Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 10
magariba sanan suka fara shirin tafiya.   Tafe suke a hanya cikin motar Asiya, wacce Ummi ce ke driving motar, k arar kiran da yashigo cikin wayar ne, ya katse wa Ummi maganar da take shirin yi.   Tabbas a yanzu ta gane number Master duk da ya kan canja lamba ya kirata. Nunawa Asiya Wayar tayi tare da cewa bana raba dayan biyu Mukhtar ke kira. Page [37&38] Daga wa tayi ba tare da tayi magana ba, sanan tasaka wayar a speaker.    Naji dadi da kika daga wayar. yafaf a cike da sassanyar muryar shi, Shiru Ummi tayi ba tare da tace komai ba.   Ranki yadade ko bacci kike?.   Mutuwa nake.  Tabashi amsa a gajarce, Dariya yayi mai sauti sanan yace.   Ay hakuri Ranki yadad e sanan agaida mini da Asiya.  Kallon Ummi Asiya tayi itama Asiyan ta kalleta.   Wake magana ne?. Dariya ya karayi sanan yace.   Dan Allah ranki yadad e alfarma Rana d aya nakeso a bani ke da Asiya, Zan zaiyyane miki komai da yafaru, idan kinji zaki iya yafe mun idan kuma baxaki iya ba, duk wani hukunci sa kika yanke zan k arb a nabi.   Shiru Ummi tayi na tsahon lokaci sanan tace.    Ka tabbatar duk hukuncin dana yanke zaka karb a.  A Ranki yadad e, sai dai ina rok on ki da ki saura reni da kunne fahimta sanan kiyi adalci agareni.   Insha Allah.  Yanzu yaushe aka bani?. yafad a da irin salon muryar shi ta da,domin yaga kamar hankalin ta baya tare dashi.   Dariya tayi mai d an sauti kafi  tace.    Duk sanda kake da lokaci.  Gobe dan Allah.  Allah yKaimu.  tafad a tare da kashe wayarta sanan ta juya ta kalli Asiya.    Mene kuma kike kallona ?. Asiya tafad a dan taga yanda take kafe ta da idanu.    Hakan yayi dai ko?.  Yayi mana Ummi daman yana da kyau a zauna a fahimci inda matslaal take, idan da rbo sai kiga shi din ne dai.  Tab da TUDU AKAN KWARI ya tabbata. Ummi tafad a taba dariya ita Asiyan dariyar tafara sanan tace.   Yanzu dai Allah yasa su Hajiya su Amshe shi.   Amin dan Annabi. Daga haka suka cigaba da hira har suka karasa gida.   Mutane ne tsaye daga k ofar gidan su Asiya.  Innullahi me yake faruwa a k ofar gidan Mu. Asiya tafad a hankali a tashe, itama Ummi cikin tashin hankalin tace.   Gadai mutane tsyaw Allah yasa Lafiya.  Wanan tsayuwar ba ta lafiya bace Ummi, ke dai yi parking. Guri Ummi tasamu tayi parking sanan su kafito zuwa k ofar gidan, ita dai Asiya tunda idon ya yakai kan Mama hankalin ta ya kwanta, dan koma mene daga bayane.  A haka suka karaso wajen, idanun sune suka sauka akan wata yagalgalliyar mata da kuma wata babbar mace sai yarinyar kimanin yar shekara uku.  Mama lafiya su waye way anan haka?. Asiya tafad a bayan sun k araso wajen. Hajiya ta bata amsa da cewa.   Anty kice da Halima da kuma yar Halima. Kallon Hajiya Asiya da Ummi sukayi sanan Ummi tace.   To me ya kawo su, su kuma mutanen da suka zagaye nan fa.  Hak uri ake bawa Maman Asiya wai ta k arbeta. Asiya ce tayi caraf tace.  