wa kuka zaɓa min."
"Zan yi maki wata tambaya ki bani amsa Baby."
Jinjina kai ta yi tana sauraren shi tare da share hawayen ta da su ka ƙi tsayawa,sai da Jubair ya nisa kafin ya ce.
"Idan har baki aure ni ba zaki dena taɓa jiki na,koda da riƙe min hannu ne sannan ba zaki dinga gani na koda yaushe ba,saboda mijin ki ba zai bari ba,shin kin yarda kin amince zaki iya jure rashi na har haka?"
Wasu zafafan hawaye ne masu tsananin ɗumi suka fara zubowa Malika,cikin sauri da kuka ta ke girgiza kai tare da ruƙunƙume shi a jikinta kamar za a ƙwace mata shi ta ce.
"Ba zan iya jure rashin ka ba papa,i love you so much, please Papa kar ka aura min kowa bana son kowa,kar ka aure ni ni dai kawai ina son ka bana so na dena ganinka."
"Idan har ba zaki iya jure rashina a rayuwarki ba to ki yarda ki aure ni Malika,i will love amd cherish you for the rest of our lives,zan cika maki burin ki na ci gaba da yin karatun ki har ki zama cikakkiyar ƴar jaridar da kike da buri,zan yi maki duk abinda kike so in dai zaki yi farin ciki,kin ga yanzu a addinin musulunci zaman nan da mukai ni da ke haramun ne,daga lokacin da kika balaga ya kamata na dena riƙe koda yatsan ki ne,ke ko da gashin kan ki ne guda daya bai halatta in taɓa ba,amma gaba ɗaya bama kiyayewa,dan haka aure ne kawai zai bamu halarcin taɓa jikin junan mu,Baby na saba da ke,na fara jin daɗin sauyawar da akalar soyayyar ki ta yi a zuciya ta,dan Allah kema ina so ki amince da soyayyata ki aure ni za...."
Ƙarar faɗuwar robar ruwa da glass cup ne ya dawo da Jubair dake amayar da kalaman soyayya zuwa ga ƴar shi Malika,jikin Kubrah ne ya hau rawa idanun ta na zubar da ruwa ta hau nuna Jubair da Malika,bakin ta na rawa ta ce.
"Daddy what do you mean ta aure ka, Ita ɗin ba kamar ƴa take a wajen ka ba? Dika-dika nawa Malika take da za ka aure ta? Ba fa da yawa ta girme ni ba,noo please bacci nake yi ko mutuwa na yi bana duniyar ne?"
Malika kuka Kubrah kuka,duk sai suka haɗu suka cajawa Jubair kai, shi kanshi ji ya yi kamar ya yi kukan,Umaimah ce ta shiga ta kama Malika ta ce.
"Duk laifi na ne da na sanar dake abinda ake ɓoyewa,bai tsara ki san maganar auren ba ta wannan hanyar,dan Allah ki yafe min,ki yi haƙuri ki karɓi tayin aure shi...."
"Dakata ! Kar ki sake maganar nan bana so,ta yaya za ku yi wannan gamin bautar? Mommyna fa za a yi wa kishiya da Malika."
Innah Habi ce ta shiga ɗakin ta ce.
"Ku zo Alhaji ya na neman ku dikan ku,ke kuma kafin ki fito ki ɗaure wannan kan naki ya gidan bushiya."
Malika bata kula Innah Habi ba ta miƙe ta bi bayan ta,suna zuwa parlour ta samu waje ta kame ta zauna tana kallon waje ɗaya cike da ƙunar zuciya,gaba ɗaya hankalinta ya kasu gida biyu,shin ta karɓi tayin Papa ne ko kuma ta haƙura ta ce ya sama mata wani mijin ko wanene za ta aure shi,ba za ta iya yin zaman aure da shi ba,matsayin uba ta bashi ba masoyin da zata yi soyayyar aure da shi ba,da wanne irin ido zata kalli Mommy?
