fadansa da
shi kar ya dinga shiga cikin samari bata gari.
Halima kam ta sami matsayi domin hatta yaran
gidan jamilu ya hana su ce mata halima, sai aunty
halima, kuma ya ce shi kuma su rika ce masa yaya
jamil. Yanzu kai babu dan kwali take yawo da wani dan
figigin mayafi da kananun matsatstsun dinkunan riga da
siket. Abin dai sai 'yan unguwa su suka iya kwatancen.
Kai duniya tana gara musu a kullum sai a sayo kaji a
kawo wa yalwa da yaranta toshiyar baki, in an tafi a je a
yi hoto ba ta hanawa, domin inda sabo an saba. Yanzu
abin ya ci gaba sai su dinga abin da bai dace ba a idon
jama'a ba mai cewa kanzil dan tsoran yalwa, domin
akwai wani mutum da ya taba zuwa wurin yalwa ya ce,
"yanzu saboda allah yalwa kina kallon abin da
31
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
yaran nan suke yi ba za ki iya yi musu magana ba?"
Sai yalwan ta ce, "to me ye? Mc suke yi? Ashe
kai ma malam baba da nake ganinka mutumin kirki ba
ka da mutunci, kai ma munafikin ne har da kai za a
dinga zagar mini 'ya dan an ga yaran nan yana tsananin
sonta, shi ne za a sata a gaba? To ta allah ba ta ku ba,
kuma dole ku ganni ni da yarana a lokacin da muke shan
wuyar waye ya taba zuwa ya taimaka mana sai yanzu da
dadin yazo za a fara kawo suka. To daga yau ma duk
wanda ya kara zuwa ya ce da ni ga abin da halima ta yi
sai na sa an daure shi munafukan banza za su kore mata
dan samun da take yi."
Shi dai malam baba ba shiri ya kama gabansa
babu ko kyakkyawar sallama, domin ya fahimci idanun
yalwa sun rufe ya barta tana ta faman bambami ita
kadai.
"iye zancen banza zancen wofi ashe duk abin da
nake yi ana samin ido an ga na fito fes da ni na daina
hakilon abincin, sayarwa da tashin asuba, domin an ga
'ya'yana su. sa wancan, su cire su sa wannan gida ya
gyaru duk dalilin halima yarinya mai kashin arziki.
Allah ya sa asabe ma ta yi kashin ta, wato an ga zamu
huta shi ne za a yi mana bita da fulli waya sani ma ko
asiri aka yi musu shi ya sa ya ki 'yarda ya turo iyayen
nasa a yi maganar aure nan?"
Ta yi murmushi.
"ga shi yaro na san ta kamar ya hadiyeta, komai
halima. Allah sarki insha allahu halima rabanka ce har
da rabo, 'yan bakin ciki kuma sai dai a mutu."
32
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Mallam shi ne ya yi mata magana domin yanzu
duk ragamar gidan ta koma hannun yalwa ba shi da abin
cewa, sai abin da ta ce, dan haka ya zo mata a matsayin
sa na mai ba ta shawara. Ya ce, "yalwa yaran nan ya
kamata a san abin da ake ciki da lamarin su, gara a
aikewa mahaifinsa in ya so a san abin da za a yi game da
maganar auran su, sai magana ake ta yi wai an bar yara
sun watse sun lalace suna tata iskanci san rai a gaban mu
muna kallo kowa da abin da zai ce."
Yalwa ta kalle shi a yatsine ta ce, 'ashe kai ma ka
zama kowan kenan tun da har kake goya musu baya.
