Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
Asiya nagode sosai da sosai, Nasan kinyi duk abinda yakamata Nakuma gode Allah yayiwa Rayuwa albarka yabaraki kema da Mansur. Dariyar yak e tayi sanan tace.  Amin tho amma ba mansur d in ba.  Oh shima bakiji zaki iya bashi ragamar rayuwar ki ba?.  Nawfal Ummi fa ba iya ta tace bazata iya baka ragamar rayuwar ta ba, nice naga haka, sanan shi Mansur ai akwai dalilin daya ja haka.  Asiya ai bakice mun Ummi ta fad a ba sanan shima mansur d in zan iya jin dalilin. Shiru tayi alamun bazata iya fad a ba.  Tom shikenan Asiya nagode.  Shikenan Nawfal Allah yasaka da Alheri. Daga haka ya shige motar shi ya huce, itama ta koma gida, gaba d aya takwashe duk abinda yafaru tasanar da Ummi sanan ta d ora da cewa.  Wallahi Ummi bakiga yanayin sa ba abun tausayi.  Nasani Asiya Amma meyasa baki fad a mishi dalilin rabuwar ku da Mansur ba? kika sani ko sonki yake.  Allah ya kyauta. Kawai Asiya tafad a domin batasan me zatace ba. ***************** Yau ne Ranar da za ayi wa Zainab Babbar tiyata wacce take sirad in ko rayuwa ko mutuwa.   Gaba d aya Tun safe Master yakasa zaune yakasa tsaye,  yana zaune kusa da zainab akan gadonta. Zainab ce ta kalleshi ya sunkuyar dakai alamun yana wani tunanin sanan tace.  Mijinaaa. A hankali yad ago kai yakalle ta batare da yayi magana ba.   Dan Allah ko bayan Raina na dinga kasancewa cikin ranka, kar kamanta dani da huri.  Zainab ki daina fad in haka ba mutuwa zakiyi ba Insha Allahu zaki tashi.  Kasani idan namutu a yanzu ba laifi na bane Allah ne ya amshe ni dan Allah ka kula da Abinda ke ciki na domin nasan ba lallai bane shi yatafi sabida a yanzu yakai wata 7. Azabure ya d ago ya kalleta tare da rik e hannunta.  Zainab daman na fad amiki ciki ne dake daman amma kika ki yarda kikace dani ciwon ne.  Nima sai a zuwan mu asibitinin Dr Shiraz yasanar dani kuma yace za acire d an cikin kafin ayi aikin.  Zainab insha Allahu zaki tashi za afito dake lafiya.  Ya maganar tura iyaye wajen Mahaifin Ummi. Damamaki yabita da Kallo sanan yace.  Zainab wai bakya ta lafiyar ki ta zancen Aure na kike, Zainab zan hakura da turawa har sai amfito dake daga theater munsake magana.  A ah yaballabai katura.  Zainab bazan turaba nagama magana. Shiru ne yabiyo baya na tsahon mintin kafinan yatashi yashiga toilet. Page[42&43] B angaren Ummi kam tun safe take jiran kiran Master Amma shiru m, har suka zo tafiya airport tawowa da Yaya Umar. Gaba d aya hankalin ta baya tare da ita yanaga Tunanin Master har suka k arasa cikin airport d in. Bawani jira sukayi ba jirgin su Yaya umar d in ya sauka, dukkaninsu suka nufi wajen fitowar su kowa fuskar shi d auke da fara a. Kyakyawan matashin dake tawowa, ya d auki hankali duk wata mace dake wajen, kallo ya koma kanshi hatta su Ummi da Asiya ido suka zuba mai.  A hankali yake taku cike da nutsuwa, gayu da kuma izza, taku yake na cikakkun maza, masu kwarjini.  Duk irin kyawun Master dasu Ummi ke fad a bai kama ko k afar wanan matashin Saurayin ba.  Nikam Ummi wanan kamar yaya fa. Asiya tafad a tana kallon yanda yake tunkarusu.  