Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
Nigeria, zaije chan kaduna makarantan Nigeria defense academy ( NDA ). Da sassafe ya shirya ya shigo dakin ummi sai murmushi yake dan gani yake dazaran yaje Nigeria zaiga khaleesat, haka yakeji a ranshi zaiga khaleesat, ummi tace hydar ka shirya? yace eh ummi, tace hydar maisa kazabi Nigeria?? Akwai makarantan sojoji na nijar maisa bazakaje wurinba kaga kana kusadamu, yace ummi zan nemo matana a Nigeria ne. tace to abu daya zan fadama shine kariki gaskiya, amana, da takwa, karka zamo mai ha’inci, kakuma dunga taimakom duk musulmin dayake bukatan taimakonka, inhar karike wanan dabi’an hydar tsawon 2 years dinan dazakayi wlh saika zama babban sojaan da akwai sojoji dasukai shekaru goma basu sami mukamin ba. Dana nahoreka dajin tsoron Allah, ka kiyaye sallolinka biyar, ka nisanci sabon Allah ka kula da kanka kuma. ya rungume ummi, ummi ta fashe da kuka hydar ya share mata hawaye yace ummi nai miki alkawari zanyi amfani da duka abunda kikace sanan ya saketa. Kallon zulaihat yayi wanda ta rakube a gefe tana matsar kwalla murmushi yayi yabude mata hannayenshi, da gudu tazo ta rungumeshi itama tafashe da kuka da kyar ya lallasheta, kallonshi tayi tace yaya hydar plz inzaka dawo ka dawo min da kawata kaji? yay murmushi yace i promise, daganan tadau ghana masgo dinshi suka rakoshi har zaure. Fadawan sarki ne suka ga sun shigo gidan suna huci kusan su 50, hydar ya daure fuska yace lpy?? Sukace sarki yace ataho daku yanzunan. Ummi ta dafe kirji tace maimu kayi kuma?? Wani bafade yace zakuyi bayanin uwar maiyasa kuka guntulema yarima faisol yat…. Bai karasa magananba hydar ya wankamai mari, yace uwata kake zagi? sauran fadawan suka kama ummi, sukace koka wuce mutafi komu nakasa mahaifiyarka yanzu, hydar zai kara magana ummi tace mutafi hydar. haka aka kamasu har fada…. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣3⃣ ********BAYAN 5 YEARS.*** Ayaune HYDAR ya kammala karatunshi na sojaa, inda yasami babban mukami as CAPTAIN HYDAR MUHAMMAD. Har hawaye saida yayi lokacin daya shiga office dinshi xama yayi kan kujera yace khaleesat all dis are 4 u, but plz khaleesat where are you?? Ina kika shiga abin kaunata?? Zuciyata kadan tarage ta fashe.. waynshi ne yay kara, yadauko wayan ganin zulaihat ne yasa ya dauka. Murya arude tace yaya hydar ummi batada lpy, hawan jinin ta yatashi, plz kaxo mukaita asibiti arude yamike yana too, to ganinan. zaran keys din motanshi yayi yafita. ….Kasancewar lokacin damai martaba ya aika akirasu hydar faisal yafadamai khaleesat ce ta guntulemai yatsa shine mai martaba yacema hydar su tttara subar garinshi yakoresu, haka suka hada kudi suka shiga mota sukazo kaduna. Da kyar hydar yasamu yakama musu daki daya anan kaduna sanan shikuma ya shirya yatafi makatantanshi anan jaji kaduna…. Yana kaiwa katafaren gidansu direct dakin ummi yawuce, yaga Zulaihat sai kuka take ta daura ummi akan cinyanta, hydar da sauri yakarasa wurin ya rike ummi yana ummi na” ummi na” ahankali ta iya bude ido amma babu amsa, kallon zulaihat yayi wanda ga dukkan alamu wanka tafito tana daure a towel sai kuka take, Hydar yace ya isa zulaihat jekisa kaya kizo mukaita asibiti, tashi tayi tashiga dakinta tazira doguwan riga tadau hijab dinta tafito, tazo gaban hydar tace yaya hydar zip, saida yajamata zip din rigan sanan yadau ummi yasa amota suka tafi FMP clinic kaduna. Suna zuwa suka tarar da baban likitan dake duba ummi baya gari, wani likita ne yadubata saida yafito hydar ya bishi office, likitan yace hawan jini yama mum dinka yawa, dan yanzu gab take da