buƙata ba? Ni ka san wanene ubana a garin nan,ban da buƙatar kuɗin ka,takaici na bai wuce fifita wannan nunar ranar da ka ke yi ba akai na tin kafin auren naku,amma babu komai,da sannu zan shayar da ku ruwan mamaki."
Tana gama maganar ta ta sa kai ta bar sashen a zuciye,Ruƙayya ma sallama ta yi masa ta wuce sashen Hajiya Dada ta gaida ta,rashin ganin Malika a waje ne ya sanya ta tambayar inda yarinyar take,nan take Hajiya ta sanar da ita tin jiya bata ci komai ba,tana can tana fushi,murmushi Ruƙayya ta yi kafin ta miƙe ta shiga ɗakin Malika,da sallama ta shiga ɗakin,tana shiga sai ta tarar da Malika kwance tana baccinta hankali kwance,bakin nan ta tura shi gaba kamar wadda take a farke,da kallo Ruƙayya ke bin Malika da ke bacci hankali kwance,ta jima tana kallon kyakkyawar surar yarinyar kafin ta haɗiye kishin da take ji a ranta ta tashe ta,cikin sanyin murya ta ce.
"Babyn Papa taho mu je sashena na dafa mana abinci,yau yunwa na tashi da ita,ke fa?"
Hamma Malika ta yi kafin ta ce.
"Ni ma yunwa nake ji sosai Mommy,jiya ma banci abinci ba da dare."
"To taso mu je mu girka abinda za mu ci ko?"
"Ai ni ban iya girki ba."
Ido Ruƙayya ta zaro waje,nan take ta gano wautar da Samhah ta yi na rashin koyawa Malika girki,duk da cewa sun yi ƙoƙari wajen koyar da ita yaren ta na fulatanci da kuma hausa a ƙasar da ba tasu ba,sun yi matuƙar ƙoƙari wajen koya mata abubuwa da dama na al'adar fulani da hausawa,amma girki ai babban jigo ne a rayuwar kowacce mace,a kowacce ƙabila macen da ta iya girki ta daban ce,shi yasa idan Hajiya Dada na hora su Kubrah akan girki Ruƙayya bata damuwa. Duk wanda ya ga Malika ya san ta sha kuka saboda yanda fuskar ta ta yi jawur idanun ta suka kumbura sukai luhu-luhu,after dress ta ɗora a saman kayan baccinta ta bi bayan Ruƙayya dake gaba,suna zuwa parlour ta tsaya ta coge sakamakon ganin Jubair da ta yi a zaune a gefen Hajiya Dada suna gaisawa,tura baki ta yi ta harɗe hannayen ta tana ƙunƙuni,Ruƙayya ce ta dakata da tafiyar ta ta koma ta kama hannun ta suka fita suka bar sashen,suna fita Jubair ya sauke ajiyar zuciya,Hajiya Dada ce ta ce.
"Ka ganta nan haka ta kwana kuka,yau ma da asuba kamar mai karatu ina tashin ta ta fashe min da kuka,a haka ta shiga ta yi alwala ta yi sallah,ni dai ban sake komawa ba dan ko abinci bata ci ba ta kwanta."
"Raina ne ya ɓaci Hajiya shi yasa na yi mata faɗa,sai da kalaman suka riga suka bar baki na na gane ban kyauta ba,amma babu komai zan shawo kanta,yau zan kai ta na haɗa mata layin waya,zuwa wani satin sai a kai ta can gidan kakannin ta ta yi musu kwanaki,kafin ta dawo an kammala duk wani shirin biki da za a yi,in so samu ne ma ta zauna a can sai an ɗaura auren an kawo ta."
"To a ina za ka ajiye ta? Ka dai san ka barta a gidan nan Uwa ba zata bari a zauna lafiya ba ko? A shawarata zai fi kyau ka ajiye ta a gidan ka na Bekaji."
"Duk yanda kika ce haka za a yi Hajiya,Allah ya zaɓa mana abinda ya fi zama alkhairi."
"Ameen Boɗɗo,in ce dai ka sallami kowaccen su da kuɗin da na ce maka?"
