ranta wannan ne na ƙarshe,idan ta je Yola ta ga a gidan uban da zata dinga yin wannan shigar. Tinda suka tafi kuwa basu dawo da Malika ba sai ƙarfe huɗu na asuba,lokacin da ta dawo Jubair ya zaci zai ganta a buge kamar yanda yake ganin yaran turawa na yin party a shawu a bugu,sai ya ganta ragas cike da farin ciki da kyaututtukan da ƙawayen ta suka bata. Ammar ne ya dafa kafaɗar Jubair ya ce,
"Broth yana daga cikin godiyar da a kullum nake yiwa Allah da ya sa Malika bata shaye-shaye,ba kuma ta biyewa samari suna aikata zina da sunan soyayya,ita tana da ra'ayin sex after marriage ne,ka bar Malika da kafiya akan abinda take so,saka matsattsu da ƙananan kaya,yawan shiga cikin maza tare da taɓa jikin namiji kamar wani ƙawarta,sai ɗan banzan son yin party da jin kiɗa da rawa,shi yasa a kullum idan ina yi mata faɗa ranta ke ɓaci saboda a ganin ta ita bata aikata komai mara kyau."
Tinda Jubair ya ji babu wanda ya taɓa kusantar Malika kuma bata shan giya,sai ya ji wata iriyar natsuwa da kwanciyar hankali sun ziyarce shi,nan take ya maida hankali yana sauraron duk wani abu da take so da wanda bata so dan su kiyaye wajen kula da ita.
Washegari da misalin uku na rana jirgin su Jubair ya tashi daga Baltimore Washington international airport(BWI),Malika ko ƙwalla bata yi ba wai dan zata rabu da iyayen nata,sune ma suka rungume ta suna jin kamar idan ta tafi ba zasu sake ganinta ba.
Tafiyar awanni sha ɗaya da minti ashirin da biyar ce ta sauke su a filin jirgin garin Yolan Adamawa ta fulanin asali,banda baza idanu da firfita da hannu babu abinda Malika take yi,domin kuwa sun dawo ana tsananin zafi.
Ruƙayya ce ta juyar da fuskarta tare da share ƙwallar dake gangaro mata saboda tunawa da rasa ɗanta ƙwalli ɗaya namijin da suka ƙwallafawa rai daga ita har surukarta,tsakanin Jubair da Hajiya Dada babu wanda ya kula da halin da take ciki saboda suna can suna lallaɓa Queen Malika dake shagwab'ar zafi take ji.
A haka suka ja akwatinansu suka nufi inda motar su ke tsaye tana jiran su, suna isa driver ya fito ya durƙusa cike da murna yana gaishe da iyayen gidan nashi,jibgegiyar motar da aka zo ɗaukan su Malika ta kalla ta ce,
"Wooww what a nice ride Papa."
Murmushi Jubair ya yi kafin ya ce,
"Sai ma mun je gida zaki ga wasu,ina fatan su burge ki."
"Da gaske Papa?"
Ɗaga mata kai kawai ya yi yana murmushi,nan take Malika ta ja hannun shi suka wuce cikin mota suka zauna,Ruƙayya kuwa sai ja ƙafafun ta tana yaƙe ta bi bayan su ta yiwa kanta mazauni a gefen Hajiya Dada,duk inda suka wuce sai Jubair ya yiwa Malika bayani har suka isa gida.
Bayan mai gadi ya buɗe ƙofa sun shiga cikin gidan ne Malika ta buɗe baki tana jinjina kyawu da tsaruwar gidan,su Kubrah ne suka fito a guje suna ihun murna suka nufo Ruƙayya tare da tambayar ta ina ƙanwar su ko ƙanin su.
Munkailah ne ya biyo bayan Ubaida dake washe baki tana son ta ɗauki rahoton abinda aka haifa ta kai wa uwar ɗakin ta batare da ta san ta riga ta sanin me ya sami jariri ba,Kulu kuwa kaya ta fara shigarwa ta na faɗin,
"Bari na je na juye ruwan wankan jego Hajiya,sannun ku da dawowa lafiya."
