ni? Wato shi. a nufinsa
bazawara ya dauke ni bayan ko lalle ba a ta6a samin ba?
To amma zan iya cewa ni bazawara ce dan samawa
kaina rufin asiri, domin in na ce ni budurwa ce zai gano
wani abu nan gaba."
"ya kika yi shiru?"
Ta ce, 'alhaji ai ni mamaki ka bani domin in ban
yi idda ba ai ba zan saurare ka ba ma, bare in kawo ka
gidan mu; domin manzon allah (s.a.w.) Ya ce "kar ku yi
neman aure cikin idda."
91
46
Kwadi Bari Java Amina 4. Sharuda
Ya cc, "sadaka rasululil karim. Wannan haka
yake kina da yara ne?"
Ta ce, 'wa ni? 'Ya ta daya ce kuma ta rasu.""
Ya ce, 'allah sarki allah ya ji kanta."
'Amin."
"ko zan iya sanin me ye dalilin rabuwar ki da wancan
tsohon mijin naki?"
"eh ba wani abu ba ne ya rabu mu ba illa
iyayensa da ba sa sona sun takura masa lalai sai ya rabu
da ni, shi kuma ya bi umarnin su domin ya faranta musu
ya sake ni. Wannan shi ne kawai dalil."
Ya ce, "Karewar zama ce. Al in zama ya kare sai
ki ga sanadi kadan an rabu. Ba rabonsa ba ce rabo na се.
Yanzu dai mu koma kan maganar mu ni fa ba na san a
dauki tsawon loakci da wuri na ke son auran nan."
"to ai babu wani abu sai a yi da wurin,"
Ya ce, "yauwa ni yanzu za koma in na sake
komowa 2a a san abinda ke cik
Ta ce, 'to shi kenan."
Ya mike suka yi şallama ya tafi, akan cewa zai
komo ranar juma'a wato sauran kwana hudu kenan.
Wannan shehakar bashir zai kammala karatunsa
na gaba da secondary yayin' da ita kuma maryam take
matakin farko a makarantar gaba da secondary din ita
ma. Tuni bashir ya fara shirye-shiryen komowa gida
babu abin da yake sai doki, dan ya zo ya ga maryam ya
take, domin tun daga wayar da ya taba yi mata yake
tunanin halin da za ta shiga. Koma ta shiga har ma yake
ta faman tunanin kar dai hajiya jamila ta sanar mata
92
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
cewa tsinto ta aka yi, domin shi ya san komai da cewa
ba shi da wani wayo lokacin da aka tsinto tan. Mana'a
bai wuce shckara goma ba, ko ma yana da wayon to zai
iya mance wasu abubuwan in aka yi la'akari da wayan
shekarun da aka kwashe wato har shekara goma sha
shida.
Maryam kam yanzu ta dan sami saukin hajiya
jamila ba ta dakura mata sosai, har ma takan dan zauna
su,yi hira, kuma takan gaya mata cewa bashir ya kusa
dawowa me ya kamata a yi mishi na maraba. Shi ne ta
ce ya kamata a yi mishi shirye-shirye masu kayatarwa,
ciki ko har da girki. Nan dai suka zauna suna tattauna
abin da ya kamata cansai ga abba ya shigo wato alhaji
usaini nan ya zauna ana ta faman hira da shi, da kuma
shawarwarin abin da za a yi wa bashir, domin faranta
masa bashir yaro ne mai biyayya ga iyaye, duk abin da
iyayensa suka sa shi ko da ransa bai so ba zai yi dan ya
faranta musu shi ya sa alhaji usaini ke matukar son
yaron. Abu daya ne za ka umarci bashir ya ki sai
maganar maryam in har abin ya sabawa san ransa to ba
ko zai yi shi ba, kowa ya san wannan dan haka mutum
daya ne yake masa dole akan maryam ya hakura shi ne
alhaji hassan, wato mahaifinsa. Domin sanin cewa yana
da zafi sosai, amma duk da haka wani sa'in baya yarda
da wani abin.
