Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
Mama domin tasan kawai masifa ce ta shiga da Anty gidan, sabida ta nuna musu suttura da kuma canjin da jikin ta yayi,  domin ko mak iyi yaga Anty yasan ta canja.     Yawwa to tunda kinga arzik i ai shikenan, kece mitsiyaciya dan haka kije ki rik e kud in gado marasa albarka.    Kud i marasa Albarka ai basu huce na bariki ba.   Cewar Asiya da tafito yanzu.   Ke Asiya bana ciki da iskanci kuma ciki yanzu.   Mama tafad a tana nunawa Asiya hanyar d aki.    Ah! kace rasa kunyar na ciki, idan kika mara kunya nan zaki k araso ki maimaita.   Halima dake wani cika da batse wa tafad a.  To idan ta maimaita dakuwa zatai ko me? ai ba k arya tayi ba, babu kud i marasa albarka kaman na bariki, kud in da huta kake ci. Ummi da tashigo yanzu tafad a. Dariya Anty da Halima suka kwashe da ita lokaci d aya.   A ah Rai ko gawa?. Halima tafad a a shak iyance.  Karya yarinya tamun rashin kunya dauje bakin ta zanyi daga ita har Asarariyar Uwarta. Ummi tafad a tana k arasa shigowa cikin gidan.  Asiya Ummi ku shige cikin d aki kafin ranku ya b aci. Mama tafad a musu cikim fad a, ba shiri suka shige cikin d akin, Halima kam cikin kururuwa take fad in.    Wallahi yaran nan sai kunsa da wacce kuke, wallahi sai kunyi danasin fad in wanan maganar.    Ficewa tai Anty tabi bayanta.  Can da sugada. Mama tafad a sanan ta k walawa Ummi da Asiya kira, fituwa sukayi sanan tace.     Ku fita sabgar yarinyar nan Halima, yanzu tayi k arfin da bawani abu bane dan ta illata ku.    Toh shikenan insha Allah Mama zamu kiyaye.   Ummi tafad a sabida tanaso Mama tabasu waje ne suyi magana da Asiya.    Mama nafita Asiya tace da Ummi.  Ina muka kwana?.     Asiya nasamu kud i 15000 nasan zasu iya tafiya zuwa sokoto, Amma bansan ta inda zanfara tafiya ba. Kallonta Asiya tayi sanan tace  Dafarko Ummi ina kika samu kudi?.  Banki na nafasa.  Ummi tabata amsa, bata k ara jan zancen ba sabida tasan Ummi tadad e tana asusu.  Ummi ni a gani na mai zai hana shi wancan mu bashi kud in yaje sokoto d in. Kallon ta Ummi tayi sanan tace.   Asiya kuma zaije?.   Zaije mana Ummi insha Allah.  Allah yasa.  Ummi tafad a sanan suka tashi suka fice, bash sha wahala ba su kasamu Rogget sana suka fad a musu buk atar su  To amma dai kunsan zaku bada ishashen kud in mota ko?.  Rogget d in yafad a yana bin su da kallo.  Kaman nawa?.   aaaiya tafad a.  Ko dubu sha bakwai haka. Ummi ce tafito da kud in jikinta dubu sha biyar zata mik a masa asiya ta masa ta k ara dubu uku yazama sha takwas.   Ga wanan dubu sha takwas ne, nasan zasu isa ko?.  Asiya tafad a tana mik a masa kud in, karb a yayi sanan yace.    Eyh zasu isa.  To yanzu zuwa yaushe zaka tafi?. Ummi ta tambayeshi.  Eyh ko zuwa jimawa ne.  To Allah yatsare sai munjika. Asiya tafad a tana kama hanun Ummi suka huce.   Dariya sosai Rogget yayi sanan yace.   Makakku, ni ko garin nasu ma ban rik e sunan shi ba balle har naje, kunyi zakka. *****   Bayan Sati guda. Abba har yagaji da jiran Ummi akan Master, kamar yadda itama tagaji da jiran Rogget da bashi ba labarin shi.    