Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
ƙalau." Ba tare da Ruƙayya ta ce komai ba ta wuce sashenta,Hajiya Dada da takaicin Uwa ya kamata sai ta ce. "Wai ke me yasa baki son a zauna lafiya ne? Yanzu ace ɗanta ya rasu ki dinga abu kamar me murnar rashin da muka yi a gidan nan?" Marairacewa Uwa ta yi kafin ta ce, "Ni dai dan Allah Hajiya kar ki fassara ni,akan me zan yi murna da rasa rai?" "Humm Allah ya kyauta,to kai da ka yiwa yara alƙawarin kai su makaranta da ƙananan kaya za ka je? Ai ya kamata a yi shiga ta kamala." "Haka ne kuma Hajiya,ina zuwa bari na je na shirya,ya banga an kawo miki abun karyawa ba har yanzu?" Sallamar kulu ce ta hana Hajiya magana,abincin ta ajiye a wajen da Hajiya ke cin abinci kafin ta gaishe da su Hajiyan,suna gama gaisawa ta wuce ɗakin Hajiya domin gyarawa. Jubair kuwa sashenshi ya koma ya shirya cikin wata shadda ruwan zuma mai haske,ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba,hula da takalmin shi kalar brouwn sai a gogon shi na fata mai tsada da ya ɗaura,turare ya fesa masu ƙamshi sannan ya tsaya gaban madubi yana kallon kan shi,ganin shi ya yi kamar wani ɗan shekara talatin da ƴan kai,gaba ɗaya jikin shi bai nuna shekarun shi ba,samun kanshi ya yi da ɗaukan brush ɗin da yake taje gemun shi ya hau tajewa,Uwa na shiga ta ga abinda yake yi sai ta tsaya tana binshi da kallon mamaki. "Wai ni Yallab'ai duk wannan shirin na menene? Yara fa zaka kai makaranta kawai ba wani waje na musamman ba." "Ah ! waje ne na musamman mana,ko kin manta yau Kubrah ke kammala secondary school? Yau rana ce ta musamman a wajen ta dole ne na taya ta murna." "Hmmm haka ne." Koda ya fita farfajiyar gidan bai ga yaran ba,zuciyar shi na kwad'aita masa akan ya je ya ga Ruƙayya da yaran,amma wani sashe na ranshi yana jin tsanar zuwa sashen nata,dan haka kawai sai ya wuce wajen ajiye motoci,driver ne ya taho da sauri ya duƙa ya gaishe da Jubair,amsawa ya yi tare da sanar da shi yau da kan shi yake son ya kai yara makaranta,cike da ladabi driver ya ce, "Alhaji da wacce za a fita na sake goge ta?" "Kar ka damu,ai na ga duk a goge suke ko? Amma da waccan farar zamu tafi." Wata haɗaɗɗiyar mota ya nuna wadda ya san zata burge Malika,dan kuwa Malika na da son motoci,shi yasa duk wata sabuwar mota da ta fito take sanin fitowarta da sunan ta,tare da kud'in da ake saida ita,Jubair ya san yanda take son motoci da party shi yasa yake son ya kai su dan kar ta je ta zaƙe. Kanshi na duƙe yana latsa wayar shi suka fito daga sashen Ruƙayya cikin shiri,ƙamshin turaren su da ƙarar takalman su ce ta sanya Jubair ɗaga kan shi,idanun shi ne suka sauka akan Malika dake sanye da atampa golden yellow da ratsin kore a jikinta,sai wani mayafi mai kyau da tsada kalar kayan jikin ta da ta yafa,golden takalmin da ke ƙafarta ya saje da fatar ta fara,Kubrah da su Ihsan sai ƙunshe dariya suke yi saboda yanda suka ga mahaifin su ya shagala da kallon Malika. Wayar shi ya saita ya hau ɗaukan ta video yana murmushi,da ƙyar ta ƙarasa inda yake tsaye saboda harɗewar da ƙafafunta ke yi,tana isa inda yake sai ta rungume shi tana murma,cike da murna ta ce, "Papa ka ɗauki