"Eh na tura musu."
"To alhamdulillahi,jiya Innarka ta kirani,wai ta ji maganar zaka ƙara aure da ƴar cikin ka kuma ni ce nake goya maka baya,ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,kar ka so ka ji irin kalaman da ta dinga furtawa akan wannan auren,lamarin Batula na bani mamaki,yanzu a ce kana babba ka dinga biyewa yaro ai ta haukan kishi da kai?"
"Hmmm Allah ya kyauta kawai Hajiya, kafin na zo nan sai da Hafsat ta je ta ƙare min tanadi,a ganin ta na basu waɗannan kuɗaɗen ne saboda darajar da Malika ke da shi a wajena,amma Ruƙayya banda godiya da addu'ar alkhairi babu abinda ta yi,ina mamakin yanda Hafsat ke da wani irin murɗaɗɗen hali da sunan kishi."
"Kar ka damu Boɗɗo,kowacce mace tana da yanda take nuna kishinta,ita ta ta hanyar kenan,bata ƙi kullum a yi rikici ba a gidan nan,amma na gode Allah da yasa babu me biye mata,shi yasa nace a raba su da Malika,domin kuwa ana kuskuren haɗa su waje ɗaya kashin mu ya bushe da ni da kai wajen rabon faɗa kullum,dan na kula yarinyar ta gama raina ta."
"Tabbas ta raina ta saboda yada girmanta da ta yi,yanzu baki ga yanda suke da Ruƙayya ba,ta kama girman ta duk da cewa ta san auren yarinyar zan yi,bata taɓa nuna mata sauyi ba ko da a fuska ne,shi yasa itama Malikar ta yarda da ita kuma take sonta tsakani da Allah."
Haka su Hajiya Dada da Jubair suka ci gaba da tattaunawa kafin ya tashi ya yi mata sallama,yana so ya leƙa office zuwa yamma ya dawo sai ya fita da Malika ya ɗan zaga da ita gari ya lallashe ta.
***********************
A can ɓangaren Ruƙayya kuwa kamar yanda ta ce haka suka haɗu suka yi girki a tare,duk da cewa Malika daga wanke vegetables sai wanke nama ta yi,amma da an yi magana sai ta ce tare suka yi girki,koda Ruƙayya ta kaiwa Jubair abinci sai ta tarar baya nan ya fita office,shiru ta yi ta na mamaki,a kaf tsawon shekarun auren su Jubair bai taɓa fita ba tare da ya ci abinci ba sai dai idan azumi yake yi,to ko dai azumin yake yi ne? Amma ai yau laraba ce,azumin me zai yi ranar laraba? Gani ta yi tunanin ya yi mata yawa,sai kawai ta samu waje ta zauna ta ɗauki wayarta ta kira shi,sai da ta kusan yankewa ya amsa,cikin tsare gida ya ce.
"Meye ki ke kirana a daidai wannan lokacin ko baki san na tafi office ba?"
"Ka yi haƙuri Daddyn Mubeena dama na kira ne na ji ka karya kuwa ka fita?"
"Tinda baki ga damar bani abincin ba kin tafi shisshigin da ban aike ki ba ina ruwan ki da karyawa ta? Dan Allah kar ki sake kira na akan abinci dan ni ba ƙaramin yaro bane da za ki dinga damuna."
Kafin ta ƙarasa bashi haƙurin da ta fara yi Jubair ya kashe wayar shi ya na tsaki,tagumi Ruƙayya ta yi tana mamakin yanda akai Jubair ɗinta ya koma haka,ita dai ta san tana yi masa duk wata kyautatawa kamar yanda ta saba yi a baya,to me ya yi zafi a tsakanin su yake yi mata haka?
Tashi ta yi ta nufi sashenta,su Kubrah ne da Malika ke yin waya,suna ganin ta suka datse wayar da suke yi suna zare ido,ta na gani ta gane basu da gaskiya,amma ba wannan ne a gabanta ba yanzu,kewar iyayen ta take ji na huda kowacce gaɓa ta jikinta, ɗakinta ta shiga ta shirya cikin wani tsadadden leshi mint color,farin mayafi mai kyau ta yafa ta sanya farin takalmi da jaka,wayoyin ta ta zuba a cikin jaka ta ɗauki makullin motar ta,sai da ta zo tsakiyar parlour sannan ta tsaya ta cewa Kubrah.
