ta ce, "hadawa
bashir da maryam nake yi."
Ita kuwa hajiya rukayya ba ta yi musu ba sai ta
hada musu. Suka koma falo suna ci har ma ta ce ai
wannan dama kara dankwan zumunci ne, su kuma suka
koma can wani dan matsakaicin falo suka zauna suna сі,
nan suka bar yaransu suna ci suna hirar su. Tsawar alhaji
hassan ce ta firgita su kamar wanda ya ga gobara. Cikin.
tsabar kidima suka tashi a guje domin ba su fahimci abin
da yake cewa. Su kuma su hajiya suna zuwa falon sai
suka yi turus wai ashe duk wannan fadan dan an hadawa.
maryam da bashir abinci ne. Nan da nan ya fige maryam
guri daya ya yar, sannan ya tashi bashir. Shi kuma
bashir ganin haka sai ya ce baya cin abincin. Ai ko shi
ne sanadin fadan yana cewa da hajiya jamila.
'Kin cuce ni wallahi kin cuce ni ni, saboda me za
su kyale su har su shaku."
Hajiya cikin bacin rai tą ce, 'wai alhaji me ya sa
kake irin wannan abu ne? Ita yarinyar nan ba ka san irin
baiwar da.allah ya yi mata ba, ya za ka bi ka tsani
yarinya sai ka ce ba mutum ba? A gaskiya irin wannan
babu kyau ka ga fa yarinyar nan tana sane da duk abin
da ake yi........"
"dakata malam an yi sai ki yi abin da za ki yi." in ji
alhaji hassan.
"wallahi akan yarinyar nan zan iya batawa da
kowa, saboda haka maza a fitar mini ita daga gida, ai
ban san ma da ita aka zo ba."
61
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
ana hayaniya. Cikin sauri alhaji usaini ya shigo, domin ya jiyo Ya same su ya ce, 'su waye ne? Me ye haka ne?"
faru. Ya
Take
juya
hajiya rukayya ta sanar masa da abin da ya
tana
ya kalli maryam ta rungume hajiya jamila
girgiza
kuka tana cewa, 'zo mu tafi gida mama." sai ya
saki ka
kai
hada
kawai ya cewa hajiya rukayya, "to ke me ya
nasa."
musu abincin? Ai sai ki warewa kowa
"wallahi ban san zai yi fada haka ba, da ban hada musu ba, amma irin wannan ai ba kyau ya za a yi ka
wannan,
debi karan tsana ka zubawa yarinya karama kamar saboda allah?"
mini
Ya ce cikin fushi, "kin ga rukayya kar ki kara yi katsalandan a cikin harkokina ni ina da hujjar ta ta tsanar wannan yarinya dan haka kar ki kara yi mini wata magana a kanta."
ta ce, "to shi kenan alhaji, amma na ga ai kai ba jahili ba re da iliminka bai dace a ce ka na irin wannan ba."
Ya ce, 'na dai gaya miki dan haka sai ki zabi na zaba kodai ki daina shiga sabga ta kan maganar yarinyar nan ko kuma in s36a miki."
Cikin fushi ta ce, "in dai akan wannan yarinyar
ne na daina magana insha allahu daga yau." Haka suka gama yininsu suka tafi. Su hajiya jamila na ta faman mamakin alhaji hassan. Ta ce a ranta, "ai wannan gara ma da allah ya sa ba shi ne mijina ba da ba zai bari in dauko yarinyar nan in rike ba."
62
a
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
6
Al'amarin halima kuwa bayan ta bar jaririyar ta
tafi gida gudun kar a ganta a gane abin da ta yi sai ta bi
wata 6arauniyar haniya wacce za ta iya kai ta gida, ta
yadda babu mai iyay ganinta. Ta ko yi kicibis da wani
famfo shi kadai a wajen; sai ta wanke jikinta. Sannan ta
wuce gida. Yalwa nà zaune tana ganin shigowarta sai ta
mike zumbur.
mata.
ba
"kin haihu?"
Ta gyada kai cikin fargabar abin da za ta -ce
"ina yarinyar take?"
