Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rausaya. "ka san rabin ranka ba za ta taba bari na zo duba ta ba ta cika fishi" Yayi dariya. र ま 151 Mariyan Masoya Rahma AbdulMajid "ban san Farida da tsantsar fishi ba, ita dai ji tayi ra'ayinku ba zai zamo daya ba shi yasa ta ji gara ku yanke. Bar wannan zancen, yaya aka yi kika'san ina nan kuma me kika zo yi?" Ya jero jumlar karshe ayayin da yake debo lemo a kofi don ya kawo mata, amma sai ta kada kai. "Bana son wannan lemon na fi son na firjin sama dake hanyar falon gabas, wannan ni na tara wa baki,can kuwa akwai Soda" Ya tsaya yana kallon ta da kofi a hannunsa. Lallai ba sai yayi doguwar tambaya ba ta yi wa gidan matukar sani, amma ta yaya? Ta san abin da ke saman da bata hau ba, har ma da cikin firjin da bata bude ba, tana karawa da cewa ita ta ajiye abin da ke cikin firjin. "kana mamaki? Nan gida na ne, na fita ne don za a kawo ka. Wannan ce amsar da ta sanya nake ganin ya kamata Farida ta gane usilin mu daya. Mahaifinta Chairman shi ne ya ba ni gidan nan don yana so na, kuma yace na koma wani wurin ne har ya-gama da kai tukuna. Ji na yi kawai ba zan iya ba sai na zo na gan ka domin abin da ake shiri gare ka ni bai yi min ba...Mahaifin Farida ya shirya maka makirci iya zaman ka a nan har sai ya ga karshen babanka kuma da sanin Farida ni kuma sai na ji kamar zaluncin yayi yawa in aka ce...." Ya ajiye kofin yana murmushi na sanin inda ta dosa a yi wa Farida zagon kasa. A 1 ر 152 Monyan Masoya Rahma AbdulMajid "Na ji nan gidanki ne, kuma Chairman na so ya amfanu da ni mu gama da babana, na san wannan don kuwa ni na mika yarda ta, abi nda ke ba ki sani ba shi ne babu sanin Farida don na san wace irin mace nake so. Me nene kuma sabo?" Ta yi dariya ta mike zuwa kusa da kirjinsa cikin kissa. "Ba ka san Na`ibi ba ne shi yasa kake son..." Ya matsa cikin daure fuska. "Ke din da kika san shi kina tare da shi ina ga ni da ban san shi ba... ji nan Merry, ina fatan mikewarki fita za ki yi daga gidan nan kamar yadda kika ce har sai na bar gidan zai sake zama naki" Ya bude kofa bayan da ya lura tana shirin kara magana na makirci sannan ya daka tsawa. "Fita kafin na sanya a fita min dake" Babu laka ko tasiri a jijiyoyinta a yayin da ta kamo hanyar kofar. "Zaka bukace ni a yayinda kayi dana sani" Ya sake daka wani tsawan da yayi waje da ita sannan ya hada kofar gidan ya dawo ciki yana nishi da sambatu na tsananin fishi. Σ 153 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid Biyar Tana kallon titin a tsorace kamar wani na biye da ita ko kuma direban baya sauri har suka iso kofar bankin inda ta sauka ta shiga da sauri ta bar me motar na jiran ta. Manaja ya sauko da sauri jin cewa ita ce suka gaisa: A wata 'yar takarda tayi sanya hannunta kasancewar ba ta dauke da cak ko katin karban kudi, ta karbi kudi masu yawa a cikin leda ta musamman ta fita ta koma cikin motar da ta dauko ta. Ita ke nuna hanya har aka zo gaban gidan sannan ta sauka ta tura get suka shiga. Ta sauko tana cewa dirba 'ka ci gaba da jira na zan dauko kaya mu tafi. Kada ka damu da lokaci da kudi zan biya ka' Har ga zuciyarsa bai damu ba domin koda bai san ko wacece ba ya san wata ce daga inda take harkar girma a tsorace zuwa gidan da ta shiga, don haka ita ya cewa 'kada ki damu' Tana tsaye zuciyarta na duka a