An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KADAY BABIJANEAmina Abdullahi Sharada
Mrs Abned sut Hade la
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharadd KWADAYI BARI JANA
1
AMINA ABDULLAHI
SHARADA
MRS AHMAD YUSIF HADEJA) 08085389470 - 0803586209
1
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
Hakkin mallaka(m): amina abdullahi sharada*
copy righ(c): amina abdullahi sharada
Shckarar bugu a: 2009
Godiya ta musamman ga allah subuhanahu
wata'ala daya bani damar rubuta wannan dan littafi mai
suna kwadiyi bari jana tsira da amincin allah su tabbata
ga fiyayyan halitta annabi muhammadu (s.a.w)
GODIYA GARE KU
'Yan Uwa Rabin Jiki
Labaran Abdullahi (Mai Unguwar Sharada)
Sulaman Abdullahi (Dangadi)
Binta Muhammad Sheka
Ummi Sulaiman Sharada
Lami Abdullahi Sharada
Hajara Abdullahi Sharada
Hafsat Abdullahi Sharada (Marka)
Hama Adam Abdullahi Sharada
KAWAYENA NA KAINA
Bilkisu H. Muhammad Zage
Zahra'u Baba Yakasai
Fuziyya D. Sulaman
Bilkisu Mai Agogo
Dija S. Sharubutu
Nafisat Muhd Sheka
2
Kwadi Bari Jana Amina 4. Sharada
GODIYA TA GARE KU
Muhammad Lawan Barrsiter
Jamila Ali Indabawa
Al-Amin B,Shop S.Titi
KANNENA NA KAINA
Shitu Sa'idu Calaba C/Riбer
Abdulhadi Abdullahi Sharada
GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU
Yakubu Usman (Uban Gari) And His Family
Bilkisu A.Y Uban Gari
Hafsat Usman Obi
Zainab Dan Asabe Usman Obi
Asma'u Usman T.Y Lafia
Aishatu Usman Isma'il Lafia Dan Asabe Isma'il
Lafia
Jamila Usman Osuko Obi
Hajiya Zainab Usman Yakubu Obi
Aminu Usman Osuko Obi
Ibrahim Usman Osuko Obi
Adamu Usman Osuko Obi Lafiya
Zuwaira Usman Osuko Obi
Ali O. Usman Obi
Safiya Usman Dan Ladi Panshin Jos
Usman Dan Ladi Panshin Jos
Huzaifa Yakubu Usman (Uban Gari)
Amir Da Amirata Isma'il Usman Obi
3
Asabc!!"
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada A
KWADIYA BARI JANA
"Wayyo! Allah yalwa. Wayyo! Allah
cikina wayyo bayana yalwa ki
taimake ni zan mutu. Asabe!.
Ta fara kiran ta akan tsananin jin ciwo, na am
asabe ta amsa a hasale domin ta zaci aike ne, gani
halima maye? Cikin tsananin dauriya ta ce mata ina
yalwa tayi ciwo yadame ni a she dama baki da lafiya?
Eh wallahi tun jiya ko barcin kirki banyi ba sai yanzu nc
ciwon ya kara yawa wayyo marata dan allah kiyi min
kiranta yanzu yanzu sannu bara inje in gani kila ta shiga
gidan su goggo hanne da kan daddawa, kunsan dazu na
daka mata lalle anamu turmin" ta ce, "to don allah
taimaka min kiraka ta to bara in dauko dan kwalina
domin na fara tsefe kaina ciwo ya hana to sake yin
magana saboda tsananin azaba ita kuma ta shiga
wancakalar da shirgi wai tana neman dan kwalin tana ji
tana ta faman wayyo.