'Na kashe kamar yadda kika umarce ni."
'In ce ko dai kin tabbatar babu wanda ya ganki/"
"na tabbata babu wanda ya ganni, domin gurin
kowa."
"yauwa shi kenan mun rabu da kaya, sai kuma allah ya
kiyaye gaba kar kwadayi ya kara jan mu mu sake
afkawa a cikin nadama. Au! Me kika haifa?"
"mace na haifa, amma suna kama da jamilu."
'To me ye na wani suna kama ina ruwanki da
kamar ta su? Ke in har kina da hankali ma har kya wani
kula da kamannin ta? Yaran da ya nuna bai san mu ba,
ko dai ba ki kashe ba ne?"
"na kashe mana."
"a to in kika barta kin shiga uku in aka gane,
domin ke za a rike babu ruwana."
"ai ba wanda ya gani."
63
Kwadi Bari Jána Amina A. Sharada
Cikin dole take maganar, domin jikinta ba dadi.
Allah-allah take ta je ta kwanta ta huta. Sai yalwa ta lura
da yadda take jan jikin nata sai ta ce, "je ki ki yi wanka ga ruwan zafi nan akan murhu, da zafi sosai idan kin yi wankan sannan ki kwanta." ta ce to.
Bayan ta yo wankan ta sanya kaya sai ta shiga
daki ta kwanta lamo tana tunanin 'yar ta da ta bari tana
cewa a ranta.
"ko yanzu tana nan tana kukan, ko an sami mai
daukar ta? Oho. Kila ma yanzu ta mutu." tana
wannan tunanin sai hawaye ya zubo mata ta fara kuka a
6oye dan kar ta jiyo ta. Tana cikin kukan ne sai ga
yalwa ta shigo, nan da na sai ta goge hawayenta. Bayan
yalwa ta shiga ne ta zauna ta dube ta ta ce, "halima ni
yanzu abin da na ga yafi sai ki tattara kayan ki ki koma
can gwale gurin kanwata abu mai danki ko kya sami
miji a can, kin ga anan babu wanda zai aure `ki da
wannan abin kunyar kin san halin kauyen nan namu ga
surutu da zagi kuma ko da a ce wani ya fito neman
auranki ba za a bar shi ba sai zoge shi. Don haka ki
koma can ki yi zaman ki kin ji?"
Ta ce, "nima yalwa sai da na ayyana a haka na
ga kamar ba za ki aminc eba, shi ya sa ban gaya miki
ba."
Ta ce, "dane me ba zan amince ba, bayan na san
irin halin da ake ciki? Yanzu dai abin da za a yi ki shirya
ki tafi tun kafin jama'a su san cewa kin haihu kin ga sai
a ce tun tafiyarki ba ki komo ba."
'To, amma sai dai da daddare in na dan ji kwarin
64
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
jikina, domin yanzu ba zan iya zuwa ko'ina ba." "ai dama sai da daran kya je yanzu zan sa asabe ta hada miki kayan ki tun da ba za ki iya hadawa ba."
Tana gama fadar haka sai ta kirawo asabe ta ce, "zo ki hadawa halima kayanta a nan dakin in ya so sai ki kai mata bakin titi da dare, sai ta tafi."
Asabe ta ce, "yalwa ina za ta je."
"gidan abu za ta can gwala ta zauna."
Sai asabe cikin tausayawa ta ce, 'a gaskiya
halima ke kika yi sake tun farko ai ni wallahi ba ma zan
taba bari ciki ya shiga jikina ba tun yaushe muke tare da
usman mai gyaran babur kin taba ganin wani abu ya faru
tsakanin mu? Sai ke kawai ki saki jikin........."
yalwa ta katse ta ta hanyar tsawa ta ce, 'wato dan uban ki
ke ma iskancin za ki yi har kike wani tutiya da usman
mai gyaran babur? To ina kudin da yake ba ki?"
duka.
"kashewa nake yi."
Ai jin cewa tana kashewa sai yalwa ta bita da
"wato almubazzaranci za ki dinga yi babu adani
ko?"