Jiki babu ƙwari Ruƙayya ta wuce sashenta tare da yaran ta da ke ta tambayar ta abinda aka haifa,tana shiga parlourn sashenta ta durƙushe a tsakiyar wajen ta rushe da wani irin kuka mai tsananin ban tausayi,kuka ne da ta riƙe shi tun a lokacin da ta farka daga gadon asibiti aka bata tabbacin yaron ta ya koma har an binne shi,kwanan ta biyu bata san inda kanta yake ba balle ta rungume shi,banda hotuna da videos da Jubair ya yi da bata san ya kalar abinda ta haifa yake ba.
Tana tsaka da kuka ta ji ƙamshin turaren Uwa na dukan hancin ta,cikin sauri ta miƙe da niyyar ta shige bedroom ɗinta, dan kuwa bata son Uwa ta ganta a wannan yanayin,sai dai ta riga da ta makaro,domin kuwa tana miƙewa ta juya idanun ta suka sauka akan fuskar Uwa da ke bayyanar da wani irin shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni masu yawa........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE....
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
*A madadin ki siya ki yi sharing da ƙawayen ki,dan Allah ki basu shawarar su saya nima na samu taron zuwa makka. Na gode. Ga mai sha'awar siya a sambaɗa 500 a wannan account 0006366584 Ja'iz bank Hamida Sanusi Ahmad. Sai a tura shaidar biyar ta wannan No 09031416423.Ko kuma a saka katin waya na MTN a wannan No 09031416423.*
PAGE 13:
Duk irin kuka da magiyar da Malika take yiwa Jubair bai sa shi ya saurare ta ba balle ya buɗe mata ƙofa ta bi su Kubrah,ƙarshe ma sai ya buga motar shi ya wuce da ita office ɗin shi,kafin su isa ta gaji da kukan ta yi shiru sai ajiyar zuciya take yi,a kaikaice ya kalle ta ya ga yanda saman idanu da laɓɓanta suka yi jawur saboda kuka,tausayinta ne ya kama shi,cikin sanyin murya ya ce.
"Mu je na nuna maki office d'ina da kike cewa yana burge ki,ki yi haƙuri da na hana ki zuwa school ɗin su Kubrah,na maki alƙawarin zan haɗa mata party ta gayyato ƙawayenta gida,hakan ya yi miki?"
A shagwab'e ta ɗaga kai ta na wani shigewa cikin kujera,murmushi Jubair ya yi kafin ya ce.
"To ki yiwa Papan naki murmushi mana ko na ji daɗi a raina."
Murmushi ta yi sannan ta rufe bakin ta da mayafin da ta sanya,suna isa wasu ma'aikatan wajen suka taso cike da girmamawa suka buɗe masa mota ya fita,hannu ya miƙa musu suka gaisa ya ɗan tsaya suna magana,ganin haka ne ya sanya Malika fitowa ta isa inda yake ta jingina da shi tana ƙarewa wajen kallo,nuna musu ita ya yi ya gabatar da ita a matsayin ƴar shi kafin ya riƙe hannun ta su shige babban building ɗin.
Sai da ya zagaya da ita sashe-sashe da ke wajen kafin su tsaya a office ɗin shi,tana shiga ta kama baki ta na yaba kyawun wajen,ita dai garin Yola ya yi mata sosai,jinta take yi kamar har yanzu a turai take,wayarta ta ciro daga cikin siririyar jakar ta ta hau ɗaukan hotuna tare da yin videos kala-kala. Kallon Jubair ta yi sannan ta ce.
"Papa taho mu yi video please."
Rungumo shi ta yi kamar wani abokin ta ta hau yi musu video tana ta ƙyalƙyala dariya,yanayin yanda take taɓa sassan jikin shi ba tare da ta damu ba abun ya fara damun Jubair,a hankali ya janye ta a jikin shi ya ce.
"Baby zauna a can na yi maki hoto sai a haɗa da na ɗazu a turawa Dad ɗin ki ko?"
Cike da murna ta je kujerar shi ta zauna tana wani juyawa,ba ƙaramin kyau ta yiwa Jubair ba da ya maida hankali wajen ɗaukan ta a hotuna da videos. A hankali ya janye wayar ya ajiye ta a saman table ɗin dake gaban shi ya ce.