kaya na a hoto kuwa? Papa ka turawa Dad da Mom su ga kaya na please" "Ai dole ne na nuna musu su ga yanda Babyna ta yi kyau da atampa,da dikkan alamu da kaina zan kira Jamila ta kawo kaya masu yawa,ai kina so ko?" Cikin sauri ta ɗaga kai,murmushi Jubair ya yi sannan ya ce, "Idan tazo kuma ku zabi duk abinda kuke so,ku shiga mota mu tafi." Sai da Malika ta zagaye motar tana ta yabawa kamar yanda Jubair ya yi zato kafin ta shiga baya ta zauna,Kubrah ce ta ce, "Addah Malika ki dawo gaba mana,zaki fi ganin gari sosai." "Ah ah ki zauna a gaba, today is your day,watarana zaki fitar dani na ga gari sosai." Gaba Kubrah ta shiga,kafin ta ce, "Ai bana driving,Daddy baya barina,ya ce na yi ƙarama." Jubair ne ya ce. "Kar ki damu,yanzu da kika kammala makaranta zan sai maki mota mai kyau idan result ɗin ki ya yi kyau amma." Murna suka dinga yi har suka isa makaranta,sun yi hotuna sosai da videos masu yawa tun a mota kafin su isa,suna zuwa yaran suka fita daga motar su ka shiga makaranta,tin daga gate Jubair ya fara daya sanin barin Malika ta je wannan waje,manyan maza magidanta da matasan samari ne suke bin ta da kallo kamar ita ɗaya ce a wajen,wani irin abu mai zafi ya ji ya taso ya tokare masa ƙirji,a hankali ya furta. "Me ke faruwa da ni ne?" Cikin sauri ya kauda kan shi ya sanyawa motar ya tada ta zai tafi,idan sun kammala driver ya ɗakko su,idanun shi ne suka sauka akan wani matashi kyakkyawan bafulatani dogo fari tass ya nufi wajen su Malika yana ƙwambo,ido Jubair ya zaro waje ya yi saurin kashe motar ya fita,direct wajen su Malika dake tsaye tana yiwa matashin nan murmushi ya nufa,ya na zuwa sai ya kama hannun Malika ya ce, "Ku me kuke yi anan a tsaye baku shige ba,shirmen da za ku tsaya yi kenan dama? To ke maza wuce mu tafi gida,ku kuma ku shige makaranta anjima TK zai zo ya maida ku gida." Kuka Malika ta sanya ta fara roƙon ya barta ta zauna da su Kubrah,ganin zata tara masa jama'a ne ya sanya shi saɓa ta a kafaɗa ya wurga ta a mota ya tada motar ya bar wajen a guje........ [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE.... RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 14: Daskarewa Uwa ta yi a wajen kamar an dasa ta tsabar shiga tashin hankali da ɗimuwa,Hajiya Dada kuwa dogara sandarta ta yi ta juya da nufin ta je ta lallashi Malika,Kulu ce ta ce mata. "Tana sashen Mommy." Wajen Ruƙayya Hajiya Dada ta nufa zuciyar ta cike da takaicin halayyar Uwa,da ace wata bare ce daban take rashin mutuncin da uwa ke yi tabbas da ta sa Jubair ya rabu da ita kamar yanda ya rabu da sauran matan da ta sa ya aura,a tsarin ta bata maraba da matar da zata ɗaga mata hankalin shalelenta,ba kuma ta son matar da zata zauna da shi ba domin Allah ba sai dan dukiyar shi,saboda tana tsoron kada wata rana a yi mata sanadin numfashin sa. Lokacin da ta isa sashen Ruƙayya ta tarar da Malika kwance a kujera ta na rizgar kuka,duk yanda Ruƙayya da yaranta suka yi dan Malika ta yi shiru ta sanar da su abinda yake faruwa ƙi ta yi,sallamar Hajiya Dada ce ta sanya Ruƙayya miƙewa cike da girmamawa ta durƙusa ta gaishe ta,sannan ta koma gefe ta ce. "Tinda ta shigo take kuka