ba tare da sanin me Ruƙayya zata haifa ba? Ai a zato na ƙarfin tsafin naka ya kai inda ya kai,ashe kai ma kamar sauran ne duk ha'inci kuka saka a gaba,aikin banza ma malam tashi ka bani waje."
Rai a matuƙar ɓace Munkaila ya kalli Uwa ya ce,
"Duk ƙarfin tsafi na bai kai ya hukuncin Allah da kike son ja da shi ba,baki da labarin akwai abinda idan Allah ya shiga lamarin babu bokan duniyan da ya isa ya kutsa ta cikin shi? Raina ƙarfin baiwar da Allah ya min ta sanin ilimin bokanci da kike yi watarana zai hana ki samun nasara akan maƙiyan ki,da ace kin tsaya mun yi magana a natse da wataƙila na baki shawarar yanda zaki kawar da ko me aka haifa namiji ko mace,ni Munkaila aiki nake da baƙaƙen rauhanai babu inda ba zan aike su ba a faɗin duniyar nan."
Kalaman Munkaila sun shiga jikin Uwa har sun sanya mata wata iriyar yarda da shi tare da imani mai ƙarfi akan karfin tsafinsa. Cikin washe baki Uwa ta ce,
"Ka yi hanƙuri Munkailan Ubaidaa,ɓacin rai ne ya sa na faɗi abinda na faɗa,na baka wuƙa da nama akan lamarin nan,idan har ka yi sanadiyyar hallakar da abinda Ruƙayya ta haifa a can turan zan yi maka kyauta mai tsoka ta ban mamaki."
Ba tare da Munkaila ya ce mata komai ba ya miƙe ya bar parlour'n ya wuce ɗakin shi dake ɓangaren ma'aikatan gidan,wata jakar shi tsohuwa tukuf da ta gaji da shan iskar duniya ya zaro a ghana most go ɗin shi. Wani buzun fatar damisa ya zaro daga jakar ya shimfiɗa ya kalli yamma,nan take ya sa hannu ya dinga zaro sauran kayayyakin da yake da buƙata. Ya jima ya na wasu irin surkulle kafin ya tashi ya tattare kayan shi ya mayar dasu maɓoyar su.
Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya hau yiwa kan shi kirari.
***************************
Tun da safe da su Ruƙayya suka tashi take jin jikinta na yi mata wani irin ciwo musamman marar ta da bayanta,Hajiya Dada kuwa na kula da yanayin ta,dan haka suna kammala cin abincin safe ta sa Jubair ya ɗauki akwatin da suka haɗa kayan haihuwar su tin a Nigeria suka wuce asibiti. Lokacin da suka tafi Ammar ya na office,Samhah kuwa dake aikinta daga gida tana can tana meeting,Queen Malika kuwa ta na ɗakinta tana bacci saboda kwana da suka yi party ita da ƙawayenta.
Kamar jira ake su isa asibitin naƙuda ta tasowa Ruƙayya gadan-gadan,cikin sauri aka shirya ta cikin rigar da masu ciki ke sanyawa aka shiga da ita ɗakin haihuwa.
A can Nigeria kuwa Munkaila na tsaye ya na aske shuka ya yi murmushi ya ce,
"Lokacin aikin ka ya yi ƙaramin su babban su"...........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH
LAST FREE PAGE.
*Idan kina son ci gaban labarin DUK NISAN DARE garzaya ki sheƙa ɗarin ki biyat #500 a wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank Hamida sanusi Ahmad,sai ki tura shaidar biya ta wannan lambar 09031416423. Da zarar kin yi haka zaki ji ki a paid group. Na gode. Saboda yanayin yau da gobe ban yi alƙawarin yin posting kullum ba,amma zan yi iyakar iyawata na dinga yin posting akai-akai inshaa Allahu.*
PAGE 7:
"Menene wannan Hafsat?"
A diririce Uwa ke kallon ƙullin magungunan da ta dawo dasu da rana daga wajen Malam. Duk maganganun da Jubair ke yi mata basa shiga kunnen ta,har sai da ya kula da hakan ya tab'o ta ya ce.
"Na ce wannan menene? Ko in ce na waye?"
Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyarta,amma sai ta sanya jarumta,cikin dakewa Uwa ta ce,
"Hammaah magani na ne da muka karɓo ɗazu a wajen mai bada maganin gargajiya,ban san ya akai suka zo nan ba,dama an gargaɗe ni kar na yi amfani da su ina zuwa."
Kafin Jubair ya yi wani yunƙuri har Uwa ta kwashe magungunan ta wuce toilet ɗin ɗaya daga cikin ɗakunan dake sashen ta zubar,flushing ɗin su ta yi tare da sauke ajiyar zuciya,hannun ta a saman ƙirjin ta ta baro band'akin tana waige tare da dudduba kowanne saƙo da lungu na sashen,a cikin zuciyar ta take ayyana,
'Anya wannan ba aikin Munkaila bane? Wato so yake ya tona min asiri shi yasa ya yi surkullen da magungunan suka kawo kansu da kansu nan ko? Babu komai mu zuba mu gani,duk nisan jifa ai ƙasa zai faɗo,haka zalika duk NISAN DARE GARI ZAI WAYE'
Firgita ta yi tare da ƙwalla ƙara ta ɗafe Jubair ta na kukan shagwab'ar da ta san yana rikita masa lissafi har ya manta kowa da komai face wannan shagwab'ar da ake zuba masa,cikin dasasshiyar murya Jubair ya ce,
"Hafsyna menene kuma? Kin ga baki yi min bayani akan wanda ya hana ki amfani da maganin da ke ce da kan ki kika...."
Kuka ta fashe da shi wanda ya sanya shi kasa ƙarasa maganar da ya yi niyyar yi,kafin ta ce,
"Hammaah ni fa ina ganin ba zan taɓa haihuwa da kai ba har abada,na fidda rai da maganar haihuwa musamman da yanzu shekaru na ke ƙara yawa."
Cike da tausayawa Jubair ya ɗauke ta a hannun shi kamar wata jinjira ya wuce da ita bedroom ya kwantar da ita a saman gado,a gefen ta ya kwanta ya fara lallashin ta da tausasan kalamai.
"Kar ki ce haka Hafsyna yara na ai naki ne,sannan yaran ki nawa ne,kar ki manta ke ɗin jinin jikina ce, ƴar'uwa ta ce ta jini,na sha faɗa maki mu ɗakko su Usman da Ali su dawo nan da zama idan hakan zai faranta maki,amma a duk sanda na yi maganar sai ki dinga fushi,na rasa me yasa baki ƙaunar zaman su a gidan nan,ko akwai wani dalilin da ya sa kike nesanta su da gidan nan ne wanda ban sani ba?"
Cike da kirsa da kisisina ta ce,
"Ba zaka gane ba Hammaah,zaman su Usman a gidan nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba,saboda a shekarun baya hutu kawai suka zo aka fara nuna musu nan ɗin ba gidan uban su bane,to tinda uban su na da arziƙi daidai gwargwado ai kaga gwanda su yi zaman su a can,su kansu basu son zuwa tinda a ganin su na guje su na yi wani auren na manta da su."
Cike da ɗaure fuska Jubair ya tashi ya zauna yana fuskantar ta ya ce,
"A kaff gidan nan waye yake ƙyamatar yaran ki? Sanar dani yanzun nan na ɗauki mataki akan hakan,koda baki aure na Hafsat kina da ƴancin kawo ɗan ki gidan nan, ballantana kuma kina aure na."
"Haka dai kace Hammaah,amma matar ka ai bata san hakan ba,a ganin ta zaka fifita yarana saboda maza ne sama da nata,ni dai dan Allah a bar wannan maganar bana so ka sake tada ita,ana zaune lafiya a zo a dinga cewa nice dama fitinanniyar da ke tada rikici a gidan nan,kuma ka ga Hajiya Dada ba zata ji daɗi ba."
Shiru ya yi ranshi babu daɗi,saboda ba karamin tausayawa Uwa yake yi ba,duba da ya san yanda take masifar son ta haihu da shi,da wannan maganganun Uwa ta ɗauke hankalin shi da salon ta,wanda ya mantar da shi maganar ƙulle-ƙullen maganin da ya gani a saman dinning table.
