hanyar cikin gidan,Hajiya Dada ya gani tsaye ta na faɗin,
"Shigo da ita nan ƴar nema sangartacciyar yarinya kawai,daga tashin ta sallar asuba fa take wannan ihun kamar na zare mata rai,tinda muka zo banga ta ɗora goshin ta a ƙasa ba fa Jubair."
A hankali Jubair ya ɗago Malika da ke sharɓar kuka kamar wata jinjirar goye,cikin sigar lallashi ya ce.
"Kin yi sallah kuwa baby?"
Girgiza kai ta yi alamar ah ah,haɗe fuska Jubair ya yi kafin ya ce,
"Maza ki shiga ciki ki yi alwala ki yi sallah,ki tabbata kin rama duk sallolin da ake bin ki kafin na je masallaci na dawo,idan ba haka ba zamu ɓata dake,kina so mu ɓata?"
Girgiza kai ta sake yi cike da shagwaba,wani irin saƙo Malika ke aikawa Jubair wanda bai taɓa jin irin shi ba,nan take ya gane hakan na daga cikin aikin shaiɗan,domin kuwa a kullum yana ƙayatawa bawa duk wani abu da Allah ya haramta,cikin sauri Jubair ya raba Malika da jikin shi ya ja hannun ta suka shige cikin parlourn Hajiya Dada,harara Hajiyar ta bankawa Malika,ita kuma ta murguɗa mata baki,ƙwafa Hajiya ta yi kafin ta ce.
"Ze tafi ya barmu ai,na ga ƙaryar iskanci."
"Ai binshi zan yi,ko na shiga ɗaki na na kulle ba zaki sake shiga min ba,Papaaa ni bana son Hajiya na fi son Mommy ka maida ni wajen Mommy please."
Murmushi Jubair ya yi kafin ya ce,
"Ok sai kin yi sallah da safe idan na shigo sai in ga yanda za a yi."
"Ki tafi wajen abinda ya fi Mommy ma ba Mommy ba,ƴannema yaluwar banza."
A shagwabe Malika ta hau dira ƙafafun ta jikin ta ko ina na rawa ta ce,
"Paaapaa ka ganta ko?"
"Ya salam Malika stop it ! Wuce ki je ki yi sallah kafin mu ɓata."
Bathroom ta nufa tana sharar hawaye ita a dole an yi mata faɗa,tana shiga ta yi tsarki,a zato na zan ga bata iya alwala ba,sai na ga ta yi alwalar ta rass cikakkiya,sannan ta fito daga banɗakin,ma'ajiyar kayanta ta nufa ta janyo wata doguwar riga irin ta larabawa ta sanya tare da ɗan ƙaramin hijabi,parlour ta nufa sai ta samu Jubair ya tafi masallaci, Hajiya kuma ta tada sallah a wajen da take sallah a parlour,wajen Malika ta nufa itama ta tada sallah cike da natsuwa da kushu'i,Hajiya na idar da sallah ta tsaya ta na kallon ikon Allah,ƙwafa ta yi kafin ta ce,
"Ayyy Allah ! Dama kin iya sallar ki ke yi mata a sha ruwan tsuntsaye? Ai kuwa ni da ke ne a gidan nan,mu zuba ɗan halas ka fasa."
Malika bata bar yin sallah ba har sai da ta yi gaba ɗaya sallolin dake kanta sannan ta miƙe tare da tuje hijabin jikin ta,hannu ta ɗaga zata cire rigar jikin ta Hajiya ta ce,
"Yi haƙuri ki zauna mu yi wata magana da ni dake mai muhimmanci kin ji yarinyar Papan ta."
Ganin Hajiya Dada ta sakko ta dena yi mata faɗa ne ya sanya Malika samun waje ta zauna ta harɗe ƙafafun ta tana fuskantar Hajiya Dada...........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 10:
"Too ni wai yanzu da mai jego zan kira ki ko kuma UWAR MAGAJIN JUBAIR? Toh ! koma dai menene sunan ki ina yi maki barka da dawowa ƙasar ki ta gado lafiya,an tafi an barmu lafiya an same mu lafiya,abinda aka rasa kuma Allah ya jiƙan rai."