kamuwa da mutuwar barin jiki, hydar ya rude. Dr yace calm down akwai wani asibiti dazan turaka, sunada good doctors kuma turawane, hydar arude yace ina?? Dr yace sunan asibitin AMAZING GRACE but a abuja yake zan muku transfer wajen saboda aba mum dinka taimakon gaggawa. hydar yace to bari naje nadau permission a office. Yana zuwa office aka bashi 7 days da kyar shima, dan ko kadan basuson hydar yay nisa,haryau cikin sojoji ba’a samu jarimi kaman hydar ba. Gida yabiya ya kwasoma zulaihat kaya da ummi yasa a box ya kulle gidan sanan yakoma asibiti. Suka wuce abuja da ummi. KHALEESAT haryau na nan yanda take ko motsi batayi, yayinda yan uwanta sun cire rai datana rayema, Abban chuchu duniyarshi yakeci da tsinke dan gani yake har abada babu mai sanin wanan sirrin. Sojaa da matarshi farida na dakin zaune jefe,jefi suna fira, farida tace honey wlh nakosa baiwar Allah dinan ta tashi, dan nasa ko ina iyayenta suke suna chna haryau hankalinsu atashe yake. Sojaa ya sauke ajiyan zuciya yace likitocin suce takusa tashi dan yanzu tana internal movement, farida tace wow dat is great! Allah yasa ta tashi gabaki daya. Wayan sojaa ne yay kara ganin abunda ke screen din yasa ya dauka yana murmushi. Yace likita bokan turai, kai alikitocin ma daban ne, likitan gawa kenan, achan bangaren hydar yace zaka farako, kazama gawa kaga inban fede kaba, hydar yace by d way kasan gobene dad zaibude ma nida khalis asibiti ko? dafatan zakazo?? Soja yace Allah sanya alheri in sha Allah i will be drr, be expecting me HYDAR!!! KHALEESAT wani irin motsi kafaffunta suka fara, ahankali take kyafta idonta, farida ne ta mike tsaye tace honey zokaga wani abu,katse wayan kazo, wlh zata tashi,.. Sojaa yace hydar later patient din tafarfado, ” hydar yace in sha Allah inhar komi yalafa zanzo nadubata ma”….jin Hydar again khaleesat tafara kokarin moving hanuwanta….. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣4⃣ Hanunta farida tarike tace yarinya kitashi dan Allah,karki kara komawa, khaleesat saikuma tadena motsi, farida tajuyo ta kalli sojaa idonta cike da hawaye tace honey takoma jeka kira Dr, da sauri soja yafita tareda Dr suka dawo dakin, Dr ya dudduba sanan ya juyo ya kallesu yace are u people sure yarinyar nan tai motsi?? Sojaa yace eh, yanzunan bamusan maiyasa ta komawaba, likita yace ok. yacigaba da dubata Murya sukaji daga waje ana cewa β€œzulaihat kiyi shiru, ki koma daki ki zauna da ummi kinji, ni yanzu pharmacy zani na karbo maganin da Dr yay prescribing” Wani irin zabura khaleesat tayi saura kiris tama fadi daga gadon amma Dr ya riketa, bakinta tabude da kyar tana β€œyaya hydar” yaya hydar” faisal zai kasheni, sojaa yazo gabanta yace yarinya babu wanda zai kasheki, ihu tasaki tafara kuka kaine ko, ka kaini dan Allah wurin yaya hydar yanzunan naji muryanshi. Dr yace wat is she saying?? Kowa yay shiru. khaleesat kokarin mikewa zaune take Dr ya kwantar da ita, yace after 5 years laying on dis bed, did u think u can walk easy my patient?? Just get some rest nw, anjima zan turo wanda zata dinga miki massage therapy. yashafa kanta yafita daga dakin. Farida ta matso kusa da ita tace mezakici?? Khaleesat da sauri ta rike hanunta tace zulaihat kene?? Farida ta girgiza kai, tace ni sunana farida mijinane ya tsinceki, khaleesat tace ruwa zansha. da sauri sojaa yaba farida ruwa taba khaleesat tasha sosai, sanan tace nagode, saikuma tafashe da kuka tace dan Allah ku mayar dani gidanmu a nijar. Sai alokacin sojaa yace dazaran an sallameki daga asibitin nan zan mayar dake, ki kwantar da hankalinki kinji ko?? Tace to nagode, farida ta taimaka mata tai brush sanan tabata tea mai zafi tasha sosai. HYDAR saida yaga ummi tasamu bacci misalin karfe 8 nadare, dama zulaihat kanta nakan cinyanshi itama ta kishingida tana gyangyadi, ahankali yacire kanta daga kan cinyarshi ya gyra mata kwanciya sanan yadau key din motanshi dan yaje yanemo hotel din dazai kwana….. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣5⃣ Tuki yake batare dayama san inda yake shigaba, sai zagaye abuja yake yana yaba kyan garin wani hanya ya shigo, titi ne mai kyau, amma babu yawan motoci, daya daya mota ke wucewa hanyar shiruuuu, hydar yana cikin tukinshi yaji kaman alamun ihu bai gasgata abunda yakejiba parka motanshi yayi agefen hanya tareda kashe wutan motan kasa kunenshi yayi sai saiyaji murya kaman tadan magidanci haka yana ataimaken, zasu kasheni, jin wanan kalmar yasa hydar ya dau bindigarshi ahankali yabude motarshi yafito ya labe abayan motanshi. Alamun gudun mutane yaji ta dayan bangaren titin wanda gefenshi dajine. hydar da sauri ya tsallaka ya shiga cikin dajin yana tafiya sadaf sadaf, hango wani dan tsoho yaci fararen malun malum dayayi yarike wani briefcase gam gam ajikinshi yana gudu yana ataimakeni, saikuma wasu mutane su 3 suna binshi fuskkokimsu na cikin safan fuska hannayensu dauke da manyan itace. Hydar yakara labewa bayan bishiyan gani yayi tsohon yafadi timmm akasa, amma still yakara kankame wanan briefcase din, mutane ukun suka karaso suka tsaya cak suna dariya sukace ALH LAMIDO kai kazaci kanada wayau ne, ai kai kuskuren fitowa batare da body guard dinkaba kuma wlh yau saika mutu mukuma kaima oga wanan akwatin. Hannu yasa zai fizge akwatin daga kirjin Alh lamido amma jikake tass hydar ya harbe hanunshi, fitowa yayi daga maboyarshi, dayake akwai hasken farin wata suna ganin kayan sojoji ajikinshi suka ruga da gudun bala’i. Hydar yay maza yadago Alh lamido yana sannu sir, rigan sojan dake jikinshi ya cire da sauri yana sharema Alh lamido jinin dake zuba daga goshinshi, alh lamido yabude idonshi kadan abunda yaganine yasa yace ma hydar ur back, amma kafin hydar ya juyo mutumin ya kifama hydar icce akai, nan kan hydar yafara jini hydar ya zube a wurinn shima. Mutumin ya koma zai kwace akawtin daga hanun Alh, hydar wani karfi yaji yazomai yatashi ya kifama mutumin mari, ya hanbareshi tareda lankwasamai hannunshi tabaya, hular fuskar mutumin yacire, hydar yasa dayan hanunshi ya ciro wayanshi daga aljihu ya kunna yana haska fuskar mutumin wazai gani…… [2:33AM, 3/5/2017] β€ͺ+234 803 052 4904‬: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣6⃣ Wanan mutumin wanda suka kusa jefa khaleesat cikin rijiya, Alh lamido gwale ido yayi yace β€œmai gadi”kaine, yace kira police wlh he is a wanted criminal, hydar yana kokarin dialing number police while hanunshi daya yana rike da mai gadi. Mai gadi iya karfinshi ya daga kafanshi ya tokari hydar agabanshi wanda hakan yasa hydar yay kara yafadi kasa, wayarma tafadi, mai gadi yadau iccen ya bugama Alh aciki, Alh yay ihu yadawo kaman sumamme, yana kokarin daukan akwatin hydar ya wawuso kafanshi daga kwance, mai gadi take yatsan hydar yayi sannan yamike batare dayakarayin takan akwatinba shima yagudu, dan ya lura hydar mayene ga shegen karfi da naci. Hydar saida yay kusan 10min kafin wurin yadena mai zafi,yadawo dai dai, mikewa yayi tsaye yakoma kan Alh wanda yake nufashi da kyar, daga Alh yayi yaciremai malun malun din, goya Alh yayi abayanshi dan yaga bazai iya tafiyaba, yakara tsugunnawa yadau wayanshi da riganshi taareda bindigarshi. Yadau briefcase din yarike ahanunshi daya, yafita daga dajin, motarshi yabude