yayin da ta saki karaurawar gidan iya karfinta ta kasa saki don zumudin a bude mata. Tsayin lokaci ba a bude ba ta sake gwada lambobinsa da take da su, duka babu mai tafiya. A nan ne ta sanya hannayenta kan kofar ta fara buga su da karfi tana kiran sunansa 154 Mayan Masoya Rahma AbdulMajid "Bally bude ni ce...Please open the door it's your wife" Da alamar ya dade a falon kuma ma ya kusanto kofar don ya leka ya ga me rangada karaurawar don haka yana jin muryarta ya hanzarta bude kofar ba tare da wani sharadi ba. Suka hada idanu kallo mai zafi cikin ma'anoni daban-daban har na wani lokaci da ya ishe ta fara kwalla. "Am sorry love" Ta ambata cikin murya mai rawa da nuna shauki. Ya dan lumshe ido ya dawo dasu kanta sannan yayi murmushi. "Dama Father yace wata rana za ki yi min ba-zata muddin ina gidan nan ki zo ki yafe min mu ci gaba da rayuwar auren mu, to ga shi kuwa ranar ta zagayo" Ta dan kalli wajen gidan a hankali sannan ta shigo ta mayar da kofa. Ba kamar yadda ya zata ba na çewa za ta rungume shi ne ko wani abu me kamar haka sai ya ga ta ci gaba da nitsawa a cikin falon farko tana 'yan dube-dube. "Amma bai gaya maka cewa cikin ba-zatan zan zo wata rana in ce ka hada yanaka-yanaka cikin mintuna biyar mu bar gidan don zuwa wani wuri mu rayu ba" Yana biye da ita cikin fargaba na rashin gane ma'anar maganarta da zumudin ya ji ya taba koda kafadarta ne. 159) Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid "But Baby ina zamu? In muka bar nan, mun kyauta wa Father ke nan? Me kike son na fahimta?" Ta juyo da sauri. "Abin da nake so ka fahimta shi ne in kana so auren mu ya ci gaba da zama da dorewa ka biyo ni yanzu mu bar gidan nan...in har kana so na Bally". Ta kura masa ido kamar yadda shi ma yake kallon ta a rude. "Ina ne dakinka?" Ta ambata cikin kokarin rage lokacinda basu da shi. Ya kalli matattakalar ba tare da ya amsa mata ba hakan ya ishe ta amsa ta juya ta haye sama, sai da ya 6ata wasu dakiku sannan ya bi ta shi ma da sauri. A uwar dakin ta sanya karamin akwati bisa gado tuni ta cika shi da abubuwan da ta san yana bukata na kamar kyamara, hotunanta da cajojin waya da kayan kwalliya, sannan ta dunkule kayansa saiti biyu ta watsa ta rufe. Har yanzu bai iya cewa komai ba har sai da ta iso gare shi ta kalle shi cikin isa sannan ta kamo hannun sa na dama ta janye shi daga uwar dakin. "Zo mu je" "What do you think we are doing Baby?"" Bata amsa masa ba jan sa kawai take har ta sauko da shi suka fita daga wannan gida ta hada kofar sannan suka hau bayan motar da ta dauko ta suka kama hanya. リ 55 Moyan Masoyo Rahma AbdulMajid Suite din da ta kama a hotel din daki ne da falo, toilet a uwar daki da daya a falo duka Kayatattu har karamin kicin din.. Ta sallami direba da bandir din kudin da ya girgiza shi ba ta tsaya karban godiyarsa ba suka shige ciki. Uwar daki suka wuce da mijinta da ke rikice yake bin ta har suka iso gaban gadon sannan ya tsaya yana fadin. 'yanzu za ki iya gaya min abin da ya baro da mu gari guda ya kawo mu nan da abin da kike nufi?" Ga mamakinsa tana juyowa sai ya ga tana kuka har ta fada can cikin jikinsa sannan ta soma fadin. 