ka yi aikin nan ka yi
ba?"
"Ka yi hakuri baba, ina son ta ba zan iya
cutar da ita ba"
Ga mamakinsa sai ya ji mahaifin nasa ya
fashe da wata dariya da ta cika falon, har yana
kamo hannun Ibrahim yana tafawa da shi a dole.
"Ka yi min wayo yaro...kai amma kana da
wayo...je ka ka huta je ka ka huta"
Ya hana Ibrahim magana har sai da ya
hakura ya tafi nasa falon a kidime be san me
mahaifinsa ke nufi ba.
Yana sosa kai kwance a doguwar kujera
wayar ya danne ta da kafadarsa can kusa da
kunnensa.
"Ina ga hala da yake yanzu ya ji maganar shi
yasa tayi masa banbarakwai, kuma ya kasa
sanin ina zai dosa da maganr kawai dariya yake
'wai na je na huta'
Ta yi shiru ta rasa abin da zata ce ban da
ajiyar zuciya, can da ya ji shirun yayin yawa
yace.
96 Mafiyan Masoyа Rahma AbdulMajid
"Zamu yi magana anjima na sani in ya soma
sabawa da zancen watakila mu kai ga wani abu
mai muhimmanci yau watakila kuma a kai wani
sati, amma kamar yadda muka tsara duk abin da
ake ciki ba zai wuce wannan satin ba..."
Ya dan hada ido da ainahin abin da ya ke ta
zaton inuwar zuciyarsa ce, ashe da gaske baban
sa ne a tsaye a falon.
"Bari zamu yi magana an jima"
Ya furta mata hankalinsa na kan baban nasa.
"Kana magana ne da matarka?"
Kalmar ta fi zamowarta tambaya haifar da
mamaki da rikicewa, kafin yace eh sai da ya
tambayi kansa ko me mahaifinsa ke nufi da
amincewa yayi amfani da Kalmar mata kan
makiyiyarsa Farida?
Ya yanke shirun da zama a gefen kujera.
"Ka ce tana da cikin ka ko?"
"Haka ne Baba"
Yanzu bai da zabi baya da amsa ko wace
tambaya yadda ta zo. AbdulHadi ya shafa kai
sannan yayi wata 'yar makyarkyata ta nuna
karaya tun kafin a fade ta.
"Da na na yi wauta, na raina ainahin son da
kake yi wa Farida, har na baka wannan hidima
da ka kasa yi min. sai dai duk da zafin da na ji
na kuma yi tunani na ga cewa ban yi asara ba...
Na'ibi ya dade yana cuta ta kuma yana yin
pasara, ban so hada zuri'a da shi ba, na so na yi
amni da 'yarsa na rama wasu sashi na cutarsa
gare ni, amma kuma a nan ma ban yi nasara
&
97 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
ba...hum! Ko da yake na hangi nasara ta wani
bangare wanda shine karin samun zuri`a a
gidana. Ibrahim ba da tsarina ka zamo shik enan
dana ba, na yi iya kokarina na sami kari, amma
abun bai yiwu ba, na mika wuya ga cewa zan
sami wannan kari ta hanyar ka, to ga shi ka fara
cika min burina..."
Ya mike tsaye ya zuba hannu a aljihu.
"Zan karbi Farida saboda jini na da ke tare
da ita ina son sa...'
Ibrahim wanda ya tuma tsalle ya mike ba
tare da ya sani ba da yake murna ce zalla ke
sarrafa shi ya doshi kirjin ubansa wanda suke
musayar idanu...
"Baba da gaske zaka amince da Farida?"
"ka je ka kawo ta, zan tafi tare da ita, zan
taka har gidan Na`ibi da farar tuta mu rungumi
juna saboda martabar abin da ke cikinta"
Ibrahim ya shige jikin mahaifinsa yayi masa
kam har ma yana juya dan tsohon mara alamar
nauyi. Yana furta, 'ina son ka ubana...na gode
ubana' hawaye suka fara zuba a idonsa.
Da kyar baban ya shawo kansa suka sake
zama, kuma ya hana shi zumudin kiran Farida
da yake ta yunkurin yi da niyar su zauna su
dumfari abin.