Ni banga kama ba amma dai gashinan yana yin inda muke. Murmushin da Yasakar musu ne yasa Asiya daka uban tsalle tare da fad in.  Yayahhhhh. Tayi kanshi da gudu tare da rungumeshi, shima kuwa ya rungume ta tare da fad in.  I missed you lil. Cikin sasannayar murya dake fitar da kowanne harafi na turanci.  i Missed you more Yaya. Cigaba da  tawowa yayi hankalin yan mata nakasan su Mussaman da sukabi Asiya tace Yaya, dawasu har sunfara jin haushin ta sunyi tunanin Saurayin tane ko mijin ta. A haka yak araso har inda Ummi take, Kallon ta yayi sanan yace.  Masha Allah yara duk kungirma, ina mai gidan nake. Dariyar yak e Ummi tayi domin tun zuwan shi wani abu ya mak e mata arai sanan cikin rawar baki tace.  Batare muke ba. Dariya Asiya tayi sanan tace.  Ni baka tambayi nawa mijin ba?.  Ke ai nasan bakiyi Aure ba. Yafad a suna cigaba da tafiya zuwa inda motar su take.  To ita wayace maka tayi Aure?.  Ai da zantafi nasan tana relationship da Master yake kowa and nasan is hardly su rabu bayan wanan soyayyar.  Basu rabu ba Yaya amma har yanzu basuyi Auren ba. Asiya tafad a dai dai lokacin da take bud e masa boat domin su sa akwatin shi. Kallon Ummi yayi sanan yace.  Ummi gaskiyya tafad a. Ummi data kasa sakewa ce ta gyad a kai alamun Eyh. Sai da suka shiga motar sanan yak ara cewa.  To yanzu yaushe ne Auren.  Yaya kacika tambya ko so kake a had e da naka auren.  Kawai ina mamaki ne, amma i know definitely something happened.  Nothing happened yaya gashi ta koma ma kamar kurma da sai tabaka labarin. Ummi dai batasan meke damun ta ba, hakan yasa ta zab i yin shiru, har suka k arasa gida. Mutane sun hallara A Gida anata murnar dawowar Yaya Umar, Ummi dai tarasa meke damunta, amma ta lak ana hakan da rashin jin Mastet da tayi tun safe. A hankali ta salub e ta koma nasu Gidan,sanan tasamu kiran Master dake zaune bayan shiga da Zainab d akin theater. Yana ganin wayar amma yakasa d auka gaba d aya tausayin Zainab yacikashi, yana ganin kanshi mai butulci, wanda yayi watsi da rashin lafiyar ta ya shiga neman Ummi. Haka taita kira baisami d auka ba ganin tayi masa kira sama da biyar, sanan ta hak ura tare da kwantawa. *********************    Affan nayi magana da Mahaifin yarinyar nan amma yanuna baisan da wanan magana ba, wai su sunjanye baikon su. Hajiya Balki ce tayi saurin cewa.  Toh Amma Alhaji haka zaka tsaya, bazaka nuna mishi power ba?. Murmushi yayi sanan yace.  Hajiya naso nayi haka amma Alhaji idi yahanani sakamakon ko da anje kotu basu da wani abu da za a iya, tunda basuyi auren ba.  But Daddu gaskiyya ni inason ta. Affan yafad a, kallon shi Abban yayi sanan yace.  Kana sonta ka tafi kabarta na tsahon shekara Hud u?.  Dad komene yafaru ya riga yafaru kawai ni kayi magana inason ta.  Daman fa Alhaji zance a hak ura bai taso ba ainaga bamu amshi kud in auren ba ko?. Hajiya Balki tafad a domin ita duk abinda d anta keso tofa tana sonshi.  Hajiya ni nagama magana, kuyi duk yadda zakuyi idan wani abu yataso sai ku nemi ni. Abba yafad a tare da tashi, Affan ne ya matso inda take tare da cewa.  Mom yanzu mene abun yi please?.  