A nesa da kujerar da ta zauna Kubrah ta zauna ta na zabga wa Malika harara,Jubair kuwa kanshi a ƙasa ya samu waje ya zauna shima,sai da Alhaji ya yi gyaran murya kafin ya kalli Abubakar wanda bai jima da zuwa gidan ba gaishe su,nan take Alhaji ya sake baiwa Abubakar labarin dambarwar da ake yi a gidan,sannan ya ɗora da cewa.
"In banda ma yaran yanzu da aka sake muku da yawa,da can ba miji ake yi wa mace ba sai dai ta ji an kawo goron tambaya da alewar saka rana. Dan haka ke Malika ina so ki sani,ita yarinya budurwa iyayenta na da haƙƙin su zaɓa mata mijin aure a musulunci,saboda kasancewarta mai ƙaramin tunani bata gama sanin ciwon kanta ba,amma su iyayenta sun san wanda ya dace su aurawa ƴar su mai nagarta,auren ki da Jubair ba haramun bane,halayan shi masu kyau iyayen ki suka duba da shaƙuwar dake tsakanin ku,suka ga babu wanda ya dace su baiwa ƴar su ya ci gaba da kula da iya har ƙarshen rayuwar ku sama da Jubair.
Ina mai yi maki nasiha da ki sanyawa zuciyar ki haƙuri,ki karɓi zaɓin iyayen ki da hannu bibbiyu,mahaifiyar shi na son ki,shi yana son ki,sannan a matan shi yana da mutuniyar kirki da yaran kirki da ke son ki, kamar yanda Iyayen ki suka zaɓa maki miji na gari kamar Jubair ina fatan Allah ubangiji ya baiwa Kubrah miji mai albarka itama."
Tinda Alhaji ya fara magana zuƙatan su sukai sanyi,ganin haka ne ya sanya Innah Habi karɓe maganar ta ci gaba da yi musu nasiha da nuna musu alkhairin da ke cikin wannan haɗin,daga ƙarshe Abubakar ya yi musu kalar tashi nasihar sannan ya ƙara baiwa Kubrah haƙuri akan yanda lamarin ya riske ta,kuka take tana tina yanda Daddyn nasu ya dinga ciwa mahaifiyarta mutunci a kwanakin baya,ashe duk dan zai ƙara aure ne? Ta ji ta amince ƙaddara ce ta sa zai ƙara aure,auren ma kuma da Malika,amma babu ƙaddarar da zata sa ta ci gaba da zama a yi biki da ita mahaifiyarta na can ita kaɗai cikin ƙunci.
Sai da suka gama tattaunawa Jubair ya tabbatar da Malika ta karɓi ƙaddarar auren shi sannan ya miƙe ya ce zai ta fi, cikin sauri Kubrah ta miƙe itama ta ce.
"Daddy zan bika mu koma na ga Mommyna."
Ta ƙarasa maganar ta cikin zubar da wasu zafafan hawaye,wani irin kishi take taya mahaifiyarta k'warai da gaske,sai dai maganganun su Alhaji sun yaye mata babban kaso a zuciyarta da yake tsananin jin haushin Malika,domin kuwa itama ba da son ranta akai hakan ba,hasali ma bata san za a yi ba sai yau ɗin.
Babu wanda ya yi mata musu haka ta koma ciki,ta ɗebi kayan ta a leda ta bar wa Malika nata a akwati ta bi bayan Jubair,a mota babu wanda ya kula kowa har suka isa gida,suna zuwa ta hau kiciniyar buɗe ƙofa za ta fita,Jubair ne ya riƙe hannun ta ya ce.
"Sweetheart dan Allah ki sanyawa zuciyar ki salama,ita wadda kike tayawa kishin ma bata damu ba,and kar ki tsani ƴar'uwar ki saboda itama bata san...."
"Daddy please maganganun sun isa haka,daidai gwargwado babu kalar bayanin da baku yi mana ba ɗazu na kuma ji na amince ƙaddara ce ta sa zaka aure ta,ina so kar ka dawo da ciwa Mommyna mutunci da yi mata faɗa saboda zaka ƙara aure,idan ka ɓatawa Mommyna ba zan yafe maka ba."
