zuane a harabar gidansa yana shan
iska da misalin karfe hudu da rabi na yamma. Sai ga alhaji
hassan ya shigo a sukwane ransa a bace, baki bude. Alhaji
usaini ya bishi da kallo yana ta faman kallonsa har ya
zauna a kujerar da ke fuskantarsa. Sannan ya ce masa,
'Zuwa na yi in karbi dana."
"wake nan? Okey to babu laifi bara in yi maka
kiransa."
Ya mike ya shiga ciki ya kira bashir, ya dawo ya
zauna. Can sai ga bashir din ya shigo shi ma ya ce da
alhaji hassan.
"to gashi."
Alhaji hassan ya dubi bashir ya ce, "wuce mu je
121
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
gida daga yau ka bar gidan nan, domin na ga abin mugunta
ne in da a ce 'yarka ce ta ke san shege da bazaka amince
ba, ko da a ce danka ne yake san shegiya za ka bi iya kokarinka ka hana, amma ni nawa dan da ba ka maida shi
dan mutum ba sai ga shi ka zake kana so ka kulla auran.
To ba zan amince da wannan ba."
Alhaji usaini ya ce, 'haba alhaji da girmanka a ce
ba ka san kaddara ba, ai ina ga ko bashir ya san kaddara wai a ce saboda abin da bai taka kara ya karya ba, ka
kwace dan da ka bar mini tun yana dan karaminsa? To ba
abin da zan ce maka sai allah ya shirya ka, ni dai wannan
abu bai isa ya hana mu zumunci ba, danka ne ka karba shi
kenan ka je."
"na karba sai me aure ne dai na hana a yi ba shi
kenan bа?"
"a to shi kenan mana."
Maryam ba ta san abin da ya faru ba. Shiru-shiru
tun jiya ba ta ga bashir ba, har yau da yamma sai ta dauki
waya ta buga masa cewa me ya ke yi.ne a gidan har yanzu
ya ki dawo wa? Domin abba ya ce mata yana gida. Ya ce
ba komai zan komo in anjima. Ta ce to shi kenan sai ka zo
din. Shiru bai zo ba ta sake masa waya, amma a banza shi
baya san sanar mata abin da ya faru ne, amma damuwarsa
har tafi tata. To amma yana mugun shakkar mahaifinsa dan
haka sai ya hakura bisa dole ya zuba masu ido ya ga iya
gudun ruwan su. Wato in sun gaji ai sa kyale su su yi
auran.
Maryam ce zaune ta yi tagumi ta rasa me yake
mata dadi, domin abba ya ki gaya mata abin da ke faruwa
a game da bashir. Sai ga.abban nata nan ya shigo. Yana
122
و
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
shigowa ya same ta zaune ta yi jigum tana tunani, sai ya
kira ta. Bayan ta zo ta durkusa sai ya ce mata,
"maryam abin da nake so da ke duk wanda kike so
in har ya amince ki kawo mini zan aura miki, amma ban da
bashir, domin bashir ya fi karfina tunda ba ni na haife shi
ba."
Tana jin abin da ya ce sai ta yi saurin tashi ta nufi
cikin gida da gudu ta shiga dakinta ta afka bisa gado tana
ta uban rusa kuka wai ita a dole sai an amince ta auri
bashir. Cikin sanyin jiki abba ya shigo ya same ta tana ta
kuka ya yi rarrashin duniyar nan, amma ta ki yarda ta yi
shiru. Sai ya zuciya, ka san in da in yaro ya kafe da san
abin da ba ka da shi ko ba ka da izinin abin nan sai ka huce
a kan dan nan. Dan haka sai ya ciro wayar rediyo abin da
bai taba yi ba kenan ya fara shimfidawa maryam tana
tsalle tana dara, tana ihu tana kiran su anti da umma. Ai
nan da nan sai ga shl suna rige-rigen shigowa dakin.
Halima da tsohon ciki hajiya jamila cewa take,
"matsala halima kar ya buge ki. Wai alhaji me ta yi
maka haka ne?"