Affan karka damu yau zanje nasamu mahaifiyar ta.  Okay Mom please. ******************************  Hinin ranar Ummi bata samu Master a waya ba, abinda ya matuk ar tayar mata da hankali tare da sama damuwa, baya ga yanayin ta datake ji badai dai ba.   Asiya ce dake zaune gefe tace.  Wai yanzu Ummi mene abunyi ko tashi zakiyi muje mune meshi. Dariyar yak e Ummi tayi sanan tace.  Lallai Asiya sai kace yarinta zan koma neman master, ai sai dai yadawo da kashi.  Dariya Asiya tayi sanan tace.   Lallai yanzu nasan kinzama mutum.  Au da ba mutum bace. Ummi tafad a tana nuna kanta, dariya Asiya tayi sanan tace.   Eyh da muna mutum ce yanzu kam nasan ko da Master yak ara tafiya ba abinda ake fata ba, bazaki damu ba, ko shiga wani hali.  Dariyar tayi sanan tace.  Uhm ayi sha ani kawai, amma banjin zank ara zurmawa a soyayyar har na k arasa Kuskuren yin TUDU AKAN KWARI wanda har yanzu yake bini shekaru Sama da biyar. K arar shigowar text a wayar Asiya ne yakatse musu hirar tasu, dauka Asiyan tayi bayan tagama karantawa sanan tace.   Ummi bansan mai Nawfal yake nema ba fa, wai yanaso muhad u muyi magana.  Uhm koma mene zamuji amma nasan Nawfal sonki yake.   Ummi tafad a tana d aukan wayar ta tare da kunna data ko zata sami messages daga Master.  Sona fa, shi yanzu har yayi healing daga rashin ki.  Ummi bakisan ana iya canja so daga wanda kakeso zuwa wani dayake kusa dashi ba?.  Bansani ba sai a bakin ki kuma banyarda ba. Dariya suka fashe da ita sanan Ummi tace kice masa yazo yau, kinga ko ma mene sai kiji. Danna wayar tayu tamayar mai da reply. ************************  Anfito da Zainab daga theater kuma ana saran samun nasara.  Dr Shirza ne ya kalli Master dake zaune a cikin office d in shi.   Mr Mukhtar Inaso kafad amun komai dake gaskiya.  Game da me fa doctor?.  Game da matarka.  Okay inajin ka.  Dafarko dai anyiwa Matarka aiki kuma muna fatan samu nasara, matar ka na buk atar kulawa ta gaske a yanzu, irin kulawar da za ace mutum yana tare da ita bbu motsi ko da na yan sakanni.   Banganeba Doctor?.  What i mean is matarka na bukatar wank a kusa da ita wanda zai dinga kula da ita ko yaushe, kamar mutum biyu yanda ko d aya bayanan d aya na nan.  To ni likita me nake da bazan iya kula da ita ba har haka?.   Bansani ba amma nasan dai ba kowanne namiji bane zai iya wanan.  To ni zan iya insha Allah. Master yafad a cike da kwarin gwiwa.  Allah yasa. Dr shirza yafad a sanan yad ora da cewa.  Abu na biyu shine akwai damuwar dake damun matarka a zuciya wand tak e boyewa. Shiru Master yayi yana tunanin daga baya kuma yace.  Dr i don t think akwai abinda Ke damun Zainab har ta boyemun.  Bakwa ko wata irin magana ko kai zakai wani abu bataso ko kana hanata wani.  Magana daya dai nasan zan k ara Aure amma kuma tanaso.  Dariya Doctor Shiraz yayi sanan yace.  Dan tace maka tanason shine kake yin zancen, mata zasu iya nuna maka suna son abu kuma ba haka bane, bare ma zancen kishi, idan badamuwa kabar maganar zuwa nan da sati d aya idan jikin ta yayi k wari.  Shiru yayi tabbas yanason magana da Ummi amma kuma lafiyar matarshi ce abu nafarko,yasan Ummi mai fahimtar shi ce.  