"Salamu alaikum ke asabę ya akayi kika bar
tumakai suna ci min garin tuwan alhalin na barki
ra?kai tayya mana kai allah waran wadan nan tumakai
masu shegen ta'adin tsiya wallahi a wakin gidan malam
rabe ne masu cin na allah ya isa, wai ina asaben ne ana
kira kina jin mutane kin shige daki gashi nan sun cinye
mana garin ta fito da gudu la wallahi yalwa bansan sun
shigo ba kinga sun cinye ta ce a to bashi kenan ba sai
kowa ya hakura da abun da ya samu dama sauran
dumaman nan ne bai isaba shi yasa zan tuka sabo a hada
4
Kwadi Bari Janа Amina A. Sharada
yi
toga
kirana
shi kuma
wai
sun cinye ta ce wallahi yalwa halima ce ta
nemo dan
inyo kiranki bata da lafiya shine na shiga
lafiya
kwalina kinga sun cinye wanne irin bata da kuna? Yanzun nan fana barta zaune a daki na tafi dakan daudawa," to kin ganta nan dai tana ta faman murkusu su wai bata da lafiya. Cikin sauri ta shiga dakin domin taga halin da take ciki, halima me ya same ki haka? Yalwa wallahi baya nane yake min ciwo da marata gashi kuma kinwash wash allah na baya.namara? Haihuwa ce kenan to wallahi ba anan gidan ba sai ki tashi ki fitar min daga gida daga kai ta yi ciki tsananin jin ciwo ta ce da kyar dan allah dan allah yalwa ki rufa min asiri! Ki yi hakuri
wane rufin asirin kika kike nema yanzu bayan kin gama tonawa kanki asiri? A garin-nan waye baisan kina da ciki ba kin tashi ko sai ranki yа баci? Tа ce dan allah yalwa kiyi hakuri! Walłahi ba zan iya tashi ba ki kyale ni yalwa wallahi ba zaki zubar mana jinin haihuwar shega a gidan nan ba ki kara mapa talauci, kin tashi ko sai ranki yayi mummunan 6aci? Ta yunkura da kyar. tana cije-clje lebe saboda azabar ciwo tana matso hawayen bakin ciki zuciyar nan kamar ta fashe dan takaici ta fitb asabe ta dube ta ta ce dan allah yalwa ki kyale ta wallahi tausayinta nake ji "ta daka mata tsawa gami da harara ta ce ke arkama gaban ki ko in hambareki yar banza mara kunya tayi cikin daki tana gunguni ita kuwa halima tuni tayi waje.
Tana fita kofar gidan suda yake akwai fili sai ga yara nan makil suna wasan kwallan kafa nan kuma
5
Kwadi Bari Jana Amina A., Sharada
yalwa ta biyo ta tana cewa fita daga gidan wallahi ba dai
kihaihu a gidan nan ba wai ya ce "kiyi cįkin? Wannan
masifa da take ta yayya fawa ita ta janyo hankalin yaran
dake gurin suna kwallonkata har suka ga halima to dama
zance ya baza gari kwaram ai nan da nan sai yaran nan
sukayi mata dafifi aka suna kallanta ita kuma yalwa
ganin haka sai ta barta da yaran ta koma gida.
Tana tafe yaran nan suna biye da ita a baya suna
rere mata waka in daya ya bayar sai sáuran su amsa suna
cewa kar ya ce tayi cikin shege karya cezata haihu karya
ce an koreta karya ce sai mu je feta ai wasu suka. fara
daukar duwatsu sukafara jifanta can sai ga wasu mutane
nan dattawa su hudu sun zo wacewa suka gansu a cikin
unguwa sun yi mata dafifi suna jifanta ita kuma gashi da
gain tana cikin wani hali sai ta su ka yiwa yaran nan
tsawa dakyar suka sami nasarar korar yaran ita ko ta
kanta take yi ciwo ya isheta tarasa yanda za ta yi ta ji
sanyi ko su da sai bin bango take yi dakyar ta na kiran
wayyo allah in ta dan tsage ciwon ya lafa sai ta ci gaba
da tafiya da haka har ta kama hanyar bayan gari ba tare
da tasan inda zata nufa ba har ta danyi nisa da gari ta
fada wani titi wanda bashi da yawan moto ci kunsan
ba wani yawan motoci gare shi ba. hanyar kauye
Can tana cikin tafiya sai ta ji ciwo taya rana da
kuma alamar haihuwarta matso dan haka sai ta bar titin
ta ratsa wata gona wace take dab da hanya ta zaga bayan
wasu jerin itatuwan bini da zugu ta durkushe a nan tana
kiran allah da neman taimakonsa tun tana yi da baki har
sai da bakin ma ya gagara tabarwa allah ikonsa, kukan
6
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
jaririne zai tabbatar maka cewa an sauka sai data dan
