Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
na yi duk sun damu akan maganar tafiyar nan ta bshir. Maryam fa har da kuka, wai ita ba ta san tafiyarsa." Ya ce, "to ai ko in haka ne wallahi sun daukar mana jidali domin in ba wani ikon ailah ba, aure a tsakanin su ba zai taba yiwuwa ba, ya ma za ai alhaji ya yarda ke in ya ji wannan zancen ai mun shiga uku, a zafin rai irin nasa ma ya ce an daina zumuncin." Ta.ce, 'lallai kam ni ai sai ma na fi kowa laifi domin ni zai ce ina hada su." "ai abin ma ba mai yiwuwa ba ne gara a yi hakuri kawai." Ta ce, 'to ai shi kenan." Da sassafe suka shirya tafiyar, dan haka da duku-· duku alhaji usaini ya dauki bashir domin kai shi gidan su. Ya ko yi sa'a shi ma alhajin ya fito suka ranka ya zuwa airport, domin jirgin shida da rabi za su bi. Bayan sun tashi ne ya komo gida ya samu maryam ta tashi ba ta 76 t Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada ga bashir ba, tana ta faman kuka. Hajiya jamila ta yi rarrashin duniyar nan, amma ta ki ji sai ya ce, "ki yi hakuri maryam in kika gama karatun ki na gaba da primary zan kai ki can ki yi karatun ki na gaba da secondary, domin ki samu kwanciyar hankali." Ta ce cikin kuka, "ni dai sai dai ka kai ni gurin bashir." "kin san halin mahaifin bashir yanzu in na kai ki can mun shiga uku ko za ki je haka?" haka ta gyada kai alamar eh. Ya ce, 'a'a na dai yi miki alkawarin kai ki london din." Hajiya jamila ta jata a jiki tana cewa, 'iye 'yar gatan abban ba wallahi abban nan na ki yana shagwaба ki sosai. Haba london sukutum ai wannan tare za mu." Ya ce, "eh a je da ke din kawai shi kenan." Daga cikin kawayen hajiya jamila akwai wata mata mai suna hajiya sa'a, sun hadi ne ta harkar cinikayyarsu da hajiya rukayya wato business din turaruka na wuta da na ruwa da ke gidan alhaji hassan ba sakin fuska a gurin sa sai ta likewa hajiya jamila, har suka shaku sosai da sosai, har ya zamana hajiya jamila ba ta boyewa hajiya sa'a sirrin ta anan shegen tsegumin ta har ta labarta mata cewa ba ita ta haifi maryam ba, to dama ita hajiya sa'a ba ta da aure, kuma tana ganin irin riguntsumin daular dadin da hajiya jamila ke ci a gidan alhaji usaini ya tsonewa hajiya sa'a ido, dan haka take ta neman hanyar da za ta samu ta janyo hankalinsa zuwa gare ta, amma ta kasa. Dan haka sai ta yi tunanin sai fa da makirci, wasu sun sata ta yi a baya, bare ita da kanta 77 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada tana so ta yi wa kanta da kanta. Ta jima tana neman hanyar da za ta bi ta shawo kan lamarin, amma ta rasa sai can wata dabara ta fado mata. Sallam ta yi gidan hajiya jamila cikin murna ta tashi ta tarye ta suka zuana a falo suna hira. Ba su jima ba ko sai ga alhaji nan ya dawo da shigowarsa maryam ta mike da tsalle ta nufi inda yake ta rungume shi, shi kuma yana murna ya ba ta jakar hannun shi suka yi sama. Hajiya sa'a ta dubi hajiya jamila ta ga hankalinta na kan su sai murmushi take yi cike da farin ciki. Sai ko nan da nan kishi ya turnuke ta. Ta dube ta ta ce, "janila wannan wacce irin sangartcciyar 'ya ce haka ke ko kina kallon ta?" Ta ce, "me ta yi hajiya sa'a?" "wato ba ki gama abin da ta yi ba ko? Yanzu saboda allah baligar 'ya kamar wannan ta dunga rungume namiji ba kuma muharramin ta ba, ba komai ba/" 'Wai wa kike nufi ne ban gane ba?" "wannan budurwar ta gabanki ko muharramar alhajin ki се?" 