Wallahi never =ØNÜ ba tayanda za ayi bayan hulaknci da sharrin da tinga bin mu dashi, yaushe taje gidan su Suwaiba, bayan har kudin auren yaya Umar ankai tace wai isakanci yake yi acan chaina sukuma suka daowa da kudin suka cw amfasa bayan wanan sharri kala nawa.  Kinga Asiya shege cikin da Hajiya ja Ummi ku shige naku gidan, duk mai tausayin su ya dauke su yakaisu nashi gidan, ai duk sun san halinta.  Nan mutane su fara watsewa, itaku Anty ko magana bata iyawa sai mungun wari dake fitowa daga cikin ciwon k afarta, ga yar shegen Halima sai taka ciwon take. Itaku halima cutar kanjamau din dake jikin tace tasa ta rame takoma kamar wata tsohuwa. Haka Asiya tashige da motar ta tabarsu a wajen domin kuwa ya watse.    Gaskiyya Atine kim cucemu, da mutane sun sanki da hali mai kyau ai da sun taimake mu, amma dik sun miki muguwar shaida.  Halima tafad a domin tagaji da tsayuwar da suke, ga kuma ciwon dake jikinta duk yagama k arar mata da karfi, dan a yanzu bama sajim warin dake tashi daga ciwon Aunty. Kuka Anty tafashe dashi tare da cewa.   Ni Atine nayi Asara nayi nadama, yarinyae da naki zaman lafiya da kowa akan ta, ita ke zagina. Haka suka k araci zaman su,kafin suka tashi suka cigaba da tafiya. *********    Wai Asiya maganar ki akan me take ne ni bangane ba?.   Mama kenan take tambayar Asiya bayan tafaa mata cewar tafasa Auren Mansur.  Mama kamar yafda nafad a miki wallahi nafasa Auren Mansur kuma shima ya yasani, kowane lokaci zai iya aiko k arbar kudin shi da kayan shi  To Asiya babu dalili ne da zaki iya fad a ko bani bawa wa yan uwanki da yan uwan mahaifin ki, Asiya bakya ganin girman da kukayi ne?.  Mama Aure lokaci ne, kuma girma ba akan wani muke ba, duk wanda zaiyi magana yaje yayi, nipa Mama har aikin shi na ajiye mishi.  Allah magani makwoci maye ni Sahura,Asiya wallahi karki ga ina sake miki kidinga iskanci ai jibi yayan naki zai dawo kya mai bayani.  Daga haka Mama ta tashi ta huce.    Yaya zaidawo Amma ko yafad amun lallai mutumin. ************ A gidan Anty Nafisa suka shirya had uwa da Master, haan yasa tun k arfe biyu suka tafi gidan.   B angaren Master kam yana zaune kusa da Zainab waccce ba a dad e da fitowa da ita daga d akin treatment be.   Katashi kaje haka, kar taita jiranka. Murmushi yayi sanan ya kalli Zainab.   Nikam bansan meyasa kike abu kamar ba kyajin kishi na ba?. Dariya itama tayi, to akan me zatayi kishi ta wahalal da kanta, tun had uwar su tafako ya gayamata wacece Ummi da irin son dayake mata.  Tsahon way anan shekarun bai dai na son taba itakuma kuma haka, to akan wane dalili zata wahalal da kanta.  Kinyi shiru?.    Me kakeso nace? kasan dai ina sonka, ina son abinda kake so wanda zai baka farin ciki, to mene zaisa nasako kishi a ciki?. ****************   K arfe uku dai dai Master yayi parking Glk dinshi a k ofar gidan Anty Nafisa, waya ya dauka ya kira lambar Ummi.   Sai da takusa katsewa sanan tasamu d agawa.   Ranki yadade na k araso.  Uhm kad an jira. tafad a tare da kashe wayar  Bata wani jima ba akayi masa iso zuwa babban falon gidan, Ummi ce tafara zama sai bayan yan mintina Asiya ta sami isowa.   Tabbas taga sauyi a jikin Master dam daman tunda yadawo basu taba haduwa ba.    