"So nake ka yi mata ba zata irin wanda na
taba yi wa mahaifiyarka... so nake kace mata ta
zo na ki yarda zaka shirya mana wani fito-na
fito. In ta zo ka bari kafin ta fara haduwa da
kowa ta gan ni kwatsam, sai nayi mata albishir,
98 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
cikin wannan muma tata mara iyaka nake so mu
je gidan Na`ibi"
Ibrahim wanda cikin zumudi daka kawai
yake ta amsawa yana shirin sake latsa lambobin
Fasrida sai da dakyar Abdul Hadi ya sake
shawo kansa.
"Dakata! In ka yi magana da ita yanzu cikin
wannan farin ciki ai zata gane. Kawai ka daure
ka kyale har sai an jima ka soma sabawa da
wannan farinciki inda zaka iya daurewa cikin
maganarka ba tare da ta gaue ba"
*
Duk da doki da damuwa da Farida da
Ibrahim ke ciki kan ganin muhimmancin
zuwanta a washegarin amincewar babansa, dole
zuwan nata ya sami jinkiri sakamakon yawaitar
hazo da ya hana akasarin jirage tashi daga
ilahirin yammacin turai, abin da ya kara jinkirin
kwanaki biyu kan yadda aka tsara, abin da ba
yana na nufin Ibrahim da Farida ba kawai, har
ma iyayen Faridar masu shirin tafiya Maroko ba
zasu sami ganinta ba kasancewar zata kara yini
biyu kan iya yadda zasu iya jiran ta. Wannan bai
zo wa Farida da damuwa ba domin a kankin
kanta ta fi son ta zo basa nan har su kammala
tsarin su ita da Ibrahim da mahaifinsa kafin su
dawo don ya zamo da sun hadu sai dai a tare su
da gaskiya tsagwaronta. Kamar yadda
AbdulHadi ke ta tsara wa dansa yadda za a yi
ko zuwa dauko Farida daga filin jirgi bai bari
yayi ba, cewa yayi duka su je ainihin kulob din
99 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
da su Faridar suka saba haduwa su jira ta a can,
Ibrahim yace mata can zasu hadu, in ya so
maimakon shi sai ta ga mahaifinsa yayi mata ba
zatan albishir. Ibrahim ya ji dadin shirin kuma
ya aiwatar duk da cewa ita Farida da bata san
dawar garin ba abin na matukar damun ta,
amma ta daure, hakan ya sanya ta tuno tsohon
aboki Farid, wanda tace ya zo ya dauke ta daga
filin jirgi zuwa wannan kulob.
Farid ya zubar da duk wani ratayayyen kaya
da ke kwabarsa yana wake-wake na jin dadi,
amma bai gamu da kayan da suka yi wa wannan
rana ba. Ya fara yanke tunanin zai garzaya
shagon sayar da kaya cikin gaugawa don haka
ya fara kwashewa yana watsa su ciki tunda babu
lokacin sake tsara su.
"Wannan da ka dauka ta dace da fitar ka da
Farida zuwa Club muddin ba matsa wa kanka
kake son yi ba"
Mahdi ne wanda ya gama huce takaicin sa a
falo ya biyo Farid faki yake fadin hakan a
yayinda ya farga da wata farar shet mai jikin
roba da gajerun hannu da Farid din zai jefa a
kwaba.
"Kai Allah? Da me zan hada ta?"
Ya karaso ya karbe ta.
"Kwarai zata kawata surar jikinka in ka
hada ta da dirty jeans. Sun dace da zuwa Club
din da ba dole ne ka sami abin da ya kai su ba a
kasuwa in ka jc yanzu"
100 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Farid ya jefa ta bisa gado ya dangana da
ma`ajiyar wanduna na musamman ya zaro
ainihin jins din da Mahdi ya kwatanta wanda
aka yayya6e shi da wasu riguna da ake hada su,
ya zare shi ya jefa shi kan gado sannan ya daga
wa Mahdi manyan yatsunsa biyu na nuna
jinjinawa kana ya fada bayan gida a gujc..
A falo ya hadu da Mahdi bayan ya gama
shiryawa har da wani farin takalmi sawu ciki
mai tsinin baki, turare na tashi, yana goge
fuskarsa da hankici na gumin zumudi dake
tsattsafo masa.
"Mota ta ba laifi kuwa? Ko kana ga...?"
"Bata ma san ka da mota ba tace ka zo ka
tare ta, haba mutum! Ka je ka tare ta a
matsayinka ba a na wani ba"
Ya juya zai fice yana girgiza kai.
"Ka ce jumla mufida! Sai na dawo"
Mahdi ya kwanta a kujera yana masa kallon
raini da dariya.
