in kuma fada ya gama su da 'ya'yan makota sai
ta sa a kamo yaron makotan ko da na ta ne ba shi da
gaskiya ta tsane shi. shi ya sa a kowanne lokaci suna
hanyar zuwa police station da jama'a, amma yanzu kowa
ya kwabi dansa a kan su. shi ya sa in ka ga 'ya'yan ta da
wasu to baki ne, kuma da sun shiga gidajen mutane ake
korar su, amma ita ko a jikinta.
Yalwa ba ga masifa kawai ta tsaya ba akwai
kuma san kudi, domin kowa ya san ta ya san ta kan
jarabar neman kudi da san banza, saboda tsananin
neman kudin ta shi ya sa kaf 'ya'yanta ba mai zuwa
makaranta daga talla sai talla. da dai su lawan da auwalu
suna zuwa wata makarantar allo da ke nan kusa da
gidan, wai dan sun makara shi ne malamin ya dake su. ai
ko nan da nan ta suri zani ta fita ta sami malamin ta kare
masa zagi ta kuma ce in ya kara dakar mata 'ya'ya za ta
yi kararsa, tun daga wannan lokaci malamin ya koro su
ya ce kar su kara zuwa. ga yaranta da' shegen kwadayin
tsiya, wato mazan duk abin da suka gani yaro ya fito
yana ci sai su fisge su zura gida a guje, kuma ba a isa a
bi sawun su ba.
A kullum sai ta yi Rosan kwano daya da rabi na
sayarwa da safe, kuma duk 'yaran ne suke daukar tallan.
in sun dau tallan nan babu wanda ya isa ya yi mata
kwantai, a dole sai sun sayar duk ranar da aka sami
tuntuben kasuwa, ai ko wannan ranar yaran nan sun
shiga uku, domin sai sun ci uban duka kuma sannan ta
ce lallai sai dai uban ya biya, dan ba za ta yi asara ba, in
16
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
ma ya ki biya to ba za ta yi abinçin rana ba, sai dai ta bar
abincin a matsayin abincin ranar ko ana so ko ba a so
wai ba za ta rabawa almajiran mallam su cin ye suna
zazzare ido a banza. hatta malam usman din shr zai ci a
wannan ranar kudin cefanan wannan ranar shi za ta cika
ta tada jarin gobe.
Da rana dama a kullum ta kan yi wa su halima
shinkafa da miya da doya da wake da taliya da salak da
dai sauran su har naman kaji, amma babu mai ci yadda
aka dafa haka za a zuba a tafi talla. asabe da halima su
dauka nan daman sai kudin ta, amma ba ta amince a yi
mata kwantai ba, su kuma su auwalu da dan lawandi sai
su saro rake su kasa a kofar gida suna sayarwa.
idan kuma yamma ta yi sai ta bai wa halima kudi
ta sayo mata goro ta kasa ta tafi talla. da dare kuma
gyada mai bawo da mai gishiri take kasawa a bakin titi
dan haka ko kaďan halima ba ta da hutu.
Gashi kuma in har ta ba ta kudin sarin garo da
yamma za ta ba ta, misalin dari biyu ta saro. to amma sai
ta ce sai ta sayar dari hudu, wai dole sai riba ta ja uwa,
in ba ta kawo haka ba to za ta ci uban duka. ai ko kullum
a haka ake domin ba ta samu abin da ya wuce dari uku,
har uwar kudin. dan haka a kullum halima ita kenan a
cikin fargaba.
Duk cikin 'ya'yan yalwa babu mai kyan halima
domin kamar ba ita ta haife ta ba, ga dai kyau allah ya
bai wa halima ga gashi. fara ce sal da yake ta biyo
mallam usman bafullatani, mutumin adamawa ne zama
ne kawai ya kawo shi nan daga neman kudi sai ya zauna
17
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
anan, gashi kyakkyawa, ga hanci. haka ma halima take
da kyau, sai dai da yake ba hutu, ba ilimi, ba wani
kimtsa kai. sai ta tashi kyan daban ita daban.
