Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE.... RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH RUBUTAWA :HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️ Wannan littafin na kuɗi ne,idan kina son karantawa har ƙarshe biya #500 ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi ko kuma 0006366584 Ja'iz Bank Hamidatu Sanusi Ahmad. Ki tura shaidar biya ta,09031416423. Mutanen Niger kuma za ku iya biya ta 96988833 Soueba sani idi,sai ku tura shaidar biya ta 09031416423. *Barkan ku da sallah mutanen k'warai masu albarka. Mun godewa Allah da ya sa muna cikin masu rai da lafiya,Allah ya bamu ikon yin amfani da su yanda ya dace.* 31/3/2025. PAGE 1: Tafe take tana bin kowanne lungu da saƙo na gidan da kallo kamar tsofaffin dubagarin da aka yi a zamanin baya. Tabaran idanunta ta cire ta kalli Kulu dake duƙe tana goge uniform ɗin Kubrah wadda ta baro kwance a saman kujera ta na yin assignment ɗin ta da bata samu damar yi ba a daren jiya,ƙwafa ta yi sannan ta ce, "Ke Kulu ban hana ki yiwa sangartattun yaran nan guga ko wanki ba? Akan wanne dalili ɗana ya ɗauke ki aikin wanke-wanke da shara sai ki dinga tsallake hurumin ki kina shiga abinda babu ruwan ki?" Nan take jikin Kulu ya ɗauki rawa kamar mai jin sanyi, kanta duƙe baki na makyarkyata ta ce, "Hajiya Dada am dan Allah ki yi haƙuri,Kubrar ce babu lafiya jiya ta kwana da zazzaɓi shi yasa bata samu damar wanke tufafin nata ba balle ta goge,amma inshaa Allahu daga yau zan dinga tsayawa a matsayi na." Cikin yatsina fuska Hajiya Dada ta ce, "Da dai ya fiye maki,idan kuma ba haka ba zan sa kema a kore ki a samo wata,babu wanda ya isa ina koyawa jikokina tarbiyyar da aka gaza basu ya rusa min." Kafin Hajiya Dada ta sake yin magana Kulu ta tattare kayan da take gogewa ta nufi ƙofar da zata sada ta da ɓangaren Ruƙayya,ta na shiga ta tarar da Kubrah zaune ta na shan tea da soyayyan ƙwai,da dukkan alamu ta yi wanka ta shirya kayan ta kawai take jira akai mata ta sanya,ganin Kulu riƙe da kayan makarantar ta rabi a goge rabi babu guga ne ya sanya ta miƙewa baki cike da ƙwai ta ce, "Baaba Kulu ina gugar kuma?" Juyawa Kulu ta yi tana kallon hanyar shiga parlourn ta kama leɓen ta na ƙasa ta haɗe da na sama ta riƙe da yatsun ta biyu,yin hakan da ta yi kaɗai ya gama isarwa da Kubrah saƙon ta,zumɓura baki Kubrah ta yi kafin ta karɓi kayan ta a zuciye ta wuce ɗakinta ta fara goge su da kanta. Zuciyar ta cike take da maganganu amma ta sani sarai yin maganarta ta daidai yake da ciwa mahaifiyarta mutunci da Hajiya Dada za ta yi,dan haka bakin ta ta tsuke ta kammala gugar ta sanya kayanta ta leƙa ɗakin ƙannen ta guda biyu Ihsan da Mubeenah,cikin ɗaga murya ta ce musu, "Wato ba za ku yi sauri ku fito mu tafi ba har sai Hajiya Dada ta shigo ta tarar da ku ko?" Cikin sauri ƴan matan da ba za su wuce shekaru sha uku da sha ɗaya ba suka fito suna rataya jakar su a kafaɗun su,a tare suka bar sashen nasu suka wuce sashen Hajiya Dada,zaune suka tarar da ita a saman tabarmar da ake ajiye mata kayan karin kumallon ta tana ta juya farfesun kayan cikin da ta zuba dan karyawa tana mitar an tsula masa ruwa. Gaishe ta su Kubrah suka yi kafin su yi mata sallama za su wuce makaranta,kamar ba ita ce ta gama masifa