А
kalla ke kan ki za ki yi talatin da biyu, ita kuma ina zaton
shekarunta ashirn da takwas, kuma ba arabi ba boko gara
ke ma kina makaranta har ma kin gama, ga shi yanzu kina
aikinki to ita fa? Gfa safiya 'yarta ta fari ajinta biyu a
makarantar gaba da firamare."
Ta ce, 'to ai ni wannan abu baba ban san irin sa ba,
wai nì na komo nan din ga shi a nan din ma abu na neman
gagara."
Ta ce, "ba komai allah zai kawo miki naki rabon da
izininsa, ke dai ki lazamci addu'a domin takobin mumuni
ce, kuma sannan ki dinga yawaita istigifari, saboda abin da
kika aikata a baya kya sami wani rangwamin."
Ai wannan magana sai ta tuno mata cewa akwai
wata magana da suka yi da malam idi cewa ta zo bayan ta
haihu zai yi mata bulala tamanin da ake wa duk wata
budurwa wacce ta yi zina. Nan take ta ayyana gobe za ta je
domin ta sauke wa kanta nauyi ta huta ma ranta tun da dai
aure in ta yi shi kenan.
Tana cikin wannan tunani ne sai ta ji an ce wai ta
zo in ji alhaji usaini. Ai nan da nan ta mike tana rawar jiki
ta dubi agogo goma saura kwata, har baba- abu ta soma
barci, sai ta tashe ta ce, 'baba alhaji ne fa ya zo."
"a daran nan?"
"kila wani abu ne ya tare shi kin san shi baya san
ya yi alkawari ya fasa."
107
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
"to shi kenan je ki sai kin dawo." ta ce to. Cikin
doki ta fice, to amma tana zuwa da ta ga yana motarsa bai
fito ba ma sai jikinta ya yi sanyi ta zaga gurin da yake ta yi
masa sallama ya amsa, gami da zuge glass din bangaren
sa. Sannan ay ce, "shigo mu tafi?"
Ta ce, 'alhaji ina za mu je a wannan daren?"
"unguwa za ki raka ni."
Ta ce, 'to bari in je in tambayi baba abu tukunna."
'a'a ai ba zama za mu yi ba, yanzu za mu dawo in mun
dawo kuma sauke ki zan yi ki shiga gida in juya."
Ta ce, 'to shi kenan mu je."
Ta shiga ya ja suka bar layin suka hau titi. Kallon
sa kawai take har suka isa wani kyakkyawan gida kato.
Suna shiga ya yi parking ya fito. Sannan ita ma ta
fito ta tsaya tana kallonsa wani fangare ya nufa. Sannan ya
ce ta shigo ita ma tabi bayansa. Suna shiga ani katon falo
kyakkyawa suka sami guri suka zauna a wasu kyawawan
kujeru, wadanda suke yi da'ira a tsakiyar falon. Alhaji ya
dubi halima ya yi murmushi ya cе,
'Ki nada bukatar in mun yi auren in aje ki a
wannan gidan?"
Ta ce, "me zai hana alhaji."
"to shi kenan nan za ki zauna shi ya sa ma na kawo
ki ki ga guri, domin nan da sati za a daura mana aure."
Cikin dadı da murna zuciyar ta fari tas, amma sai
ta boye ba ta nuna masa ba.-Ya mike ya matso kusa da ita
ya ce, 'ya kamata mu dan ji dumin juna kafin zuwan
ranar."
Cikin mamaki ta matsa can nesa ta ce, 'haba alhaji
kana sane fa da cewa wannan abu haramun ne ta ya ya zan
108
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
amince?"
Ya ce, 'ai ba wani abu za a yi ba kawai ki dan bani
hadin kai na minti biyu."
Cikin shashshekar kuka ta ce, 'alhaji ban san haka
kake ba, in da a ce na san haka kake da ba zan biyo ka ba.
To amma shi kenan na gode maida ni gida in kuma ka ki
zan tafi ko a kafa ne?"