'yanzu mun tsira Bally...mun sake tsirar da soyayyar mu da auren mu, ga ni da kai" Ya karbe ta kamar yadda yake jiran ta inda shi ma ya ji kwallar ta cika masa ido yana sunbatar duk inda ta bar masa tsakanin kanta da wuyanta. Suka sunbaci juna na tsayin lokaci har duhun da idanunsu ya dauka dake lumshe ya zame musu haske sannan ta zare bakinta suka kura wa juna ido. Ya sanya hannu a gefen goshinta yaana tattare mata gashinta da ya zubo a yayin da take dan share gashin bakin wahalar da yayi. Mahaifina bai so mu sake shaida wannan ranar ba ni da ke Farida... duk abin da ya faru shi ya shirya don ya raba mu ..ya kuma so ya raba mu da ranki dungųm...bana jin zan sake と 157 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid jin sa a mai so na in har ba zai taba son ki ba har zai nemi ranki da ran abi na dake cikinki" Tayi wani murmushin takaici. "Haka ma nawa mahaifin wanda ka fada tarkonsa don neman yardata ya nemi ya kashe ruhin soyayyar mu da ka wuce yau. Ya shirya abin da da ba zamu sake saura tare ba" Nan kallon sa gare ta ya sauya zuwa na mamaki da mai do da rikita. A gefen gadon suka kame inda ta fede masa labarin har wutsiya yana kallon ta cikin rasa mafita wa zuciyarsa da ta fada kogin mamaki da tausayin yadda ya yarda aka sake jefa shi a wata yaudarar. Can ya ji ba zabi ban da ya fashe da kuka musamman a yayin da ya rattabo musu wata tambaya mara amsa 'ke nan iyayenmu ba za su taba amincewa da soyayyar mu ba?" Suka rungumi junansu suna kuka dukansu, hakan yayi musu jagora zuwa fanshe búkatun zuciyarsu na soyayya. * Ta cira kanta a hankali bayan ta kalli agogon bango dake dakin wanda ya nuna mata a kalla sun share ya kai awa biyu da rabi a dakin, ta dubi Ibrahim wanda yake cin moriyar baccinsa har wannan zamani. Ta yaye kayanta dake gefe guda ta shige bayan gida inda ta share mintuna sha uku sannan ta fito a shirye ta debi wasu kudi ta zuba a jakar dake rataye a kafadarta 8 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid sannan ta fita daga dakin a hankali ta ja kofa don tabbatar da bata tashi mijinta ba. Shi kadai ne a ofis din yake fada da takardu. Ko wacce ya dauko sai ya jefar da ita ko ya mai da ita inda ba nan ya dauko ta ba. Ya ki gaya wa kansa gaskiyar cewa ba sune ke cikin bukatunsa ba har sai da ya kammala tarwatsa su sannan ya kalli katuwar talabijin din bangon gabansa dake watsa labaran CNN ita ma tuni ya san hankalinsa baya tare da ita illa ga mafitar da bai da ita kuma ya kasa nema. Kamar yana daf da abin da bai taba yarda zai yi ba a rayuwarsa, shi ne ya je ya kwankwaşa kofar Na'ibi ya mika masa farar tutar sallamawarsa kan yakinsu na kasuwanci da ya rikide ya zamo na cikin gida. Ya shafi fuskarsa da hannu biyu sannan ya zuba hannayen a keya yana juya kujera. Baya so ya ci gaba da gaya wa kansa hakan ba za ta taba yiwuwa ba don kuwa dole ya nemo mafita kan tuggun da ya saura awoyi ya fuskanta a hannun Na`ibi. Maimakon hakan sai ya ji yana bukatar ya waro wa kansa abin da yake jin ya maida wannan fadan na cikin gida a gurguje. Ba wani abu bane illa shigar Farida da nuna kwarewarta a kan kamfaninsa. A lokacin tana son dansa ba wai bata so ba, kuma ya zaci hakan zai sassauta kayen da yake sha muddin za ta yi amfani da alakarta da dansa a ofis ta sassauta masa, amma ga mamakinsa sai ga Faridar har cikin ofishinsa ta kawo masa takardar sanya hannu kan amincewarsa da kayen da ta ba shi a fagen 159 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid fayyace talla. Da fari