Ah Asiya abinda yasa na nemi ganin ki, shine inaso kiyi adalci a cikiin duk abinda zanfad a, sanan nasan ke zaki bawa Ummi shawara tagari akan duk abinda yakamata.   Insha Allah zanyi duk abinda ya dace.  Masha Allah. yafad a cikin muryar shi mai zak i da amo.   Tun a lokacin da Abba yahana ni Auren Ummi a karo na farko naji nayi danasanin duk wani hali da nake dashi. Page [39&40]   Tabbas nayi duk wani danasani da yakamata, har zuwa kwanciya ta a asibiti da sallama ta.  Ummi samum labarin mutuwar ki, ya tsayar mun da duk wani karf i, da kwarin gwiwa da nake dashi a rayuwa, na gwammace  ace nima tawa rayuwar ta k are.   kwatsam kuma naji labarin farfad owar ki  Ummi wani abu yashige ni a wanan lokacin, nida nasaki a wanan halin bani da yadda zanyi na taimakeki sai yan uwanki da nasa kika bijirewa, sune suke taimakokin ki.  Menene amfani na cigaba da zama dake tunda nasan ba karb a ta zasuyi ba, nasa ki cigaba da bijire musu kina musu abinda bai kamata ba kinayim TUDU AKAN KWARI wanda bazai taba tsallakuwa ba.   Hakan yasa na yanke shawarar yin nesa,wanda nasan dole zaki ji ba dad i amma nasan hakan zai amfane ki gaba, na yanke shawarar yin can nesa ko rayuwata ta gyaru ko ta k arasa b aci duk d aya.   Natafi ba tare da nasan inda nakama ba, natafi ba tare da nasan inda na nufa ba, natafi ba tare da nasan me zan samu can inda zani ba.    Anan k addara ta mik ani garin legos, na yanke shawarar zuwa garin ne domin nasan duk wata rashin kunya ta akwai wayanda suka fini.  Sauka ta garin legos yayi dai dai da cin karo da Zainab da nayi tare da wasu matasa su uku , suna neman yi mata fashi. Da farko nayi kamar na kyalesu natafi abinda ya shafe ni, sai kuma naji baxan iya ba. Nayi iya kacin yi na, sanan na kora way anan matasan, tabbas Zainab taji dad in hakan har yasa ta dage sai taji wani abu akaina. Ummi ban boye mata komai ba tinda ga sanda nasan rayuwa har zuwa haduwa dake da kuma rabuwar mu. Zainab ta kasance mace ta gari, domin ita ta d auke ni a gidan ta har na koma na gyara diploma ta sanan tabani aiki a companin ta. Daga baya tazo mun da kud irin tanaso ma aure ta, Zainab bata tab a saremun gwiwa akan sonki ba har takai ga na Aure ta. A zabure Ummi ta mik e tare da fad in   What?.  Mukhtar kayi Aure?.  Zauna Ummi na k arasa gayamiki mana dan Allah.  Babu abinda zan k arasa ji mukhtar. Asiya ce ta rik eta tare da cewa.  Ummi nutsu dan Allah.  Asiya to me zan zauna nayi tunda yariga yayi Auren shi, Ai yasan ina sonshi yasan dani ya tafi ya barni, bai damu da halin da zan shiga ba, to kasani a bayan tafiyar ka Abba dakanshi yasa na nemo ka zai bak  Aure na. Nan tashiga shaida mishi duk abinda yafaru.  Wanan takardar tun kafin wanan lokacin nabawa Baddo shine bai kawo ba sai da yaci kudin ki amma baimasan garin su Abdullahi ba.  Ummi Allah bai kaddara Auren mu ni dake a wanan lokacin ba sai yanzu.  