"Kina so ki je gida yanzu na haɗa ki da driver ya kai ki ko zaki zauna anan in je in yi wasu ayyukan in dawo?"
"Papa zan zauna ka gama abinda za ka yi mu koma gida tare."
"Kin tabbata?"
"Yes Papa."
"Ok tom Idan kina jin yunwa ki buɗe fridge ɗin can zaki samu wani abun ki ci kafin mu je gida,in kuma bacci zaki yi ki tafi can ga kujeru can ki kwanta ko ki kunna kallo ki yi,i just don't want you to come out."
Nan take Jubair ya ɗauki wayar shi ya kira PA ɗin shi,suna nan zaune ba jimawa ya shigo,sai da ya sake gaishe da Jubair sannan ya fara karanto masa abubuwan da zai yi a ranar wanda za su fara ne da meeting da misalin ƙarfe tara.
Agogo Jubair ya kalla ya miƙe tsaye ya ce,
"Is almost time,muje ko?"
Sashen da Malika take ya kalla ya ga ta kunna kallo tana yi hankalin ta kwance,gaba ya yi PA ɗin shi na take masa baya suka fita daga office ɗin,har Jubair ya yi gaba ya koma baya ya sanyawa ƙofar key sannan suka wuce.
Malika kuwa na can na kallo har 11am na safe Jubair be dawo ba, yunwa ta fara ji sai ta miƙe ta buɗe fridge ɗin da ya nuna mata,wani cake ta gani an yanka an rage,sai fresh milk da grapes da Apple,kwasar abincin ta dinga yi tana lodewa a saman table ɗin dake girke a tsakiyar inda aka jera kujeru a office ɗin,zama ta yi ta hau ci tana ci gaba da kallon ta hankali kwance. Tana kammalawa ta hau baza hamma,babu wani jinkiri ta kwanta a doguwar kujera ta fara bacci hankali kwance.
Tinda Jubair ya tafi bai dawo ba suna can suna aiki,daga wannan taro su faɗa wancan,hankalin shi gaba ɗaya ya tafi wajen Malika,tunanin kiran wayar ta ya yi sai ya tuna bata da sim card da WiFi take amfani,tsaki ya ɗan ja ya duba agogon shi,ƙarfe ɗaya da rabi na rana ya yi,cikin zafin nama ya miƙe ya ce.
"Mu je mu yi sallah mu dawo ko?"
Yana fita ya nufi office ɗin shi cikin sauri,ko da ya buɗe ƙofa kwance ya ganta ta dunƙule waje ɗaya saboda sanyin Ac da ya mata yawa ta na ta sharar baccin ta,rage ƙarfin AC ya yi kafin ya shiga banɗaki ya yi alwala ya sake rufe ta a office ɗin ya wuce masallaci.
Tinda ya dawo ya koma wajen abokan aikin shi,be dawo ba sai uku da rabi,a zaune ya tarar da ita ta na shirin yin kuka,ta na ganin shi ta miƙe ta nufe shi ta rungume shi,cikin muryar shagwab'arta da bata ko gajiya ta ce.
"I am hungry Papa."
"Ok mu je gida ko? Ai kin yi ƙoƙari, i hope kin yi sallah?"
"Ban yi ba,yanzu na tashi daga bacci fa."
Ɗaukan jakar ta da mayafin ta tayi,sannan ta riƙe ɗankwalinta da ya tuje a hannu,Jubair na kallon ta ya ce.
"A haka za mu tafi Baby?"
Kallon jikinta ta yi daga sama har ƙasa bata ga wata matsala ba,murmushi ya yi sannan ya isa gaban ta ya karɓi ɗankwalin ya ɗaura mata ya yafa mata mayafin ta,kallon shi ta yi da mamaki ta ce.
"Laaa Papa a ina ka iya d'aura ɗankwalin mata?"
Nan take ya tuna da rayuwar soyayya da ƙaunar da suka zuba shi da Ruƙayya,madadin ya ji farin ciki kamar yanda yake ji a baya idan ya tuna da ita,sai ya samu kanshi da jin wani matsanancin haushinta,tsaki ya ɗan ja kafin ya ce,
"Dogon labari ne,mu je gida ko kin dena jin yunwar na koma bakin aikina?"
Cikin sauri ta saki hannun shi ta yi gaba, buɗe ƙofar ya yi suka jera har suka isa bakin mota suka shiga. Lokacin da suka isa gida Uwa ta gama cika ta batse sakamakon labarin da su Kubrah suka bayar na abinda ya faru a makarantar su tsakanin Jubair Malika da wani yayan ƙawar Kubrah.
Suna fita daga mota Malika ta wuce sashen Hajiya Dada ta wuce ɗaki,wanka ta fara yi kafin ta yi alwala ta rama sallolin dake kanta,tinawa da alƙawarin da taiwa Hajiya na dena tara sallah ne ya sanya ta jin babu daɗi,a hankali ta furta.
"To ai Allah muke yiwa sallah, shi na saɓawa ba Hajiya Dada ba,itan ta tunatar dani abinda bana yi ne,Allah na tuba ba zan sake ba Allah."
Ta faɗa ta na matso ƙwalla,Kulu ce ta shiga ɗakin ta ce.
"Wai ki zo in ji Hajiya Dada ki ci abinci."
Zillo Malika ta yi ta yi wurgi da mayafin rigar da take sallah da shi ta miƙe ta yi waje,Kulu ce ta tsaya ta kama haɓa ta ce
"Ikon Allah,da alama dai yarinyar nan bata rabo da ci,acici kajin binni kenan,haka fa ɗazu da safe ta tashi da abincin da nai wa Hajiya Ruƙayya se da na sake dafa wani,to Allah yasa ta so abincin Hajiya Dada,dan na ga duk abinda Hajiya Ruƙayya ke so itama shi take so."
Kulu na nan tsaye ta ji Malika ta k'wala mata kira da karfi, cikin azama ta isa parlourn ta ce.
"Gani ƴar gidan Papa akwai abinda kike so ne?"
"Me kika dafawa Mommy please? Ko me kika dafa mata ni shi zan ci,bana son wannan swallow ɗin."
"Ikon Allah menene kuma wallo? Ai ni tuwon alkama na yi da miyar taushe ba wallo ba."
"Whatever,bana son shi."
Hajiya Dada ce ta ce,
"To tashi ki je can wajen Mommyn taku,bana son saka babba aiki kamar wata sa'ar ki,mu nan ba haka muke lamuran mu ba,miƙe ki je can ku ƙarata,dama su Kubrah sai yawon zuwa neman ki suke yi."
Babu musu kuwa Malika ta shiga ɗakinta ta sauya kayan jikin ta zuwa ƙananan kaya,sai dai wannan karon suna da ɗan mutuncin su,tinda ta kula Hajiya Dada bata son ta saka ƙananan kayan sosai,shi yasa ta ke ƙoƙarin rage sakawar.
Tana fita ta ji hayaniya sama-sama daga sashen Papan nata,ɗan tsayawa ta yi ta na tambayar Kulu can ɗin ina ne? Kulu ce ta ɗan kalle ta da mamakin tambayar ta ta,dan kuwa yaran gidanma ba sa zuwa,iyayen ne kawai ke bidirin su a wajen,sai dai idan shi Jubair ne yaso yana zuwa sashen matan nashi lokaci zuwa lokaci,dan haka bata ga dalilin da zai sa Malika ta tambaya ba,shiru ta yi bata sake magana ba har sai da Malika ta sake tambayar ta ina ne can,sannan ta ce.
"Sashen Alhaji ne,amma yara basa...."
Kafin Kulu ta rufe bakin ta Malika ta sa kai ta nufi sashen Jubair,ta na zuwa babu wani ɓata lokaci ta sa hannu ta buɗe ta shige,tsaye ta ga Uwa a kan Jubair dake turawa Ammar hotuna da videos ɗin Malika tana ta zabga masa masifa,ganin haka ne ya sanya Malika zuwa ta tsaya a tsakiyar su ta kalli cikin idanun Uwa ta ce.
"Ki dena yi masa shouting,sannan ki dena kira na yarinya mara tarbiyya,na sani ni ban taso a inda ake practicing addini da al'ada ba,amma daidai misali ina kwatantawa,idan ni da na taso a cikin mutanen da ba namu ba na koyo d'agawa na gaba da ni murya,to ke a ina kika koyi ɗagawa mijinki murya?"
Kalaman Malika ba ƙaramin dariya suka baiwa Jubair ba,dan haka bai ɓata lokaci ba wajen fashewa da dariya ya ce.
"Very good Baby tambayar min ita,yanzu dan Allah baki ji kunya ba Hafsat? Yarinya karama ƴar cikin ki ta zo tana yi maki irin waɗannan maganganun?"
Cike da tsananin fushi Uwa ta ja hannun Malika ta kai ta bakin ƙofar fita daga sashen,kafin ta ce
"Fita ki bar nan, wannan wajen ko yaran gidan basa shigar shi balle ke karere,and for your information,idan ina magana da mijina ba a shiga,ki kiyaye ni kar ki yi zaton ƙaramin karuwancin da kike yi a turai zai yi tasiri akan mijina,kin yi kaɗan."
"Hafsat !"
Jubair ya kira sunan Hafsat a cikin tsananin fushin da bata taɓa ganin ya yi ba,kafin ya ci gaba da cewa.
"Ki na da hankali kuwa? Malikar kike dangantawa da Karuwa?"
A daidai wannan lokacin ne Hajiya Dada ta shiga,dan kuwa Kulu na ganin Malika ta shiga sashen Jubair ta tsaya cike da tashin hankali,sanda ta jiyo hayaniya da musayar yawu tsakanin Hafsat da Malika kuwa da gudu ta shiga wajen Hajiya Dada ta taso ta,Malika na tsaye ta na latsar waya tana nemo ma'anar kalmar Karuwa a Google,kafin Hajiya Dada ta yi magana Malika ta fashe da kuka ta na faɗin.
"Ni ba PROSTITUTE bace, Papa ka ji tana kira na prostitute ko? Na tsane ki, bana son ki."
Da gudu Malika ta bar sashen Jubair ta wuce wajen Ruƙayya ta na gunjin kuka,Hajiya Dada ce ta maida kallon ta wajen Uwa da babu ɗigon nadama a kan abinda ta yi ta ce.
"Kin san me? Tinda kina ganin zaki iya faɗa da kishi da Malika,to ni kuma gobe idan ƙannen mahaifin shi sun zo zamu tattauna a tsakanin mu Jubair zai auri Malika kamar yanda na yi sanadiyyar ya aure ki,kin ga sai sunan ta ya tashi daga KARUWA ya koma MATAR JUBAIR."...........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE....
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 12:
"Me yasa kike wasa da sallah?"
Shine tambayar da Hajiya Dada ta yiwa Malika,cikin tura baki irin na shagwaɓɓun yaran nan Malika ta ce.
"Ni bana wasa da sallah,kawai idan bani da time ne nake bari sai sanda na zama less busy sai na yi,ai Allah ma yace babu matsawa a addini ko?"
Murmushi Hajiya Dada ta yi irin na manya kafin ta ce.
"Malika manya,ga sani ga take sani,to baki san inda Allah ya ce mu yi sallah akan lokaci ba? Sannan ya ce azaba mai tsanani zata tabbata akan wanda basu yin sallah akan lokaci? Mu ma bar wannan maganar Malika kin san menene dalilin da Allah ya sa ya halicci mutum da aljan kuwa?"
"Na sani mana,dan su bauta masa ne shi kaɗai,ai ni bana shirka."
"To alhamdulillahi,Allah ya ƙara tsare ki daga aikata shirka,amma ke da kan ki kin faɗa,Allah ya halicci mutum da aljan ne domin su bauta masa shi kaɗai ba tare da sun haɗa shi da wani ba a wajen bautar,to kin ga kenan duk wani aiki ko wasa ko party da zaki yi,yana da kyau ki fara gabatar da sallahr ki,sai ya zamana su ne zaki dinga yi idan kina less busy ɗin ba wai sallah ce zata jira ba,bari na watsa maki turancin nima,dan ki san nima na ɗan tsinci abinda na tsinta a zamana da ƴan boko."
Dariya sosai Malika ta yi,kafin a hankali ta ja jikin ta ta kwanta a saman ƙafafun Hajiya Dada,hannayen Hajiya ta kama tana wasa da su,a hankali ta ce,
"A can gida Baltimore bana nunawa friends ɗina ni musulma ce shi yasa ba kowa ya san addinina ba sai ƙawayena na kusa,a can ana ƙyamatar musulmi sosai da baƙar fata,Afdhal shine wanda ya nuna min kuskuren da nake yi,Afdhal baya tsoron bayyana addinin shi ko ya tsaya ya kare shi,yana ƙoƙari sosai akai na,shi yasa Dad ke son shi,a hankali nima na fara jin son shi cikin rai na,and now gani na dawo Nigeria,na san shine dalilin da yasa jiya ya ƙi amsa call ɗina,i missed him so much,i think ba zan wani jima ba zan koma gida,na miki alƙawari daga yau zan dinga yin sallah akan lokacin ta."
A hankali Hajiya Dada ta zame hannun ta guda ɗaya ta fara shafa kan Malika dake lumshe ido kamar mai jin bacci,cikin sanyin murya Hajiya ta ce,
"Allah ya baki ikon tsaida sallah akan lokaci Malika,Allah yasa kuma ki yi domin shi,lallai zuciyar ki na son Afdhal da yawa tinda har kike maganar shi haka,sai dai ina yi maki jajen rabuwa da shi,rabuwa ta har abada kuwa,dan kuwa ba zaki sake ganin shi ba sai bayan igiyar aure ta hau kan ki."
Cikin baccin da Malika ta fara yi a saman cinyar Hajiya Dada ta yi juyi tana fuskantar Hajiyar tare da zagaye hannun ta a ƙugun Hajiya Dada ta ce,
"Ah ah ni ba zan yi aure ba sai Papa ya zaɓo min miji me kyau kamar shi,Papa ya ce miji na ba daga nan duniyar yake ba,miji na me kyau ne irina."
Murmushi Hajiya Dada ta yi kafin ta jingina da kujerar da take kusa da ita,a haka itama bacci mai daɗi ya ɗauke ta.
Suna nan zaune gari ya waye sosai,Kubrah ce da su Ihsan suka nufi sashen Hajiya Dada domin gaishe ta,cike da zumuɗi Kubrah ke son ta gayyaci Malika zuwa makarantar su,domin kuwa ranar suke yin shagalin kammala sakandire,a hanya suka haɗu da Jubair da Uwa suma suna tafe dan zuwa wajen Hajiya Dada,sai da suka gaishe da mahaifin nasu suka sa kai za su wuce,cike da kisisina Uwa ta ce,
"Ah ah kubrah yau laifin me na yi muku da ba za ku gaishe ni ba? Hammaah kana ganin su fa ko ka yi musu magana akan abinda suka yi?"
Ɗaga kan shi ya yi daga latsa wayar da yake yi ya ce,
"Ke Kubrah me yake faruwa baku gaida Auntyn ku ba? Oya maza ku gaishe ta bana son na sake ganin irin haka ta faru."
Cike da ɓata rai suka gaishe ta,amsawa ta yi tana wani irin murmishi,kafin su kai ga shiga parlour Ruƙayya ta fito cikin adon ta kamar yanda ta saba,kallo ɗaya Jubair ya yi mata ya ɗauke kai,nan take Uwa ta saki wani shu'umin murmushi ta riƙe hannun shi suka shige sashen Hajiya Dada,mamakin halin ko in kulan da Jubair ya yi da Ruƙayya ne ya kama su Kubrah dake jiran ta ƙarasa su shiga tare,Ruƙayya kuwa kauda kanta ta yi daga kallon wajen da Jubair ya yi ta bi bayan yaran ta.
Yanayin da Jubair ya tarar da Hajiya Dada da Malika ba ƙaramin burge shi ya yi ba,nan take ya saita camera ɗin wayar shi ya hau yi musu hoto,a ƙufule Uwa ta ce,
"Meye haka zaka wani hau ɗaukan su hoto? Ke ! Ke ! Dalla malama tashi ki gyara kwanciyar ki ko ki wuce ɗaki ki kwanta."