na rasa dalilin wannan kuka nata,na yi iya yi na ta sanar dani me akai mata taƙi sai kuka,kuka na maganin damuwa ne? Ko dai kewar gida kike yi?" Sai a daidai wannan lokacin ne Hajiya Dada ta ɗan ji nauyin hukuncin da ta yanke,amma ya za ta yi,haka kawai take ji a jikinta Malika ce maganin warwarewar duk wata matsalar su ta rashin ɗa namiji a gidan,zama Hajiya Dada ta yi a kujerar dake kusa da Ruƙayya kafin ta ce. "Ke Kubrah kama ta ku tafi can waje na,Kulu za ta kawo mata abinci ki tabbata ta ci,ke kuma ki dena wannan kukan banzan,ko baki ga kina da ƙanne bane? Gasu nan sai su yi miki dariya ai su ce gotai-gotai dake ki na kukan banza." Fuska jawur Malika ta ɗaga kai ta kalli Hajiya Dada ta tura baki ta na kyaɓe shi irin na masu kuka ta ce. "Prostitute fa ta ce min,me na yi mata da ta tsane ni tinda na zo gidan nan? I don't want to be here ni gidan mu zan koma." "To je ki ki haɗa kayan ki sai ki sanar da uban naki ya maida ki gida." Tashi ta yi tana tafe ta na kuka su Kubrah na biye da ita suna bata haƙuri,sai da suka tafi ne Kulu ta ɗebar mata abinci ta fita sannan Hajiya ta kalli Ruƙayya da ke kallon ƙasa tana jiran ta ji abinda Hajiya zata sanar da ita,ba tare da ta san me Hajiyar zata sanar da ita ba ta ji ƙirjin ta na bugawa,cikin zuciyarta ta ke ayyana, 'Ina ganin kamar na san irin wannan yanayin? Wannan karon kuma wa aka samo mana?' Kamar daga sama ta jiyo muryar Hajiya Dada na faɗin, "To kin dai ji kalmar da Uwa ta faɗawa yarinya ƙarama ƴar cikin ta ko kunya bata ji ba,shine nake so na goge mata kalmar karuwa da ta kira ƴar mutane da shi ta koma MATAR JUBAIR,wataƙila a samu abinda ake nema ta wajen ta,ina so kamar kowanne lokaci ki sanyawa zuciyar ki haƙuri,babu abinda kika nema kika rasa a gidan nan,kina da soyayyar mijinki,ga yaran ki,duk wata sutura da abinci da kike buƙata kina samu har ki yiwa iyayen ki da ƴan uwan ki,to dan haka kar ki ce zaki tada hankalin ki akan mijin da kika san dama mijin mace huɗu ne shi." Cikin murmushi da kwantar da kai Ruƙayya ta ce, "Babu komai Hajiya,Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,Allah ubangiji ya haɗa kammu ya bada abinda ake nema mai albarka." Murmushi Hajiya ta saki kafin ta ce, "Allah ya miki albarka Ruƙayya,da na biyewa mutane da surutan su da ban samu suruka mai natsuwa da kamala irin ki ba,tabbas da na tafka babbar asara." "Yaushe za a yi abun Hajiya?" "Kwanan nan za a yi, dan bana son ta sani ma yanzu,so nake sai an ɗaura daga baya ta san me ake ciki,gobe idan Allah ya kaimu taron ahalin da za a yi zan gabatarwa da iyayen Jubair maganar auren,idan yaso zuwa wani satin mun sanar da Ammar sai a yi komai." "Allah ya kaimu Hajiya da rai da lafiya,Allah kuma ya sanya albarka." "Amin ya Allah,to bana me kike so? Umara zaki je ko a baki kud'in a hannu?" Shiru Ruƙayya ta yi,hakan da ta yi kuwa ya sa Hajiya Dada ta gane kud'in take so,kasancewar iyayen ta masu ƙaramin ƙarfi ne shi yasa tafi so ana bata kyautar kuɗi,a cewar ta ta je Hajji ta je umara da yawa,dan haka ta fi buƙatar kuɗin,da su take yiwa iyayenta da ƴan'uwan ta hidima. Tashi Hajiya Dada ta yi bayan ta yi mata sallama ta wuce