Washegari da asubar fari Jubair ya tashi kamar koda yaushe,wanka ya yi tare da ɗaura alwala sannan ya fito ya sanya jallabiyar shi blue mai duhu tare da wandon ta,turaruka masu matukar tsada da ƙamshi ya fesa kafin ya tada sallah a saman abun sallah. Uwa kuwa a lokacin ta yi wani sabon juyi ta ci gaba da baccin ta cikin kwanciyar hankali da nishad'i. Jubair kuwa na idar da sallah ya miƙe ya fara haramar tafiya masallaci,dan kuwa duk rintsi duk wuya baya sallah a gida sai a masallaci,koda kuwa a wajen aiki yake ya ga lokacin sallah ya yi yakan wuce masallaci,wanda hakan da yake yi ba ƙaramin baiwa mutane mamaki yake ba,duba da cewa shi ɗin ɗan siyasa ne mai faɗa a ji,ba safai aka fiya ganin irin su a masallatai ba suna sallah kullum.
A hankali ya taka ya isa gaban Uwa da ke kwance lamɓas a cikin bargo,ɗan bubbuga pillown da take kai ya yi a hankali,ganin ko motsawa bata yi bane ya sanya shi tada ita da kyau,be ƙyale ta ba sai da ya ga ta zauna da kyau sannan ya ce,
"Ki tashi ki je kiyi wanka ki yi sallah,kar ki bari na dawo na tarar dake kina bacci zan saɓa maki,kin san bana son wasa da lokacin sallar nan da kike yi ko?"
Ɗaga kai ta yi tana miƙa kamar wata macijiya,da sauri Jubair ya wuce ya barta tana zaune tana nazarin shin ta tashi ta bi umarnin sa ne,ko kuma ta ɗan ƙara baccin kafin ya dawo? A hankali ta lallashi kanta ta miƙe ta faɗa bathroom ta yi wanka. Daure da towel ta fito tana waƙe-waƙe kamar ba lokacin sallar asuba bane. Kanta ta hau gogewa da ƙaramin towel tana tsane dogon gashin ta irin na fulanin asali mai yauƙi da santsi,tana ɗago kai ta kalli madubi sai ta ga wani abu ya gilma da gudu wanda bata gama tantance ko menene ba,ihu ta kurma ta haye gado tare da ƙanƙame bargo tana kuka,a haka Jubair ya dawo ya tarar da ita tana naɗe cikin bargo,tambayar duniya ya yi mata amma ta ƙi bashi amsa sam, ƙarshe ma kuka ta sanya masa tana faɗin ya lulluɓe ta ita tsoro take ji.
Da jin haka sai Jubair ya saki murmushi ya rungume ta a jikin shi yana tsokanar ta ya ce,
"Kin san Allah idan kina wani abun sai in rasa ke da Kubrah waye babba,kin yi sallah?"
Tsoron kar ya yi mata faɗa ne ya sanya ta cewa,
"Eh na yi sallah."
Maida musu bargon ya yi suka koma bacci.
Da safe bayan sun kammala duk wani abu da suka saba yi kafin Jubair ya fita aiki ne, Uwa ta koma sashenta ta sa Ubaida ta kira mata Munkaila,tana nan zaune ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya Munkaila ya shiga parlourn nata ya samu waje a ƙasa ya zauna,sai da ta gama ƙare masa kallo tin daga saman kan shi har ƙafafun shi sannan ta ce,
"Munkaila ko za ka iya sanar dani abinda ka ke so a gare ni da ya sa ka fara yi min kutse a cikin rayuwata? Idan dan ɗan abinda ya faru ne a tsakanin mu jiya ina so in sanar da kai na janye maganganu na,ni da kai na zan haɗa maka lefe na gani na faɗa na zame maka uwar ɗaki har ka mallaki Ubaida,sai dai ina da sharaɗi."
Cike da zumuɗi Munkaila ya ce,
"Hajiya na amince da kowanne sharaɗi zaki gindaya min,matsawar buri na zai cika."
Kallon shi ta yi tana nazarin sa da kyau,cikin murmushi ta furta,
"Kenan ka amince kai ne ka kai min magungunan da na dawo da su sashen Jubair,tinda babu wanda ya san da zaman su daga ni sai Ummahna sai malam da ya bani su."