'Wai wane irin zan ce kike yi mini ne?" 'Za ki gane, amma ba a bakina ba sai lokacin da wani abu ya faru tukunna. Ana baki kina kin karba nawa muka gani an yi a gaban mu? Hajiya kulu 'ya bayan ta girma mijin ya aura, ta koma kashima ya fi hajiya kulu daraja a gidan nan. Haka ma hajiya laure ya kasance karshe rabuwa suka yi. Haka allah ya ji karai hajiya ai ita wannan ma bacin rai ne ya kashe ta kamar ke din nan 78 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada kin tsinci yarinya tana karama kin rike ta ta girma kamar dai maryam din nan sai kawai bayan an matsawa yarinya ta fidda miji sai ta ce alhaji aka ce wanne alhaji ta ce na nan gidan. Ai ko da yake shi ma munafuki ne sai ya ce ai wai allah bai haramta ba. To ya zo ya aure yarinyar nan daga karshe sai da ta zo duk 'ya'yan da yarinyar nan ta haifa ba sa ko shiga dakin hajiya ai, wai kar ta kashe mata yara tana bakin ciki ta haihu dan ita ba ta taba haihuwa ba." Hajiya jamila ta ce, "ai 'yar iskar yarinyar ba ita ta raina ta tun tana karama ba?" Ta ce, "kamar kina zaune, to ai karshe bakin ciki ne ya kashe ta ga shi nan tana ta cin duniya, ita da yaran ta a bagas." Hajiya jamila ta yi shiru tana mamakin wannan abu sai ta ce, "allah ya kyauta." 'amin." sannan suka yi sallama ta fice. Tun daga rannan sai hajiya jamila ta fara juya zancen nan a ranta tana so ta kauda shi ya na komo mata sabo. Sai ta dinga zuba ido ta gani wai ko abin da hajiya sa'a ta fada zai faru da gaske. Kawai sai ta dinga jin haushin yadda maryam take nananewa alhaji sai ta fara nuna kishinta. Rannan alhaji na falo a zaune yana cin abinci maryam na kusa da shi tana ta yi masa shagwa6a, domin ita a zatonta sune suka haife ta. Sai ga hajiya jamila nan tana gani sai ta daure fuska ta ce mata, "wai ke me ye haka ne sai ki dinga wani nannane masa wai yaushe za ki san kin girma ne?" 79 a a 11 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada Sai ta mike cikin jin kunya ta matsa daga can ma da taga ba fuska gurin hajiya jamila sai ta yi waje kawai ko kadan ba ta kawo komai a ranta ba, domin ta dauka dai ta na san ta dinga hana ta nanikar sa ne, domin ta girma. Shi ma alhajin bai dauki komai ba, domin bai san komai a kai ba. Maryam yanzu ba kamar da ba, domin duk abubuwa sun fara sauyawa mata a gidan, domin in ta yi irin tahowar nan za ta rungume hajiya jamila in dawo daga unguwa sai ta ingije ta guri daya ta ce mata ke matsa can mara mutunci ke ba ki da kunya ne? Sai jikinta ya yi sanyi ta koma ta zauna. In kuma tana zaunan ta dinga tunani kenan wai ko wani laifi ta yi wa hajiyar ne take mata haka. Shi kuwa can alhaji a kowanne lokaci sai ya ga hajiya jamil na daure wa maryam fuska, kuma ba ta so ta dinga rabar sa, bai dai ce komai ba, ya dai zuba mata ido kawai domin bai san abin da take nufi ba. Rannan maryam na zaune a dakin hajiya jamila