Malam ashe in daina cewa ana nunan bakin ciki a kan
'yata tun da kana daya daga cikinsu? Ashe a masu nunan
bakin ciki har da kai? Ni nake ta babatun banza cewa a
na yi mini bakin ciki, ga babban makiyina a gida. To
dadin abin dai duk abin da ake kawo wa da kai ake
cinye wa in ba dan darajar haliman ba yarinya mai
kashin arziki me kake da shị? Kai da ka yi tunani ko
wani ne ka ji yake fadar wannan magana aí sai inda
karfinka ya kare malam." יית
A gaskiya malam usman bai taa jin bacin rai
irin nan wannan rana ba, dan haka tun da ta fara
maganganun ta bai tanka mata ba, har sai da ta kare,
sannan ya dube ta ya ce, "yalwa wato ya dace ki dinga
gaya mini wadannan maganganun akan na fada miki
gaskiya ko? Wai har ki ce ni nake miki bakin ciki ko?"
Ta ce, "to ai kai ne malam.........."
"dakata insha allah daga yau in dai nine na daina
nuna miki bakin ciki, ki yi duk abin da kike so da su
33
I
Amina A. Sharada Kwadi Bari Jana
ya'yanki nc, amma nan gaba duk abin da ya faru kar ki
nuna kin sanni ma barc......"
"dakata malam kar ka yi mata baki."ta tsaida shi
da fada.
"in har ka zare hannun sai mc? Cewa akai maka
za su daina rayuwa? To wai da can din ma me kake
tsinana musu?"
"ai dan ba a canzawa tuwo suna ne da yanzu kin
canja ko?" in ji malam yayin da ya mike ya kade rigar
sa ya ce, 'allah ya kyauta." ya fice.
Yau satin halima biyu kenan babu ita babu
dalilin ta. Al'amarin da ya tashi hankalin yalwa kenan, ta
fara tunanin duk inda take ta san tana wurin jamil. To
amma me ya zaunar da ita har sati biyu ba ta ko tunanin
gida ma? Kai wannan shashanci da yawa yake ai sai ki
taho gida ko kadunan suka koma ne? To allah dai ya
kyauta.
Ashe kuma can halima na kwance babu lafiya а
gidan jamil. Zazzabi, ciwon ciki da ciwon kai, ga amai.
Suna tare da jamil yana lura da ita wai. da sai ta sami
sauki sai ya maida ita. Da ya ga abin babu sauki sai ya
kai ta asibiti, domin a duba lafiyar ta suka yi sa'ar ganin
babban likita, ya auna ta har ya gano abin da ke damnta.
Wato ta samu ciki na wata uku. Ai yana sanar musu sai
halima tun a wurin ta rushe da kuka, domin bakin ciki
da tsoro ba wai ita da cikin yake jikin ta ba, hatta shi
jamilun sai da ya razana, domin abu ba zato.
Nan take abin ya yi masa zafi ya rasa inda zai sa
kansa, domin shi ba haka ya yi nufi ba. Shi da kawai ya
34
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada fasnhe ladansa ya yi gaba, sai gashi ya buge da shige makadi da rawa. Ita kuwa ban da gunjin kuka ba abin da take yi har sai da ya gaji ya ce ta zo su koma gida, sai a
san abin yі.
Suka kama hanya suna tafe shiru kake ji cikin motar sai sautin kukan ta kake ji, shi kuma ban da aikin tunani babu abin da yake yi. Ya ce a ransa, yanzu ni ya zan yi in rabu da yarinyar nan in guje musu? Lallai ba zai yawu in 6ata ma kaina suna ba, wallahi sai dai sy san yadda za su yi ba zan karbi cikin ba. Ya waigo ya dube. ta.
"to ki yi shiru mana sai wani kuka kike yi wa
mutane kamar an yi mutuwa?"
Ta yi banza dashi ta ci gaba da kukan ta. Ya ce, "wai ba cewa na yi ki yi shiru ba ne?" ya yi rarrashin
duniya amma ta ki yin shiru. Sai bayan ya yi parking guri daya ya juyo ya kale ta ya ce, "dan uwarki tun da kin ki yin shiru to fitar mini daga mota ta yanzu ko
kuma in nuna ta dukan ki har sai kin galabaita."
Cikin kuka ta ce, "jamil yanzu haka za ka yi mini?"