Nan da nan sai mamaki ya kama halima wato
yalwa ba ta yi bakin cikin abin da asabe ta fada ba sai
bakin cikin kudin da ba ta kawo mata? Ta ce lallai
yalwa ba ta saduda ba, kawai abin da za ta yi sai ta bar
musu gidan su ta daina bakin ciki, domin gidan ba gidan
zama ba ne, in har suna tare da yalwa za ta iya jefa ta
wata hanyar kan san kudinta.
Dare na yi yalwa ta bawa asabe kayan halima a
65
Kwadi Buri Jana Amina A. Sharada
boye ta fita zuwa can bakin titi ta tarar mata adaidaita
sahu ya kawo wasu mata ya aje su har kofar gida ta
kawo su. Halima ta yi sallama da mutanen gida har da
babanta shi ma ya yi farin cikin komawarta can gwalen,
kuma ya yi mata fada sosai akan kar ta sake shashanci
irin na da ta zamo mai kamun kai. Sannan ya sanya mata
albarka. Suka yi sallama hawaye na zuba a idon halima
ba dan komai ba sai dan tausayin babanta, wanda a
kullum girma kara kama shi yake yi, kuma ga shi
kullum gidan ba kwanciyar hankali sai kara 6ata masa
rai ake yi.
Tana zuwa gidan baba abu ta yi sallama, safiya
'yar gidan baba abu na ganin halima sai ta tashi da gudu
ta taryo ta, ta rungume tana tsallen murna. Baba abu ta
leko da sauri tana ganin ta ta ce, 'wa zan gani a gidan
nan? Lallai ma halima sai yau?"
Halima ta shiga daga ciki ta zauna. Sannan ta
gaida baba abu. Baba abu ta ce, "yanzu da daddaran nan
in çe ko dai kalau ko yalwa ta yi tsiyar ne?"
Ta ce, 'a'a lafiya kalau sun ce ma in gaishe ki."
"ina amsawa?"
Sannan ta dubi halima ta ce, 'wai yana ganki
haka ina cikin kuma?"
Nan take halima ta kwashe abin da ya faru da
haihuwarta ta gayawa baba abu da kuma yadda ta bar
'yar da rai dama shawarar da suka yanke da yalwa cewar
ta komo gurin ta ko ta samu mijin aure duk ta sanar
mata. Nan da nan baba abu ranta ya yi matukar baci ta
ce wai me ya sa yalwa take haka ne? Kullum sai rashin
66
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
mutuncinta ne yake karuwa? Ya za a yi a jefar da dan
mutum sukutum, saboda allah? Haba halima ke ma kin
yi wauta anan."
Ta ce, 'baba wallahi yalwa ce ta ce kar in komo
mata gida da jaririn ita cewa ta yi ma in kashe ni ce dai
na ga ba zan iya ba shi ne na ajiye na taho na bar ta a
can."
"don ubanki da ta gaya miki ki yar ba sai ki gudu
gidana da jaririyar ba? Ai ko ni na rike ai 'ya ba ita ce da
laifi ba iyayen ta ne masu laifi."
Nan da nan sai halima ta ji kaunar baba abu ta
kara shigar mata rai, domin nuna cewa tana san 'yar da
ta haifa. Sai ta fara da ta sani da ta kawo mata 'yar tun
farko. Baba abu ko har yanzu fada take yi.
"halima kin yi wauta wallahi sai ka ce akan ki
aka fara? An sani wannan abu babu dadi, to amma tun
da ya faru ya za a yi ai sai dai kawai a kiyayi gaba,
amma ba kya yarda da sukutum kamar dabba ba. Kai ko
dabba ba za ta yi abin da kika yi yanzu ba, wallahi
yanzu in ba wani ikon allah ba ke ba 'yar nan har abada,
kai wannan bakin ciki da yawa yake."
Halima cikin shashshekar kuka ta ce, "baba ko
cigiya za a yi a ji ko wani ya tsince ta?"