Daga haka yatashi yakoma d akin da aka mayarda Zainab sai kuka jaririn ta dake wata 7 ansa shi cikin kwalba. *****************  Da misalin karfe 4 na yamma Hajiya na zaune tsakar gida sai kuma Goggo daga gefe tana faman b are wake.  Sallama hajiya Balki tayi tare da shigowa, da fara a Hajiya ta amsa sallamar tare da fad in.    Balki yau ke ce a gidan maraba. Daga tsaye Hajiya Balki ta amsa da.  Nice zuwa nai akan maganar Ummi da Affan.   A ah to shigo ciki mana. Hajiya tak ara fad a tana tafiya.  Bafa sai nashiga ba nazo sanar daku cewar za akawo kayan lefe gobe. Dariya Hajiya tayi sanan tace  Wane kalan kayan lefe kuma?.  Kayan lefe na Aure sanan sati d aya zamuzo dashi.   Da ke a garin jahilai kika taso ko me?.    Goggo tafad a tana mikewa.  Ke matar nan na fahimci ba hankali a tare da ke, ko a zamanin turawan mallaka ba ayi haka ba balle yanzu a zamamin yancin kai da kai.  Goggo tak ara fad a, Hajiya kam cewa tayi.  Balki Affan yariga da yayi wasa da damar shi, a yanzu Ummi tafi k arfin na tan k wara ta kamar baya, idan Affan ya nemi soyayya a wajen ta, tabashi madalla, idan kuma ta hana shikenan, ba zamuyi mata auren dole ba.  Tsaki Hajiya Balki tayi sanan tace.  Wallahi Baki isa ba, kuma dani kike zancen. Daga haka tafice suka suka shige d aki kamar komai bai faru ba. Page [44&45] _________Bayan Sati guda_______ A yanzu sati guda kenan Ummi bataji daga Master ba, tayi fushi ta fusata har k arshe ga Abba ya matsa mata kan ta samu tafitar da wani.   B angare Asiya kam sun dai dai ta da Nawfal an saka musu rana wata biyu masu zuwa. Soyayya suke tare da mutunta juna, inda Ummi a wani b angaren take ganin kamar tayi biyu babu.  B angaren Hajiya Balki a sati d ayan nan tayi duk yansa zatayi amma duk inda taje sai ace bata da wanan damar, Affan kam yadamu matuk a akan lamarin Ummi.   B angaren Umar kam hutun kwana biyu, yafara zuwa interview da manyan campanunawa damam tun yana chaina yafara applying hi  A yanzu ya zab i wani babban campanu guda d aya da suka bashi babban muk ami  ***************   Umar ne cikin shigar k anan kaya da k ara fito da asalin kyawun shi, kai tsaye gidan Hajiya ya nufa, inda yasame ta zaune ita da Goggo data dawo gidan da zama.  Sallama yayi musu tare da gaidasu,Goggo cike da fara a ta amsa haka ma Hajiya.  Daman Hajiya nazo ne muyi magana da ke,domin bansan ta inda zanfara da Mama ba shiyasa nazo nayi dake a matsayin ki na Uwata.  Har cikin ran Hajiya take jindad in yadda Umar ke girma mata, ita daban dan kar ace tayi son zuciya ba ma da Ummi zafa nemawa auren shi.  Shikenan Umar zamu iya yi anan ko sai munshiga ciki.  A ah Hajiya muyi anan d in.  To ina jinka.  Hajiya maganar Gaskiyya guda d aya itace inason Ummi, nanu nawa Mama alamu amma tace babu ruwanta wai naje nasami Ummin dakai na hatta itama Asiya abinda take cewa kenan, kuma ni a iya bincike na Ummi babu wanda ke zuwa wajen ta, bansani ba ko kune kukayi mata miji.  maganar gaskiyya a yanzu bamuyiwa Ummi miji ba, kuma babu wani dake zuwa wajenta, sanan ni shawarar da zanbaka itace kasami mahaifin ta da maganar tunda dai shawara kazo ne ma. Hajiya tafad a ranta fari fat.  