Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
da Jubair ba wajen kulawa,tufatarwa,shayarwa tare da makarantar da suka je. Kasancewar mahaifiyar Ammar ta rasu sai mahaifin shi yaso ya maye gurbinta da ni,sai dai kafin hakan ta kasance ya kamu da mummunan ciwon ciki,cikin dare ya rasu ya barni da Ammar da Jubair cikin maraici da kaɗaici,kasancewar bashi da kowa ne ya bani damar ci gaba da kula da Ammar da Jubair har suka girma na aurar da su,dake Allah shine mai yanda yaso sai ya ƙaddara Ammar ba zai zauna ya yi rayuwa damu anan ba,yana can turai a Baltimore yana zaune da matar shi da yarinyarsu. Ina fatan a cikin wannan ɗan taƙaitaccen tarihin da na baki zaki gane dalili na na son samun yaro namiji da nake fatan ya zamewa Jubair da dikkan musulmi sanyin idaniya tinda har yanzu iyayen Jubair na bibiyar shi,duk dukiyar da suka danne ta ƙare babu ita saboda ba mallakin su bane,yanzu sun dawo suna manne masa suna son su samu wata damar da zasu cutar min da yaro,shi yasa duk satin duniya sai sun zo wai sun kawo masa ziyara ne,ni ba zan raba shi da dangin mahaifin shi ba,tinda ko banza siyasa yake yi,bana son saboda abinda ke tsakanin mu a samu wanda za su yi masa yarfe ko ƙage irin na ƴan siyasa ace bashi da uba ko wani abu makamancin haka." Ƙwallar da Uwa ta gani a idanun Hajiya Dada ne suka sake sanyaya mata jiki, tabbas ta fahimci dalilin Hajiya Dada na son haihuwar ɗa namiji a gidan Jubair,amma me yasa ita har yanzu ko ɓari bata taɓa yi ba balle ta saka ran zata iya zama uwar magajin gidan Jubair? Cikin sanyin murya ta ce. "Na fahimce ki Hajiya Dada,inshaa Allahu ba zaki mutu ba sai kin ga jika namiji daga Yah Jubair,ina fata Allah yasa nice zan kasance mai sa'ar da zata faranta ran ki anan gaba,ki taya ni da addu'a ni kaina ina son na haihu,na rasa dalilin da yasa shekara goma da aure ban taɓa ɓatan wata ba." "Inshaa Allahu zan ci gaba da taya ki da addu'a fiye da yanda nake yi a baya,ni kaina zan fi son na samu jika namiji daga wajen ki,domin kuwa bahaushe yace so sone amma son kai ya fi." Ruƙayya dake tsaye a ƙofar ɗakin Hajiya Dada ce ta shafa cikin ta cikin wani irin yanayi ta juya zata bar sashen gaba ɗaya,zuciyarta banda bugawa da tashin hankali babu abinda take ci gaba da yi,idan bata samu ɗa namiji ba a yanda Hajiya Dada ta ƙwallafa rai tabbas akwai matsala,dole ne ta je asibiti a duba mata abinda za ta haifa ko dan kwanciyar hankalin kowa. Karo ta yi da Jubair da ya shiga sashen dan gaishe da mahaifiyar shi,cike da jin nauyin shi ta raɓe gefe ta bashi waje dan ya shiga, kallon ta ya yi ya ga sauyin yanayi a tattare da ita,nan take ya jata jikin shi yana tambayar ta dalilin sauyawar yanayin ta,cikin sanyin muryar da take da shi ta ce. "Babu komai, na dai kula kamar Hajiya na tattaunawa da Uwa ne,shi yasa na dawo gudun kar na katse musu hira." Murmushi Jubair ya yi mai sauti kafin ya shafi kuncin Ruƙayya ya ce, "Ruƙyna sarkin hankali,a kullum natsuwar ki da kamun kan ki tare da sanin yakamatan ki ke ƙara dasa min zazzafan son ki a raina,har abada ba za ayi macen da zata samu irin son da nake maki ba a zuciyata,taho mu je mu ma a