Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
kiyi addu’a tatashi da wuri to. Yau kwanan khaleesat 7 chipchip Hydar yafita parauta, zulaihat na makaranta, ummi ce kadai adakin kusa da khaleesat tana zaune. Gani tayi khaleesat tafara girgiza kafanta tana kokarin daga hannu, ummi ta matso kusa da ita tana murna tace yarinya mike karki bari ciwon yakara komar dake rayuwar bacci, mikewa tayi zaune tare da sandara ihu, dan Allah kuya kuri karku sani a rijiya, ummi ta tsaya tana kallonta kaman mai nazarin wani abu. Khaleesat kokarin bude idonta take tana bude idon wanda yanzu yakoma fari gaba daya taga bata ganin komi, saidai wani azaba datakeji kaman anzuba mata barkono da sauri ta kulle idon tana kuka, gashi intana kukan saitaji idon namata zugi. Ummi ce takomo hanunta tana yarinya zokici abinci, khaleesat daddagewa tayi ta fusge hannunta tana kuka tace mai gadi kun kashemin iyaye shine yanzu zaka kawoni gurin matarka ko, tonima ku kasheni, ihu kawai take tana wasu maganganu da ummi batama gane abunda take fadaba, jisukayi anfashe da dariya sosai. Khaleesat takara firgita ta kankame jikinta tana addu’a Allah kareta daga shairin mutanenan, zulaihat ce ta shigo tace kawata dan Allah cigaba da magana, wlh muryanki dadi kaman ta kananan yara tacigaba da dariya. Khaleesat takara haukace musu tana nasan kasheni zakuyi kawai ku kasheni nahuta, kun riga kun kashemin ido bana gani kawai ku kasheni, ummi ta matso kusada ita tace yarinya kidena kuka idanunki zasuyi miki ciwo sosai, ayanda kike yanzu bai kamata ko digin hawaye yafito daga idonki ba, Khaleesat ta fizge hanunta tana kokarin tashi sai tattaba bango take duk sunbita da ido tsayawa tayi chak saikuma tafara kuka. Tace Abban chuchu baxan taba yafemaba, kiri kiri ka maidani makauniya wlh duk wanda kedasa hannu harda ku duka banyafe mukuba, in sha Allah kuruwan iyayena bazai barku lpy ba, tacigaba da kuka sosai ta dafa idonta saboda yanda yake mata zugi. Tundaga kofar gida Hydar yaji alamun ana ihu a gidansu daure dokinshi yayi ya dauko wasu naman ragon daya kawo da yawa yakaraso cikin gidan dasu ajiyesu yayi yakarasa dakin yaga khaleesat tsaye sai kuka take, Ummi tace yauwa hydar kadawo, kaga bakuwarku ta farka sai ihu take mana wai mukasheta tahuta, taki yarda taci abinci kuma nace tadena kuka saboda zaikarama idonta matsala. Khaleesat kara bude baki tayi tace wayyo mamana gashinan yadawo zai kasheni, Hydar wani tsawa yadaka mata yace keee yimana shiru, tunda take bata tabajin anmata irin tsawanan a duniya ba kama bakinta tayi ko tari bata karaba. Yace banason ihu, na tsani yawan kuka, so kikiyaye, muba cutarki zamuyiba, mukuma ba kasheki zamuyiba, mu muntaimakekine, yanzu zulaihat tarakaki ki wanke baki kizo kici abinci anjima da daddare mayi magana kisan maiya kawoki gidanmu, Yanda taji hydar na magana yasa tatuna da yayanta hydar na Abuja, daga muryanshi da yanda yake magana yasa duk wani fargaba dake zuciyarta yafice tanemesu tarasa, daga kafanta tayi tafara tafiya so take tazo inda hydar yake, Zulaihat ta rike hanunta tace kawata mekike nema?ina zaki? Kome kike nema kidinga fadamin saboda nabaki abu. budan bakinta tace niki kaini wurin wanda yay magana yanzunan yayana ne, murysnshi irin na yayana, haka yayana ke magana, plz kaini wurinshi nasan shikadai ne bazai bari su maigadi sukasheniba. [2:20AM, 3/5/2017] β€ͺ+234 803 052 4904‬: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣1⃣ Hydar da ummi kafeta sukai da ido, zulaihat tace tozo na kaiki gashinan zaune kusa da ummin mu, tako rike hanun khaleesat harkusa da hydar takai khaleesat ta zaunar da ita. Hydar bai cemata komiba itama tai shiru, daga hanunta biyu tayi tafara shafa fuskanshi, jitayi yanada saje, takara kai hanunta kan lips dinshi taji karami ne kuma sunada taushi, takai hanunta kan hancinshi taji yanada tsini gashi