Sosa ƙeya Munkaila ya yi kafin ya ce,
"Sai kuma Allah ba, Hajiya Allah ya taimake ki."
Murmushi ta sakar masa kafin ta ce,
"Malam Munkaila kenan,ashe dai kai ɗin ba na wasa bane."
Kallon ta kawai ya yi ya saki wani irin shu'umin murmushi,kafin ya ce,
"Ni dai Hajiya ki ƙoƙarta min ku aura min Ubaida,ita ce farin ciki na,na jima ina son na aureta amma tana ƙi saboda tana jin tsoron kar ki hana..."
Cikin ɗaga hannun ta na hagu Uwa ta ce,
"Magana ai ta ƙare,zan yi ƙoƙarin ganin ka auri Ubaida,ni kuma daga baya za ka tsaya tsayin daka ka cika min alƙawarin da ka ɗauka,idan ka amince shikenan."
"Na amince Hajiya,Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma."
"Amin,kana iya tafiya sai na sake neman ka."
Godiya Munkaila ya yi yana murna ya koma bakin aikin shi,itama Uwa murmushi take ta zabgawa tare da faɗin.
"Mu je zuwa,wai mahaukaci ya hau kura,yanzu za a fara wasan."
******************************
Babbar makaranta ce da ta ƙunshi ɗalibai masu matuƙar hazaƙa a garin Baltimore dake jihar Maryland a ƙasar US. Dare ne amma kai ka ce da tsakar rana matasan ke kai komo a cikin babban hall ɗin dake a tsakiyar makekiya kuma hamshaƙiyar makarantar,rana ce da kowanne ɗalibi ke cike da tsantsar farin ciki da annashuwa kasancewar rana ce ta prom,kowa ka gani tare yake da date ɗin shi.
Wasu matasa ne su uku a tsaye a waje suna kallon hanya tare da duba wayoyin su daga lokaci zuwa lokaci,suna kurɓar abun shan dake cikin kofunan hannayen su,cike da ƙaguwa Elsa ta kalli Mark cikin harshen turanci ta ce,
"Ni fa ina tunanin Queen ba zata samu damar zuwa ba,ina mamakin yanda iyayen ta ke juya rayuwarta,mun gode Allah ma mun kusan cika shekara 18,a lokacin da muka cika shekarun nan babu wanda ya isa ya nuna mana yatsa,barin gidan ma za mu yi."
Mark ne ya kalli Elsa ya mayar mata da martanin maganar ta cikin harshen turanci ya ce,
"Ba daga iyayen ta bane,daga wannan addinin nasu ne na musulunci,da an yi magana sai su ce haram kar mutum ya sha giya,haram kar mutum ya yi zina,haram kar mutum ya saka kaya bai rufe jikin shi ba, haram...."
Wani matashi ne fari tass dake tare da su ya katse Mark cikin sauri ya ce,
"Kar ku sake ku yi magana akan addinin mu haka,mu ci gaba da girmama junan mu kawai,mu jira zuwan Queen,idan kuma ba za ku jirata ba zaku iya tafiya,ni zan jira ta,kar ku manta mu abokai ne tin muna aji ɗaya,yau ranar farin ciki ce a wajen mu kar mu ɓata shi da surutun da bai dace ba."
Ganin yanda ran matashin da Elsa ta kira da Afdhal ya ɓaci ne ya sanya ta riƙe hannun shi ta na faɗin,
"Kwantar da hankalin ka,taron ya fara kawai ku zo mu shiga ciki."
Hannun shi ya zame ya ƙi bin su,yin hakan kuwa ya ɓata ran Mark dan haka sai ya fizgi hannun Elsa suka shige suka bar Afdhal tsaye yana ci gaba da jiran Queen ɗin tasu, ya jima a waje yana jiran ta bata zo ba dan haka sai kawai ya wuce wajen da suka aje motocin su ya ɗauki tashi ya wuce gidan su Queen dan ya ga abinda ya hana ta zuwa prom ɗin.