yi hirar da mu." Kalaman shi ba ƙaramin daɗi suka yiwa zuciyar ta ba,har sai da suka yi sanadiyyar sauyawar kalar fuskar ta ta yi ja saboda kunya,kanta a ƙasa ta ke bin shi har suka isa parlourn Hajiya Dada,sallama Jubair ya kwaɗa kafin su yiwa kansu mazauni a kujerun dake jere a parlourn. Babu jimawa Hajiya Dada da Uwa suka fito a tare,sai da Uwa ta yi matsanancin ƙoƙari kafin ta iya danne kishin dake barazanar sanya ta hauka ta iya gaishe da Jubair,sanin cewa ba zata kula Ruƙayya bane ya sanya Ruƙayya gaishe ta tare da tambayar yanda ta kwana,a yatsine Uwa ta ce, "Ƙalau na kwana ya son ran ki?" Murmushi kawai Ruƙayya ta yi ta miƙe dan haɗawa Hajiya Dada shayi,Uwa na ganin haka sai ta sha gaban Ruƙayya tana faɗin, "Ni fa bana son baƙin iyayi da son a sani,sai wani tafiya kike ki na turo ciki gaba ke ga mai ciki ko? Mtsssww ! matsa ni dan Allah ki bani waje." Ba tare da Ruƙayya ta yi jayayya da Uwa ba ta yiwa Hajiya Dada sallama ta bar sashen ranta na mata suya akan abinda Uwa ke yi mata. Jubair kuwa kafe Uwa ya yi da ido,dan kuwa bai isa yi mata faɗa a gaban Hajiya ba ya riga da ya san da wannan,a tsarin tarbiyyar gidan ma gaba ɗaya idan Hajiya na waje babu mai yanke hukunci. Uwa kuwa duk kallon da Jubair ke wurga mata tana sane da shi,hakan kuwa ya ƙara zama sanadiyyar ƙarin tsanar Ruƙayya a ran ta,sai da Hajiya ta bari Uwa ta ɗauki mug zata haɗa shayi ta ce. "Kema ajiye ki bar nan,da alama duk maganganun da muka yi dake basu zauna a zuciyar ki ba,kunnuwan ki suka shiga suka fita." Cike da zumɓura baki ta baro wajen ta tsaya a tsakiyar parlourn ta ce, "Hajiya to kin amince na je gida yau?" Kallon Jubair Hajiya ta yi sannan ta ce, "To kai ka ji,matar ka na son taje gida neman maganin haihuwa,ka amince ta tafi?" A ladabce Jubair ya ce, "Hajiya ai duk abinda kuka ce shi za a yi." Sai da Hajiya ta nisa sannan ta ce, "Ki gaishe min da Batula,kar kuma ki sake ki kwana dan na san halin ki sarai." Cike da farin ciki Uwa ta bar sashen Hajiya Dada,sai da ta gama shiryawa tsaf cikin tsadaddun tufafin ta sannan ta ɗauki makullin motar ta ta sallami Ubaida ta nufi harabar gidan. Su Kubrah ta gani sun shiga mota za a kai su makaranta,ɗauke kai ta yi ta kunna ta ta motar ta shige tana ƙwafa,cike da ƙunar zuciya ta ce, "Matan ma ba barin su zan yi ki mora ba balle har ki haifi magajin mai gidan,matsiyaciya dangin babu" A hasale ta dinga dannawa mai gadi horn duk da cewa gate ɗin gidan a buɗe yake,bata dena horn ba har sai da ta bar gidan,girgiza kai mai gadi ya yi yana jinjina masifa da gadara irin ta Uwa. A bangaren Ruƙayya kuwa tana komawa sashen ta sai ta samu waje ta zauna tare da lumshe idanun ta,rayuwar gwagwarmaya da hannu baka hannu ƙwaryar da ta yi a baya ita da iyayenta da ƙannen ta mata biyu ta tinano,sannan ta koma kan irin daular da take ciki a yanzu,shin haihuwar namiji wata ɗaukaka gare shi ta musamman har da ake ta nanata zance daya akai? Menene makomar ta idan har bata samu haihuwar namiji ba kenan?........ [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE... RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH PAGE 3: Sai da Jubair ya kira wayar sama da sau biyu kafin a amsa,a can ɗaya ɓangaren ya jiyo ana ta yin faɗa da harshen turanci,murmushi Jubair ya yi kafin ya ce, "Bro ka kwantar da hankalin ka ka dena tada jijiyar wuyan ka akan ƙanƙanin abu,ji yanda ka ke faɗa da tsakar daren nan dan na san ku yanzu dare ne a wajen ku." 'Exactly my point bro,ita to bata san dare ba sam,can you believe this girl wai fita zata yi da friends ɗin ta?' "Please ka dena matsa mata,she is just a kid,ka dinga yawaita yi mata addu'a tinda kai da kanka ka san irin wajen da kuke,dole ne irin haka ta faru dama." 'No ba dole bane ta zama kamar su,mutane nawa ka sani a nan ƙasar da ke riƙo da addininsu da al'adarsu? Amma ita a kullum abinda take so shi zata aikata ko muna so ko bama so,kana ganin hakan ya dace?' Jinjina kai Jubair ya yi kamar Ammar na ganin shi kafin ya ce, "Bai dace ba gaskiya,yanzu yanda za ai bani ita na mata magana." Cikin abinda bai fi mintuna biyu ba Jubair ya ji muryar matashiyar budurwar ta na gaida shi a shagwab'e,da jin muryar ta zaka gane kuka take yi,da wata iriyar murya Jubair ya kira sunan ta,sai da ta gaji da yanga da shagwab'a kafin ta amsa da, 'Yes Papa.' Da harshen hausa Jubair ya furta, "Babyn Papa me yasa kike rashin jin magana? Yanzu dare ya yi ki koma ki kwanta kar na sake jin kin fita da dare." 'Me yasa Papa?' "Saboda ke musulma ce babu kyau mace ta fita da dare da friends maza,haramun ne Allah ya hana." 'Ok idan da mata ne fa?' "Wai ina za ku je ma tukunna?" 'Club' "Subhanallahi ! Ku yi me da ƙananan shekarun ku?" 'Today is Elsa's birthday Papa,we just want to have some fun, please Papa ka barni in tafi suna ta jira na.' Yarinyar ta ƙarasa maganar ta cike da matsananciyar shagwab'a,nan take Ammar ya lumshe idanun shi cike da takaici dan ya san ta taɓo daidai inda yake gudu a wajen ɗan'uwan nashi,Jubair kuwa sake narkewa ya yi a kujera ya na jin yanda Babyn tashi ke zuba shagwab'a kamar ta na ganin shi,cikin sanyin murya ya ce, "My beautiful Queen ki yi haƙuri ki je ki kwanta ki yi bacci,na yi maki alƙawari zan aiko maki da kuɗi mai yawa da zaki sai mata wani abu mai kyau ki bata, bana so ki dinga fita da dare,duk abinda iyayen ki basu so ki dena yin shi kin ji? Haramun ne Allah na ƙona masu tsallake maganar iyayen su a wuta,ko ki na so ki shiga wutar Allah?" A shagwab'e ta girgiza kai,cike da murmushin samun nasara Ammar ya karɓi wayar ya ce, 'Bro na gode,ka ganta can ta fita waje,na tabbata sallamar su zata yi,ina mamakin yanda yarinyar nan ke tsananin jin maganar ka,ko da yake bari na dena mamaki,abun na tsakanin ƴa da uba ne,babu mai shiga gudun jin kunya.' Murmushi Jubair ya yi mai sauti kafin ya ce, "Lallai kam,gwanda da ka gano hakan da kan ka." 'Ka yi haƙuri mun ɓata maka lokaci,me ya sa ka kira ni a wannan lokacin? Na san in dai ba wata matsalar ce ta taso ba baka kira na da dare.' Ajiyar zuciya Jubair ya sauke mai nauyi kafin ya ce, "Humm same matsalar da na saba fuskanta ce wannan karon ma ta tunkaro ni,Hajiya ta kafe sai na ƙara aure saboda samun magaji,na rasa ta yanda zan ɓullo mata,fata na Allah yasa wannan cikin da Ruƙy ke ɗauke da shi mu samu namiji,ka ga hankalin kowa sai ya kwanta." 