"Allah Ya ba da sa'a
Ibrahim na zaune a motarsa ya kwantar da
kujerar direba gefensa akwai mahaifinsa da suke
ta hira ta annishuwa har zuwa lokacinda ya
hangi tsayawar motar da yayi zargin Farida ce a
ciki. Cikin murmushi ya dada lafar da kansa ya
dubi mahaifinsa
99 "Ga ta nan"
Suka zubo mata ido yayinda take musayar
dariya da saurayin da ya dauko ta wanda shi ma
101 Maliyan Masoya Rahma AbduMajid
har ya sauko daga motar, amma da alamun
Farıdar ta gamsar da shi wasu maganganu da
suka sanya ya koma cikin motar koda yake
jikinsa babu laka.
"Wa nene wannan tare da ita kuma?"
AbdulHadi ya tambaya idanunsa na
kaikomo tsakanin Farida da Ibrahim.
Daya daga cikin ma'aikatan babanta ne da
tace ya je ya dauko ta tunda ni ban je ba, ina ga
sun dan fi shakuwa ne shi yasa"
Ya dawo ga babansa firgigi.
"Ta shiga Baba ka je ka same ta ku tattauna
ina so in je wurinta ina kewar ta, ba zan iya kara
dadewa fiye da wannan ba"
Yayi murmushi sannan ya doki kafadar dan
nasa.
"An zo karshe ai me kake ci na baka na
zubewa? Yanzu zan ba ta kyautarta kai kuma ka
shirya duk taka ce"
Suka tafa ayayinda wayarsa ta yi wani kuka
na musamman. Ya zaro da murmushi na ganin
lambar Farida.
"Toh ga ni na zo baka dauko ni ba, baka kai
ni gidanka ba, ka ce na zo Club duk na cika
umarninka me gida sai ka ba ni goro na"
Yayi murmushi ya lumshe idp.
"Minti biyar yayi yawa zaki sami goron ki
na san kin iso wurin ai, kuma ni ma ina nan
kusa dake kin ji?"
Mahaifinsa yayi dariya ya kashe masa ido
sannan ya fita a yayinda shi ma ya kashe waya
102 Mofiyan Masoya Rahma AbdulMajid
yana bayyana dumbin farin cikin da ya cika
masa ciki.
Can gefen wani ruwan ninkaya ta zauna kan
wata doguwar kujera da ta fi kana da tsinin
bishiya, idanunta na kan masu kada jitar da basu
fara waka ba amma ba don tana matukar tare d
su ba. ta kan dakata tayi waige-waige, amma da
ya tabbatar mata da saura mintuna biyar sai ta
gwammace ta mayar da hankali ga wuri daya
har zuwa cikan mintunan.
Ya bayyana a gabanta kamar mafarki sanye
da fararen sut da wando, ciki akwai shet mai
ruwan kofi. Yana murmushi har suka haďa ido a
yayinda ta mike tsaye ba tare da ta san ta mike
ba illa da zuciyarta ta tilasta mata yin hakan.
Kwarai gaban ta ya rikito kasa, amma can cikin
kwalkwalwarta sai ta ji kamar ta soma samin
fassarar wannan ba zata da mijin ta ke son yi
mata yana cakudewa da faduwar gabanta.
Mahaifin sa ne zai yi mata maraba da kansa
zuwa cikin wannan zuri'a ke nan!. Ta ji
faduwar gabanta na cakuduwa da murna, bugun
zuciya, da. saukar wani nauyi da jin nauyin
kuma. Mutumin da ta jima tana taka rawa a
ofishin mahaifinta a fannoni da dama na dakile
kasuwancinsa duk kuwa da suna soyayya da
dansa. Bata dauki hakan komai ba illa yakin
kasuwa da ofishinta keyi da wani ofishi don
nuna kwarewa kuma shi ya san ta a hakan,
sannan a zaton ta hakan zai taimaka wurin kara
fada-a jinta a kunnen nata mahaifin da take
:
103 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
ganin kamar shine wuka da nama na wannan
gaba. Da fari saurayinta kuma mijinta a yanzu
Ibrahim ya sha kira da babbar murya kan tayi
watsi da wannan taka leda da take a madadin
mahaifinta da cewa abin zai ci gaba da jan kafa
kan harkar soyayyarsu, amma a lokacin gani
take Ibrahim na hakan ne kawai don ya kasa iya
ja da ita a harkar kasuwancin. Amma a karshe
ya samu ya fahimtar da ita cewa ko kadan baya
nuna iyawarsa don kayar da ita shi yasa suke kai
labari kuma hakan na janyo wa mahaifinsa
asarar da kansa shi ma ya ji yana zargin son ta a
gare shi. Ta gamsu da wannan dalili wanda ya
sanya ta kaddamar da murabus dinta daga fadar
mahaifinta a ranar da Farid zai fara dora
idanunsa a kanta. Ko da yak eta dade da rage
zuwa aiki ko wannan taka leda.