Halima ta kama wayar ta rike shi kuma rai a баce
sai huci yake. Ya ce, "haba! Ninan taba ganin yarinya da
naci, sai ka ce mayya? Uban yaran nan ya hana auran nan
kememe, amma kin ki hakura. To ya fasa shi ma bashir
din sai ki san yadda za ki yi mai bakin nacin tsiya. Halima
ta ce, "haba maryam yanzu ke duk samarin garin nan ba su
yi miki ba sai lallai bashir? Wallahi ba ki kyauta ba abban
nan naki yana ta taki komai kika so ya yi miki, amma ke
ba za ki faranta masa rai ba?"
Hajiya jamila ta ce, "kyale ta mana mara mutunci
123
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
wallahi sai ranki ya baci mara mutunci. Alhaji ka je ka
samo duk wanda ka ga dama ka hada su ma kowa ya huta."
"a'a ni na ba ta zabi ta je ta zabo wanda take so in
ya so shi kenan na hutawa raina wannan jangwam."
Suka fice baki daya suka bar ta nan jiki ya yi rudurudu, sai faman shashshafa shaidar dukan take yi tana
zubda hawaye mai domi. Ta sa hannu ta dauki wayarta ta
bugawa bashir ta shaida masa abin da abba ya yi mata.
Bashir ya ce, "amma ban ji dadi ba wallahi, ai ba laifin mu
ba ne, laifin daddy ne. Ni wallahi sna ma rasa yadda zan
6ullowa lamarin, kawai mu yi ta addu'a akan neman zabin
alheri yanzu ki daura alwala ki yi sallah raka'a biyu ki fada
wa ubangiji dukkan bukatunki allah zai biya miki da
izininsa." ta ce to. Ta tashi ta yi sallah raka biyu. Bayan ta
idar ne ta fara addu'a a cikin kuka kamar haka.
"la'ilahaillallahu azimul halimun. La'ilahaillallahu
rabbil arshil azim. La'ilahaillallahu rabbus samawati wa
rabbil aradi wa rabbil arshil azim."
Sannan ta shafa addu'ar. To wannan addu'a ta
tafiyar da kuncin rayuwa ne. Bayan nan ta sami nutsuwa ta
soma addu'ar neman zabin allah akan wannan. lamari
kamar haka:
"allahuma inni as asuluka bi'annna asshahadu
annaka anta allahu la'illahàillallahu anta ahadu samadullazi
lan yalid walam yulad walam yakullahu kufuwan ahad."
Bayan ta gama sai-ta yi masa waya ta sanar masa
cewa ta gama. Ya ce shi ma yanzu ya gama, saboda haka
su ci gaba da irin wannan har su ga mai zai biyo baya. Тa
ce to, ban da abin sa tun da suka san sun kai kukan su ga
allah sai su zuba ido su ga yadda allah zai yi, sai suka.yi
124
3
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
gajan hakuri shaukin so da kaunar junan su ta tunzura su
suka hada baki ta waya suka lababa ba tare da sanin iyayan
ba suka gudu.
Tun safe har kusan azahar ba a lura da cewa
maryam ba ta gida. Kasancewar tun da abbanta ya doke ta
ba ta kara zama a falo ba. A kullum tana daki ita kaðai
kuri ba ta fitowa sai ta yini a daki, an yi an yi ta saki ranta
ta ki har an yi an hakura. Shi ne ba ta zo ta dau abincin
rana ba, har mai musu abinci ta shiga domin dora na dare
sai ta ga na maryam ba ta dauka ba. Dan haka sai ta je ta
sanarwa hajiya jamila cewa yau maryam ankoshi ko
abincin rana ba a nema ba, Hajiya jamila ta ce ai ko ba ta
ma fita ba tun safe bara in je in gani ko lafiya. Tana zuwa
sai ta samu ba kowa a dakin. Abin ya ba ta mamaki. Тa
shiga toilet nan ma ba kowa, Sai ta koma bangaran halima
ta ce, "ko maryam na nan?"