sai kawai alhaji ya zo wucdewa sai ya ji tana cewa, "na gaya miki kar ki kara ganin kin shiga dakin alhaji in dai ba ina nan ba, ko kuma nina aike ki." Ta ce, "to." Kawai abin ya yi mata wani banbarakwai. Shi kuma ya na jin haka sai ya kasa daurewa sai ya shiga maryam na na ganin ya shiga sai ta fice. Tana fita sai ya zauna ya dubi hajiya ya ce, "wai hajiya jamila me kike nufi da yarinyar nan ne?" Ta ce, "me ka gani?" 80 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada 'Ai gani na yi kin sa mata tsanani a kai na wai shin kin mata irin alkawarin da keka dauka ne na wannan yarinyar?" "to alhaji saboda allah ina akwai alkawari ya za a yi kawai yarinya ta girma, amma sai ka dinga janta a jiki kana wani shafarta?" Cikin sauri ya ce, "auzubillahi haba jamila yanzu ko wani kika ji zai mini wannan zargin a kya hana bare ke da kan ki kuma?" ya yi tsaki ya fita ransa a басе. Maryam kam na zaune ranta a bace tana tunanin abin da ta ji a bakin hajiya jamila, wato ummanta. Ta cе a ranta, "wai me ya sami umma ne?" Nan da nan sai hawaye daga nan sai kuka, ta yi ta kuka kamar ba za ta daina ba. Sai can jamilar ta yi kiranta domin ta kai wa abban ta abincin sa. Ta karba ta kai masa nasa. Ta na direwa sai ta yo baya da sauri dan kar ta tsaya ma ya sa ta wani aikin hajiya ta zargi wai abu a tsakani. Haka ta dinga yi masa in ta gan shi ya shigo sanmu kawai take masa ta koma daki. Shi kuma sai ya fara zargin ko wani abu ta ce mata, dan haka ya ce zan yi maganin ta ne tun da haka take so aure zan nema ba shi kenan ba, a da ba ni da niyar kara aure, to amma tun da ta biyo'mini da wannan hanyar sai ta yi mamakina mara kunya. 8 Bashir na can misira yana ta karatu, babu abin da yake damunsa sai abu daya. Wannan abu kuwa shi ne tunanin maryam, domin shi a yanzu in ban da tunanin ta ba abin da yake yi, gashi bashi da lambarta dan haka sai 81 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada ya yi wa abban sa karamin waya wato alhaji usaini ya ce, "abba dan allah ka bani lambar maryam yau." To da dai kamar ba zai bayar ba. Sai ya tuno maryam na halin kunci sakamakon uzzurawar hajiya amila shi ne fa ya sake tunani ya bashi, domin ta haka he za ta sami damar kwanciyar hankali, domin shi bashir wani ne gurin iya lallashe shi. Samun lambar maryam ke da wuya sai ya buga nata a lokacin tana daki ta ci kuka ta koshi. Tana jin an pugo ba ta san kowaye ba, sai ta daga. Jin cewa bashir he ai sai murna, amma duk da haka sai da ya fahimci bin da take ciki. Nan da nan ya tambaye ta ko lafiya, Ta te masa lafiya lau. Ya ce a'a da sake a kwai abin da yake lamun ki. Ta ce, 'wallahi ba komai." "to shi kenan in ba ki gaya mini ba zan daina ugo miki waya kuma in kashe tawa." Tana jin haka sai ta ce, 'kai dai dama umma ce a ullum sai ta yi mini fada shi ne ni kuma ba na p.........." yana gama jin haka sai ya katse wayar, ashe mman ya bugawa tana dauka ya ce, "umma bashir ne." Ta ce, "au bashír kuma lafiya?" Da dai ya ji za ta yi dogon bayani sai ya katse ta a cewa, "umma wai me maryam take miki ne?" Ta ce, "me ta ce na yi mata?" 