Shiru kawai ya yi ya zuba mata ido yana kallonta
har ta yi shiru. Sannan ya ce, "kin ki ni ko? To na gode shi
kenan je ki."
Cikin sauri ta mike za ta fita, sai ya yi kiran sunan
ta, 'halima." ta amsa, amma ba ta waigo ba, domin
idanunta cike yake da kwalla. Ya ce, "yanzu halima tafiya
za ki yi??"
"to ya kake so in yi maka? Ni wannan bukata taka
ba sana'a ta ba ce, ka ga kuwa sai in tafi in ya so sai kai ma
ka hakura da auran allah sai ya baka wacce ta fi ni, amma
ka ba ni mamaki a yadda na ganka da girma da daraja da
mutunci da kamala ina murna allah ya bani kamilin miji
sai gashi abun bakin çiki wai kai kake furta mini kalmar da
ban taba zaton jin ta a bakinka a aynzu ba."
Ta ci gaba.
'Ba komai haka allah ya so ni na tafi."
Ya ce, 'a'a tsaya in maida ke gida."
"ka bar shi kawai zan sami abin hawa a bakin titi."
ta fice abin ta sai da ta kai bakin gate sai ta ga ba za ta iya
budewa ba, sai ta koma ta ce, "ka zo ka buďe mini in fita."
ya yi murmsuhi ya ce, 'halima kenan abin da ya sa na kyale
ki har kika fita dan na ga kin dau zafi ne, amma ba dan
haka ba zan sanar da ke dalilina na furta miki wannan
109
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharadu
magana ba, amma yanzu in kin yi mini izini ki zauna in
fada miki."
Ta ce, 'ka ga sha daya ta kusa yanzu in har babab
ta leka ba ta ganni ba za ta nemi inda nake in ko tá ga ba
na area mu sai ta tuhume ni inda na je, gara ka maida ni in
ya so ka fada mini a can kofar gidan mu."
"to shi kenan mu je in kai ke." ta ce to.
Bayan sun iso ne ya tsaya ta fita. Sannan ya rakota
har ksua da kofa. Sannan ya tsaya ya ce, "halima." ta amsa
gami da kallonsa cikin ido dan jin abin da zai ce sai ya ce,
'alima ina sonki ina kaunarki wallahi wannan abin da na y!
miki na yi miki ne kawai dan na gwda ki in ga halin ki,
domin a gaskiya na tsargu da abin da kanwarki ta fada, to
amma tun da ba halinki ba ne shi kenan zan turo a daura
mana aure ranar asabar din nan mai zuwa."
Halima ta ce, "shi kenan allah ya kai mu."
Suka yi sallama akan zai dawo gobe in sha allahu.
Haka dai suka rabu tana mamakin abin da ya yi mata, to
amma kalaminsa sun sa ta hakura a kan dole domin in ma
ta ki auran nasa ba ta san wanda zai zo kuma ba.
Kashe gari halima sammako ta yi ta ce za ta je can
gidan su wato medilee baba abu ta-ce in ce ko lafiya? Tа се
lafiya kalau. Ta ce mata shi kenan ki gaishe su. Ta ce to.
Ta kama hanya ta tafi. Da zuwa ko gidan ma ba ta nufa ba
sai gidan malam idi na layin su ta same shi yana karatu a
zaure ta sanar masa cewa ta zo-ne akan batun wannan
hukunci da suka taba magana cewa sai an yanke mata
hukuncin bulala tamanin ne za ta fita daga fushin ubangiji
dangane da abin da suka aikata. Ya ce to shi kenan kin ko
yi sa'a yanzu ba kowa sai ai miki bulalar ki ki tafi ba tare
110
Kwadi Buri Jana Amina 4. Sharada
da sanin wani ba ma tun da don allah kika yi. To babu
wanda zai sani, sai shi din da kika ya yi domin sa, Haka
ma in da ba ki zo ba yana sane da ke sai kin je kin same shi.