Shin sirikin nata zai kale ta da wannan tariya
da take yi, ta tambayi kanta a gaggauce a
lokacin da ya nuna mata kujera da ta koma ta
zauna, shi ma yana kokarin zama da alamar
zancen nada tsayi matuka. Ya sake dariyar da ta
fan rikita ta ta ji ba ta bukatar sakankancewa da
zaton alheri.
"Farida kenan! Nice meeting you! Na ji
dadin ganin ki don mun dade bamu hadu
ba....ina jin tun a Honalulu ko wajen gabatar da
taswirar bankin lantarki ga central bank na
Kasar Kenya da muka gabatar ni dake bayan
dana ya ki halarta a saboda ke"
104 Моyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ta ji hantarta ta kada. Babu yadda za a yi a
tuno da wannan rana cikin mutunci ba ta ji
kunya ba. Rana ce da cikin ido da ido babu wani
shamaki ta kayar da sirikin nata a daya daga
cikin kwangilolin da suka kara fintikau ga
kamfanin babanta kan nasa kuma ta hanyar
siddabarun da lallai ya san ita ce ta aikata.
Ya dan shafa gefen hancinsa da yake fitar da
maiko sannan ya katse tunaninta.
"Na zo miki da ba zata kamar yadda dana ya
gaya miki, amma bana jin ba zatan irin wanda
kika taba zata ne"
Ta ji ta amince da maganarsa amma da me
ta amince ciki bata sani ba.
"Dana ya so ki Farida so na hakika, amma
daga baya ya amince cewa rawar da kike takawa
wurin daidaita mahaifinsa ba wai kawai ba zai
bar ku ku yi soyayya ba, a a sai ma kina bukatar
a dauki fansa a kanki... Farida kin yi gagarar da
ta baki kariya ta hanyar komai da zamu iya afka
miki da ita baya da soyayya, don haka in na
gama yi miki bayanin abin da muke nufi dake
ina fatan ba zaki yi fishin mun yi amfani da
zuciyarki ba, mun kasa yi ne da kasuwa"
"Me kake son gaya min?"
Ta ji ta tambaye shi ba da saninta ba
"Farida kamar yadda nace miki dana yana
son ki kuma na bukaci da ya ba ni daman a
dauki fansa a kanki ta hanyarsa kasancewar ya
ji ciwon abin da kika yi min, shi yasa muka
sami yarjejeniya na cewa zan dauki nauyin
约
105 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
zamansa dake a Jamus don ya more dake kamar
yadda ya dade yana fata, amma bayan kin sami
ciki wannan kwangila zata kare ya rabu dake...
maganar aure da kuka yi duk akwai matakai da
muka dauka kan hakan da zasu tabbatar da shi a
bogi, don haka yanzu zamu koma yakin mu ne
yadda muka saba don dana ya ji dadin iya ja
dake na tsara hakan, domin bayan ma a ce ya
gama biyan bukatar soyayyarsa dake, na san
zaku iya kulla kiyayyar da zata ba shi damar
mara min baya mu fuskance ki da kyau. Don
haka cikin da ke jikinki ya zamo wata kyauta
daga garemu da zaki iya yin yadda kike so da
ita
Ya dai ga tana dariya da hakora, amma daga
shi har ita basu san ko ta me cece ba, don haka
ya ciro wata waya daga aljihun kirji na ciki ya
kunna ya mika mata.
"Idan baki yarda ba zaki iya gani a hóto
yadda muka tsara wannan yarjejeniya ni da
dana. Kuma zaki iya yarda tunda kika ga ya
amince da cewa ni in yi miki bayani dalla-dalla
don shi ba zai iya fuskantar ki ba...."