"Ban san me kuke aikatawa ba,amma ina fatan ki kiyaye duk abinda zai jawo zubewar mutuncin gidan nan,idan Daddyn ku ya hanata hulɗa da kowanne namiji kar ki zama mu'assasar haɗa ƙullin da ba zai taɓa ƙulluwa ba har abada,ni zan tafi gidan Baffajo,ku kula da kan ku, idan su Ihsaan sun dawo a yi homework a ci abinci,kar wanda ya shigar min ɗaki na,sai na dawo."
Sashen Hajiya Dada ta je ta yi mata sallama sannan ta wuce wajen motarta ta shiga,mai gadi na ganin haka ya tashi da sauri ya buɗe gate, cikin ƙwarewa da gwanancewa Ruƙayya ke tuƙi har ta fita ta bar gidan, duk abinda take yi akan idon Ubaida take yin shi,ta na fita Ubaida ta shiga sashen Uwa da ta bata labarin abinda ke faruwa,murmushi Uwa ta yi sannan ta ce.
"Ke kuwa yau account ya cika da kuɗi ai dole a sai wa masu dattin ɗankwali da hula shinkafa da sugar ko sun tada komaɗa."
Dariya Ubaida ta sanya ta na sake zuga Uwa,nan suka zauna suka dinga gulmar Ruƙayya,cikin nuna isa da ita wata ce Uwa ta ce.
"A yanda na ji labari fa mahaifin ta facin robobi da ƙwarya yake yi a kasuwar ƙauyen su,daga haka Allah ya sa ya fara shigowa birni,idan zai taho ne yake shigowa da ita surbajon ta taho da tallan nonon ta a manyan ƙwarya,dan kuwa Allah ya azurta su da nagge,idan Baban nata ya zauna a kasuwa aikin facin shi,ita kuma sai ta bazama gari,sai ta saida Nono sai ta koma wajen shi su koma gida,a haka har ya yanke shawarar dawowa cikin birni da zama,to shine fa ya saida nagge uku ya sai musu gidan da suke ciki a yanzu. Garin yawon tallan Nono suka haɗu da Jubair,kyawun ta da natsuwarta ne ya ribace shi ya aureta,wanda ni ba wai na yarda bane,tinda akwai zarge-zargen da mutane ke yi akan mahaifinta."
Shiru Uwa ta yi bata karasa maganarta ba sakamakon wayarta da ke haske,hannu ta sa ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta bayan ta amsa,da hannu ta kori Ubaida ta miƙe ta shige ɗakinta,hira suka fara yi da ƙawarta Mansurah ta kwashe duk abinda ke faruwa a gidan nasu ta sanar da ita,shiru ta ɗan yi alamun tana sauraron abinda ake faɗa mata daga ɗaya ɓangaren,shewa ta yi ta samu bakin gado ta zauna kafin ta ce.
"Kema kin san shiru na ba gazawa bace ƙawata,lokaci nake jira da zan aiwatar da duk wani ƙudirina da nake shiryawa,ni fa yanzu ina da mataimaki wanda ya fara share min kukana,da ace na san da zaman shi tin farko ai da na jima da juya sitiyarina yanda na so a gidan nan,amma yanzu ma lokaci be ƙure min ba,ya ce na kwantar da hankali na,aure dai dole ne sai an yi shi,idan na ce zan matsa ko dai nawa auren ya mutu ko na rasa rayuwata ne gaba ɗaya,a da ban yarda ba sai da Ummah ta je wajen malamai kusan uku ana faɗa mata amsa ɗaya,to shine na kwantar da hankali na for now,ina jiran lokacin da ya dace na kai hari na tarwatsa muguwar alaƙar tasu."
Dariya ta yi sannan ta shige band'aki tana ci gaba da wayarta.