Nan da nan ya yi mata bulalar ta tamanin kamar yadda shari'a ta tanadar. Ai ko nan'da nan jikinta ya rikice
domin sai da ta sume. Bayan ta farfado ya ce za ta iya
zuwa gida ko sai an kai ta? Ta ce ba za ta iya zuwa ba. Ya
sa mai adaidaita sahun kofar gidan sa ya dauke ta, domin
maida ita gida. Ta ce a kai ta gwale kar a kai ta gidan yalwa, domin in an kai ta gidan yalwa za ta fara babatu har
gari kowa ya sani, kuma zancen dyniya baya buya zai iya
zuwa kunan alhaji usaini. Nan da nan aka kai ta har kofar
gidan baba abu. Tana shiga baba abu ta ganta ta ce cikin
fargaba.
"lafiya halima?"
"lafiya kalau."
"ina fa lafiya kin tafi kalau kin dawo jiki duk jini?"
Ta ce cikin jin ciwo, 'wallahi baba ba wani abu ne
ya same ni ba zuwa na yi aka wanke ni bisa ga laifina na zina."
Ta ce, "kamar ya ya?"
"hukuncin bulalar aka yi mini."
"allahu akbar shi kenan kin hutawa kan ki. Allah
ya kiyaye gaba ya kara rufa man asirt."
'Amin baba."
Sannan baba ta ce, "to yanzu abin da ya gama a yi shi ne ki zo mu je in kai ki asibiti a baki magunguna shi kenan." ta ce'to.
Ta bude bayan ta ta ce, 'baba dubi baya na ki gani."
111
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
baba ta duba ta ce, "kai! Kai!! Kai!!! Ai duk bayan a fashe
yake."
'Wallahi ni na san irin azabar da nake ji."
"to ke ko bulala tamanin ai da yawa ko goma ce
ma mutum ai zai dandana, bare tamanin in ce ko dage
karinsa ya dinga yi kamar ya sami jaki?"
"oho! Ni dai a lokacin da na fara jin zafin sai na
cikuwikuye zanina na cusa a bakina dan kar in yi kara ta
janyo hankalin jama'a a san abin da nake ciki. A gaskiya
baba ba karamin karfin hali na yi ba."
'Ai shi kenan allah ya kiyaye gaba ga dukkan
alamu wanda ya yi haka ai ba shi da niyar komawa ga sake
aikata wani sabon makamancin wannan."
"wallahi kuwa."
Sun je asibiti an yi mata allurai da magunguna suka
komo gida. Baba abu ta ce ai yau in al aji ya zo za ki iya
fita kuwa? Ta ce kayya baba ba zan iya fita ba." ta ce to ya
ya za a yi kenan? Ta ce kawai sai in ce masa ba ni da
lafiya. Ta ce ai kin san shi cewa zai yi ki zo yay kai ki
asibiti. Ta ce ai sai in ce masa na je asibitin. Ta ce to shi
kenan.
Haka ko aka yi bayan ya zo ne aka shaída masa ba
ta da lafiya, sai ya shiga har ciki, domin ya duba ta. Yanzu
ya same ta a kwance ya tambaya ta me yà same ta. Ta fada
masa cewar wato zazzabi ne sai ya ce to su je asibiti. Sai ta
ce ai ta je har ta sayi magunguna ta sha. Ya ce ina katin?
Nan sai jikinta ya yi sanyi. Haka dai ta fito da shi ta nuna
masa sai ya ga an saka mata babin liman wato duka ne
kuma magungunan ma na maganin taruwar jini ne da kuma
gajiya da dai sauran su. Cikin sauri ya kalleta ya kara
112
Kwadi Bari Jana Aminu A. Sharada
kallon sunan mai katin ya kuma tabbatar ita ce sai ya ce,
'Halima ai duka ne wa ya yi miki wannan danyan
aikin?" ta yi shiru hawaye na zuba mata dan fargabar abin
da zai biyo baya ya ce cikin tsawa, 'ina magana kina jina
wai waye ya yi miki wannan abin?"
Nan da nan baba abu ta amshe.
"waye ko ban da kanin mahaifinta?"