'Allah sarki Hajiya,ta kasa manta baya ne shi yasa,ka san bayan Allah da manzon sa Uwa tafi kowa so da tausayin ɗan ta,dan haka ni duk abinda take yi baya damu na,hasali ma daɗi nake ji a ƙalla muna da ita,ka sani bani da kowa yanzu a duniya da ya wuce Hajiya Dada, dan haka dole ne mu haɗa kai mu faranta mata matsawar abinda ta nema a wajen mu bai kaucewa hanyar addini ba,wanda na sani, ka sani ba zata taɓa umartar mu da mu yi abinda yake haramun ba.' "Haka ne Bro,yanzu to menene mafita?" 'Mafita ɗaya ce ka lallashe ta for now,ka nuna mata ta yi haƙuri a jira a ga me Ruƙy zata haifa,idan aka samu abinda ake nema shikenan,maganar aure babu ita,idan kuma ba a samu ba sai ka nemo matar aure kamar yanda take so ka aura,kaga kafin nan sai mu dage da addu'ar Allah yasa a dace da rabon alkhairi.' "Alhamdulillah, na gode ɗan'uwana,ban taɓa neman shawara a wajen kaba ba tare da ka kawo min mafita ba,wannan shawarar ita zan bi...ƙarar me nake ji haka kamar kiɗa?" Dariya Ammar ya yi kafin ya ce, 'A gida ake Birthday party ɗin,kai wannan ƴar taka duniya ce,mugun tsoron ta ƙawayen suke ji har mazan,na tabbata zuwa ta yi ta ce musu a yi party'n anan,ni kuma ba zan hana su ba,i have my CCTV camera everywhere,a yi party lafiya.' Dariya suka yi,kafin su ci gaba da hirar su akan business ɗin da Ammar ke yi da kuma ɓangaren aikin gwamnatin da Jubair ke yi. ****************************** Tinda Hajiya Dada ta tabbatar da cikin dake jikin Ruƙayya take bata wata iriyar kulawar da bata taɓa bata ba a lokutan baya da take haihuwa,domin kuwa tana ji a jikin ta lokacin samun Magajin Jubair ne ya zo. Ita kuwa Ruƙayya a kullum cikin zullumi da tunani take,shin ya Hajiya Dada za ta yi idan ta sake haifar mace? Wannan tunanin na gigita ta har ya sanya ta fara ramewa. Hajiya Dada kuwa ta yi zaton ko rashin cin abinci ne yake sanya ta rama,dan haka da kanta watarana take shiga kitchen da su Kubrah tai ta nuna musu yanda ake wasu girke-girken na gargajiya,musamman wanda masu ciki suka fi kwaɗayi,dangin su; alalen gwangwani da manja da yaji,dambun masara da manja da yaji,dambun shinkafa da zogale da gyad'a da yaji,ɗanwakeda mai da yaji,ƙosan rogo da masar gero wanda take sanya Kulu ta daka ƙuli-ƙuli mai daɗi. Duk abinda suke yi Uwa na samun labari a wajen mai aikin ta Ubaida,dan haka baƙin ciki da damuwa sun taru sun mamaye zuciyarta ta rasa ta inda zata ɓullo wa lamarin,takaicin duniya ya haɗe mata waje ɗaya musamman idan ta tina maganar ƙarin auren da Hajiya Dada ta sanya Jubair yi,gaba ɗaya sai hankalin ta ya kasu kashi biyu. Yau ma kamar kullum kwance take ta gaza rintsawa sai juyi take yi a gado,kewar mijinta da a kullum take jin da ita ya fara aura ko bata haihuwa babu wanda ya isa ya sanya shi ƙara aure ballantana su raba wajen kwana. Ƙwafa ta yi ta ja dogon tsaki kafin ta tashi zaune ta ja rigar baccin ta ta rufe jikin ta da kyau,sauka ta yi daga gadon ta faɗa banɗaki ta yi fitsari ta fito,hamma ta yi kafin ta kalli kanta a madubi tin daga sama har zuwa faffaɗan ƙugun ta,a hankali ta furta, "Me na nema na rasa a jiki na da