Cikin kuka ta buɗe motar ta fita ta shige gidan da gudu,Uwa da ta fito dan tarbon Jubair ce ta ga wucewar Kubrah cikin sashen Ruƙayya ta na kuka,dariya ta yi mara sauti kafin ta ce.
"An yi dare gari ya waye kenan,to alhamdulillahi,ko ya ita rigimammiyar Papan take oho."
Cike da yanga ta ƙarasa jikin motar da Jubair ke zaune ya lumshe ido yana cikin matsananciyar damuwa,cike da kashe murya da yanga Uwa ta ce.
"Ranka ya daɗe mamallakin zuciyar ƴar shila mijin tsofaffin mata me ya same ka ka ke zaune a mota? Taso mu shiga daga ciki kar ka bar abin faɗe wajen masu aikin gida,kasan kaɗan suke jira su saka faifanmu."
Jubair ya gane magana ta ke gaya masa,sai dai bashi da lokacin bata amsa,sai kawai ya buɗe mota ya kulle ta kafin ya wuce ta ya shiga sashen Hajiya Dada,Uwa kuwa taɓe baki ta yi ta wuce ɗakin shi ta jera masa abinci sannan ta samu waje ta zauna ta hau chatting da ƙawarta ta na labarta mata yanayin da Jubair ya dawo da shi.
A can ɓangaren Hajiya Dada kuwa Jubair ne zaune ya gama bata labarin duk abinda ya faru,murmushi Hajiya ta yi kafin ta ce.
"Na zaci bomb ɗin da yarinyar nan zata tayar sai ya ƙona garin Yola,ashe ma rashin hankalin nata da sauƙi,to alhamdulillahi da Allah ya ƙara taƙaita damuwa,yanzu sai ka dage ka kafa soyayyar ka a ran ta,ba wai soyayyar ƴa da uba ba,ita kuma Kubrah ka barni da ita na san ta inda zan ɓullo mata."
"Dama ni yanzu damuwa ta kenan Hajiya,na san ta Malika mai sauƙi ne,a hankali idan ta cire tinanin alaƙar mu watarana za ta so ni,amma bana son Malika da Kubrah ƙi junansu."
"Inshaa Allahu haka ba zata faru ba,muna nan muna addu'a Allah zai shiga lamarin."
Anan Jubair ya ɗan taɓa abinci sannan ya miƙe ya nufi sashen Ruƙayya,a zaune ya tarar da su Ruƙayya da yaran tana sharar hawaye Kubrah na taya ta gogewa,wata iriyar karaya zuciyar shi ta yi wadda yake jin har abada ba zai samu mai ɗorata ba,yana son Ruƙayya,baya son duk abinda zai sosa mata ranta. Cikin sanyin jiki kamar magulmacin da aka kama yana tsakiyar gulma ya ƙarasa shiga parlour'n,da sauri Ruƙayya ta hau goge hawayen ta tana yaƙe tace.
"Ahh Daddyn Mubeena ka dawo? Sannu da dawowa."
"Zo nan matata ƴar aljannah,taho ki taya ni baiwa princess Kubrah haƙuri,yau dai akan taya ki kishi har warning aka yanka min mai tsada."
A zaton shi zai ga Kubrah na murmushi,sai ya ga ta miƙe ita da sauran ƙannen ta sun shige ciki sun basu wajen,yaƙe ya yi sannan ya ce.
"Kin ga ƴan albarka ko? To gwanda ma ki faɗa musu babu mai shiga tsakaninmu,tare suka gammu da ke ah toh."
Murmushi kawai Ruƙayya ta yi sannan ta ce.
"Ai kuwa dai,nima abinda nake nuna musu kenan,haƙuri shine jigon rayuwa har mutum ya kai matakin nasara akan abinda ya sa gaba."
"Tabbas ! Maganar ki gaskiya ne,dan haka na baki wuƙa da nama,ki zama ji na da gani na a wajen yaran nan,ki wakilce ni wajen yi musu bayani da basu haƙuri,Allah ya yi muku albarka dikan ku,ƴar gidan ki ta ce na gaishe ki kafin na taho,ko har Kubrah ta riga ni isar da saƙo?"
"Eh ta sanar dani,ina godiya,Allah ya nuna mana ranar auren ku."