Ya ce, "waye kenan mahaifin nata me ya hada su
har ya yi mata wannan mummunan dukan haka?"
Ta ce, "wai saboda ta ce ba ta son mijin da ya kawo
mata har gida ya zo ya dake ta."
Ya ce, 'amma kuka kyale shi?"
'A'a alhaji kanin ubanta ne fa uwa daya uba daya
to me zance?"
'Ai wannan zalunci ne a ina yake da zama?"
"a kauye yake."
"to shi kenan ya yi na farko ya yi na karshe, na ce
aure kuma babu fashe. Ai zaluncin ya yi yawa yanzu su
mahaifan nata suna kallo?"
"to me za su ce masa magana ai tana gurin yarinya
ita kuma ta.ce kai take so ka ga ba shi da magana sai dai
dukan."
"a to ya dai yi na farko ya yi na karshe domin
wallahi ko uban ta ne ya yi mata wannan dukan sai na yi
kararsa, an bi mata hakkinta."
"kai dai a bar maganar, daurin aure kuma babu
fashi sai an yi."
Ya ce, 'yauwa shi kenan. To ni zan tafi, amma sai
na kai ta wani asibiti tukunna."
"to alhaji ai ba komai."
113
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Sannan ta yunkura da kyar baba ta kama mata suka
fita har gurin motarsa. Sannan bayan ta shiga ya kai ta
asibiti aka aunata sosai aka ba ta wasu magunguna masu
kyau. Sannan ya maido ta gida ya wuce abinsa.
An dai yi biki sosai abin gwanin ban sha'awa kowa
na san barka. Baba abu ba ta yi gayya a can unguwarsu
halima ba, gudun kar wani ya tona asirin 6oye sai ji suka
yi halima ta yi aure wadanda aka gayya ta sai surukan
goggo hanne domin ita ta tsufa sosai, 'ya'yan basa barinta
fita ko'ina. Domin kafarta na mata ciwo kun san jikin
girma.
Bayan an gama biki tsaf kowa ya fashe sai alhaji
usaini ya kira matarsa hajiya jamila ya tara su a dakinsa
har amarya halima. Ya fara musu nasihar su zauna da
junansu lafiya ban da yawan rigingimu, domin shi ba mai
san tashin hankali ba ne. Hajiya jamila ta e,
"ai ba komai alhaji sai kai ma ka dinga kamantawa,
domin in gida ya gyaru daga namiji ne, in ma ya bace to
shi ne in har mu mutum yana kamanta gaskiya ba wai sa
rai ba babu ta yadda za a yi wasu fitintinu su dinga kunno
kai cikin gidansa."
Ya ce to ya dauki alkawari zai daidai ta na sa
bangaren, domin ganin an sami zaman lafiya da kwanciyar
hankali.
Tun da aka yi bikin, sai hajiya jamila ta kara jan
maryam a jiki, ta nuna mata so fiye da da, domin ta kwabi
alhaji cewa kar ya soma nunawa halima maryam ba 'yar ta
ba ce, 'yar tsintuwa ce. Kuma ya amince da hakan dan ya
sami zaman lafiya.
Suna zaman su lafiya, sai dai hajiya jamila mace ce
114
コ
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
mai shegen san girman kan tsiya. Sannan kuma ga gadara
ko juyin miya ba ta bari maryam ta yi, wa halima aunty
take cewa halima, amma sai cewa ta yi me ye wani aunty
in za ki ce halima ki ce, banza uwar iyayen tsiya. Ta cе,
"haba umma in na ce halima ai abbana ba zai ji dadi ba,
kin ga aunty da nake kiranta ba karamin dadi yake ji ba."
"a to dama tun da ke ubanki ne ai sai ki faranta
masa, ni ki munana mini: To wallahi daga aunty babu kari,
kin ji ko?"
"to umma."