Yau ce ranar dawowar bashir dan haka maryam
da mama wato hajiya jamila suna ta faman shirye-shirye
an gyara gida, an shirya shi ko'ina ya hadu sai kamshi
yake tashi. Domin gidan ya turaru da turaruka kun san
93
47
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
sana'ar su ce dama. Bare yanzu idonsu ya bdue sun san
sirrin turaruka kala-kala, dan haka ko harabar gidan ka
shiga za ka ji kamshi. Sai biyar na yamma bashir ya iso
kano, dan haka sai suka shirya tsam, domin tararsa a
aiport. Alhaji usaini shi ne zai kai su. Hajiya jamila ta ce
har ita za a je tarar dan nata, dan haka sai suka yi
kwalliya maryam wani tsadaddan less ta sanya mai
ruwan zuma riga da siket da dan kwali. Ya yi mata
bala'in kyau sosai. Sai wani dan mayafi irin na 'yan mata
da ta yafa shi ma kalar less din. Sannan farin takalmi da
jaka kuma ya sha fashion kalar kayan, har abin hannu ga
wani kamshi mai dadi da ke tasi a jikinta, gashi dama ta
kara girma wato a yanzu ta zama budurwa sosai, ba
kamar yadda bashir ya tafi ya bar ta ba. Kyanta ya kara
fitowa gashin nan har gadon bayanta, dan ma tana nade
shi, domn haramun ne bace ta fito waje da gashin ta. Ko
da sili daya ma wasu su gani ko da budurwa wacce in
dai baliga cе.
Don haka a yi hattara. Maryam ba ta barin gashin
ta ya bayyana kuma tama fi yawan amfani da hijabi dan
dai wannan karon ta ga damar. sanya mayafi duk da
cewa karami ne babu inda surar jikinta ta bayyana,
domin hajiya jamila ba ta barin ta wanan kwaliyar
banzar.
Suna zuwa a daidai lokacin jirgin su bashir ya
sauka yayin da fasinjojin ke ta haramar fitowa, su kuma
'yan'uwa na ta zare ido ko za su ga na su. To suma su
maryam suna waje suna hange. Can sai suka hango shi
ya fito. Ai ko sai suka fara daga masa hannu har ya
94
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
hange su ya nufo inda suke. Wata hadaddiyar shadda ce
a jikisna galila ta sha aiki irin aikin nan da ake yinsa har
kasa, haka tun daga kafada har hannu. Shaddar dank
blue ce ta yi masa kyau sosai. Sam bai san sanya
kananun kaya shi ya sa ma mafiya yawan dunkunan sa
duk abin da ya danganci yadi ne ko shadda ko na wani
abun dai. Yana zuwa ya rungume abba wato alhaji
usaini. Sannan ya durkusa ya gaida mama, hajiya jamila.
Sannan ya tsaida idonunsa a kan maryam kir ba tare da
ya ce komai ba, ahr sai da alhaji usaini ya yi gyaran
murya. Sannan cikin jin kunya ya shafa gashin kansa ya
sunkuyar da kai ya ce cikin kasa da murya.
"maryam an girma.'
Ta yi murmushi ta sunkuyar da kai ganin su abba
na gurin ta ce, "yaya sannu da zuwa."
"yauwa."
Sannan suka juya zuwa gurin motar su abin da
ya hana alhaji hassan zuwa dan baya gari ne da shi zại
zo ya dauke shi
Suna kan, hanyar su ta komawa gida hajiya
jamila na gaba dralhaji usaini, su ko su maryam na baya
suna dan taba fira kadan-kadan, ba tare da su bajiya
jamila suna jin hirar su ba, domin suma ta su hirar suke
yi. Bashir ya kalli maryam ya yi murmushi, yayin da ita
kuma take satar kallon sa, domin kunya ta hana ta
kallonsa sosai Sai in ya kalli wani wajen sai ta zura
masa ido. Hakika bashir ya hadu karshe, shi ba fari ne
can ba, amma yana da dan haske. Sannan kuma yana da
dan tsayi, amma ba can ba, gashi da dogon hanci da
95
1 Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
manyan ido. A warwaje idanunsa suke tulutulu kuma
sun yi wa fuskar kyau sosai ga wani siririn saje da ya
ajiye. Sannan ga gashin bakin nan shi ma siriri.