Ta ce, 'wallahi hajiya ba ta nan yau ma ni banga
maryam ba."
Ai nan da na nsai hankalin ta ya tashi ta ce, "to ta
gudu kenan."
Sai kuwa ta yi wa alhaji usaini waya cewa maryam
dai ta gudu alhaji usaini cikin kaduwa ya ce ga shi nan.
Nan nan suka tsaya cirko-cirko ita da halima har ya iso.
Sannan ya tambaye su ta ya ya aka bari har ta fita? Ta ce
ita ba ta san ma ta fita ba, sai yanzu da sa'a mai musu
abinci ta zo ta ga abincin ta na rana ba ta dauka ba. Sannan
aka farga ba ta nan. Alhaji ya ce to yanzu ni ina za ni
neman ta? Wallahì ban san inda ta tafi ba. Ta ce to ai shi
kenan bara na aika gidan hajiya kawata in ji ko tana can.
Ya ce ki je kawai wane irin ki aika, ai abun ba abin wasa
125
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
ba ne. Ta koma ciki ta dauko mayafinta ta fito ta tafi, su
kuma sun juya kenan shi da halima yana tunanin inda za
shi sai ya ji dirar mota a get ya dauka wasu ne sai ya
hangos motar alhaji hassan. Nan da nan sai ya yi tsaye
yana jiran karasowarsa ko maryam na can ya zo kawo
masa kashedi ne. Yana karasowa sai ya ce,
"zuwa na yi in fada maka 'yarka ta je ta janye mini
da sun gudu, saboda haka tun da wuri ka nemo su kuma
wallahi sai na hukunta ta."
Cikin mamaki ya ce, 'alhaji ka san ko me kake
fada? Ya za a yi mace ta ja namiji ai sai dai namijin ya ja
mace. 'Ya ta ta ja dan ka ko dai danka ya ja 'yata. Yanzu
ma nemanta muke ba mu ganta ba."
"to me ya dame ni ni dai dana za a fitowa mini da
shi in ba haka ba ko rai ya 6aci."
> Alhaji usaini ya fusata ya ce, 'duk abin da za ka yi
to ka yi, domin na fahimci kai ba ka bukatar a zaunan
lafiya, da me zan ji da rashin 'yar ko da fadan? Haba alhaji
ka dinga nutsuwa mana."
Ya ce a fusace, "an ki a nutsun kuma wallahi zan je
in duba in har na gan su tare sai ta yabawa aya zakin ta."
"ka yi abin da za ka yi."
Ya shige gida ransa a bace ya dauki mota ya fice
abinsa.'Shi kuwa ya juya ya tafi shi ma.
Cikin yawon neman su ne alhaji hassan ya nufi
wani gurin shakatawa. Ai ko abin mamaki sai ga su suna
zaune su biyun suna ta hirar su babu abin da ya dame su.
Cikin tsananin bacin rai alhaji hassan ya karasa ya clakawa
bashir tsawa a fusace suka mike ganinsa ya sa svuka yi
tsuru-tsuru ya zaro waya ba magana ya bugawa alhaji
126
A
E
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
usaini ya yi masa kwatancan inda suke. Alhaji usaini ya ce
ga shi nan.
Cikin gaggawa ya nufi gurin yana zuwa ya gan su
sai ya yi salati ya ce, "yanzu ku ko saboda allah me ya sa
ba kwa jin magana? Ai tun da kuka ga alhaji ya ki abin nan
sai ku hakura. To wai ku ya kuke so ne?"
Sai alhaji ya ce, "ka ga alhaji ba fa nasiha na ce ka
yi musu, kiran ka na yi dam na nuna maka cewa 'yarka ce
wacce ta gaji rashin magana ta janyo dana nan, domin ni
na san dana in na gaya masa' yana ji kuma daga wannan shi
ne na karshe ka ja kunnın 'yarka kar ta bata mini da,
domin ni dana dan halak ne ba na son akwata abin da ya
faru a baya."