Kafin ta ce wani abu kuma ya fisgo ta daga cikin motar a fusace ya jefar da ita guri daya ya ce, "kuma muddin kuka sake zuwa gurina sai na karya ki shegiya 'yar iska mara mutunci. Cikin kuma ki nemi wanda ya yi miki ba ni ba ne, domin ba ni kaďai kike kulawa ba." Ya juya zai shiga motarsa sai ta yi saurin rike hannnunsa ta ce, "haba jamilu ya za a yi ka ce ba cikin ka ba ne, ka yi mini rai jamilu ya zan yi da cikin nan ka
35
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharauda
guje ni? Ka ji tausayina jamilu kar ka yi mini haka ka
san ba ni da wani gata sai kai, yau in ka guje ni ya zan yi
da raina?"
Take ya ji zuciyarsa ta karaya tausayinta ya
kama shi, amma da ya tuna in iyayensa suka sani
kashinsa ya bushe. Sai ya fisge hannunsa ya shige mota
ya ja yana cewa, "in na kara ganinki a gidana sai na yi
miki illa." nan ta yi ta faman kukan takaici bayan ta
gama kukan sai ta tsaida dan acaba ta tafi gida.
Da zuwan ta gida kan cinyar yalwa ta fada tana
kuka. Cikin firgici yalwa ta ce, 'lafiya halima me ya
same ki? Ke da waye?" ta ka sa cewa komai sai kuka.
Nan da nan ran yalwa ya sosa ta ce, "ke kin ji yarinya
ina tambayar ta tana jina ta maida ni 'yar iska in wani ne
ya takura miki ki gaya mini mana in ya so in yi kararsa
in ga abin da zai turewa buzu nadi, domin na fahimci
mutane sun bura mana wuta sun hana mu sakat da
magana wallahi sati biyun nan da ba kya nan har na ji
shiru ni da ma kin yi zaman ki a can dan kawai wallahi
ba dan na yi da gaske ba da yanzu an raba ku. Ki gaya
mini na ce sai faman kuka kike yi kar kisa raina ya 6aci
yanzu."
Ta dan tsagaita da kukan. Sannan ta dago kai ta
ce, "ba ni da lafiya ne tun da muka yi tafiyar nan da
jamilu ina kwance."
Yalwa ta yi dariya ta kara kamo kanta ta kwantar
a cinyarta ta ce, "to me ye abin kuka kuma a cuta? Ni
wallahi har kin ban dariya ma dama in dadi ya yi ma
mutum yawa ai har cewa yake allah kashe ni in huta,
36
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
dan dadi ke wallahi shigwa6ar ma sai karuwa take yi a
kullum duk jamilu ya maida ke 'yar lelensa, ya dan ba ki
da lafiya sai kuma ki yi ta kuka ko kukan ne zai sa ki
warke? Allah ya sa ba haka kike masa wannan
shagwabar a can ba sai ki yi ta faman ihu kamar wacce
aka aikowa da mutuwa."
Ta zaro katinta ta nuna mata ta ce, "kin gani
yalwa." ta karba tana dariya ta ce, "to na me ye kuma
wannan ai kin san ni ba iya boko na yi ba."
"wai cewa aka yi wai ina........" sai kuma ta yi shiru
yalwa ta ce, 'kina da me? Allah dai ya sa ba hawan jini
kika samu ba, domin na ga kwanan nan kin fiye tunani
halima don allah ki dinga rage yawan tunani."
"yalwa cewa suka yi wai ina da shigar ciki wata
uku."
Cikin zafin nama yalwa ta sanya hannu ta ingiza
ta gefe daya ta mike jiki na rawa ta sanya hannu a kirji
ta ce, "halima ciki? Ciki halima?" kamar ta yi kuma
domin tsabar bakin ciki. Halima kuwa tụni ta Kara
rushewa da kuka. Yalwa ta ce, 'to waye ya yi cikin?"
Cikin kuka ta ce, 'jamil ne."