"dan hauka, wato ki tonawa kan ki asiri kenan ki
janyo mana dauri domin wannan abu da kika yi ya zama
dole ya zama sarri in ba haka ba kin shiga uku har da mu."
Safiya ta ce, 'wallahi abin dai aunty halima babu dadi, to amma komai mukaddari ne haka allah ya so."
67
Kwadi Bari Jana Amina A, Sharada
Baba abu ta ce, "tashi ki kai mata jakar daki sai
ki hado mata abinci ta ci tukunna zuwa da safe mu ga
me ya kamata ta yi game da wankan jegon in ba haka ba
ai sai ta kumbure ko ta yi wankan ko kuma ta sha
magani. Kai gara ma maganin domin wankan tonan asiri
ne."
Haka dai halima ta ci gaba da zama gidan baba
abu ta yi bulbul da ita da yake babu wani abin da yake
damun ta kyanta ya kara fitowa, domin tun da ta sami
ciki take cikin bacin rai ga shi ta yi duhu. To yanzu babu
wani abun da yake damunta sai dai ta wanke goma ta
tsoma biyar, dan aikin gidan ba wani mai yawa ba ne,
kuma su biyu suke yi wato ita da safiya. Ga shi safiya na
koya mata karatun alkur'ani mai girma, har ta yi nisa.
Baba abu ta ce, "in kin yi arba'in zan saki a
makarantar gidan galadima ki yi karatunki na firamare
da sakandire, domin wannan abu da ya faru ma da rashin
ilimin in da a ce da ilimin wani abu ma ba zai faru ba."
Halima ta yi ta faman murna jin cewa za a sanya
ta a makarantar boko, domin tana da sha'awar ta yi
ilimin ita ma.
Watan ta biyu a gidan baba abu ta shiga
makarantar gidan galadima har shekara shida. Sannan ta
yi jarabawa ta ci gaba da secondary duk a can ga shi
kuma tana da kwazo sosai. Kuma duk abin da ya kamata
a saya da ma sauran matsalolin makaranta baba abu се
mai yi, domin kuwa baba abu tana da sana'ar ta ta dinki
da saka har ya kasance ta yi suna a gwale, duk inda ka
ce kana neman gidan abu mai dinki za a kai ka. Baya ga
68
Kwadi Bari Juna Amina A. Sharada
kwarewar ta akan dinkin har ma dinkin 'yan makarantar
nursery take yi a kawo mata kwangilar hukuma
makarantar ta biya ta. Sannan ga shi tana da satifiket na
kungiyar mata manoma, domin tana dan taba noman
rani da damina kuma ta yi noma sosai dan haka baba
abu ba wata mai wadata ba ce, amma akwai rufin asiri
sosai. Sannan mai gidan ta ya rasu, 'ya'yanta biyu kacal
wato ta fari sunan ta saudat tana aure a tukuntawa,
'ya'yanta uku wato akwai ummi ta farin, sai sadik mai
bin ta. Sai kuma kabir mai sunan baban alhaji dahiru
mijin ta. Tana sana'ar sayar da lemon kwalba wato
mineral. Sannan kuma tana kulla so6o. Tana kuma yin
cake da cincin da dubulan da alkaki wato dai ita ma
sana'arta take sosai. Kun san an ce ba a maraya sai rago
shi ya sa rashin mahaifinsu bai sa sun shiga matsala
sosai ba, domin suna da sa'anarsu ta rufin asiri.
Ita kuma safiya ta kusa gama makarantar
sakandire dan haka auranta za ta yi, dama tana da tsohon
saurayinta tun tana primary ga shi yanzu suna tare, har
secondary in ta gama za a yi mata auran ta domin har an.
sa musu rana.