Yauce ranar k arshe da Abba yabata, idan bata kawo Master ba, zaiyi mata baiko da wanda Hajiya ke so, sanan kuma zata koma makaranta.   Tun safe Ummi da Asiya ke yawon bulayi a gari, sun rasa ina zasu dosa, Kamar daga sama suka hango Rogget yana tawowa inda suke. Suma fara tafiya sukayi zuwa inda yake har suka had u, da sauri Ummi tace.    Ya ake ciki?. Hannu Rogget yasa a alajihu ya ciro takarda ya mik awa Ummi.   Ta mece wannan?.  K arba mana. Page [31&32] yafad a yana mik ama ta, hannu tasa ta amsa tafara bud ewa.   Rubutun Master idon ta yasauka akai.    Meena nasan duk lokacin da wanan takarda ta isa gareki nayi nisa da ganin ki, nayi nisa da zuciyar ki. ina mai baki hak uri akan hakan Ummi.   Matsalolin da suke tun karar mu masu yawa ne Ummi kuma bazamu iya yak i dasu ba.  Ummi yan uwanki, ahalinki bazasu so ni ba, kina da kyakyawan ahali Ummi, dakika taso cikin farim ciki da soyayya.  Bazan tab a yafewa kaina ba idan nazama sanadiyar ruguza wanan farin ciki na ahalin. Muna da abubuwa guda biyu da muke yak i akansa. A halinki Gobe ta Yakamata Ummi muyi duba akan wanan, abubuwa ne masu mahimmanci ga kowanne mu. Ina so Ummi kije kiji da Ahalinki nima zanje na gyara gobe ta. Idan muna da rabon sake had uwa zamu had u Ummi insha Allah    Daga naki har kullum  Mukhtar Master.   Wani mugun ihu Ummi tasaku tare da zubewa k asa da sauri Asiya tayi kanta, tana fad in.     Ummi! Ummi!! Ummi!!!.    Yanzu Asiya Mukhtar ya kyauta mun? , duk fad i tashin da nake dan ganin soyayyar mu takai gaci, nayi fad a da yar uwata, nayi da aminiya ta, Mahaifiyata ta fita sabgata duk akanshi, amma bazai iya jurewa ba shi, sai yanzu da komai yazo k arshe.  Kuka ne yaci k arfin ta, takasa k arasa maganar.   Kiyi hak uri Ummi, kowanne d an Adam yana rayuwa ne akan doran k addarar sa kuma baisa ya canja wanan ba.  Amma yanzu Asiya wanan ita sakayya itace ribar TUDU AKAN KWARI. kuka ne mai k arfin gaske yaci k arfin ta, wani irin dum dum take ji acikin k irjin ta.  cikim kuka tak ara magana.  Ya Allah kaine kasa ka mun soyayyar Mukhtar Allah ka ciremun ita, ko da hakan zaija na rasa raina.    Ummi wai mene haka dan Allah kiyi hak uri. Asiya tafad a itama cikin nata kukan   A yanzu wanan yazama izina gareku bake kad ai ba Ummi. Mama dake tsaye bakim d akin nasu tafad a tare da shigowa ciki.     Bata hanasu kukan da suke ba sai ma ta d ora da cewa.  Duk abinda ku kaga iyaye sun hanaku tun a lokacin farko, to wanan abun ba alheri bane a gareku, iyaye basa tab a bawa yaro abinda zai cuceshi, sann kusani duk wani wanda zai so ku a duniya a bayan uwar da ta d auke ku a ciki ne.     Tabbas Mama yanzu nayi nadama nayi danasin bijirewa Mahaifiya ta tun a lokacin farko.   Ummi tafad a cikin matsanam cin kuka, Rungume ta Asiya tayi suka fara kuka mai tsuma zuciyar mai sauraru.  Dukkanin su zuciyoyin sa fal da rauni.  Ummi yanzu lokaci bai k ure miki ba, kije kins mi yafiyar Mahaifiyar ki sanan ki nuna mata a shirye kike domin yi mata biyayya.  