Jubair ya fi son Ruƙayya akai na? Ko da na san ba zan nuna mata komai ba a fagen kyau amma na fita wayewa da sanin duniya,duk yanda nake sake masa jiki na na gatanta shi bai sa hankalin shi ya karkato waje na ba,ga uwa uba ɗokin haihuwar nan da suke yi kamar ba a taɓa haihuwa ba a gidan nan,meye laifi na dan ban haihu ba ake fifita wata akai na? Ba zai yuwu na zauna ina ji ina gani wata banza ƴar fulanin rugga ta fini daraja a idon miji ba,ko banza ni jinin shi ce dole ya so ni fiye da yanda zai so ta,Allah ya kaimu safiya komai zai zo ƙarshe a gidan nan." Uwa na gama cin alwashi da surutan ta ta bi lafiyar makeken gadon ta ta kwanta,sai da ta daidaita sanyin AC'n ɗakin sannan ta lulluɓe jikin ta babu addu'ar bacci ta ajiye remote ɗin AC a gefen gadon ta rintse ido. Washegari da sassafe ta tashi ta sheƙa wanka ta kira Ubaida ta ce ta gyara mata ɗakin ta da wuri dan zata fita,a ƙa'idar ta idan zata fita ko zata bar sashen ta a bude sai ta kulle ɗakunan ta guda ukun. Cikin sauri kuwa Ubaida ta hau gyaran gidan da ba wani datti ya yi ba ta haɗa musu abin karyawa,sai da suka ci suka ƙoshi sannan Uwa ta fita sashen Hajiya Dada cikin kwalliya ta alfarma sai baza ƙamshi take yi,ko da ta isa ta tarar da sashen Hajiyan shiru,hakan ya nuna har a wannan lokacin Hajiya Dada bata fito parlour ba. Bakin ta ɗauke da sallama ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Dada,sai da ta sanya fuskar tausayi sannan ta murɗa hannun ƙofar ta shiga ɗakin, a zaune ta tarar da Hajiya Dada riƙe da littafin addu'o'in ta tana karantawa,sai da ta kammala abinda take yi ta kalli Uwa dake ta sharar hawaye ta na goge majinar da babu ita a hancin ta,murmushi Hajiya Dada ta yi dan kuwa ta riga da ta san halin ƴar ta ta, ta san watarana haka zata faru,dan haka sai ta yi mata nuni da kusa da ita,cike da shagwab'a Uwa ta isa gaban Hajiya Dada ta tanƙwashe ƙafa ta sake fashewa da kuka,a hankali Hajiya Dada ta ce, "Ki sanar dani abinda ya kawo ki wajena Uwata, ko kuma ki koma sashen ki,idan kin gama kukan sai ki dawo." Hawaye Uwa ta share sannan ta gyara zamanta ta ce..................... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE... RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 6: Lokacin da ta isa gida ta tarar da gidan shiru kamar babu kowa,kasancewar yara suna makaranta kowa kuma na sashen shi,Jubair ko ya tafi office sai dare zai dawo. Tana fitowa daga mota sashenta ta wuce,a bakin ƙofa ta tarar da Ubaida da Munkaila mai share-sharen harabar gidan da kula da shuke-shuke suna hira kamar wasu tsofaffin masoya,a wulaƙance take bin su da kallo kafin ta dakawa Ubaida tsawa ta ce. "Inyeee lallai ne Ubaida,meye haka nake gani da rana tsaka a sashena? Wuce ciki mu je shashasha kawai wadda bata nemawa kanta nasara a rayuwa,ke yanzu fisabillahi ki zo aiki gidan nan sannan ki ɓige da soyayya da ɗan aiki?" Cike da ɓacin rai Munkaila ya kalle ta ya ƙure ta da idanu,kallon shi Uwa ta yi taga irin kallon da yake yi mata,nan take ranta ya ɓaci,cikin fushi ta hau masifa ta na faɗin. "Maza ka zo ka tattara naka ya naka ka bar gidan nan mara mutunci kawai,ni ka ke