Jin abin da ya ce sai hankalin sa ya tashi ya ce a
ransa wato dai alhaji so yake ya sanar da yarinyar nan ba
mu muka haife ta ba? To na san abin da zan yi kawai. Sai
ya ja maryam ba tare da ya yi magana ba, domin in ya yi
magana zai iya fayyacewa maryam komai ana. Shi kuma
kenan ya hada shi da rigima domin maryam ba ta san abin
da yake faruwa ba, shi ya sa.
Suna zuwa gida sai maryam ta shige gida da gudu.
Alhaji ya bita har dakin hajiyar ya sami bulala zai dake ta
sai hajiya ta ce, 'alhaji shi yawan dukan fa ba shi da wata
fa'ida abin da ya kamata a yi 'shi ne a yi ta addu'ar har allah
ya sassauta wannan lamari, amma a gaskiya abin da yake
faruwa ba shi da wani amfani kuma kai abu kadan ka ce za
ka yi duka shi kuma duka baya shiryarwa. In ya yi yawa
sai dai ya kara sangartarwa kawai. Je ka ka zauna ka yi
tuannin abin yi a wannan lamari."
Ba magana ya fice zuciyarsa cike da tunani kala127
2
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
kala, domin abin yana ba shi ma mamaki.
Maryam ce zaune ta sami hajiya jamila ta ce,
'umma kin ji kowa abin da alhajin su bashir ya ce?"
'A'a."
"wai ccwa ay yi shi dansa dan halak ne baya san akwata.
Shi ne na ce zan tambaye ki me yake nufi?"
Take gaban hajiya jamila ya fadi cikin tsananin
kidima ta ce, "kin san shi afhaji in ransa ya 6aci bai san
abin da zai ce ba kila ransa ne ya baci har yake fadar
wannan magana, amma don allah ki mantar da wannan
magana kar ki sata a rai kin ji ko?"
"to." kawai ta ce, amma ganin yadda hajiya ta rude
da wannan tambaya ya sa ta fara tunanin akwai wata a
kasa, dan haka sai ta fara tunanin to wai me' ma yake
faruwa ne? Me yake nufi? Duk wannan tambaya babu
amsa, domin ba ta san abin da yake faruwa ba dan haka sai
kawai ta koma dakinta ta fara tunani, abin ya zame mata
biyu; ga bakin cikin ana raba ta da bashir ga kuma wata
sabuwa in ji 'yan cacan.
Ana cikin wannan hatsaniyar ne sai allah ya
kawo wa halima nakuda. Bayan an kai ta asibiti da 'yan
mintunan ta haifi danta namiji santalele kyakkyawa.
Abin dai ai kun san ba magana, domin murna gurin
alhaji sai ba sai an fada ba. Da kansa ya dinga fadawa
'yan'uwa da abokan arziki wasu ta waya, wasu kuma ta
baki da baki, wasu arke har gidan alhaji hassan ya je ya
fada hajiya rukayya ta yi farin ciki sosai, amma shi
alhaji hassan saboda wannan abu cewa ya yi kawai allah
ya raya. Ya fice abinsa. Wannan abu bai yi wa alhaji
usaini dadi ba, domin ai ya ci a ce ya nuna nasa farin
128
수
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharuda cikinsa, ganin bai taba haihuwar nan ba, kuma daga
bisani allah ya bashi ai sai a taya shi murna, amma
dan'uwansa ciki daya akan abin da bai taka kara ya
karya ba, ya kullace shi dan haka sai ya ayyana zai je ya
sami dan'uwansu gambo ya sanar masa duk halin da ake
ciki. Ko da yake ma ai tun da halima ta haihu zai fada
masa cewa ya zo a yi suna da shi, sai ya sanar masa abin
da ake ciki.