Tabbas Ummi idan kika nutsu akwai abinda Allah yake so ya nuna muku shiyasa bai bada damar yin Auren ku a wancan lokacin ba. Asiya tafad a hannun ta na rik e da Ummi, Shiru dai Ummi tayi tabbas tasan har yanzu tana son Master so kuma ba kad an ba. Tashi yayi daga inda yake zuwa gabanta tare da durkusa wa da dukkam gwiwam shi a k asa, a hanakali cikin kwantar da murya yafara magana.  Ummi nasan na kasance mai laifi a wajenki tun daga tafiya ta har zuwa auren zainab, amma inaso kisani komai yafaru ne bisa tsari na ubangiji dan Allah Ummi kiyi hak uri ki k ara karb a ta akaro na biyu.  Shiru Ummi zuciyarta na wani irin bugu dum dum.  Please>ØzÝ. Yak ara fad a a hankali.  Shikenan Mukhtar i will think about it.   What think please>ØyÝ.  Yafad a murya kaman zaiyi kuka, A hankali Asiya ta zame jiki tabar wajen zuwa d aki.   Mukhtar kasan dole sai nayi magana da iyayena, banaso na k ara jawo abinda zaka gudu kabarni.  I will fight the battle with you Ummi. Shiru tak arayi daga baya kuma ta mik amasa hannunta.  da sauri ya bud e zoben ya zura mata a hannu tare da cewa.  Insha Allah Ummi i will stay with you forever no matter what. Shirun tak arayi tabbas inda ta zuciyar ta ne tanajin dama takasance a haka tare da Mukhtar domin tabbas zuciyar ta na mugun son Mukhtar. Zama tayi shima ya zauna a kujerar dake kusa da ita, yafara magana a hankali cikin kwantar da murya. ****************** Tun a airport yake zuba idon ganin Ummi amma shiru hakan yasa yakasa daurewa ya tambayi mahaifiyar shi Hajiya Balki.  Mom where is my Wife?. Kallonshi tayi sanan tace.  Ai kai zamu tambaya tunda kai kad ai muka gani.  No Mom ba Angelina ba, wanan yarinyar ya ma sunan ta?. Banza tayi masa dan ita bata gane wacce yake nufi ba.  Mom magana fa nake please. Yafad a murya cike da shagwab a kaman zaiyi kuka.  Affan bana ciki da iskanci wace matace dakai da ta huce wacce mai sunan arna da har ka manta sunan ta.  Mom yarinyar da kuka aura mun fa.  Ni bansan yarinya da aka aura ma ba sai dai wacce akayi maka baiko kuma iyayen ta sun janye wanan baikon.  What Mom baiko kuma i thought anyi mana Aure da ita.  Oh kana tunanin anmaka aure da ita shine kabarta a hulak ance kenan.  No mom ba haka bane.  To kuma yane kai kasani iyayenta sunyi duk mutuncin da zasuyi kuma sungaji Last week Mahaifinta yasamu naka da maganar dawowa  da kud in domin sungaji kuma tasami wani da takeso.  That s impossible Sabida nema cikin nema haramun ne kuma sun riga sa sun ba da ita.  Ehh daman abinda yasa Mahaifinka ya d an tsaya kenan kadawo aji idan kana da interest akanta sai ayi muku auren idan kuma baka dashi sai a barmu su kud in. Da sauri ya tare da cewa.  Momi nidai inason ta.  Ai shikenan sai kaje kasameshi kagayamai. ************** Zaune yake gaban Dad d in shi bayan yaga ma zayyana mai cewa shi yanason Ummi kuma yana son Auren ta.  it s okay Son zan tura uncles dinka suje suyi magana a tsaida date na d aurin auren.  