'Cewa ta yi kina fushi da ita." "ni karya take yi mini." Daga ji maganar ba ta shige shi ba, dan haka sai a ce, "to umma ki yi hakuri don allah in ma wani abu ta 82 U Kwadi Bari Jana yi miki ki yi hakuri." 'to shi kenan ya wuce." "to na gode umma." Amina A, Sharada Sannan ya sake buguwa maryam waya ya cc, 'maryam in kin san kina mata wani laifi ne to ki daina, domin kuwa ba na son in dinga jikin ki cikin takura." Ta ce, 'to ni me na ke yí mata? Wallahi ba komai." ce to. Ya ce, "akwai dalili dai ke dai kiyaye kawai." ta 9 Halima yanzu ta gama makarantarta ta gaba da sakandire har ta kama aikin koyarwa a primary tana daukar albashin farko sai baba abu ta ce ta je ta kawai iyayenta ko rabi ne. Ta yi, ta yi baba abu ta karbi albashin, amma ta ki karba, domin tausayawa halin da baban ta yake ciki na rashin ido da rashin cikakkiyar lafiya. Ta hada kudin ta, domin a yi masa aikin idon. Nan da nan aka yo masa. Yalwa ce a gurinsa da ya ke sai da ya kwana. Sannan suka tafi gida. Suna zuwa gida suka samu lawandi ya sha giya ya yi, mankas abin shi, duk ya fada kwata ya daddauje jikinsa. Sai yara ne ke bin sa suna cewa ya yi marisa ya sha kafso. A maimakon yalwa ta ga wannan abin ranta ya ci sai haushin yaran ta ji. Nan take ta fara zage-zage tana kunkunduma wa yara zagi cikin takaici halima ta bar ta a gurin ta komo gida ran ta a 6ace. Can jimawa sai ga su shi ko dama malam usman gida ya taho bai ma tsaya ba, halima ce ta dan tsaya kafin daga baya ta komo gida. Ita 83 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada ma yalwa kuma ta sawo shi a gaba tana ta 6abatun fada har cikin gida. "kai ma duk da kai wallahi dan lawandi na се maka in za ka sha a bar nan ka dinga shan daidai gwargwado, amma kai ba ka jin magana. To ai gashi nan ka tarawa kan ka jama'a." Ran halima ya kara baci, jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin ta. Sai da ta bari yalwan ta daina fadan ta nutsu. Sannan ta sami yalwan zaune a dakinta ita ma ta shiga ta zauna. Sannan ta ce, "yalwa a gaskiya abin da kike yi a kan yaran nan bashi da kyau ki duba ki ga irin shaidancin da yake yi amma maimakon shi ki ji haushin sa sai haushin yaran gari kike ji. A gaskiya wannan ba tsari ba ne ai kamar kin ce ya je ya kra aikatawa ne. Duk tsiya da kina yi musu fada da haka ba ta faru ba. Wai a ce mai rai kullum sai ka ce dabba? Yara gaba daya babu na gari sai ka ce aikin baki? To ni dai gaskiya yalwa in har irin a wannan za ta ci gaba da kasancewa ba zan kara zuwa ba, wallahi allah da a ce na yi aure dauke baba zan yi in har muku gidan ga ki ga yaran nan sai su yi yadda suke so, amma ya ma za a yi a ce duk unguwa ana ganin su suna shaidanci ke ko a jikin ki. Ni dai ba zan iya jure wannan abin ba." •Yalwa ta ce cikin fada, 'amma dai ba ni na ingiza yaran nan na ce su je su dinga şata ko shaye-shaye ba ko? Sha'anin rayuwa ne in allah bai shirya maka zuri'a ba babu aydda za ka yi." Ta ce, 'a'a yalwa wannan ta neman shiri ba laifin 84 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada kowa ba ne laifin ki ne domin tun da ke kika sangartar da su har suka zama tamkar marasa galihu a