Da yamma liss Jubair ya dawo a matuƙar gajiye,ganin har wannan lokacin Malika na fushi da shi ne ya sanya shi sanar da ita ta shirya zuwa ƙarfe biyar za su fita ya haɗa mata layin waya.....
*Wacece zata bi su ko chakulan a sai mata daga nan?*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE.....
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 17:
Washegari da misalin 12:30am na rana su Malika suka fita da ƙaramar motar da Jubair ya baiwa Kubrah a matsayin gift ɗin ta na kammala sakandire,Malika ce ke jan motar,ta hanyar amfani da GPS suka isa haɗaɗɗen saloon ɗin da manyan mata ke zuwa a garin na Yola,babu ɓata lokaci ma'aikatan wajen suka hau gyarawa Malika da Kubrah gashin su,ana gamawa da gashi aka yi musu wankin ƙafa da gyaran farce,nan take suka fito fess da su,bayan sun biya kuɗin aikin da aka yi musu ne suka kama hanyar komawa gida.
Lokacin da suka isa gida azahar ta wuce,direct wanka Malika ta shiga ta yi,ta na gamawa ta ɗaura alwala,sai da ta yi sallah sannan ta sanya doguwar riga mara nauyi ta fita parlour,abinci ta ci sama-sama,a cewar ta bata son ta cika cikin ta kafin a fara partyn,tana nan zaune ta ga Kubrah ta shigo cikin shiri sanye da wasu ƙananan kaya masu kyau,sai ta sanya ƙaramin hijabin da ya ɓoye dogon gashin ta,tsayawa ta yi ta na kallon Malika da ko shiryawa bata yi ba,cike da mamaki ta ce.
"Me kike yi har yanzu baki shirya ba ga ƙawaye na can har sun fara zuwa?"
"What ! Sun fara zuwa fa? Amma dai da wasa kike yi ko? Ku anan da rana tsage-tsage ake yin irin wannan partyn?"
"To me za mu jira Addah Malika? Ai yanzu za a fara kafin magarib an gama kowa ya kama hanyar gidan su,yanzu ma masu snacks ɗin nan suka kirawo ni wai suna hanyar kawowa,dan Allah tashi ki shirya,kin san me ke faruwa ma kuwa?"
Kubrah ta ƙarasa maganar ta tana dariya ƙasa-ƙasa,a hankali ta isa gaban Malika ta raɗa mata magana a kunnen ta,waro ido Malika ta yi waje kafin ta ce,
"Lallai idan Papa ya gan shi sai ya yi mana faɗa,ni dai babu ruwa na ki kore shi kar azo ana ganin laifi na bana so,bari na je na shirya na zo."
Ɗakinta ta shiga ta shirya cikin riga da wando masu kyau ta baza gashin kanta kamar yanda ta saba yi a can turai,turaruka masu ƙamshi ta fesa a jikinta kafin ta sanya takalmanta masu tsini ta ɗauki wayoyinta,ko leƙa ɗakin Hajiya Dada bata yi ba tai waje inda Kubrah ke zaune tana jiran ta.
Suna fita ƴan matan da suka fara zuwa suka hau kallon Malika,duk da cewa da damar su suna ji da kyau da nera,sai suka ga Malika ta kere su,kyawun fatar ta daban ne da nasu,kamar wadda rana bata taɓawa,kiɗan dake tashi a parlourn ne ya sanya Malika ɗaga murya ta ce.
"Ke me yasa ƙawayen ki ke ta kallo na ne?"
Dariya Kubrah ta yi kafin ta ce.
"Da damar su ma sun ce suna son ƙawance da ke,kin ga waccan...ita ce Wahidah,yayanta ne yace yana son ki,gashi can a waje yana mota yana jiran ki,dan Allah kar ki bani kunya,na riga na sanar da su baki da boyfriend."
"Wa ya ce maki bani da boyfriend? Se na haɗa ki da Afhdal duk da cewa ya watsar dani tinda na zo nan,a gaskiya ki kore shi bana son matsala da Hajiya Dada."