dogo, takara matsar da hnunta kan idanunshi daya lumshesu tun lokacin data fara tafabashi, hanunta takara matsar wa sama taji ta chusa hanun cikin gashin kanshi mai yawa mai laushi da santsi irin nayan India, zata kara matsar da hanun yakamo hanun ya rike, saboda wani yarr yaji yanaji ajikinshi gakuma ummi a wurin yace mai haka kikeyi?? Tabe baki tayi tace sorry, kana kama da yayana, banbancinku kai kafishi gashin kai, tace ya sunanka?? Zulaihat tace sunanshi yaya hydar, Khaleesat tace wlh sunan yayana shima hydar tace dan Allah zaka zama yayana?? Kawai kallonta yake tunda yake daidai daso daya baitabajin mace ta burgeshiba, sai wanan bakuwar, yanda take magana dakomi nata kawai yadaiji daban. Magananta yakaraji tace zaka zama yayana?? Kaga bazaka bari Abban chuchu yamin komiba. budan bakin hydar yace A’a. Ni yayan zulaihat ce kadai, ita kadaice kanwata ke bakuwar muce, dazaran kin gama warkewa zaki fadamana garin dakike mu komar dake. Jikinta yay sanyi, taji wani abu ya tsaya mata amako goro, kaman tafashe da kuka saikuma ta daure ta rike kukan, mikewa tayi tsaye murya na rawa irin wanda ke shirin kukan nan tace zulaihat dan Allah kaini na wanke ba..ba… kin kuka yadan kufce mata amma tai maza ta hadiye. Zulaihat,ummi, dashi kanshi hydar din sai sukaji basuji dadin abunda hydar yayiba. Kama hanunta tayi suka fita brush dinta takawoma khaleesat tasa toothpaste tabata tazuba mata ruwa abuta tasa brush din abaki tayi, tace ma zulaihat zanyi fitsari, zulaihata takaita har bayi, ita tacirema khaleesat pant tai fitsarin ta maida mata da komi sanan tariko hanunta suka fito. Khaleesat tace nagode zulaihat, zulaihat tai murmushi tace kidinga cemin kawarki, tace nagode kawata. Zulaihat taja hanunta oya mutafi daki, khaleesat tace zan zauna anan tsakar gida in yayanki yafita kifadamin saina koma dakin, sai kuma tafara kuka ta durkushi a wurin tana wani kuka, tace kawata agabana suka kashe mamana, suka kashemin babana, bansan inane nanba, amma sainaga yayanki naji inajinshi kaman yayana, amma yanuna bayason kanwar dani bakomi, nima Allah yaban lpy in sha Allah zanga yayyina kusan su biyar nakedashi nidama nafison hydar acikin yayyina dan yafiji dani little pumpkin ma yake cemin. zulaihat hawayee yazubo daga idonta tace kawata kyale yaya hydar ni ina sonki ummi ma nasonki, zamu kula dake harki warke ta rungume khaleesat. Hydar yana tsaye abakin kofa dama yafito yabata hakuri ne saboda ummi tamishi fada yanda yay mata magana, yanda take kuka gashi ashema har iyayenta suka kashe yaji wani tausayinta karasawa wurin yayi yace BAKUWARMU!!!… πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣2⃣ NIJAR Bata amsashiba amma tadago kanta, yace kiyakuri nayarda nadawo yayanki daga yanzu, tadanyi murmushi mai kara mata kyau wanda yabayyana dimple dinta batare datacemai kalaba, hydar ya tsaya kallonta kaman yana nazarin abu. Zulaihat tace kawata muje daki, daki suka koma ummi takawo mata abinci ita kebata khaleesat abaki, kuka ya kufece ma khaleesat , ummi tace maiya faru? tace akaro nabiyu yarinya nace kidena kuka zai tsananta ciwon idonki, bakinta narawa tace ummi wai yanzu ko abincin gabana bani gani, bana ganinku bana iya yima kaina komi, ummi mai amfanina yanzu? inda sun kasheni danafi hutawa dawanan azaban da nakasun dasukasamin. Hydar da hawaye ya ciko idonshi tashi yayi yabar dakin, ya shiga dakinshi arayuwanshu ya tsani yaga mace na kuka bayaso, barinma bakuwar nan da intana kuka sai zuciyarshi tadinga mishi zafi. Ummi tace yarinya karki damu komi lokaci ne, yanzu bayan yan kwana biyu zakiga kin soma sabawa kin fara yima kanki wasu abubuwan, karki damu kinji ke yatace zan cigaba da kula dake harki warke insha Allah khaleesat tace nagode ummi. Saida taci abincin shinkaface da miya yaji nama abunku da Hunter agida lol. Bayan tagamaci ummi da kanta takaita