gari. Dubi yadda lawan ya shawo barasa ba ya kwasowa kansa gayyar yara. Ina jin 'yan majalisar kofar gidan mallam idi suna ta faman magana wasu na cewa allah ya shirye shi, wasu kuwa sai faman zagin sa suke har yalwan kin ga irin wannan babu dadı. Yalwa yanzu saboda allah ba kya gudun kar ki mutu ki rasa mai miki addu'a? Yanzu suna cikin wannan halin ta a za su tuna da ke su yi miki addu'a wadanda sallar ma ba ta dame su ba. Kina kallon rannan ma fa da na zo na kwana na sami auwal mai dan bankalin ma kenan kusan tara na safe ko sallar asuba bai yi ba, dana ce me ya sa bai yi sallar ba cewa ya yi wai shi ya gaji. Wai mutum ya yi ta faman dungurawa wai shi in ya yi sallar duk ga6obinsa ciwo suke yi. Yanzu saboda allah mai muke zo yi duniyar? Wai a ce duk ball din da suke ba su gaji ba, sai sallah ce za ta sa su gaji. Sai su yi awa uku suna dukan ballamma ba su nuna gajiyawa ba; sai sallah. Sallar da duka-duka in sun dade su yi rabin awa kafin a idar. Yalwa duniyar nan fa ba ma tabbata ba ce, in mu ne yau ba mu ne gobe ba. Mutum yana can yana haukan sa bai san lokacin da allah zai karbi ransa ba, shi kenan sai abin da ka aikata. In ka yi khairan ka ga khairan, in sharran ka yi shi za ka gami. Duk abin da ka aikata shi za ka girba. Dan haka yalwa kisa ida akan yaran nan an san sun riga sun sangar ce, amma ya kama ta a ce ki na yi musu addu'a da kuma fadan baki. Ubangiji shi ne mai shiryarwa in ya so zai shirya duk wanda ya so, amma zama haka cikin irin 85. Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada wannan halin ba babu inda zai kai mu sai 6ata." Jin wannan nasiha ta ta ashe duk a kunnan lawan takc yi, dan haka yana jin ta gama sai kawai bazato ba tsammani sai kawai suka ji ya ce, "allahu akbar lallai yau mun gamu da malama." sai ya fito sanye da doguwar farar riga jalla biya da hula irin tashi kafiya naci din nan fara da wani tsohon carbi kato a wuya. Wai masallaci zai je ya yi sallah a lokacin sha biyu na rana ta yi. Ya sake ficewa. Halima ta ce, "allah ya shirya man azuri'a, domin arzikin annabi muhammad (s.aw.) Da alkur'ani." yalwa wacce jiki a yanzu ya yi sanyi ta ce, "amin. To ai ni kin kashe mini jiki ma halima dadin neman ilimin kenan kin ga kin yi karatun ki, amma muna nan muna ta bauma-hauma dama wani abu ai dan ba ka da ilimi ne shi ya sa ake yinsa in akwai ilimi wani abu ai ba za a yi ba. Ga shi yanzu tsufa ya riske mu, babu wani ilimin kirki." Halima ta ce, "ai yanzu ma ba ki makara ba gemu ai baya hana ilimi akwai makarantu da aka bude domin manya sai ki shiga ki dinga zuwa ga su baba abu sun kusa sauka ita gidan gidan gadalima take zuwa." Yalwa ta ce, "yanzu abun da girmanta karatu take zuwa?" "ai na gaya miki gemu baya hana ilimi shi ya sa na ce ki daure ki shiga." Ta ce, 'to zan shiga. A kwai wata makaranta da yaran nan dan gidan jummai mai kuli ya bude na ji an ce matan aure ne suke zuwa bayan isha'i. Sannan su taso 86 Kwadi Bari Jana karfe goma." Amina A. Sharada Ta ce, 'yauwa to kin gani sai ke ma ki shiga bara in je in gani in yana nan sai in saya miki form din." cike." Ta ce, "me ye kuma form?" 