mutunci take. Kai wannan mijinta ya
shiga uku da masifa."
"ai wallahi dan tana shayin ka ne ma da wallahi
sai an yi wacce za a yi yau ka san dan kuka shi ke jawo
wa uwarsa jifa da bai kula mata 'yar ba ai ba za ta yi
haka ba."
Ya ce, 'ashe ke ma kin yarda da abin da ta ce
kenan?"
'Na yarda mana ai wallahi ya aikata ne na ga kai
ma din sau nawa za a kawo maka kararsa amma ka
share su ka nuna sharri suke masa. Ka so na.ka fa duniya
ta ki, ko ki shi duniya ta so shi....."
"kin ga dakata don allah kar ki bata mini rai
yanzu ya ki ke so mu yi wa dan shi kenan sai in hana shi
fita saboda kar ya dauko mini magana ko ko in ki shi in
tsane shi, dan duniya ta so shi?"
Ta ce, "alhaji ai wannan karin magana ne kuma
ni ban ce ka hana dan ka fita ba, kuma ni ba wai na ce
ka ki danka ba, abin d anake so da kai shi ne kawai ka
tsawatar masa, domin ba na san a kwata abin da aka yi
yanzu."
Ya ce, 'wato kenan kin tabbatar shi ya aikata
ko?"
"a'a ba shi ya aikata ba, amma na san......in ma
shi din ne ai babu musu."
Ta sauya zancen. Al'amarin akwai kamshin
gaskiya ji bi fa yadda ya shigo ya gan su sai da ya
razana, idan a ce bai san su ba to me ye na razanar? Nan
fa alhaji hamidu amininka ya sanar maka cewa ka
46
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
tsawatar masa yana tara 'yan mata a gidnasa, ya kuma yi abokai 'yan iska 6ata gari. Yanzu ko wannan kadai ba ta ishe ka shaida ba? Ya kamata a ce ka na yi wa yaron nan fada, amma fa kai kamar tsoronşa kake ji ba ka san
ransa ya baci. To ni zan gaya maka gaskiya muddin ba ka dauki wani mataki akan yaran nan ba wata ran zai
janyo mana abin da ya fi wannan bakin ciki."
Duk maganganun nan da suke yi jamil din fa
yana zaune, kuam yana ji ya yi shiru yana sauraron su.
Sai can alhaji ali ya yi ajiyar zuciya ya dubi jamil din ya
cę, 'wannań haka yake duk abin da kake yi babu wanda
baya zuwa kunnena, wato dan na barka ka sake bana san
takura,ka shi ne za ka wuce makadi da rawa ko? To
daga yau na rufe zamanka na wancan gidan ka rufe sai
ka kawo mini makullin gidan. Sannan ka koma nan
gidan da zama kafin nan da kwanaki biyar masu zuwa
ką bar kasar nan ka koma can amuruka da zama a can
mazaka yi digiri din ka na biyų ba za ka dawo yanzu ba
bare ka dinga dauko mini magana kai da nan gida
nijeriya sai wani jikon. Mara kunya kana wani sunkuyar
da kai kamar wani mutumin kirki.".
Jamil ya tashi simi-simi yana shafa keya. Bayan
ya fice ne sai alhaji ali ya dubi matar ya ce, "wallahi
zainab ba wani abu ne ya sani na ki amincewa yaron nan
shi ya yi cikin nan ba, sai gudun kar mu bar abin tarihi а
family din mu."
Hajiya zainab ta ce, "ai ko mun bari alhaji sai dai
allah ya kyauta kuma suma can su yalwan ai an yi musu
ba daidai ba saboda allah wannan shi ne a daki mutum a
47
Kwadi Bari Jana
hana shi kuka."
Amina A. Sharada
"ke manta da su suma ai kwadayi ne ya ja su
suka like masa yana diban dukiya ta yana 6arnatar
musu."
Ta ce, 'a to ai dama haka abin yake kwadayi
mabudin wahala."