bayi taimata wanka khaleesat sai dukar dakai take wani irin kunyan matan taji tanaji, bayan sun dawo daki ummi tashafa mata wasu magunguna ajiki, zulaihat takawo mata wani atampha ta talakawa tai musu godiya sosai ranan. sanan aka bata tabarma tai salla. Da daddare bayan anci abinci ummi ta gyara zama tace yarinya ya sunanki?? khaleesat tace sunana β€œKHALEESAT HYDAR” ummi tace munason muje dalilin, sanadin kokuma ince abunda yakawoki wanan garin nijar akauyen doso?? Kirjinta ne yabuga kaman zai fashe tace ummi nijar?? Nida nake Nigeria maiya kawoni nijar? na shiga uku ni khaleesat shikenan bazan kara ganin yan uwana harna fadanmusu maiya faru dani ba. Yanda sukaga tarude yasa ummi tace ya isa haka, hydar kai fadamin a ina kasamo Khaleesat?? Take a wurin hydar ya fadan musu komi amma saiya boyema khaleesat zancen an harbeshi saboda ita, khaleesat kuka take da yanzu ta mutu badan hydar ya cecetaba, atake itama tafada musu komi da komi daya faru. ummi da zulaihat kuka wiwi suke Hydar kam idanunshi sunyi jajir kaman yay mata kuka haka yakeji. Ummi ta share hawayenta tace khaleesat bazanso ki koma gida da makantan nan ba saboda mutumin zai iya kasheki batareda kinsaniba, nai alkawari zan nemo miki maganin idonki ya warke, mutara kudi dazai kaimu Nigeria mukaiki har gidan kanin babanki Alh lamido. ki kwantar da hankalinki nai alkawari zan kula dake harsai randa numfashina yadauke. Khaleesat ta rungume ummi tana kuka zulaihat itama ta rungume ummi hydar tashi yayi yabar dakin. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣3⃣ ABUJA Khalis da hydar sunje har gidan bincike sukai sosai, abu na farko dasuka samu shine akwai labulen dabai kone dukaba, khalis ya shishina labulen yaji warin kalanzir yamikama hydar shima ya shinshina sunsan cewa Hj jabo bata taba amfani da kalanzir hasalima da gas take girki dat was d first thing dat made dem suspicious, Hydar ya tsinci bullet kwaya 3 akasa wanda hakan yasa gabansu yafadi suka fara tunani koyan fashi ne suka shigo gidan. Waya hydar yaciro yakira babanshi Alh lamido sanan yakira police. dasuka iso hydar suka nuna musu abunda suka gani, investigation police suka shigayi sosai inda haryakai ana neman mai gadi yayi bayani ko da wanda suka shigo gidan aranan gobara, amma annemi mai gadi anrasa. Har gidan mai gadi akaje amma akaga a kulle, yan anguwa suce tun randa mai gidanshi yarasu mai gadi yabar gari, takenan mai gadi ya shiga cikin suspect aka buga hotonshi as a wanted crimanal ana nemanshi. Securities ma duka anje gidajensu amma basunan suma aka buga hotonayensu ana nemansu. Pathologist da dama police sun kira an bi diddigin tokan da abubuwan dasuka kone amma ba’aga alamun konewan gawan khaleesat ba, hankalin kowa yatashi barinma khalis to ina kanwarshi wai shin ina KHALEESAT??? Ina tashiga?? Ina suka kaita?? Inhar bata mutuba ina suka kaita, khaleesat kina ina my lil sis plz kifito, da kyar Alh lamido ya lallabashi yay shiru. Har lokacin komawansu hydar da khalis makaranta yayi ba’aga su maigadiba, hakanan suka tattara suka koma dan dama semester daya yarage musu sugama karatun duka sudawo cikakkun likitoci. Duk garin Nigeria duk inda ka shiga zakaga poster na hoton khaleesat har kudi naira miliyan 5 Alh lamido yasa duk wanda yaganta amma shiru. Abban chuchu tun ranan dayaji hydar nacewa zaiyi bincike fitan dayayi zuwa yayi yabiyasu mai gadi, sanan yasasu barin garin gabaki daya. yanzu hankalinshi kwance yasan cewa yariga yataushe hanyar da za’a iya gane yanada hannu a kisan Alh hydar. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣4⃣ NIJAR Rayuwa a nijar ba laifi dukda khaleesat bata sababa amma ganin yanda ummi da zulaihat ke sonta ke kula da ita yasa taji itama tana sonsu sosai, hydar nedai haryau bata sake dashiba dukda shi yana kokarin ganin yajata ajiki amma bata bari ko fira take da zulaihat dazaran ya shigo bazaka karajin bakintaba. Ummi ta dage wajen nemama khaleesat lpy idanunta, alhamdulillah yanzu idon khaleesat ya washe duk hakin sun bace saida bata gani kwata kwata dan idan kaganta zaka zaci tana ganin mutane ma amma ko kadan bata gani. Yau asabar zulaihat tadawo daga hadda, ta zauna suna fira da khaleesat ummi ta shigo dakin tace zulaihat tace naam ummi, ga maganin nan ki kaima humaida tasha jiya ta haihu, khaleesat tace ummi nadan bita tunda nazo ban taba fitabafa, ummi saida taidan jim tace shikenan amma zulaihat ki kula da ita da kyaufa. Kuma karku jima, banda biye biye, kuna mika sakon ku dawo sukace to khaleesat harda murna. Zulaihat ta dakko hijab tasa mata sanan tarike hannunta suka tafi. Sunkaima humaida maganin, humaida tace zaliha wanan wacece?? Zulaihat tace kanwatace kuma bakuwarmu ne, humaida tace amma wlh tanada kyau gatadai baka amma duk tafi yan matan garinan kyau ga diri, zulaihat tace ummi tace muyi sauri sai anjima. Suna fitowa suna tafiyansu ahankali sukaji ana busa sarewa alamun kodai sarkin kauyen kokuma dan sarkin kauyen mai suna FAISOL zai wuce. Khaleesat tace kawata wanan sarewan fa?? Zulaihat tace hala ko sarkin garinan ko danshi ne zasu wauce. kinga mu tsaya dan inhar suna hanya ka shiga hanya sai anmaka duka 80, khaleesat sarkin tsoron bulala takara kankame zulaihat tace wlh mu tsaya har suwuce. FAISOL nakan rakumin shi wanda anmishi ado irin nadan sarauta yazo wucewa kawai idanunshi suka sauka kan khaleesat wanda take sanye da doguwan riga ta atampha kanta kitson yan nijar ne wanda ummi tamata jiya hijab din datasa yafito da tulin kitson gaban goshinta wanda hakan yasa tai kyau sai jujuya fararan idanunta manya take tana waige waige kaman tana gani, kallonta yayi yaji tabala’in bashi sha’awa ta, bai taba ganinta a kauyenan ba. Safkowa yayi daga kan rakumin ya tunkaro inda suke fadawanshi na biye dashi. Zulaihat takara rike hanun khaleesat gam dan kowa yasan FAISOL dason mata yarone 25 years yake amma yanzu matanshi 4, auri saki, dazaran yaga kakkyawa saiya saki daya daga cikin matanshi ya auro. gakuma khaleesat daya mutu akanta, tun kafin ya iso zulaihat tafarama khaleesat magana a kunne tace wanan dan iskan dan sarki na zuwa karki kulashi. Yana karasowa yace kee kanwar hydar wacece wanan dakika rike?? Zulaihat jikinta yafara rawa tace bakuwarmuce, yay murmushi yace to kutafi gida amma kicema mamanki aurenta gobe dan haka kushirya, khaleesat jin maganan aure yasa tace nacema ina sonkane?? FAISOL yace basai kinceba, kuma bawai amincewarki nake nemana, nidan sarki ne kome nakeso akemin, a tsiwace khaleesat tace niko bazan sokaba, jitayi ya fincikota tafada kirjinshi, iya karfinta ta daddage takaima duka wanda bama tasan a inda ya saukaba ashe a fuskane take nan ranshi yabaci, Yace nuna sarkin bulala yace amata 50 masu kyau, da gudu zulaihat tazo ta tsugunna gabanshi tace dan Allah kayakuri wlh kanwata makauniyace bata gani, kayafe mata batasan waye kaiba bakuwace, hankade zulaihat yayi yace amusu tare, haka aka musu bulala 50 khaleesat harda suma. Ya kalli zulaihat yace kushirya gobe za’azo adaura auren nafada miki, kuka babu wanda ya isa yahana, garina kuka dan haka kome na garin nawane, yay tsaki yahau rakuminshi sukai gaba. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣5⃣ Zulaihat kuka take sosai gashi garin inhar dan sarki yadaki wani baka isa kataimakeshiba duk yan garin sunki taimakonta, ga khaleesat asume itama bayanta zafi kaman ta mutu ta kifa kanta kan cikin khaleesat tana kuka sosai. ana haka Allah ya jefo hydar kan dokinshi yadawo daga daji yana goye da kwari da kwafanshi, sakkowa yayi yataho wurinsu arude yace zulaihat dago kanta tayi yace maiya faru?? Kafin tafada mishi ya koma kan dokinshi yaciro goran ruwa yazo yayyafama khaleesat ta farfado tana kuka ta rirrike hydar tana cewa zulaihat karki bari yadakeni. Hydar yace maiya faru zulaihat khaleesat najin muryan hydar takara sautin kukan tana yaya hydar wani mugune wai zai aureni gobe plz karka bari ya auren dan Allah. ya sharemata hawaye yace kutashi mutafi gida khaleesat takasa mikewa hakanna yadagata yasata akan doki nanma ihu tayi tace menene wanan yaya hydar?? Yace dokina tafara wayyo Allah wlh ni faduwa zanyi, kacire daga kan doki, nibantaba hawaba, tsaki yayi yadaura zulaihat tana bayan khaleesat, hawa yayi kan dokin suna fara tafiya khaleesat tasa hanunta tarike cikinshi gam, wanda hakan yasa suka kusa kifawa takara sandara ihu, zulaihat duk kukan daya cita saida tai dariya, hydar yace wai mehaka cire hanunki a jikina takara kankmeshi tana kuka ai faduwa zanyi to, tsaki yayi ya kyaleta suna kaiwa gida saida yakara saukar dasu. Dasuka fadanma ummi abunda yafaru hankalinta yatashi tace nifa saisa banason tafitan dama, yanzu yazamuyi wazai iya da bala’in FAISOL a garinan?? Hydar yace ummi Allah kaimu goben yazo gidanan dazancen aure yaga inban sassareshi da addanaba tace kai hydar lallabasu fa zamuyi yaza ayi haka. Idan yadage saiya aureta kasan saiya aureta mukuma bazamu iya aurar da yarinyar dabamusan iyayentaba, da kyar ranan khaleesat tai bacci har firgita take saida ummi tahada da mata tofi tukun tai bacci. Washe garin ranan hydar bai fitaba aiki ba. wuraren 10 yaji busan sarewa khaleesat ihu tafara takankame ummi tana kuka, ummi dake salati tana shikenan mun bani yanzu da gaske yake FAISOL yake. hydar dakinshi yakoma ya dauko kwari da kwafa ya goya sanan yadau wata sharbebiyar adda yafita waje ummi nakiranshi hydar ina zaka kisa zakayi ko?? Amma ko kallonsu baiyiba yawuce yafita kofar gida. Tsayawa yayi a kofar gidan ya daure fuska kaman baitaba dariyaba, hanunshi daya na rike da sharbebiyar adda, kafin sukaraso kofar gidan cikin wata irin murya katuwa wanda ban tabajin hydar da itaba yace wlh duk wanda yakaraso kofar gidanan saina sassareshi…. Turus kowa ya tsaya har fadawan, shi kanshi FAISOL gabanshi faduwa yake dan kowa agarin yasan ko waye HYDAR HUNTER!!! [2:22AM, 3/5/2017] β€ͺ+234 803 052 4904‬: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣6⃣ FAISOL ne yace kai hydar nazo auran bakuwarkune, hydar yace inka isa ka sauko kazo wurinann kaga yanda zanyi gunduwa gunduwa dakai, faisol gabanshi yacigaba da faduwa arayuwanshi yana tsoran hydar sosai, juyawa yayi yacema fadawanshi mutafi, suka tafi hydar yakoma cikin gida ya zauna yana huci. ummi tace hydar yatafine?? yace eh, khaleesat tafashe da kukan murna, batare datace komiba. Shikuma hydar ya shige cikin dakinshi yahau bacci. Wuraren 11 na safe yana cikin bacci yaji alamun ihu firgigita yatashi yaji ummi da khaleesat suna kwallamai kira yana fitowa yaga fadawa rike da ummi da khaleesat ga sarki bulala rike da bulala a hanunshi, wani bafade yace sarki yace kodai kabimu muje fada yanzu, ko muyima uwarka dukan tsiya agabanka, ummi cikin kuka tace hydar dan girman Allah kavisu nasanka da taurin kai, jin mamanshi tahadashi da Allah yasa yace musu suje aka saki su ummi shikuma yabisu sai fada. Fada na cike mai martaba sai waziri dawasu makaraban mai martaba aka shigo da hydar. Sarki yace kai harka isa ka wulakanta dana ka disgashi gaban jama’a dan yace yanason bakuwarku da aure wanan makauniyar?? To bari kaji Ko kanaso ko bakaso saiya aureta, ku daukeshi a kulleshi sai bayan kwana 7, sanan abashi bulala 80 abaya tareda horo mai kyau aka tafi da hydar kurkuku. Kowa afadan kallon kallo suke, sunsan inhar an kulle hydar sun bani, kauyenan inba hydar fanko ne, suda cin nama sai randa aka sakeshi dan basu da Hunter a garin dayawuce hydar. Waziri yace Allah ja zamanin sarki, Allah taimaki sarki takarawrka lpy uban gidana ko zan samu daman fadin wani abu?? Sarki yace anbaka. Yace mai