Duk sanda halima ta sami dogon hutu takan je
gidan su, domin ta gaida iyayenta wato su yalwa da
malam usman abin takaici har yanzu babu abin da ya
sauya a gidan nan game da nutsuwa kullum in halima ta
je da abin bacin ran da za ta tarar a yanzu haka su
auwalu sun maida kan su kamar sarakunan arna, ban da
shaye-shaye da neman matan banza ba abin da suke yi
sai ka ce karnuka sata ko kamar beraye. Tun suna sace
69
Kwadi Bari Jana Amina dSharada kajin dane mutane da agwagi yanzu ta kai su su bi dare su Ssacı akuyay ko tunkuya su sayarwa da mahauci ya ba su dan abin da bai taka kara ya karya ba Yanzu sun sn tolitisZ SO 59 !ln 2nI JgUS
buwayi gari kowa sai allah wadai yake yi da wannan Yrа sx yalwa is202, Asabe воa kam ba miji, domin tabshiga hanyarபயம் banzą, ga எம் shi ta gandame duk wanda ka gan su tare fo Ба eure De ya kawo shi ba zuwa ya yi ya hole ya lalnn SWEDUயர் wadannan abubuwan su suke damun halima har
a 0 a 7zo gidan. Ga yalwa da malam usman sun kara
Isul ullum karfi na dada karewa, ga babu wani mataimakı sai allah olsw sdк поl ab s62 16'ns2 am
піх виma halima ce ta yi shirin la tsaf za ta gaida Yau
su yalwa, Sai baba abu tata bab ta kayan miyada su
0961 shinkafa danya kwana uku ta ce ta kai musu. Sannan ta 162 6VEL E ЕU 30 DS E2 0
saya musu goro da su sabulu da omo, domin ba komai
yanzu sai wahala. Tun da ita kuma ta sha kwanar gidan
take jin tashin kidan zamani kamar wani hotel. To amma Was BM B
da yake ba a raba matasan samari da wannan ba ta damu полог в
ba Kai tsaye ta shiga cikin gidan domin ita da kanta kai 18 st
musu abin da baba abu ta bayar a kawo musu. Ta shiga 48 ம
shagon gidan domin ta sanar musu ta zo. Me za ta gani?
Hayakin tabar wiwi ne ya yi dan karamin gajimare a
saman dakin. Sai da ta toshe hanci, ta dan jima sannan EDidanta ya gane mata wasu 'yan mata su biyu bisa gado
kowacce daga ita sai shimi iya gwiwa suna busa hayaki.
A nan ta gane cewa yawan da suka yi shi ya sa har
hayakin ya zama tamkar girgije a dakin. Kuma kowacce
kanta bisa Kirjin sauryain ta. Warin tabar wiwin ne ya sa
ta saurin fita daga dakin ba tare da ta iya cewa komai ba. タン
70
Kwadi Bari Janа Amina A. Sharada
'Yan matan nan suka ce da su auwalu, kai wannan wacce
ajawowa ce take sa mana ido. Suka ce wallahi wata
aunty din mu ce ai duk abin da muke yi a gunta muka
samu. Ai ko sai 'yan amtan nan suka kece da shewa da
ihu suna cewa, "sai aunty."
Cikin bacín rai ta shiga cikin gidan tana ta faman
fada. Sai ko ta yi kicibis da asabe ta ci kwalliya ża ta
fita, sai ta tsaya da baki a sake tana kallonta ta sanya
wasu damammun riga da siket na atamfa wadanda suka
matseta sosai. Tsagar siket din ta kai kwarin gwiwarta ta
baya. Kanta babu dan kwali ta yi karin gashi an.yi mata
kalba kanana sun zubo har bayan ta. Bakin ta da kan
idonta duk ta fante da janbaki ruwan toka ga wani ta
kalmi mai shegen tsini wanda ya kara mata tsayi. Dinkin
rigar kuwa iya cibiya, gashi da gani sai da ta dauke
numfashi sannan ta sa su har sike din.
Kallo daya za ka yi mata ka zaci ba musulma ba
ce. Halima ta yi karfin hali ta ce, "ke kuma ina za ki
haka?"
"fati za ni?"
'Amma ki rasa kayan da za ki sa ki je fatin sai
wadannan? Haba asabe don allah ki dinga sanya kayan
kirki."
"kai halima yanzu me ye laifin wadannan kayan?