Toh Mama. Ummi tafad a cikin kuka. Tashi tayi ta wanke fuskar ta, sanan ta nufi gidan su.   Kai tsaye d akin Hajiya ta nufa, inda ta same ta zaune kan gado tana danna waya.   A hankali tashiga d akin bakin ta d auke da sallama.   Ciki ciki Hajiya ta amsa sallamar tare da cigaba da abinda take. Zama tayi daga k asa cikin sanyi da rauni tafara magana.   Hajiya nasan ni mai laifi ce a wajenki Amma dan Alah dan girman Annabi kiyi hak uri kiyafemun, Wallahi Hajiya nayi nadamar zab ar soyayya akan iyaye na, sanan nayi miki alk warin daga rana irin ta yau zan kasance maiyi miki biyayya har k arshen numfashi na.   Sosa da Sosai Hajiya taji dad in maganganun Ummi, amma sabida nuna mata girman laifin ta yasa tace.    Shikenan Allah yasa da gaske kike.  Amin dagaske nake Hajiya dan Allah kice kinya femun ko na samu sauk i a zuciya ta, kuma namiki alk warin dakaina zan sanar da Abba cewar na shirya Auren Affan.   Ummi idan nace banji haushi akan ki ba nayi miki k arya, Amma kuma bantab a rik e ki a raina ba ko da na kwana d aya, kije Allah yayi miki albarka nagode. Tashi Ummi tayi tanifi cikim d aki ta kwanta. Da dare da kamta ta sanar da Abba komai na cewa t hakura da Master. Sosaj Abba yaji dad i.   Washe gari kafa da kafa taje gidan Goggo tabata hakuri da Gidan Anty Nafisa.  Haka Rayuwa ta juya Ummi zuwa farin ciki, duk da lokaci da dama tana tuna master kuma tanajin sonshi a cikin ranta, ta sawa ranta yau da gobe dole zata manta Master.   Ana haka su Ummi suka gama rubuta jarabawar su ta Waec, a lokacin ne kuma akayi musu baiko da Affan wanda ya shirya zuwa k asar America k aro karatu.    Haka rayuwa ta cigaba da juyawa yau fari gobe baki, har zuwa sanda su Ummi suk rubuta jamb sanan suka sami Addmission a jami ar Bayaro University kano.   A yanzu Ummi tacanja daga ita har Asiya sun k ara kyau, da gayu tsakanin su da iyayen su biyayya ce da soyayya sai kulawa.   A yanzu Hajiya ta komawa Ummi kamar da Yar gata yar lele haka Abba da Anty Nafisa.   Tana aji biyu a jami a Dr Affan yadawo hutu tare da Matar shi yar asalin Nigeria dake karatu a america, ko da Hajiya Balki tayi masa maganar Ummi sai cewa Yayi yana jira tagama karatu.  Kwance tashi ba waya a wajen Allah a yanzu har su Ummi sun kammala jami a sa sakamako mai.   A yanzu tabbas kaga Ummi da Asiya bazaka ce sune ba domin sun zama kyawawan yan mata masi ilimi da wayewa, sai dai fa Ummi ta rage dik wata rawar kai da hayani ta zama so cold abubuwa da yawa bata fiya magana akai ba.   Duk wasu burinka rayuwa Ummi tacire su. Ana haka akayi wa Asiya baiko inda akasa shekea d aya ita kuma Ummi ana jiran dawowar Affan.   Suna wanan zaman ne Asiya tasamu aiki a asibiti na wanda yakawo kud in ta, kasancewar ita fanin hak ori ta karanta ita kuma Ummi Entrepreneurship hakan yasa tasamu aiki a company.    Tun zuwan ta company MD din companin yake nuna mat soyayya, duk yadda Ummi taso tasa ka soyayar shi arai takasa, duk da tasan babu soyayyar Affan ko kad an aranta kuma tasan ba auren ta zaiyi ba.   