da muzurai ba haka ta sake musu fuska suka gaisa sannan ta yi musu addu'ar dawowa lafiya tare da samun ilimi mai albarka,sai da suka miƙe za su tafi Hajiya Dada ta kirawo Kubrah ta ce, "Wato Kubrah jiya saboda ɗan aikin girkin da na saka ki da yamma,shine ya sa ki kwana da zazzaɓi har kika baiwa Kulu wanki da guga ko? Ki kiyaye ni fa Kubrah,kar na sake ganin haka ta faru daga yau,ni ba zan lamunci sakarci da sangarta ba,tinda iyayen ku sun kasa haifar min jika namiji ba zai yu ku kuma ku zama malalata ba,wuce ki bani waje kar ku makara." Duƙar da kai Kubrah ta yi kafin ta sake yiwa Hajiya Dada sallama ta bar sashen nata rai a ɓace,a hankali ta furta, "Wai girkin mutum goma sha takwas ne ɗan aiki a wajen ta,da alama tsohuwar nan so take ta nakasa wata gaɓar ta jiki na kafin rai ya yi halin shi a kan ta." Sashen mahaifinsu ta bi ƙannen ta suka gaishe shi sannan suka yi masa sallama suka wuce wajen da motocin gidan ke ajiye. Drivern dake kai su makaranta ne ya taso da sauri yana washe baki,gaida shi suka yi kafin su rankaya gaba ɗaya su shiga haɗaɗɗiyar motar tasu su wuce makaranta. ********************** Cikin shiga ta alfarma wadda ke nuni da irin dukiyar da ahalin Alhaji Jubair Ɗan Fullo ke da ita Ruƙayya ta fito dan zuwa gaishe da Hajiya Dada wadda take a matsayin surukar su. Tana shiga ta tarar da Uwa zaune a saman kujerar dake nesa da ta Hajiya Dada suna gaisawa,cike da murmushi ta ƙarasa shiga ta samu waje ta ɗan duƙa ta gaishe da Hajiya Dada,babu yabo babu fallasa Hajiya Dada ta amsa gaisuwar ta kafin ta ce, "Maza samu waje ki zauna dama ina da magana daku dikan ku,ke Uwa ban san me kike nufi ba da har yau kin kasa maida hankali ki yi abinda ya sa na aurawa ɗana ke,shekaru fa tafiya suke yi,ku bar ganin Allah ya yi maku kyawun ƙira da wadata kuna nan kamar yara kuna lokacin ku,nan gaba kaɗan haihuwa zata tsaya maku,to idan baku kama jiki kun haifawa ɗana magaji ba sai yaushe za ku yi hakan?" A yatsine Uwa ta kalli Hajiya Dada ta ce, "Hajiya Dada ni dai dan Allah ki dena ci min mutunci a gaban kishiya,kullum kika tashi magana sai kin goranta min dalilin auro ni da kika sa Alhaji ya yi,haihuwa ai nufin Allah ne ba na mutum ba ballantana na baiwa kaina." Baki Hajiya Dada ta saki tana kallon Uwa dake wani jujjuya idanu ta na murguɗa baki,maida kallon ta tayi ga Ruƙayya da ke zaune kanta duƙe ta na wasa da zoben zinaren dake yatsan ta,fuskar ta ɗauke da murmushi kamar koda taushe,cikin murmishi da son kawar da ɓacin ran da ta jiyo alamun Uwa ta dasawa Hajiya Dada ta ce, "Inshaa Allahu Hajiya ba zaki bar duniya ba sai kin ga magajin Alhaji,ki yi haƙuri ki kwantar da hankalin ki,mu barwa Allah komai." A hankali fushin da ke saman fuskar Hajiya Dada ya sauka,ta ce, "Allah ya yarda Ruƙayya,Allah kuma ya sa wannan jika da nake ƙwalafucin samu ya fito daga wajen ki,dan ko babu komai ba ƙiyayya ce ta sa na ce Jubair ya ƙara aure ba,babban burin dake cikin zuciyata shine ya yi sanadiyyar da yasa na ce Jubair ya auro Uwani,duba da cewa a gidan da ta baro dika yara maza take haifa,sai gashi anan ta kasa koda ɓatan wata ne." A zuciye Uwa ta buɗe baki da nufin gaggayawa Hajiya Dada baƙar magana,cikin sauri ta ja bakin ta ta kulle saboda shigar Jubair