4
Bayan su yalwa sun koma gida ne sai bakin ciki
ya sa yalwa ta fara yi wa halima fada tana cewa, "duk
wannan abu ke kika janyo mana shi shegiya mara
mutunci. Ko matsa miki ya yi ai sai ki ki ki gudu ki bar
shi, amma sai kika biye masa ai ga shi nan ya yi miki
ciki ya gudu ya barki sai ki san yadda za ki yi da cikin.
Wallahi ba ruwana da ke sai ki hada kayanki ki bar
gidan nan ki san inda za ki shiga."
Halima na jin haka sai ta fashe da kuka tana
rokon yalwa ta yi hakuri ta bar ta a gidan. Yalwa ta ce,
"ba abin da ya yi mini zafi da ke zan bar ki ina ganin
takaici."
Nan da nan sai ta shiga daki ta fara watso mata
kayan ta. Halima ta fara ihu tana.bai wa yalwa hakuri,
amma ko a jikinta. Wai da ta zauna da wannan bakin
cikın gara ta rasa ta dangurugu. Suna cikin haka sai ga
malam usman ya shigo yana jin abin da yalwa ta ce ya
ce, wallahi halima ba inda za ta je sai dai su fita tare da
yalwan, domin komai ya faru ita ta ja mata, shi yaro
tamkar dabba yake sai da nusarwa, wannan abin da
halima ta yi laifin yalwa ne dan haka halima babu inda
za ta jc.
48
Kwadi Bari Jana Amina A. Shárada
Yalwa na jin haka sai ta sa hannu a ka ta fara
gunjin kuka wai malam ya goyi da bayan halima, saboda
haka halima babu jin dadi cikin gidan nan.
Haka halima ta zauna da ciki a cikin bakin ciki
da 6acin rai. A kullum tana san ta ga.yalwa na mata
magana ko ta faranta rai, amma a banza dan dai yalwan
ta dinga kula ta a kullum da safe sai ta dauki tsintsiya ta
share gidan nan.sannan ta hada wanke-wanke ta yi.
Sannan kuma ta dafa abinci ta rabawa kowa na gidan.
Wani lokacin sai yalwan ta ba ta wanda ba zai isa ba,
domin ita ta rasa haka za ta raba ba ta samu ba, kuma ta
hakura har sai ta gama na dare za ta ci hakan ne ya
sanya ta rame wa sosai. Gashi dai cikin baya bata wani
wahala, amma a kullum sai kara kadewa take, saboda
bakin ciki, ga yaran nan a kullum cikin hantara da kyara
suke. Sun yi bala'in raina ta musamman ma asabe da
wani lokaci har marin halima take yi wai akan ta ce ta ba
ta aron mayafi za ta tallan wake da shinkafa sai haliman
ta ce "ba zan bayar ba,, wancan ma dana baki sai kuka
zuba mini mại na ce kuma ki wanke ki ka ki wanke
mini." sai ta ce to kar ki bayar mayafin ki din banza."
Ta ce, 'amma dai yana yi miki rana, domin kina
ara."
Wai a kan me za ta ce haka, sai ta wanka mata
mari wai ta yi mata gori. Ran halima ya baci ta ce,
'asabe ni kika marа?"
"an mare ki ki yi abin da za ki yi.
"to shi kenan amma sai kin yi da kin sani."
'Allah ya kare ni da yin dana sani ban taba yi ba,
49
Kwadi Bari Janа Amina A. Sharada
ba ko zan yi ba."
Cikin tsabar 6acin rai balima ta shiga daki tana
tunanin maganganun da ta gaya mata. Nan ta yi kukan
ta, ta share hawayenta cikin 6acin rai duk san da za ki ga
halima to da guntun hawaye a idonta. A kullum tana ta
faman tunani.
Aiki kuwa a gidan halima yi take tun karfinta,
amma babu godiya; domin har yau tsanar ta na nan a
zuciyar yalwa. Ga shi dai babu abin da ba ta yi mata na
kyautatawa, amma a banza. Wata rana ma sai tana
tsakiyar barci cikin dare sannan za ta tashe ta ta ce wai
ta yi mata wanki, domin an kawo ruwa kar a dauke,
Haka za ta katse barcin ta yi musu wankin. Sannan ta
kwanta. Shi ko malam usman ya sa musu ido baya
magana domin ya ce yà zare musu'hannu daga kan su ba
sa ma sauraron sa, shi ma baya sauraron su; amma wani
lokaçi yana tausayawa halima abubuwan da yalwa ke
mata. Domin takurawär ta yi yawa, ga shi tabi ta rame,
ta lalaces, ga cikí kuma ya fara tsofa, domin yanzu ya
kai wata na bakwai.
Nan fa yalwa ta kara ta kura mata da aiki,
musamman ma shara da ta fahimci sunkuyan sharar na
ba ta wahala, sai ya zamana duk ita za ta yi, domin ta се
ba za ta iya ba ta ci mata mutunci. Kuma har kawo yau
ba ta fasa dora mata talla ba, wai in an zauna haka me za
a ci?
Haka halima za ta dauki tallan abincin nan da
ciki wata bakwai kuma yà fito kowa yana gani. Har ya
zamana yanzu ba a ganin laifin halima a unguwa sai na
50
Kwadi BarJana Amina A. Shurada
yalwa, domin yanzu tausayawa halima ake yi, duk inda
aka taru ba a maganar kowa sai ta su. Har wata sara aka
bayar a garin in mace ta fiye san abin duniya sai a dunga
ce mata 'kwadayi bari jana kar ka kai ni gidan surukaina.
Wato habaici ne fa akewa su yalwa da halima kun san
kauye, amma yalwa ko a jikinta. In sun hadu a gidan
biki ko suna sai a yi ta yi mata habaici, amma ko ta kula
sai ma ta kan ce halima ta yi nata saura na asabe, kuma
tana jira a kawo mata na auwalu da lawan duk a zube za
ta dauka.
Kwaci tashi cikin halima ya kai wata tara, amma
har yau ba ta samun wutu ba, a kullum tana faman tallan
abinci. Ga shi allah ya ba ta kasuwa duk sanda ta kai za
ta sayar masu aikin gini take kai wa abincin nata. A ko
yaushe haka take tafiya salo-salo babu kuzari. Har wani
mutum ya tausaya mata ya ce ta dinga samun dan dako
yana dauko mata abincin domin nauyin kayan zai iya
zama ilia a gare ta. Ta ce to.
Bayan ta koma gida ta gayawa yalwa sai ta ce,
wallahi ba za ta biya kudin wani dan dako ba, sai dai ta
biya da kanta in tana nda su. Haka halima ta dinga nadar
kayan tallan nan tana kawowa gurin sayarwa. Jama'a da
dama sun sha zuwa gurin yalwa akan ta hana halima
zuwa ko'ina, domin maganar da ake yi ta isa.
Nan da nan sai ta fada bakin masifa. War wallahi
ba za ta hana halima fita ba, domin ciki ba karyar sa ake
yi ba, kuma jamilun gidan alhaji ali ne ya yi na sabuwar
gandu kowa ya ganewa idonsa.
A irin masu zuwa wajen yalwa suna hira akwai
51
1
3
Ċ
2
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
wata tsohuwa makotan yalwa ce mai suna goggo hanne,
to ita ce kullum sai sun zo hira gurin yalwan kuma ita ce
mai zuga yalwa akan halima wai kar yalwa ta soma
yarda halima ta haihu a gidanta domin jinin shege yana
kawo talauci. Ku ji jahilci. Sannan kuma wai in ta kore
ta ta haihu a waje kar ta sake ta kawo mata dan da ta
haife, wai fitsarinsa in an tsallaka yana jayo masifa da
yawan tashin hankali. To ire-iren wadannan maganganu
na goggo hanne. Shi ya sa yalwa ke kara tsanar halima.
Sannan ta takura mata. Halima ta rame, ta kode, ta jeme,
babu inda za ta sanya kanta ta ji sanyi. Ta ji takaicin
wannan abu da ya same ta, gwara a ce mutuwa ta yi yafi
mata sauki.
Halima wani na zaune gurin sana'ar ta sai ga
saurayi nan ya zo mai suna nura. Yana zuwa ya ce ta
bashi abinci na naira ashirin, ta ce to. Ta zuba masa.
Bayan ya ci sai ya cire naira hamsin ya ce ta bashi canji.
Ta ciro canjin shi ta bashi, sai ya ce ta barshi. Ta ce a'a
ba ta so. Ya ce ta rike man ai shi ya yi niyar ba ta. Jin ya
fadi haka sai ta hakura ta karba. Ai ko sai ya zamana
duk sanda ya zo sai ya ba ta kudi. Kafin wani lokaci har
sun saba da halima sosai.
Rannan ya zo sai ya ce ta zuba masa abinci ta
kawo inda yake zaune yana gadi, halima ta yarda ta zuba
masa ta bishi, domin kai masa. Tana kai masa sai ya
tsaida da ita gami da bijiro mata wata bukata. Halima
cikin jin nauyin maganar ta ce ita sam ba ta yarda ba. Ya
fara rarrashinta ta ce ita wallahi ba ta amince ba, ganin
haka sai ya sa halima a gaba wai lallai sai ta amince da
52
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
abin da ya ce. Nan sai kokawa ta sarke tsakanin su.
Halima ta fara ihu tana neman taimako, ammam ina ba
kowa ga tsohon ciki, sai faman kukawa suke yi yana
cewa;
Sai kin biyani kudina ai ba don allah na baki ba,"
Cikin sa'a wasu mutane biyu sun zo wucewa
akan babur sai suka ji ihu ta. Ai ko nan suka tsaya, suka
kawo mata dauki. Da kyar suka samu suka ceceta, shi
kuma ya gudu. To tun daga sannan ta ce da yalwa dan
allah ta taimaka mata ta daina yin tallan. Ta yi sa'a
yalwan 'yan kirkin na kusa sai ta ce to shi kenan ta bar
shi asabe kwai ta dinga dauka, to shi halima ta sami
saukin tallan, sai aikin gida kawai. To amma bayan
wannan ya faru sai goggo hanne ta dawo da zugar. A da
halima ba ta samun zama, domin tana gurin sana'a to
amma yanzu ta sami zama a gida sai goggo hanne ta ce
da yalwa,
"ke ko yalwa yaushe za ki zauna tana tsakar gida
kina tsakar gida, sai ka ce wata kishiyar ki? Shi ya sa a
unguwar nan ake cewa ke kika daure mata gindi, ai wato
in kina waje tana daki shiru za a gane cewa ba laifin ki
ba ne."
Nan ma yalwa ta zugu ta fara hantarar halima. A
kullum ita kenan a daki tsuru. Ta yi kuka ta yi kuka har
sai ta gaji. A kullum neman mafita take, domin kucin ya
isa haka kamar ba ita ta haife ta ba. Wani lokacin in
balima na tunani sai ta ce wai ba ta san kaddara ba ne?
Kai ni wannan abu ya dame ni, gashi kowa ya tsane ni
ba a so ne, ko gudu zan yi ne in bar garin ko na huta da
53
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
bakin ciki? Kai wannan abu da ciwo yake. Ta yi kukan
har kukan ya daina dadi, har ciwon ido ta yi dan kuka. A
yau zaman halima ta yi nadama sosai. Tana ta yawaita istigafari, domin wannan abu da suka aikata, kuma ta ma
rasa me za ta yi. Sai a 6oye ta je gurin wani malami
wato malamin nan na layinsu ta ce me ya kamata ta yi domin ta tubarwa allah? Sai ya ce ta yi istigifari kuma ta kuduri niya akan cewa ba za ta kara aikata zina ba. Ta
ce to yanzu ya sakamakonta yake a gurin allah? Ya cе hukuncin dai budurwar da ta yi zina bulalace tamanin, haka saurayin ma, amma bazawari mazinaci da bazawara wannan hukuncin su rajamu ne wato a jefe su in har an yi hakan to an tsarkake su ga laifin su. Ta ce to
tana so a yi mata bulalar, ya ce a'a ki bari har sai kin haihu sai ki zo a yi miki ba tare da kowa ya sani ba, ta ce
to. Ta yi masa sallama ta tafi.
Yau kam halima ta tashi jikin babu dadi dan haka a haka ta yini sukuku har dare kuma ta kwana ba
barci. Da gari ya waye shi ne ta fara wanke-wanke,
amma ba a cikin jin dadi ba, har dai ta gama domin ba ta
so ta bar su gudun bala'in yalwa. Har ta samu ta rarrafa
daki ta kwanta ciwo na gaba. To shi ne fa ta shiga kiran
"wayyo allah yalwa, wayyo cikina. Wayyo zan mutu."
To dama shigar yalwa gidan goggo hanne tana ta
faman aikin zuga akan karta bar ta ta-haihu a gidan, ita
kuma yalwa ta biye mata ta kori halima fata-fata.
Wannan shi ne tushan labarin.
9
54
Kwadi Bari Jana Amina A. Shurada
5
Alhaji usaini shahararren maikudi ne kuma dan
kasuwa. Yana zaune a gadan kaya anan kano. Yana da
dan'uwan tagwaitakarsa wato alhaji hassan. 'Yan biyu ne
uwar su ta haifc su a gurin haihuwar gambon su ne allah
ya yi mata rasuwa. Gambon na su namiji ne ana ce masa
alhaji gambo. Su ne na fari a gurin iyayen su, gambo ne
auta. Har yau kuma su ukun ne a gun matar uban su
suka girma da yake mutuniyar kirki ce, sam ba ta nuna
musu komai ta dauke su kamar ita ta haife su. Sai da
suka girma suka kama kasuwanci bayan sun gama
karatuns una gaba da firamare. Mahaifinsu bai ga auran
su ba, shi ma ya rasu.
Hassan ya riga ussaini aure, domin sai da ya
haihu ma da namiji aka sanya masa suna mukhtar.
Sannan shi kuma ya fara zancen auran hajiya jamila, 'yar
wani hamshakin mai kudi tun tana budurwa uban ya kai
ta ta sauke farali. Suma kuma su alhaji usaini da
dan'uwansa hassan sai da suka je makkan, sannan suka
yi auran shi hassan wata 'yar fulanin adamawa ya aura.
Sun hadu ne a makotan su ma'ana ta zo gidan.
'yan'uwanta, sai suka hadu har soyayya ta shiga tsakanin
su. Sunan ta rukayya. Alhaji hassan ne ya kai ta
saudiyya, shi ne ake ce mata hajiya rukayya, amma
hajiya jamila aunty take ce mata a gabanta, domin matar
wan miji ce, kuma suna matukar zaman lafiya da
kwanciyar hankali. Sai dai shi fa alhaji hassan yana da
matukar tsatstsauran ra'ayi ga, ga shi miskili wani sa'in
kanin na shi ma wato alhaji usaini hakuri yake da shi.
55
Amina A. Sharada Kwadi Bari Janа
Shi ko gambo ma baya gari, shi cewa ya yi ba zai yi
kasuwanci ba, waje zai fita ya yi wadataccen ilimi.
Sannan ya kama aiki. Yana karatun likita, dan haka baya
ma kasar yana jamus, sai dai waya da sako kuma ba ma
ya maganar auran sam-sam.
Tun da aka yi auran alhaji usaini da hajiya jamila
ko batan wata ba su taba yi ba, har hajiya rukayya ta
sake haihuwar yarinyarta santaleliya aka sa mata suna
fatima. Wato kanwar mukhtar kenan. Bayan haihuwar
fatima ne sai aka sake samun ciki aka haifi bashir. Har
yau alhaji usaini ko 6atan wata. To da hassan ya ga ba
su haihu ba, sai ya ce to ya zabi daya a cikin 'ya'yan sa
ya ba su, to dama bashir ya isa yaye, sai hajya jamila ta
yaye shi ya zauna a hannun su daga yaye ya zama
tamkar dan su. Ya sa shi a makarantar nursery, ya gama
har ya shiga primary one. Sai rannan wata kakar hajiya
jamila matar alhaji usaini ta rasu sai hajiyya jamila ta ce
za ta gaisuwa, ya ce to su tafi tare. To a wannan hanya
ne ta zuwa gaisuwar bayan sun komo suka tsinci
yarinyar da halima ta haife ta tafi ta bar ta. Kun ji fa
yadda abin yake kun kuma gano waye ya tsinci 'yar da
halima ta yar.
Tun da aka tsinci yarinyar nan ko kadan alhaji
hassan bai nuna farin cikinsa da wannan abu ba. Dama
sun daka ta tasa da tuni sun maida 'yar ga hannun
hukuma, dan dai sun kafe ne shi ya sa a dole suka
hakura suka rike yarinyar. Kuma suke nna mata
matukar gata, domin ko su suka haifeta sai haka.
Shi ko alhaji hassan ko gidan ya je in ya ga
56
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada hajiya jamila da maryam a hannu baya kulata, bare ya
dauke ta sai ma ya yi kicin-kicin da shi. Maryam ko
kadan ba ta kaunar hada ido da shi, da ta gan shi za ta
razana shi ya sa ma in ya zo gidan ba ta fitowa har ya
gama abin da yake ya fita. Hajiya jamila na bakin cikin
wannan abu, to amma babu yadda za ta yi, domin wan
miji ne. Shi kuma alhaji usaini baya cewa komai sai dai
ya zuba musu ido kawai, abin ka da dan'uwa in ma
hajiya jamilan ta fiye mita akan lamarin haushinta yake
ji, dan haka in ma za ta yi ba ta yi a gabansa.
Duk da irin kin da alhaji hassan yake yi wa
maryam toshi kuma alhaji usaini yana matukar son
maryam. Bayan ta kai kimanin shekara biyar da
haihuwa, bai daina yawo da ita ba, duk da cewa in har
ya hadu da dan'uwansa ya ganta a hannunsa ya yi ta yi
masa fada kenan. Ita kuwa hajiya jamila dama akan dole
take bari kuda yana sauka akan maryam. Wannan dalili
ne ya sa maryam ta zama 'yar shagwaba, domin sun
shagwaba ta sosai. Kuma wani abin allah, bashir jinin su
ya hadu da maryam ko da yaushe suna tare. Har rannan
alhaji hassan ya gan su sai ransa ya baci ya ce da alhaji
usaini in har ba zai dunga hana bashir kula maryam ba,
to wallahi zai karbe dansa. Wannan abu ya yi wa alhaji
usaini-ciwo, to amma dan'uwansa ne babu yadda zai yi
sai ya kira bashir din ya ce masa in ya ga ubansa kada
ya sake daukar maryam har sai baya nan. To wannan shi
mafita. Kuma fa kiyayyar babu wani dalili kwakkwara
wai kawai dan ba su suka haifeta ba, kuma sun rakito ta
sun rike shi baya san irin wannan, haka kawai ka kwaso
57
Kwadi Bari Jana Amina 4. Sharada
dan wani wanda ba a san ma asalinsa ba ka rike.
Wannan shi ne kawai hujjarsa ta nuna wannan tsantsar kiyayyar.
Tun tana shckara uku aka sata a pre-nursery.
Yanzu ga shi ta kai shckara biyar. Bashir ne mai nuna
mata yadda za ta yi rubutu, domin shi ne mai koya mata
duk wani abu da ake bukata ta yi a gida. Bayan wasu
malamai masu koya mata extra lesson da alhaji usaini
ya dauka wato na english daban, na maths daban, na
arabic daban. Babu yadda za a yi bashir ya iya cin abu
bai ajiye wa maryam ba. Haka ne ma ya sa abincin su
ake hada musu domin ita ma tafi ci da bashir din. Ga shi
kuma makarantar su daya, ita tana bangaran nursery, shi kuma yana aji daya a sakandire.
Yau alhaji usaini ne ya yi shawarar ya kwashe su
su ti gidan alhaji hassan, domin yana ta mita sun jima ba
su zo ba, dan haka har hajiya jamila. Duk yin can za a
yi, sai dare kuma. Sai hajiya jamila ta ce "yanzu abin da
ya kamata a yi shi ne a kai maryam makota in ya so in
sun dawo a zo a dauke ta."
Ya ce,, "haba dai a tafi da ita mana kawai."
"to ai ni tsoran fadan alhaji nake yi."
"ba zai yi ba, mu je kawai."
Suka fito bashir shi da alhaji kayan su iri daya,
kamar za su je daurin aure ko sallar idi. Wata shadda cе
mai tsada suka dinka iri daya har babbar riga ta sha aiki
ita kuwa hajiya janmila leshi ne baki. Sannan kuma ta
sanya wa maryam wata doguwar riga (after dress) mai
kyaun gaske da tsada ta raba gashin kanta gida uku,
58
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
wanda gashin sai da ya kawo mata har kafadarta. Da yake tana da gashi sosai, sannan ta sanya mata dan kunne da sarka na gold ta kuma kawo wani takalmi mai
kyau ta dana mata,. Ta sanya mata ribon kalar takalmin.
Sannan suka kama hanya sai gidan alhaji hassan.
Da zuwan su hajiya rukayya ta tarye su cikin fara'a da murna. Yaran gidan ma suka rude cikin murna
suka tarye su wato mukhtar da fatima suka dauki
maryam suna murna suka karasa falo, kowa na murna. Fatima ce ta kawo musu lemo da cake. Sannan ta koma
ta zauna ta gaida hajiya,hamila. Sannan ta kama hannun
maryam suka shiga ciki. Shi ko dama alhaji usaini wurin
dan'uwansa ya wuce kai tsaye. Wato 6angaren sa suka
zauna a wani falo na musamman suna hirar su ta
zumunci.. Fatima ce ta shiga ta kawai alhaji usaini lemo
da nasa cake din, wanda dama an yi shi ne musamman
saboda zuwan su na yau. Bayan ta gaishe shi ne yake
cewa,
biki."
'Fatima kin zama 'yan mąta mun kusan shan
Cikin jin kunya ta rufe fuskarta. Ya ce, 'ai tun da
kin yi candy sai aure ko?"
Ta ce, 'lalala! Uncle'ai wata zan ci gaba."
'Wacce kenan?"
Ta ce, "higher institution zan yi."
"nan kano kike son ki yi ko ta ina?"
Ta ce, 'a'a nan kano."
Ya ce, 'okey shi kenan sai yadda shawara ta
zauna, amma inn san samu ne sai ki yi auran ki tukun
59
Kwadi Bari Jana
nan sannan in ma karatu nc kya yi."
Amina A. Sharada
Na ce, "uncle don allah ka kyale ni ko farawa ma
in yi sai in yi auran.
Ya ce, 'to shi kenan allah ya ba da sa'a."
"amin." ta ce da shi. Ta mike ta koma ciki.
Can kuma hajiya jamila ce da hajiya rukayya ake
ta faman bira. Hajiya rukayya ce mai cewa, 'wai ni
yaushe za mu fara wani dan business ne?"
Ta ce, "nima na so mu yi wannan maganar da ke,
yanzu ya kike ganin za mu fara?"
Hajiya rukayya ta ce, 'ai ni abin ne. To mu fara
da turaran wuta mai kyau da na ruwa, kamar su humra
da bahur mana."
'to dama ko suna shiga a garin nan sosai, domin
muddin kika yi mai kyau za su kare. To yanzu jarin
nawa za mu fara da shi?"
Ta ce, "mu sa, kamar dubu dari ko du hamsin, kin
ga shi kenan sai mu ga kamun ludayin da yake farkon yi
ne."
"to.shi kenan in kasuwar na garawa ai sai mu
kara jari. Yanzu wa zai mana jigilar? Wannan kayan fa
sai maiduguri." in ji hajiya rukayya. Hajiya jamila ta ce,
'ai ina da kanwa a can maidugurin sai mu kai mata
kudin ta hada mana komai da komai, domin sana'ar ta
kenan."
Ta ce, 'to ta kwana gidan sauki."
Sannan suka Tara shawarar san da za su fara.
Sunanan har lokacin abincin rapa. Tare suka
shiga kitchen wato hajiya rukayya da hajiya jamila suka
60
Kwadi Bari Jana Amind A. Sharada
shirya abincin ranar mai dadi. Bayan sun gama suka
baiwa kowa nasa. Sai hajiya jamila