Ta kud ri Aniyar fara son Nawfal tunda taga itama Hajiyar a yanzu tadawo daga rakiyar Affan d in, Sai dai har yanzu zuciyar ta takasa k arb ar Nawfal bata san kome ne dalili ba.    A yanzu bikim Asiya Saura watanni shida, Amma ita ba ko labari, idan Goggo tayiwa Hajiya maganar Affan sai tace ita ma batasna abinyi ba.   Baiko ne dai gashi Anyi wajen shekara Biyar amma har yanzu shiru babu wata maganar.   Hakan yasa A yanzu Asiya ke bata k warin gwiwa kan ta koyi son Nawfal tunda dai yana son ta kuma mutumin arzik i ne.   Bata tab a tunanin sake ganin Master ko jin shi ba A rayuwar ta.   WANAN SHINE LABARIN TUDU AKAN KWARI NA UMMI. Page [33&34]   B ud e idanu wanta tayi ta gama ganin rayuwar ta gaba d aya a majigi, duk irin Butulcin nan da Master yayi mata shine yake k ara mata magana.    Tashi tayi tashiga bayi, wanka tayi sanan ta d aura alwala tafito.   Dadduma ta shimfid a bayan tasaka bakar doguwar riga da dogon hijabi, ta tada Sallah.  Addu a tayi sosai bayan ta idar da Sallah akan Allah yakare ta daga k ara fad awa komar Master a karo na biyu, domin tabbas ta ga zuciyar ta na shirin jama ta wani aikin.   Saida Ummi tayi kwana uku ba tafi ko nan da can ba hatta wajen aiki ta daina zuwa sabida gudun sake had uwa da Master.    B angaren Master kam Rashin Lafiyar Matarshi tasa shi a gaba hakan yasa yabawa Ummi hutu.    Zaune yake cikin d akim asibitin da aka kwantar da Zainab.    tana daga kwance kan gadon, shi kuma yana daga gefen gadon, cikin muryar mara lafiya take magana.    Yallab ai yakama ta ace ka k ara dagewa akan lamarin Ummi domin gudum sake rasa ta a karo na biyu.   Kallon Zainab yayi cike da su da kulawa sanan yace.     Ranki ya dad e idan har nasake rasa Ummi a karo na biyu ya tabbata ba rabo na bace, ke daice rabona kuma ina mai godewa Allah a hakan ma.  Murmushi tayi a ranta kuma tana godewa Allah domin tasan duk sanda Master kewa Ummi bazai sa ya hulak anta ta ba, bayan ya sameta.    Yallab ai a yanzu kace duk abinda take yi bata san ma kayi aure ba, to ya kake gani kuma idan tasani. Girgiza kai yayi sanan yace.   Ranki ya dad e Wallahi bansaniba, rigimar Ummi karuwa tayi a yanzu data girma ma.     A gani na karka sanar da ita hakan yanzu, kabari ka fara samun kanta sanan kuma kaga lafiya ta, kasan ciwom da nake dashi ba lallai nayi tsohon rai ba, ba lallai nafita daga asibitin nan ba&    kidaina fad in haka Zainab da rayuwa da mutuwa duk na  Allah ne, insha Allahu yanda kika shigo asibitin nan da k afarki haka zaki fita da ita. Murmushi tayi sanan tace.  To Allah yasa, Amma ranka yadad e ka d auki shawarar tawa, kafara shawo kanta a yanzu sai kayi mata bayani daga baya, insha Allah zata fahimta.  Zainab a ko dayaushe zaka sance mai yiwa Allah godiya da yabani ke, sanan zan k ara gode miki da shigowa rayuwa ta da kikayi, kika tallafe ta dai dai lokacin da narasa madafa, kika tashk rayuwa ta lokacin da nake ganin ta mutu, Zainab a duniya banj da kalaman da zanyi amfani dasu wajen yi miki godiya, A matsayin a na mijinki indai har aljannar ki tana k ark ashin kafata Zainab na d aga miki ki shige.    *** Nawfal ne Zaune cikin office d in Asiya, Kallonshi tayi sanan tace.    