Da wannan hirar Malika ta bar Kubrah tsaye ta hau rawarta,babu jimawa masu abinci da abinsha suka zo suka hau raba musu abun sha kamar yanda suka tsara,party ya yi party babu zato ko tsammani Malika ta ji hannu ya kama ƙugunta an juyo da ita,cike da dariya ta juya dan ta ga waye da wannan ƙoƙarin,idanun ta ne suka sauka akan wani matashi fari tas mai bala'in kyau,babu musu Malika ta biye masa suka ci gaba da rawa saboda tsananin kyawun da ya yi mata,dama ita ba yau ta saba rawa da maza ba a wajen party,ihu wajen taron nasu ya ɗauka,a hankali matashin ya kai bakin shi saitin kunnen Malika ya ce mata.
"Suna na Taufiƙ,ni ne Yayan Wahidah,na aika ki zo kin ƙi zuwa,shi yasa na zo da kai na ba saƙo ba."
Gaba ɗaya Taufiƙ ya gama kashewa Malika jiki, cikin kasala ta ce.
"I have a boyfriend."
"Wow ! A ina ya ke? Ni ban ga kowa ba,daga ni sai ke nake gani anan,dan ni ko mutanen dake wajen nan ma bana gani,kin cike min idanuna da zuciyata da surar ki,ki taimaka ki karɓi so...."
Tasss ! Shine ƙarar marin da ya katse Taufiƙ ya hana shi ƙarasa maganar shi,cikin hargowa da hauragiya Jubair ya kalli ƴan matan dake tsaye suna kallon Malika da Taufiƙ ya daka musu tsawa ya ce.
"Kowa ta kama hanya ta tafi gidan su,tinda ba shagalin azziƙi kuke yi ba."
A gaggauce kowaccen su take tattara nata ya nata dan barin parlour'n,Kubrah kuwa ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando,dan kuwa bata taɓa zaton Daddyn nasu na gida ba balle har ya ga abinda ke faruwa,cike da tashin hankali Taufiƙ ya kafe Jubair da kallo,domin kuwa tinda ya taso ya yi hankali iyayen shi basu taɓa ɗora hannun su akan shi ba da sunan duka,ya taso cikin gata da kulawa tare da tarairaya,mahaifin shi minister ne dan haka shima iyayen shi manyan mutane ne,a tsaitsaye ya ke kallon Jubair dake sake jaddada masa ya fita ya bar masa gida,cikin wani irin yanayi Taufiƙ ya ce.
"Ni ka mara? Ka san wanene ubana a ƙasar nan kuwa? Ka tafka babban kuskure Alhaji,ƴar ka ce dai baka son na kula ko? To ina so ka rubuta ka ajiye,komai daren daɗewa sai na wulaƙanta ƴar ka,sai na yi yanda na ke so da ita,da fari auren ta nake so na yi,amma yanzu ka sauya min tunani na da mari ɗaya."
Cike da zafin zuciya Taufiƙ ya fita ya bar parlourn,wajen sai ya rage daga Malika sai Kubrah dake ta kuka tana jiran mummunan hukuncin da mahaifin nata zai yanke akanta,cikin matsanancin fushi Jubair ya kalli Kubrah ya ce
"Haka muka yi da ke? Baki yi min alƙawari babu maza a wajen partyn naku ba? Me yasa kika saɓa alƙawarin da kika yi min bayan kin san na tsani karya alƙawari? Ashe ba daban Munkaila ya sanar dani abinda ke faruwa ba da shikenan haka zaku zauna wani ƙato yana rungumarta yana shafa jikinta ko? Ke kuma zo nan,wato rashin ɗa'ar da kuke yi a can turai shi kike so ki kawo min cikin gida har ki koyawa yarana rashin tarbiyya ko? To ba zan ɗauka ba,maza ki wuce cikin gida kafin na ɓalla ku."
A guje Kubrah ta fita tana hamdala da abun ya tsaya a haka,Malika kuwa kalaman Jubair ba ƙaramin dukan zuciyarta suka yi ba,cikin hawaye take kallon shi ta ce.
"Papa ni ce zan koyawa yaran ka rashin tarbiyya? Ba fa ka tambaye ni ya abun ya fara ba,amma ka yanke min hukunci har ka ke kallon ni ce nayi laifi."