Idan kuma bazaka iya ba ni sai nayi mai maganar.  Goggo tafad a itama nata ran fari k al. Abba da yashigo ne yace.  Ai ba ma sai an tambayamun ba. Yafad a yana shigewa d akin Ummi wacce kijin su tinda ga farko, ita bata masan me take ji ba, domin bazata ce tana farin ciki ba sanan kuma bazata ce tana bak in ciki ba, ita kanta tasan samun Yaya Umar sai dace.  Ummi kinji abinda dik suka tattauna, kuma banaso nayi miki dole, amma a shawrar da zanbaki karki karbar wanan zab in.  Abba na amince Allah yasa hakan alheri ne.   Amin Ummi Allah yayi miki albarka.     Fitowa yayi sanan yace da Hajiya.  Kiramun Maman a waya kice ta shigo nan. Kiran Mama Hajiya tayi bayan mintina sai gata tashigo tare da Asiya. Bayan kowa ya zauna ne Abba ya kalli Mama sanan yace.   Umar yazo mun da magana wacce kuma babba ce akan yarinya Ummi .  Tom muna jinka Alhaji. Mama tafad a duk da tasan mecece maganar.  Umar yazo akan yanasom Auren Ummi, kina da masaniya?.  Eyh ina da masaniya Alhaji, amma Ummi y atake a wajena, nasan komai akan rayuwar ta, har mutum da takeso nasani, sanan a baya angwada yimata dole amma ba a haifi d a mai ido ba, shiyasa na hanashi sanar daku. Abba baice komai ba sai kiran Ummi da yayi, wacce tafito jiki ba kwari.  Ummi kinji maganar da muke tattaunawa?. d aga kai tayi sanan tace.  Abba naji.  Me kika yanke game da maganar.  Abba na amince zan auri Yaya Umar. Da matuk ar mamaki kowa yad ago yana kallonta harda kuwa Asiya.  To kowa yaji dai, Allah yasa albarka. Amin kowa ya shiga fad a kansa tsaye. *********** Bayan kwana uku. Abu kamar wasa Ummi ta daina shiga gidan Mama sai dai Asiya tashigo. Sunsami magana da Yaya Umar, tare da fahimta mai k arfi, sanan kuma Ummi bazatace batason Yaya Umar ba, domin a kwana ukun nan yarage mata kaso mai nauyi nason master da damuwa. Mujuya bangaren Master. Zainab tatashi sanan kuma duk wata kulawa yana bata, duk da duk rabim tunanin shi naga Ummi da a yanzu baya samun ta a waya.  Tunda Zainab tatashi bai maganar Ummi ba, da farko idan tayi banza yake mata har ta daina, tabbas taji dadi hakan, ko da kuwa bai janye ba amma ya daina nunawa a gabanta. Soyayya tskanin Nawfal da Asiya kamar wasa sai karfi takeyi, an sanya lokacin Auren su da nasu Umar Sati hud u. Kowanne b angare soyayya suke zubawa mai tsafta domin shima Yaya Umar kwararreni a b angaren soyayya. Lokaci d aya Ummi tayi blocking numbers d in Mastet daga bayama ta canja sim. Master yayi tryiing yafi a k irga amma bata tafiya, sai dai Zainab tayi kwana goma a asibiti sanan yasamu fitowa, sakamakon zuwan rogeet wanda shima a yanzu yasamu nashi rufin asirin, sosai da sosai.  Baba inason zuwa wajen Ummi Wallahi. Kallon Master Rooget yayi sanan yace.  