nas mai saurin tsiya ta iso gare
shi ta yanke tunaninsa da kalmomi masu alamun
Farida ce ta farka. A zabure ya bi ta a baya suka
iso wani daki ba wanda ya san an kwantar da
Farida ba.
A tsaye akwai likitan wanda ya karbe ta
kuma ya tuhumce shi, suka matsa masa don ya
doshi gadon Farida cikin sauri wadda take
kallon shi da murmushi a galabaice.
ji?"
"Alhamdulillahi tun da kin farka yaya kike
Ta dan yi fari da ido.
"Kalau nake yanzu duk da na zaci ba zan
sake rayuwa da ku ba"
SO
Ya kada kai cikin yi mata kallon tausayi da
114 Mafiyan Masoyа Rahma AbdulMajid
Ällah Ba Zai nuna mana rashin ki ba, Allah
Ya Kara miki sauki"
"Likita yace wai na sami shakar wani
sinadari ne har sun dan dakatar da kai. Shi ne
nake gaya masa cewa ba za ka taba cutar da ni
ba ko ta halin kakа"
Ya dan dubi likitan sannan suka yi wa juna
murmushi.
"Suna yin aikinsu. ne kuma haka ya
dace...Basu san ma asibitin ku ba ke nan ashe
garin saurin na kawo ki asibiti mafi kusa na
kawo ki gida"
Likitan ya sanya baki.
"Aikina ne ya sanya ni in yi maka abin da na
yi kuma aiki na ne na nemi ahuwa gare ka, ka
yafc mana, muna kula da lafiyar wadanda kake
kauna ne kuma suka yarda kana Caunarsu.
Malama Farida na bukatar kara hutu da rashin
tuna duk wani mummunan tunani, don haka sai
a tace irin hirar da za a yi mata"
Suka sake gaisawa sannan ya juya ya fita ya
bar Farid wanda ya baro jikin gadon Farida ya
zauna kujera mai kallon ta.
Ta dan nitsa tana kallon sama cikin wani
takaici mai cakuduwa da dauriya.
"Bayan abin da suka yi min kuma suna son
kashe ni. Zan mai da martani kan wannan cikin
hanya mai tsanani"
Ya dan rankwafo.
A
115 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"da ba don likita yace kada a dame ki ba da
na so sanin ko su wa nene suka sanya miki
wannan abu, don bai kamata a kyale ba
Ta sake jaddada murmushinta na takaici,
sannan ta kau da kai daga gare shi.
"Ba maganar ka bane yanzu Farid. Abokan
yi na ne kuma zamu yi"
Ya yi shiru yana kallon ta har zuwa lokacin
da ta dawo da idanunta gare shi fuj'atan.
"Farid na yarda da kai kuma ina son boye
wani sirri na a cikinka... na san likita ba zai rasa
gaya maka ina da ciki ba, amma bana so su
father su sani yanzu... daga ni sai kai muka sani
sai likita, kuma zan bari ya fito a lokacin da ya
dace"
Farid ya kasa um ballantana um-um! Kalmar
da yake ta sha`awar tabbatar wa yanzu tabbata
ta kafar da motsinsa, wani duka yake ji a duk
ilahirin wani abu mai agazawa nunfashi da
kuzarinsa. Farida na da ciki da gaske. Ya kasa
koda gyadawa ko kada kai don nuna mata
matsayarsa.
"Farid zai ba da mamaki in a ka ce ina da
ciki ko...baka yi min wannan zato ba? Ka daure
ka amince, ban yi wannan ciki ta hanyar banza
ko lalata ba...ina da aure ne Farid, kuma cikin
yana da ubansa..."
Wayarta da take ta kokawa ta dauke
hankalinta daga Farid, bata wasa da duk wanda
ya san wannan lamba da aka kira ta a kai domin
ba ta wasa bace, ta karkata kai ta dauko ta. Bata
116 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
san lambar ba, amma haka ta daga. Farid wanda
yake jin mintsini a zuciyarsa ha jin wani karin
labarin dugunzuma zuciya ya tsinci kansa yana
mai amfani da damar kawuwar hankalin Farida
daga kansa don ya fice daga dakin kafin ta
ankara da kwayar idanunsa da ta kasa бoyс
labarin zuciyarsa.
"Farida don Allah ina kike? Just gibe me a
chance to edplaine, Please!"
Ta yi murmushi, tana me shaida muryar
Ibrahim wadda ta bayyana cikin damuwa.