Ba tare da Jubair ya amsa adduar Ruƙayya a fili ba ya tashi ya wuce sashen shi,sai ya ji nauyin da yake ji a baya ya ragu masa,dik da cewa a cikin zuciyar shi bai samu wata natsuwa ba balle kwanciyar hankali.
Koda ya koma wajen Uwa ya tarar da bata parlour har ta kashe wuta ta wuce bedroom, ko ta kan abincin be bi ba saboda yanda yake jin cikin shi a cushe da damuwa,ruwa kawai ya sha ya wuce banɗaki ya yi wanka ya yi brush sannan ya ɗaura alwala,sai da ya yi sallar isha'i da bai yi ba sannan ya jera shafa'i da wutiri ya naɗe abin sallah ya ajiye a inda suke ajiyewa,gado ya samu ya haye ya kwanta a gefen Uwa dake kallon shi tana ayyana abubuwa da dama a cikin ranta...........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 19:
Ba ƙaramin kai ruwa rana aka yi ba tsakanin Jubair da Malika kafin ta haƙura ta sakko daga dokin naƙin da ta hau,dan kuwa sai da ya yi mata alƙawarin kai ta shopping da gidan kakannin ta sannan ta amince za ta bishi. Mamakin kafiya da shagwab'a irin ta Malika ce ta sanya shi zama a mota ya yi zugumm ya na tunanin darun da za ta yi masa a duk sanda aka aura mata shi a matsayin miji. Yana nan zaune suka fito cikin shiri ita da Kubrah da madaidaicin akwatin su a hannu sai hand bag,kallon Kubrah ya yi da mamaki,dan bai tsara yin tafiyar da ita ba,jiki babu ƙwari Kubrah ta isa jikin motar shi ta ce.
"Daddy na ga kana kallo na ko in koma gida ne? Daddy dan Allah kar ka ce in koma ina so in bi Addah Malika please Daddy."
Murmushi ya yi mata kafin ya ce.
"Ai kin riga da kin kashe bakina tinda ki ka haɗa ni da Allah,shiga mu je,Mommyn ku bata dawo bane har yanzu?"
Kallon juna yaga yaran sun yi a lokaci ɗaya da mamaki a fuskokin su,shi kanshi ya yi mamakin tambayar Ruƙayya da ya yi duba da yanda yake jin matsananciyar tsanar ta da haushinta a kwanakin nan,kafin Kubrah ta bashi amsa gate ya buɗe,motar Ruƙayya ta shiga cikin gidan,ido Jubair ya kafe ta da shi,nan take ya ga yanda ta faɗa ta rame tai haske sosai,tausayinta ne ya kama shi dan haka cikin azama ya buɗe motar shi ya isa gare ta,riƙe take da jakar ta bayan ta yi parking ɗin motar ta a wajen da ta saba ajiyewa ta fito,daga ɗan nesa da shi ta tsaya gudun kar ya ce ta na wari,gaishe shi ta yi tare da isar masa saƙon gaisuwar da iyayenta suka bata,langaɓe kan shi ya yi gefe sannan ya ce.
"A haka dama muke yin barka da dawowa Ruƙyna?"
Cikin sauri tare da murmushi mai sauti Ruƙayya ta kalli Jubair dake murmushi,ba tare da tunanin masu aiki na kallon su ba ta isa gare shi ta faɗa a ƙirjin shi,babu ɓata lokaci Jubair ya rungume ta yana lallashin ta,cikin muryar shi dake ɗauke mata duk wata damuwar da take ciki Jubair ya ce.
"Menene na kuka kuma? Dan Allah ki yi haƙuri ki yafe min duk abinda na yi miki a kwanakin nan,ni kaina ban san me yake damuna ba,iyaka na san a yau ɗinnan na sanar da Hajiya Dada matsalata ta yi min addu'a sosai,nima kuma na dage na yi addu'a akan Allah yasa na ci gaba da farantawa Ruƙyna rai a koda yaushe."