Okay Dad thanks you. Affan yafad a tare da tashi ya fice, Kai tsaye part dinshi ya nufa ya zuba wanka cikin lallausan farin yadi da ya matuk ar amsar kyakywar fuskarshi. Sai kamshin turare yake zubawa, hannushi sak ale da agogon rolex, yayi kyau matuk ar kyau. Cikin Bak ar GLK dinshi yashiga kai tsaye gidan su Ummi ya nufa. ******************  Yanzu kai Nawfal kana ganin Auren yarinya da bata sonka ba TUDU AKAN KWARI bane, wanda zaiyi maka wahalal wajen tsallakewa, Nawfal k iyyar wata macen tabbatacciya ce fa. Anty Amina yayar Nawfal ke fad a masa bayan yasami Mahaifin su da maganar kan a tura gidan su Ummi.  Yaya Abban yace zasu je shida su Uncle, idan Mahaifin ta ya amince yabada Shikenan idan kuma ya hana zan hak ura Amma tabbas inason Ummi, Akan Ummi zan iyayin TUDU AKAN KWARI ko da kuwa bazan iya tsallakewa ba.    Idan da alkhairi a lamarin ka da yarinyar nan Allah ya tabbatar idan babu Allah ya watsar da lamarin. Shiru Nawfal yayi batare da yace komai ba, shi dai kawai fatanshi ace Abban Ummi yabawa su Abban shi Auren Ummi komai zaizo mai da sauk i daga baya. Wayarshi ya d auka ya kira number Asiya wacce ke zaune d aki suna shirin dawowar Yaya Umar gobe. Tana ganin wayar tafara ring takai hannu zara d auka amma sunan Nawfal da tagani yasata tsayawa. Wani irin tausayin sa ne yakamata, tabbas zata gayamasa ya dakata da lamarin Ummi a yanzun. D aga wa tayi tare da fad in  Assalamu alaikum. Daga can b angaren nashi amsawa yayi da  Barka da Safiya fatan ban tashe ki ba. Dariyar yak e tayi sanan tace  Katashi lafiya ya mutan gidan?.  Lafiya klau Asiya mutan gida na lafiya ya naku.  Lafiya klau suke wallahi.  Masha Allah. sanan yad ora da cewa.  Asiya nayi magana da Mahaifina d azu da safe kam suzo su nema mun auren Ummi. Daram haka kirjin Asiya ga buga, idan akace mata Nawfal yaji yanda kirjin ta yabuga bazatayi mamaki ba.  Naam Nawfal ke kace.  Nace nayi magana da Abbana yau da dadare zasu zo tambayamum auren Ummi, ko da matsala ne?.  Eyh A ah.  Mene Eyh A ah kuma?.  Nawfal da bakayi gaggawa ba.  Haba Asiya wace Gaggawa kuma duk jiran da nayi shine zakice nayi gaggawa.  Bahaka nake nufi ba Nawfal amma da kasani kasanar da ita. Shiru yayi dan a maganar Asiya ya fuskanci akwai matsala.  Asiya zan iya samun a gida. Shiru tayi na yan mintinan daga bisa ne tace.  Yes. Bayan sun kammala wayar ne ta danna lambar Ummi sai dai taji alamun tana wyaa ne, tashi tayi tare da Hijab din ta ta nufi gidan nasu.  Hajiya na zaune a tsakar gida tagaisheta tare da fad in.  Hajiya Ummi na ciki. Kallon tara saura Hajiya tayi mata sanan tace.  Kajimun yarinya da kinibibi idan tana nan aikin sani idan batanan ai kinsani.  A ah Hajiya nakira wyaarta ne naji bata tafiya.  To tana ciki. Hajiya tafad a tare da cigaba da Abinda take, tashi Asiya tayi tanufi d akin, kwance ta sameta waya a kunne tana magana k asa k asa.  D aka mata duka tayi tare da cewa bakiga nahsigo bane.   Zan kiraka anjima Asiya bazata barni nayi wayar nan ba. Ummin tafad a murya can k asa, Asiya bataji abinda kace ba sai Ummin da taji tace.  Bye love you.  Ke da ubanwa kike waya haka Ummi?.  To uwata da ubana nake waya.  Ke banason iskanci bawanan ne yakawo ne ba. Gyara zama Ummi tayi sanan tace.  