"A ina nake? Ina duniya Balala ba daga
lahira nake amsa wayar kamar yadda kuka tsara
ba. Balli har da kisa abin yayi zafi haka? Kai
amma ka siyo aikin da tsada, Ibrahim haduwa ta
da kai ta saura a fagen daga ne kawai"
Baya iya cewa komai ban da Farida tsaya ki
ji amma duk maganar da ya dauko ta hana shi
karasawa.
Ibrahim na shaki sinaderin..... wanda tabbas
babanka ne ya sanya min a wayar da ya ba ni
domin na duba ajandar ku... tsarinku shi ne na
mutu da bugun zuciya sai a ce don ka ki karban
cikin dake jiki na ne ya sanya na mutu ko? Kai
da wannan tsari na ku ya kai ga nasara da kun
gama da duk wani abu mai suna Na'ibi, amma
kash! Na farka, kuma ina so ka daure ku sake
sabon shiri, ka san Farida bata san sallamawa
ba"
117 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ta kife wayar. Sannan ta dubi gefenta amma
babu Farid wamda ta zaci ya fita ne don ya ba ta
dama ta yi magana a waya.
*
Har dare Mahdi na kai komo tsakanin falo
da kofar dakin Farid wanda ya dawo ya wuce
dakinsa ya kulle ya ki budewa duk bugun da
kofar ta sha. Da misalin karfe takwas da rabi ne
Mahdi ya samu magiyarsa tayi kai ya samu
Farid ya bude masa kofa ya shiga dakin. Ya
same shi dunkule cikin bargo da alamar yana
fama da zazzabi. Duk dauriyarsa na kada suyi
abin da suka saba sai da ya ji Farid ya kule shi.
"Yanzu batun Faridar ne zai sa ka kashe
kanka? Ka zo ka kunshe kanka a daki har ka
fara zązzabi? Wai kai Farid..."
Ya juyo ya katse shi.
"Farida cikinta na aure ne ka san ma`anar
hakan gare ni...mad Farida na da aure da wani
ke nan tana soyayya da wani ba ni ba"
Ya zaburo ya tashi zaune kwalla na fita daga
idanunsa
"Ban taba zaton haka ba... na jira ta da
zaton zata zo ta ba ni isharar na fayyace zuciya
ta ban san tana son wani ba har na yi nisa,
amma ashe Farida ta yi nisa a soyayya...tabbas
in ba don tayi nisa a soyayya ba da me zai sanya
ta aure shi babu sanin iyayenta?"
Ya dan daki cinyoyinsa sannan ya harde
yatsunsa.
118 Mafan Masoya Rahma AbdulMajid
"Dama ya zamo wanda take so shi ne ya so
kashe ta...dama ya zamo wanda take so baya
son ta dukiyarta yake so don ta dawo neman
mai son ta da gaskiya ta same ni....amma kamar
abin yayi nisa sai dai na yi ta fata"
A hankali mamaki ya shigi mahdi kamar yadda ya tambaya a hankali.
"Kana fatan ka sake komawa son Farida duk
da tana son wani har tayi aure tana da ciki.Farid
kana da hankali kuwa ko dai kishiyar uwa ta
jefe ka? Ina zaton yaki kake da zuciyarka don ta
mance Farida ashe zaka sake komawa son ta har
da wani fata na banza?"
Ya dube shi ya mike tsaye.
"Zan iya baro soyayyar Farida ballantana na
sake koma mata? Mad ka san me na ke yi wa
Farida kuwa...Son ta nake, ita zallarta nake so
ka san ma`anar haka kuwa? Na isa in gaya wa
zuciyata ta bar Farida?"
Ya tura Mahdi waje.
"fita min daga daki, fita tun da kai ba me
ganewa ba ne"
Ya gwama kofarsa ya koma ya zauna cikin
rike kai yana furta Farida na da cikin wani da
aurensa ba Farid ba. A yanzu dai kuka yake.
*
Ibrahim ya ciro wani saitin kaya na karshe
mai ruwan toka ne wandon da riga maras hannu
mai ruwan kasa ya kalle ta da kyau sannan ya
jefa ta cikin akwatinsa sannan ya mai da murfin
akwatin ya rufe wanda ya dan rufe fuskar
119 Matiyan Masoya Rahma Ab duMa
babansa da ya dade yana tsaye a dakin tzbayan
akwati suka hada ido da Ibrahim da bai san
yana nan ba, amma ya ki nuna wani mamaki ya
mai da hankalinsa ga hada kayan da ke gabansa.