girma inhar aka kulle hydar fada bazata kara samun namaba, duk kauyenan bamu da jarumi kaman hydar, shike zuwa mana farautan namun daji, yaza ayi inhar an kulle hydar?? Hakan zaisa ko antashi bikin bazamu samu namabacinba koba hakaba?? Sauran yan fada sukace haka. Shi kanshi sarki faisol ne ya matsa mai saisa ya kulle hydar, amma kowa yasan hydar nada amfani a kauyenan, shikadai ke zuwa farauta yasamo namun daji yasayarma fada yanzu yazasuyi?? Gaskiya dole nasa asakeshi, gyaran murya yayi yace naji zancenku zan sakeshi amma sai bayan azahar. Ummi suna gida sukaji labarin an kulle hydar kuka sukafara, ummi lallashin kanta tayi sanan tafara lallashin khaleesat dake kuka kaman tamutu yanzu yazatayi?? Ankulle yaya hydar mai kareta. Bayan azahar kaman yanda sarki yafada duk suna zaune yasa aka sako hydar aka gurfanar dashi agabanshi. ya kalli hydar a wulakance yace na kwanceka ne saboda kaje kayomana farautan namun daji wanda za’ayi sha’anin bikin dashi kafin la’asar. Yanzu katashi katafi bayan la’asar zamuzo a daura aure, faisol murna kaman yakasheshi harda yima hydar gwalo. Hydar baice musu komiba ya mike idanunshi jajur bayan riganshi duk jini saboda bulala 80 dayasha. Direct yabar fada yana zancen zuci, nasan faisol bazaitaba kula da khaleesat ba, wulakantata zaiyi, bama hakaba yarinyar da bamusan kowa nataba sai nabada ita aure ga wanda baisan darajan mace ba, yace noooo hakan bazai yuu ba dole nasan abunda zanyi na taimaki khaleesat, i have to save her. duba aljihun riganshi yayi yaga yanada dubu biyu, yadau dubu daya yasai goro da sweets, direct yawuce wani babban masallaci kauyen, imam din yasan hydar suna shiri dan hydar akwai mutunci ga yawan ibada yana ganin hydar yace dana wanan goron fa?? mai zakayi dashi??, hydar yace ya imam inaso ka dauramin Aure da khaleesat yanzunan!!! πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣7⃣ Imam yace hydar ban ganeba na daurama aureba, wai meke faruwane?? Nan hydar ya sanar da imam komi, imam yace Allah maka albarka hydar, irinku akeso a musulunci, babu wanda baisan halin yarima faisol ba bari ina zuwa. Waje yaje yakira mutane nanfa masallaci ya cika makil na”ibi ya wakilci hydar, imam ya wakilci khaleesat inda dunbin mutanen nan suka shaida daurin auren HYDAR da KHALEESAT akan sadaki dubu daya. Hydar take yaji hankalinshi ya kwanta sai murmushi yake wanan fararan hokoran nashi na shining. Diban sweets yayi da wasu goro ya dumfara gidansu gabanshi nafaduwa badan komiba saidan khaleesat yanzu yazata karbi alamarin nan?yazataji? Tabe baki yayi yace nima ai ba sonki nakeba, nayi hakane dan na tsira dake daga hanun faisol. Yana shiga gidan da sallamanshi ummi ta taso tana shafa kanshi hydar sannu yaushe suka sakeka?? Yace dazu nan ummi, kallonshi ta tsayayi sama da kasa, saikuma ta duba bayanshi tayi ihu, muje nasama magani hydar yay murmushi yace basai kinsaba ummi. ya kalli khaleesat dake rakube agefe tai tagumi tana hawaye rana tafarko daya fara kiran sunanta yace khaleesat da sanyi muryanshi, da sauri ta daga idonta ta kalleshi kaman tana ganinshi, ya dauke idonshi daga kanta ya kalli ummi yace ummi akwai abu mai mahinmanci dazan fada muku. Ummi ta zauna shima ya zauna yace khaleesat inaso kisani cewa nai hakan ne danna ceci rayuwarki badan komiba, banason faisol ya wahalar dake, banaso ya cutar da rayuwanki, burina daya shine ki warke nakai ki wurin iyayenki, inaso kisani cewa yanzunan aka dauramana aure kafin na shigo gida akan sadaki dubu daya, ke matata ce yanzu khaleesat! Ke matata ce!!!πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣8⃣ Ummi tace hydar maiya kaika yin wanan danyar aikin? yarinyar dakasan bakuwace haryau batasan muba, batasan kalanmuba, batasan ya kamaninmu sukeba, batasan siffarmuba, haba hydar maisa zakai irin abunan batare dakayi shawara daniba kokuma ka tambayi yarinya kota amince dakai. Khaleesat dai batace musu komiba sai kuka datakeyi sosai. Hydar yace ummi abunda kike fada bahaka bane wlh mai martaba dasu faisol bayan sallan la’asar sukace zasuzo a daura auren faisol da khaleesat. ummi nina tsinci khaleesat hakkinane nanema mata lpy, nakula da ita, nakareta daga shairin mutane, har sai randa namikata ga iyayenta. To aganina hanyar dazan iyabi na taimaki khaleesat daga hanun faisol shine nasa adaura mana aure da ita kafin su suzo alokacin tazama matana, ummi ban auri khaleesat dan komiba saidan wanan dalilin. Yajuyo ya kalli khaleesat dake kuka sosai murya irin ta lallashin yaro yace khaleesat kidena kuka, dazaran komi yalafa sati 2 ko 3 zan sake ki kinji ko?? Ta girgiza kai, yace to share hawayenki kimin addu’a Allah bani nasara idan sunzo, ta share hawayen tana murmushi tace amin yaya hydar. mikewa tayi tadau sandarta ta shiga daki dan yanzo tana iya yawo a tsakar gidansu da sanda. Ummi tace Allah maka albarka hydar tatashi ta shiga daki, shikuma hydar yadibe ruwa abotiki ya shiga bayi yin wanka, bayan yafito yasa riga da wando na English wears. Dukda sun kode amma sunmai bala’in kyau sumanshi a kwance lub lub dasu sai kamshi turarenshi yake dan duri lol. Bayan sallan la’asar sarki da mukarabanshi harda wasu sarakuna daya gayyato nawasu gari aka dungumo akayo hanyar gidansu hydar. Khaleesat na zaune daki taji busan sarewa afirgice ta daukan sandanta tayi tana doddogarawa har ta kusa faduwa tayi dakin hydar tana tattaba bango tana wayyo yaya hydar ina kake gasunan sunzo wlh kaboyeni, karsu kamani. Yana daga kwance ya kifeta, hannayenshi biyu abayan keyanshi, ya kafeta da ido batare dayace uffan ba. ko dan kwali babu akanta tanata juya manyan idanunta masu kama da madara tana waige waige alamun nemanshi take, cigaba da shigowa dakin tayi tana kwalamai kira tana kuka, yaya hydar ! yaya hydar! wlh sunzo yau na shiga uku ina kake? kafito kaboyeni dan Allah kar faisol yatafi dani, sandar hanunta ne yafadi tasaki ihu garin kokarin neman sandar tatafi luuu zata fadi hydar ya maza ya finciko hanunta tafada kanshi akan katifa….. πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 1⃣9⃣ Wani irin abu sukaji kaman shock yabi jikinsu da sauri yadagata daga jikinshi yace haba khaleesat kidena ganganci fitowa ke daya saida dan jagora. kokarin rikomai riga take dukta rude tace yaya hydar ai sunzone plz kaboyeni, murmushi yayi yace karki damu babu abunda zai faru in sha Allah kimin addu’a kinji ta girgiza kai tana kuka sosai jikinta ko ina rawa yake. Jawota jikinshi yayi ya rungumeta tai lamoo saida yaji bugun kirjinta yarage sanan yasaketa yace ki zauna anan karki fita kinji bari naje naga…. Jisukayi ana bubbuga kofar gidansu kara fashewa da kuka tarike gefen riganshi gam yaya hydar sune wlh sunzo. Yace khaleesat bazasu miki komiba sakeni naje to. da kyar tasakeshi ya zaunar da ita sanan yay addu’an daura mutum kan makiyanshi sanan yafita. ummi tana daki tana nafilfili Allah yakare danta yasa kar rigiman nan yaja akoresu daga kauyenan. Yana fita waje yaga sarakuna azaune anshimfida babbar tabarma kowa yay shiga ta alfarma. faisol ya gyra zama yace zaka iya zama mufara daurin auren, hydar yay mai kallon rainin wayo wanda saida cikin faisol yajuya hydar yace wace kake magana?? Faisol yace bakuwarku khaleesat makauniya. Hydar saka hanunshi yayi cikin aljihun wando yaciro sweets da goro cike da ladabi ya ajeyi sweet daya da goro daya agaban kowani sarki a wurin harda gaban faisol din sanan yamike ya kalli mai martaba da shima kallonshi yake. Hydar ya gyara tsayuwa yace matar da faisol yazo aure MATATA CE, auren sunna, auren soyayya dan haka babu wani batun aure dan matata….ce bai karasa magana ba FAISOL ya mike yana huci yace kama rainamin wayo to wlh dole kasaketa yanzunan, babu wanda ya isa yahanani