A rikice Kubrah,Ihsan da Mubeenah suka sauke idanun su akan mahaifiyarsu dake rizgar kukan da ta kasa riƙewa,cikin sauri ta bar parlourn ta shige ɗakinta,rai ɓace Kubrah ke bin Uwa da kallo tana hararar ta,dariya Uwa ta yi kafin ta ce,
"Allah sarki kar ki damu yarinya,ai tinda uwar ku ta iya haihuwar namiji shekarar nan,to ki bata shekara ɗaya zata sake haifo wani,kina son ganin hoton shi in nuna miki? Zo ki kalla Daddyn ku ya tura min,God the baby was so cuteee."
Hawaye Kubrah ta share ta wuce ɗakin da mahaifiyarta da kannen ta suka shige,ganin ɓacin rai a saman fuskokin Ruƙayya da yaranta ba ƙaramin faranta ran Uwa ya yi ba,cike da takun ƙasaita da yanga ta fita harabar gidan dan zuwa yiwa Hajiya Dada barka da dawowa,gayun da ta sha kaɗai ya isa ya nuna maka irin hutawar da Uwa ke yi a gidan. Ta na daf da shiga sashen Hajiya Dada Munkaila ya fito daga yi mata barka da dawowa,yanda yake sunkuyar da kai sai mutum ya rantse da Allah limamin wata unguwar ne,ido suka haɗa da Uwa ta zabga masa murmushin gamsuwa da aikin shi,shi ɗin ma murmishi ya yi mata tare da faɗin.
"Yanzu ma aka fara wasan Hajiya."
Ba tare da ta bashi amsar maganar shi ba, sai ta ce,
"Ka shigo sashena da safe ka karɓi tukuicin aikin ka."
Zubewa ya yi a wajen ya na zabga mata godiya,ba ta tsaya amsa godiyar shi ba ta wuce cikin sashen Hajiya Dada,ta na saka kanta cikin parlour'n ta ci wani wawan burki tare da ƙunduma wani irin ashar ɗin da babu wani mahaluƙi da ya taɓa yin irinsa a gidan. Cike da tsananin mamaki Hajiya Dada da Jubair suka ɗaga kai suna kallon ta,Malika kuwa da bata san ma'anar kalaman da ta furta ba tinda ta kalle ta sau ɗaya sai ta kauda kai ta sake gyara kwanciyar ta a jikin Jubair ta na latsa wayar ta. A harzuƙe Uwa ta karasa shiga parlourn ta janyo Malika ta wurgata gefe ta na sauke numfashi kamar mai ciwon hawan jini,cikin wata iriyar ƙwallar baƙin ciki Uwa ta ce,
"Wannan wacce ƴar iskar ce kuma ta zauna a jikin ka Jubair?"
A yatsine Malika ta kalli Uwa ta ce,
"Don't you ever call me that,suna na Queen, ohh sorry Malika,i am Ammar's daughter,idan baki sani ba ki sani,kar ki sake kirana da ƴar iska."
Cike da jin haushin abinda Uwa ta yi mata ta wuce ɗakin da aka shigar mata da kayan ta ta kulle ƙofar da ƙarfi har sai da su Jubair suka rintse idanun su,wata gwauruwar ajiyar zuciya Jubair ya sauke tare da faɗin.
"Hankalin ki ya kwanta kin ɓata mata rai daga zuwan ta,wai me yake damun ki ne Hafsat? Malikar ce baki sani ba ko kuma me?"
"Idan na san ta fa? Idan na san ta sai aka ce ta zo ta ruƙunƙume ka ta maƙale ka haka sai kace zata shige cikin ka?"
"She is just a child Hafsat,nawa Malikar take da zaki ɗaga hankali akan ta haka? Ke kin san a matsayin ƴa na ɗauke ta,haka zalika itama a matsayin uba ta ɗauke ni,a kaf duniyar nan bayan ke wa nake da shi a matsayin ɗan'uwa da ya wuce mahaifinta? Haba Hafsat ki dinga abu da hankali mana."