"Ibrahim zaka tafi ne ka bar gidanku?"
Ya hado wata jaka ta kayan wankansa ya
ajiye gefen gadon kafin ya mai da amsa.
"Zan dai bar gidanka ba wai gida na ba"
"Ko me nene dalilin da zai sa ka bar ni din,
ko dai saboda mace zaka bar ubanka?"
Sai da ya kulle akwatinan ya tsayar da
sannan ya fuskanci mahaifinsa.
"Musamman nake gaya maka Baba zan bar
gidanka kuma saboda mace, sai dai ba kowace
maçe ba, mace wanda nake so amma kake son
raba ni da ita saboda son zuciya. Ba kawai don
ka so raba ni da ita bane na yanke shawarar
karewar zamana da kai sai don niyarka ta raba
wanda baka so da ransa... Baba ka yi yunkurin
kashe Farida da dabara don kawai ka raba ta da
danka shi ne zaka raba ta da ranta da duniyarta,
zaka kashe matar danka ka kashe masa dansa
dake cikinta wai duk don danka ya tabbata
yadda ka zana rayuwarsa. Haba Dad! Mutum
irin wannan ya cancanci mu ci gaba da zama
tare?"
"Ita ta ce maka na shirya kashe ta?"
İbrahim ya kaďa kai cikin murmushin
tafasar zuciya.
"Ta ina zata gaya min? ka raba mu ai, kai ka
gaya min yadda ka raba mu ka nuna mata abin
120 Mafiyan Mosoya Rahma AbdulMajid
da ka dauka ban san ka dauka ba a waya ka raba
mu domin ba ni da hanyar kubutar da kaina a
wurinta...sai dai abin da ka 6oye ba ka gaya
min ba shi ne yadda ka sanya sinadarin bugun
zuciya a bayan wayar da ta shafa da hannunta
kai ka je ka wanke naka hannun ita kuma ta
shiga tayi ta shaka har abin ya kai ta ga
kwanciya a asibiti rai a hannun Allah. Ka so ta
mutu ka yada cewa kin karban cikin da nayi
mata ne ya sa ta sami bugun zuciya. Baba
kiyayya ta kai zaka kashe wa Na'ibi yarsa
kuma macen da danka ya fi so duk cikin matan
duniya don kawai ka tsara yakin kamfaninka,
ashe ke nan jita-jitan da nake cewa kuna amfani
da rayuka wurin yakin kasuwa kuna yi ke nan.
Ka cire ni daga littafin rayuwar nan Dad, ba za a
yi da ni ba, na rabu da kai da komai naka, mota
da zan dauka da kudi na aikin da na yi ne ba
wai na dukiyar uba da da ba. Tun da ba zan iya
zuwa na kai ka kara wurin hukuma ba a
matsayinka na uba na zan yi abin da zan iya
shine nisantarka a iya rayuwata a karo na farko
kuma na karshe. Sai wata ran"
Ya dauki akwatinsa da jakar kayan kwalliya
ya rataya daya ya ja daya ya kaikaita ta gefen
mahaifinsa wanda ya kasa cewa komai ya fice
daga dakin. Abdulhadi ya bi shi a guje ya tsaya
a faranda yana kallon fitowarsa zuwa harabar
motoci, duk ya ji ya karaya bai san abin da ke
damun sa ba tsakanin karaya da takaici. Shin
yakinsa da Na`ibi har ya kai yayi asarar dansa
こ
121 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
daya tilo ko kuwa dai shi ne ba shi da gaskiya?
Tun Ibrahim bai tafi ba duk kewarsa ta dame
shi, karo na farko ke nan da zai rayu babu dansa
masoyinsa Ibrahim da sunan yayi fishi ya bar
masa gidansa kuma wai sun rabu. Lallai shi ya
so kashe Farida amma laifin ne da ba zai taba
bayyana amsawarsa ba. Gogewarsa ta fi gaban
hakan don haka sanya ido dole ya kalli dansa
yana barin rayuwarsa shi ne hanyar hakan,
domin Ibrahim ba zai sake yarda da shi ba
muddin bai amince da wannan laifi ya mika
wuyan cewa shi yayi ba, ya san hakan domin ya
gina rayuwar yarda da juna tsakaninsa da dansa
ta hanyar da karyata ta wannan hanya zata yi
wuya ta sake gina irin yardar da ke akwai a can
baya. Ya daga hannu kamar ya kira Ibrahim a
lokacinda yake kokarin tayar da mota, amma
zuciya ta hana shi har sai da dan nasa ya sa
motar a waje ya fice sannan ya ji ya jingina da
bangon farandar ya kasa komai.