Tana kallon duk yadda abin ya faru a waya,
yadda Ibrahim ya zo ya karanta wa mahaifinsa
amincewarsa da yarjejeniyarsu da yadda suka
tafa suka ci gaba da tsarawa kuma Ibrahim din
yana dariya yana murna. Ta ji ya ishe ta bata
bukatar iya karasawa, saboda mintsinin da duk
ilahirin jikinta ke yi mata. Ta sami kanta tuni ta
106 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mike tsaye tana mika masa wayarsa ba tare da
ya mike ba shi.
"Me yasa kika tashi bamu gama magana ba
ai, a kalla kya tsaya ki gama kallon wannan film
din ko?"
Ta girgiza kai ta watso jajawur din idanunta
da basu da niyar kukan da ke son su da abota.
"Zan duba yadda zamu hadu...zan rama ta
yadda ya dace... ban da abin cewa yanzu
Ta saki wayar da ya ki karba sannan ta fice
daga wurin a guje cikin rangaji na nuna rashin
ikonta da ilahirin jikinta.
Motar Farid a yanzu tana makwabtaka ne da
ta Ibrahim a inda suka yi sabon faki. Yanayinsu
ne kawai baya makwabtaka da juna domin a
yayinda Ibrahim ke tsugune a kujerarsa kamar
me jin kashi yana jiran ko dai mahaifinsa ko
Farida ko su biyu ko waya mai kiran ya shigo.
Ya bi ya damu amma cikin farinciki, yarda da
zumudi. Ya kan dauko wayarsa kamar ya buga
ya ji sai kuma ya zargi kånsa da kansa na rashin
jimiri da yawan gaggauwa, a haka yake duk da
ya kan saci kallon Farid wanda ya kawo Farida
wannan wuri, amma da yake bai da wata sana'`a
da shi bai dame shi illa dai kallo na wanda zasu
gaisa nan gaba bayan Farida ta fito.
A nasa bangaren Farid ya rasa abin da yake
masa dadi. Ya kwantar da kujerarsa ya kwanta
yana kallon rufin motarsa. Iyakwandishan na
buga shi amma baya jin tana komai ban da kara
masa azaba. Wa Farida ta je gani a club kuma
C
이
107 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
me take nufi da shi, watakila fa tana son wani
ba shi ba abin da bai san yadda zai yi ba in ya
faru. A iya tasa wayewar na miji da mace ne
kan zo Club kuma shi na miji ne da mace Farida
suka zo, amma ba a shiga da shi ba ta shiga ita
kadai. Bangaren lallashine kawai a zuciyarsa ke
kokarin bai wa Farida wani uzirin da cewa hala
wani fannin kasuwancin su take yi a Kulab. Shi
ma kamar Ibrahim idanunsa basa nisa da kallon
kofar da Faridar ta bi ta shiga sai dai shi baya
satar kallon Ibrahim don wata manufa sai pon
kawai idanunsa sun ketara, domin bai gan shỉ da
Farida ba bai kuma san shi ma ita yake jira ba.
Duka sun yi arba da fitowar Faridar cikin sa`a
sai dai damar da Ibrahim ya samu na 6allo
motarsa ya fito don ya tare ta Farid wanda ya
farga da tana nufo motarsa ne bai sami wannan
damar ba sanadiyar tsayawa ya gyara kujerarsa
da ya kwantar, watakila saurin Ibrahim ya kara
samun alaka da lura da yayi da fuskar Farida,
wadda tuni ya ji ta kayar masa da gaba sabanin
Farid da ke fatan ta sami 6acin ran a wannan
wuri da ya ke jin ba a shiga da shi ba. Ga
mamakinsa sai ya ga makwabcinsa ya sha
gaban Farida har da daga hannunsa na dama
kamar zai ruko wani sashi na jikinta baya da
wani kallo da ya lura tayi masa na tsayar da
hakan. Farid ya ji yana jiran karin abin da zai sa
ya fita ya nuna wa Farida mazakutarsa ko
kiftawa baya yi.
"Sako ya isa yadda ka tsara"
108 Mofiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Farida ta ambata cikin murya mai rauni
amma cike da kuzari. Ibrahim tsakani da Allah
ya rikice sai da ya hadiye wani yawu da ya
tsaya masa kafin yace 'Baby me ke faruwa ne?
Baba na ne ya...?"
Tuni ta kaikaita ta wuce shi tana sauri ta
doshi motar Farid yayin da shi yayi tsaye a
rikice ya dube ta ya dubi cikin kulab din bai san
abin da zai yi ba. Tuni Farida ta fada mota ta
buga murfin da karfi.