sashenta,tana fita Ruƙayya ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa da ƙarfi. A can ɓangaren Jubair kuwa tinda Hajiya Dada ta faɗi wannan maganar ya shiga cikin wani irin yanayi,a wannan lokacin ne ya tabbatarwa da kan shi yana son Malika,so irin na soyayya ba wai iya soyayyar ƴa da uba yake yi mata ba,wani irin abu ya dinga ji yana ratsa kowacce gaɓa ta jikin shi,bayan Ruƙayya da ya gani da idanun shi,ya mu'amalance ta har ya aure ta,babu wata mace a kaf matan da ya aura a baya ya furta da bakin shi yana son ta,gaba ɗayan su zaɓin Hajiya ne,wasun su ya so su bayan aure, wasu kuwa har suka rabu ko shimfiɗa be haɗa da su ba. A wannan karon ji yake idan wani abu ya gilma aka fasa auren shi da Malika to fa tabbas wani mummunan abun zai iya samun shi,wani ƙayataccen murmushi yake saki lokaci zuwa lokaci,Uwa kuwa ta jima da barin sashen Jubair ta wuce sashenta,Munkaila ta aika Ubaida tace ta kirawo mata shi da gaggawa,Ubaida na fita ta shiga ɗaki ta kirawo mahaifiyarta ta sanar da ita mugun labarin da ya same ta,salati Ummah ta sanya sannan ta ce. 'Amma dai Dada bata so a zauna lafiya a gidan nan naku,yaushe zata aurawa Jubair yarinya rainon turai irin wannan? Sam ba zai yuwu ba,bari baban ki ya fita zan kira ta na ji bahasin da zai sa ta yi mana haka.' Suna kashe waya Uwa ta zauna a bakin gado ta zabga tagumi,hawaye take so ta zubar amma sun maƙale sun ƙi fita,wani irin azabar zafin kishi ke yi mata tururi a ƙirjin ta,ina zata saka kanta yanzu idan Jubair ya auri wannan shagwaɓɓiyar yarinyar? Sallamar Ubaida ce ta dawo da ita hayyacinta,kanta ta ɗaga ta kalli Ubaida da idanun ta da suka kaɗa suka yi jawur kamar an saka mata barkono,a hankali ta furta. "Ki shiga ɗakin ki,ina so mu yi maganar yanda za a ɓullowa maganar auren ku ke da Munkaila." Kunya ce ta kama Ubaida,dan haka cikin sauri ta bar ɗakin Uwa ta na murmushi ta wuce Munkaila,kallon ta ya yi shima yana murmishi har ta ɓacewa ganin shi,Uwa na fitowa sai ta samu waje ta zauna tana fuskantar Munkaila,suna haɗa idanu ta ji wasu zafafan hawaye na zuba daga idanunta kamar ta kawo kukan ta wajen wanda take da yaƙinin zai bata maganin matsalar ta,ji take yi zuciyarta na yi mata tsananin suya,a haka ta buɗe baki za ta yi magana,Munkaila ne ya ɗaga mata hannu ya ce. "Tin ranar da suka dawo daga turai na shiga bincike akan ta saboda hasken da na gani a tsakanin su,maganar gaskiya Hajiya ba ni bama,duk duniya babu wajen bokan da zaki je ki samu mafita akan wannan lamarin,domin kuwa auren nan dole sai ya ɗauru,sannan dole ne a haifi magajin Alhaji ta wajen wannan nunar ranar,abinda nake so da ke kawai shine,ki saki jikin ki, ki kwantar da hankalinki bayan auren zan samar maki mafitar da zata zame maki alkhairi na har abada. Dan haka ina so in san shin kin shirya yin duk wani abu domin kawar da duk wanda zai shiga gaban ki?" Cike da takaicin abubuwan da ya gama faɗa mata ta ɗaga kai ta ce. "Na tabbata zan iya kawar da kowaye akan hanyar cimma muradi na,dan haka na baka wuƙa da nama akan aikata duk wani abu da ka ke ganin za ka iya koda a bayan auren ne kuwa." "Hajiya ba fa yau na saba jin amincewar