Cike da ɓacin rai Jubair ya miƙe ya bar sashem Hajiya Dada da ke bin su da kallo cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara,suna haɗa ido da Uwa sai ta sakar mata murmushi,Uwa kuwa zumɓura baki ta yi ta zauna a gefen Hajiya Dada ta ce.
"Yanzu dan Allah Hajiya menene laifi na dan na yi kishi akan Hammaah Jubair? Ina ce cikar soyayya kishi?"
"Ah ah cikar soyayya shine haƙuri,a koda yaushe idan kina so soyayyar ki ta yi nasara a zuciyar mijinki,ki sanya haƙuri,ki rage ƙorafi da bani-bani,zafin kishi da mahaukacin kishi na rusa soyayyar da aka gina ta cikin shekaru masu yawa,idan ba haka ba sai soyayyar da aka gina a ƙanƙanin lokaci ta yi mata zarra."
Hawaye ne suka fara zuba a kuncin Uwa kafin ta ce,
"Na riga da na san soyayyar Hammah Jubair ce ajali na watarana,ina son shi,ina kishin shi,ina tsananin ƙaunar shi,da so samu na ne kar wata ƴa mace ta kusance shi balle har aure ya haɗa su,da so samu na ne na kasance matar shi ni kaɗai har ƙarshen rayuwar mu."
Murmushi Hajiya Dada ta yi kafin ta ce.
"Wannan shine babban dalilin da ya sa kika ƙi zaman gidan mijin ki,kika baro ƴaƴan ki kika kaso auren ki dan kawai ki kasance da Jubair?"
"A yau ba zan ƙi amsa laifi na da kuka jima kuna tuhumata akai ba,na yarda na amince soyayyar Hammaah Jubair ce sanadiyyar rabuwata da gidan uban ƴaƴana,na baro yarana saboda na zama a ƙarƙashin kulawar mutumin da na fi so a duniya fiye da yanda nake son kai na,har yau idan na tuna kukan da Usman yake yi tare da yi min magiya akan kar na tafi na barsu abun na taɓa zuciyata,amma ya zan yi Hajiya? Zuciya ta da ruhina mallakin Jubair ne,idan ina so su ci gaba da rayuwa dole na sanya su cikin gangar jikin shi."
"Tirƙashi !"
Itace kalmar da Hajiya Dada ta furta tana kallon Uwa dake magana cikin wani irin yanayi na farin ciki da baƙin ciki,hawayen ta ta goge ta miƙe ta wuce sashen Jubair. Tana shiga ta tarar da shi yana waya da Ammar,bata ce masa komai ba ta wuce ɗakin shi ta haɗa masa ruwan wanka a kwamin wanka,tare da zuba duk wani kayan wanka da turarukan da Jubair ke amfani da su,maganin da Munkaila ya bata a ranar da ya sanar da ita rasuwar yaron Ruƙayya ta zaro ta zuba a cikin ruwan wankan ta juya da kyau sannan ta soke maganin ta fita,ko kallon inda take Jubair bai yi ba saboda har a wannan lokacin yana fushi da ita akan abinda ta aikata,cike da kirsa da kisisina Uwa ta isa gaban Jubair ta fara balle masa botiran rigar shi,idanunta ta zuba masa tana wani lumshe su tare da ware su a saman fuskar shi,cikin kashe murya da shagwaɓe ta Uwa ta ce,
"Haba Babyn Hafsy meye na ɓata rai haka? Kai ka san son da nake yi maka ne ya jawo nake tsananin kishin ka,sannan kar ka manta laifin ka ne fa har hakan ta faru,me yasa da muka yi waya da kai kafin ku dawo baka sanar dani zaku dawo tare da Malika ba? Sannan yarinyar nan na jima ban ganta ba,rabona da ita tin tana da shekara goma a duniya,yanzu na ganka da macen da ta fini tsawo da diri ka yi zaton zan kwantar da hankali na?"
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Jubair ya sauke,dan kuwa ya gano inda ya yi ba daidai ba,tabbas bai kyauta ba da bai sanar da Uwa zuwan da zai yi da Malika ba,dan haka sai kawai ya lakace mata hanci ya yi gaba ya na faɗin,
"To a min afuwa ba zan sake ba shikenan? And please ki kama girman ki,kar ki bari raini ya shiga tsakanin ki da yarinyar nan,tarbiyyarta daban da wadda kika saba gani."