"Mu bar wurin nan da sauri Farid"
Yadda ta fada haka a ka yi domin ya hadiye
tambayar da ya shirya yi mata na lafiya, ya bi
umarni yayi wa motar wawan taku.
Ibrahim ya fada cikin kulab din da iya iskar
nunfashinsa amma sai suka hada kirji da
mahaifinsa mai shirin fitowa. Ya dan ja da baya
kafin yace masa.
"Mai ka cewa Farida?"
Ya dan daga kafadunsa sannan ya soka
hannu a aljihu
"Babu komai na dai raba ku ne da yadda zan
iya.. tun da ka zaci ka fi ni wayo shi ne ni ma na
nuna maka ni na haife ka"
Ya matsa can kusa da mahaifinsa kamar
zasu daku duk kuwa da kokarin da yake na ya
mallaki zuciyarsa.
"Dad! Na yarda da kai ka yi min haka..."
Ya dawo da baya cikin nishi sama-sama a
yayinda mahaifin ke cewa.
3
E
109 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Me kake jira? Doke ni mana, mu yi dambe
saboda na raba ka da wadda ba zata taba son ka
ba sai don ta ruguza ka. Am sorry, na raba ku"
Ya girgiza kai ya fice daga wurin inda
mahaifin ke karar kiransa amma bai tsaya ba ya
fada motar kamar me sukuwa ya fige ta daga
wurin ya bar fasinjansa tsaye wato babansa.
*
Farida ta fara kasa kallon gabanta, duk da
tana zaton damuwa ce tayi mata kanta, amma
kuma abin ya soma faskara, tana jin muryar
Farid daga nesa yana tambayarta 'Are you
Okay?' ta gyada kai na amsawa wanda koda ta
gama, ji take har yanzu kanta na kaďuwa, ta sha
shiga damuwa iri-iri amma bata taba jin yanayi
irin na yau ba. Ji tayi ta rufe idanunta da sauri
saboda duk abin da take kallo gizo yake mata
kamar ruwa na narkewa, Farid na narkewa,
gaban motarsa da take faman kallo yana
narkewa kanta na ta gyadawa, babban su shine
nunfashinta da kamar yake fin karfinta. Tana jin
muryar Farid a tsorace yana kiran sunanta,
amma kuma muryarsa kara nisa take har ta dena
jin sa dungum sai wani yanayi maras dadin
kallo ko ji.
Farid tsaye a kofa idanunsa na zagaye
asibitin amma zuciyarsa na can tare da tunani
dubbai. Mai ya sami Farida ne ko kuma me ya
hada ta da wani? Dama tana da wani ciwo ne
bai sani ba? Uwa uba idan wani abu ya sami
Farida me zai cewa iyayenta? Yayą zai yi da
1
t
1
S
1
110 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mafarkin rayuwarsa? Duk rokonsa ga Allah
cikin buga bango shi ne kada ya ji mugun labari.
Yana jin tsoron kadaicinsu a wannan asibiti. Ko
shi bai san asibitin ba amma watakila su Farida
su san shi. Asibitin masu dashi ne kuma shi ne
mafi kusa da wannan kulab duk da yana wani
kadaitaccen layi, ma`aikatan asibitin har sun
soma dena kama da `yan kasa saboda tafiya bisa Ka`ida.
Likitan me kama da marasa lafiya saboda
kiba da katon ciki ya fito yana gumi ya
Бaбballe gaban rigarsa. Balaraben Misra ne
daga gani har ma a irin turancinsa. Ya dafa
kafadar Farid bayan ya tare shi.
"Ka kwantar da hankalinka da sauki, an cecі
Fayuwarta"
Şannan ya wuce da shi ofishinsa bayan
doguwar ajiyar zuciyar da suka yi duka. Ya
dauko robar ruwa daga firijinsa ya bude wa
Farid. Sannan ya koma kujerar sa yana magana.
"Da ta kara minti talatin ba a kawo ta asibiti
ba sai dai wata... kuma zai yi wuya a gane abin
da ya kashe ta baya da bugun zuciya da za a ce"
Wannan kalmomi suka sanya makoshin
Farid jin yana bukatan wannan ruwa ya
kwankwada idanunsa na kan likitan.
"Месе се taka?"
Tambaya mai tsauri, amsarta ta zuciya ta
wato rayuwa ta ta sha bamban da amsar da ya
daure ya fada cikin in-ina wato 'shugaba ta ce'
"Gaya min, kana bukatar mutuwarta ne?"