Ai sune suturar duk wacce kanta ya waye, amma wacce
kanta bai waye ba ita take sanya manyan kaya. Ina nake
iya sanya wannan kayan." ta kama less din jikin halima.
'Sai ka ce wata jakadiya ai wannán sai ku."
Ta juya ta na cewa, 'na tafi in kwana za ki yi in
71
}
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
na dawo ma gaske, domin ina zaton sai kusan daya na
dare zan shigo yau."
Cikin bacin rai halima ta finciko ta ta baya tana
cewa, "ke yanzu ba a isa a gaya miki ki ji ba? To koma
ki cire wadannan kayan ki sanya na kirki in ba haka ba
yanzu ranki ya baci kin ji ko?"
Asabe ta kalleta a yatsine ta ce, 'kin yi haliman
nan ni da allah cika mini wayan riga kar ki yamutsa mini
guga ke lokacin da kika yi ta ki holewar waya sami kí
ido? Sai nis za ki takurawa wai ke ga ustaziya to karatun
na ki na ga ai na bayan an gama holewa ne, kuma
yanzun ma ba a hanaki ba, dadin ma rashin dabara ne da
wayewar kai shi ya sa kika dauki cikin, amma yanzu da
kina yi amfani da magani ai babu abin da zai same ki ga
shi ni yanzu ina ta sha'anina ba wani abu."
Tana gama maganar ta sai ta yi waje abin ta ta
bar halima nan tsaye cikin bakin rai sororo. Sai ta yi ciki
da gudu tana kuka. Ta sami yalwa'a zaune ta ce, "yalwa
muddin ba za ki dinga tsawatarwa yaran nan ba zan
daina zuwa gidan nan, domin ba zan zo ina ganin irin
wannan takaicin ba."
Yalwa ta ce, "me kuma suka yi miki uwar
korafin tsiya ke dai ba dama ki zo ki ga yaran nan sai ki
dinga tonan su da fada, to muddin bab ki ja girman ki ba
za su raina ki a banza.".
To ashe duk abin da suke yi a kunnan malam
usman ne yana daga dan dakinsa a kwance da ke bashi
da lafiya shi ya sa baya magana, to amma jin yadda suka
yi da kuma abin da yalwa ta ce sai ya sa baki ya kira
72
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
halima. Ta zo ta tsugunna bayan ta gaishe shi ta kuma
cc, "baba abu na yi maka sannu da jiki." ya ce yana
amsawa in ta je ta gaida ita. Ta ce to za ta ji da kyau.
Sannan ya ce, "abin da ya sa na yi kiran ki shi ne duk
abind a kuke yi ina jin ku, dan haka nake so in gaya miki
daga yau in har kin zo gidan nan kika ga suna yin wani
abu to kar ki kuma yi musu fada kar ki sake yi wa kowa
magana kowa ya gyara halinsa, kyale su kowa duniya za
ta gyara shi, gani suke yi fadan da ake muşu kamar ba
san su ake yi ba shi ya sa."
Ta ce, 'to baba waye ma zai musu fadan duk
fadin unguwar nan? Dama kai kadai ne, kai din ma
kuma in ka yi ba sa ji."
ya ce, "wannan mahaukaciyar uwar ta ku ai ba san a yi
musu fadan take yi ba, in ta ji ana yi musu fada sai ta ce
wai an takura musu. Ke dai ki tayani addu'a musamman
akan asabe, domin ita mace ce gara su maza ne."
'baba ai ba gara su din in riga an san halin su wa zai ba
su 'yr su su aura? Ka san dai ana ganin kashi da rana ba
za a bari a taka ba?"
su."
Ya ce, "wannan haka yake allah dai ya shirya
'Amin."
Sannan ya ce, "wai ni halima yau she za ki yi
aure ne kin ga fa ko asabe ta isa aure tuni, bare ke
halima."