Hakorinsa na sama da siririyar wushirya mabaiyaniya
sabanin maryam da take da tata wushiryar a tsakiyar
hakorin kasa, kuma kowanne ya dace da shi. Gaskiya
bashir ba wai boyayyan kyau ne da shi ba. Kallo daya za
kai masa ka gano cewa shi kyakkyawa ne, domin
mabaiyyanin kyau gare shi.
"maryam kin yi shiru ba kya yi mini magana
kamar ba ki sanni ba."
Cikin alamar zancen bebaye ta nuna masa cewa
kunyar su mama da abba take ji. Ya yi murmushi. Har
suka je gida idanunsa sun ki aukewa daga kanta.
Bayan sun je gida ne suka ci suka sha, suka yi
hani'an. Sannan ya tashi ya koma dakinsa wanda dama
tuni maryam ta gyara masa. Ya bude ya shiga ya watsa
ruwa. Sannan ya dan zauna dan ya huta. Hajiya jamila ta
ce, "alhaji in çe ko ka gani da idonka?"
Ya ce, 'me fa?"
"kai yanzu ba ka lura da irin kallon da yaran nan
suke wa junan su ba?"
Ya ce, "na gani mana hajiya. To yanzu ya za a yi
abin dai da ake gudu shi yake shirin faruwa."
'Wane irin yake shirin faruwa? Ya ma faru."
"to yanzu ya za a bullowa lamarin?"
'A to nima wallahi ban sani ba, ka ga kuma alhaji
hassan in ya san wannan lamarin mun shiga uku kawai
dai mu nuna musu kamar ba mu san komai ba. Sannan
96
3
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
kuma mu gargade su da kar su yarda su nuna wa kan su
kauna, domin ba za mu amince ba."
Ya ce, "lallai ba ki da hankali ai komai kika gani
daga allah ne ni wallahi in har suna san junan su ba zan
hana ba, sai dai duk abin da zai yi ya yi. Haba mutum a
dinga jin tsoronsa kamar wani mala'ikan mutuwa."
Ta ce, "to ni dai babu ruwana wallahi a gaskiya
rigima ce wannan tsantsa ba na san abin da zai zo y
taba zumuncin ku."
Ya ce, "ai daga baya zai gane in ma ya ki in da
rabo ai ya je ya mutu a banza, wallahi ni babu abin da ya
sha mini kai."
'Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi, a yi shi
cikin kwanciyar hankali, ba tare da tashin hankali ba."
Ya ce, 'amin, allah dai ya sa haka din."
Maryam na daki ta yi jigum tana wassafa irin
yadda take ji a game da bashir.
"hakika ina. Da a ce shi ma haka zai soni da na
more wallahi, sai dai matsala daya alhajin su wato
daddy ina tunanin in ya sani ya abin zai kasance? Ni ina
mamakin irin wannan kiyayya da daddy yake nuna mini
sai ka ce ba 'yar dan'uwansa ba. Wai shi baya ganin irin
son da abbana yake wa dansa bashir ne? Why?Shi da ba
zai so ta sayar ba, shi ma mai 'ya'ya da yawa aka so na
sa bare abba mi kadai ce a gurinsa? Laifin abban ne
domin shi yake nuna yana tsoronsa. Ai shi ne babba
wannan ai zalunci ne so."
Sadaf-sadaf ya shiga ba tare da ta sani ba, ya
sanya hannayenta ya rufe mata ido yana murmsuhi.
97
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Hannu biyu ta sa ta rike hannayensa, domin banbarewa
daga idanunta. Ta yi nasarar cire hannun, ta juya ta kalle
shi suka yi murmushi. Sannan ta sa hannu ta kare
fuskarta. Ya kewayo ya zauna yana fuskantar ta.
murya.
"why?" ya tambaye ta. Ta ce cikin kasa-kasa da
"wallahi kunyarka nake ji shi ya sa ka ga ina ka sa yi
maka.........."
Kallon da yake mata ne ya sa ta saurin dauke
kai. Ya ce, "haba my sweet heart ai bai kamata a ce kina
nuna mini irin wannan ba, domin tare muke dama ba
wai bakin ganin juna ba ne."