mata ba irin wannan,amma da sun ga bala'i su zame." "Baka haɗu da shaiɗanun mata masu kalma ɗaya ba irina ne shi yasa suke guduwa." Munkaila na jin haka sai ya gyaɗa kai kawai sannan ya miƙe ya ce. "To Hajiya yaushe za a cika alƙawari na ne?" "Kar ka damu ban manta da kai ba,da anjima Jameelah za ta zo,na faɗa mata ta haɗo maka akwati biyar ina fatan sun yi maka? Zubewa Munkaila ya yi ya na ta godiya,daga ƙarshe ya tafi yana jaddada mata zai sama mata mafita kar ta saka damuwa a ranta. Hajiya Dada bata yi tunanin ta ga Malika ta ware tana cin abinci ba da wuri haka,sai ta tarar da ita ta na baiwa su Kubrah labarin Office ɗin Jubair,su Kubrah na yi mata ƙarin bayani akan wajen,daga ƙarshe bayan Hajiya ta shiga ne suka tattara suka koma cikin ɗakin Malika suka zauna suka ci gaba da hirar su. Da yamma liƙis bayan ƙarfe shida Jamila mai kaya ta iso a haɗaɗɗiyar motar ta,koda ta fito sai na ga mace mai tsananin gayu da ado da kwalliya,ga kyau ga diri irin na fulanin asali,baƙace ita irin baƙin nan mai kyau,taku take irin na mata masu aji ta gaishe da su Munkaila da Baba Mai gadi sannan ta buɗe bayan motar ta ta cewa Munkaila. "To ango sai azo a kwashe akwatuna a kai sashen Hajiya Uwa ko?" Cike da washe baki ya hau kwasar akwatuna yana saukewa ƙasa,Baba Mai gadi ne ke ta washe baki yana faɗin, "Ka duba ka ga yanda ake harkar arziƙi malam,fisabillahi da Kulu ta amincewa soyayya ta muma da ba ai mana wannan kaɓakin azziƙin ba?" "Ah to dai,kana namiji ace ka kasa tsara mace ai ka zama hotiho." A haka ya kwashe kayan tas ya kai sashen Uwa,ita kuwa Jamilah ta dauki ƙatuwar jakar da ta zo da ita ta rufe motar ta ta shige wajen Hajiya Dada. Tana shiga ta tarar da Hajiya zaune ta na kallon Sunnah TV,gaisawa suka yi sannan ta cire mayafinta ta zauna,gaishe da Hajiya Dada ta yi kafin ta fara fitar da kayan dake cikin jakarta,wayar Kubrah Hajiya ta kira ta bata umarnin su fito parlour gaba ɗayan su. Cike da hayaniya da sowa suka fito,idanun Jameelah ne suka sauka akan Malika da ke sanye da ƙananan kaya,kyawun yarinyar ne ya yi matuƙar ɗaukan hankalin ta,nan da nan ta ji tana ƙaunar ta,da kanta ta dinga zaɓarwa Malika manyan atampopi masu kyawun zane tana ajiyewa gaban ta,a haka saida ta zaɓa mata bakwai sannan ta ce. "Hajiya wannan ya kamata a ɗinka mata shadda mai kyau,a haɗa mata da manyan lesuna." "Kar ki damu Jamila,ai bana kakar ki ta sake yanke saƙa,ina so da kin koma gida ki yo min haɗin da ya fi kowanne da kika taɓa yi a baya,ina nufin bana akwati seti biyu zaki yo,bana son a saka ƙananan kaya,ina so a zuba manyan kaya da takalma da jaka masu tsada da suka amsa sunan su,idan kin gama ki tura masa kuɗin da aka kashe ki kawo kaya." Guɗa Jameelah ta saki sannan ta miƙe ta hau taka rawa ta na yiwa Hajiya Dada kirari,irin wannan harkar girman ne yasa ƙananan mutane ba su iya siyan kaya a wajen Jameelah,daga matan gwamnoni sai kwamishinoni irin su Jubair take siyarwa da kaya,sai kuma manyan ƴan kasuwan da suka ci suka tada kai,ita kanta motar da take hawa da gidan da take rayuwa ita da marayun yaranta abun kallo ne. Cike da farin ciki Jameelah ta ce. "To Hajiya ya