Kyaɓe baki Uwa ta yi ta isa gaban dinning table ta hau buɗe abincin da Ubaida ta jera tin kafin su dawo. Sai da ta tabbatar da Jubair ya shiga wanka sannan ta buɗe miyar ta barbaɗa maganin da ta saka a ruwan wankan Jubair ta jujjuya ta mayar ta rufe. Waje ta samu a saman kujera a parlour ta kwanta tana kallo hankalin ta kwance.
Koda Jubair ya fito daga wanka ɗaure da towel sai ya duba inda kayan shi suke ya zaɓo wasu ƙananan riga da wando masu laushi ya sanya,turarukan shi masu sanyin ƙamshi da tsada ya fesa kafin ya ɗan shafa lotion sama-sama ya fita,cikin ranshi yake yabon Ruƙayya,domin kuwa da girkin ta ne da ya ga tarairaya fiye da yanda ta saba yi masa,shi yasa a duk sanda ya yi tafiya yafi so ya dawo a ranar girkinta dan ya samu kulawa ta musamman.
A kwance ya ganta a kujera ta na bacci,murmushi ya yi sannan ya gyara mata kwanciyarta ya wuce saman dinning domin ya ci abinci,a hankali ya furta,
"Yanzu fa saboda girkin nan da ta yi shine take jin ta gaji har bacci ya ɗauke ta,Hafsyna raguwa kenan,shi yasa Ruƙy ke burge ni,sam bata da ƙiwa da lalaci."
Tana kwance tana jin kalaman shi da suka sanya ta murmusawa,fatan ta bai wuce ya zauna ya ci abincin nan ba,dan kuwa tana sane ta kwanta tai shiru dan kar ya ce su ci tare. Sai da ya kammala cin abincin shi ne ya wuce ya wanke bakin shi sannan ya duƙa ya ɗauke ta ya wuce bedroom da ita.
Malika kuwa tinda ta shiga ɗaki take fushi akan abinda Uwa ta yi mata,ba ƙaramar ƙiyayya take yiwa Uwa ba,gaba ɗaya sai ta ji bata son ta dama ba a gidan take ba,tsaki ta ja kafin ta shiga banɗaki ta yi wanka ta sauya kayan ta daga dogon wando da T-shirt zuwa wasu ƙananan kaya masu matuƙar bayyana surar jiki,tana kammalawa ta haye gado ta buɗe laptop ɗin ta ta yi connecting da WiFi ɗin gidan da Jubair ya sanar da ita password ɗin tun shigar su parlourn Hajiya Dada,sai da komai ya daidaita ne sannan ta kira iyayen ta video call,sun jima suna hira tana basu labarin tafiyarta da irin daɗin da ta ji na ganin su Kubrah,nan take ta sanar da mahaifiyarta tana son Kubrah,tana so su zama ƙawaye,murmushi Samhah ta yi ta ce,
'Sai ki dinga yi mata kirki idan kina son ta zama ƙawar ki,mu a Nigeria ba a bullying ƙawaye,ba kuma a nuna musu sarauta,wannan sunan naki na Queen ajiye shi za ki yi ki zama Malikar ki,ta haka ne za ta zama ƙawar ki.'
Buɗe baki Malika ta yi kafin ta ce,
"Dama yin abota da mutanen Nigeria wahala ne da shi haka?"
Dariya sosai Ammar da Samhah suka dinga yi,suna tsaka da hira ne Hajiya Dada ta buɗe ƙofa ta ce,
"Idan kin gama ki zo ki ci abinci kar ya yi sanyi."
Tura baki Malika ta yi sannan ta ce,
"In dai wannan mayyar na nan ba zan fito ba,bana so na ƙara ganin ta she is so mean."
"Bata nan,ta tafi tun d'azu,maza ki gama ki zo ki ci abinci kin ji jikallena?"
Cike da shagwab'a ta ɗaga kai tare da rufe laptop ɗin ta ko sallama bata yiwa iyayenta ba ta bi bayan Hajiya Dada,ta na zuwa ta buɗe abincin ta ga yawanci carbohydrates ya fi yawa,tsaki ta yi sannan ta miƙe ta ce.