huta tukunna sannan ta duba abin da ta haifa wato
jaririya ce kyakkyawar gaske jawur da ita kamar tsada
bayan yarta fado sai ta zamana ta sami tafiya dan haka
ta kurawa 'yar ido kir a nan ne ta gano yarinyar tana
kama da ubanta wato saurayin halima maí suna jamil
kamar an tsaga kara ta ce jamil ya cuce ni amma bani ya
cuta ba kansa ya cuta sai allah yayi min sakayya babu
wanda zai ga yarinyar nan ya ce "basa kama amma ya cе
"wai wani ba cikin sa ba ne ba komai akwai allah, tana
gama fadar haka sai ta yi ta faman kuka kamar ranta zai
fita duniyar tayi mata baki duk taji ta tsani kanta, sai da
ta gaji da kukan sannan ta sa hannu ta dauki yar har ta
juya zata tafi sai ta tuna da maganar yalwa yayin da take
mata amsa kuwa a kunne in kin haihu karki soma yarda
kizo min da dan ko 'yar gidan nan ki tabbatar kin
makure kin kashe sannaņ ki taho ki bar shi a can domin
ba zan ga ma irip abin da kika haifa ba "tana gama
wannan funa ni sai.ta mayar da jaririyar ta a jiye tana
ajiye ta sai jaririyar ta sake rushewa da wani sabon
kukan domin da ta dauke ta shiru tayi kukan jaririyar ne
yasa taji kamar karta tafi ta barta domin kunsan sha'anin
da mahaifi sai jikin yayi sanyi ta kasa tafiya Kaunar
yarinyar nan ta shige mata rai, da dai taga kukan ba zaiyi
magani ba kuma in har ta sake za'a iya zuwa a kamata
sai ta dauki mayafinta ta nada yarinyar da shita kwantar
da ita tafi to mata da fuskar ta yadda zata dinga shakar
iska sannan ta mike tsaye idanunta na mai fidda hawaye
ta ce. Ya ubangiji ni baiwar kace dana sabe ka da aikin
7
Kwadi Bari Jana Amina 4 Sharada
da kayi hani da kada bayin wadanda suka yi imani su
aikata wannan sa6o wato, (zina) sai gashi san abin
duniya da san zuciya da tirsasawar mahaifiyata sun
janyo min aikita sannan Garna da taimakon shaidan
la'anan nan allah gashi har na haifi 'ya ta wannan hanya,
ya allah ina rokonka kada ka saka abin da muka aikata
akan wannan jariirya ka kuma tsareta daga duk wani
sharrin shaidanu sanan ya allah in har wannan yarinya ta
zamo rayayya ka jefata a hannuna gari, allah kana ganin
zuciyata ba'a san zuciyata zan tafi in bar yarinyar nan ba
domin ina kaunar 'yata sai dan in sami nutsuwa da kanciyar hankali domin muddin ina tare da wannan
yarinya bansan halin da zan shiga ba sakamakon izayar
da yalwa zata yi mini.
Tana gama wannan addu'ar saita dubi yarinyar ta
sake fashewa da wani sabon kukan mai ban tausayi
zuciyarta cike da kuna da bakin ciki mara misaltuwa
yarinya sai kuka take yi gashi ta gaji da kwanciya ko
cibiyar ba a yanke ba bare wanka duk ta bushe kayokayo tausayi ya kara kama uwar nan dai ta fara tunanin
tafiya domin in ta dakata tausayin yarinyar wankin hula
zai kaita dare dan haka sai ta juya kawai ta bar jaririyar a
gurin tana tafe tana faman wai wayyo ta domin kuwa ji
take kamar ta koma ta dauko ta sai faman daga yan kafa
fuwa dahanaye take tana ta calla kuka sautin kukan
yarinyar har cikin zuciyarta sai kwai ta fashe da kukan
itama.
Ba tafi rabin awa da barin gurin ba sai ga wata
mota kirar jeep baka ta yi ta zo hucewa harta gota sai ta
8
'Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
dawo da baya ahankali ta tsaya dai dai sai tin inda
wannan jaririyar take tsayuwar ta kuda wuya sai murfin
motar ban garen zaman na kusa da dare ba ya bude a
hankali bude wársá ka dawoya wata kafa ce fara sol ta
fara bäyyana sannan daga baya sauran jikin ya fito cikin
nutsuwa wata hajiya će kyakkyawa fara soł bako gidan
baki ajinanta in 'kin dubi gashin girar ta dana kanta
wanda ta daure shi da wata blue din atamfa super
holland kafar nan ko kamar ta jarirai domfh kuwa babu
yadda zata nuna she dana taka kasa da itą kallo daya
zakayiwa takalmin da mayafinsa darsa"tona masa asiri
jakar ko tana mata kunnuwan nan'da hannayen nan da
wuyan nan' sun sha gold.