za a yi da size ɗin undies kuma? Ko za a tura min ta WhatsApp?" "Kar ki damu,ki yi masa magana zai faɗa maki komai." "Godiya Jamilah ta yi,ta ga yanda yaran ke zaɓar kaya suna ajiyewa kamar basu san irin dukiyar da suke ɗauka ba,sai da kowannen su ya gama zaɓar abinda yake so aka kira magariba,anan Jameelah ta yi sallah ta ci abincin dare,sannan Jubair da ya dawo daga masallaci ya tura mata kuɗin ta ta tafi gida tana ta zabga godiya. Tinda rikicin ya faru Malika ke fushi da Papan nata,saboda be je ya lallasheta ba,tana ganin ya zauna ta miƙe da kayan ta a hannu ta shige ɗakin ta,murmushi kawai ya yi ya girgiza kai,dama ya san za a rina,wai an saci zanin mahaukaciya. ************************** Washegari da sassafe bayan kowa ya yi sallar asuba sun gama abubuwan da za su yi suka fita can babban kitchen ɗin dake bayan sashen Hajiya Dada. Kubrah kuwa murna kawai take bana ta samu wadda zata taya ta ayyukan girkin sati da suke yi duk Juma'a,cike da zumuɗi ta nufi sashen Hajiya Dada dan taso Malika..... *Tooo lallai ko Kubrah zan ga yanda za ai wannan girki. Gud luck.* [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE..... RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 16: Cike da girmamawa Jubair ya samu waje ya zauna ya dannawa Ammar kira,bata jima ta na ringing ba Ammar ya ɗauka,sallama suka yiwa junan su suka gaisa kafin Ammar ya ce. 'Ai ɗazu ina bacci ka tura min hotunan mutuniyar taka,a gaskiya ba ƙaramin kyau ta yi ba,ai da na san haka kayanmu na hausawa za su yi mata kyau da na dinga haɗawa da ita idan za a yiwa Samhah ɗinki.' "Humm gaskiya dai kam ta yi kyau,ammm ga Hajiya za ku yi magana." Jiki a sanyaye Jubair ya miƙawa Hajiya Dada dake kallon shi wayar,tana karɓa Ammar ya gaishe ta,tare da tambayar lafiyar jikinta,cikin murya mai rauni Hajiya Dada ta ce, "Alhamdulillah Ammar da sauƙi,ya Samhah da jiki-jikin nata? Ina fatan dai babu wata matsala ko?" Ba tare da Ammar ya amsa tambayar Hajiya Dada ba a ɗan rikice ya ce. 'Hajiya lafiya nake ganin kamar kin yi kuka? Broth me ya sami Hajiya?' Hawaye Hajiya ta ƙara sharewa kafin ta ce. "Ammar zaka iya tuna abinda muka tattauna da kai a lokacin da muka je wajen ku?" 'Kwarai zan iya tinawa Hajiya,ai ban taɓa mantawa da wannan abun alkhairin da kika yi min tayin shi ba,ni da Samhah duk mun amince,kai da kaya ai duk mallakar wuya ne Hajiya,ke kaɗai nake gani na ji daɗi a raina,ke ce uwata ke ce ubana,babu abinda za ki nema a waje na ban yi maki ba matsawar ba saɓon Allah bane,ni kai na ina sha'awar ace alaƙar mu ta zamo ta jini,ta haka ne kawai zamu zama ƴan'uwa na jini dani da ku.' "To alhamdulillahi tinda har yanzu kana nan akan bakan ka,nima ina nan akan baka na ban sauya ra'ayi ba,ina so yau ta zama ranar da za mu saka ranar auren Jubair da Malika,bana so watan nan ya wuce ba tare da an yi auren su ba." Cike da mamaki Jubair ke bin wayar shi da kallo,a hankali ya furta, "Dama kun yi maganar haɗa ni aure da Malika amma Ammar baka sanar da ni ba? Me yasa ka ɓoye min bayan bama ɓoyewa junan mu komai?" 