"ai ka dade ba ka nan."
"okey ashe bakunta ake mini? To daga yau na
zama dan gida."
Ta sake yin murmushi.
11
Kwanci tashi soyayya ta mika à tsakanin
maryam da bashir ta yi nisa, har ta kai kowa ya sani. Shi
ma ałhaji hasşan ya fara jin kishin-kishin dan haka, sai
ya yi wa alhaji usaini waya ya ce ya zo yana nemansa.
Bai dauki lokaci ba kuwa ya je ya same shi, domin jin
musabbabin kiran. Bayan sun gaisa ne ya dube shi.
"alhaji wani kishin-kishin nake ji wai bashir
yana son wannan tsintacciyar yarinyar ko?"
Jin wannan magana sai alhaji usaini ya yi tsuru
da shi, đomin abin 6oye ya fito sarari. Abin da yake
gudu ya faru dan haka ya ga babu mafita. Sai ya fada
98
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
masa gaskiyar lamari. Ai ko nan da nan ya mike da
fada.
"kar ka soma, na ce maka kar ka soma wallahi ba
zai auri 'yar da ba a san asalinta ba."
Ya ce, 'alhaji da fa na kowa ne, ni ban ga abin ki
a wannan lamari ba. Mace ce fa ba namiji ba, yanzu
saboda allah in ba a tausaya mata ba sai yaushe?"
"kai dai da kake son tausayawar ka yiyi tata yi,
amma ni in nina haifi dana ba zai auri wannan yarinyar
ba, dan haka nemar mata miji tun da wuri."
Nan take ran alhaji usaini ya baci ya mike gami
da haura takalman sa ya mike ya fice abin sa.
Bayan ya komo gida sai ya kira bashir
bangarensa ya ce masa, "bashir ina son ka samo duk
yarinyar da kake so in aura maka, amma ka kyale
maryam."
Cikin fargaba ya kalle shi ya ce, "abba saboda
me ka ce haka?"
Ya ce, "mahaifinka ya ce ba za ka aure ta ba,
kuma ka san halinsa bai ki a bata a sakamakon haka ba.
Shi ya sa na ce ka hakura."
'A gaskiya abba ba zan iya hakura ba, domin ni babu wacce nake so sai maryam.'
"bashir na san in na fadi magana ba ka musa mini dan haka yanzu ka yi mini afuwa ka hakura."
"to ka fadawa ita maryam din in ta ce ta hakura da ni shi kenan, nima na hakura."
Ya ce, 'a'a ai wanan ba magana ba ce, domin ba za ta iya hakura ba. Sai in kai ka fara furta ka hakura."
99
Kwadi Bari Jana
"ai ba zan iya ba ne."
Amina A. Sharada
"ka taimaka bashir dan allah, saboda ba na son in
sami sabani da dan'uwana."
Tuni idanun bashir ya ciko da hawaye. Ya dube
shi zai yi magana, amma ya kasa sai ya mike kawai ya
fice yana ta kira, amma ya kasa amsawa ma bare ya
dawo. Ganin haka sai ya kyale shi ya ce, "to komai na
allah ne nì dai wannan lamari allah ya sa masa ruwan
sanyi kar ya yi zafi."
Shi bashir bayan ya tashi sai ya nufi dakinsa ya
fada kan gado kawai ya saki kukan takaicin abin da zai
iya biyo baya, domin shi dai ba zai iya rabuwa da ita ba,
ko me za a yi masa dan haka sai ya kulle a ransa in har
aka ce za a hana shi shi kuma ba zai yi auran ba.
Yana nan kwance shiru, sai ga maryam nan ta
shigo ta same shi a kwance bayan ta yi masa sallama ya
amsa ta sami guri ta zauna. Shiru kawai ta kasa magana
domin ita ma ya fada mata abin da ya fadawa bashir.
Kiran sunan sa ta yi ya dago kai suka haďa ido, nan take
gaban ta ya fadi, domin idansa ta gani ya yi jawur cikin
sauri ta sauke na ta. Ranta ya bace, ta ce, "yaya kai ma
ya gaya maka abin da ya gaya mini ne?"