yasaka Alh ciki sanan ya shigo shima. Alh da kyar ya iya magana yace ciro wayana daga aljihu kaduba contact dina ko hydar ko khalis duk wanda kafara gani kace suzo ina Iwofe road. Hydar yaciro wayan sunan khalis yafara gani shiya kira. Khalis yace dad haryanzu baku gama meeting din bane? hakanan hydar yaji kirjinshi ya buga jin muryan bawan Allah. Da kyar hydar yasamo natsuwa yace Alh yasamu matsala kazo iwofe road yanzu ka daukeshi arude khalis yace maiya sami dad?? Hydar yace kadaizo. Alh yace ruwa, da sauri hydar ya dauko ruwa yafara bashi yasha sosai…. Hydar dake tare da khalis yace maiya sami dad khalis?? Khalis yace wani yace muzo iwofe road dad na wurin ba lpy, arude suka shiga mota hydar kejan motan har iwofe road din. Khalis suna kaiwa suka parka, yaciro waya yakira hydar ya dauka, khalis yace motarka ce wata black jeep haka by ur left hand side?? Hydar yace nine zaku iya zuwa. Khalis da hydar suka bude mota suka fito, ganin fuskan khalis yasa kirjin hydar yafara dukan 50 50, wanene wanan mai kama da khaleesat? Wanene wanan mai kama da matana? πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣7⃣ Hydar basar da tunanin yayi, tareda cewa Allah kenan, maiyin hallita yanda yaso kwankwasa glass din car din sukayi hydar yabude motan tareda fito da Alh wanda goshinshi ke fitar da jini har yanzu, hydar da khalis suka rude tare da cewa subhanallahi maiyasameshi?? Hydar yace wasu mutane suka biyishi, suna kokarin kwace briefcase dinan, ya mikama khalis briefcase din yakara goya Alh duk suka bude baki suna mamakin karfin hydar, hydar yadanyi murmushi yace muje saina samukushi a mota, haka suka jera saida hydar yasashi a mota sanan ya juyo sukai musa baha da khalis da kuma hydar sanan ya juya dan yakoma motarshi. hydar Abj yace dan tsaya, chak ya tsaya, hydar Abj yace tnx 4 saving my dad, hydar yace my pleasure. yacigaba da tafiya, hydar Abj ya biyoshi yace can we be friends?? Hydar yace sure why not, Hydar Abj yaciro card dinshi yabama hydar, shikuma hydar ya ciro nashi card din yabama hydar Abj. Hydar Abj ya kalli card din yace wow! So u are a captain?? Kasan wani abu kuwa bakai kama da dan nigeria ba?? But hw come kuma kazama sojaa a Nigeria?? Hydar yay murmushi yace is a long story friend kabari saimun zauna, all i can tell u is my biological dad is a nigerian. suka kara sallama hydar yace bari naje na sami khalis a car. Daga kafan da hydar zaiyi yatafi wurin motanshi yaji jiri na dibanshi, wurin da mai gadi ya tokareshi yay mishi wani irin zafi tareda rikewa, hydar Abj shi dama yariga ya juya baisan halin da hydar ke ciki ba, Alh lamido dayariga yadan farfado saboda taimakon gaggawan da khalis yabashi shine yataba khalis yace khalis yaron daya taimakaen zai fadi. Khalis yafito daga mota yacema hydar dake kokarin bude mota ya shiga yace hydar mutuminchan zai fada kaman yana ganin jiri, sa sauri sukai kan hydar amma kafin su kai hydar ya fadi a wurin sumamme hanuwannshi na rike da abun. Alh lamido dabaida ishesn karfi shima yafito daga mota yazo yasamesu, ganin inda hydar yarike yasa Alh buga salati INNALILLAHI Wa innailahi raji’un!! Hydar da khalis suka juyo suka kalli Alh, Alh yace kutashi musashi a mota mutafi dashi gidanmu khalis ka dubashi, Allah yasa basuyima wanan yaron illaba. Hydar yace dad wani illa kuma?? Alh yace garin taimakona daya daga cikin mugayen mutanen ya tokareshi a agabanshi sosai wlh, arude hydar da khalis suka kaishi motansu, khalis yaja motan da sauri, shikuma hydar Abj yafito yaja motan hydar suka tafiiiiiiii…. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣8⃣ suna kaiwa gida Alh yace ashiga da hydar dakinshi, hj benazir tafito arude tana maiya faru?? Alh yace zakiji komi nan da gobe hydar da khalis suka kwantar dashi kan gadon Alh sanan kowa yafita daga dakin akabar daga khalis sai hydar nijar. Khalis ANDROLOGIST ne (likitan maza ). Ya dade akan hydar yana dubashi, daga baya yamashi allurai yasamai drip yafito daga dakin. kana ganinshi kaga alamun tashin hankali akan idonshi. Alh lamido yafara mikewa yace meke damun yaron khalis?? Khalis ya share gumin dake keto mishi tareda yin shiru, Alh yace kamin bayani mana meke damun shi?? khalis yay gyran murya yace dad adan binciken danayi ya nunamin yaron yasami matsala da TESTICLES dinshi, sanadiyar bugun wajen da akayi… Saikuma yay shiru, Alh lamido yace sooo?? Khalis yace am afraid to tell u dis dad, da kyar in yaron nan ya iya samun HAIHUWA!! Alh yace INNALILLAHI shikenan najama yaron mutane, hydar shima hankalinshi yatashi. Khalis yace dad banda garanteen bazai iya haihuwaba danni ba Allah bane but all wot i can said is TESTICLES dinshi yasamu matsala bazai iya secreting enough sperm dazai bada baby ba. Idon Alh lamido yacika tafff da hawaye, wani irin kaunar hydar yaji Allah yasamai, in sha Allah kuma zai nemanma hydar lpy. Khalis yace nan da gobe zai tashi in sha Allah. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 3⃣9⃣ Washegari da safe duka family antaru da dakin Alh lamido cikinsu harda teema, Alh yay gyaran murya ya dubi matarshi hj benazir yace wifey kina ganin mufadamai abunda ke damunshi idan yatashi?? Hj benazir ta gyara zama, tareda gyara zama glass din idonta tace husby yes yaron have d right to know what is wrong with him, Alh yace tom, ya kalli hydar da khalis yace kufa mekukace? Sukace mum is absolutely right dad, gwara yasani…. Wayan hydar sukaji yay kara babu wanda ya dauka, anata kira, ana uku ne Alh ya mikama hydar wayan yace gashi sa’a loudspeaker ka amsaa. Wata zazzakar murya, mai shegen dadi sukaji tace yaya hydar, kazo asibitin Dr ya nemanka, kuma ummi taji sauki sosai itama tanata tambayarka, i think za’ayi discharging namune, hello yaya hydar kanajina?? Alh ya dagama hydar kai alamun ya amsata. Hydar yace ba yayanki ke maganaba, yayanki yadan samu matsala, zulaihat tace wayyo Allah maiya sami yaya hydar?? Hydar yace bawani matsala bane yanzudai fadamin wani asibiti kuke zanzo, ni sai muyi maganan, cikin sheshekan kuka tace AMAZING GRACE ne, hydar yace to kidena kuka ganinan zuwa, tace toni mezan cema ummi na?? Hydar yay murmushi hakanan yaji yarinyar na burgeshi yace kicemata hydar na zuwa tunda bata da lpy karki fada mata komi tace to sanan ta katse wayan. Hydar yace dad zanje hospital din dama anan sojaa abokina aka kwantar da yarinyar daya tsinta a nijar kuma naimai alkawari zanzo na dubasu…… Bai karasa maganan bane saboda yaga hydar na motsi, hydar kallonsu yake daya bayan daya Alh lamido ne yafara matsowa kusa dashi yace dana katashi?? Ka ganeni kuwa?? Hydar yadanyi murmushi yace yes sir, i recognize u sir, but maiya kawoni nan?? Alh yace ga bayi kaje kai wanka tukun idan kafito mayi maganan hydar baiyi musu ba ya shiga bayi hakanan yaji yanajin kunyar mutumin. Alh ya kora teema, idris da isya waje, ya rage dakin daga hj benazir,sai hydar da khalis dakuma dad. Hydar yafito ya zauna ya gaishe dakowa a falon, hj benazir tace nakawoma abinci?? Murmushi yayi yace no ma’am, bana breakfast . πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 4⃣0⃣ Alh yace hydar inaso ka gafartamin, dan nasan kome yafaru dakai nine sanadi, hydar yay shiru kanshi akasa, Alh ya cigaba yace