Nawfal ina fatan dai lafiya ko?. Girgiza kai kawai yayi batare da yace uffan ba.   To yanzu kayi shiru bansan me zan iya ce maka ba?.    Asiya kinsan matsalal, kinsan damuwar tawa, da ina fama da iya neman soyayyar ta, yanzu gashi tsohon saurayin ta yadawo.    Ga kuma wanda akayi mata baiko dashi, zaidawo cikin wanan satin, kuma bamusan da me zai dawo ba. Asiya ta fad a, da mamaki yad ago ya kalle ta sanan yace.    Ba an warware baikon nasu ba.  Eyh Abban ta yaje zancen awarware baikon har ma an mayar masu da kud in su, sai dai basu amsa ba.    Wanan Ai shirme ne. Nawafal yafad a yana k ok arin tashi.   Nawfal tsaya kaji dan Allah kad inga sawa kanka sauk i akan lamarin nan, idan Ummi matarka ce to dole sai ka aure ta, idan kuma ba rabon ka bace duk tashin hankalin ka bazaka aure ta ba.    Hakane Asiya nagode, insha Allah zan kula. Daga haka yasa kai yafice, ita kuma ta tashi ta nufi office d in sahibinta Dr Mansur.   Tana tafe tana ta lissafin k alubale na rayuwa da Ummi tasamu. A dai dai bakin k ofar office d in ta tsaya, ganin office d in a kulle yayi matuk ar bata mamaki.    Daga inda take ta lek a can parking space,ganin motar shi wajen ya k ara bata mamaki.    Komawa office d in ta tayi ta d auko spare key na office d in nashi ta dawo. A hankali tasa Key ta murza, sanan tashiga bakawo falon hakan yasa tafara kok arin nufar d aya room d in.  Kasancewar office d in mai Room and falo ne a hankali take tafiya gaba d aya jikin ta ya mutu, zuciyar ta tayi nauyi, batasan mene zaifaru ba amma jikin ta ya bata abu mara dad i.    Motsin da ta jiyo a cikin d akin yasata k arasa wa wajen, tare da sa hannu ta murd a.   Da sauri ta gimtse idon ta, tare da sakin k ofar.  Dr mansur kam a zabure ya mik i yayi kanta yana fad in.    Asiya! Asiya!! Asiya!!!. Bata tsaya ba tafice, domin tabbas abinda tagani ya matuk ar bata mamaki.   Gani ta fice yana sashi dawowa cikin office d in nashi, tare da kallon yaron dake kwance.    Ahmad get out.  Tashi yaron da aka kira da Ahmad yayi tare da fara sa kayan shi, yana abu kamar mace har ya shirya sanan yazo inda Dr mansur yake sanan yace.    Yanzu sai yaushe?.  Zanbiyo gidan naku da daddare. Dr mansur yafad a, domin shi tsoran shi ba ganin da Asiya tayi masa ba, yanda zata je ta yad ashi.    Tashi yayi bayan yaron yafita ya nufi office d in ta, dai dai lokacin da tagama had a kayanta.    Asiya dan Allah kitsaya kiji ni.  Mansur me zanji daga gareka, so kake kacemun karya ne abinda nagani ba haka bane.    Asiya nasani abinda kika gani gaskiyya ne, Asiya ina neman maza amma wallahi a yau nayi nadama kuma natuba, dan Allah Asiya kiji k aina kiji tausayina Asiya, natuba Wallahi.   Shiru Asiya tayi tana kallon sa, sanan tace.  Allah ubangiji yasa tuban gaske kayi, kuma insha Allahu zan rufa ma asiri tare da tayaka da addu a , amma sai dai nafasa auren ka mansur domin abinda na gani bazai taba gogewa daga rainaba cikin sauk i.   Duk da yaji ba dad i na fasa auren shi da tayi amma cewar zata rufamai asiri yasa shi jindadi, domin daman ba auren yakeso ba, zaiyi ne kawai sabida bakin mutane.    