*
Farid wanda ke bin Mansur Nai`bi ka fada
da kafada yana ba shi bayanan abubuwanda
suka faru lokacinda yayi tafiya a yayinda masu
aiki ke shigar da kaya, kuma matarsa wadda aka
gama gabatar da Farid a gabanta take kokarin
shigewa ita ma ta tsaya a yayinda ta ji
tambayarta ta cewa wai ina Farida ta sami wata
kaikaitacciyar amsa daga bakin Farid mai cewa.
'sir dama na ce kada na 6ata muku hutunku ne
122 Mariyan Masoya Rahma AbdulMajid
da aiyukanku a lokacin da ake nesa domin wani
abu ya faru duk da an dauki mataki'
"Me ya faru? Da fatan babu Farida a ciki?"
Ya tambaya fuskokinsu iri daya shi da
matarsa don damuwa.
"kan Farida ne kuma tana kwance a asibiti
domin...
"Farida na asibiti? Me ya sami yata, wa ya
taba ta?"
In ji mahaifiyarta wadda ta soma kara.
""Wasu sun yi yunkurin kashe ta ne ta
hanyar busa mata faudar sanya bugun zuciya,
amma na kai ta asibiti yanzu dai komai dai dai
ta sami sauki"
"Mu je asibiti"
Inji Na`ibi wanda ya taso matarsa gaba suka
juya suka koma motar da ta dauko su daga filin
jirgin. Suka shiga baya cikin sauri Farid ya
shiga gaba direba ya ja da sauri.
Ita ce zaune gafen gadon Farida rike da
yatsunta tana bibiyan duk wani motsinta cikin
damuwa da tsarguwa na alamun zargi dake idon
'yar ta ta wadda ke yawan korafin bata damu
dasu ba. A yanzu tana son ta zazzage duk
damuwar da bata nuna wa 'yar tata bane na
tsayin shekaru a wannan kwanciyar asibitin,
amma a nan Farida da mahaifinta Na'ibi wanda
yake tsaye da hannayen nan nasa a aljihu kan su
a hade yake wurin wannan zargi, don haka duk
kalmomin habaici tare suke aika wa wannan
talika a iya zaman nan. Farid tuni ya fita tunda
123 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
zama ne na iyali duk da Farida ta sake
gayyatarsa don ayi masa godiya amma bai wuce
mintuna biyar ba ya koma waje. Abin da ya
damu iyayen Farida kuma ta kasa gaya musu
gaskiya shi ne waye ya nufe ta da wannan
sharrin. Sam! Ta ki sanar da su duk kuwa da ta
yarda da faruwar farmakin amma tace wani yaki
ne da ya shafe ta ita kadai. Mahaifinta wanda ya
nuna matukar bacin rai yayi alkawarin ba zata
sake fita ita kadai ba sai da me gadin lafiyarta
na musamman da zai kawo daga waje ba
wadanda ta saba zaba a matsayin abokan yawo
ba, amma nan ma ta dage da cewa bata bukatar
a sauya mata irin na ta tsaron.
"Father wannan fa ba wani abu bane da ya
shafi tsaro ba, ni na kai kai na kuma na gaya
maka yaki na ne, yanda ko zan yi wannan yakin
zai ba ka sha`awa"
"Farida ni da na fi ki sanin makamar duniya
na amfanu da taimakon ki kan yakin kasuwanci
da nake yi yaya za a yi ki ce akwai wani yaki
naki ke kadai da baya bukata ta kuma ga shi har
sun soma yunkurin kai ki lahira....Kada dai
yana da alaka da shegen saurayin nan naki da
kika guda saboda zalamarsu shi yasa kike son yi
ke kadai"
Ta lumshe idanu don ta 6atar da faduwar
gabanta na gane wanda yake nufi.