jiya bayan ka suma muka kawonan gidanmu, nacema khalis dana yadubaka, sakamakon daya bamu shiyafi komi tadamin da hankali, hydar har ilayau kanshi akasa. Alh yace sakamakon da muka samu shine bazaka iya haihuwaba!! dummm dumm hydar yaji gabanshi yafadi amma bai dago kanshi ba, Alh yace Hydar kayakuri dan Allah nasan nina jama. Hydar yay shiru batare daya dago kanshi ba, Alh ya matso kusa da hydar ya dago kanshi yace hydar say something, shirunka na azabtar dani, am feeling guilty, hydar idonshi ya cika da kwalla sosai murya narawa yace sir am scared, sir wlh tsoro nakeji, Alh cike da rashin fahimta yace tsoron me hydar?? Hawayen daya cika idon hydar ya zubo yace tsoro nakeji idan matana tasan inada matsalan nan tace bazata zauna daniba, sir if dat happen i will just die, cos i can’t leave without her, she is my everything, hawaye ya gangaro idonshi. Alh ya dafa kafadanshi yace be a man, be strong we all promise u kafin matarka tasan da matsalanan ka warke, Hydar Abj ya dawo kusa da hydar shima ya dafashi, khalis shima ya dawo kusa dashi ya rikemai hannu har hawayen idonshi suka dena zuba. Hydar Abj yace dama kanada mata ne?? Hydar nijar yace eh inada mata, khalis yace to ina take?? Hydar nijar yace tabata, bangantaba, hydar Abj yace hw com?? Ya akayi kanada mata kuma tabata baka gantaba?? Hydar yace is a long story all i can tell u now is matana na kama da wanan ya nuna khalis, kowa yajuyo yana kallon khalis. Hydar yace duk lokacin dana kalleshi saina tuna da matana… [2:39AM, 3/5/2017] β€ͺ+234 803 052 4904‬: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 4⃣1⃣ Khalis yay murmushi yace inda ace lil sis bata rasuba da sainace itace hala matar taka, amma nasandai hallitan Allah ne, dama hausawa sunce kowa aduniyanan bibbiyu ne, akwai irinka mai kama dakai awata kasa. Hydar nijar yace hakane, yamike tsaye yace bari naje asibiti ummi na ankwantar da ita, hj benazir tace hydar kabari duk mubika mu gaida mamanka, hydar Abj yace nima abokina na asibiti ya tsinci wata yarinya batada lpy duk saimu tafi tare mudubasu, haka ilahirin family suka dunguma harda su teema aka tafi asibitin. A haraban asibiti suka hadu da sojaa, soja ya gaisa da kowa, ya rungume hydar Abj yace mutumina kai fresh fa. yace kuzo muje farida na tare da yarinyar abinci take bata, ni nafito siyo mata maganine. hydar Abj yace bari mufara duba maman abokina sai muje soja yace ok muje tare mana. sukaje dakin Maman hydar. Zulaihat na ganin hydar ta taso da gudu ta rungumeshi tana kuka, ya bubbugi bayan ta yace am ok yanzu ai, ummi sai hira take da hj benazir kaman sun dade da sanin juna, yayinda teema anga kawa kakkyawa buzuwa aka makale ma zulaihat, hydar Abj sai satan kallon zulaihat yake. Duk ana zaune ana fira Dr ya shigo yabasu sallama, Alh shiya biya bill hydar zaiyi magana Alh yace shiii daga yanzu kai danane, ummi ma sai godiya take, hj benazir da teema suka taya zulaihat hada duka abubuwan dasuka zo dashi asibitin har mota suka rakosu ummi da zulaihat suka shiga mota suka zauna. hydar yace ummi bari nadan bisu mugaida wat mara lpy, ummi tace to. Sojaa na gaba ilahirin family din tareda hydar nijar na binshi a baya har room 29. ganin number dakin yasa gaban hydar fadi dan yasan rana 29 ga watan agusta yataba haduwa da KHALEESAT. Gaban hydar ya tsananta bugawa lokacin da Sojaa ya bude kofan dakin suka shiga tareda sallama mezasu gani…….. .. …. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 4⃣2⃣ Gani sukayi gadon wayam, ba kowa adakin, soja yace ku shigo ciki mana ku zauna, sun shiga wankane halan, duk suka shigo, hydar nijar wani irin sanyi yaji yana shiga jikinshi dabaisan dalilinsaba,ba’a kunna Ac ba, ko fanka ba’a kunnaba amma amma ya rasa maisa wanan sanyi ke ratsa jikinshi. Soja yatashi yaje gaban bayi yace farida da baki a dakinfa inkun gama wankan ki fito kidau kayanta kafin kifito da ita, tace to honey. Hydar nijar ganin shiru shiru gashi yabar su ummi a mota yasa ya mike yace sir i have to go, kaduna is a long journey kuma nabar ummi a mota, Alh yaja kunnenshi yace am not sir, am ur dad, Hydar yay murmushi yace to dad, yaje wajen hj benazir yace mum natafi tace to dana Allah kiyaye hanya. yay musabaha dasu hydar sanan yayma teema bye bye, itama da murmushinta tamayarmai haryakai bakin kofa zai fita yaji anbude kofa…… Wani irin sanyi wanda yafi nada ya kara shiga jikinshi wanda yasa saida ya busar da iska, da sauri ya daga kanshi ya kalli kofan da’aka bude saiyaga wata kakkyawan matace tafito gaisheta yayi ta amsa tace baza ka tsaya ku gaisa damai jikinba?? Yace wlh sauri nake nabar ummi a mota tace gaskiya yi sauri babu kyau shanya uwa yasakai yafice, tareda mamakin maisa yakejin sanyi acikin dakin. Farida ta gaida su Alh da kyau sanan tadau dogowan rigan khaleesat na atampa pink takoma bayin, saida tasama khaleesat kayan, khaleesat tace anty farida nagode, farida ta shafi gefen fuskarta tace nace kidenamin godiya, ta gungurata akan keken guragun datake kai dan haryanzu ta~ta~ta take tafiya daya biyu saita fadi dan kasusuwanta basu riga sun fara aiki dukaba. Duk suna zaune kowadai yakosa yaga mara lafiyan, dad da mum sunata hira sama sama, yayinda hydar da soja suma suna hiransu, khalis ne ke danne danne waya danshi haka Allah ya yishi baida magana shiru shiru ne, jin karan anbude kofa yasa kowanensu ya dago kanshi dan yaga mara lafiyan daza’a fito da ita daga bayi, Khaleesat sukaga farida na gungurowa a keken guragu, kowanensu yakara goge idonshi dan gani sukeyi kaman a mafarki, farida tace Alh ga maijikin nan tafito, saidai fa ba ganinku takeba dan makauniyace. Alh bakinshi yana rawa yace k..haa… lllee…sat.. Khaleesat kece ko kuma?????? yama kasa karasa maganan saboda kuka dayazomai. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 4⃣3⃣ KHALEESAT jin muryan dad yasa tace dad is dat you?? Ina kake? dad wai plz mafarki nakene? ba muryan dad baffana najiba?? Kokarin tashi tayi daga kan keken da kyar ta mike tsaye, lalube take da hannu tana dad ina kake?? Hawaye na zuba daga idonta, taku daya biyu a na ukun dazatayi tayi kasa zata fadi da sauri dad ya tarota tafada jikinshi, ya shafi gefen fuskanta yace jidda ganinan, nine, baffan kine, wani ihu tayi mai hade da kuka, dakuma murna ta kankame dad tace dad ya akayi kasan ina nijar?? (Dan ita haryanzu batasan tana abujaba ), kafin dad ya amsa tambayan tace dad ina mum?? Hj benazir da hawaye yagama wanke mata fuska maiya dawo da khaleesat makauniya?? tace jidda ganinan tare da rike hanun khaleesat da sauri khaleesat ta rungumeta tana mum i missed u alot, hj benazir kuka takeyi bana wasaba, khaleesat ta dago kanta itama cikin hawaye tace mum ina yaya ishak?? Da sauri ishak yazo inda take ya rike kafadanta yace khaleesat ganinan, shima kuka yake khaleesat ta rungumeshi tana kukan murna, ta dako kanta tace ina yaya idris?? Idris yazo yarike hanunta yace khaleesat gani rungumeshi tayi tana kuka sanan ta dago kanta tace ina yaya hydar?? Hydar da hawaye ya wanke fuskanshi ya rungumeta tsam tsam a jikinshi yace ganinan little pumpkin, itama kuka take takara kankameshi jin yafara shafamata baya yasa ta tuna tanada aure ta kwace jikinta da sauri tana hawaye tace yaya hydar