'takardar shiga makarantar ce da za a saya a "to je ki ki gani in yana nan, domin shi ma makarantar yake zuwa." "ai na gan shi dazu ya wuce mu har ya gaida baba da jiki." 'Au! To ashe wannan yaran shi ne?" "shi ne mana." 'Ai yaron ya girma sosai, shi ya sa ban shaida shi ba. Ikon allah koma shi ne mai korar yaran nan ne dazu da suke bin lawandi?" "ina ga shi ne." 'Ke shi ne ma ba koriyar riga ce a jikinsa ba?" "eh shi ne fa mai koriyar shadda." Yaran yana da hankali. Lallai zan yi kokarin zuwa makarantar nan. 10 Alhaji usaini kam yanzu neman aure yake tukuru, domin ya yi ko hajiya jamila ta sassauta wa maryam abin da take mata a kullum. Shi kenan cikin ban baki kar hajiya jamila ta kuskure ta sanar wa maryam cewa ba su ne iyayenta ba, amma ita nema take ta tona abin wai ai so yake ta sakankance ya aure ta. Ai ba almuharramarsa ba ce. Maryam har yanzu ba ta gane halin da ake ciki ba, ita a zatonta wani liafi ta yi wa 87 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada ummanta, wanda ya ba tạ haushi. To amma kuma har yau ba ta san wanne laifi ba ne shi ne ta ke ta faman tunanin abin duk ta bi ta rame ta rasa yadda za ta yi, gashi ita ba ta da wata wacce suke hulda ita a gidan su sai gidan su bashir. Can kuma ba sakewa saboda alhaji hassan ko sha'awar zuwa gidan ma ba ta yi dan haka ko yaushe tana zaune a gida ko ďaki, ko kuma a falo sai in alhaji usaini ya ganta sai tausayi ya kama shi ya се, amma hajiya ta dauki tsarar banza haka kawai ana zaune lafiya ta dauko wani lamari na daban mara tushe bare asali ta kawo shi gidan, dubi yadda yarinyar nan ta rame, saboda damuwa a kullum ba ta da kwanciyar hankali. Wallahi da a ce gambo na nan sai ya kai ta gidan sa ya ajiyeta domin ta fi samun nutsuwa a can. Yau halima ta koma daga aiki wato makarantar da take koyarwa sai ta yi tsaye a bakin titi tana jiran motar da za ta hau wato in ta hau motar asibiti za ta kai ta can bitinariya in ta sauka sai ta wuce gidan su. Amma ta fi awa a tsaye ba mota,, bini-bini sai ta duba agogo. Can sai ta ga wata bakar jeep ta yi parking a gabanta kallo daya ta yi mata ta dauke kai, domin a zaton ta akwai abin da ya tsayar da mai motar. A sannu a hankali glass din motar'ya suaka wani kamshin dadi gami da ni'imtaccen sanyin ac ya buso fuskar ta a hankali ta dago kai suka yi ido hudu da wani hadaddan alhaji, fari tas da shi, ga kwarjini da kamala. Suna haďa ido sai ya saki murmushi. Sannan ya ce, "ba tafiya za ki yi ba ne? Zo mu tafi mana." Ta ce cikin sunkuyar da kai, 'ai gani na yi motar 88 Kwadi Bari Jana ba ta haya ba ce shi ya sa." Amina A. Sharada 'ai rage miki hanya zan yi na ga ana wuyar mota." "haba alhaji yanzu da kimar ka da girman ka da darajarka ka tsaya Daukan talaka kamar ni." 'Ai abin san rai ne domin tun da idona ya ganki na ji ina matukar kaunar ki." Ta ce, "to na gode da kaunar ka gare ni, amma je ka kawai." 