Da jin kalaman Malika sai jikin Jubair ya ɗan yi sanyi,amma kishin da ke cin zuciyar shi ne ya hana shi tsayawa ya bata damar kare kan ta,a tsawace ya kora ta cikin gida itama,waje ya samu ya zauna ya na sauke numfashi a hankali,a hankali zuciyar shi ke dawo masa da hoton Malika riƙe a hannun yaron da a kallo ɗaya ya gano dacewar da suka yi da juna,babu ƙarya badan zuciyar shi ta kamu da son Malika ba tabbas da babu namijin da ya dace da ita da ya wuce Taufiƙ,yaro ne mai jini a jika,ga kyau ga tsarin halitta ta cikar mazantaka,a ƙalla shekarun Taufiƙ za su yi ashirin da tara ko talatin. Iskar bakin shi ya furzar ya sake lulawa duniyar tunani,yana nan zaune aka fara kiraye-kirayen sallar magariba, Munkaila ne ya shiga parlour'n ya risina a gaban Jubair,cike da ladabi ya ce.
"Allah ya taimake ka Alhaji lokacin sallah ya yi,a yi haƙuri na san ba za ka so ganin abinda ya faru ɗazun ba shi yasa na kirawo ka,saboda ni ba zan taɓa iya ganin ana cin amanar ka ba ba tare da na yi wani yunƙuri akai ba."
"Na gode Munkaila,ba dan kai ba da ban san me zai faru ba kuma,dan Allah a duk sanda ka ga irin haka zata faru ka gaggauta kira na kamar yanda ka yi a yau."
"Inshaa Allahu Alhaji zan ci gaba da riƙe maka amana har ƙarshen zaman mu."
"Na gode Munkailan Hajiya Dada."
Da wasa da dariya su Jubair suka bar parlour,Munkaila ya wuce ɗakin shi ya yi alwala,shima Jubair sai ya wuce sashen shi da yake jin duk ya sauya saboda warin da Rukayya ke yi. Yana fitowa masallaci ya wuce,har aka yi sallar isha'i bai sake bi ta kan Malika ba balle ya bata haƙuri.
Malika kuwa taso ta kira Ammar ta sanar da shi tana so ta dawo gida,sai ta tina ko tace zata koma gida kafin ta samu visa ma aiki ne,tinda Daddyn ta ya sanar da ita ko waccan Visa ɗin da suka samu sai da ya sha wahala kafin ya same ta,kuma ya kashe kuɗi sosai akai.
Kwanciyar ta ta gyara ta sake rushewa da kuka,tinda take a duniya ba a taɓa yi mata faɗan da ya shiga zuciyarta ba irin wannan,me yasa kalaman shi suka yi mata zafi? Ta riga ta saba yin rashin ji a yi mata faɗa,amma wannan karon kusan laifin ba nata bane ita kaɗai,hasali ma cewa ta yi a kore shi ba zata je wajen shi ba,amma shine Papa ke ganin ita ce mai laifin har yake kiran zata koyawa yaran shi rashin tarbiyya.
A haka Hajiya Dada ta aika Kulu da fruit salad dan ta kaiwa Malika ta sha,tinda ta riga da ta san cimar ta da dare baya wuce salad,chips da fruit salad ɗin,sai kuma soyayyar kaza da kayan maƙulashe dangin su ice cream, biscuits da chocolates.
Ko kallon Kulu Malika bata yi ba,haka ta bar abincin ta ci gaba da kukan ta,ƙarshe a haka ta tashi tana kukan ta yi sallar magariba da isha'i sannan ta kulle ɗakin ta ta kwanta,duk a zaton ta Papa zai biyo ta ya bata haƙuri.
A can sashen Jubair kuwa baƙin ciki goma da ashirin ne suka taru suka yi masa yawa,tinda ya yi sallar isha'i ya koma sashen shi warin da jikin Ruƙayya ke yi ya addabe shi,ga kuma kewa da tinanin halin da Malika ke ciki da ya mamaye zuciyar shi. Rashin sanin yanda zai yi ne ya sanya shi shiryawa cikin kayan bacci ya fita ya wuce sashen Uwa........