In ba ku manta ba gambo shi ne kanin su alhaji
usaini da alhaji hassan, yana zaune ne a kasar jamus tun
da ya kammala karatunsa na likita a kasar sai suka rike
shi yake aiki da su, har ma ya yi auransa a can ya zauna
tare da iyalinsa jar fata yake aure, 'ya'yansa hudu duk
sun zama samari, kuma biyu maza ne, biyu mata. Akwai
mai shekara ashirin da takwas, wato namijin kenan.
Akwai mai ashirin da daya shi ma namiji ne, akwai mai
sha shida, sannan mai bin ta ita ma mace ce. Na farin
sunan sa faruk ake ce masa abba kasancewar sunan
mahaifin ubansa kenan wato mahaifin su alhjai usaini.
Sai mai bin sa mai suna ibrahim, sai macen da take bin
ibrahim mai suna sameera, sai kanwar ta zainab. To tun
da suke ba su taba zuwa najeriya ba, a kullum suna can
kasar su ta jamus kun san sha'anin ruwa biyu dole ne a
same su da canjin yanayi na jiki da harshe bare su a can
suka girma ba sanin wata cikakkiyar hausa suka yi ba.
Uban na koya musu sun kuma dan iya, amma basa iya
fitar da ita sosai rai-rai, kamar yadda muke yi. Sai dai
sukan yi ta ne a harde, amma dai kai da kake cikakken
bahaushe in ka ji za ka fahimci ko me suke nufi.
129
69
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Tun da fa suka ji maganar alhaji cewa matarsa ta
haihu sukc ta uban murna da su zo su ga nijcriya
Maman su sai faman dariya take musu wai ba su taba
zuwa ba, ita ko ta zo a lokacin da za su yi aure da
gambo. Daga cikin 'ya'yan na su abba shi ya fi diban.
kama da mahaifiyarsa, ga shi kuma dogo, amma ba can
ba. Kyakkyawa ne sosai, ba shi da yawan magana
sabanin sauran 'yan'uwansa wadanda suke maganannu
Yau ce ranar da zu biyo mahaifin su zewa kasar
nijeriya daga can jamus. Tuni kowa ya gama shirya
jakunkunan sa in ka gan su tamkar in sun tafi ba za su
dawo ba. Maman su ma ta ce za ta je, amma ya ce ta yi
hakuri bayan sun komo zai kai ta. Ta ce to shi kenan
allah ya kiyaye hanya. Sai faman doki sukc za su je
nijeriya tana ta yi musu dariya.
Ga su nan, ga su nan dai har kasar nijeriya tun
daga airport ya yo waya cewa sun sauka fa. Alhaji usaini
ya ce ai yana nan airport din yana jiran su. Sannan suka
gane inda juna suke suka hadu aka rankaya ana ta faman
murna dama shi alhaji usaini sun san shi, domin yana
zuwa can din. Shi ko alhaji hassan bai taba ziyartar su
ba, kuma ba ma ya ba wa iyalinsa su su gaisa, shi ko
alhaji usaini hatta auran da ya kara sai da ya ba su
halima suka gaisa, hajiya jamila ko sun saba da husna
mahaifiyar su kuma suna da hotunan su; su ma suna da
na su. Dan haka an san juna a fili ne kawai ba a hadu ba
sai yau.
A gidan alhaji usaini suka sauka murna kam ba a
magana sai zare ido suke yi suna ganin gari suna kuma
130
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
yabawa, domin su gani suke ma ina ma anan suke da
zama. Suna bala'in kaunar nijeriya sosai. Bayan sun huta
sun ci abinci sun yi wanka sai suka shiga bangaran
halima, domin su ga jaririyar maryam na kwance a
gadan halima ko murnar ganinsu ba ta yi, saboda abin da
yake faruwa a kanta nan suka zauna suna ta faman hira
da halima. Maganar ta su abin dariya wai lokacin in sun
fadi wani abin sai maryam ta yi murmushi kawai. Duk
da ta juya baya ba ta ga fuskokinsu ba, ba su ga na ta ba,
ba su san ma cewa ita ce a kwance ba. A zaton su 'yar
uwar mai jegon ce. Can sai ibrahim ya ce, "wai aunty
ina maryam ne tun da muka zo ba mu ganta ba."