Cikin isa ta jingina da motar hannunta harde
abisa kirjinta dä hand set dinta a hannu can sai kofar
mazaunin dare bata bude wani alhaji ne fari yasako kafa
shima ya fito cikin shiga ta alfarma da kamala ga alama
mijin wanan hajiyar ne farin danyan boyel ne a jikinsa
sai takalmin shi ma hard cober fari ya murza wata hula
mai suna dar kunnan marayam ya zago inda hajiya take
tsaye ya tsåya shima ya ce "to sai kije kiduba ni ina nan
ta ce haba alhaji ya zan shiga cikin wanna surkukin dajin
ni kadai? ya ce "bake kika ce kin ji kukan jariri a cikin
ba nace mu wuce kin ce wani sai mun tsaya? kasa kunne
kaji in bakukan jariri bane "ya ce "ai fa lallai gashi nan
yana tsanyarwa sai ki dauko alhaji kai fa na mijine kana
iya shiga ko maye maza ka iya karawa dashi "ya ce haka
ne amma ai ba irin wannan ake nuna jarumtarta ta ba
domin wucewa kawai za mu yi kika ce wai tsaya kin ji
9
Amina A. Sharada Kwadi Bari Jana
kukan jariri to gashi mun tsaia sai kije ki dauko din, ke
wallahi ba kida hankali ai rashin haihuwa fa ba haukaba
ce ba inda zan je aljanu ne su kamar ki kafai. ta ce
“alhaji ai ba irin kukan aljanu bane yace "aikin san na
aljanu mazaje ki, in kuma kika zauna in yi tafiyata in
barki "ta ce ka bar ni a wannan dajin? ya ce "ya za ki ji
kukan jariri a wanan guri kice a tsaya dan sai da rai
"tace to shi kenan in kaji shiru ka biyo ni ya ce "allah ya
kiyaye tayi dariya haba alhajina ai na san ba zaka iya
bari in halaka ba ya ce e sai in biki mu tafi tare tayi
dariya.
Ta nufi dai dai inda take jin karar kukan na
fitowa gabanta na daddara domin kasada ce kawai irin
nata can sai ta isa gurin cikin tsananin mamaki ta ga
jariri sabuwar haihuwa a nade da mayafi kiyashi na ta
binsa yana ta calla ihu duk fuskar tayi jawur saboda
cizon kiyashi muryara kuwa har ta fara dashewa akan
sauri ta sa hannu ta dauki jaririn sai taga ashe ma mace
nan da nan ta fara kade mata kiyashin.
Shi kuma can alhaji na tsaye a jikin motar ya
kura idonsa akan hajiya da ta bi yana hange cikin
zuciyarsa yana cewa wannan-wannan akwai ta da fitina
wallahi, to amma allah ya kiyaye ya kare amin, yana
cikin wannan tunanine sai yaji hajiyarsa na kwala masa
kira tana magana amma baya jiyo abin da take cewa, ita
cewa take alhaji kazo ka gani jaririya ce sabuwar
haihuwa aka yar a nan shi kuma da yake gurin akwai
rata sai ya ji kamar tana cewa alhaji zo maza mucijiya ce
tatsare ni a nan maza kazo ka ceceni ai nan da nan ya
10
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
kidıme ya rude yama rasa me zai yi sai ya fara kwalla
mata kira hajiya hajiya kizo mu tafi na gaya miki gudo
mana nace kizo da sauri, fito daga nan wai ko bakya
jine? ita kuma cewa take kazo ka gani mana-albaji da dai
taga bai fahimciabin. da take nufi ba sai ta taho da
jaririyar a hannunta 'domin ta sanar masa aiko. yana
ganin ta taho da wani abu a hannu sai ya fada mota a
guje ya dinga yi mata inkiya da hannunsa wai ta' yar da
wannan abin da ta dauko sai faman muni yake yda
hannu ya ma kasa magana har ta karaso yana ganinta
dakyar yake kakaro kalmar "jefa rmana Ri shłge mu tafi
ta ce wa zan jefar? dan mutane ne fa jaririya ce aka haifa
aka yar ina gama agurin aka haife ta cikin in ina ya to ta
za a yi? ta kwashe da' dariya
"Lallai alhaji ka tsorata me ye abin yi? ya 'daure
fuska ina jan kunnanki karki daukar mana jaririyar nan
ta ce haba alhaji:ya zaka hana ni? gaskiya ba zan iya
hakura da wannan yar ba gara mu hakura mu tafi da ita
ya ce "shi ne nan izan tafi sai ki zauna ke da jaririyar a
nan tana jin abin da ya ce. sai ta zuro kanta kasa ta се
"haba alhaji kai kanka kasan dan mutum ce kuma
wannan yarinya tana cikin halin neman taimako domin
inta kara a wuni a haka zata gala baita ka yi hakuri mu
taimaka mata ko ba komai zamu samu lada a gurin allah
maganar da take masa cikin laryar da ki take masa nan
take ya saki gwauran numfashi idan sa yayi zuru-zuru ya
ce "yanzu kin tabbata mutum ce? ta ce na tabbata
mutum ce ya ce "to allah ya kyautaya bude mata motar
ta shiga ba tare da ya bukaci ganin jaririyar ba.