'Broth ka fahimce ni,ban ɓoye maka hakan dan wani abu ba sai bisa umarnin Hajiya,ita ce ta buƙaci da kar na sanar da kai,har sai ta yiwa su Baffah Sale magana.' Ajiyar zuciya Jubair ya sauke,shi dai duk inda ta faɗi shane ai a wajen shi,amma dai ya yi mamakin yanda Ammar ya ɓoye masa wannan babban al'amarin duk kusancin dake tsakanin su,daga haka suka ci gaba da tattaunawa da tsara yanda komai zai tafi. Bayan sun yi sallama da Ammar da Samhah wadda itama ta tofa nata albarkacin bakin,ta ƙara da cewar,danginta kawai take gudun kar su ga wautar ta na aurawa Malika sa'an mahaifinta, Ammar ne ya kwantar mata da hankali ta hanyar nuna mata an yi auren da yafi wannan ma kuma an zauna lafiya,albarka kawai za su sanya wa lamarin,shikenan su ja baki su tsuke,sai bikin ya gabato daf ya rage sati guda sai su sanar da ƴan'uwanta,da wannan shawarar Samhah ta bar maganar tare da yin fatan alkhairi. Ta ɓangaren Malika kuwa da su Kubrah suna can suna jiran Jubair ya yi musu izinin yin party a bayan gidan da kawayen Kubrah,wanda yin hakan gaba ɗaya shawarar Malika ce,duk yanda Kubrah taso ta nuna mata Jubair ba zai amince ba ta ƙi yarda,a cewar ta su gwada tambaya,idan be amince ba sai su haƙura su yi a babban parlour,ita dai tana so ta yi nishaɗi ne kawai. Da yamma bayan Hajiya Dada ta zauna a wajen da take zama duk yammar Juma'a ta yi addu'o'in ta da salatin Annabi,sai su Kubrah suka zame suka bar sashenta,direct sashen Jubair suka nufa,a bakin ƙofar shiga Kubrah ta toge saboda basu saba shiga sashen mahaifin nasu ba sai dai idan kiran su akai,Malika kuwa kanta tsaye ta kutsa ciki bakinta ɗauke da sallama,tana shiga ta tarar da Ruƙayya na hawaye kanta a ƙasa ta na sauraren faɗan da Jubair ke yi mata kamar ba Ruƙyn shi da yake tsananin so ba,cikin zafin rai yake faɗin. "...akan me? Na faɗa maki ki je ki yi wanka amma kin zo min kina wari kamar na mushe,to ni gaskiya ba zan ɗauki wannan shashancin rashin kulawa da jikin ba,idan zaki kula da kan ki ki kula,idan ba zaki kula ba daga yau duk ranar girkin ki kiyi zaman ki a sashen ki ba sai kin zo ba na yafe." Cikin shan majina irin na masu kuka Ruƙayya ta share hancin ta ta miƙe tsaye da niyyar barin sashen nashi dan tsira da mutuncin ta,Malika ce ta tsaya a gaban Jubair ta kama ƙugu ta na kallon shi daga sama har ƙasa kafin ta ce. "Mommyn ka ke yi wa shouting haka Papa? What is wrong with you? Mommy bata cancanci haka a wajen ka ba even if she smells like a rotten egg, ba zaka iya haƙuri ka jurewa duk lalurar ta ba? Me yasa wanda ba musulmi ba sometimes suka fi riƙe matan su a lokacin daɗi d wuya? Marriage is a sacrifice,she has sacrificed a lot for you,why can't you do the same? Ka duba ka ga meye matsalar warin da ka ke complain akai kafin ka yi mata wulaƙanci har ka saka ta kuka haka,Mommy please don't cry,nima zan yi kuka." Rungume Malika Ruƙayya ta yi ta fashe da wani sabon kukan kafin ta fara shan majina ta na kallon Jubair da jikin shi ya yi sanyi da jin kalaman da Malika ta yi,tabbas bai kyauta ba,kuma shima yana jin rashin kyautawar da yake yi a ran shi,amma ya rasa dalilin da yasa yake jin shi kamar wani sabon mutum idan yana tare da Ruƙayya, kwata-kwata baya so ta raɓe shi,kallon su

Chapter 7 of 11