"Ah haba! Father kada ka sanya Ibrahim a
wannan salon, an rufe caftarsa kada ka
124 Малyan Masoyа Rahma AbdulMajid
bude....Ibrahim ba zai iya cutar da ni ba har ga
neman mutuwa"
"Well ki na da zabi na ki gaya min ko kada
ki fada ba zan yi wasa da `yancin ki ba, amma
ki sani `yancina ne in bincika duk abin da ya so
taba min iyalina kuma in kin ga ban gano ba to
ban bincika bane"
125 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Hudu
Motar na garzaya wa hanyar fita asibitin ba
ta inda ta shigo ba fitilunta na haska ko ina duk
da ba har karshe direban ya kunna ba. Farid
wanda ke kallon waje zuciyarsa na neman
tsaigumin da zai ba shi ainahin makomarsa
idanunsa suka yi arba da wani bawan Allah
tsaye sanye da riga shet mai dogon hannu ruwan
yashi shara-sharar da a na íya hango singiletinsa
ta ciki ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon
jins. Ya ga wannan fuska wadda ta fara kona
masa zuciya a ranar da Farida ta sami wannan
tsautsayi, fuska ce ta wanda ya sha gabanta
bayan ta fito daga wannan kulab kuma ta nuna
masa 6acin rai. In zai tuna mutumin ya taba
hannun Farida ko ta nan ne ya shafa mata abin
da ba ta son ta fadi shi ne, ko shi ne ma na mijin
da yayi mata ciki.
"Direba tsaya"
Ya umarci direban ba tare da ya tuna ba shi
da hurumin yin hakan tun da me gidansu ne a
motar ba har sai da direban ya tunasar da shi ta
hanyar kallon sa da kin tsayar da motar kafin
Na'ibi ya sanyo baki da umartar direban yá
tsaya.
"Wani abu ne Farid?"
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya bukata yana me daga labulen wundonsa
don ya hanga.
"Sir yaron da na hanga tsaye shi ne wanda
na ga ya sha gaban Farida daf da lokacin da
wannan ciwon nata zai faru, yanzu kuma ga shi
a asibiti, ina tsoro kada ya zo wani abun ne
na..."
"Kana da gaskiya koma da baya Micheal mu
gan shi ko na san shi"
Suka dan yi baya ba don suna jin tafiyar
motar ba sai don ta iso bayan. A yanzu Na`ibi
ne ya leka da kansa yana kallon wannan yaron
wanda ya ke kaikomo maimakon tsayiwar da
yayi da fari. Ya dan gyada kai.
"Ok! Na san inda zancen ya bulla. Micheal
mayar da mu baya ka ajiye motar zan zo ga
yaron nan ina jin ina da hira da shi"
"Baka zaton yana iya cutarwa?"
Matarsa ta bukata murya a tsorace. Ya bigi
kafadarta.
"Wannan me saukin kai ne baya cuta, akwai
magana ne tsakanin mu”
"Mansur ba na son irin wannan gangancin
naka, yaushe ka fara yarda da mutane a irin
wannan kasar cewa akwai me son ka akwai
mara son ka?"
"Kwantar da hankalinki ina zuwa"
Ya dan bugi kafadarta mafi kusa da shi wato
ta dama, ya sauka daga motar nesa da wannan
yaro.
127 Maryan Masoya Rahma AbdulMajid
"Ibrahim na can tare da hankalinsa baya lura
da mai shiga ko mai wucewa har sai da ya ragu
yan mitoci tsakanin sa da Na'ibi sannan ya
waigo da kyau ya kara tsayuwa cikin maye
gurbin damuwarsa da fargaba. Na'ibi ya doso
shi fuskarsa cike da murmushi sannan ya fara
magana tun daga nesa da shi.
"Ibrahim lafiya kake tsaye a nan?"
Ya mika masa hannu kafin ya ba shi amsa
suka yi gaisuwa irin ta maza masu shirin taryar
duk abin da zai faru.
"Babu lafiya... ina nan ne ina jinyar matata
bata da lafiya"
Na`ibi ya zumburo baki sannan ya share
gumin hancinsa.
"Oh! Barka! Kayi aure, Allah Ya ba ta
lafiya".
Yayi murmushi na karfin hali sannan ya
kura masa ido.
"Sir ko zan iya magana da kai kamar da da
uba... ina da damuwa"
Na'ibi ya tura hannu aljihu bisa al'ada
sannan ya gyada kai.
Ibrahim ya dan nisa sannan ya sake kura
masa ido.
