,Sunan dake yawo Wato *POL1*๐Yayi Saurin latsa mata Line busy ,yana Saukowa daga Saman Steps din cikin Sassarfa yake Rubuta mata Text.
_Meet me in my Guess House Now..._
Da hanzari ya Tura mata kafin ya Maida wayar aljihun wandonsa,Josepen dake ta kokarin Jera breakfaat a kan Dining table ya Duka yana Fadin"Gud mrning Sir.."Hannu kadai ya daga mishi kafin ya karisa tsakiyar Falon inda yaci karo da Kannen Matarsa Wasila Wato Jamila da Hafsa wadanda Suke Sanye dakkansu da Skin Tied da kuma wasu kananann Riguna wadanda suka Fitar Musu da Duka Tsiraicinsu,Kowacce ta baje kan Kujera suna ta Latse latsen waya,Kallo daya yayi musu ya kauda kai,suma cikin Yanga suka gaisheshi ya amsa Sama sama kafin ya Fice da Hanzari koda ya isa haraban gidan Direbansa Emeka dake jiransa yayi Saurin Bude mai Bayan Motarsa prado ya Shiga da hanzari ya zagaya ya Shiga bangaren Direba yaja da Karfi suka Fice daga gidan Bayan Megadi yabude musu get.
*Masha Allah,ya kukaji Salon ya Tafi daku..? Kun samu Natsuwa..?Kun Himmatu da Zuwan lbrin...? Ko kuwa kun Shiga Rudani ne...?HHhhh...Kada ku Damu wannan karon Tafiyar zata zama Kamar ta Wahainiya ce,Zamu Dade Muna Tafiya Cikin Shahara Koda zamu Rasa guzurinmu ne,ammh sai munyi Hakuri mun jira tare da Uziri Wajen Bin Rayuwar M.A azare da matarsa Wasila,kar ku kamanta Ma"u na geFe..? wai ya Abun yake ne...? Hhhn muma bamu sani ba,In kuna son Sanin amsa ku Tambayi Janafty..*
_*Wai Sister Jamila ya Abun yake ne.....*_?..
_Abun bashi da Wahalan Samuwa Matukar Zaku Taru wajen Nuna kaunarku gareni ta hanyar Siyan Littafina na *ZAMAN GIDANMU..* mai Cike da kunci Wanda zaki samu damar karantashi akan Naira 300kachal๐ta Wannan Account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai Aturo da Hoton Trancsation din ta Wannan Nombar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta Wannan Nombar 09069067488,bayan an Dauki Hoton katin kai tsaye,basai kin Wahalar da kanki wajen kwafe Nombar katin ba juz kiyi Snaping din Katin ki aikomin dashi ta Nombar Dana bada,Ga yan Niger masu bukatar biyan Kudin karatu Suma Zasu Biya 500cf ta wannan Nombar +22796515805 Rahma Ummu Fareesa In yayi mata mgana bayan ya Biya kudin Kai Tsaye zai Tsinci kansa agidan da zai Dinga samun Posting dinsa,Ina maraba daku Masoyana Masu Son Cigabana..._
*Jamila Umar*๐
*13/03/2020*.....
*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_
*Jamila Umar(Janafty)*
*Free page* ๎ฅ๎
*Area-Rumoula*
Hon Emeka ya zuba abakin Wani dan karamin get dan Madaidaici Wani inyamuri ne yazo Ya bude get din yana Faman kai gaisuwa ga oga cikin Harshen Turanci.
Tana Tsaye Aharaban gidan Sanye da Wani karamin wando Wanda ko Cinyoyinta bai Rufe ba,sai wata karamar Riga mai hannu Daya wanda ta bayyanar Da duka Tsiraicinta waje,wanda ko Ramin Cibiyarta yana Waje,Kanta kuwa dauke da gashin Attachement Brown ta Zubosu har gadon baya,Wuyanta dauke da Wata sarka ta alamun Cross ,kafarta