ya zaci wani sassaucin ne ya kawo ta koda ba wanda ya zata ba, amma duk da ba ta yi masa wani rashin kunya ba ta bayyana bukatar ya sanya hannun da ya tuno mata da nata bukatun gare shi, murmushi ta yi ta kada kai ta ce 'Uncle wannan batun kasuwa ne ba batun alakata da gidanka ba, kada mu juya shi zuwa çan, nan ina gwada kwarewata ce kan abin da zan iya a fagen karatuna, babu mamaki in ka taya ni murna da cewa 'yar nan taka tayi nasara kan aikinta ba a kan ka ba ta juya ta tafi bayan sallama. Yana isowa nan a tunanin ya ji baya bukatar ci gaba da tuno baya illa gaba, amma sai wayar ofishin ta katse shi indaya danna yace me nene? "Sir Miss Farida Bici ce a nan ta zo ganin ka Muryar sakatariyarsa da ta furta wannan kalmomi ta sauya a zuciyarsa inda sunan Farida da ya nanata a zuciyarsa cikin fargaba da tsoro yana zatoa kan harshensa ne har ma yayi tambayar me ta zo yi, amma bai san bai ce komai ba sai da ya ji daga can sakatariyar tana ce masa, 'Sir kana ji na?' Ta shigo' Ya mayar da wayar yana jaddada wa kansa bukatar ta shigo koma da me ta zo tun da babu abin da ya ragu masa da zai iya ko zai guda, daga wannan 6angaren, duk da zuciyaarsa na tsoro da kunyar hada ido da Farida, amma can 160 Мадyan Masoya Rahma AbdulMajid wani bangaren na son sanin me ya kawo ta. Ta tako a hankali idanuwanta suka iso kansa da yake kallon ta babu abin cewa, tayi murmushi sannan ta kalli baya ta mayar da kofa. Yana ta sha'awar ya tambaye ta me kika zo yi a ofishina, amma salon da zai fara tambayar da shi cikin salallakin da ke cunkushe a zuciyarsa ya kasa zabar ko guda. Har-zuwa lokacin da ta iso ga wata kujera ta dafa jakar hannunta ta zazzalo zuwa wuyan hannunta. Та karade ofishin da ido a yayin da ta fara magana kamar haka. "Na taba shigowa ofishin nan a wasu shekarun baya a matsayin yar kasuwa" Ta zuro ido a kansa yanzu.... na zo ne a matsayin matar auren danka..wato sirikarka mai dauke da jikanka a ckinta kuma wadda ta zamo rukuni a iyalinka da son ka ko babu...idan za ka iya ba ni mazauni mu tattauna abin da ya kawo ni bana wato matsalar gidanmu ni da kai zan gode" Kalmomin sun shige shi ta inda yake jin zasu iya zuwa da sassauci daga Farida amma ba zai so su ba, sai dai ba shi da zabi ban da sanyaya murya ya nuna mata kujera don ta zauna. Ta gode masa cikin murmushi sannan ta zauna ta dora Jakarta kan cinyarta ta rungume tayi gyaran zama sannan ta fara magana. 1 Mafiyan Mosoya Rahma AbdulMajid "Na san ba ka mamaki in ya zamo zuwa yanzu na san cewa ka yi yunkurin kashe ni ni da fan cikina don ka rabu da matsalar mu ka * huta...Amma ni har yau ina mamaki da takaici da murna, domin na yi iya tunanina na ga matsalata bata kai wadda za ka rabá ni da raina, dalilin mamakina kuwa shi ne ni har yau duk da abin da ka yi min ba zan iya raba ka da danka ba. Amma ka san abin da yake sanya ni murna? Shi ne yadda ka sallama cewa fitar ran daya ne tsakanina da Ibrahim shi ne zai iya raba mu amma ba wani tuggu ko makirci ko hargagi da takunkumi ba....oh! dama yadda ka fahimta da wuri haka nawa uban ya fahimta" Ta sake dauke batu ta gayara zama a yayin da yake kallon ta cikin ransa yana cewa me kike so Farida? '"Abin da ya kawo ni zai ba ka mamaki idan ka ji shi...shi ne nace ba na tare da abin da na sami labarin mahaifina na shirin yi maka...kamar yadda