"ka yafe min Father in zaka iya. Ba wata
bace mata ta ba illa `yarka Farida. Ba ina nufin
mata ta in ka ba ni ba, ina nufin mata ta da
muka yi aure a Jamus cikin sunna da tsarin
shari`a. mun zauna cikin jin dadi da kwanciyar
hankali da kauna. Hah! Ranakun mu tare sune
128 Motiyan Mosoya Rahma AbdulMajid
ranaku mafi girma da daukaka a rayuwata, har
muka samu ciki. Wannan ciki shine kwarin
gwiwar da muke jin zai ishe mu mu fuskance ku
kuma da shi muka fara tunkarar babana. Ya
nuna min ya hakura kuma ya amsa, amma
haduwarsu da Farida ya muzanta ta ta inda
bayan ta sami wannan 'ciwo ta ji ba ta son
ganina...
Ya dan matse kwallar da take shirin hana
shi magana da kwarin gwiwa, me wuyar ta fito
yana bukatar ci gaba da bayani ya tunasar da
kansa.
"A yanzu na rabu da babana, na kawo kaina
gare ka, ko me kake so kayi masa da ni ina
karkashin mulkinka, amma ina so kada kayi irin
halinsa ka sada ni da matata"
Ya matsa jikinsa a yayin da ya fara kwalla.
"Tunda na san Farida na so ta ban taba nisa
da ita a waya ko a ido ko a yanar gizo ba sai a
wannan kwanakin. Ina asibitin nan duk
kwanakinta a ciki, amma ta ki yarda ta gan ni.
Na damu ina so na gan ta. Ina son ta ba zan taba
yin wani abu da zai cutar da ita ba"
Na'ibi wanda yayi zako ya kasa sabawa da
kalmar cewa Farida da Ibrahim sun yi aure duk
kuwa da kokarin da yake na ganin ya shigar wa
kan sa da sabo koda kuwa zai tsaya a fuskarsa
ne a matsayin wanda ya saba da gwagwarmaya.
"Da kai da Farida kun yi aure a Jamus kuma
kun zauna tare har kun sami ciki"
129 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya jero labarin a hankali yana kallon
Ibrahim wanda ya sanya hannu a aljihu ya fito
da kwafi na takardar aurensu ya mika wa Na ibi
wanda bai yi ragon azanci ba ya karba sai da ya
dubi Ibrahim da kyau sannan ya soma dubawa.
Ba shi da zabi baya da ya yi murmushi ya
kawar da kai gefe guda don yayi tunanin da ya
san ba zai iya ba. Yana so yayi girman kai wa
mamaki, amma ya kasa sai ya soma niyar
magana ya kasa. Babu tababa akwai kan sarki
na nuna doka da like-like a takardar da ma
zancen da ke ciki mai nuna cewa Farida da
Ibrahim mata da miji ne.
"Na san bamu kyauta muku ba, amma babu
yadda zamu yi ne Father, muna son junanmu ni
da Farida, kuma ba zamu iya sadaukar da kan
mu ga gasar ku ba, ba ma ciki"
"Dakata"
In ji Na'ibi kan sa a sunkuye sai da ya ji
Ibrahim shiru sannan ya dago.
"Kun yi aure da Farida ba da sanina ba ko
sanin mahaifinka, yanzu kun so mu sani ke nan,
kuma ni yanzu ma kake sanar da ni....na san dai
ba zaka sanar da ni a banza ba ko akwai abin da
kake so na yi maka?"
Ibrahim ya dan sunkuyar da kai sannan ya
dago da nuna gazawa.
"Ina so ka karbe ni ne a matsayin sirikinka
ko da hakan na nufin na yi nisa da uba na ne,
mahaifina ya kasa amsar Farida a matsayin
sirika, kada ka zamo irinsa"
130 Matan Masoya Rahma AbdulMajid
"Kasa karbąn mahaifinka neiyawa ta? Me
nene asirin rashin lafiyar Farida?"
Ya Kura masa ido a wannan lokacin don
samo amsa koda kuwa ba a bakinsa ba.
"ban da masaniya, Farida ta ki magana da
ni, tana fishi da ni kan wani makirci da aka so-a
raba mu don shi, na ji an ce ba ta da lafiya ne
na zo nan asibitin, amma ta ki yarda a bar ni na
shiga wurinta"
"Uhummm! Wane irin makirci ke nan aka
hada muku?"
"Baba na ya ce mata tare muka shirya
wannan aure don mu cuce ka, baya đa na rantse
da Allah ba tare muka shirya ba, ta yarda da
shi"
Yayi ta kada kai sannan ya dubi Ibrahim
karo na uku.