cikin parlourn sanye da wani yadi mai azabar laushi da kyau ruwan ƙasa,agogon shi na fata ruwan ƙasa da takalmin shi baƙi su suka ƙara yiwa shigar tashi kyau,karin hular shi Ruƙayya ta kalla ta saki murmushi ta sake duƙar da kanta ƙasa ta na wasa da zoben ta,murmushi shima ya sakar mata yana jin daɗin yanda take da tsananin kunya da kawaici. Ƙamshin turaren shi ne ya sanya Uwa sake matsawa daf da shi ta narke jiki da murya ta ce, "Har ka fito kenan gorko am." "Eh alhamdulillah Allah ya nufa na fito,Hajiya Dada barka da safiya." "Barka dai Boɗɗo manga,ka tashi lafiya?" "Lafiya ƙalaou ya tashi Hajiya,ai cewa..." Kallon da Jubair ya watsawa Uwa ne ya sanya ta tsuke bakin ta,nan take Ruƙayya da ta fahimci me yake nufi ta miƙe ta yiwa Dada Sallama ta bar sashen,sai da Uwani ta gama jan jiki tana zumɓura baki sannan ta miƙe ta bar sashen. Tana fita Hajiya Dada ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Boɗɗo kana ji na ko? Yau idan ka dawo daga office ka zo zamu yi magana mai muhimmanci da kai." Nan take gaban Jubair ya yanke ya faɗi,dan kuwa a duk sanda Dada ta ce masa tana da magana mai muhimmanci da shi abun baya ƙare musu ta daɗin rai........ [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...... RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH *Ko labarin bai yi maki ba yanzu ki adana a wani wajen,saboda kada sai na yi gaba ki ce a tura maki daga farko.* PAGE 2: Sai da Hajiya Dada ta gyara zama ta karɓi mug ɗin da Jubair ya gama haɗa mata tea ta kurɓa sau uku kafin ta ajiye a gabanta ta kalle shi,tanƙwashe ƙafafunta ta yi ta sake kallon shi da kulawa ta ce, "Boɗɗo am kar ka ga na dame ka akan maganar samun magajin nan da nake yawaita yi maka,ina so ka sani tin a shekarun baya rayuwa ta sauya balle kuma a yanzu da zamani ya kara tafiya,ba wai ina kushe yara matan da Allah ya baka bane,kai ka san ina son su sosai a zuciyata,kawai ina jin tsoron duk sanda aka ce yau babu kai bamu san ya rayuwar su zata kasance ba,ina jin tsoron kada ƴan'uwan mahaifinka su maimaita musu abinda suka yi maka a lokacin da mahaifin ka ya rasu ya barmu daga ni sai kai tare da tarin dukiya,kar ka manta sai da muka rasa muhallin zama duk yawan gidajen mahaifin ka,sannan sai da ƙwayar hatsi ta gagari bakin da ke ciyar da mutane sama da goma a rana,Jubair ka dage ka nemi wani auren ko Allah zai sa a dace ka haifi ɗa namiji wanda zai taso ya tallafi zuri'ar ka bayan babu kai." Cikin zuciyar Jubair cike take da maganganu masu tarin yawa,sai dai ba zai iya furta mata su ba,tinda ba yau ne suka fara irin waɗannan maganganun ba,fatan shi bai wuce Allah ya cika mata burin ta ba ya bashi ɗa namiji mai albarka. Cikin sanyin murya Jubair ya ce, "Inshaa Allahu Hajiya burin ki zai cika,zaki ga ɗa namiji a gidan nan watarana,abinda nake so ni dake mu yi shine,mu ci gaba da tsananta addu'a,sannan mu zuba idanu har Allah ya amsa mana ya cika mana burin mu." Sosa ƙeyar shi ya fara yi yana sunkuyar da kai tare da murmushi,kallon shi Hajiya Dada ta yi itama fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce, "Sanar dani daddaɗan labarin dake cikin zuciyar ka Babana." Miƙewa ya yi tsaye ya ɗebi wayoyin shi ya kama hanyar fita,sai da ya kusan zuwa bakin ƙofa sannan