Tana jin haka sai ta rafka salati ta ce, 'yanzu
halima abin kunyar da 'za ki janyo mana kenan a gari?
Yanzu abin da jama'a kan fada gaskiya ne?"
Sai ita ma ta fashe da kukan ta ce, 'amma
wannan yarinya kin cuce ni, amma ba komai sại mu
sami jamilun a sasanta a yi biki, kya haihu a dakinsa tun
asiri bai tonu ba."
Ta yi jiran jamil yau ya zo, gobe ya zo; amma
37
1
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
shiru kake ji bashi ba dalilinsa ta aika asabe ta yi kiransa
nan ma ta je har gidan sa ta same shi har ya sauya
budurwa ya duba wata mai tsautsayin da kwadayin irin
na halima da yalwa suna ta harkar su. Tana shiga ko
gaisuwa ba ta sami damar yi ba ya daka mata tsawa,
"ke malama me ye?"
"dama yalwa ce ta ce ka zo ťana san ganinka."
'Wace ce yalwa kuma? Maza ki fitar mini daga
gida, kuma in na kara ganinki sai na halaka ki a gidan nan."
Nan da nan ta yi waje tana cewa, "waime ye ya
samu jamil ne, domin ni ban taba zaton zai yi mana haka ba?"
Tana zuwa gida ta sanarwa yalwa abin da ya faru, hankalin yalwa ya tashi fiye da da. Ta tashi ta
sanarwa malam usman halin da ake ciki, domin sai
yanzu ne ta yi tunanin gaya masa. Shi kuwa ba abin da
ya ce illa, "da kin ce ina miki bakin ciki kina samun
kudi to yanzu ina taya ki farin ciki samun karuwa, domin kar in sami sabanin haka ki ce ina miki bakin ciki."
Tana jin haka sai ta sa hannu a ka ta rusa ihu tana cewa, 'yanzu malam abin da za ka yi mini kenan? Wallahi dama na san baki ka yi wa yaran nan dan su lalace, na san ba kaunar mu kake yi ba ni da 'ya'yana. Ka riga ka hada kai da su malam uba makotanka suna zugaka ka na yi mana wulakanci to mu dai ba dai
mutum ba sai dai allah."
Ya ce, "duk abin da za ki ce ki ce ni dai ba abin
38
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
da ya dame ni da ku sai na ga dama zan kula ku."
Shi dama baya zama a yi ta hayaniya da shi. In
an yi na daya ba a na biyu dan haka sai ya haura
takalmansa ya fice abinsa da abin ya yi mata zafi sai ta
figi mayafi da kanta ta sa asabe ta rakata gidan jamilun.
Suna zuwa suka yi sa'a suka same shi zaune shi
kadai abin mamaki tun da yalwa suka shiga bai daga kai
ya dube su ba, sai ya yi kamar bai san su ba. Yalwa ta
sami guri bisa carpet ta zauna ta gaishe shi ya amsa.
Sannan ta ce cikin karya kai.
"jamilu zuwa na yi in ji ya a ka yi ne da wannan
'yar banzar yarinyar halima rashin kunya ta yi ma ko?"
"ba wani rashin kunya ciki ta samo a wani wurin
za ta lika mini na ce ban amince ba."
"haba jamilu, halima babu wanda take kulawa
sai kai ni na san haka to amma tun da haka ta faru sai
mu hadu mu rufawa kan mu asiri ko ba haka ba?"
Ya ce, "kin ga malama ki fice min daga gida na
ce ni ciki ba nawa ba ne ya zan yi in karba?"
"jamilu kar ka yi mana haka ciki dai na ka ne kai
ma ka sani kawai ka rufa mana asiri ka taimaka mana."
Ya mike tsaye ya ce, 'wallahi tallahí ko ki bar
gidan nan ko kuma ki ci duka yanzu, sai in karairayaki
in zube anan ba abin da za a yi gida na ki ka z0."
Cikin tsananin bakin rai ta mike ta ce, 'asabe mu
je kawai."