"baba zan yi ne kai dai ka yi ta yi mini addu'a
domin ina so in sami nutsatstse mai hankali wanda in
mun yi auran zai rike ni da daraja ba wanda zai koro ni
73
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
nan da nan ba, ka san tun da abin nan ya faru ba kowa
ne zai iya jurewa ya kyaleni a gidan sa ba, in har ya
sami wannan labarin kila za su iya koro ni ka ga kuwa in
na sami mai hankali zai iya hakuri ya bar ni domin na
san zancen duniya baya 6oya komai jimawa wata rana sai zanan nan ya fito."
'Haka ne allah ya kawo na gari."
'Amin baba."
Ya ce, "kin gama karatun ne?"
Ta ce, 'e to na kusa dai ina gama secondary, to
amma in dai ban sami mijin ba zan ci gaba da karatuna
ko diploma in samu na yi, in samu wani dan aikin."
Ya ce, 'to shi kenan allah ya taimaka." ta се, 'amin baba."
7
Alhaji hassan ne zaune a falon alhaji usaini gefe
kuma hajiya jamila ce da alhaji usaini da kuma bashir
sun yi kasake suna sauraron abin da alhaji hassan ke
cewa;
'Abin da ya kawo ni ina so ka bani bashir zan kai
shi misira ya yi karatunsa a can, domin can, nake bukata
in kai shi."
Babu ko musu alhaji usaini ya ce, "to shi kenan
alhaji ai wannan babu komai zai tafi."
Daga ganin fuskar bashir ka san cewa sam bai so
wanna tafiya ba, dan dai yana matukar tsoron uban ne
sai ya amince bisa dole. Alhaji usaini ya tambaye shi,
"yaushe za a yi tafiyar?"
Ya ce, "ai ya gama komai gobe-goben-nan ma
74
Kwadi Buri Jana
zai zo a tafi."
Amina A. Sharada
"to shi kenan allah ya kai mu."
Sannan ya tashi ya fice suka raka shi har bakin
motarsa wato bashir da alhajin. Hajiya jamila na shiga
cikin dakin sai ta sami maryam tsuru a rakube a jikin
bango ta ce, "au ke kuma me ki ke yi anan? Ai ya tafi sai
ki fito."
Ta mike jiki na rawa ta ce, 'umma ina na ji ana
cewa bashir za shi?"
Ta ce, 'bashir misra za shi karatu in ji abbansa."
tana jin haka sai ta dafe kirji ta fice da gudu ta bar hajiya
jamila a tsaye, ta yi 6angaren bashir. Hajiya jamila ta ce,
"oho! Ni jamila wadannan yara sun shaku da juna ga shi
alhaji hassan sai sa musu birki yake ta faman yi to yanzu
ya za a yi? Ai sai hakuri."
Ita kuwa maryam na shiga dakin bashir sai ta
same shi zaune a gefen gado ya yi tagumi kawai yana
tunani sai ta ce masa, "yaya bashir wai misira za ka je?"
Ya daga kai kawai ya kalleta, sai ya kasa ba ta
amsa, domin yana ganin idon ta duk ya cicciko da
hawaye. Sai ta ce, 'yaya yanzu ba yarda za a yi a hakura
da wannan tafiyar?"
"to ya za a yi maryam tun da ya ce sai na je ai sai
na je kin san halinsa."
Tana jin abin da ya ce sai ta durkushe kasa ta
saki kuka. Ya ce, 'ki yi shiru maryam kar abban nan
gidan ya zo ya ganki ki na kuka in ya tambave ki me za
ki ce masa?"
Ta ce cikin shashshekar kuka, 'a gaskiya yaya
75
Kwadi Bari Jana Amina A. Sharada
mun riga mun shaku to sai yaushe za ka komo?"
Ya ce, 'ni kaina ba so nake in tafi in barki ba sai
dai dan babu yarda zan yi ne."
lokaci.
Nan dai suka yi ta tattauna lamarin har wani
Can kuma hajiya jamila ce zaune a falon alhaji
usaini suna hira. Inda hajiyar ki cewa alhaji, 'anya kuwa
ba wata soyayya tsakanin yaran nan?"
Ya ce, "suwa kenan?"
"bashir da maryam mana."
"kai haba me kika gani?"
Ta ce, 'to ai gani