Ya ce, "ya fada mini yanzu maryam ya zan ył?"
"mu je mu ba wa daddy hakuri mana."
"baki san halin sa ba ne maryam ai sai in ya ce
ya ki abu to ya ki kenan, sai hakuri."
"yau mun shiga uku wai shin bashir ita rayuwa
haka take ne? Wai a ce babu yadda za a yi mutum ya
dauwama a jin dadi?"
100
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
"ai ba wani abu ne wannan ba jarrabawa ce ta
allah in ka yi hakuri to imanin ka ya cika. Wannan yana
daya daga cikin shikashikan imani guda shida da sai sun
cika sannan imanin ka ya cika, wato wannan shi ne
kaddara, duk abin da allah ya kaddara maka sai ka yi
hakuri da shi. Wannan rashin yarda ta daddy haka allah
ya shirya mana sai mu bi su a sannu har su amince in
sun ki ya za a yi ai sai hakuri kwai."
"mu hakura da juna kenan bashir?"
Ya ce, 'ya za a yi?"
12
Hajiya jamila na zaune sai ga alhaji usaini shi ma
ya sami guri ya zauna. Bayan ta yi masa sannu da zuwa,
sai ta mike domin kawo masa ruwan sha mai sanyi. Bayan
ya sha ruwan ne wanda aka sirya da lemo juice ya aje cup
din ya dube ta yace, "hajiya jamila albishirin ki?"
"goro."
"zan samo miki abokiyar zama...."
"wacce irin abokiyar zama kuma alhaji?"
"wallahi wata yariya ce na gani zuciyata ta tafi
akan yarinyar shi yà sama na ga ya dace in sanar miki,
yarinyar tana da kirki ba ruwan ta za ku zauna lafiya."
Duk tunaninta a zatonta maryam ce, shi ya sa yake
kewaye-kewaye, dan haka sai ta ce, "wai a ina take ne
alhaji?"
"a gwale take haihuwar ta daya ta fito daga gidan
miji, sai ta kama karatu ba ta yi aure ba har sai da ta
kammala, amma dai za ki girme mata ba wai babba ce can.
101
1
d
b
Si
'y
Π
y
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharadu
ba, za la yi irin talatin da biyu din nan."
"oho! Ka ce ba ma budurwa ba cc? To 'yar waye kenan?"
ne."
"yar lalakawa ce, iyayenta ba wasu masu kudi ba
Ta ce, "a gaskiya ya kamata ka auro 'yar manya
domin mu goga da ita, in ka auro 'yar talakawa, ai ba zan
san matsayina ba, domin na san na fita in ko 'yar masu
kudi ce anan zan rabe da irin son da kake mini, domin ina
da shi. Ita ma tana da shi, babu wani wanda zai nuna wa
wnai tunkaho da abin duniya."
Ya ce, "to ai ni ita na gani kuma ta yi mini, dan
haka ni ita nake so."
"a gaskiya alhaji ka sauya."
Ya ce, 'yau zan ga ikon allah wai zamana za ta yi
ko zaman ki?"
Ta ce, 'zaman ka."
"to in ni za ta yi wa zaman to ba zan sauya ba."
"to shi kenan ai gata ga gidan nan sai ta zo ta zauna."
Ya ce, haba jamila kin ba ni mamaki saboda allah
ue ye na tada hakarkari haka?"
"wallahi ban ga matar da za a yi wa kishiya ba ta
una kishi ba."
"shi kenan allah ya sanya alkhairi."
"yauwa haka nake so. Shi kenan."
Kwanci tashi har an sanya bikin halima. Murna a
gurin su su baba abu ba a magana, ita ta zama uwa dan
haka komai ita take yi, amma ta ce su je su gano gidan su
yalwa, domin dole ne a ba su na su hakkin na iyaye. Haka
ran halima bai so ba, domin gudun kar ya je ya gano wani
abu da zai sa ya ce ya fasa, domin dai ita tarbiyar ta ce ta
102
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
bashi sha'awa har ya ce yana so kar ya je ya ga gidan na su,
kuma baba an ce sune mahaifanta, ba wani abu take tunani
ba sai matsalar kannanta da ta uwarta wato yalwa.