111 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
Ya dan matso da kirjinsa ga teburin ba da
saninsa ba, sai da zuciyarsa ta yi shakkun rashin
jin tambayar sosai kafin ta amince da cewa
tambaya ce wadda bata san ta ina zata ba da
amsarta ba saboda yawan amsoshin.
"Me ya same ta? Za ta mutu ne? Farida? Na
so kashe ta? Ka san ko me cece gare ni?"
Ya zubo tambayoyin wasu a hankali wasu
da karfi, amma likitan ko gezau.
"Shi ya sa na tambaye ka ko mece ce gareka
ai don ban sani ba"
"Ita ce komai na ina rayuwa don ita a halin
yanzu, ina kaunar ta da dukkan kaunata...gaya
min me ya same ta ba dai za ta mutu ba ko?"
Likitan ya karanci yanayin gaskiyar da yak
enema a kwayar idanunsa sannan ya dauki biro
ya kama rubutu.
"Mun sami sinadarin.... a shafe a
danyatsanta na tsakiya ta inda tsakaninsa da
hancinta baya wuce cm sha biyar har tsayin
mintoci biyar. Shakarsa da take da sauri kuma a
matsayin mai ciki na iya gaggauta toshe jijiyoyi
masu kai iska ga zuciyarta wanda hakan na
nufin bugu da karfi na tsaya daga zuciya cikin
kasa da sa'a daya, ka san me bugun zuciya ke
nufi...."
Ya tsayar da rub utun ya dubi Farid wanda
tuni ya mike tsaye.
"Ba zata taba kai kanta ga abu mai
halakarwa irin wannan ba, kenan mai iya
kusantarta ko ta jiki ko ta waya ne ka iya bata,
112 Mariyan Masoya Rahma AbdulMajid
kamar a lokacinda take tare da kai ne kenan ta
samu
"Shine zan kawo ta asibiti kafin ya gama
aiki in ni na sa mata? Baka tunani ne, Farida
shugaba ta ce kuma ina son ta....Amma ta...ta
sanya ni na kai ta Club... wani saurayi ya tare ta
daga waje kamar zai rike ta sai ta kauce...ranta
a bace ta fito daga club din amma ni ban shiga
ba... me ya faru kenan wannan saurayin ne ko
wani daga ciki?"
Likitan ya mike daga kujerarsa sannan ya
dawo ga Farid.
"kamar kana da gaskiya...amma zaka zauna
nan tare damu har sai ta farfado ta nuna mana
gaskiyarka... Nan ne asibitin iyalan gidansu...na
santa ita da babanta tun a turai...b azan yi wasa
da tsaron lafiyarsu ba. Don haka ka yi hakuri
nan da wasu a woyi zata dawo hayyacinta, zamu
sani ko baka da laifi ko zamu kira hankalin
jami`an tsaro kan lamarin"
Farid ya mike yana murmushi.
"Ko kwana nawa ne ba zan bar nan ba har
sai Farida ta farfado, ba don tuhumarka ba sai
don ta isa hakan a wurina..."
Masu aiki suna ta kai komo idanun su tun
suna kan Farid har suka soma aminta da shi
domin yanayin damuwar sa. Yayi wa abokinsa
waya sau daya don ya sanar da shi halin da yake
ciki, amma da ya bukasci dole ya zo ya same shi
kuma ya ki yarda da maganar Farid na kada ya
zo sai komai yayi daidai sai Farid ya kashe
•
113 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
wayarsa ya kara rasa abolkin hira. Wata kalma
da ta hanashi tsaye ko zaune sai zarya itace
Kalmar cewa Farida na da ciki. Ya rasa hanyar
samin tabbacinta domin kuwa likitocin basu
wata magana da shi ban da na cewa tana samun
sauki. Ya fi kokarin ya amince da zargin jin
kunne amma hakan ta ci tura. Cikin wa Farida
ke da shi? Bata da aure, kuma kamar ta fi karfin
tayi cikin da bai da uba. To me ake nufi?
Rainon turawan ne ya motsa? Koma me nene
ina ne mafita gare shi in har zancen ya zamo
gaskiya? Kalmar na dukan zuciyarsa ya ji yana
Allah-Allah Farida ta farka ya sami tabbacin
hakan fiyc da tabbacin wanke shi da laifi.
"Tana son ganin ka"
Wata bakar