Nagode Asiya, bazan hanaki fasa aure na ba domin tabbas duk wacce taga namiji a irin wnn halin baza ta fara auren shi ba.  Sanan zan ajiye aiki na. Kallon tayayi sanan yace.     Dan Allah a ah karkiyi haka.  Bazan iya zama ina kallon a haka ba domin bazan iya mantawa da abinda nagani ba, amma tabbas nayi nisa dakai zan mata da abinda nagani.   Shiru yayi sanan yace.  To dan Allah zanema miki ai wajen abokin Dr Lamir, Wallahi shi mutumin kirki ne.    Shikenan zanyi tunani. daga haka ta d auki jakar ta tafice ***   Wai ni Saliha ina aka kwana maganar wanan yaron da ya zubar mun da jika.   Kallon Goggo Hajiya tayi sanan tace.   Wallahi Hajiya nima abun ya dameni sabida ko jiya sai dai yak ara yiwa mahaifin yaron magana amma sunki amsar kudin, haka ita ma mahaifiyar yaron sabida butulci wai haushi na takeji.  D an Adam kenan, tamanta tsanar da tasa kikayi wa yar ki, akan tak i d anta, amma yanzu yaro ya ajiye yarinya shekara hud u shine zataji haushinki.  Bari dai Goggo ni dai yanzu muntsya akan yanda shi Alhajin ya yanke, babu baiko tsakanin Ummi da Affan, duk sanda suka shirya su amshi kud in su.  Tabbas hakan yayi Saliha, kuma yanzu wanan lokaci ne da zamu bawa Ummi damar gabatar da wanda takeso.   Hakane Goggo Amma kamar kince ta gabatar miki da Nawfal ko?. Gyad a kai Goggo tayi sanan tace  Eyh ta gabatar da shi Amma banga wata soyayya a idon ta ba, kuma ni baiyimun ba, wani d an tuturna dashi.  Dariya Hajiya tayi sanan tace.  To Goggo idan kuma shine mijin jikokar taki fa?.   Haka Allah yaso kuma bayanda zanyi. Goggo tafad a da haka suka cigaba da hira,domin tabbas a yanzu ansamu fahimta mai k arfi tsakanin Goggo da Hajiya, daman tunda akan lamarin Ummin d in ne. ***   K arar Wayar Ummi ne ya katse ta daga kallon da takeyi, wanda a zahiri ne take kallon tv d in amma ba kallon take ba.   Hannu tasa tad au wayar ganin sunan Lil sister wanda tayiwa Asiya saving dashi.   Hello Asee.  daga can b angaren Amsa Asiya tayi tare da fad in.    Kina ina?.  Lafiya kike kuka Asiya?.  Ba lafiya ba da matsala tsakanina da Dr Mansur.   Subhanallahi, kibiyo ina gidan Anty Nafisa. To tace sanan ta katse wayar Page[35836] Anty Nafisa dake zaune ce tace.   Wai Ummi kinzo tun safe, gadamuwa fal ranki amma kinkasa magana. Kallon Anty Nafisa tayi, ido cikin ido sanan tace.    Anty bani da bakin magana domin bansan ne zance ba.  Maganar Affan ce? ina ba Abba yagama magana ba? Girgiza kayi tayi sanan tace.   A ah Anty matsala Affan k arama ce akan wanan.  Innullahi Ummi wace irin matsal ce wanan?. Shiru Ummi tayi na tsahon sakanni sanan tace.   Anty Master yadawo.     Yadawo daga ina?. Anty Nafisa ta tambaya cikin rashin ganewa.    Yadawo daga inda yaje, sai dai ba a wanan salon yadawo ba.  A wane salo yadawo?    Anty A salon da inda akace miki Master ne bazaki yarda ba Anty. Nan Ummi tashiga bata labarin duk wasu gifts da akatura mata har zuwa binciken da sukayi suka gano wanene shi da kuma kamfanin mAm.   mAm kikace Ummi?. D aga kai Ummi tayi sanan tace.  