ina teema na?? Teema cikin wani irin bala’in kuka tazo da gudu ta rungume khaleesat tabaya tana kuka sosai sama dana kowa a dakin, khaleesat ta juyo ta kankameta. sojaa da farida sudai sun shiga duhu suna gefe. Khaleesat ta dago kanta tace teema where’s my chuchu?? Teema cikin sheshekan kuka tace tana gida, Khaleesat tace ina YAYA KHALIS?? Teema tace gayican, khaleesat tace kaini wurin yayana, teema ta rike hanunta, khaleesat tafiya take kaman mai koyon tatata, kafanta rawa yakema sosai, dan karfin datake dashi yakusa karewa, Teema ta kaita gaban khalis wanda kukanshi yafi na kowa adakin majina taff a hancinshi, idonan yay jajur, teema tace gashinan agabanki. Khaleesat daga hannayenta biyu tayi tana shafan fuskanshi, muryan na rawa tace yaya khalis dena kuka, ta sharemai hawaye am back, wani irin runguma khalis yay mata ya fashe da kuka banawasa ba kaman mace, itama kukan khaleesat tafashe dashi, babu wanda yay yunkurin lallashinsu saboda ansan mesukema kukan. Da kyar khalis ya iya controlling hawayen idonshi yashare na idon khaleesat, kokarin faduwa take saboda tagaji da tsayuwa ya rike da sauri ajikinshi, teema da sauri ta gunguro kekenta khalis ya daurata akai. Tsugunnawa yayi agabanta ya Rike gefen fuskanta yace lil sis maiya sameki??? Ciwon me kikayi haka?? Where have u been all dis while?? Ya akayi kika dawo MAKAUNIYA??? πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 4⃣4⃣ Khaleesat kuka yaci karfinta tama kasaba khalis amsa, kowa ya nemi waje ya zauna danson jin maizatace. Khalis ya dago kanta ya share mata hawaye yace lil sis kukan ya isa haka tell me maiya sameki??maiya dawo dake makauniya?? Khaleesat tasa hannu ta share hawayen idonta tace bayan school bus ya saukeni, naja box dina na shigo cikin gida, abu nafarko daya faraban mamaki shine babu mai gadi, securities ma duk bangansuba nacigaba da tafiya na bude kofan falo na shiga. Kuka yaci karfinta tadaura hanunta biyu akan na yaya khalis dake kan fuskanta, tace yaya dey murdered our parents, kashesu yayi agabana, kowa na falon saida yadago kanshi ya kalli khaleesat a firgice. tace yaya dad took his last bullet in front of me, dad yay numfashi shi na karshe agabana batare da mutumin ya barni naje nataba dad ba. Murya chan kasa tace dey shoot dad and mum agabana, i was helpless, powerless, ban iya tabuka komiba na ganin na taimaki iyayenaba har suka mutu agabana. khalis kokarin rike kukanshi yake amma yakasa, kara fashewa yayi da kuka hydar yataso ya rikemai kafada yana girgizamai kai,shima idonshi cike da hawaye. Khaleesat tace mutumin yazo gabana yasa aka rikeni gam, yadauko shaltos, saikuma tayi shiru tareda sauke ajiyan zuciya. Tace yaya bantaba going through azaban danai going rananba tunda mum ta haifan, dauko shaltos yayi, ta rike hanun khalis gam, tace yaya yasa aka budemai idanuna da kyau ya fesamin a idona yaya, i screamed, i hala, i shout, but no one was dr to help me. Teema fashewa tayi da kuka tafada jikin mum dinta benazir wanda itama kuka take, farida ko kuka take ba’a magana sojaa idonshi yay jajir. Khalis kukanshine worse, khaleesat tacigaba daga lokacin ban kara sanin inda kaina yakeba, sai alokacin dasuka kaini nijar zasu jefani cikin rijaya, tasaki wani kayatachen murmushi tareda cewa, Allah send me a guardian angel, my saviour,d only man dat help me without asking 4 anything in return, my one and only yaya HYDAR HUNTER!!! Ta sauke ajiyan zuciya, wani siririn hawaye ya sauko daga idonta tace, shiya taimaken, ya kwaceni daga hanunsu, yakaini gidansu shida iyayenshi suka cigaba da kula dani, mamanshi

Chapter 4 of 10