na gaya maka ba zan iya raba ka da danka ba musamman yanzu da nake shirin zamowa uwa na san yadda uba ke zama uba a idanun danka na san ciwon rabuwarsu tun ba mu haifa ba....na san cewa ya hada kai da babana ne don kawai ka so raba shi da iyalinsa...ina nufin dansa da matarsa, ka ga ha san zafin rabuwa ba zan so in yi muku haka ba kuma abin da mahaifina ke shirin yi muku ke naa... ba don kai ne ba zan bar haka ta faru ba sai don kasancewarka uba...don haka ina so ka Motiyan Masoya Rahma AbdulMajid iya sanyawa zuciyarka igiyar rahma ta amince da cewa ni da danka da jikanka iyaline da raba su laifi ne....in har ka yi haka na yafe maka yunkurin kisan da kayi mana har ga zuciyata, ba zan kai ka kotu ba, ba zan bari mahaifina ya raba ka da danka ba." Ta dan sassauto tausayi da ladabi a fuskarta tana kallons. "Ba wani aiki ba ne na kaskanci ba...aiki ne na mutuntaka da sanin ciwo da hekkin dan adam...ka daure ka yi domin wandn kake rufe ido kana son yi ba zai taba samuwa ba...ba za ka taba iya yi ba...danka na kubutar da shi daga wurin babana, na gamsar da shi cewa bai kamata yayi abin da babana yake son yi ba...yana Amana Suite, a Adamawa Suite zaka same shi...zan so ka je ka same shi ku sasanta. Bai san zan zo wurinka ba na bar shi yana bacci don bana so ya guji ganinka....na bar sunanka a reception cewa za ka zo su baka mukulli,ni zan je kasuwa in sayo mana kaya, don Allah don jini ka daure ka je ku sasanta ka bar komai ya wuce, a shirye muke mu bar komai ya wuce ku bar mu mu rayu alaluma"" Ta mike da sauri ta bar kujerar. "Wannan shi ne abin da ya kawo ni... kamar yadda na ce a farko a matsayin rukunin iyalinka ba a `yar kasuwa abokiyar gasar kasuwanci ba, na bar ka lafiya" Har ta kai kofa bai iya cewa komai ba kamar yadda zuciyarsa ke cikin sauki, kunya da 163 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid kauna. Sai da ta murda kofar za ta furta sannan ya ambaci sunanta a hankali. Ta juyo ba tare da ta cire hannunta daga kofar ba. Kallon ta yake. 'Na gode kwarai, kin yi min abin da ban san wa zai iya yi min ba...ni ma zan yi abin da kika ce har da dori...na gode matuka" Ta dan lumshe ido ta yi murmushi. "Na gode ni ma uncle sai na ga aikinka'" Ta juya ta fita ta rufe masa kofa. * Wilson da mai gidansa dukansu shiru suke tsit suna tunani. "Waye ya san wannan sirrin da ya gaya wa Farida...Wilson daga ni sai kai muka san lamarin nan (in details) kuma yadda Farida ta iya sani ta gudu ta je inda Ibrahim yake ta gudu da shi yana nuna ta san labarin filla-filla'" Wilson yayi murmushi kamar yadda ya saba. "Amma ogana ka san ni da kai ba wanda ya fada mata ko?"" Ya kada kai. "kwarai kuwa! Bana tuhuma ko shakkar ka ina ta tunanin waye zai hada mata zancen yadda yake'" Ya tashi daga hannun kujerar da yake. "Ogana ka bar tunanin yadda aka yi ta sani ta riga ta sani yanzu muna bukatar su a hannun mu nan da awoyi goma sha biyu" Bici ya sanya kara. 4 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid "Mu yi me da su? In sun zo hannu kana zato Ibrahim zai bi tsari na ne bayan ya san Farida na hannunsa kuma ban ce mata komai na alheri kansa ba?" "idan sun shiga hannu sai mu sake tunani Master... muna bukatar su domin ko ba komai in muka bar su suka shiga hannun Abdul Hadi an kwafsa" Sai da ya jima yana kallon Wilson don matukar yarda da hangensa sarnan ya girgiza kai. Ya sake tuno wannan hangen a matsayin wata barazana mai karfi. 