Ba tare da Ruƙayya ta ce komai ba ta saki murmushi cike da jin kunyar shi ta fara ƙoƙarin shiga cikin gidan,Malika suka gani tsaye ta na ta ɗaukan su hoto tana murmushi,Kubrah na gefen ta tana dariya ƙasa-ƙasa,cikin dariya Malika ta ce.
"Papa na sauya favorite couples d'ina daga yau,amma kar ka faɗawa Daddy."
Dariya Jubair ya yi kafin ya ce.
"Ohhh na gane me kike nufi,tom shikenan muna godiya ba kuma zan sanar da Daddyn ki ba,yanzu ku wuce mu je dare na yi,amm dama zan kai su gidan su Samhah ne su ɗan yi sati biyu haka."
Da jin haka Ruƙayya ta gane me yake nufi,ji tayi wani irin kishin mijinta ya daki zuciyarta,murmushin yaƙe ta yi kafin ta ce.
"Ohh babu komai,Allah ya kai ku lafiya,idan kin je ki ce ina gaishe da Innah Habi da sauran mutanen gidan."
"Za su ji,amma fa ni Mommy bana son zuwa,Innah Habi faɗa ne da ita,duk sanda ta kai mana ziyara barin gidan nake na koma gidan su Elsa,ta fiya ƙorafi akan komai na yi,tana cewa ba a koya min komai ba kamar ba jinin fulani ba."
"Kar ki damu,inshaa Allahu zaku zauna lafiya,musamman ma da yake baki taɓa zuwa Nigeria ba, za ta ji daɗi sosai idan ta gan ki."
"Allah yasa to."
Suna hira sama-sama suka isa bakin motar Jubair, Ruƙayya da kanta ta buɗewa Malika gaba ta saka ta a cikin motar kafin ta rufe ta ja baya,sai da Jubair ya yi mata wani kallon soyayya tare da hura mata kiss sannan ya shiga ya zauna,Kubrah kuwa dama ta jima da shigewa sai ta hau ɗagawa mommyn nasu hannu.
Suna fita a harabar gidan ta ga gilmawar Ubaida ta shige sashen Uwa cikin sauri,murmushi kawai ta yi ta kalli wajen da masu aikin gidan maza ke zaune,cikin takun ta mai ɗaukan hankali ta shige ta gaishe da Hajiya Dada kafin ta wuce sashen ta ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka.
Sai da su Malika suka fara siyan sim card aka yi mata register layin sannan suka wuce shopping,dogayen riguna uku ta ɗauka sannan ta kwashi kayan kwalama,sai ta saiwa kakannin nata turaruka da fruits,Kubrah kuwa sarkin kwalliya kayan kwalliya ta kwasa Jubair ya biya kud'in sannan suka wuce Bekaji.
Suna isa Malika ta ga gidan kakanninta kamar yanda ta yi tsammani,gida ne mai kyau sosai wanda ke nuni da irin dukiyar da masu gidan suke da ita,sai da mai gadi ya tabbatar da alaƙar su da masu gidan kafin ya buɗe musu su shiga,wani matashi ne ya yi musu jagora bayan ya ɗauki kayan da su Malika suka fitar ya kai su har parlourn da yake na baƙi.
Basu wani jima a zaune ba wata dattijuwa mai ƙaramin jiki ta fito,baki ta washe haƙoran makkan ta suka bayyana,tana ganin Malika sai ta buɗe mata hannu,cikin sauri Malika ta nufe ta suka rungume juna,da hannu Innah Habi ta kira Kubrah,cikin jin kunya ta isa gare ta,rungume ta Innah Habi ta yi kafin su samu waje a doguwar kujera su zauna.
Jubair ne ya zame daga kujerar da yake zaune akai ya gaishe,cikin mutuntawa Innah Habi ta ce.
"Lafiya kalaou Jubair,ya wajen Hajiya Dada? Zumunci ya yi mana wuya ana gari ɗaya,tsufa da yawan ciwo duk ya hana zumunci."
"Ta na nan lafiya ƙalou alhamdulillahi,ta ce ma a gaishe ku sosai."
"Allah sarki muna amsawa,Alhaji na nan fitowa ya na ɗan kammala wasu ayyuka ne."