*Jubairrr.*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE.....
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 20:
A ƙofar gidan su Samhah Jubair ya tsaida motar shi, cikin sauri ya buɗe ya fita ya hau buga gate ɗin gidan,mai gadi ne ya leƙo da kan shi ta jikin wata ƙaramar ƙofa kafin ya mayar ya rufe,buɗewa Jubair ya yi yana faɗin.
"Alhaji ba za ka shigo da motar bane?"
Ba tare da Jubair ya saurare shi ba balle ya bashi amsa ya shiga cikin gidan,yana shiga Innah Habi ta ce.
"Alhamdulillah,gwanda da Allah yasa ka dawo,ni wai wannan yarinyar ashe har yanzu bata yi hankali ba? To gata can ka tattara ta ka maida ita gidanka ku ƙarata,in ba haka ba anjima zan sa mata hannu,ni ba zan ɗauki wannan sakarcin da sangartar ba."
Cike da damuwa Jubair ya ce,
"Dan Allah Innah ki yi haƙuri,lamarin ya zo mata a ba zata ne,tana ina yanzu?"
"Gata can a ɗaki duk ta fashe min gilasai kamar ubanta ne ya siya min,maza ka ɗauke ta ku wuce ba zan lamunci rashin hankali a gidana ba."
Cikin sauri Jubair yabi bayan Umaimah ta kai shi ɗakin da Malika take,Kubrah ya gani tana ta lallashin ta amma sai turjewa take yi tana ci gaba da watsi da duk abinda ta ɗauka,tsawar da Jubair ya sakar mata ne ta sanya ta tsayawa cak tana kallon shi,a hankali ya fara sassauta fuskar shi daga ɗauretan da ya yi,Malika na ganin haka ta tafi da gudu ta faɗa jikin shi ta fashe da kuka,a bakin gado ya yi musu masauki ya kalli Kubrah dake tsaye ta na sharar hawaye,ajiye kwalbar turaren da Malika ta yi niyyar fasawa ta karɓe ta yi sannan ta fita ta basu waje.
A hankali Jubair ya raba jikin shi da na Malika yana kallon ta,cikin sanyin murya ya ce.
"Amma baby kin bani mamaki,ashe dama da kike cewa ni ne zan zaɓa maki miji a duk sanda kika tashi yin aure ƙarya ne? Me yasa za ki ɗaga hankali ki irin haka har ki ɗagawa grandparents ɗin ki hankali?"
Kuka ta fashe da shi sannan ta ce.
"Papa aure fa za ku yi min da ƙananan shekaru na,Papa ni dai dan Allah kar ku yi min aure ina da future mai kyau kar ku dakushe min shi,Papa ban san mijin da za ku aura min ba fa,what if bana son shi?"
"Duk na ji uzirin ki,yanzu faɗa min wanne irin miji kike so?"
Ajiyar zuciya take ta saukewa hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta kamar ruwan pampo ta ce.
"Ina son miji mai tsoron Allah,saboda ta haka ne zan san abinda Allah ya halatta da wanda ya haramta wanda a baya bana kiyayewa,ina son mijin da yake da wayewa,amma hakan ba yana nufin ya zama mara riƙe al'ada ba,ina son miji kyakkyawa Papa kamar dai kai ɗinnan."
Ta karasa maganar ta cikin kukan shagwab'a,murmushi Jubair ya yi kafin ya ce,
"To idan kuma kika same ni a matsayin mijin ki fa zaki iya zama da ni?"
Dariyar yaƙe ta yi wadda har a wannan lokacin hawaye bai dena zuba a idanunta ba ta ce.
"Papa i can marry someone like you,but I can't marry you."
"Why?"
"Kai Papana ne,ƴa bata auren Papan ta ai."
"Kin manta alaƙar dake tsakani na da Daddyn ki? Akwai aure a tsakanin mu."
"Ni dai Papa ba zan iya auren ka ba,dan Allah ka bar yi min maganar nan bana so,ka sanar dani