jid
kwarewa ta kawo nasara gare shi da asara ga
AbdulHadi sai dai tana hakan ne don samun
damar gabatar masa da bukatarta ba tare da ya
wadata da ita ba, don haka Farida ita ta fi
amfani da wannan kasada da fari bayan da ta
sanar da rmahaifinta cewa tana soyayya da dan
abokin gasar kasuwarsa, amma babu bata lokaci
ya nemi da ta bukaci ko menene a wurinsa
amma ba wannan ba, ganin Ibrahim ya kawo
kansa ga Na'ibi a guje ya zaci cewa wata
makarkashiya ce daga mahaifin yaron domin ya
bullo masa ta wata hanya tunda ya zame masa
karfen kafa, don haka babu bata lokaci ya kori
Ibrahim cikin bakaken maganganu, a karo na
biyu Ibrahim ya sake bayyana masa a mai
neman auren Farida ko da kuwa hakan na nufin
ya nisanta da mahaifinsa, amma maimakon
sassauci Na'ibi bai kore shi zalla ba sai da ya
hada da marinsa. Mahaifinsa yayi masa Allah
Ya kara ya kuma yi masa alkawarin nisanta shi
da duk abin da ya zamo nasa muddin ya dage da
son Farida. Ibrahim ya fara jin sadaukarwa,
amma bayan haduwarsa da muradin zuciyarsda
wadda ta ke kiransa Balala maimakon Balarabe
ta zubda hawaye maras iyaka da nuna masa
cewa dole su ci gaba abinda ya sanya ya ji
wauta ce ma gare shi yayi tunanin rabuwa da
Faridar wadda tuni ta kaurace ta yanke alaka da
duk wani abu na mahaifinta da ta fara yiwa
jagoranci musamman abin da ta fi kwarewa
wato harkar sadarwa muddin bai amince da
20 Mofiyan Masoya Rahma AbdulMajid
soyayyarta da Balalanta ba. A yau takanas
Na`ibi Bici ya bukaci ganin 'yar tasa bayan da
ya sake tika AbdulHadi Bici a kasa a gasar
samin wata kwangilar samar da sadarwar gidan
gwamnati da suka yi tare kan dasa maduban
hangen nesa a barukokin kasar nan. A ofshinta
ya shaida mata wasu shaidu dake nuna kokarin
yakarsa da Ibrahim yake yi don farfado da
mahaifinsa don haka wannan waazi ko dama
itace ta karshe muddin ba zata rabu da Ibrahim
nan da kwanaki uku ba, to shi ma zai dora mata
takunkumi hana kusantar dukiyoyinsa. Farida ta
rasa amsar da zata ba shi da ta wuce na baro
ofishiinsa cikin fishi yana kira bata ko waiwaya
ba ta fice ilahirin ofishin.
*
A tsallaken filayi oba din, gefen wata mata
wadda take ta faman gasa dankali tana sayar wa
uku paihamsin nan Farid yake zaune bisa
wani dogon benci shi da wani dattijo wanda da
alama shi ma ba shi da wurin zuwa ya ci
dankalin ban da nan wurin. Ba hira suke ba
amma sukan tono kalma daya biyu su yi musaya
ko kan titin ko kan dankalin. Dattijon wanda ya
cinye guda biyu ya kunshe daya da alamar yana
da wanda zai kai wa, ya mike bayan ya biya
kudinsa da wata dunkulalliyar wazobiya ya dan
dubi Farid yace masa 'bie'. Farid ya bi shi da
kallo bayan ya amsa har zuwa lokacinda ya isa
ga titin yana ta shirin tsallakawa don kada kafar
tsufa ta yi masa tawaye. Farid bai dena kallon sa
21 Maliyan Masoya Rahma AbdulMa jid
ba ba kuwa don yana birge she ko kushe shi ba
sai don ganin da alamar wannan tsoho tsohon
dan boko ne, da jin kalmomin turancinsa ba na
ji a bakin hanya bane na zaman aji ne, kuma
ajin me kyau, watakila ma bai yi yawon cin
dankali abakin titi ba a yayinda yake kamar sa
amma dubi yadda rayuwa ta mayar da shi, babu
amfanin bokon babu amfanin yawon neman
kyakkyawar rayuwa, to ina ga shi wanda tun a
samartakarsa ya fara yawon cin rogo ko dankali
daga arewa har kudancin Najeriya, kada fa ya
zamo tsufansa kenan zai zamo irin na wannan
dattijo?! Gabansa ya zaftaro ya fado bayan tuna
wannan kalma daidai lokacinda wata jeep-salon
mai kirar bayan kwado launin azurfa samfurin
Infinity ta yi sama da wannan tsoho da
dankalinsa ya dawo kasa ba don ta dawo da shi
ba, sannan ta kaikaita ta ci gaba da gudu. Ihu bai
kaure a titin ba sai na motar da tsohon
kasancewar babu kowa bisa titin, sai shi sai me
dankali da karamar `yarta da suka taso a guje.