Cikin magagin bacci Malika ta sake ƙanƙame Hajiya Dada tana surutan da ba a ganewa,Hajiya ce ta farka ta hau miƙa tana salati,dukan bayan Malika ta yi ta ce,
"Ke ni ɗaga ni duk kin jibge min nauyi, ohhh Allah ka taimake ni ƙuguna ya ƙara moruwa a gidan nan,gashi gobe muna da girkin Juma'a."
Dariya su Kubrah suka yi kafin su gaishe da Hajiya,amsawa ta yi tana bin Kubrah da ta sha wankan ƙananan kaya da kallo,ƙanƙance ido ta yi ta ce,
"Wannan kuma daga ina? Ina zaki je a haka?"
"Hajiya yau ne fa za a yi partyn kammala makarantarmu."
"Shine kuma ki kai wannan shigar? To ita kanta uwar tsirarar yau zan kira Jamila ta kawo kaya a sai mata,a yau za a kaiwa Salman ya ɗinka mata wasu,saura an kawo daga baya,maza ki wuce ki saka kaya da kyau,ku kuma kuna kallon ta ta saka wannan kayan kamar wadda ta haɗa dangi da yahudawa."
Malika na jin haka ta zumɓura bakin ta da already ya yi tudu ya yi jawur saboda tashin ta daga bacci kenan,a hankali ta murguɗa baki zata miƙe,cikin zafin nama Hajiya Dada ta fizgi hannun ta ta maida ita ta zauna a gaban ta,bakin ta kama ta murɗa kaɗan sannan ta ce,
"Daga yau idan ina maki magana kika turan baki gaba ya tsuliyar biri se na yanke miki shi,mu ta nan ba a raina manya,ko baki san hakan raini bane?"
Ƙara Malika ta ƙwalla,ta fizge hannun ta ta tafi wajen Jubair tana nuna masa Hajiya Dada,wani takaici ne ya kama Uwa ta tura ta gefe tana zabga mata harara,a hasale ta nuna Malika da yatsa ta ce.
"Ke wai baki san kin girma bane ba ko ina ya kamata kina jinginuwa ba? Ko a gidan ku ba a koya maki tarbiyya bane?"
"Eh ɗin ba a koya min ba,ke ai a gidan ku masifa da shiga abinda babu ruwan ki aka koya miki."
"Malika ya isa haka muje ki shirya ki bi Kubrah,kin ga sai ki ga gari ma ko? Ko kuna so na kai ku da kai na?"
Cike da murna suka hau ihu suna faɗin.
"Eh Daddy ka kai mu please,dama ka jima baka kaimu makaranta da kanka ba."
A guje Malika ta wuce ɗakin ta tana murna,Hajiya Dada ce ta k'wala mata kira ta ce.
"Kar ki sake ki saka mana kayan yahudawa a gidan nan,ki saka irin wannan rigar ta jikin ki,idan baki da wata ki je Ruƙayya zata baki kaya tinda kusan girman jikin ku ɗaya."
Da jin haka sai Malika ta tsaya a gaban Rukayya ta na washe baki ta ce,
"Mommy please ki bani irin kayan ki please ina son su."
"Kar ki damu Babyn Papa,ku je can ki yi wanka ki karya,idan na zo zan baki ki zaɓi wanda kike so ok?"
Hannu suka riƙe ita da Kubrah suna hira suka bar sashen Hajiya Dada,Ruƙayya ce ta duƙa ta gaishe da surukar tasu kafin ta gaishe da Jubair,kanshi na kallon wayar shi ya amsa mata ba tare da ya ɗaga kan shi ba,mamakin sauyin halin da ta samu daga wajen Jubair ne ya sanya ta miƙewa da sauri za ta bar wajen,Uwa ce ta kashe murya ta ce.
"Mai jego ya ruwan zafi? To Allah ya ƙara lafiya."
Yaƙe Ruƙayya ta yi ta ce,
"Amin ya Allah,da fatan kun tashi lafiya."
"Rass muka tashi kamar yanda kika ganewa idanun ki."
"Uhumm to Alhamdulillahi,ai haka ake so."
"Ahayyee idan ma dai ba haka mutum ya so ba,to gamu