yiwa mugun kallo kamar wata sa'ar ka?" Karkace kai Munkaila ya yi sannan ya ce, "Hajiya ita soyayya babu ruwanta da talaka balle mai kuɗi,babu ruwanta da babba ko yaro,Ubaida na so na nima kuma ina son ta,rayuwar nan fa ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi,ni ne daidai ita,itama kuma ita ce daidai ni,maganar barin aiki Hajiya ai ba ke ce kika ɗauke ni aiki ba,Hajiya Dada ce ta ɗauke ni aiki,dan haka ita kaɗai ce zata kore ni na koru a gidan nan." Baki sake Ubaida da Uwa ke kallon Munkaila,cike da tsananin fushi Uwa ta tunkare shi zata mare shi,babu ɓata lokaci Munkaila ya sanya hannu ya tare marin sannan ya yarfe hannun ta gefe yana binta da wani mugun kallo,a hasale Uwa ta nufi sashen Hajiya Dada ta na masifa,ko da ta shiga sai ta same ta kashingiɗe ta na karanta ƙur'ani idanun ta sanye da farin gilashi,suna haɗa ido da Hajiya Dada ta ji wani irin kwarjinin Hajiyar ya dirar mata,cikin sassauta murya ta ce. "Hajiya kina da labarin cewa gab kike da jin mugun labari a gidan nan?" A kaikaice Hajiya Dada ta kalle ta ta ce, "Sallamar kenan Uwa? Sannan wanne irin mugun labari kike magana akai?" "Munkaila Hajiya zai jawowa gidan nan mugun tabo,yanzu na dawo na ganshi a sashena yana zubawa Ubaida soyayyar zamani wadda za ta iya kai su ga dana sani,da na yi masa magana sai ya nemi ya gaggaya min baƙar magana,har yana ikirarin babu wanda ya isa ya kore shi a gidan nan ko wanene tinda ya riga ya shigo ya shigo kenan." Kallon ta Hajiya Dada ta yi na wasu ƴan sakwanni kafin ta ce, "Miƙo min wayata." Kamar Uwa zata kifa dan sauri haka ta ƙarasa kujera ta ɗauki wayar Hajiya ta miƙa mata,babu ɓata lokaci Hajiya ta kira Munkaila ta ce su je shi da Ubaida sashen ta tana son ganin su,nan take Uwa ta samu waje a gefen Hajiya ta zauna ta na ci gaba da yi mata pampo,Hajiya kuwa na ci gaba da sauraron ta tana nazarin maganganun ta,basu wani jima suna zaune ba Ubaida da ke sanye da wani uban mayafi ta fara shigowa,Munkaila na biye da ita a bayan ta,waje suka samu suka fara gaishe da Hajiya Dada kafin daga baya su ce "Hajiya gamu." Ajiye waya Hajiya Dada ta yi a gefen ta kafin ta ce, "Munkaila menene tsakanin ka da Ubaida?" A kunyace Munkaila ya ce "Hajiya soyayya ce ta tsakani da Allah a tsakani na da ita wadda nake fatan ta kaimu ga aure." "Ubaidah abinda Munkaila ya faɗa gaskiya ne?" A kunyace Ubaida ta gyaɗa kai ta ce, "Eh Hajiya abinda ya faɗa gaskiya ne." Murmushi Hajiya tayi kafin ta ce, "To Alhamdulillahi,ai babu wani aibu a tarayyar su,sai dai idan ba auren ta za ka yi ba Munkaila kar ka kuskura ka yaudare ta,zan ci mutuncin ka sannan zan maida kai inda ka fito,darajar zaman tare da muka yi da iyayen ka a can baya shi yasa na ɗakko ka na kawo ka nan dan ka yi aiki ka dinga kyautata musu,ka riƙe aikin ka da kyau bana son shiririta,na baku nan da wata ɗaya ku daidaita kan ku, da yardar Allah manya za su shiga maganar ku a ɗaura maku aure." Cike da murna da farin ciki Munkaila da Ubaida suka bar parlour'n bayan Hajiya ta sallame su,Uwa kuwa ji ta yi kamar an watsa mata ruwan zafi,nan take wata iriyar tsanar Munkaila ta mamaye zuciyarta har tana