"Ni bana son wannan,salad nake so na ci."
"To zauna na kirawo Kulu ta haɗa maki,bayan shi akwai wani abu da kike so kuma?"
"Eh sai smoothy ɗin abarba da kankana a ɗan saka ayaba guda ɗaya a ciki."
Waya Hajiya Dada ta zaro ta kirawo Kulu tare da bata umarnin abinda zata haɗawa Malika,tana ajiye wayar Malika ta ce,
"Grandma ina su Kubrah suke? Tinda muka zo ban sake ganin su ba."
"Suna ɓangaren su,ko zaki je ne? Sai ki ci abincin ki ma a can ku yi hira."
Cike da zumuɗi Malika ta tashi zata tafi,Hajiya Dada ce ta yi mata kwatancen ɓangaren Ruƙayya,har zata fita Hajiya ta kalli shigar dake jikin ta,sai ta kira ta ta ce,
"Malika kin san da cewa kin dawo Nigeria ko? Mu ta nan ba a saka kaya irin wannan sun yi ƙanana da yawa,a ɗaki ake saka su inda babu wanda zai gan ki,dan haka ki je ki duba a kayan ki idan akwai irin dogon wandon da kika saka da za mu zo gwanda ki saka irin shi,amma wannan ya yi guntu da yawa."
Baki Malika ta zumɓura ba dan ta so ba ta koma ɗakinta ta sauya kayan jikin ta,duk da cewa su ɗin ma babu abinda suka ɓoye na daga shape ɗin ta,sun dai fi wanda ta cire tsaho. Cikin fara'a ta fita dan zuwa sashen Ruƙayya,tana fita ta ci karo da Munkaila da Ubaida na tsaye a ƙofar da zata kai mutum sashen Uwa suna hira,suna ganin ta suka tsaya cak suna binta da kallo. Tana wucewa Munkaila ya kalli Ubaida ya yi ƙasa da murya ya ce...........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 9:
Banda addu'a babu abinda Hajiya Dada ke yi ita da Jubair,ƙarshe waje ya samu ya zauna a gefen Hajiya Dada ya jingina kanshi a kafaɗarta tare da lumshe idanun shi,sun jima sosai a haka suna jira kafin nurses su buɗe ƙofa a gangaro da Ruƙayya a saman gado kamar matacciya,cikin azama Hajiya Dada da Jubair suka miƙe suka nufi inda Ruƙayya ke kwance kamar gawa, a rikice Jubair ke tambayar su dalilin da yasa ya ga matar shi a haka,kwantar masa da hankali suka yi kafin likita ya hau yi masa bayani cikin harshen turanci.
"Mr Jubair ka yi haƙuri da abinda zan sanar da kai yanzu,abu na farko shine duba da yanayin wahalar da matar ka ta sha kafin ta haihu,tana buƙatar hutu sosai kafin ta sake ɗaukan wani cikin,yana da kyau ku bi duk wata hanya da zata fiye maku sauƙi ku yi tsarin iyali na kimanin shekaru biyu zuwa uku, abu....."
"Dr. Dan Allah ka sanar dani me ya same ta naga bata motsi? Sannan ina abinda aka haifa yake? Na ji kuka sau ɗaya daga nan ban sake jin komai ba wai me yake faruwa ne?"
Hajiya Dada dake zaune a saman kujera a gefen Ruƙayya da ke sanye da bututun dake bata oxygen ce ta kalli Jubair ta share hawayen ta sannan ta ce,
"Dan Allah ka tambaye su me ya sami ƴar mutane ta ke a sanƙame kamar gawa? Sannan ina jika na dan kuwa na jiyo kukan shi."
Ɗaga kan da Hajiya Dada zata yi sai ta ga an shigo da jariri cikin wani irin yanayin da ya sanya ta dafe sandar ta zata tashi, da sauri Jubair ya kama ta ya taimaka mata yana rarraba idanu tsakanin likita da jinjirin dake naɗe kamar gawa. Banda kiran sunan Allah babu abinda Hajiya Dada da Jubair ke yi.