Wallahi Anty.  Gaskiyya Master yazo da wani salo,Amma Ummi idan har ya shiryu mene zai zama matasala ?, daman ai bashi ne ba aso ba halin shine ba aso.   Kallon Anty Nafisa Ummi tayi sanan tace  Anty Abunda yayi mun fa?.  Wane abu yayi miki Ummi?. Anty Nafisa ta tambaye ta domin son sani.   Anty kar kice mun kin manta mana. Sallamar Asiya ce ta dakatar da maganar da Ummi keyi.  Da sauri Ummi ta tare da cewa.   Me nake gani kamar hawaye a idonki.   Zama Asiya tayi sanan tace.   Ummi mai zanyi? idan ba kuka ba. Anty Nafisa ce ta tare su da cewa.  Asiya lafiyan ki kuwa?. Girgiza kan ta tayi sanan tace.   Anty Mansur ba mutumin arzik i bane kwata kwata. Da mamaki Anty Nafisa tace.   Subhanallahi shi Mansur din kuma?. Ummi kam cewa tayi  ai daman nasa kuma nafadamiki tun lokacin farko. Kuka Asiya tafara sanan tafara basu labarin duk wani abu da yafaru   Amma Allah la anci Mansur dan uban sa, shege. Ummi tafad a cikin Masifa sanan ta d ora da cewa.    Daman tun farko na tsani wanan shegen Mansur d in da rayuwarsa, Allah ya taimake mu ya kuma rage mana wahala.  Ke fa Ummi yaushe ne zakiyi hankali dan Allah?.  Anty Nafisa ta tambaya, Kallon ta Ummi tayi sanan tace.   To Anty wanan ai rage mana akayi da ace sai bayan Auren aka sani fa, azo ai ta fama da shi wajen saki, kuma mutane sufara magana, yanzu kam idan sukaje ance anfsa maganar da zasuyi kadan ce.  Alllah ya kyauta, yanzu Asiya mai kika yanke?. Anty Nafisa ta tambaya, sai da ta d anyi Jim sanan tace.   Na yanke shawarar fasa Aurensa sanan na ajiye masa aikin sa, Amma yace wai zai samo mun wajen abokin shi, duk da nace banaso.  Me zakiyi da wani Aiki wajen Abokin shi ke kam?. Ummi tafad a tare da tashi ta dawo kusa da ita, hannu ta d ora kam kafad ar ta sanan tace.    Ni ina ganin wanan abun ayiwa Allah godiya ne, da ya rage miki wahala, domin tabbas dai sai bayan auren ku kika gane wanan labarin kinga ai babban Abune mai wahala, kuma hukunci da kika yanke shine dai dai, Asiya muna zaune Allah zai kawo miki mijin Aure nagari, gaba d ayan mu.  Tabbas Asiya maganar da Ummi tafad a miki gaskiyya ne.  Anty Nafisa ta k ara fad a.  Nagode Anty Nagode Ummi. Duka Ummi tad akawa Asiya sanan tace.  Sannu da Godiya.  Nikam Ummi ya maganar Nawfal da Master?. Asiya ta tambaya.  Uhm Nawfal ba mu samu munyi magana ba shikuma Master ban sake fita ba balle muhad u.    Yawwa wai nikam Asiya mai Master yayiwa Ummi ne?. Anty Nafisa ta tambaya.  Bangane ba Anty?. Asiya ta mayar mata da tambyar.  Laifin da zai sa har takasa Amsar soyayar shi a wanan karon.   Haha Lallai Anty, duk ba mu san uzirin shi ba, Amma tabbas Master bai kyauta ba, duk da zamu iya cewa hakan yafi Alheri domin da awanan lokacin ya tsaya to tabbas Ummi ko ta k arfi ne sai ta bishi duk inda zai kaita, ya rabata da yan uwan ta da kowa na ta.    Hakane Asiya Amma ina ganin a yanzu ai yadawo a matsayin da kowa ce mace zata so samun shi a matsayin Miji.    Hakane Anty. Asiya tafad a daga haka hirar ta tsaya, sai da sukayi sallar

Chapter 7 of 10