To meya kawoki har zaki katsemun waya da masoyina.  Ummi Nawfal ne yakirani tare da fad an mu wai yayi magana da mahaifin sa kan zasu zo wajen Abb anjima. A furge ce Ummi ta tashi tare da fad in.  Me yake damun Nawfal haka ne?.  Ummi zauna kiji. Asiya tafad a tare da kamo Ummi ta zauna.  Relax wanan abun fa muma da namu laifin sabida bamu sanar dashi komai ba kan dawowar master.  Amma kuma Asiya yasan koda wasa bantaba cewa ina sonshi ba ko hirar soyayya bantaba dashi ba kuma yasan akwai baiko akaina.  Hakane Ummi yanzu yace zai zo ya sameni kawai ina ga kifito ayi duk maganar da za ayi ta k are.     Kinga fa yanzu wayar da muke da Mukhtar kan gobe yau da daddare zaizo gaida Abba. Sallamar da suka jiyo a tsakar gidan ce ta katse musu maganar da suke. Hajiya ce ke fad in.  Wanake gani haka kamar Affan. Har rige rige ake tsakanin zuciyar Ummi da Asiya wajen bugawa kafin suka maimaita sunan.   Affan.  Chab.   Ummi tafad a tare da ficewa wajen dai dai lokacin da zai zauna. Bai kai ga kallon ta ba Asiya taja ta cike tare da fad in.  Ke Ummi me yashiga kanki, tijara zakije kiyi masa ko me?.  Wallahi zagen sa zanje nayi nasa shi yafita daga gidan tunda bana ubansa bane?.  Shikenan kina numai kinji haushin watsar dake da yayi.  Bangane ba Asiya.  Nitsu ki fahimce ni, ai tunda kika yazo bayan yadawo to da alamun akwai abinda yakeso, to da wanan zakiyi amfani kici uban shege sanan ki watsar dashi.  Taya bangane ba?. Ummi ta tambayi Asiya.  Kinyi wanka ko bakiyi ba?.  Nayi. Ummi tabata amsa baki asake kamar sha sha sha.  Tashi ki d au wanka d an ubansu nima aramun doguwar riga. Tashi Ummi tayi ta d akko musu kayan cikin yan mintuna suka shirya, sun tsala uban kyau ko wacce rik e da jaka suka fito. Hajiya dake zaune ce takalli tare da cewa.  Ni Saliha ina kuma zaku haka?. Affan da tunda suka fito idan sa ya sauka kan Ummi,  a hankali k asa k asa yake kallonta. Asiya ce tayi saurin cewa.  Zamuje Gidan anty nafisa ne zancen anko.  Ankon wa kuma?. Hajiya ta tambaya dan ita bata harbu jirgin su ba. Dariya sukayi mai cike da aji ba tare da sunce komai ba.  Ummi wai bakiga Affan ba. Anzo wajen da Asiya ta fad awa Ummi, kallonshi tayi sanan tace.  Waye shi?. Kama baki Hajiya tayi sai yanzu ta d ano jirgin nasu. Shikam Affan jin maganar yayi kamar saukar aradu wai tambaya take waye shi.  Dr Affan fa. Hajiya ta k ara fad a, Asiya ce tai saurin cewa.  Oh wai Doctor Affan d inan.  Shi Asiya har kun mantashi kenan. Dariya sukayi sanan Asiya tace.  like wanda kace anmasa Engagement da Ummi ko?.  Like. Affan yafad a a ranshi yana k ara mamakin irin girma da kyan da yan matanan sukayi sanan gashi ko ganeshi ba suyi ba ita gwanar tashi ma ko magana bata iyawa Dariyar Ummi ce ta dawo dashi daga tunanin da yake sanan tace.  Dr Affan how far me yakawo ka kuma?. A hankali ya furta.   Tafiya da Matata. Page [41&42] Dariya suka tuntsire gaba d aya dai dai lokacin kuma wayar Ummi tayi Ringing, d agawa tayi tare da fad in.  Hello Babe. Da sauri Affan ya runtse idonsa domin ji yayi kamar ta buga mai abu akansa.  