Sallamar Alhaji ce ta katse musu hirar su,cikin girmamawa Jubair ya miƙe ya isa har inda dattijon yake ya bashi hannu suka gaisa, wajen zama Alhaji ya nunawa Jubair kafin ya amsa gaisuwar su Malika.
Cikin fara'a da sakewa Alhaji yake ta jan su Malika da wasa,a haka aka kawo musu abun taɓawa,lemo kawai Jubair ya kurɓa ya ajiye,su Malika ma ruwa da lemon kawai suka sha,daga ƙarshe Innah Habi ta kirawo mai aikinta ta kai su Malika ɗakin da za su zauna, bayan fitar su ne Alhaji Kabir Manga ya kalli Jubair ya ce.
"Shekaran jiya Ammar da wannan yarinyar sun kira sun yi mana bayani game da auren ka da Malika,sai dai yanda kuke son a ɓoye mata mijin da zata aura tsarin bai yi min ba gaskiya,dan ban ga dalilin ɓoye mata mutum mai nagarta kamar ka ba a matsayin mijin da zai aureta,da kai da Ammar yara ne ku masu hankali da kamala,tinda muke bamu taɓa jin Samhah ta faɗi wani abun assha akan ku ba,ku yara ne da kowanne uba zai so ace ya aurawa ƴar shi ɗaya daga cikin ku,dan haka nake ganin ko an sanar da ita hakan ba laifi bane."
Cike da tsananin farin cikin samun nasara Jubair ya sunkuyar da kai ya ce.
"Alhaji na gode sosai da karamci tare da yabawar ka a gare mu ni da ɗan'uwana Ammar,amma ina so ka sani ba na ce a ɓoye mata bane dan wani abu face sanin halinta da muka yi wajen tirjiya akan abinda bata da ra'ayi akai,muna so sai bayan an ɗaura auren sai na sanar da ita a hankali ta yanda abun ba zai dame ta ba,domin ita a uba take kallo na ba wani mutum na daban ba."
"Nima dai ina goyon bayan ku Jubair,dan wannan botsararriyar yarinyar na sha jin labarin idan ba kai ɗin ba babu wanda take gani da gashi,to kaga kuwa gwanda ku je can ku ƙarata idan ma botsarewar za ta yi ka san ya zaka yi da ita."
Murmushi Alhaji ya yi kafin ya ce.
"To da alama dai kun yi galaba akai na,haka ma Abubakar da Umaimah suka ce jiya da na sanar da su,to ubangiji Allah ya sanya alkhairi da albarka ya baku zaman lafiya da iyalin ka baki ɗaya."
"Amin Alhaji,ni zan wuce,na gode da haɗin kan da kuka bani akan wannan lamarin,Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma,a cikin satin nan za a kawo lefe, Juma'a ta sama kuma a ɗaura aure."
"Ah ah ku ajiye lefen ku a can gidan da za ku tare ba sai an kawo nan ba tinda ba wani taro za a yi ba,sai dai kuma idan akwatin faɗar kishiya za a min."
Dariya sosai Jubair ya yi kafin ya yi musu sallama ya wuce ba tare da ya sake ganin Malika ba,tafiyar shi babu jimawa aka hau kiraye-kirayen sallar magariba,masallaci Alhaji ya wuce su Malika kuwa suka yi sallah a ɗakin su.
Suna nan a zaune a parlour Umaimah ta dawo daga aiki,tana aiki ne a babban asibiti na garin Yola,murma sosai suka yi da ganin junan su ita da Malika,nan take ta hau kiran ta da Amarya,cikin ruɗani Malika ta kalle ta ta ce.
"Aunty Umai wacece amaryar kuma?."
"Ke mana Queen Malika nake nufi,ko baki da labarin yau saura kwana goma a ɗaura maki aure da haɗaɗɗen mijin ki na nunawa sa'a?"
Innah Habi ce ta shigo ta ga yanayin Malika dake a rikice sai ta dafe goshi ta zauna ta ce.
"Wai me yasa Umaimah ba kya tunani ko dogon nazari kafin ki yi magana? To yanzu da kika sanar da ita wa kika yi shawara da shi a gidan nan?"