To mai kake jira muje mana. Motar Rogeet suka shiga kai tsaye suka nupi gidan su Ummi. Dai dai lokacin  da Ummi da Yaya Umar suka zasu fita zuwa kasuwa, fiowarsu daga gidan  Hajiya yayi dai dai da parking d in motar su Master. Sai dai Ummi takalli motar amma bata gane ba sabida ba acikin mototicin Master domin shi number d inshi sunfita daban. Master kam bugun zuciyarshi ne ya tsaya na lokaci guda domin ko makaho indai zai kalli Ummi da Yaya Umar yasan akwai soyayya a tsakanin su. Har su Ummi suka bud e mota suka shiga Master bai iya cewa komai ba.  Master yaushe rabon ka da Ummi.  Sama da kwana goma kuma babu kira babu text, kuma dai dai lokacin da take jiran iyayena su sami nata.  Amma kasan wnn shneYayan Asiya K awarta wanda yatafi k asar waje?. Girgiza kai Master yayi sanan yace.  Banganeshi ba gsky.  A iya tunani rashin ka yasa Ummi ta bashi dama, tabbas a yanzu Ummi tayi give-up akanka Master.  Nagani Wallahi, kuma nima a yanzu lokaci ne da zan duk ufa akan Raywuar Zainab da abinda ta haifa. Daga haka Su Master suka juya zuwa Asibiti Page [End] B angaren Su Ummi kam cike da soyayyaa suka je kasuwa suka siyayyar dazasuyi har suka dawo. Akwana a tashi Gashi yau Allah yakawo mu ranar da ake daurin Auren Su Ummi da Asiya, Tunsafe Ummi ke faman kuka wanda babu wanda yasan na mene,anyi rarrashin har angaji. Itakuwa Ummi tana tunanu duk wata wahala da tasha a rayuwa sabida Master sai gashi k arshe bashi ne mijin taba, lallai alamarin Allah da girma yake. Tana wanan tunanin Yan d aurin Aue suka dawo tare da shaida an d aura auren Ummi da Yaya Umar, Asiya d Nawfal. Shikenan komai yafaru ba kuma yadda aka iya da hukuncin ubangiji. Ummi ta d auki aniyar yin biyayya ga mijinta iyaka cin yinta, domin tabbas a yanzu Master ba ma harramin ta bane, zata cirewa rayuwarta gaba d aya tunanin shi. Wanan kenan Haka b angaren Master ya d auki alwashin cire Ummi da duk wani tunanin ta a rayuwar shi, ya kuma yardar wa kanshi komai nufine na ubangiji, duk wata tataburza da suka sha shida Ummi a karshe ita d in ba rabon sa bace. Zainab na zaune yashigo cikin shiri, kallon ta yayi sanan yace.   Zaki iya shiryawa mufita unguwa.  Zan iya mana, jirani. Tafad a tana mik ewa, yan mintina kad an tafito cikin shirin ta, tayi kyau abinta. Sai da suka fara biyaea ta wani Babban shop da ake sai da kayan electrics, sukayo Ummi mahaukaciyar siyayya, da mamaki Zainab take kallonshi wanan kayan ko na waye oho?. fitowar su kenan bayan angama zuba kayan a yar k urk ura su kuma suna k ok arin shiga tasu motar suka ji ana cewa.  Dan Allah ku taimaka mana da Abinda zamuci. Zainab ce ta tsaya tana k ok arin bud e jakarta ta zaro kud i, shikuma Master ya juyo, idanun sa ne suka sauka akan matashiyar buduruwa mai suffar tsofaffe sai kuma k aramar yarinya. Kallon sani yakeyi wa matar haka itama, can kuma matar tace.  Maater. Kallonta yak arayo ko zai ganeta amma yakasa.  Halima ce.  Wace Haliman?.  Halima gidan su Asiya makwafciyar Ummi. Sai a lokacin Master yaganeta.  Me kuma kikeyi anan?. Nan Halima tafara bashi labarin irin halin da suke ciki ga kuma yarinyar ta sanan Anty na wani kango a ajiye sai sunyi bara suke kaimata.  Lallai duniya abun tsoro ce, Yaran da kuka gama bi da sharri gasu can yau ake auren su kuk gaku kunk are a hulakance. Da mamaki Halima tace,   yau ake auren Ummi da Asiya, duk asirin Da anty tayi na karsu Auro gashi yagama k arewa.  Asiri kuma?. Master ya tambayeta, cikin kuka halima tafara fad in.  Ai Aunty ce tayi Asiri akan kar su Auro Asiya tak i samun miji da huri sanan Ummi aka hana auren ku sanan aka cirewa Affan tunanin ta a tafiyar da yayi.  Duk abinda yafaru yana rubuce a k adaddarmu amma haka yafaru ta sanadiyar ku, kuje Allah yasa rayuwa ta sa kuyi hankali, dukda yanzu gashinan tajuya muku. Kuka Halima tak ara fashewa dashi, sukuma sh Mastet suka huce. A cikin mota kam Zainab ce ta kalli Master sanan tace.  Yanzu yau ake auren Ummi da kuma wani bakai ba?.  Gashi kinji.  To su wayanan d insu Waye?. Zainab tak ara tambayar shi.  Zainab A labarin Asiya da nabaki nace miki akwai kishiyar Mamanta da yarinyar ta, to itace wanan.  Amma basu yiwa kansu Adalci ba.  To gashinan rayuwa tafad a musu ai. Maater yafad a dai dai lokacin da suka shiga layin su Ummi. Da mamaki mutane suke kallon yar k urk ura maj cike da kaya ta tsaya dai dai gidan su Ummi. Master ne yace da Zainab.  Ki sauka kifara shiga. Tom tace tare da fitowa, daga cikim gida Zainab ce tashiga da sallama, bayan ra kuma masu shigo da kayane. Anty Nafisa dake faman kawo abinci ce ta tare da cewa.  Maraba sannu da zuwa. Cike da wayewa, halin Anty Nafisa tabbas ya burge zainab.  Yawwa Amaryar na cike ko.  Ey wancan d akin zaki shiga. Anty Nafisa tafad a tana nuna mata d aki. Tom zainab tace sanan ta kalli masu shigo da kayan tace.  Ku ijiye kayan anan t sakar gidan. Sana tahuce, Ummi na zaune cikin d akin da wasu kawayen ta yan uwan su, Da gefe kuma Asiya ce wacce take shiri domin ita yanzu za azo tafiya da ita. Da sallama zainba tashiga sanan tasamu waje ta zauna bayan sun amsa mata tare da bata izini. A kallon farko Zainab ta gane Ummi hakan yasa ta kalleta tare da cewa.  Sunana Zainab, Matar Mukhtar. Wani irin dum Ummi taji a k irjinta amma cike da dakewa tace.  Sannu Zainab.  Yawwa Amarya, Allah yasanya Alheri.  Amin Amin. Ummi tafad a taba kallon wata a cikin k awayenta sanan tace.  Kice ma Anty Nafisa akawo mata abinci.  Ai tare muke dashi yana daga waje. Zainab tafad a tana kallon Ummi, wani irin abu Ummi taji da kyar ta iya cewa.  Allah sarki nakam gode sosai. Asiyace tace.  Ai kya tashi kije ku gaisa dai ko. Ummi batace komai ba ta tashi tasa mayafin ta tare da ficewa. Mutanen dake tsakar gida nata mamakin uban kayan da akw zubewa. Dan harsu Hajiya da Gaggo sunfito, da kallo suka bi Ummi da tafito, itama da mamaki take kallon kayan.  Ke wanan wace?. Anty nafisa tafad a cikin kasa kasa da murya.  Matar Master ce. Ummi tafad a hankalin ta na kan Uban kayan da aka zube. Komawa tayi tare da cewa Asiya   zo ke. Tashi Asiya tayi tafito itama mamakin ne ya hanata magana dan tasan wnn aikin Master ne.  chab aiki ga mai k are ka, fita kika dame yazo. Asiya tafad a tana tura Ummi, fita tayi, ta hangeshi ya kafe k ofar gidan nasu da ido, sai da taji wani abu yabi jikinta lokacin da suka had a ido. A hankali tak arasa inda yake tare da cewa.  Gani. Murmushi yayi sanan yace.  Yanzu dai kin girma kinyi aure yakamata ace

Chapter 9 of 10