Isar shi gidan su Queen ke da wuya,sai ya tarar da gidan cikin hayaniya da ihun ta tana ta fashe-fashem abubuwa,duk yanda iyayen ta ke bata haƙuri akan ta nutsu ta ƙi natsuwa balle ta daina fasa musu kayayyakin gidan nasu.
Da sallama ya shiga gidan kamar koda yaushe ya gaishe da Ammar,Samhah mahaifiyar Queen na ta riƙe ta dan kar ta taka kwalabe amma haka ta ƙwace ta yi kan Afdhal da gudu ta rungume shi tana kuka,a daidai wannan lokacin ne ƙofar gidan ta sake buɗewa a karo na biyu Hajiya Dada,Jubair da Ruƙayya suka bayyana a gidan. Salatin da Hajiya Dada ta sanya ne ya dawo da dika mutanen gidan cikin hayyacin su suka zuba mata ido, cike da mamaki Hajiya Dada ta ce,
"Ammar me nake gani haka Malika kwance a ƙirjin wani ƙaton? Ko aure ka ɗaura mata da arne bamu da labari? Na shiga uku ni uwar Zubairu,ashe da bamu zo ba yau da mun ji mugun labari."
Ganin Hajiya Dada na kallon su Malika ta na maganganu tare da zubar da hawaye ne ya sanya Afdhal kwace jikin shi da ƙyar daga wajen Malika ya gudu,a gigice ta bi shi zata kamo shi ta yi tuntuɓe da kujerar da ta wurgar a hanya,kafin ta faɗi ƙasa cikin zafin nama Jubair ya miƙa hannu ya taro ta ta faɗa saman ƙirjin shi,wani irin bugawa zuciyar shi ta yi da karfi,idanu Malika ta zubawa kyakkyawar fuskar shi tana kallo ko ƙiftawa bata yi.........
*Shin me ya kawo Hajiya Dada da mai tsohon ciki ƙasar waje a daidai wannan lokacin?*
*Wace iriyar rayuwa Malika zata gudanar anan gaba a rayuwarta?*
*Uwa na samun nasarar cutar da Ruƙayya da yaranta kuwa? Ko dai reshe ne zai juye da mujiya?*
*KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA,KAR KU ZAUNA DA DOGON NAZARIN DA BABU INDA ZAKU SAMU WARWAREWAR SHI FACE A WANNAN LITTAFI NA DUK NISAN DARE....*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 11:
"Ke Hasken zuciya waccan zabayar daga ina su Alhaji suka zo da ita ne? Barakallah masha Allah,Allah ya yi halitta a wajan can."
Rai a ɓace Ubaida ta kalli Munkaila dake cizon yatsa yana yaba kyawun Malika,tsaki mai ƙarfi ta doka cike da kishi ta shige sashen Uwa,Munkaila kuwa bai dawo hayyacin shi ba sai da Malika ta shiga sashen Ruƙayya sannan ya juya da niyyar ya yi wa Ubaida maganar Malika sai ya ga wayam bata nan,murmushi ya saki har sai da fararen haƙoran shi suka fito sannan ya yi wani ihu irin na fulani ya yi juyi yana rawar murna,cike da farin ciki Munkaila ya ce,
"Allah ka kai damo ga harawa,yau dai Allah ya nuna min yanda Hasken zuciyata Ubaida ke ƙaunata,so da ƙauna ke kawo kishi,har na matsu safiya ta yi na je wajen Hajiya Uwa na ji wanne irin tukuici za ta bani akan aikin da na mata."
"Au wai dama baka tafi ba kana nan har yanzu? Ihun me ka ke yi mana anan,sannan wanne irin aiki ka yiwa Hajiya har ka ke jiran tukuici?"
A diririce Munkaila ya kalli Ubaida da ke tsaye fuska a haɗe tana watsa masa harara,cikin sarƙewar harshe Munkaila ya ce,
"Wan...wanki mana..kin manta ni na wanke mata bargunanta wancan watan? Ba wannan ba ma,dama haka kike bala'in so na amma kike faman wahal da ni? Kullum se kin sa na kashe maki kuɗi,idan ina son na yi hira da ke sai kin ja min aji,kin kuwa san irin ƙaunar da nake miki Ubaidata?"
Murmushi Ubaida ta yi ta sake shigewa gida ta bar Munkaila a tsaye,ƙwafa ya yi sannan ya ce.