Lokacin da likita ya sanar da shi mutuwar kyakkyawan jaririn nasu ƙarfin imani da Allah ne ya sanya su kamewa ba tare da sun yi hargowa ko nuna karaya ba,hawaye wani na dukan wani haka suke zuba a kuncin Hajiya Dada.
Jubair ne ya karb'i kyakkyawan jaririn nasu fari tasss mai kama da iyayen shi yana kallo,ƙwallar idanun shi ya share ya sumbace shi kafin ya zaro wayar shi ya ɗauke shi hotuna da videos,yana gamawa sai ya miƙawa Hajiya Dada ta karɓe shi tare da fashewa da kuka mai tsananin cin rai,cikin kuka da sarƙewar kalamai Hajiya Dada ta ce,
"Allah..Allah..mun gode maka...Allah ka sa mai ceto ne,Ruƙayya Allah ya baki lafiya,shikenan mun rasa magaji Jubair, innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."
Haƙuri Jubair ya dinga baiwa Hajiya Dada kafin ya samu ya kira Ammar ya sanar da shi abinda ke faruwa. Suna nan ana ci gaba da kula da Ruƙayya Ammar ya iso shi da Malika da Samhah da ke ta kuka mai tsanani na tausayawa,ganin irin halin da Jubair ke ciki ne ya sanya Malika rungume shi ta fashe da kuka,cike da shagwab'a ta ce,
"Papa please don't cry, don't be sad ba gamu ba,har yanzu kana da ni da su Kubrah, ka dena damuwa please."
Murmushin karfin hali Jubair ya yi mata ya shafi kuncin ta kafin ya miƙe ya isa gaban gadon Ruƙayya dake ta sharar bacci,kallon ta yake yi cike da tausayawa,ta ci burin samarwa Hajiya Dada farin ciki ta hanyar haifar ɗa namiji,ta yi yawon asibitoci dan ta san gender ɗin abinda zata haifa sai dai Allah ya lulluɓe mata duk binciken da akai ba a gane gender ba,ashe Allah hakeem ya yi musu kyautar ɗa namiji ne,hamdala ya samu kanshi da yi a ƙalla yana saka rai watarana za a haifa masa ɗa namiji a gidan shi.
Sun jima zaune kafin daga baya duk su tafi gida a bar Jubair a wajenta koda zata tashi cikin dare ta yi tozali da shi,cemetery ɗin da ake binne musulmai Ammar ya nufa da jinjirin bayan an yi masa wanka an sallace shi aka binne shi.
Bayan kwana biyar da haihuwar Rukayya,Hajiya Dada ta ce su fara shirin komawa gida,washegari Jubair ya ɗauki Malika suka fita zaga gari dan yin bankwana da juna kamar yanda ya saba yi duk zuwan da yake yi,tinda suka fita tun safe basu dawo ba sai da dare,sun ci su sha a waje sun yi siyayya niƙi-niƙi kamar wanda za a buɗe ƙaramin shago,Ruƙayya ce ta ga yanda Malika ke ta ɓata rai kai da ka gani zaka san kaɗan take jira ta saka kukan rikici,murmushi ta yi kafin ta ce,
"Yanzu duk yawon nan da kuka sha bai ishe ki ba Queen? Lallai akwai aiki kenan ranar rabuwa."
Kamar an watsawa Malika kashin akwaki a kayan sallah haka ta buɗe baki da murya ta dinga rusa kuka,cikin tsananin takaicin halayyar ta Samhah ta hau yi mata faɗa,Ammar ne ya sakko daga bene yana bin Hajiya Dada da kallo,da ido ta yi masa alama kafin ya ƙarasa sakkowa ya zauna kusa da Malika,kama hannun ta ya yi ya zaunar da ita a gefen shi cikin sigar lallashi ya ce,
"Queen meye haka kike yi ne uhum? Nan da wasu watanni fa za ki cika 18 years,ke ba karamar yarinya bace kuma,yanzu ki yi shiru ki faɗa min me kike so ayi."