Halima ta yi murmushi ta ce, "maryam kenan ga
ta nan tana jin ku tana ganin ku."
To kun san fa maryam ba ta san su a fuska ba,
sai dai hoto su ma ba su san ta a sarari ba, sai a hoto.
Hakan ne ya sa ta taki waigowa to tana jin haka sai ta
dan juyo domin ta gan su. Sai ko suka yi ido hudu da
abba, wato faruku, yana ganinta sai gabansa ya fadi.
Cikin tsananin jin wani iri a zuciyarsa ya zuba mata ido.
Hakika yarinyar ta hadu. Kallonta kawai yake bai
magana ba, su ko sauran sai carí suke ta faman yi mata.
"lallai maryam kina jin mu kin yi' mana shiru? Тo
wallahi mu ba baki ba ne."
Ta tashi ta zauna gami da tabe baki.
"kan ku ake ji."
To dama sun saba yin wannan wasan a waya, shi
ya sa ba su damu ba. Ibrahim ne mai cewa, 'maryam ashe kin fi haduwa a fili?"
131
66
Kwadi Bari Jána Amina A. Sharada
Sai faruk ya harare shi, "to me yc kuma sai ka
fada a fili an ji?"
Duk gurin suka yi dariya, amma ban da maryam
ta mike za ta fice sai halima ta yi kiranta suka shiga
wani dan falo da ke gefan bed room dinta. Ta ce, 'haba
maryam bakon ka fa annabin ka yaran nan suna ta taki,
amma ke ba ki ma lura da su ba, in kin yi banza da
wasu, ai bai kamata ki wulakanta su faruk ba dan su ba
sa'o'inki ba ne. Ina kallo fa faruk tun dazu ke yake kallo
Kilama yana yi miki kallon rashin tarbiya ne in ranki ba
a dadi yake ba ai dole ne ki hadiye 6acin ranki ko dan
bakin nan. A gaskiya ba ki kyauta ba, kuma wallahi ban
ji dadin haka ba."
Sai maryam cikin sanyin jiki ta ce, 'shi kenan
aunty zan shiga yanzu."
Sai da ta hada musu leman kwakwa da abarba
mai sanyi. Sannan ta dora da wani cake mai bala'in
laushi ta kai musu a wani jug mai kyau da cups din su
da 'yan plate masu sha'awa da wata 'yar wuka da za su
dinga yankan cake din suna ci. Sannan ta shiga ta
durkusa ta basu. Sannan ta gaida su faruk, har yake
tsokanarta.
"Kanwata in ce ko ba a yi murna da zuwan mu ba
ne shi ya sa ba a yi mana magana ba?"
Ta yi murmushi ta ce, "na yi mana."
"ba sai kun yi magana ba yaya faruku."
"a'a ni ban ji."
a lokacin miskilan ne a kusa sai yanzu suka
matsa?"
132
3
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Ta yi dariya ya ce, 'to zauna mu ci da ke." da za
ta tashi sai halima ta yi mata wani irin kallo sai ta fasa
tashi ta koma ta zauna suka gama ci. Sannan ta kwashe
kayan ta mayar ta wuce dakinta ta yi kwanciyar ta. Tana
tunanin wai kallon me wannan faruk din yake mata ne
kamar wani mai san hadiyeta? Ni fa ba na san kallo ya
yi yawa. Ta ce a ranta.
Can kuma alhaji usaini da alhaji gambo suna ta
hirar su ta zumunci sai ya fara fada masa abin da ya faru
tun daga tsintuwar maryam wanda ya zamo tamkar tuni
ne a kan abin da ya faru har zuwa inda maganar auran su
da bashir ya taso da kin da alhaji hassan ya yi da kuma
irin abin da yake gudana dangane da barazanar batawar
zumunci duk ya shaida masa baki daya. Alhaji gambo
ya yi shiru yana tunani. Can sai ya ce,
"shi alhaji hassan kamar wani jahili? Ai ban ga
abin ki a wannan lamari ba, domin kuwa ailah shi ya san
irin abin da ya faru da wannan yarinya za ta yiwu uwarta
ba mai hankali ba ce. Ta yiwu ba tada uba, in ma ba ta
.da uban to ai ba laifinta ba ne laifin masu aikatawa ne.