"Yanzu Farida na da cikinka a jikinta...."
"zaka sami jika father, ka yarda da aurenmu,
shi ne abin farinciki mafi girma da ya tabа
samin zuri`ar mu baki daya"
Ya sake mai da hannunsa cikin aljihu.
"ka je ka huta, zan kira ka nan da wasu
awoyi don tattauna sakamakon tunani na, a
yanzu ba zan iya fitar da komai ba ina dan
kidime tukuna"
Ya karbi lambarsa ya ki karban rakiyarsa
zuwa ga motarsa sannan ya wuce yana tafiya a
hankali yana kada kai da murmushin mamaki.
A mota bai iya cewa kowa komai ba baya da
dariya da yake, babu wanda yake amfanuwa da
131 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
tambayar da matarsa take, kamar Farid wanda
ya matsu ya ji wani abu, amma babu abin da
Na'ibi yace ban da 'Ibrahim Abdul Hadi ne, ya
zo ganin Farida, amma bata yarda ya gan ta ba
da ga nan ya rufe bakinsa ya na duba wayarsa,
sako ya tura wa Wilson cewa su hadu a gidansa
yanzu.
A farfajiyar motoci ya tsaya ya sallami Farid
cikin godiya da nuna jin dadin yadda ya kula
masa da iyalinsa sannan ya bar shi ya dauki tasa
motar shi kuma ya doshi falon da ya san lallai a
nan Wilson zai jira shi. Yana zaune yana duba
wani littafi dake kan tebur kusa da inda ya
dogara kugunsa, yau tsayinsa ya kara fitowa
saboda sanye yake da bakin wando da T shirt
fara sol mara adon komai.
Ya dago da sauri ya dubi fuskar Na'ibi
wadda ta sanya shi saurin daure nasa bayan ya
karanci damuwa a cikinta.
"Me gida da fatan ba wata damuwa?"
Shi ma ya zauna kan irin wannan tebur din.
"Ashe Farida ta fi ka wayo, ta kuбuce makа
tayi abu ba tare da ka iya sani ba"
Ya sunkuyar da kai bayan yayi mitsi-mitsi
da ido.
"ban sanya wa madam Farida ido ba tun
lokacin da ka ce a kau da ido ta je ta shakata
wani abu ya faru ne, sir?"
"Abubuwa ne suke juya kwalkwalwata.
Farida ta auri Ibrahim aure na hakika, sun zauna
tare duk iya zaman da na zaci tayi tana
132 Manyan Masoya Rahma AbdulMajid
shakatawa a Jamus.Farida na da ciki a yanzu
haka na Ibrahim, amma ba sa shiri, babansa ya
san zancen kuma ya ki yarda. Farida na kwance
a asibiti wani ya auna rayuwarta dakyar ta sha"
Ya dan taso cikin mamaki.
"Duk wannan ya Faru, Me gida?"
"zauna in baka labari yadda komai ya faru
filla-filla ba kuma na kira ka ne ka zo mu yi ta
mamaki ba, so nake ka yi tunani, don ni na
kasa"
Lokacinda ya fadi hakan tuni shi ma ya sami
kujera ya zauna, Wilson ya dawo da sanannen
murmushinsa kan fuskarsa ya soma sauraron
labari yadda Na'ibi ya samo.
"Farid bai san wani abu kan duk wannan
ba?"
"Farid bai san komai ba, ya ma damu ya
sani, shi ya ingiza ni na gano Ibrahim da ya sani
da zai 6oye domin biyayyarsa ga Farida ta fi
biyayyarsa gare ni
Suka yi shiru na tsayin lokaci.
"Amma hadin labarin nan na nuna da
hannun Hadi a cutuwar Farida"
Wilson ya ambata yana kallon nesa da inda
suke kamar yadda tunaninsa ke yin nisa.
"Me ka gano?"
Na`ibi ya bukata a zumude.
Ranka ya dade dubi lissafin nan. Hadi me
saurin fushi da rashin dabara me dorewa, ya riga ka samun labarin auren Farida da dansa
kuma ya ki amincewa biyu sau biyu kullun
E
133 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
hudu take bayarwa, ta bayar da kwanciyar
Farida don kada a haifi wannan jika. Me zai
sanya Farida ta 6oye maka wanda ya nemi
kashe ta in ba yana da irin kusancin da Hadi ke
da shi ga jininta da son ta ba? Me