"Baki wahal da ni a banza ba,za ki shigo hannu ne,a lokacin ne zaki gane wanene Munkaila Ɗan Malam ka ƙi halin Malam."
Ɓangaren masu aikin gidan ya wuce ya samu mai gadi ya zauna a wajen shi suka hau hirar duniya.
Tinda Malika ta shiga sashen Ruƙayya ta ga babu kowa a parlour,sai kawai ta nufi saman dinning table,tana zuwa ta hau buɗe manyan warmers ɗin da aka zuba abinci,salad ɗin dankalin bature ta gani ya ji kayan haɗi har da hanta a ciki,gefe kuma ga fruit salad da ya sha madara har wani kauri ya yi,ya sha fruits kala-kala ciki har da inibi,yawu Malika ta haɗiya ta ja kujera ta zauna,plate ta ɗauka ta ɗebi salad ɗin sannan ta ɗauki wani ɗan kwano ta zuba fruit salad ɗin ta na gamawa ta ɗauka ta koma parlour ta zauna ta kunna TV,kallo ta fara yi ta na cin abincin ta hankali kwance. A haka Kulu da ke kitchen tana haɗa mata salad ɗin ganyayyakin lambu ta ganta tana ta cin abincin da ta haɗawa uwar ɗakin ta,baki sake Kulu take kallon Malika da irin shigar da ta yi,ganin kallon da Kulu ke yi mata ya yi yawa ne ya sanya Malika da ta cika baki da dankali cewa.
"What? Ko akwai abinda zan taimake ki da shi ne?"
Cikin sauri Kulu ta hau girgiza kai,sai ta ƙarasa gaban Malika ta ajiye mata salad ɗin lettuce da cabbage ɗin da ya ji dafaffen ƙwai da waken gwangwani,a yatsine Malika ta ce,
"Ba zan ci wannan ba,ki je ki zubar, daga yau a dinga yi min irin wannan,ya yi daɗi,amm nace ba,ina mutanen gidan suke? Ina Mommy da Kubrah?"
"Suna cikin ɗakin Hajiya,maganar mutuwar jaririn ta ya girgiza yaran,ta na can ta na lallashin su."
Miƙewa Malika ta yi ta ce,
"Nuna min inda suke please."
Gaba Kulu ta yi Malika na biye da ita tana share bakin ta da ya ɓaci da tissue,suna zuwa ƙofar ɗakin Ruƙayya Kulu ta sa hannu za ta ƙwanƙwasa ƙofa Malika ta wuce ta ta murɗa hannun ƙofar ta shige,kwance ta gansu a gado duk sun rungume juna sun saka mahaifiyarsu a tsakiya,wadda har a wannan lokacin zubar da hawaye take yi,nan take suka baiwa Malika sha'awa,cikin sanyin jiki ta isa cikin ɗakin ta na riƙe hannayen ta waje ɗaya ta ce,
"Zan iya shiga cikin ku nima?"
Murmushin karfin hali Ruƙayya ta yi,kafin ta share hawayen ta ta ce,
"Yes you can join us please,zo ta nan babyn Papa."
Malika na jin wannan sunan sai ta samu kanta da murmusawa,cike da zumuɗi ta isa saman gadon ta kwanta a gefen Mubeena,cikin sanyin murya ta ce.
"Mommy please ki dena kuka,idan kina kuka su Kubrah ba za su dena kuka ba,and na san kin gaji you need some rest,ya kamata ki ci abinci ki kwanta ki yi bacci,ko kin manta likita ya ce ki dinga samun hutu?"
Kalaman Malika sai suka sanyawa yaran tsananin ƙaunar ta cikin ƙanƙanin lokaci,cikin dasasshiyar murya Kubrah ta ce,
"Yes Mommy gaskiya ta faɗa,ya kamata ki tashi ki yi wanka ki ci abinci,sai ki zo ki kwanta ki huta,ki yi haƙuri bamu yi tinanin lafiyar ki ba muke ƙara miki damuwa."