Me ye na ita yarinyar a ciki? Shi ma a gaskiya bai yi
tunani ba yanzu ina shi bashir din?"
dansa."
Ya ce, 'yana can ai na gaya maka ya karbe
"to ba ga shi nan kai ma allah ya ba ka ba? Ai
irin wannan babu dadi a dinga yi wa zumunci karan
tsaye ba wata kiyayya in ma akwai ai hakuri. Ka ganni
nan amma dai ban ji dadin wannan abu ba, zan same shi
a yi kokarin sasanta lamarin, amma sai bayan an yi
133
Kwadi Bari Jana
suna." Amina A. Sharada
haihuwar
Ya ce, 'zai zo ne ka duba fa tun da aka yi nan wasu ma da ba mu hada komai da su ba
iyalinsa
sun zo bare shi da muke ciki daya ina gay amaka fa ko
dauke shi
bai
da
wasa
bar su sun zo gidan nan ba. Abin fa bai ba."
"kyale shi kawai ni zan je in same shi. To ma ban
kuma?"
da abin sa tun da ya karbe dansa me ye na gabar
"borin kunya ne."
Shi ma ya ce, 'haka nake zato."
Yau suna, an hallara 'yan uwa da abokan alhaji usaini hatta na waje ma sun zo, domin taya shi murnar
samun kyakkyawan da aka radawa yaro suna muhamamad auwal, domin shi ne na farko. Sai ake kiran
sa da muhd, domin babanta da kanin halima wato auwalu an ci an sha, an yi walima mai kayatarwa, kuma alhaji hassan ya zo sunan an yi komai da shi. Hajiya rukayya ma ta zo haka su bashir sun zo har sun gaisa da
su faruk a waje sun ma jima suna hira, domin abbansu faruk ne yake sanar musu ko su waye. Nan su ka yi ta hira kamar sun san juna, amma ko daya bashir bai shiga ba, domin mahaifinsa ya ce masa in har ya shiga ciki
gurin wannan shegiyar yarinyar bai yafe masa ba. Kuma
sai ransa ya baci, shi ya sa yana ji yana ganı bai shiga
ba. Da su faruk suka tashi ma cewa ya yi ba zai sami shiga ba, shi zai koma sai ya dawo kuma. Nan suka yi sallama. Ita kuwa maryam tun da ta ji an ce bashir ya zo take faman zuba ido ta gan shi, amma ba ta gan shi ba
134
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
har leke ta dinga yi ta wundon sama ko za ta gan shi,
amma ina ba ta sami hango shi ba. Haka ta koma ta
zauna cikin bakin ciki mara iyaka. Halima ma sai da ta
yi ta tambayar hajiya rukayya ina bashir. Ta ce ai ko
bashir ya zo gidan nan, amma ya ce sauri yake yi akwai
inda za shi, shi ya sa bai shigo ba. Haka dai aka yi
shgalin suna duk dangin mai jego sun zo, amma ban da
asabe, domin wai ita ba ma ta gari tana can abuja. Yanzu
likkafa ta yi gaba (ci gaban mai hakan rijiya kenan).
Aka yi suna aka watse kowa na farin ciki sosai.
Bayan an yi suna da kwana biyu sai alhaji gambo
ya je ya sami alhaji hassan akan maganar bashir da
maryam. Ai ko yana fara maganar alhaji hassan ya mike
da fadansa.
'To ina ruwanka a cikin wannan harka za ka sa
baki? Ko kai ma so kake mu 6ata? To wallahi za mu
6ata domin ni ba zan iya jure wannan rashin mutuncin
ba. Haba wai ko kana da hankali ko kai ma ka zare