Kar ku yi mamakin jin cewa duk wannan kyan
na halima ba tada saurayi, domin kuwa a kullum sai in
saurayi ya nuna ya na son ta har in ya yi ma ta alkawarin
zai zo sai ta ji shiru. ko kuma in ya zo sau daya baya
dawowa, wani lokacin mutane ne suke zugawa. wani
lokacin kuma ita yalwan ce za ta kore su, domin ita da
zarar an zo zancen sai ta fara kitsama 'yar cewa to in zai
tafi ki ce ya sayo miki kayan kwalliya, in zai dawo kuma
ki cc ya saya miki a tamfar, kin ga kayanki duk sun
kude, sannan in ya baki dari biyu kudin zance kar ki
karba sun yi kadan sai ki ce masa haba wane yanzu duk
sauran da na sha, da sanyin farin watan nan dari biyu
kacal za ka ba ni? in ya ki kara miki to kar ki ba shi
wadancan, amma in saurayi ya zo bai baki kudi ba gobe
in ya dawo kar ki fita. wannan hudu ba ta yalwa da ma
halima ta saba tun ba yau ba.
Daga cikin samarin halima akwai wani saurayi
wai shi garba, wanda shi ne ya kafę da naci wai ala dole
saí ya fito neman auranta daman dai shi yana san halima
da gaskiya, sai dai ba shi da wani abin hannu. aikin
kamfani yake, kamfanin atamfa, dan albashin nasa ba
wani yawa: to amma haka yake figewa ya yi musu
hidindumu, domin hatta kayan sallah shi yake yi wa
halima ko anko, ko dai wani abu da ya danganci haka.
Halima tana san garba, domin a kowanne lokaci
tana yawan tunaninsa har ma ta amince masa da ya turo
18
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
magabatansa, to amma sun zo sun tambaya sai yalwa ta
cc su dakata domin tana da wani shiri da za ta yi. ba
wani shiri da za ta yi ba face wai ita a nufin ta ya daí
dakata ko wani mai dan maikon zai fito kar ta riga ta
bada ita, wani kuma ya shigo. babu wanda ya san
wannan tsari na ta sai ita kanta, dan haka garba bai turo
ba, amma yana zuwa dan ko zai sami nasara, ta ce ya
aiko din, kuma har wannan lokaci yana yi mata
hidindumun bai fasa ba.
Alhaji ali wani hamshakin mai kudi ne а
sabuwar gandu yana da matarsa daya da dansa daya mai
suna jamil. shi kadai ya taba haifa har yau kuma bai
sake samun haihuwa ba, tun suna sa rai bar sun daina,
domin a yanzu haka jamilu ya zama saurayi, har ya
gama sakandire ya tafi jami'a da yake baban mai kudi ne
sai ya ce dan sa ba zai yi jami'ar sa anan bab sai can
waje. dan haka sai ya tura shi can ya kuma ce kada ya
dawo sai ya gama karatunsa, sannan ya dawo. haka
kuwa aka yi mahaifiyarsa hajiya zainab da ba ta so
hakan ba, amma sai ta hakura a bisa dole.
Yau ce ranar da jamil ya dawo mahaifarsa wato
garin su. dan haka iyayen sa sun yi matukar farin ciki da
zuwansa, sun kuma sa masa albarka bisa ga samun
nasarar abin da ya je nema.
Jamil yaro ne fari, kyakkyawa na kwatance,
domin kuwa babu wata budurwa da zai ce yana so ba ta
amsa masa ba. ga shi matashi, dan kwalisa ga kudi, ga
gata, domin, saboda gata ma har wani dan karamin
kyakkyawan gida uban ya gina masa wai ya ci
19
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada samartakarsa
illa cc babba
a can shi kadai, ba su san cewar yin hakan ba.
Jamil kam dan kyauta, akwai kyauta; amma fa ga 'yan mata. domin yana da zubar da kudi a gurin 'yan mata idan sa idon budurwa, wato sai dai allah ya kyauta. domin sai ya san yadda ya yi ya yaudari yarinya ya bata ta, sannan ya kore ta korar kare, kuma uban ya sakar masa kudi sosai.
Yau da la'asar ya yi wankansa ya fita, domin zaga gari, don nishadi kawai sai ya kawo shi unguwar su halima, abin kamar abin kaddara yana tsaye da motarsa ya sanya kida yana ji sai ga halima ta zo giftawa cikin sauri ya dago kai ya kira ta, domin tallan goro take yi. ba musu ta kawo masa duk da tana mamakin yaro kamar
wannan dan gayu me zai yi da wani goro? haka dai ta kai masa ta durkusa ta ce, 'ga shi."
Ya yi murmushi ya ce, "ba goran zan saya ba ni
na gan ki ne kuma na ga kin yi miní shi ne nake tambayar ki ina ne gidan ku?"
ta yi murmushi ta ce masa kwatance wato gidan
yalwa mai kosa layin gidan malam idi mai almajirai. ya
ce ya san layin. ta ce masa to kana zuwa ka ce gidan
yalwa mai kosai a kai ka. ya ce to shi keħan zan je. nan take ya zaro kudi 'yan naira ashirin-ashirin ya mika
mata, ta karba cikin murna da doki tana godiya. suka yi sallama akan cewa zai zo yau da daddare. tana tafe tana ta faman murna da dokin ta kai wa yalwa domin ta ga irin farin cikin da yalwa za ta yi in ta ga wadannan kudin.
20
Kwadi Bari Jana Amina A. Shárada
Tana zuwa gida cikin daki ta sami yalwa na
tsantar waken kosa gobe, tana ganinta sai ta daurc fuska
ce, "ya aka yi kika dawo mini da wuri haka, gashi
goran bai kare ba?"
ta
Ta yi dariya gami da mika mata kudi, ta ce,
"yalwa kin ga abin da ya dawo da ni."
tana ganin kudin nan sai ta sa hannu ta karba,
hannunta har rawa yake yi, saboda doki. ta kirga kudi
dubu biyar. ta cę, "waye ya baki wadannan kudin?"
"saurayi na yi wani wai shi jamilu dan gidan
alhaji nan alhaji alj?"
"ke 'yár nan, cewa, ya yi yana son ki?"
"eh."
ai nan take ta rike hanci ta rangada guda daidai
har sau uku. ta ce, "alhamdulillahi allah ya kawo arziki
tsiya ta ji kunya."
ai nan da nan sai rawa tana waka.
"kai duniyar a gidan mu take dadin a gidan mu
yake, arzikin a gidan mu yake. kai budirin a gidan mu
yake."
ita kuma halima na ta faman dariya. yalwa ta yi
murna da abin da ta kawo mata.
"yalwa dan ba ki gan shi ba kyakkyawa."
"to kar ki soma yarda ki 6ata masa rai, domin in
har kika 6ata masa zan sa6a miki, wannan da shi za a yi
domin ya nuna da gaske yake yi."
haka dai suka yi ta budurin murna sosai.
shi kuwa can jamil in ban da tunanin halima
babu abin da yake yi, domin kuwa ya hango abin da
21
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
yake muradi yarinyar ta hadu sosai, kawai matsalar ta ba
wayayya ba cc, dan haka yana da gagarumin aiki a
gabansa. to amma sai ya kai ga cimma nasara, domin
sahun samari zai bi manema aure ya nuna cewa da gaske
yake yi sai ya sa ta kori duk samarinta. sannan ya fara
tunanin shigar da bukatarsa bayan ya saye su đa kudi.
Dare na yi sai ya shirya sai gidan su halima a
motarsa. yana zuwa dama tuni yalwa ta sa ta yi kwalliya
ana jiran zuwansa sai ko can yaro ya shigo ya ce, "wai
ana sallama da halima."
lokaci."
yalwa ta ce, "in ji wa?"
"in ji jamilu."
"jeka ka ce tana zuwa."
'to." ya fita ta ce, "maza ki tafi kar ki 6ata masa
Halima ta ce, "to yalwa."
Ta fito cikin rawar jiki ta same shi zaune a kan
motarsa yana jiranta. Bayan sun gaisa'ne yake cewa,
"wai me ya sa kike yin italla ne?"
"to ai tallan ne ya zama dole ka şan mu ba wasu
mawadata ba ne, shi ya sa."
"to nawa ake samun riba a góran?"
"ana samun ribar dari biyu, amma ba shi kadai
ake sayarwa ba har da abincin rana da kosan safe."
"kai amma duk ke kadai ki ke yin tallan?"
"eh nina ke yi, amma ina da kanne masu taya ni."
"ya kamata ki bar kannan naki su dinga yi, domin kuwa
ke bai dace da ke ba, kin ga kuwa yadda kika hudu?"
ta ce, "to ai mahaifiyata ba za ta amince in daina talla
22
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
ba, domin ni ce karfin neman kudin."
"ki gaya mata zan dinga biyan ta kudin da ke kike samo
mata riba a rana daya ta daina kasa miki tallan komai."
Ta ce cikin mamaki, "haba dai!"
"kina shakka ne?"
'Ai gani na yi abun ba na kare ba."
Ya ce, "ai ni duk abin da kike so zan iya yi miki
dan baki ga yadda nake jin ki a raina ba n. Wallahi tun
da na dora idona na ganki na ji babu wacce nake so
kamar ki, amma sai na ga kuma ke ba ki damu da ni ba."
'ai gani na yį kai mai kudi ne ni ko talaka ce shi ya sa
nake ganin kamar wasa kake yi."
Ya ce, "lallai ba ki san so ba, ai ni ko ganye kike
yafawa sai na aure ki."
Ta ce, 'shi kenan,"
'Yanzu je ki ki tambaya cewa nawa kike kawo пі
ba?"
"to."
Ta zura cikin gida a guje ta sami yalwa har ta
soma barci ta ce, "yalwa wai in jamilu ya ce nawa wai
nake kawo miki riba a rana zai dinga biyanki ki daina
dora mini talla?"
Ta tashi firgigit.
"ina jin zai kai dubu daya da dari biyu. Lallai
møsu abu da abin su malam! Malam!! Ko barci yake
ne?" ta shiga kwalawa mallam kira.
Ya tashi cikin sauri.
"na'am lafiya?"
"a'a lafiya kalau arziki ne ya zo wannan yaron
23
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
dan gidan alhaji aliyu shi ne yake son halima ka gan shi
can ya zo zance a motarsa har ma ya ce wai baya son ta
dinga talla wai ko nawa ne ribar da take kawo wa in
fada zai biya."
Ya ce, "yalwa ba wai na-kì ba nc, amma a dunga
sara ana duban bakin gatari, kin dai san.lamarin yanzu
babu sake.........."
"to malam ka fara ba? Ai ni ban ga abin da za a
yi da ni da yarana ka yi farin ciki ba, babu shi komai ya
sa haka? Oho. Kai kenan a kullum sai neman yi musų
baki kake yi."
Ta dube ta a fusace, 'je ki ki ce dubu daya da
dari biyu zai dinga biya a kullum."
"to."
Ta fita da sauri. Shi ko mallam usman bai Kara
magana ba.
Zaune suke da yalwa da, halima. Yalwa na yi
mata fada, "saura ki dinga rashin kwalliya ga shi nan kin
sami saurayi mai kudi, kar ki'dingą yi masa shashanci
da ballagazanci kin ga' yanzu kin sami daukaka, domin
wannan ba karamar daukaka ba ce duk 'yan matan
unguwar nan waye ya samu yana ki, ga shi daga
haduwar ku kudin gurin mu sun fi dubu ashirin."
Ta ce, 'wallahi kuwa yalwa."
'Kuma ba ya zancen zai turo a sa rana ko?"
"wallahi bai yi magana ba.'
"kin san su masu hali a nutsue suke abin su."
"haka ne, ya ce ma gobe zai zo ya duba ki."
"a'a to allah sarki to kuma ga shi gidan na mu
24
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada duk ya yi kaca-kaca yanzu ya za a yi kenan, ga faggon wanki ba mu yi ba, ga daki ba ko katifar kirki?"
Ta ce, "to ko in ce masa ba kya nan unguwa kika tafi in ya so in mun gama gyaran gidan ya zo?" "eh fada masa hakan."
Haka dai jamilų ya dinga shiga yana fita yana kashe musu kudi da kuma maganganun na jan hankali, har sai da ya ga ya saye zuciyar su tukunna, domin yanzu ko wuta ya ce'da hálima ta fada za ta afka. Kai ba
ma halima ba hatta yalwa ya saye ta tsaf, domin har
sutturu yake dinka mata ya saya musu kayan abinci, ya
dinka wa kannanta kaya, ga kuma gyaran da ya yi musu
ya sa musu ruwa, ya rushe katangar ya gyara dakin yalwa da yake kamar bola ya sa aka fita da tsummar katifar ya sanya mata gado da katifa da kujeru da sauran kayayyaki masu kyau. Aka yi musu filasta a sabon ganin, sannan aka hada musu wutar lantarki ya dai fito da su tsaf. Wannan abin ya sa suka kara amincewa da shi.
Malam usman tun yana gudun abin yana janye. jiki, har ya fara amincewa da lamarin ya ce da jamilu a
wani zuwa da ya yi.
"tun da dai allah ya sa an'gama fahimtar juna sai kuma a yi yinkurin turo magabatan da maganar aure, domin a san abin yi."
Jin abin da ya ce sai jikin sa ya yi sanyi ya ce a
ransa in har fa ban yi kokarin aiwatar da abin da ya kawo ni ba to lallai zan gudu in bar ladana, dan haka sai
ya sauya salo.
25
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Rannan da yamma afujajan ya zo ya sami yalwa
bayan sun gaisa yake cewa, "ina halima?"
"yanzun nan na aike ta,"
"dama zuwa na yi in gaya mata ana bikin wani
abokina ya kamata mu je ta taya shi murna."
Yalwa ta ce, "to ai babu komai sai kun dawo.
Kai lawandi je ka ka ce halima ta zo a gidan inna
hanne?" ya ce to, ya fice.
Can sai gasu sun shigo, yalwa ta sanar mata
bukatar jamilu. Ta ce to. Ta shirya suka tafi fati. Ba su
suka koma ba sai sha biyu da rabi na dare. Ya kawo ta
kofar gida ya juya abin sa. Yalwa ta kasa barci saboda
fargaba, can sai ta ji dirar mota. Cikin sauri ta tashi ta
leka tana gannsu nan take wani dadi ya kamata ta ce,
"kai na gode allah, amma halima ko lafiya wannan dare
haka?
"Yalwa motarsa ce ta yi faci a hanya sai da ya
nemo mai gyara ya sa masa wata tayar."
"to ai shi kenan ya yi daidai allah ya kyauta."
"au! Yalwa ga wannan ki sai goro in ji shi."
Ai sai kuma ta saki fuska ta ce, 'au to an gode
madalla shi dai baya gajiya."
Halima kam ta badu karshe ‘sakamakon irin
kudin da jamil yake kashe mata, wannan abu ba karamin
bawa mutane mamaki yake ba, domin kuma ba ta da
wani abin yi a yanzu, illa ta yi wanka ta tsala kwalliya
sai fita da jamilu. Za dai a ga fitar su, amma babu mai
cewa ga lokacin dawowarsu. Yanzu ba ta kula kowa a
unguwar nan sai dai jamilu. 'Yan matan ma da suke dan
26
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
yin kawance a da to yanzu sun daina domin tana ganin
yanzų ta yi musu zarra ta goge, ta kile ta yi jawur,
sakamakon mayukan da yake sayo mata da sabulai iriiri. Ga shi yanzu duk inda yake san ya dauke ta ba mai
hana shi, sai su tafi sayayya, ya sayo mata suturu iri-iri.
Yanzu ba ita ba ma har ta asabe kanwarta ba ta rashin
sutura, bare kumá ta kanta duk yayin da ya shigo ita ce
farkon yi kafin kowa ya yi a unguwar nan, ta sake da
jamilu sosai duk kuma irin daran da za su yi in sun fita
yalwa ta daina magana, tun da wai ai ta san suna tare da
jamilu.
Duk unguwar ban da zagin yalwa ba abin da ake
yi, ta bata yarinyar ta da kanta kowa ka gani sai
zundanta ake yi. Ga shi dai ana tsoran masifar ta, amma
ba a fasa zagin ta ba, har malam usman wa suke zagi
wasu kuma sải su ce ai shi babu ruwansa domin matarsa
ce shi ma kansa tafi karfinsa bare kuma shi ya ce zai
mata fada. Sau da yawa mutane sun sha yi wa malam
usman magana cewa don allah ya dinga duba harkokin
da suke gudana a gidansa ya kan ce to shi ya zai yi? Ya
sha yi wa yalwa nasiha a kai sai ta fi shi fada akwai
lokacín da ya yi mata maganar sai ta hana yaran yi masa
magana baki dayansu halima ce mai yi masa magana
domin ita halima ba ruwan ta laifinta daya kawai
wannan yawo, amma ba ta raina ubanta ba, kuma in ya
kira ta ya yi mata fada a boye cewa ta daina zuwa tana
wannan yawan ta kam amsa, amma daga bisani sai ta
koma ruwa, sai dai duk yawan da za ta je ta yi ba ta
kwana, ba ta taba kwana ba, komai dare za ta dawo gida.
27
C
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada Ina zaton za ku yi mamakin jin cewa duk
damar
wannan budurin da ake yi har kawo yau jamilu bai sami cimma burinsa a wajen halima ba, domin har yau
bukatarsa
bai 'samu wata hanya da zai bi ya bullo mata da ba, domin shi abin da yake dubawa kawai shi ne ya sami abin da zai fake da shi ya ja ta zuwa wani gari, to a wannan lokacin ne komai zai iya faruwa. Rannan sai wata dabara ta fado masa ya zo ya sami yalwa ya ce akwai wani yayansa a kaduna bashi da lafiya zai je ya dubu shi, shi ne yake son su tafi tarc da halima. Halima ta ce zani, yalwa ta ce to ai shi kenan ba sai ku je ba, amma dai kar ku yarda ku jima sosai. Ya ce, "ai sati daya ne."
Ta cc, "to shi kenan allah ya kiyayc hanya." 'Amin." ya ce da ita.
sannan
Ya kawo kudi ya bata, ta yi godiya mai yawa, suka fita.
Ba inda ya dosa da halima sai wani hotel suka kama daki, amma ba tare da sanin haliman ba, kun san ba ta iya boko ba, duk kilewar ta dan haka da ta tambaye shi me zai yi anan sai ya ce mata so yake ya huta tafiyar dare zai yi zuwa kadunan, domin tafi dadi. Ba ta yi musu ba ta bi shi sukà shiga dakin da suka kama. Suna ta hira susu cici wannan, su ci wancan, ga lemoka masu dankaran dadi, ga shi dama hirar halima. Suka ci gaba da hira su, sannan a yi ciye-ciye ba su ankara ba har kusan sha biyu na dare, sai halima ta ce wai sai yaushe za mu yi wannan tafiya ne dare fa ya yi? Ya ce la ai ban san dare ya yi ba, wallahi in ina tare da
28
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
ke sai in dinga mance komai dan haka ki bari kawai goabe sai mu wuce. Ta ce in kwana anan? Ya cc to me ус? Ta сe a'a ni dai maidani gida ma dawo da safen. "yanzu ai babu dama mu fita darc ya yi. Shi kenan na ji amma dai don allah ki daurc ki kwana nan din."
"shi kenan zan kwana sai gobe za mu tafi?"
'Ai gari hawaye wa za mu tafi."
Ta ce, 'to."
Iya yaudara da kisisna da iya jan hankalin 'yan mata da nuna kwarewa ba irin wadda jamil bai yi wa halima ba. Daga bisani ya yi nasarar samo kanta, har ma
ya sami abin da ya jima yana nema. Kashe gari kuma ta
ce su tafi ya ce su bar shi kawai su gama kwanakin su a
nan. Nan dai suka zauna har sati gudan ya kare, suka kuma kara wani satin. Sannan ya biya kasuwa ya sayo
mata kayan tsaraba ya sakata a mota suka dawo gida.
Da zuwan su cikin doki yalwa ta tare su ta fara
yi musu sannu da zuwa a cikin murna tana sannunku
mutanan kaduna, amma fa kun sha hanya. Sannan ta kama akwatin ta shigar ciki ta ce su shigo ta ba su ruwa da lemo. Kun san har firij ya saya musu, suna lenton
sayarwa. Yalwa ta zauna suka gaisa da 'jamil tana tambayarsa ya mai jikin? Ya ce da sauki. Ta ce, "amma kaduna da nisa take ko?"
"wallahi saukar mu kenan ko gida ban je ba."
"to yaushe za ka koma gidan?" 'Yanzun zan tafi."
Ya faki idonta ya kalli halima suka hada ido ya
29
15
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
daga mata gira ta yi farfar da ido suka yi murmushi
Sannan ya mika mata tsarabar kaya ne iri-iri masu kyau.
Ya ce duk yayansa ne ya cc a kawo wa yalwa, sannan
kuma halima ta zage jaka kuudi dubu hamsin ta ce gashi
an cc ta kawo mata. Ai nan da nan yalwa sai kuka take
yi, ya mikс.
mana."
gidan."
'Yalwa zan koma sai an kwana biyu."
'Au! Har za ka tafi? Ka tsaya har in gama abinci
"a'a gida zani yalwa."
"shi kenan an gode madalla ka gaida mutanen
"to za su ji da kyau."
Ya mike suka fice tare da halima har wurin
motarsa. Sannan ya dube ta.
"to halima sai yaushe kuma? Kin fa lasa mini
zuma a baki ba zan iya hakuri ba."
"sai dai jibi ka ga yau muka dawo, gobe kuma a
ce mu sake fita?"
"a gaskiya jibi ta yi mini nisa ina laifin ma
goben?"
Ta ce, "to shi kenan, malam dabarar da za mu
yi?"
"yauwa sai goben zan zo."
Suka yi sallama j'a tafi.
30
1
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
3
Kwance tashi asarar kwana. Yau kusan wata
hudu kenan da sauyin salon soyayya tsakanin halima da
jamilu yanzu in har ka ga halima ba za ka taba zaton 'yar
talaka ba ce, domin kuwa ta dawo abin kwatance shi
kansa jamilu yanzu ba shi da wata magana sai ta halima,
domin in yana tare da halima sai ya yi sati biyu bai je
gidan iyayensa ba. Uban ya rasa in da yake zuwa ya
lafe, domin ya yi iya bincikensa ya rasa gane inda ya
makalle, kullum a cikin karya yake yi wa uban, yau ya
ce yana kaduna wurin wan, ya kasance dan yar alhaji.
Gobe ya ce sokoto ya je wurin wani abokinsa da suka yi
makaranta tare. Abin da ba wani cikakkiyar gaskiya, to
amma da yake uban baya son 6ata wa yaran baya matsa
bincike sai ya hakura ya kyale shi, illa dai