'Saboda me ba kya so ki zo mu je in kai ki?" Ta ce, 'haba alhaji in jama'ar unguwar mu suka ganni an kawo ni da mota kamar wannan wacce fassara za a yi mini kenan?" Ya ce, 'ai wato shi kamannin mutumin banza ma ai ya fita da ban kin ga dai ban san ki ba, amma ina dora ido kan ki sai na ji nan da nan zuciya ta ta harba begenki." Ta ce, "to sai ka bi a sannu." "to dai yanzu yi mini kwatancen gidan na ku." "to shi kenan nan." ta yi masa kwatance ya kuma fahimta. Sannan suka yi sallama akan cewa sai jibi zai zo ta ce to allah ya kawo ka. Ya ce 'amin. Sannan ya mika mata kudi masu yawa. Kememe ta ki karba. Ya yi ya yi, amma sam ta ki karba, Haka ya hakura ya tfi, amma ya karbi lambar wayar ta, kuma ya ba ta tasa. Sannan ya tafi, bayan ya tambayi sunanta ta gaya masa cewa sunan ta halima, shi kuma ya ce sunansa alhaji usaini. 89 45 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada Halima na zuwa gida ta sanarwa baba abu abin da ya faru, ta yi murna domin wannan shi ne karo na farko da halima ta ta6a kawo saurayi gidan su tan komowarta gidan baba abu ta yi fadan har ta gaji ta bari. To sai yau sai ga shi kwatsam ta zo mata da maganar. Kwana biyun kuwa da misalin hudu da rabi na yamma sai ga alhaji usaini ya zo ya aika wani yaro a yi masa sallama da ita. Nan da nan kuwa ta shirya ta fito. Tana ganinsa sai ta ce, 'au ashe kana tafe?" Ya ce, "me zai hana tun da na yi miki alkawari kyan alkawari ai cikawa, kuma masu hikimar magana sun ce mai san dan tsuntsu shi ke binsa da jifa." Ta yi murmushi ta koma ciki ta dauko masa irin farar kujerar nan ta ba shi daya ya zauna ita ma ta zauna a bisa daya. Sannan suka gaisa. Ya dube ta ya yi murmushi ya ce, 'wallahi tun da na rabu da ke ban kara samun sukuni ba, duk abin da nake yi hankalina na wajen ki; domin tunanin yadda za ki karbi maganar da na zo da ita. Wato ni ba wani abu ne ya kawo ni ba sai maganar aure, domin ni tun da na dora ido kan ki na ji ina da sha'awar ki zama mai dakina, domin bayan son ki da nake yi to na yaba da hankalin ki da tsarin tarbiyarki, shi ya sa na ga ya dace ki kasance mai dakina."" Murmushi kawai ta yi, amma cikin zuciyarta ban da bugun uku-uku babu abin da take yi. Fargabar irin halin da take ciki da kuma irin tarbiyar gidan su, babu yadda za a yi ya aure ta ba tare da ya san asalin iyayenta ba. To amma ba komai take ji ba illa rashin tarbiyr gidan in har ya gani zai iya cewa ya fasa, dan haka ta fara 90 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada tunanin ta goce masa kawai ya tafi ta huta. To amma, kuma in ta yi haka ba za ta yi aurc kenan ba, domin duk irin mijin da ya zo dole ya san gidan ainihin iyayenta. "halima! Halima!! Ya kika yi shiru, tunanin me kike yi haka?" in ji alhaji usaini. Cikin sauri ta daga kai ta yi murmushi. "ba komai." stli nd Ya ce, "ai na fuskanci baki da san magana sośai, gashi kuma ni mutum ne mai san a sani a gaba ana ta yi mini hira." ta yi murmushi. "alhaji an ai in dai hira ce to an gamu da ita, domin nima ina da srutu." Ya yi dariya. "an ya kuwa za ki` yi magana? Kai da wuya." ta yi dariya, sannan ya ce, "to mu koma kan zancen mu ban ji kin ba ni amsa ba, koani ya rigani?" Ta ce, "babu wanda ya riga ka." 'To amma dai ina fatan kin cika idda ko?" Nan da nan sa gabanta ya fadi. Ta ce, "wai shin alhajin nan a me ya dauke

Chapter 6 of 10