Suna fitowa ta ce, "daga nan mu wuce can
sabuwar gandu gidan iyayensa domin ni ba zan yarda da
wannan tataccen wulakancin ba."
39
SYkay
Γ
1
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Asabe ta ce, "to yalwa ai dole sai dai da halima
ya kamata ki je ba da ni ba."
"au haka ne nama mance idona ya rufe wallahi
mu koma gidan."
Suna komawa ta sa halima a gaba suka tfi gidan
iyayen jamil din.
Tun daga bakin kofa ta san cewa gidan ya hadп
sosai, domin kana shiga ka san an narka kudi wajen
giminsa. Suna yin sallama hajiya zainab ta amsa musu
sallamar ta ba su umarnin su shigo. Hannu bibbiyu ta
karbe su kasancewar ta mace ce mai daraja mutum duk
da tarin dukiyar da allah ya ba su ba ta wulakanta
mutum.
Nan dai ta yi musu umarni su zauna. Suka zauna
ta tafi kawo musu dan lemo da ruwa, suka sami damar
karewa falon kallo. Yalwa ta ce cikin rada, "ai irin
wannan gurin in ba ka yi da gaske ba sai ka shagala ka
mance abin da ya kawo ka."
Ita dai halima bakin ciki ya ishe ta ta ce, "uhum."
kawai domin tsabar bacin rai ita gani take ma dama ta
mutu kowa ya huta kawai.
Suna nan zaune sai ga hajiya zainab nan ta fito
da ruwa da kuma lemo da cups guda biyu a hannunta ta
dire musu. Ba su iya sha ba yalwa ta dube ta ta ce,
"hajiya don allah ko maigidan yana nan?"
Ta ce, 'eh kun yi sa'a dazu ya shigo, amma bara
in gani in ya gama kimtsawa sai in yi muku magana da
shi, suka ce to mun gode." ta tashi ta shiga. Jim kadan ta
fito ta ce, 'yana zuwa."suka yi mata godiya ta koma ciki
40
Awadi Bari Jana Amina A. Sharada
ta bar su a gurin domin ba halinta ba ne in mai gidan ta
ya yi baki ta zauna ta ce lallai sai ta ji abin da ya kawo
4.
Jim kadan sai gashi ya fito ashe narkeken katon
gaske ne sai juya jiki yake da kyar kamar giwa, daga shi
sai dogon wando da singilet cikin nan nasa kuwa kamar
gorar da ake hawa ana su wato kamun kifi (duma). Kan
sa babu suma sosai ya zo ya zauna shirim da shi a
doguwar kujera yana kallon bakin naşa cikin rashin sani.
Yalwa ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa sannan
halima ma ta gaishe shi. Yalwa ta ce, 'wato alhaji na san
ba ka san mu ba, ka san komai sai ta yi dalili."
"haka ne."
"wato abin da ke tafe da mu shi ne yaron wajen
ka jamilu yau wajen wata shida kenan yana soyayya da
yarinyar wajena halima ga." sai ta nuna halima ya kalli
haliman. Sannan ya jiyo da ganinsa ga yalwan., Yalwan
ta ci gaba da cewa;
"tun tuni mahaifin yarinyar nan ya sami shi
jamilu ya ce masa ya sanarwa iyayensa akan su fito a yi
abin da ya kamata, ya ce to. Ko ya fada maka ko bai
fada maka ba? Ba mu sani ba. Mu kuma ba mu sake
fada masa zancen ba, domin muna tsammani kuna tafe
kuma sa kara fahimtar juna. Sai gashi katsam wai alhaji
abin bakin ciki da 6acin rai yarinyar nan ta zo mana da
ciki da muka tsare ta sai ta ce wai yaron wajen ka ne
jamil shi ne na zo in sanar maka halin da ake ciki."
Tun da ta fara maganganunta bai ce mata kanzil
ba, sai can ya ce, 'bara in yi kiransa in ji ta bakinsa
41
a
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
domin ga maciji ai ba a nuna ja."