auren khaleesat, ina sonta dole kasaketa ya kalli babanshi yace waikai baba bazakace wani abuba ne? maisa kake diganine baba? Wlh baba bakayiba na rantse. Mai martaba jiyayi kaman ya nutse kasa saboda kunya wanan wani irin yaro Allah yabashi, jibi yanda ya disgashi gaban sarakuna gumi yacikamai goshi. Gefe daya danshi nason abu, gefe daya kuma bazai iyayin rashin adalci gaban sarakunaba sunanshi da kimarshi tabaci kafin yay magana sarkin chadi yace. Yarima Faisol bakaji yaro yacema matar aure bace? Katabajin anyi aure kan aure? Faisol yace dalla munafuki yimin shiru fadawan sarki mali suka mike suka dumfaro faisol dan sudakeshi amma sarkin mali yace su barshi tashi yayi yahau dokinshi mai martaba ya ballama faisol harara yatashi yanaba sarkin mali hakuri. wurin dai yakacame da hayaniya hydar kam sai murmushi yake. Sarakuna suka kira sarki gefe suka tattauna sanan aka zauna mai martaba yace hydar munji tunda matarkace yanzu faisol ya hakura kutashi mutafi magana tawuce. Faisol wani ihu yayi yazo gaban hydar ya nunashi da yatsa yace ka sauraren wanan abun bai kareba khaleesat saina aureta ka rubuta ka ajiye. yahau dokinshi hydar sai murmushi yakemai saida suka tafi sanan hydar yakoma cikin gida ya sanar dasu abunda yafaru. Bayan kusan sati 3 da faruwan hakan khaleesat taji shiru hydar haryai bai saketaba, yaudai tagaji da daddare ta shiga dakinshi ta gaidashi ta zauna, yace khaleesat menene?? Murya na rawa tace yaya hydar sakin saikuma tai shiru, hydar ya kalleta sosai sai kuma ya dauke kai yace khaleesat dare yayi yanzu kitashi kitafi gobe mayi maganna mikewa tayi ta turo baki saida takai bakin kofa sanan tace STUPID VILLAGE MAN U BETTER DIVORCE ME OR ELSE HMM arayuwanta bata taba tunanin hydar yaje school ba dan bata tabajin yanayin turenci ba kafa tasa zata fita daga dakin taji ankamo hanunta yana huciiii kaman zaki… πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž πŸ’žπŸ’žπŸ’ž 🌹 *_KHALEESAT_*🌹 πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ ```Maman Abd shakur``` _PAGE_ 2⃣0⃣ Fitsarine kawai khaleesat batasakiba amma ta harde kafafunta saboda yanda taji alamun zai zubo, hydar ya daka mata tsawa yace nikike cema stupid village man khaleesat?? 4 d 1st tym khaleesat sai taji tai nadaman zagin datamai, tai dana sani, mema yakaita? jikinta ko ina rawa yake dan duk azatonta dukanta zaiyi, jitayi ya saki hanunta yace tafi ba laifinki bane. Jikinta yay mugun sanyi, wani irin nadama ya shigeta saita fashe da kuka a wurin taki tafiya, yana daga kan katifanshi ya daka mata tsawa kidau sandarki gashinan wurin kafanki kifita daga dakinan kafin nasaba miki. laluben sandar tafara tai maza ta dauka tana dogarawa tabar dakin tana kuka sosai. Kusan sati daya kenan kwata kwata hydar yafita harkan khaleesat, ko gaisuwanta baya amsawa. wanda hakan yasa hartafara rama, ko ummi saida ta tambayeshi maiya hadashi da ita yace bakomi. Dukta damu kullum saitai kuka aboye wanda hakan yasa idanunta yanzu sunfara komawa jaa. Yau tunsafe take zazzabi sosai ummi da zulaihat duksun damu. Da yamma hydar yadawo daga farauta yana shigowa gidan zulaihat taje da gudu tace yaya hydar Khaleesat batada lpy sunanka taketa kira wai kayakuri kuma takicin abincima. Tare suka shiga dakin hydar ya zauna kusa da ita hakan yasa ummi da zulaihat fita, idonta biyu amma batasan yana dakinba, tsayawa yayi ya kalleta wani irin tausayinta da sonta suka shigeshi a once. Riko hanunta yayi ya matse tareda cewa” khaleesat β€œdukda ba karfi jikinta amma tafara kokarin tashi tana kuka yaya hydar dan Allah kayakuri abunda nama. Nasan banyi daidaiba plz kayakuri dan girman Allah, kuka take sosai gashi idonta yay jajir jikinta zafi sosai, hydar ya shafi gefen fuskanta zuwa lips dinta yace shiiiii, karki kara cewa komi maisa kike wahalar da kanki kinkicin abinci?? Tace yaya

Chapter 2 of 10