Halima komai a daddare take yinsa a cikin gidan,
domin kuwa hajiya jamila ta fita iko akan komai, ku
makullin store yana hannunta, sai ta tambaye ta. Sannan ta
ba ta, kuma kafin ma ta ba ta sai ta san me za ta yi, domin
wai irin su 'ya'yana marasa abu hannu sunan da matsala in
sun auri mai kudi za su dinga satar abinci suna kaiwa
iyayen su. Ko abinci halima za ta yi sai ta tambayi hajiya
jamila wane iri za ta girka, ga shi dai akwai masu aiki a
gidan; amma sai hajiya jamila ta hana su yi wa halima aiki
wai ai ita ta saba da aikin wahala a gida su kyale ta ta yi da
kanta. Da yake masu aikin gidan nan kaf tsoran hajiya
jamila suke yi mazan su da matan su ba sa yi wa halima
aikin komai. Ita ke yin abin ta a gidan, ta yi abincin kuma
ta rabawa masu aikin da masu gadin suna mike da kafa.
Alhaji usaini nasa ake masa, amma sai hajiya jamila in
girkin halima ne ta sa ta ta hada nasa da na mutanen gidan
sai kuma ta kwauranta mata magi da nama sai ka ji girkin
kamar an wanke kai, babu mai iya ci sai a zube shi a jabejabe a cikin gidan. Shi kansa alhajin baya iya ci sai duk
ranar girkin halima ya tafi can rasturant ya ci abinci bai san
115
Kwadi Buri Jana Amina A. Sharada
dalilin rashin dadin abincin ba, kuma ya san dal masu
girkin nan dai daya ne ba bambanci. To amma baya
magana ita ko halima sai in abin ya dame ta sai ta shige
daki ta yi ta faman kuka. Kuma wani abin allah jininsu ya
hadu da maryam a kullum ta ga halima cikin wannan hali
sai hankalinta ya tash, ta faki idan uwar ta shiga Bangaran
haliman ta dinga rarrashinta tana cewa,
'Aunty wai ke da waye? Aunty don allah ki yi
hakuri ba na san in ga kina cikin kunci."
Sai halima ta ce mata ba komai. Ita ma halima tana
matukar son maryam. Sáu da yawa alhaji usaini da
sa'adiyya yake kiran halima, amma hajiya jamila dubu take
ce mata, har ma bakinta ya saba da dubun, ita ma halîman
amsawa take dan ba yarda za ta yi.
Tana zaune ta yi jigum sai alhaji usaini ya shigo ya
same ta a zaune ya ce, "wai ni sadiyya me yake damun ki
ne kin bi duk kin rame a kullum sai in gan ki kin yi jigum
kina tunani?" sai ta ce ba koami. Ya ce a'a akwai dalili. Tа
ce wallahi babu wani abu. Ya ce to na fi san ki dinga sakin
ranki ai bai kamata a dinga zuwa ana samun ki cikin
wannan hali ba.
In ba ke ce da da girki ba, babu yadda za a yi ta
tunkari 6angaran alhaji, amma in ita ce da girki hajiya
jamila na can har sai lokacin barci sannan da kyar tana
cika tana batsewa ta baro dakin. Da halima ta ga haka sai
ta daina shiga sai in shi ya yi mata magana ako da yaushe
tana dakinta, wani lokaci suna tare da maryam suna hira
shi ne hajiya jamila ta ce wai maryam munafarci take zuwa
yi dakin dubu, dan haka ta daina. Halima ta yi ta mamakin
hajiya jamila ta ce in ban da abin hajiya ai mai san danka
116
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
tunanin in hajiya jamila ta sani to ta shiga uku.
Kwanci tashi yau watan halima biyar da auran duk
cikin 'yan'uwanta babu mai zuwa, sai baba abu kawai,
domin gudun, kar su lawan su je su gano gidan su dinga
zuwa har su sa a korota, shi ya sa ba wanda ya sake ya
nuna musu gidan. Kowacce shawara ce da baba abu suke
kulawa har halin da take ciki a game da hajiya jamila ta
sanar mata. Baba abu ta ce, sai hakuri halima da sannu
abin zai dinga saki, kin san halin mai gidan ki in kika fara
kai masa kara ke zai bawa rashin gaskiya ki yi hakuri har
idansa ya nuna masa. Ta ce to shi kenan baba.
Yau wata uku kenan da samun cikin halima tana so
ta fada tana fargabar abin da zai biyo baya game da hajiya
jamila. Shiru ta yi ta ce a ranta cikin dai dan duma ne yado
yake in ya bayyana sa gani, amma ba zan fada abu ya
zame mini dan gyauto ba. Kwanci tashi sai halima ta fara
laulayi ita ce yawan amai, ga yawan kwanciya, ga shi ba ta
san shiga kitchen saboda kamshin dahuwa wahala yake ba
ta. Sannu a hankali har dai alhaji ya gano cewa ba ta da
lafiya sai ya ce ta shirya'ya kaita asibiti. Ta shirya suka
tafi. Da za su fita sai da ya ce ta biya ta sanarwa hajiya zai
je asibiti dan kar su fita bai san sun fita ba, sai da ta gama
gaya mata sai ta dako tsalle.
"yana ina alhajin?"
'Ga shi can yana jirana a mota."
Ta yi saurin fita ta same shi. Ta ce, 'alhaji ai da
kamata ya yi ka kai ta kyamis (chemist) yaushe har sai kun
wani je asibiti?"
"ai da ma ba asibiti za mu je ba kyamis za mu
ya rufe kofar motar ya ja suka tafi abin
le
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
tunanin in hajiya jamila ta sani to ta shiga uku.
Kwanci tashi yau watan halima biyar da auran duk
cikin 'yan'uwanta babu mai zuwa, sai baba abu kawai,
domin gudun, kar su lawan su je su gano gidan su dinga
zuwa har su sa a korota, shi ya sa ba wanda ya sake ya
nuna musu gidan. Kowacce shawara ce da baba abu suke
kulawa har halin da take ciki a game da hajiya jamila ta
sanar mata. Baba abu ta ce, sai hakuri halima da sannu
abin zai dinga saki, kin san halin mai gidan ki in kika fara
kai masa kara ke zai bawa rashin gaskiya ki yi hakuri har
idansa ya nuna masa. Ta ce to shi kenan baba.
Yau wata uku kenan da samun cikin halima tana so
ta fada tana fargabar abin da zai biyo baya game da hajiya
jamila. Shiru ta yi ta ce a ranta cikin dai dan duma ne yado
yake in ya bayyana sa gani, amma ba zan fada abu ya
zame mini dan gyauto ba. Kwanci tashi sai halima ta fara
laulayi ita ce yawan amai, ga yawan kwanciya, ga shi ba ta
san shiga kitchen saboda kamshin dahuwa wahala yake ba
ta. Sannu a hankali har dai alhaji ya gano cewa ba ta da
lafiya sai ya ce ta shirya 'ya kaita asibiti. Ta shirya suka
tafi. Da za su fita sai da ya ce ta biya ta sanarwa hajiya zai
je asibiti dan kar su fita bai san sun fita ba, sai da ta gama
gaya mata sai ta dako tsalle.
"yana ina alhajin?"
'Ga shi can yana jirana a mota."
Ta yi saurin fita ta same shi. Ta ce, 'alhaji ai da
kamata ya yi ka kai ta kyamis (chemist) yaushe har sai kun
wani je asibiti?"
"ai da ma ba asibiti za mu je ba kyamis za mu je."
ya rufe kofar motar ya ja suka tafi abin su, yana mita.
118
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
'Kai hajiya akwai ta da bakin kishi, to me ye dan
an je asibitin? Ta fiye neman husuma a yi magana ta tayar
wa da mutane hakarkari da hayaniya."
Halima ta yi murmushi ta ce, 'alhaji ni fa ina son in
gaya ma wani abu ina tunanin in hajiya ta sani ban san
abin da za ta yi ba."
Ya ce, 'mene ne?"
'Ciki fa gare ni wata uku........"
Ai sauran kiris kan motar ya kwace daga hannunsa.
Allah ya kiyaye, ya ce cikin rawar baki, "ciki halima?"
"hakika."
Ina ai komawa ya yi gefe ya tsaida motar ya juyo
ya zura mata ido kawai ya ma rasa me zai ce, domin abin
ba zato. Sai ta ce, 'alhaji ka gode wa allah bisa wannan
baiwa da babban rabo da ya baka."
Cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa alhaji ya
yi shiru kawai sai ga hawaye na gudu a fuskarsa. Ya daga
hannunsa sama domin yin addu'a ta godiya ga ubangiji mai
kowa mai komai kamar haka.
"subhannallahi walhamdullillahi allahu akbar."
Wannan tana daya daga cikin addu'ar da in farin
ciki ya same ka ko bakin ciki za ka fade ta. Ya dubi halima
ya ce, 'tun da nake a duniya ban taa jin abin da ya faranta
mini rai kamar yau ba, wallahi kin yi mini albishir da ba
zan taba mantawa da ke ba."
Sadiya kanta sunkuye tana murmushin farin ciki
mijinta ya yi murna kamar bai taba haihuwa ba. Sai ta dan
dago kai ta kalle shi.
"amma fa ina tsoran hajiya wallahi."
"ki cire duk wani shakku ko tsoro ai wannan abu
119
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
yin allah ne babu wanda ya isa ya hana yin allah."
'Haka ne."
Kwanci tashi hajiya jamila ba ta san maganar ciki
ba, sai gani take abu na tsiri tun tana kin yin magana har
dai ta kasa hakuri. Rannan suna zaune da alhaji ranar
girkinta sai kawai ta ce masa, "wai ni alhaji dubu ko ciki
gare ta ne?"
Ya ce, "me kika gani?"
"ni gani nake kamar cikin tana girma kuma sai ta
dinga wasu abubuwa irin na masu ciki kamar zubda
yawu."
ba."
"kila cikin gare ta kin san ta da kunya ba za ta fada
Ai nan da nan sai gaban hajiya jamila ya fadi ta ce,
"ta6dijan! Yanzu ya zan yi?"
"to ya ko za ki yi? Ai komai nufin allah ne.""
"alhaji ka ga fa yarinyar nan ba tawa ba ce, kai ma
ka sani, ga shi kai ka haihu ni ba ni da da kenan matsalar
haihuwar ba a gareka take ba a kaina take ko?"
Nan da nan sai tausayin ta ya kama shi ya ce, "iyi
akan ki take sai dai kawai mu yi miki addu'a allah ya ba ki
ke ma."
Nan da nan sai ta fashe da kuka ta ce, 'shi kenan
yanzu dubu za ta zama 'yar gaban goshi tun da har ta sami
karuwa da kai."
"a'a ba haka ba ne ai kowaoce da halinta za ta
zauna kin ga ke ce uwar gidana da a ce ke wata mai wayo
ce sai ki yi zaman ku lafiya ba sauran wasu fitintunu kin ga
zan sami nutsuwa nima ai duk abin da aka samu na mu ne
ba ki daya. Hajiya jamila dan ki fan sadiya.ne, dan sadiya
120
Kwadi Bari Jana
dan ki ne?"
"ba sai za ta bari ba."
Amina A. Sharada
"bari kai. To wai ke za ki nuna mata bake kika
haifi maryam ba ne?"
"haba ai ni kai nake ji."
"to ki nuna mata cewa maryam 'yar ki ce kar ki
fasa kin ga ko da za ta yi miki wani hali irin na ku na mata
ta san cewa ke ma kin haihu a gidan."
"to shi kenan."
13
Al'amarin soyayyar maryam da bashir na nan sai
abin da ya karu, domin dai ba sa iya rufa kwana biyu ba su
ga junan su ba. Duk da cewa gida daya suke tare abbansu
ya yi ya yi su hakurewa juna sun ki su amince. Ya gaji ya
hakura ya zuba musu ido, domin dai ya san da wuya
wannan abu ya dorc.
Alhaji usaini na