ya ce, "Da alama wannan karon baki gano cewa Ruƙayya na ɗauke da juna biyu ba,wataƙila addu'ar mu Allah zai amsa shi yasa baki gane ba har ya kai watanni huɗu a duniya." Yana kaiwa nan a maganar shi ya buɗe ƙofa ya fita yana dariya mai cike da jin nauyin mahaifiyar tashi,Dada kuwa kasa motsawa tayi saboda wani irin farin ciki da ya lulluɓe ta,murmushi take ta zabgawa tare da godewa Allah a fili. Kasa ci gaba da karyawar ta yi ta miƙe ta ja sandar ƙarfenta da take amfani da ita saboda ciwon guiwa ta nufi sashen Ruƙayya. Ko da ta shiga ta tarar da Kulu na goge parlour tana ƴan waƙe-waƙenta irin na dattijan da suka taso a ƙauye,cikin fara'ar da Hajiya Dada ta kasa ɓoyewa ta ce, "Kulu aiki ake yi ne?" Sai da Kulu ta durƙusa ta kwashi gaisuwa sannan ta washe baki ta ce, "Eh Hajiya Dada aiki nake ɗan ragewa kafin na je na ɗora girkin rana." "Allah ya taimaka, ina ita uwar ɗakin naki take?" "Ta na ciki Hajiya, ko a kira ta ne duk da dai na ga bata jima da kwantawa ba,da alama bacci zata maida." "Allah sarki,barta ta rintsa anjima zan sake dawowa." Kakarin aman da Hajiya Dada ta jiyo daga ɗakin Ruƙayya ne ya sanya ta takawa ta nufi ɗakin cikin sauri,tana shiga ta tarar da Ruƙayya zaune a ƙasan makeken banɗakin nata da ya gaji da haɗuwa ta na ta kelaya amai wanda banda ruwa da majina babu komai a cikin shi. Cike da tausayawa Hajiya Dada ta kamata ta zaunar da ita a saman toilet wanda marfin shi ke sanye da carpet,a galabaice Ruƙayya ta buɗe idanun ta da suke lumshewa saboda azaba ta kalli Dada, cike da jin kunya ta hau kame-kame tana son ta ja towel ta rufe jikin ta dake sanye da wata doguwar riga mara nauyi. "Ke samawa kan ki lafiya ki wanke fuskar ki kin ji,wataƙila aman ma ya ragu,yo Allah na tuba wace kunya ce kuma kike ji Ruƙayya aure shekara da shekaru ana tare? Maza yunƙura ki kwarawa fuskar ki ruwa ko kin ji salama,anya ma kin karya kuwa? Dan na ga alamar babu komai a cikin ki da ya wuce ruwa, Kulu !" Hajiya Dada ta ware murya ta ƙwalawa kulu kira,kamar wadda ke tsaye a bakin ƙofa haka Kulu ta shiga banɗakin ta duƙa a gaban Hajiya Dada cike da girmamawa,idanun ta ne suka sauka akan aman da Ruƙayya ta yi sai ta hau yi mata sannu tare da fatan Allah ya bata lafiya ya rabata da abinda take ɗauke da shi a cikin ta lafiya. Shiru Ruƙayya ta yi ba tare da ta amsa ba saboda tsananin jin kunyar Hajiya Dada,murmushi Hajiya Dada ta yi sannan ta ce, "Kulu kama ta ki taimaka mata,da ta kimtsa a dafa mata wani abun ta ci ta sha shayi,idan kuma kunu take so a dama mata,kar a bari ta dinga zama da yunwa,Allah ya baki lafiya ya sa wannan karon ki haifa min magajin Boɗɗo." Kulu ce ta amsa addu'ar Hajiya Dada kafin ta tashi daga durƙuson da tai ta fara taimakawa Ruƙayya kamar yanda Hajiya ta yi mata umarni. Ita kuwa Dada sashen Uwa ta nufa ta same ta zaune a parlour ta na waya da ƙawarta, jin shigar Hajiya Dada parlourn ta ne ya sanya ta yin saurin kashe wayar ta miƙe tsaye tana zare ido tare da fatan Allah yasa Hajiya Dada bata ji maganganun da take yi a waya ba. Ko zama Hajiya bata yi ba ta kalli Uwa ta ce, "Uwa ina so ki sani wannan rashin kunya da firiritar da kike yi a gidan nan babu inda za su kai ki,ki bar ganin alaƙar zumuncin dake a tsakani na da mahaifiyar ki har ya yi sanadiyyar da na roƙi alfarma aka aura wa Boɗɗo ke,kamar yanda na roƙi ƴar'uwata aka bani auren ki,ina iya sanya ɗana ya sake ki ya kawo wata,domin ba kan ki farau ba,kar ki manta mata ɗai-ɗai sama da uku Jubair ya aura kafin ke,dan haka a kullum ki dinga sanyawa ran ki zaki iya komawa rayuwar zawarcin da kika bari in har baki dena sa'insa da ni ba,ni ba sa'ar ki bace,ba zan lamunci rashin tarbiyya ba,kin ji na faɗa miko? Ga mata can sun dage suna ɗaukar ciki ke kina nan kina kishin banza." A gigice Uwa ta kalli Hajiya Dada,domin kuwa duk a cikin maganganun ta babu wanda ya daki fatar jikin ta balle ya huda tsokar jiki da ƙashin ta har ya yi nasarar shiga zuciyarta,cikin tashin hankali ta buɗe baki zata yi magana sai ta ga Hajiya Dada na rufe mata ƙofar parlourn ta. Hankali a tashe ta ɗauki wayar ta ta wuce sashen Rukayya,ta na shiga ta ganta zaune Kulu ta kara mata pillow ta kwanta,cike da kasala ta ce, "Kulu kin dai san warin farfesun nan ne ya tada min da zuciya har nake aman nan ko? Ni dai a barni da ruwan sanyi idan na sha ina jin daɗi a rai na,lafiya kalau na tashi gashi nan yanzu kin sa na rabke." Cikin murmushi Kulu ta ce, "Daurewa zaki yi ki ci koda kaɗan ne Hajiyata,ko ba dan ke ba ki ci dan abinda ke cikin ki,zaki samu kuzari." Shagwab'e fuska Ruƙayya ta yi kafin ta ce, "Wancan ma fa ban ci ba,na ajiye na koma ɗaki na kwanta,shine fa ina kwanciyar na ji amai na damuna,dan Allah kar ki sake kawo min shi ki dai bani ragowar kunun gyad'ar Alhaji na sha." A gigice Uwa ta kalli Kulu da Ruƙayya ta ce, "Wacece ke da cikin? Kar dai ki sanar dani Ruƙayya ciki kika sake yi ni ina zaune ko ɓatan wata ban taɓa yi ba?" Wani irin kallon mamaki suka bi Uwa da shi,nan take idanun Uwa suka fara zubar da hawaye ta bar sashen Ruƙayya a guje ta na kuka kamar wata ƙaramar yarinya,kallon juna su Ruƙayya suka yi suna tambayar junan su da ido me hakan ke nufi? Kasa baiwa junan su amsa suka yi sai kawai Kulu ta ci gaba da zubawa Ruƙayya ragowar kunun gyad'ar da ta damawa Jubair. A bangaren Jubair kuwa tinda driver ya ajiye shi a office ya shiga ya samu waje ya zauna yana nazarin maganganun Hajiya Dada,shin ya zai yi ne ya samar mata da farin cikin da take nema shekara da shekaru? Ganin kan shi ya kulle ne ya sanya shi ɗaukan wayar shi ya lalubo lambar da yake ganin zata bashi mafita akan matsalar da ke damun zuciyar shi.............. [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE... RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH PAGE 4: Idanu Hajiya Dada ta zubawa Uwa da ke sharɓar kuka ta na bayani,ganin yanda kalaman ta ke dukan zuciyar Hajiya Dada ne ya sanya Uwa sake rushewa da kuka ta ce, "Na gaji Hajiya, na gaji, shekara ɗai-ɗai har shekara goma ace har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yi ba? Gashi yanzu Yah Jubair ba ta ni yake yi ba,dama haka yake yi min a duk sanda Ruƙayya ta samu juna biyu,ballantana yanzu da ya ƙwallafa ran zai samu magaji daga wajen ta,dan Allah ki yi mini izini na je gida in nemi maganin haihuwa ko Allah zai sa na dace nima." Kukan da take rizga ne ya sake karyar da zuciyar Hajiya Dada, nan take ta ɗauki duka laifin abubuwan dake faruwa ta ɗorawa kanta,domin kuwa da bata