'Ina son ganinsu nan da awa goma sha biyu ba sama ba...ka san yadda za a yi karnika su shinshino su" Ya mike zai fita. "Sai dai a kara, amma tuni an fara haka'" * A shago daya ta ke duk tsayin lokacin nan tana zabar wa Ibrahim riguna guda hudu kala daban-daban da wandunan jins guda biyu da takalmi daya, sannan ita ma ta zaba wa kanta takalmi da jaka biyu da siketi da riga guda biyu. Ta koma бangaren tirare da kayan shafe-shafe na maza da mata ta zabo musu duk abin da ta san suna amfani da shi sannan ta zo ta biya kudi da kwalin Master Card sannan ta fita ta dauki mota. A kofar suite din ta dinga jiwo shewa da wasa da dariya. Tuni ta tsinci fuskarta cikin murmushi domin tuni ta dauki muryarsu. Uba ne da dansa suke jin dadi. Wato AbdulHadi ya zo kuma har 165 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid sun sasanta bá sai ta zo tayi dogon baki ba..ta ji tana farin ciki da tinkaho kan abin da ta hada sai da ta dauki mintoci a haka sannan ta dan danna karaurawar.daga ciki muryar babba ne ya amsa da cewa. "Yes coming, the door is opened, and am here with my son, I cant wait to see my daughter-inlaw with us' od ida ab d Da sauri ta shigo cikin jin Rarfi. Ibrahim idanunsa na kanta cikin dariya kamar yadda mahaifinnasa ma ba a bar shi a baya ba duk suna zaune a doguwar kujera makale da jikin juna.Duk suka mike bayan ta zubar da kayan hannunta wuri guda ta tsaya, suka zó gare ta inda dukansu biyu AbdulHadi ya rungumo su a kafadas ninhns "Sannu da zuwa yata Farida.ga ni nan da iyalina dake da dana da jika na dake jin mu a cikinki cikin farin cikin da ba wani bane ya hada shi ba sai ke'w ot iuk ad ass usnsA Ya juyo gare ta musamman bayan ya saki Ibrahim wuri daya wanda yake kallon ssu cikin farin ciki. w isade sh ninetms io vIn "Farida.. na gode da farin cikin da kika sanya ni da ilmantar da hi da kika yi da kúma uwa uba yaye min takaicin laifin da na so yi ta hanyar yafe min da kikä yi. Hakika da na fi kowa danasani inda a ce kin mutu a yanzu da na san amfanin ki. Farida ke sinadari ce me kyau ba guba ba, kuma zamu ci gaba da zama iyali. Dama ke 'yata ce Farida, na kalle ki a matsayin yata funda aka haife ki, wannan kallo ya dawo da kansa yanzu a zuciyata, ke ba surika ba ce kawai ba, yata ce da 165 Mafyan Masoya Rahma AbdulMajid jini na ba zai sake nisanta ba...na san kina kewar mahaifinki a nan...dama a ce shi ma yana nan yana samun madadin fahiıntar da muka samu, kada ki damu, dama tare muke a da, kuma yanzu zamu koma tare, zan dawo da abokina cikin iyalinsa a yau ba a gobe ba shi ne goro na gare ki....zamu maimaita wannan zaman a cikin satin nan har da shi ko a gidansa ko a gidana kafin ku koma na ku gidan" Ya juyo ga Ibrahim cikin murmushi. "Ibrahim ko Bally kamar yadda matarka ke kiran ka...ga Faridar kaka so ta iya so ka rike amanarta iya iyawarka ka rayu ka mutu da ita domin ita ce me son ka Ja gaskiya... na gane amfanin aurenka da Farida yau kamar yadda na gaya maka dazu, domin da babu Farida a iyalina yau da na halaka, amma ta ceto ni kuma na cetu. Ku zauna tare ku ci gaba da nuna wa juna kauna, yanzu zan bar ku in je wurin abokina kuma mahaifinta mu sasanta, ina so ya san amfanin wannan dadin zama da muka