A hankali ta fara rage kukan ta ta koma gefen Jubair ta zauna,cike da shagwab'a ta ce,
"Ni ina son Papa ya zauna anan,bana son ya barni in jima ban gan shi ba."
Dariya Ruƙayya ta fashe da ita kafin ta yi saurin rufe baki tana ƙunshe dariyar,Jubair ne ya yi mata harar wasa kafin ya kalli Malika ya ce,
"Baby i can't stay here kin sani,ko kin manta da sauran ƴan'uwan ki dake gida Nigeria? Kin manta da muƙami na a garin mu? Ba zai yu na zauna anan ba."
Ammar ne ya miƙe ya zaro visa ya damƙa a hannun Malika sannan ya ce,
"To me zai hana ke tinda kin gama High School ɗinki ki bisu? Dama ba abinda kika jima ki na so bane wato zuwa Nigeria wajen Papa?"
Kallon Ammar ta yi cike da maɗaukakin farin ciki,sai ta maida kallon ta ga Jubair da ke cike da mamaki shima,Hajiya Dada kuwa kafe Malika ta yi da ido ta na jiran ta ji amsar botsararriyar jikar ta ta,babu zato ko tsammani suka ga Malika ta kurma uban ihu ta ɗale mahaifinta tana murna tare da sumbatar shi. A guje ta haye sama ta shige ɗakin ta ta kulle ƙofa,Jubair ne ya kalli Ammar ya ce,
"Yanzu ka tabbata ba zata yi rigima ba idan ta bi mu?"
Kafin Ammar ya amsa shi Hajiya Dada ta cafe maganar ta hanyar cewa,
"Ai kar ka wani damu da rikicin da za ta yi,dama na jima ina fatan yarinyar nan ta koma gida duba da yanayin tarbiyyar ƙasar nan ya sha banban da al'adu da ɗabi'unmu tare da addinin mu,dole ne idan muna son kare iyalan mu daga wuta kamar yanda Alkur'ani ya ce to fa sai mun tsaya tsayin daka mun haɗa ƙarfi da ƙarfe mun basu tarbiyya ta gari,Allah ya sani na yi iya bakin ƙoƙari na dan ganin tarbiyyar ku ta inganta,to fa ba zan tsaya na zuba ido da raina da lafiyata ita kaɗai ta taso a sangarce a lalace ba,a gaban idanun mu yarinyar nan ke rungume a ƙirjin wani namijin da ba muharramin ta ba,kuma bata ji cewar ta aikata ba daidai ba balle ta gyara,zaman ta a wajen mu zai sa a hankali,yau da gobe ta gane abinda take yi ba daidai bane."
Ammar ne ya amshe maganar da faɗin,
"Shi yasa muka haɗa baki da Hajiya Dada akan ta bi ku kawai,shaƙuwar dake tsakanin ku zata sauyata watarana."
Duk da cewa cikin zuciyar Samhah bata son yin nesa da ƴar ta amma kuma ta san cewa hakan shine mafita akan gurɓacewar da tarbiyyar Malika ta samu. Haka suka ci gaba da tattaunawa ba tare da Jubair ya ji menene ra'ayin Ruƙayya akan tafiya da Malika ba,ita kuwa Ruƙayya hirar ta take yi da Samhah,inda Samhah ke yi mata ƙarin bayani akan halayya da ɗabi'un Malika da ba kowa ne ya san tana da su ba.
Malika kuwa na ɗaki tana sanar da ƙawaye da abokan ta maganar tafiyar ta,tare da gayyatar su party kafin su tafi,Afdhal ba karamin shiga tashin hankali ya yi ba har sai da ya fara zuba mata larabci ba tare da ta san me yake faɗa ba. Farin cikin da Malika ke ciki ne ya mantar da ita kewar abokan nata da iyayenta,Nigeria da mutanen cikinta kawai take hangowa a idanun ta,daren ranar da ƙyar ta yi bacci saboda murna da haɗa kayan ta da za ta yi tafiya da su.
Washegari da yamma su Afdhal suka zo a mota suka ɗauki Malika dake sanye da wata siririya kuma yaloluwar rigar da za a kira da rigar shan iska,Hajiya Dada na kallon su bata tanka musu ba dan kuwa ta ƙudurta a