Cikin wani irin yanayi da ita kaɗai ta barwa kanta sani Ruƙayya ta sauka daga gadon ta wuce bathroom ta fara wanka,wanka take yi zuciyarta na mata suya musamman idan ta tuna da kalaman Uwa,a haka ta kammala wankanta ta ɗaura towel ta fita,kafin ta fita Malika ta sa Kubrah ɗakkowa Ruƙayya kayan da zata saka,murmushi Ruƙayya ta yi sannan ta ce,
"Dama Mom ɗin ki ta ce min kina da tausayi,sannan kina da kulawa,thank you."
Gyaɗa kai kawai Malika ta yiwa Ruƙayya kafin ta sauka daga gadon ta bar ɗakin,ta yi haka ne dan ta baiwa Ruƙayya damar shiryawa a tsanake,Kubrah na ganin haka itama sai ta bi bayan Malika. Tin daga wannan lokacin har zuwa dare Malika da Kubrah na tare suna hira,cikin ƙanƙanin lokaci suka samu wata iriyar shaƙuwa ta musamman,daga ƙarshe sashen Hajiya Dada suka tafi Malika ta kira su Mark video call ta nuna musu Kubrah,nan da nan Mark ya ce yana son Kubrah saboda tana da kyau,Elsa kuwa kishi yasa ta kwaɗe masa kai ta hau dukan shi da pillow,dariya sosai suka dinga yi suna nishaɗi,lokacin da ta kira Afdhal kuwa ƙin ɗauka ya yi,saboda a ganin shi tinda ta tafi ba zata dawo ba,dan haka yana so ya sabawa kanshi da rashin ta,baya so ya ci gaba da yin riƙo da soyayyar da ba zai cimma burin shi akan ta ba,haka Malika ta gaji da Kiran shi ta haƙura ba dan ta ƙyale shi ba,sai dai kawai ta yi masa uziri ne ko baya kusa da wayar shi,ko yana wani abu mai mahummanci.
Washegari da asuba Hajiya Dada ce ta taka har zuwa ɗakin Malika,kwance ta same ta daga ita sai wata riga mai santsi karama da gajeran wandon ta da ya tsaya a can saman mazaunan ta, baccin ta kawai take shaƙa cikin kwanciyar hankali,gashin kanta Hajiya Dada ta kalla,cikin zuciyarta ta furta,
'Barakallah Masha Allah.'
Takawa ta yi har zuwa bakin gadon da Malika ke kwance ta sanya hannu ta tashe ta dan ta yi sallar asuba,hannun Hajiya Dada ta doke tare da faɗin.
"Dad ka ƙyale ni,idan na tashi zan yi,bacci nake jiiiii."
Ido Hajiya Dada ta zaro waje,cike da takaici ta sa hannu ta ɗasawa Malika duka a cinya,a gigice ta farka tana kurma ihu kamar an zari ran ta da ƙarfi,
"Rufe min baki dan ƙaniyar ki,sallar ce za a ƙyale ki sai sanda kika tashi gotai-gotai dake? Ina sane da tinda muka zo baki kalli gabas ba da sunan sallah,a zatona ma hutun sallar kike yi,sai daga baya na gane iskanci ne kawai ke damun ki,to tashi ki wuce ki rama sallolin dake kan ki a gabana kafin na sa carbin nan na zane ki."
Kuka Malika ta sake ɓarkewa da shi ta na faɗin.
"Paapaaa come and help me za ta kashe ni."
A can ɓangaren Jubair kuwa kamar kullum,sai da ya yi wanka ya yi sallolin nafila sannan ya fito dan tafiya masallaci,ihun Malika da ya jiyo ne ya dakatar da shi daga fita daga gidan,a sukwane ya nufi sashen Hajiya Dada,jin ƙofar ya yi a kulle,cikin sauri ya hau bugawa,Hajiya Dada dake tsaye ta na yiwa Malika faɗa akan ta tashi tai sallah sai ta juya ta kalli ƙofa,kafin ta yi wani yunƙuri Malika ta sauka daga gadonta ta fita da gudu,tana zuwa bakin ƙofar fita ta buɗe ƙofa ta faɗa jikin Jubair da ke a rikice,rungume ta ya yi da kyau a jikin shi yana lallashi tare da tambayar ta me ya faru,cikin kuka ta hau nuna masa