jin zata iya rabuwa da Ubaida a matsayin mai aiki ta samu wata,babu ko sallama kamar yanda ta shigo ta mike zata bar sashen Hajiya Dada,cike da murmushi ta ce "Uwa kenan,ki dinga sanyawa zuciyar ki salama,na rasa me yasa zuciyar ki ke cike da ƙiyayya mai tsanani,to ba wannan ba ma,in ce dai kin samo abinda ya fitar dake daga gidan?" Wani irin shu'umin murmushi ne ya ƙwacewa Uwa saboda tina inda suka je da Ummahn ta da ta yi,cike da jin daɗi mara misaltuwa ta ce, "K'warai na samo maganin matsala ta,wanda nake fatan ya baiwa kowa mamaki a duk sanda buri na ya cika." "To Allah ya cika miki burin ki na alkhairi Uwata,ina fatan kin baro Batula lafiya da Baban naki ko? Ya labarin su Usumanu mai duniya?" Murmushi Uwa ta yi kafin ta ce, "Kowa yana nan lafiya,su Usman kuwa ni banda wani labari akan su Hajiya,tinda uban su ya nuna min fin ƙarfi akan su,ni kuwa na tattara su na watsar su je can su karata tinda ba nema na suke yi ba suma." Girgiza kai Hajiya ta yi,dan kuwa bata son hirar ta tsawaita Uwa ta zuba mata shirmen ta wanda a kullum bata gajiya da shi,a shekarun ta talatin da bakwai a duniya bata san ciwon kanta ba to yaushe zata sani? Sashenta ta wuce hannun ta riƙe da jakar ta da wayoyin ta,tana daf zata sanya ƙafa cikin sashenta ne Munkaila ya fito daga inda yake a laɓe,a matuƙar tsorace Uwa ta juya suka haɗa idanu da Munkaila,nan take ta ji wani irin yarrr tin daga kanta har zuwa kafafun ta,murmushi ya sakar mata wanda ya sanya jikin Uwa ɗaukar wata iriyar rawa,cike da tsoro ta ja baya baki na rawa ta ce, "Munkaila menene haka? Kar ka matso nan zan yi maka ihun kwarto." Wata iriyar dariya mai sauti Munkaila ya saki kafin ya nuna ta ya ce, "Ke a zaton ki ɗan asirin da kika je kika karɓo zai yi tasiri a wajen yaran da kakar su ke nema musu maganin tsari kullum? Lallai Uwa ban taɓa sanin ke sokuwa bace sai yau,an faɗa maki Hajiya Dada a zaune take? Bari na sanar dake wani abu da baki sani ba,Hajiya Dada macece mai tsananin ibada,ta na son jikokin ta matuƙa gaya kamar yanda take son ɗanta,kwalafucin ɗa namiji da take yi ba shi ne yake nufin su matan bata son su ba,duk wani tsari da ake baiwa yara saboda mugun baki da maitar ido babu wanda bata baiwa jikokin ta ba,kuma ni ɗinnan da kike gani nine ke samo mata,dan haka wannan ɗan abun da kika karɓo babu abinda zai yi musu,idan kuma kika dage sai kin yi amfani da shi to tabbas ƙaiƙayi ne zai koma kan masheƙiya,shawarar da zan baki shine ki nemi magani a inda aka san magani,ba wai inda ake koyon sanin magani ba." Munkaila na gama faɗa mata kalaman da suka sanya zufa tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikin ta ya bar wajen ya koma bakin aikin shi,hankalin Uwa a tashe ta shige ɗaki ta kulle ƙofa ta zauna a ƙasan carpet ta zabga tagumi,cikin zuciyarta take faɗin, 'Ya akai ya san na dawo da magani? Anya Munkaila ba aljani bane? To ko dai maye ne? Na shiga uku ni Uwa ya zan yi da wannan sabon al'amarin da ya tinkaro ni? Hakan na nufin mun yi asarar kuɗin mu kenan a banza?' Wayarta da ta yi ringing ce ta firgita ta ta miƙe tsaye a tsorace,a hankali ta dawo cikin natsuwar ta

Chapter 2 of 11