oh you re outside already. tak ara fad a sanan kuma tace  okay gamu nan. wanan duk shirin Asiya ne wanda kuma suna da tabbacin komai yayi yanda yakamata.  Hajiya sai mundawo. Ummi tafad a batare da sun jira cewar ta ba suka fice. Da gudu suka shige gidan su Asiya sabida kar tsautsayi yasa ya biyo su yaga inda suka shiga.  Hajiya zan huce.  Tun yanzu Affan?.  Eyh Hajiya daman nazo na gaida ki ne.  To shikenan Affan nagode Allah yayi albarka.  Amin ya Allah ga wanan tsaraba ce. yafad a yana mik amata tulin kayan da yazo da su. Ko a waje bai gansu ba hakan ya tabbatar mai da Saurayin nata yatafi dasu,ko da yakoma gida bai boyewa Hajiya Balki komai ba  da yafaru a gidan.  To yanzu Affan komene yafaru laifin kane, yarinyar nan bawani sonka take ba tunda akayi muku baiko kaita hulak anta ta, to yanzu gashi har ta tsayar da wani kuma kasan ta da taurin kai tun tana k arama ba abune mak sauk i zaisa ta karb i auren ka akaro na biyu ba.  Amma Mom nima da bana sonta sai yanzu kuma ai already anyi mana engagement.  Affan engagement fa ba aure bane, ana iya sokeshi ko wane lokaci. Tashi yayi ya huce office d in Abban shi.Sai da yasan yayi duk yanda zaiyi wajen tunzura daddyn shi akan maganar auren sanan yabar office d in. ************  Gaskiyya Asiya bansan brain d inki yafi nawa jaa ba sai yanzu Wallahi Allah. Dariya Asiya ta fashe da ita sanan tace.   To Ummi ai da nabarki naga hauka kike shirin yi mana to ina dalili. Kirani Nawfal ne ya shigo wayar Asiya, da sauri taja wayar tare da cewa  ke ya zamuyi da Nawfal.  Ni Wallahi Asiya bansaniba kawai mu fad a mai gaskiyya.  Gaskiyyar me Ummi wace k arya mukai mai?.  To ni bansaniba. Ummi tafad a tana cire kayan jikin ta, daukan wayar Asiya tayi tare da karawa a kunne.  Ranki ya dad e na iso fa.  To shiknan bari nazo. tafad a tare da kashe wayar sanan ta kalli Ummi.  Idan nakiraki sai ki fito.  To kifara dubawa kiga wancan d an rainin hankali yatafi dai ko.  Ni kinga har na ma manta. Asiya tafad a tan ficewa bayan tasa Hijab domin a ganin ta wanan kwalliyar bata kamata taje masa da ita ba. Tsaye yake jikin motar shi tasame idon shi a rufe,  k arasawa tayi tare da yin Sallama, amsa ma ta yayi tare da cewa.  Ban takura ki ba ko?. Murmushi tayi sanan tace  Wace takura kuma?.  Nasaki fitowa akan damuwa ta.  Uhm ba wani nan. Dogon numfashi yaja sanan yace.  Asiya dan Allah fad amun gaskiyyar komai karki boyemun.  Duk abunda zai fito daga bakina zallan gaskiyya ce sai dai ba lallai tayi maka yanda kakeso ba.  Ina jinki Asiya.  Nawfal tun a farko ka nuna kanason Ummi Amma bata amince ba, ganin yanda kake nuna soyayya yasa nake k ok arin nuna mata kyawawan halayenka ko Allah zaisa taso ka, to kasan so shiyake ganin guri bawani ke gane mai ba.  Hakane Asiya go straight to your point.  Nawfal har a yanzu Ummi bataji zata iya baka ragamar rayuwarta ba, bawai dan baka da kyawawan hali ba ko kuma baka kaiba, kawai har yanzu zuciyar ta bataji zatayi naam dakai ba. Shiru yayi for atleast 10mins sanan yace.  Shikenan

Chapter 8 of 10