fifita haihuwar ɗa namiji akan mace ba da ƴar ƴar'uwar ta bata riski kanta a cikin wannan hali na tsangwamar kai da damuwa ba,uwa uba ƙiri-ƙiri take nuna banbanci tsakanin surukan nata biyu,lallai son samun magajin Jubair na neman ya jefa ta ga halaka ta hanyar raba kawunan matan ɗan ta,cikin murya mai taushi Dada ta ce, "Uwata ki yi haƙuri akan duk wani abu da kika ga yana faruwa a gidan nan,ke yarinya ce baki san irin wahalar rayuwar da muka fuskanta bane a lokacin da na rasa mahaifin Jubair,na yi zaton rayuwata zata ƙare nima saboda tsananin shiga ƙunci,damuwa ɗimuwa da tashin hankali,na fuskanci tsangwamar dangin miji da tsananin ƙiyayyar su bayan rasuwar mijina,wanda a lokacin ne ya kamata su lallashe ni,su tallafe mu kasancewar mun rasa wani babban jigo a rayuwar mu,amma inaa su ba ta rasuwar jinin su suke yi ba,babban abinda ke gaban su shine na yi na gama takaba a raba dukiya su karɓi ɗan su,sai su barni na sha wahalar rayuwa,sun manta cewa bani da kowa sai miji na da ɗana,sun manta cewa miji na shine ya zame min uwa,ya kuma zame min uba,ƙanwata mace ce ba namiji ba itama a ƙarƙashin wani take,to da wa zan jingina na ji sanyi? Zuciya ta ta yi sanyi ta samu natsuwa a wancan lokacin saboda na san koda sun karɓi ɗan su zan samu muhallin da zan zauna ba zan wulaƙanta ba duba da cewa Abbahn Jubair na da dukiya mai tarin yawa,sai dai kashh ! Abinda nake fata bai samu gare ni ba,domin kuwa ina gama takaba,ƴan'uwan miji na suka kore ni a gidan da muke da zama suka bani dubu uku wai iya wannan na samu a matsayin gado na,ina gidajen Alhaji? Ina makarantu da ya gina ake karɓar kuɗaɗe masu yawa? Ina asibitin da ya gina? Ina motocin da ake masa fatauci da su? Dubu uku su ne kawai gadon da na samu ko sune kawai abinda suka ga damar bani? Me dubu uku zata yi min? Shin wulaƙanci ne ya sanya suka bani dubu uku a matsayin gado na ko tozarci da cin amana?" Numfasawa Hajiya Dada tayi idanun ta sun kaɗa sun yi jawur,tsananin ɓacin rai da damuwar dake cikin ranta ne suka bayyana a fuskar ta har suka yi sanadiyyar dasawa Uwa nadamar tunkarar ta da zancen haihuwa,a hankali Uwa ta ji muryar Hajiya Dada na ci gaba da magana. "Da na zauna na yi nazari sai na ga to me zai dame ni dan sun tattare dukiya sun cinye? Na rasa mai dukiyar ma na haƙura nake ci gaba da numfashi sai dan an karɓe dukiyar da ya tafi ya bari,inda ya je fa suma za su je,lokaci kawai suke jira,abu ɗaya na sani kawai shine babu wanda ya isa ya raba ni da ɗana,ko shi wanene,domin kuwa na san tinda basu ƙaunaci mahaifin shi domin Allah ba,shima ba son shi suke yi domin Allah ba,dan haka ba zan bar musu yarona ba ko mai rintsi komai wahala. Wannan shine dalilin da ya sa na ɗauke Jubair yana da ƙananan shekaru a duniya muka bar gidan mahaifin shi,gidan da na yi rayuwar jin daɗi da mulki da sarautar da mijina ya bani,gidan da na haifi gwarzon namiji kamar Jubair. A lokacin da na bar gidan ne muna tafe cikin tsananin yunwa da ƙishirwa motar mahaifin Ammar ta buge ni,kusan shine dalilin da ya sa nake da wannan ciwon guiwar da ya ƙi ci yaƙi cinyewa. Mahaifin Ammar ya kula da mu,ya wadata mu da duk wani abun more rayuwa da muka buƙata a wancan lokacin,bai taɓa banbanta tsakanin Ammar

Chapter 1 of 11