"Dan Allah Innah ki yi haƙuri,nifa na zaci ta riga ta sani duba da cewa.."
"Ya isa haka ! zo nan Malika na sanar dake abinda ke faruwa."
A ruɗe Malika da Kubrar ke kallon bayin Allah'n dan son gasgata abinda suke sanar da su,idanun Malika tini suka fara zubar da hawaye,jiki a sanyaye ta zauna a gaban Innah Habi ta tanƙwashe ƙafafun ta ta na kallon ta,cikin kalamai na hikima Innah Habi ta sanar da ita Iyayenta da Papan ta ne suka sama mata mijin aure,shine dalilin da ya sa Papa ya kawo ta gidan. Kuka Malika ta dinga yi kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu,wata iriyar tsana da jin haushin Jubair da iyayenta ne suka dirar mata a cikin zuciyarta, dama sun rabota da mahaifarta ne dan su yi mata auren dole irin na Fulani da Hausa da take yawan jin labari a wajen iyayen nata? Dama Jubair da ta ɗauki matsayin uba ta bashi zai iya nakasa rayuwar ta? Ya zata yi da karatunta da take so ta ci gaba da yi? Wanene mijin da Iyayen nata da Papan suka zaɓa mata shin tsoho ne ko yaro matashi? Sun ma san kalar mijin da take da buri da fatan aure ne a rayuwarta? Har yanzu fa bata cika shekara 18 ba,wannan ai child abuse ne suke son su yi.
Da gudu Malika ta tashi ta wuce ɗakin da aka sauke su ta hau neman wayar ta,tana samun wayar ta ɗauka ta cire password ta nemo lambar Jubair ta hau Kiran shi babu ƙaƙƙautawa,Jubair kuwa a daidai wannan lokacin yana masallaci yana azkar ɗin yamma kafin a yi isha'i ya yi ya koma gida,jin ringing ɗin ya ƙi ƙarewa ne ya sanya shi ɗaukan wayar ya fita daga cikin masallacin. Kukan Malika ne ya daki dodon kunnen shi,da sauri ya sauke wayar ya duba ya ga tabbas sabuwar lambarta ne da aka haɗawa layi ɗazu,cikin sauri bakin shi na rawa Jubair ya ce.
"Babyna waye ya taɓa min ke? Ko in dawo in ɗauko ki mu dawo gida ne?"
Cike da matsanancin kuka Malika ta ce.
"Papa kun rusa min rayuwata, da na san abinda kuka ƙulla min kenan tabbas da ban amince na biyo ku ba,na ɗauki soyayyar mahaifi na baka,na baka yardata da amanata amma ka ci amanata,bana son wannan auren da za ku yi min,bana son koma wanene za ku aura min,ina so ku janye maganar auren nan idan ba haka ba za ku rasa ni,rasawa ta har abada."
Wani iri saukar dalma kalaman Malika ke yiwa Jubair a cikin zuciyar shi,shin wanne me yoyon bakin ne ya sanar da ita abinda ke faruwa tin yanzu? Lallai yau ya jinjinawa haukan Uwa,tinda duk haukanta da baƙin kishinta ta iya jurewa ta danne bata sanar da Malika abinda ke faruwa ba,ya tabbata wannan ɗanyen aikin bana Innah Habi ko Alhaji bane,to waye ya fallasa sirrin da ake ɓoyewa Malika?
Buɗe baki ya yi zai yi magana ya ji ashe ta kashe wayar,layinta ya fara nema dan ya lallashe ta sai ya ji baturiya na sanar da shi lambar a kashe take,cikin tashin hankali Jubair ya faɗa mota ya tada ita ya hau saman titi......
RUBUTAWA :HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️
Wannan littafin na kuɗi ne,idan kina son karantawa har ƙarshe biya #500 ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi ko kuma 0006366584 Ja'iz Bank Hamidatu Sanusi Ahmad. Ki tura shaidar biya ta,09031416423. Mutanen Niger kuma za ku iya biya ta 96988833
Soueba sani idi,sai ku tura shaidar biya ta 09031416423.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya