ya yi ya ga yanda suka rungume juna suna kuka, miƙewa ya yi ya ɗauki wayoyin shi ya fita. A bakin ƙofa ya tarar da Kubrah ta na ta kaiwa da komowa,tana ganin Jubair ta tsorata da yanayin fuskar shi,cikin rawar murya da saurin baki ta ce.
"Daddy na ce mata ba za ka amince mu yi party a wajen pool ba sai dai a babban parlour,i swear babu ruwa na Daddy."
Murmushin yaƙe ya yi ya kalle ta ya yi mata nuni da hannu akan ta je wajen shi,a tsorace ta ƙarasa inda yake ta duƙar da kanta,har a wannan lokacin bata manta yanda ya shiga sashen su ba yana yiwa Mommynta magana cikin ɗaga murya,wanda hakan bai taɓa faruwa ba,cikin sauke wata nannauyar ajiyar zuciya Jubair ya ce.
"Kubrah na taɓa dukan ki?"
Da sauri ta girgiza kai alamar ah ah,sake rungume ta ya yi a jikin shi sannan ya ce,
"To me yasa kike jin tsoro na?"
"Daddy naga kana fushi da Mommy kuma kana ta faɗa,abinda ba halin ka bane."
"Good, Alhamdulillah tinda kin san ba halina bane,ina buƙatar addu'ar ki,ban san me yake damuna ba,ban san me yake damuna ba this days,yanzu dai ku yi party amma banda wajen pool,bana son wani ya ƙara shiga ya kasa fitowa,ni zan yi ma magana da Munkaila a zubar da ruwan a bar wajen haka."
"To Daddy mun gode,amma muna so mu je shopping."
"Kar ki damu zan tura maki,bari naje wajen Hajiya...andd zaki iya shiga ciki,just for today."
Ya ƙarasa maganar shi yana nuna mata da yatsan shi,a tare suka yi murmushi kafin ya wuce wajen Hajiya,da sauri Kubrah ta nufi sashen Jubair ta shiga tana murna,ganin Malika na sharewa Mommynta hawaye ne ya sa jikinta yin sanyi,a sanyaye ta zauna kusa da Mommyn nata ta ce,
"Mommy menene yake faruwa?"
Cikin yaƙe Ruƙayya ta ce,
"Babu komai,kawai ina kewar ƙaninku ne."
"Mommy ki yi haƙuri ki dena kuka,kina da mu zamu zame maki tamkar yara mazan da ake da burin ki haifa a gidan nan watarana,dan Allah ki daina kuka."
"Inshaa Allahu ban cire ran zaku zama wani abu ba watarana,daga yau na miki alƙawarin ba zan sake kuka ba,hawayen baƙin ciki sun gama zuba daga idanuna sai na farin ciki,ki sa a ran ki duk sanda kika ga ina hawaye to na farin cikin samun nasara ne daga cikin nasarorin da na sa a gaba a rayuwata."
Yanda Ruƙayya ta dake tana magana ne ya basu tabbaci tare da gasgata kowacce kalma da ta fito daga bakinta,dan haka warewa suka yi suka ci gaba da tsara yanda za su yi partyn su.
"Yanzu yanda za a yi mu je mu gayyaci ƙawayena,after magrib sai mu je shopping ko ya kika ce?"
"Yes this is a very good idea sis,lets go."
Cike da farin ciki suka bar parlourn Ruƙayya na bin su da kallo har suka ɓacewa ganin ta.
Da magariba su Malika na idar da sallah suka shirya dan zuwa shopping,Hajiya Dada na nan zaune ta na jiran ta ga shigar da Malika za ta yi su haura,sai ta ga ta sanyo ɗaya daga cikin ɗinkin da Salman ya kawo mata da rana, ɗinki ne riga da skirt mai kyau,ɗankwali kawai ta ɗaura ta riƙe wayarta za su tafi,Hajiya ce ta kalle ta a karkace ta mere baki ta ce.
"Ke wannan farar balbelar wai a haka zaki fita? To ba dani ba gaɗa a kufai,ke Kubrah ki bata mayafi,idan kuma ba zata yafa ba ta bar fitar."
Tura baki Malika ta yi tana jujjuya jikin ta alamar tana son yin kuka,Jubair ne ya shiga hannun shi riƙe da makullin mota ya na saka agogo a hannun shi ya ce.
"Idan kun shirya ku wuce muje na ajiye ku,bana son fitar daren nan dan dai kun dage ne,amma banda abinku ai da da safe zaku je tinda partyn sai gobe da yamma."
Kamar ba Malika bace ke fushi a da,tini ta ware ta nufe shi ta karɓi agogon tana karasa saka mishi ta ce.
"Papa yanzu muke son zuwa,saboda gobe zamu je saloon a wanke mana kai da ƙafa,ni ina so na gyara nails d'ina ma."
Cikin sauri Hajiya Dada ta ce,
"A ina za a ƙara saka mana wannan faratan? Ai yankan farce zan miki yarinya,dama ɗaga maki ƙafa nake dan kar ki ce na takura miki,amma ba wanda ya isa ya sake loda mana farcen arna a gida."
Narkewa Malika ta yi cike da kyaɓe baki irin na shagwab'a ta ce,
"Papaaa ka ga Hajiya kooo?"
Dariya Hajiya da Jubair suka sanya kafin ya ce,
"Ai duk abinda Hajiya ta zartar a gidan nan ya zauna Babyna,ballantana ma ba faɗin Hajiya bane,ai ko a musulunci hakan ba daidai bane,idan kika zo yin alwala wajen da kika sakawa nails ruwa baya shiga,kin ga kin bar lam'a kenan ko? To ya zaki yi da azabar Allah ranar gobe ƙiyama akan barin lam'a da kika yi? Ai yanzu godewa Hajiya zaki yi sannan ki hau istighfari."
Shiru Malika ta yi tana tuna yanda Mahaifinta ke hana ta sanya farce da ƙarin gashi,dik kuwa da cewa tana daga cikin matan da Allah ya azurta da gashi mai tsawon gaske da cika,amma idan ta tashi haka zata ƙara ta saka farata da gashin ido,suna tsaye Kubrah ta dawo riƙe da mayafi ta baiwa Malika,su Ihsaan da Mubeena ne suka yiwa Hajiya sallama suka fita.
Suna zuwa wajen da motoci suke sai suka ga Uwa a tsaye ta sha riga da wando sai ta ɗora after dress a sama,sai tashin ƙamshi take yi,tin kafin magariba Ubaida ta kai mata rahoto shi yasa ta shirya dan a tafi da ita,ta yi kyau sosai sai dai da ka ga kwalliyarta kasan bata saba kwalliya ba,Jubair ne ya kalle ta ya na murmushi ya ce.
"To Auntyn yara sai ina kuma?"
Yatsina fuska ta yi tana kallon Malika da kyawun ta ke matuƙar tsone mata ido ta ce,
"Inda duk kuka yi niyyar zuwa."
Tsaki Malika ta yi ta wuce tayi gaba ta tsaya jikin motar da take tinanin da ita zasu fita,ganin haka ne ya sanya su Kubrah cewa.
"Daddy mu kirawo Mommy mu tafi da ita itama?"
Wani irin ɓacin rai ne ya taso masa,amma ganin yanda Malika ta kafe shi da ido tana jiran ta ji amsar da zai bayar,sai ya yi yaƙe ya ce.
"To ai motar ba zata ishe mu ba."
"Sai mu ɗauki waccan."
Inji Malika da ta nuna wata ƙatuwar mota mai masifar kyau,babu yanda Jubair ya iya haka ya sa Uwa dake ta cika tana batsewa ta d'akko masa makullin motar,kafin ta dawo Kubrah ta kirawo Mommyn su,kamar babu abinda ya faru haka Ruƙayya ta fito,duk ta bulbule jikinta da turare gudun kar Jubair ya sake cewa tana wari,a gaba ta zauna Uwa ta zauna a bayan kujerar da Jubair yake yaran duk suka shiga suma suka yiwa kansu wajen zama. Cike da rashin mutunci Uwa ta toshe hancinta ta ce.
"Hummm menene yake wari haka kamar warin mushen jaɓa?"
Gaba ɗaya yaran kallon ta sukai dan kuwa su dai basu jin wani wari,Jubair ne ya buɗe windows ɗin motar sannan ya tsartar da yawu waje kafin ya tada motar yana ƙunƙuni,Uwa na ganin halin da Jubair ya shiga da yanda Ruƙayya ta muzanta sai ranta ya yi mata fari ƙal,haka ta dinga fitar da kai ta na tsartar da yawu ita a dole wari ya ishe ta,a haka suka isa super market suka yi siyayya mai tarin yawa,Jubair ya biya suka kama hanyar komawa gida.........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE....
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 15:
A duƙunƙune ta tarar da ita a bargo tana ta sharar baccinta hankali kwance,ba dan kayan sallar da Kubrah ta gani a watse a ƙasa ba,to da ta ce ko sallah bata yi ba,a hankali ta fara tashin ta tana faɗin.
"Queen tashi mu je mu fara aiki safiya ta yi."
Cikin magagi Malika ta ja bargon ta ta sake rufe jikinta da kyau ta na faɗin,
"Mom please give me 10 more minutes."
Dariya Kubrah ta yi ta yi tsalle ta faɗa gadon ta na cewa.
"Ke ni ce Hadizatul Kubrah ba Mom ba,zaki tashi mu tafi ko sai Hajiya ta zo tashin ki da kan ta?"
Malika ce ta hau shure-shure tana kuka ƙasa-ƙasa ta ce,
"Kin dame ni Kubrah,ina so na yi bacci,jiya mun kwana video call da su Mark,bacci nake ji sosai dan Allah ki barni na koma."
"Hajiya Dada ce da kanta tin jiya ta ce idan zamu je aikin abinci na je da ke,so kike yi ta yi mana faɗa? Dan Allah taso mu tafi."
Kamar Malika za ta yi kuka haka ta tashi rai a ɓace,duk jan jikin da ta dinga yi bai sa Kubrah tafiya ta barta ba,sai da ta yi brush ta yi wanka sannan ta saka wata ƴar yaloluwar riga mai siririn hannu,ko guiwarta bata ƙarasa rufewa ba a haka ta ɗaure gashin ta suka fita,ita dai Kubrah tana da tabbacin da Hajiya ta ɗora idanu akan Malika zata kora ta zuwa sauya kaya,dan haka sai ta yi shiru kafin ta kai ta maƙura dan kuwa ta ga yanda take a hasale saboda tashin ta da akai daga bacci.
Koda suka fita waje ta bayan ɗakunan gidan Malika ta hango wani fili har da swimming pool a wajen sai ta manta da ɓacin ran da take yi ta nufi wajen da gudu tana ihun murna,cike da farin ciki Malika ta ce.
"Dama kuna da pool baki faɗa min ba Kubrah,ya kamata ki gayyato mana ƙawayen ki a weekend ɗin nan mu yi pool party,dama Papa ya yi mana alƙawarin haɗa mana party."
A rikice Kubrah ta hau kiran Malika ta ce,
"Malika ki dawo nan,an hana mu zuwa wajen nan babu ruwa na,ni tsoron ruwa nake ji."
"Ke kike tsoron ruwa ni bana tsoron shi."
Kafin Kubrah ta yi wani yunƙuri Malika ta faɗa ruwa,ƙara ruwan ya bayar "Tinjimmmm" dariya sosai Malika ta saka ta hau iyo, Kubrah kuwa na ganin za ta ɓata mata lokaci sai ta bar wajen ta na faɗin.
"Ni dai babu ruwa na,tinda kin iya ruwan kin fitar da kan ki,na wuce sai kin taho."
"I need some towel please."
Malika ta ɗaga murya tana faɗawa Kubrah.
"Ai kuwa babu ruwana ni na yi nan."
Kubrah kitchen ta wuce ta tarar da Kulu har ta hura wuta ta marƙada kayan miya tana tafasa nama,yanka albasa da kayan lambu ta zauna tana taya Kulu,Ubaida sai wani tura baki take yi ita a dole ga mai aikin amaryar gidan,babu wanda ya kula ta suka ci gaba da aikin su. Wutar da Ubaida ta haɗa har ta kama sosai nan da nan ta ɗora tata sanwar,a daidai wannan lokacin ne Hajiya Dada ta fito ta same su suna aiki tuƙuru,domin kuwa bayan abincin da ake baiwa iyayen Jubair har da na sadaka da ake baiwa almajirai,dube-dube Hajiya Dada ta hau yi bata ga Malika ba,kallon Kubrah ta yi ta ce mata.
"Ke me na faɗa maki jiya? Ina ita wannan uwar son jikin kamar mage take?"
Cike da tsoron faɗan da Malika ke shirin janyo mata ta kalli Hajiya Dada ta ce.
"Se da na hana ta na ce kar ta je,amma ta ƙi kula ni."
Hajiya Dada na jin haka ta gane me Kubrah take nufi,kaɗa kai kawai ta yi ta ce.
"Ku ci gaba da aikin ku,dama me nake tunani ma da na ce ta zo taya aiki? Wannan ko a gas ko a electric stove aka ce tai girki ai sai an kai ruwa rana."
Kulu ce ta yi dariya kafin ta ce,
"Ai kuwa dai nima na yi wannan nazarin Hajiya, yarinyar da ko abinci ta ci sai an ɗauke kwano me zata iya?"
Murmushi kawai Hajiya Dada ta yi ta zauna a kujerar da takan zauna a duk sanda ake aiki,nan da nan girke-girke suka kankama,daga an soya wannan a sauke a ɗora wancan,a haka har suka gama Malika bata ji zata baro wajen ruwan nan ba.
Tinda suka kammala suka kwashe komai suka kai babban parlour'n gidan inda baffanin Jubair da manyan baƙi ke zama, daga nan sai suka zuba na sadakar da suka sa a robobin take away suka zuba a buhu,Munkaila TK da Baba Mai gadi ne suka dinga rabawa almajirai abinci da lemon roba,su kuwa su Kulu sai kowa ta wuce sashen da take dan yin wanka su shirya. Hajiya Dada bata sake bi ta kan Malika ba dan bata son ɓatawa kanta lokaci,ita kuwa gimbiyar tana can ta yi wanka ta gaji ta yi hotuna da videos sai ta yi zaman ta a ɗaya daga cikin kujerun dake wajen,daga nan bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita,a haka kayan jikinta suka bushe.
Tinda Jubair ya tashi ya shiga gaida Hajiya Dada be saka Malika a idanun shi ba,babu inda bai leƙa ba da Hajiya na wajen girki dan neman Malika amma bai same ta ba,nan take ya shiga WhatsApp ya yi mata magana ya ji shiru babu amsa,tunanin shi ya bashi da dikkan alamu tana sashen Ruƙayya,dik da cewa ranshi baya son sanya ta a idanun shi haka ya nufi sashen nata rai a matuƙar ɓace.
Yana zuwa bai kula kowa ba ya fara ƙwalawa Malika kira,cike da mamaki Ruƙayya dake zaune a parlour ta na karyawa ta ɗaga kai ta kalle shi,a ganin ta ai ko darajar sallama ta ci a wajen shi ballantana ma basu gaisa ba,rabon da ta saka shi a idanun ta tin jiya da safe da za su je gaishe da Hajiya Dada,murmushin yaƙe ta yi ta danne ɓacin ran dake cikin zuciyarta ta gaishe shi,kallon ta ya yi rai a ɓace ya ce.
"Ina Baby? Na duba ko ina ban ganta ba."
Kubrah ce ta shiga parlour'n ta ji abinda mahaifin nata ke faɗi,cike da rawar murya ta ce,
"Daddy ta na pool area,na hana ta amma..."
A tsawace Jubair ya ce,
"Kin manta me ya faru a wajen ne ki ka barta ta je? Ko so kike itama idan bata iya ruwan ba ta yi drowning?"
A hasale Jubair ya fice ya bar sashen Rukayya ya nufi pool area,yana isa ya ganta kwance a kujera tana kallon sama tana baccin ta hankali kwance,tsayawa Jubair ya yi yana kallon ta,nan take wani irin kwanciyar hankali da natsuwa suka fara shigar shi a hankali,nan take abinda ya yiwa Ruƙayya da Kubrah ya dawo masa a ran shi,cikin zuciyar shi yake ayyana.
'Shin me yake damuna ne? Me yasa bana son ganin Ruƙyna? Me yasa nake yiwa Kubrah ihu? Tabbas akwai abinda ke damu na,this is not me.'
A hankali ya isa wajen da Malika ke kwance ya tashe ta,cikin haɗe fuska dan kar ma ta kawo masa raini ya ce,
"Me kike yi anan bayan kin ji an sanar dake na hana zuwa? Ke baki jin bari ko? Maza wuce mu je ciki,ki wuce wajen Mommyn ku ta baki wasu kayan ki saka,bana son na ganki da wannan kayan again,ko baki san gidan akwai wasu mazan dake aiki ba?"
"Me yasa zan saka kaya manya a gida? Ni na riga na saba ko makaranta zanje ko party ko mall da irin wannan nake yawo,me yasa kuke son takura min ne?"
Yanayin yanda take magana tana kallon cikin idanun shi alamar babu tsoro a tattare da ita ne ya sanya shi rage murya ya ce.
"Baby Uncles d'ina ne za su kawo mana ziyara yau,suna zuwa every friday a gaisa a yi zumunci su tafi,shi yasa nake so ki suturce jikin ki,sannan ke yanzu baki ga alamun ajin ki yana zubewa ba idan su Munkaila da Tk na kallon jikin ki? Masu aikin gidan nan ne fa,come on baby kin wuce haka mana."
Kanta ta ji ya yi girma saboda yabon da akai mata,ɗan tura baki ta yi sannan ta ce,
"Na ji zan sauya kaya,amma ba zan dinga takura kaina ba idan ina ɗaki."
"Na amince mu je ciki."
Hannun shi riƙe da na Malika suka kama hanyar shiga cikin gidan,a daidai wannan lokacin ne motocin Uncles ɗin shi suke shiga gidan,cikin sauri ya zare hannun shi a nata ya ce ta yi sauri ta shiga wajen Hajiya,kallon shi kawai ta yi ta ci gaba da tafiyar ta yanda ta ke yi tin a farko,cike da kunya Jubair ya ƙarasa wajen Uncles ɗin nashi da suka fito a mota suna bin Malika da kallon mamaki,hannu Jubair ya isa yana miƙa musu,bayan sun gama gaisawa ne suka ɗunguma zuwa babban parlour.
Sai da suka zauna suka sake gaisawa,sannan suka hau hirar zumunci,daga nan kuma suka ci abinci suka sha,su Munkaila ne suka fara tattara kayan wajen suna kaiwa kitchen ɗin baya inda su Kulu ke aiki. Sai da komai ya lafa ne Ruƙayya da yaranta da Uwa suka shiga suka gaishe su,suna gama gaishe su suka tashi suka basu waje.
Hajiya Dada ce ta shiga ta samu waje ta zauna,gaisawa suka yi cike da girmamawa,har wani rissina mata suke yi,murmushi ta yi kawai sannan ta ce.
"To alhamdulillahi mun godewa Allah da ya nuna mana wannan rana ta Juma'a mai albarka,a yau ina mai sanar da ku cewar Jubair ya samu matar da zai ƙara da ita da izinin Allah,wannan yarinyar ba kowa bace face ƴar ɗaya yarona Ammar dake can US wato Malika,ina fatan za ku saka masa albarka kamar yanda kuka saba yi a duk sanda irin haka ta bijiro."
Baffah Sale da Baffah Habu ne suka kalli juna,cike da isa da nuna taƙamar dangin Uba Baffah Sale ya ce.
"Ni fa ina mamakin yanda kike zaunawa ki yanke hukunci ke kaɗai ba tare da neman shawarar mu ba,mu kammu yau abinda ya kawo mu kenan ni da ƴan uwana guda bakwai gamu nan,saboda ƙudirin dake ran mu ne yasa bamu zo da su Buba ba tinda su zumunci ne na nesa. Dan haka ki tsaya ki saurare mu da kyau,wannan isa da mulkin mallakar da kike nuna mana akan ɗan ɗan uwanmu ya ishe ki haka,mu nan muna da yarinyar wajen Habu mai suna Shafa'atu da ta kammala degree ɗin ta da muka yi mata alƙawarin aura mata Jubair,dan haka sai dai ya haɗa su su biyu ya aura,ko kuma ya fasa auren bare ya auri ƴar gida."
Wani irin murmushin isa da kasaita Hajiya Dada ta yi kafin ta kalli Jubair ta ce,
"Boɗɗo tashi tsaye ka zo nan."
Cikin sanyin jiki Jubair ya miƙe ya isa gaban ta ya ɗan duƙa,cikin isa Hajiya Dada ta ce,
"Miƙewa za ka yi da kyau su gan ka,wannan da kuke gani magidanci ne ba wai yaron nan ƙarami da mahaifin shi ya rasu ya bar tarin dukiya kuka handame ba kuka kore shi da mahaifiyar shi daga muhallin su kuka yi rubda ciki a dukiyarsu,wannan babban mutum ne da jihar nan tamu ta Yola da Nigeria baki ɗaya take alfahari da shi,dan kun samu ina dannar zuciyar shi ina nuna masa abinda Allah ya ce akan sada zumunci shine har kuke da bakin nuna ikon dangin uba akan shi? Ku kun san yanda nake fama da shi kafin ya danne zuciyar shi akan hana mu abinci da kuka yi a baya? kuka barmu a wancan lokacin ko mu mutu ko mu yi rai ba damuwar ku bace,kun ya nake fama da shi kafin ya cire sisin shi ya yi muku hidima? Dan haka yanzu ruwan ku ne ku ci gaba da zumunci da shi ni kuma zan ci gaba da nuna masa hanyar gaskiya,ruwan ku ne ku yanke zumunci da shi idan kun so,amma auren shi da Malika babu fashi."
A hasale Baffah Habu ya miƙe tsaye,wanda da ka ga fuskar shi tin farko zaka gane shi ya kitso maganar auren ƴar shi da Jubair,cikin masifa da kumfar baki ya ce.
"Ke Alawiyya mu ne zamu yanke hukunci akan ɗanmu ki sa ƙafa ki ture? Me kike so na cewa Shafa'atu da naiwa alƙawarin aura mata Jubair?"
"Ka bata haƙuri ka ce ta fitar da wani masoyin ta aura,amma ba ɗana ba,ɗan nawa ganima ne da kuke ƙoƙarin raba shi a tsakanin ku? Kun ga,dan Allah tin kafin maganar nan ta fi haka zafi ku zo ku tattara ku wuce,mun gode da zumunci Allah ya kai mu wani satin."
Miƙewa suka yi gaba dayan su rai a ɓace kowa na tofa albarkacin bakin shi,da ƙyar suka samu muryar Baffah Habu ta fito,cikin tsananin ɓacin rai da cin alwashi ya ce.
"Ba dai mu kika wulaƙanta ba Alawiyya? To a yi aure lafiya, za ki ga abinda zai biyo baya,kuma maganar zuwa gidan nan da kike yi wani sati ai mu har abada mun yanke zumuncin da kike ƙoƙarin yankewa shekara da shekaru Allah bai nufa ba."
Ko ci kan ku Hajiya Dada bata ce musu ba, murmushi kawai take bin su da shi har suka zo fita,ran Jubair idan ya yi dubu ya ɓaci saboda kalaman da suke jifan mahaifiyar shi da su,a hasale ya yinƙura zai yi magana Hajiya Dada ta zuba masa ido da kallon gargaɗi,gefen ta ya koma ya tsaya yana taune cikin bakin shi yana fitar da wani irin huci mai zafi.
Motocin su suka hau suka bar gidan cikin ɓacin rai da cin alwashi kala-kala. Sai da suka tafi ne Hajiya Dada ta saki hawayen da ke maƙale a idanun ta,nan take ta cewa Jubair ya kirawo mata Ammar video call tana son magana da shi........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 18:
Da sassafe ya dawo ya kwanta a parlour kamar dama a wajen ya kwana,Ruƙayya kuwa sai da ta gama gyara sashen Jubair tas ta wanke bathroom sannan ta yi wanka,ba ƙaramin dirza ta dinga yiwa jikinta ba saboda ta kauda warin da yake mata ƙorafi akai har ya yi sanadiyyar hana shi kusantar ta a wannan daren ya kwana a parlour. Ɗaure da towel ta fito ta wuce wajen da take ajiye kayanta ta ɗauki wata shadda da suka yi anko ita da Jubair da yara ta saka,sai da ta kashe dauri mai kyau sannan ta fesa turarukan ta masu daɗin ƙamshi da tsada,makulli ta sa ta rufe wajen kafin ta tsaya a gaban madubi ta ƙarewa kanta kallo. Tin daga gashin kanta zuwa yatsan ƙafar ta Allah ya kyautata mata halittar su, Ruƙayya na daga cikin fulanin nan masu kaurin jiki,tana da faffaɗan ƙugu da manyan cinyoyi,ta ɓangaren fuskar ta kuwa bata da manyan ido,amma madaidaita ne farare tas, baƙin idanun ta sun fi kama da brown irin mai duhun nan,hancin ta ba siriri bane yana da girma irin mai tudun nan,ya yi matuƙar dacewa da laɓɓanta masu kauri jajaye.
Lumshe idanunta ta yi gashin idanun ta masu kama da an dasa mata su ne suka ƙarawa idanunta kyau,hawayenta ta share kafin ta ɗauki wayarta da taji karar shigar saƙo,a hankali ta sanya password ɗin ta ta buɗe wayar,hoton su ne a wallpaper ɗin ta ita da Jubair da yaran su uku,a hankali ta furta,
"Duniyata"
Wajen message ta shiga sai ta ga alert,budewa tayi dan ta ga wanda yatura mata kudi,makudan kuɗaɗen da taga Jubair ya tura mata ne ya sanya ta saurin buɗe baki cike da mamaki,kasa kunne ta yi ta na sauraron maganganun da ke fitowa daga parlour,cikin sauri ta nufi parlourn dan ganewa idanun ta abinda ke faruwa,tana isa ta ga Uwa ta kama ƙugu tana masifa,cike da mummunan kishi Uwa ta ce.
"Amma dai Hammaah ka bala'in raina min hankali,wannan kuɗin satar kwanan da ka yi ka kai min ne ko kuma kana nufin darajar yarinyar nan har ta kai ka bani wannan kud'in?"
A kunyace Jubair ya kalli Ruƙayya da ke bin shi da kallo cike da mamaki,cikin borin kunya ya ce.
"Darajar Malika ta zarta kuɗaɗen da na tura muku tinda ba ke kaɗai na baiwa ba,kawai na yi la'akari da baya ne,idan ba makka zan kai Ruƙayya ba a baya ina bata kuɗi ne kwatankwacin kuɗin kujerar Umara ko Hajji,dan haka idan zaki karɓa ki karɓa idan baki so kuma ke kika san yanda zaki yi da su tinda ba a yi maki abun arziƙi ke."
Kafin wani ya sake magana a cikin su Ruƙayya ta ƙarasa tsakiyar parlour'n,cikin sanyin muryarta mai daɗin sauraro ta ce.
"Daddyn Muneeba na gode Allah ya ƙara arziƙi,yanzu na gama shiryawa na ji wayata ta yi ƙara ina dubawa na ga kuɗi masu yawa haka,Allah to ya ƙara arziƙi."
Duk da haushin Ruƙayya da yake ji wanda bai san dalilin jin haushin nata ba,sai ya ji ta burge shi,cikin ɗan sakin fuska ya ce.
"Babu komai,idan akwai wani abu da kike da buƙata ki sanar dani,kar ki ji nauyin komai,babu abinda ba zan yi maku ba matsawar ina da shi."
Dariya Uwa ta yi ta buga cinya kafin ta ce.
"Ba dole a tambayi ɗiyar gyartai ko da abinda take da