Nan da nan ya dauki wayarsa ya kira shi ya
kuma shaida masa cewa yana son ganinsa yanzu yanzun
nan. Sannan ya kira hajiya da ta zo ta zauna sai ya sanar
mata abin da ake ciki. Cikin mamaki ta rike baki tana
mamaki ta kasa cewa komai. Sai can ta ce, "to bara ya
z0 mu ji ta bakinsa, lallai dan yau sai hakuri.
Jim kadan sai ga jamilu ya shigo. Yana shigowa
sai ya yi ido biyu da su yalwa, ai nan take ya hade rai ya
yi kamar bai san su ba. Ya wuce gaban mahaifinsa ya
ce, "daddy gani." ya dube shi sannan ya nuna su yalwa
da ke zaunc ya ce,
"ka san wadannan?"
Ya kalle su, sannan ya kalli mahaifinsa ya ce,
"ban san su ba."
Cikin mamaki yalwa za ta yi magana sai
mahaifin nasa ya dakatar da ita ya ce, "sake karanto
masa laifin ya ji tukunna."
Ta ce, "to." ta sake maimaito yadda aka yi ta
zayyana masa. Yana jin abin da ta ce sai ya mike
zumbur cikin kukan karya ya ce, 'haba baiwar allah a ina
kika san ni?"
Yalwa ta ce, "da halima. Ke dan ubanki ba ki da
baki ne ki yi magana mana?"
Halima ta marairaice ido ya ciko da kwalla ta ce,
"yanzu jamilu ni din ce ba ka sani ba? Ka manta zuwan
da kake yi gidan mu ka yi ta daukana muna tafiya
yawo? Ka manta gidanka har kwanaki ina yi, shi ne za
ka ce ba ka sanni ba? Wallahi daddy in ya ce karya nake
42
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharuda
1
yi mu je asibitin da ya kai ni aka sanar mana iną da ciki. Wallahi shi ma......" sai ta fashc da kuka. Ya dubi alhaji ali ya ce;
"wallahi daddy sharri ta ke yi mini ba kuma wani abu ne ya sa su yi mini haka ba sai dan sun ga kai mai kudi ne shi ne za su yi amfani da wannan damar su ci dukiyar ka kalle su mana duk talakawa. Ina ni inan kula wadannan tumakan ko da a ce neman matan nake yi?" Yalwa ta yi şalati ta ce, "yanzu jamil sharrin da
za ka yi mana kenan? Ka fitirtike wai ka ba ka san daga
inda muke ba? Yanzu alhaji tun da ka ke in ba yanzu ba da ta yi dalili ka taba ganin mu?"
Sai ita ma ta sa kukan. Suka yi ta koke-koke ita
da 'yar halima. Alhaji ali ya ce, "kin ga dakata baiwar
allah ya za ku cika mini gida da koke-koke kamar gidan
mutuwa? Tun da kika ga yaron nan ya kafe to sharri
kike masa ba shi ya yi cikin nan ba, domin da na ba dan
iska ba ne sai ki je ki nemi wanda ya yi wa 'yar ki ciki
tun da wuri. Maza ku bace mini da gani banzaye jahilai.
Ku tashi mana ina magana kuna jina?"
Ya fada cikin tsawa yalwa ta ce, "yanzu alhaji
haka za ku yi mana ina ganinka da kima da mutunci
ashe abin ba haka ba'ne? Dan ka ne fa ya zo har gida ya
yaudari 'yata, amma saboda kai ka isa sai ka goya masa
baya irin wannan ba shi da kyau ai ko sharrin muke
masa ka bi kadin abin, amma a gabansa ka nuna goyan
bayansa ai ka ce ya je ya yi wa wasu kenan......."
"ke dakata!" in ji alhaji ya nuna ta da danyatsa cikin tsawa.
43
d
1
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
"maza ki fitar mini daga gida yanzun nan."
Ta ce, "shi kenan alhaji ai garin ba daya ba ne in
babu duniya da labira allah zai mana sakayya."
"ni kike gayawa haka? In fa ba ki bi a hankali ba
zan sa abi mini hakkin sharrin da kika yi wa dana."
Ta ce, "to alhaji ka kai karar mana kan kukukai.
Ai na fi son haka wato ka shigar da karar duk garin nan
waye bai san danka ne ke zuwa daukar 'yata ba haka ma
akan an san shi ne dan babu wanda take bi sai shỉ, dan
haka in ma gudun abin kunya ne ya sa ka yi mana haka
to abin kunya yana tare da kai gara ni ma za a cе
yaudarar mu ya yi da kudi idan za a zage mu za a ce
kwadayi ne ya ja mu. Amma kai kuwa fa? Wallahi ba
zan zubar da cikin ba, sai an haife shi ko mace ko namiji
kowa ya ga abin da dan ka ya yi na san dai duk in da ya
gilma za a ce wannan fa jikin alhaji ali ne shegen nan da
dansa ya yi ciki, kuma mu talakawan da ka ki jini ka
hađa iri damu ba yadda za ka yi jinin ku masu arziki ya
gauraya da na talaka duk da ba dan halak ba ne sai ya
ya?"
Tun kafin yalwa ta kai karshan maganar nan
zuciyar alhaji ali ta yi zafi dan haka ya mike gami da
nuna ta da yatsa ya daka mata tsawa ido a rufe ya matse
yana tura ciki kamar salka. Ya ce, "fitar mini daga gida
in ba haka ba yanzu in yi wa 'yansanda waya su zo su
kama mini ke."
Yalwa ta ce, "ka ka karawa kan ka abin fada
gari ba? Dan ka ya yi wa 'yata ctiki, kai kuma ka sa an
kama mu an daure."
44
a
Kwadi Bari Jana Amina 4. Sharada
Ba ta jira ya kara magana ba ta ja hannun halima
suka yi waje ba ko sallama, ta bar alhaji a tsayc yana
hura hanci kamar butorami.
Fitar su ke da wuya sai ya koma ya zauna ya sa
hannu biyu ya rufe fuskarsa yana tunani. Hajiya zainab
da ke gefe ba ta yi magana ba tun sanda aka fara wannan
abu sai ta koma kusa da shi ta dafa kafadarsa. Ya juyo
ya kalle ta domin a tsatstsauran ra'ayin irin na alhaji ali
in an yi baki bai amince ko me za a yi ta sa baki ba sai
dai in gurinta suka zo shi ya sa ba ta yi magana ba, kuma
shi mutum ne đa ba ya son bacin rai. Shi' ya sa ma ya
hakura da mace daya, domin baya son hayaniya ga shi
kuma da zafin rai sosai. Ita ma tana matukar hakuri da
shi tun tana 'yar shekara goma sha ukucu ya auro ta, tare
suka yi arzikin dan haka wuyarsa babu irin wacce ba ta
sha ba. Kuma haihuwarsu daya ba su kara ba, wato
jamil shi ne ma ya sa aka sakar masa gata, kuma yana
jin dadin zama da matarsa, saboda nutsuwar ta da sanin
ya kamata da hangen nesa, gashi kuma suna matukar
son junansu, ba wani tashin hankali a tsakaninsu.
Ta ce, 'alhaji ya kamata ka kwantar. da
hankalinka wannan 'yar hayaniyar bai kamata ta sanya
ka 6acin rai ba."
Ya ce, 'zainab ai abun ne da bakin ciki yanzu tun
da muke da ke kin taba ganin wani ya shigo gidar nan
ya ci mana mutunci irin na yau? Kai yau allah ya hada
ni da mace mai masifa. Wallahi zainab da ba dan nima a
tsaye nake ba da sai ta sa mun karbi wannan ciki dole ke
wannan mace da baki take ido rai a soye kamar aya, sai
45
Amina A. Sharada Kwadi Bari Jana
faman zazzago cin