fara ci kum ya zo mu ci amfanin da shi... sai na dawo" Ya juya bayan sun masa godiya cikin matukar annishuwa suka yi masa rakiya har ga motarsa ya tafi. Ibrahim ya mayar da kofar falon ya rufe bayan Farida ta shigo suka fuskanci juna. Ya kamo hannayenta ya zubo su a kugunsa sannan ya rike ta. "Ban san me zan ce miki ba Farida, kin cika kirki, ba ko wane ya kai ni sa`a a duniya ba tunda na same ki...yau in kin san farin cikin da kika 167 Mallyan Masoya Rahma AbduMajid samar mini da cewa zaki yi in kwanta karkashin kafarki....Farida kin kwance min duk abin da na kasa kwancewa kwanaki da dama...ke ce rayuwata" sa. Ta dan langaba wuya tana ci gaba da kallon "Ina eikin matukar farin ciki Bally...ina jin dadi ban san ina zan sanya kai na ba" Ya janyo ta zuwa kirjinsa ya sunne kanta [sakanin Kasusuwan hakarkarinsa na sama. 'sanya min shi a inda ake bukatarsa.... Ina son ki Farida rayuwa baki ba rayuwa ba ce" A falon karatunsa ya tsaya bayan ya sanya teburi a bayansa don majingina yana kallon 'yar karamar talabijin din dake nuna masa wanda ke shigowa. Lallai baya dauke da makami ko wani sinadari me cutarwa, amma bai gama amincewa ba tunda talabijin din ba ta da hurumin ta nuna masa zuciyar mutumin da abin da ta kunsa. Tunaninsa bai wuce biyu ba kan dalilin da zai sanya AbdulHadi ya bukaci ganinsa har gida ba sai abu biyu. Ko dai don ya sami ganin su Farida ya san makircin da aka shirya masa ya kwance, ko kuma bai riga ya gan su ba ya zo sallamawa. Ya fi damuwa da zaton farko domin ya fi ba shi tsoro, kuma na biyun bai saba da faruwa ba. Tunda Abdul Hadi bai taba sallamawa ba sai ya ga kayen da ya sha a gabansa. Yana kai wa ga isowa ga kofar falon sai ya kashe talabijin din ya gyara tsayuwa. "Come in" S Mafivan Masexa Rahma AbaulMajid Bayan Karaurawar ta nemi izinin da va bayar da damar bayxanar, AbdulHadi kemarayaddo KSIS gan shycikin shigar, ofis amma babu tayi a wuya KKMW Ya dunfare shi suka hada hannaye fuskarsa cike LSAUWRIS da zargi da rashin wawalwala ST SOUW duk BOaghai da Kokarin da பாத AbdulHadin yake yi na wanzar da zaman lafiya a fuskarsa, amma ya dauki hakiujjar aukuwar zatou tist sease niss sai nee as bab а zauna mang swux si ovnsj BY AbdulHadina ambala mushi. Amma ya kasa don Kara kuiybMe fire "Me kake neme Hadilsd ewys gbinsh it 02 Ya nemi kujera ya zaunı yana dariya. syasKujera pake nema kaizg ka sauya balsd Bey enignijam nob gansysd siурor ок рема majinginarsa,daYO sw ox imsalem shotusb sved islls swogina sallamawa ba w baSm harabarka he d "e lde d an kave aகின் hannumka,Bic, amna ni namUAAY GAISDS da hana imaniW da karewar nast/butf epuw isd aninврит ad Raar, da fyskarra kameriradda hah ДОВ ТЕ wnkashwannan zanesda balsabajhe nee sv ne na fahimtar da kaidyanikayenla muka sha daer hiharker kon m kai abaiya yanmyFarida de hrghHvibayan un mutane 1 doron duniva deba atsun deany dakowa h b da doo haka mnikin mallake,kay rayuwargy de muke son yi ba zai samar mana da nasaara ba..hakika mu muke fada kuma muka dulmiyar.. da I GOC 169 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid kamfanonin mu da suke jingine da mu a husumar, amma lokaci yayi da za mu san cewa su Farida ba kamfanunuwa ba ne don haka ba za mu sanya suı a abin da basa ciki ba... ni dai a nawa bangaren na zabi mu bi su maimakon su bi mu

Chapter 9 of 11