Yau ce ranar da aka tsayar alhaji usaini zai zo
halima ta raka shi gidan su wato can madile kenan, domin
ya ga iyayenta saboda an riga an fayyace masa cewa baba
abu kanwar uwarta ce. Tana nan tana ta faman-shiri har ta
gama ta zauna zaman jiransa. Can da misalin karfe hudu
da rabi sai gashi ya zo ya same ta ta gama shiri. Ya ce to su
tafi. Ta yi wa baba abu sallama suka tafi abin su. Suna tafe
suna hira har suka isa. Sannan ya tsaya ta shiga ciki ta
sanarwa yalwa tare suke da wanda za ta aura. Yalwa ta yi
murna sosai aka aka kintsa guri. Sannan aka ce ya karaso
daga ciki. Nan ya shiga suka gaisa har ya tambayi malam
usman. Yalwa tace dazun nan ya' fita masallaci zai komo.
Nan dai halima ta gabatar da shi ga yalwa. Sannan ta
gabatar da yalwa a gurin sa. Sannan suka shiga hira har
malam usman din ya dawo daga masallaci.
Malam usman ya tsufa ainun, da sanda ma yake
tafiya. Yalwa ta ce, "malam surukin mu ne fa ya zo gaishe
mu?"
Ya ce, 'a to daga ina?"
"har ka mance da wanda zai auri halima?"
"at to na ji kuma to bari in zo mu gaisa."
Alhaji usaini cikin tausayawa ya ce, 'a'a baba yi
zaman ka babra in fito."
Ya fito nan suka gaisa. Sannan ya fara yi musu rin nasihar su ta manya. Wato dattawa har wnai lokaci, ya
sanya musu albarka. Sannan alhaji usaini ya kawo kudi
masu yawa ya basu, suka ki karba. Sai da suka ga ya
103
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
matsa, sannan suka karba. Ita dai yalwa dan dai ta ga baba
ya ki karba ne shi ya sa ita ma ta dan wuce ta yin, tana
ganin ya karbe sai ita ma ta karbe. Nan suka yi sallama ya
tashi akan cewa sai ya komo, domin bayan biki zai komo
ya sake gaishe su suka yi musu addu'ar neman zaman
lafiya.
A hanyar su ta fitowa daga gidan ne sai ga asabe ta
zo wucewa da gani a bige take sosai, domin har hada
hanya take yi sai ko suka yi kicibis a soron karshe. Cikin
sauri ta kalli halima yayin da gaban halima ya yi
mummunar faduwa, domin abin da take gudun shi ya faru.
Saboda bangazar kafadar alhajin ta yi ta wuce, amma a
rashin sani cikin bacin rai alhajin ya ce, 'wannan wace ce?"
Kunya ta kama halima sai ta ce, 'wata 'yar makotan
mu ce da take zuwa diban ruwa a rijiya in an dauke na
famfo."
To fa ashe asabe ta jiyo sai ko ta dawo da baya ta
danki kwalar halima ta danna mata ashar, "dan haka ta
kazar baban ki ni ce 'yar makotan?"
Ran halima ya yi mugun 6aci ta ce, 'asabe ni kike
zagi?"
Ta ce, 'an zage ki ke wace ce? Banza kawai dan za
ki auri me kudi shi ne za ki nuna mana wariya har da wani
cewa ni ce 'yar makota? To masomin taushiya dawa ke ma
ai 'yar talakawan ce banza kawai."
Nan da man sai idon halima ya ciko da hawaye,
saboda bakin ciki. Tana ganin a lokacin da alhaji usaini
yake cewa asabe ta sake ta yana kau da kansa, saboda
warin tabar wiwi da ta shawo. Can kuma cikin gida su
yalwa ne suka ji asabe na zunduma ashariya a soro sai suka
104
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
taho su ji me yake faruwa. Sai ko suka ga ta cakumi wuyan
rigar halima. Alhaji usaini na ta fama da ita akan ta sake ta,
amma ta ki. Wai wallahi sai ta fada mata ko waye uban ta
tun da ta kawo wannan banza saurayin nata ita 'yar makota
ce. Baba ne ya yi salati ya ce, "asabe me yc haka kuma?"
Ta ce, 'ba..ba.. Abin da idanka ya gani shi ake yi."
'Sake ta dan iyayen ki, na ce ki saketa mana?"
Ta ce, 'wallahi sai ta fadan abin da iyaycna suke ba
cewa ta yi da wannan alhajin wai ni 'yar makota ce ba?"
Baba ya ce, 'to ai gani ta yi ba ki da nutsuwa shi ya
sa ta fada miki haka. Ai da kunya ta ce ke kanwarta
ce.......
Cikin tsawa ta tari numfashinsa.
"to me ye? Ko cewa na yi zani gidanta? Wallahi in
kin ga kafa ta a gidan ki ki yanke."
Halima ta ce, "nima ba na so ki zo, domin ba ki da
tarbiya ko kadan."
Ta ce, 'ai ke ma ba tarbiyar ce da ke ba, domin kura
ba ta isa ta ce da kare maye ba, gara nima duk iskancina
ban taba.
Yalwa ta yi kukan kura ta rufe asabe da duka tana
tsine mata. Wannan ne ya hana asabe fadar abin da ta yi
niya. Har dai aka 6anbare yalwa aka tura ta cikin gida.
Sannan alhajin ya ce da halima ta zo' su tafi. Hankalin
halima a tashe ta bishi suka tafi, har suka yi nisa ba ta iya
magana ba. Kuma ba ta san hukuncin da alhaji usaini zai
yanke ba.
Sai da ya kai ta har kofar gida. Sannan ya cc, 'to ni
zan wuce cikin."
Cikin sanyi na kunyar abin da ya faru ta ce, 'to
105
Kwadi Bari Janu alhaji sai yaushe?"
tga 1 Sharada
Ya ce mata, 'zan dawo gobe da aagriba wato misalin karfe takwas kenan ko?"
Ta ce, 'to shi kenan allah ya kai mu."
Ta dai amsa ne, amma a tunanin ta ba zai dawo ba.
Tana shiga ciki ta sami baba abu na zaune tana yanka
dankuna sai ta sami guri ta zauna. Bayan ta gaisheta ne
take tambayar ta ya su yalwan? Ta ce suna nan lafiya.
"yana gan ki ido ya yi ja lafiya dai?"
'Baba wallahi yau asabe ta ci mini mutunci a gaban
bawan allah nan kila ma daga yau shi kenan ya tafi kenan,
sai dai a je a kai masa kudinsa."
Ta ce, 'to wai me ya hada ku?"
Nan take ta kwashe yarda suka yi ta sanar mata tun
farko har karshe. Baba abu ta yi salati ta sanar da ubangiji
ta ce, 'yanzu halima haka asabe ta koma?" halima ta ce ai
baba, asabe ta wuce nan. Ta ce ai shi kenan ba laifin kowa
ba ne laifin yalwa ne, ai shi ice tun yana danyc ake
lankwasa shi, yanzu kam shirin asabe ai sai allah, domin ta
rigaya ta gama fandarewa. Halima ta ce, dan ba ki ji abin
da ta dinga cewa ba ne, wai duk iskancinta wai ba ta kai ni
ba."
"ki ce ma so ta yi ta gaya masa abin da ya faru dan
dai yalwan ta kwace ta ne shi yasa?"
Kashe gari halima tun takwas take zuba idon ganin
alhaji usaini shiru ba-zo ba, duk minti daya sai ta duba
agogo, har zuwa karfe tara. A nan ne ta fidda ran zuwansa
ta ce, "baba kin ga bai zo ba, dama na ga da wuya in zai
dawo."
Baba abu ta ce, 'ai ni ma sai da na ayyana haka ai
106
4
Kwadi Bari Jana Amina A. Shurada
nan gaba in kika kara samun wani saurayin ba zan kai shi
ba, sai an yi auran kwaje in ba haka ba wannan la'anannıyar yarinyar ba za ta bari ki yi auran ba, ta fi so
yadda ita ta ki auruwa take zaman sheke ayarta ke ma ki
zauna haka. Saboda allah in ba ku yi aure ba sai yaushe?