11
Kwadi Bari Jana Amipa A. Sharada
Sai da suke yi nisa babu wanda ya sake cewa
uffan sai can ya cc "to yanzu ya za mu yi da wannan
'yar? ta ce mu rike kawai allah ya bamu ya ce "wai mata
me yasa a kullum tunaninku ragagge ne? ya zaki ce
kawai mu dauki shegaya mu kai gidan mu? ta ce ya aka
yi kasan shegiya ce? ya ce to ke a ganinki wa zai haifi
da dan halak ya jefar? kuma ga alama ma a nan dan aka
haifeta ta ce to yanzu ya kake so miyi? ya ce kawai mu
wuce da ita gidan rainonyara mukai musu muyi musu
bayani ta ce "a gaskiya ni ba zan iya rabuwa da ita ba
"ya ce cewarta ma ta hakura bare ke "shiru tayi ba ta се
komai ba har ya gana sarutunsa ba tayi magana ba sai ya
ce "ai sai ki yi ta dauka kinsan dai taci yar mage bata
mageta ce to in allah ya yarda wannan magenta alherice
ya ce "to shi kenan naji amma nan gaba duk abin da ya
faru babu ruwana "ta amsa ba ma wani abu da zai faru
wanda ya wuce alheri, ya ce "amma sai mun farakaita
can police station sannan mu sanar da abin da ya faru
ko? ta ce hakane sannan sai mu kai ta asibiti domin
tabbatar da lafiyarta ya ce "shi kenan."
Suna isa police station suka snar da tsuntuwar
yarinyar sannan suka nemi a basu ita su rike har ta
girma a hannunsu a ka yi 'yarjejeniya dasu akan zasu
rike ta bisa gaskiya da amana kamar su suka haifeta suka
kama rantse sannan aka amince aka basu ita bayan an
basu takar da sun cike sun sa hannu sun karbi daya an
barwa police daya domin ya zama shaida ko dan gaba
wato an rabuta rana da kwanan wata da kuma sunan
yarinyar da za'a sanya mata wato maryam hajiya ce ta
12
Kwadi Bari Jara Amina A. Sharada zabi wannan sunan, suka ba su police daya domin jagorantar su kai yarinyar asibiti a duba lafiyarta. Bayan sun je asibiti an gama mata kamai sai suka sallami wannan police suka ba shi kudi masu yawa, dan da shi aka yi ta jigilar a asibitin. sannan suka biya kasuwa ya sayawa yarinyar kayan sawa ya dai hada
mata komai kamar kayan barka, har da su gidan sauro da bargo da tawul da katifar jarirai. sannan suka sayi
mayukan jarirai da dai sauran su, suka koma gida. ta dafa ruwan zafi ta sallawa yarinyar wanka. sannan ta
shafa mata mai, ta yi sumul ta sanya ma ta kaya da
turare. ai sai ka ce ita ta haihu. Alhaji ya dubi jaririyar
ya ce, "amma wannan yarinya da kyau take. wallahi
kyakkyawa ce sosai."Na ce, 'haka ma kuna magana da
d.p.o. na ji wani dan sanda yana fada."
"a gaskiya shawarar da zan ba ki kar mu soma
nunawa yarinyar nan ba mu muka haife ta ba in ta
girma." Ni zan kvwabe ka a kan wannan?" ta ce da shi.
ya yi dariya ya ce, "ai wato wallahi yadda na ke
ganin yarinyar nan a yanzu, sai na gan ta kamar 'yata ta cikina."
Nan fa suka fara buga waya gidajen 'yan'uwa da
abokan arziki cewa sun yi 'ya, aka dinga zuwa musu
barka ana mamakin irin wannan kyau na wannan yarinya, ana kuma tausaya mata bisa halin da za ta kasance in har ta girma, kuma ta fahimci ba su alhaji ne iyayenta ba, domin dole ta sani saboda ba yadda za a yi
a raba gado da ita, duk da cewa alhaji bai taba haihuwa ba, sai dai 'yan'uwansa da matarsa.
13
ba ta?"
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
"Hajiya yanzu wanc irin abinci ya dace mu ringa
Ta ce, 'wallahi ban sani ba, amma dai ni a ganina
mu koma gurin likitan da ya duba ta sai ya fada mana
kala abin da za mu dinga ba ta ko?"
"Haka ne ai ba sai kin je ba zauna ki lura da ita
nina jc."
bayan sati daya aka sanya wa yarinya suna
maryam, kamar yadda aka rada mata a police station.
hajiya sai da ta yi taron suna a ka yi abinci kala-kala aka
ci, aka sha dangi da abokan arziki da makota aka sanya
wa yarinya albarka kowa ya watse. wasu kuma na
la'antar lamarin a 6oye wai kawai daga tsintar 'ya sun
dauka, wasu 'yan bakin cikin ma cewa suka yi allah ya
sa ta zame musu masifa. sun mance allah yana tare da
masu tausayi da alheri. to alakulli halin dai haka duniya
take daidan wani karkataccen wani.
Haka dai yarinya ta ci gaba da rayuwa a cikin
gata da kulawa na musamman, ba a ko so ko da kuda ya
taba 'yar nan dan tsabar so, ga shi da ta yi kuka har rigerige ake tsakanin hajiya da alhaji, domin a duba a ga me
ye ya same ta. saboda maryam yanzu alhaji baya zama a
kasuwa nan da nan yake dawowa gida, in ko zai fita
harabar gidan sa shan iska tana hannunsa. har yarinya ta
iya zama, ga ta 6ubbukekiya kyauta kuma a kullum
karuwa yake kamar 'yar turawa, kuma kamannin uban
sai kara bayyana suke a gunta da yake shi ma a fagen
kyau ba baya ne ba, domin kyan ne ma yake sashi rudar
'yan mata.
14
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
2
CIKAKKEN LABARIN M
allam usman wani dattijo ne bawan allah, Iwanda ba shi da cin yau bare na gobe yana zaune ne a unguwar (medilc) nan cikin kano a Raramar
hukumar kumbotso. yana da mata guda daya mai suna yalwa da 'ya'yan su hudu biyu maza, biyu mata. a
kullum sai ya fita ya nemo abin da za a ci wato ba shi da
wani cikakken aiki, kasancewar sa ba wani ilimi ya yi
ba, sai arabiya, ita ma bai yi zurfi a ciki ba.
Babbar 'yar ta sa ta fari ita ce halima, sai mai bi
mata asabe. halima da shekara goma sha bakwai asabe
na da sha biyar. sai auwalu, mai sha uku da lawan mai
shekara tara. asabe sunan ta na gaskiya asma'u da yake
sunan mahaifiyar mallam usman ne da ita, sai ake
kiranta da sunan ranarta wato asabe.
Daga kan lawan yalwa ta daina haihuwa domin
kuwa haihuwar ta tsaya mata da wuri shi ya sa take
kiran lawan da dan autan yalwa, ko ta ce dan lawandi.
Ita dai yalwa allah ya yi ta masifaffiyar macece,
ko shi mallam usman din hakuri yake yi da ita, domin in
ta- fara masa yayyafin masifa akan abu kadan sai dai ya
bar mata gidan dama baya zama. ya kan ce in ta ga na
fita ai ta yi shiru, bare in ya dawo bai samo komai ba ai
wannan lokacin ba shi ba kwanciyar hankali. hatta 'ya'yanta ba ta kyale su ba sai ka ce ba ita ta haife su ba,
da zarar sun yi mata wani yanzu za ta hausu da zagi da tsinuwa da daidaitawa da la'antawa. makotan ta babu
wanda ta bari, mazan su da matan su. sai ka ce karya,
15
Amina A. Sharäda Kwadi Bari Jana
kuma babu wanda ya isa ya mori dan ta, ko da sayo mini
gishiri.