Ban da tsalle da ihun kiran tsohon nan babu
abin da mai dankali take yayinda `yarta tuni ta
bi motar a guje amma da ta ga ba zata iya kamo
ta ba tuni ta dawo, shi kuwa Farid ya sami
damar daga kyallen hankicin sa a kan titin inda
motoc suka lura suka soma sulo sannan ya
durkusa ya dauki kan tsohon wanda yake ta
kakari kafarsa ta yi raga-raga. Wata mota kirar
pijo 307 an manna mata stiku a gilasin gaba
daya an rubuta Press daya an rubuta The Nation
22 Mofiyen Mosoya Rahma AbdulMajid
ita ta fara tsayawa inda wani akawu mai janta
sanye da shet da wando da ta yi ya sauko da
sauri ya agaza wa Farid wurin kokarin bai wa
tsohon nan kulawar farko, sannan ya fara kiran
taimakon gaugawa kan wayarsa a lokacinda
mutane ke ta fitowa don agaji.
Da shi da Farid ne suka shiga motarsa suka
bi ta ambulance a baya inda suke hirar abinda
ya faru cikin jimami. Farid ne ke ba shi labarin
abin da ya faru kasancewar ya shaida komai,
amma wata tambaya da mutumin yayi ta kusa
da karshe ta ja hankalinsa. 'Yaya? Wace irin
mota ce?' itace tambayar kuma tana nufin
abubuwa da dama. Da fari tana nufin aikin
jarida da ya tabbatar wannan dantaliki na yi,
watakila ma ya sami labari kenan aikin kudinsa
yake bayan na ceto, na biyu shine kamar ya san
motar nan, ya san ta ya san kalarta da lambarta.
Ita ce motar da yarinya Farida ta hau ta wuce ta
busa masa kura, duka abubuwan da suka shafi
Farida babu wanda ya manta ko ina ya gani zai
tuna. Kenan wannan tambayar ba zai iya sayar
da amsarta duka ba akwai bukatar tsanaki a ciki.
"wata Infinity ce silber color sai dai ban ga
lamba da mutumin ciki ba, amma da alamar irin
masu hali din nan ne da basu mai da rai a bakin
komai ba"
A kofar asibitin tuni an gabatar da makarar
daukan wannan mutum, kuma ga mamakin
Farid wasu 'yan jarida masu daukar hoto tuni
sun isa wurin da alamar abokan aikin wannan
23 Matiyan Masoya Rahma AbdulMa jid
abokin taimakon nasa ne, haka nan shi ma mai
taimakon tuni ya fitar da rediyonsa yana son yi
masa tambayoyi. "kada ka damu abin da muke
kokarin yi shine tona asirin irin wadannan masu
kudi dake daukan rai a banza a idon duniya, ina
son rubuta rahoto kan wannan hatsarin da ma
wasu da suka fara zamowa ruwan dare a kasar
nan. Amma dole sai da taimakon irinku masu
gani a ido da kuma karatu"
Bai musa ba domin tuni ya riga ya kullaci
abin da zai iya. Suka yi hira da bata wuce abin
da ya bayar a mota ba, a yayinda ' yan sanda ma
suka ja shi domin yin nasu binciken shi da mai
suyan dankali.
*
Farida ta shigo gida a tsorace tana busa mota
kamar tana cikin gosilo, me gadi har wuntsilawa
yake saboda ya bude mata. Ta shige cikin
sukuwa ta sanya motar cikin wata farfajiya dake
kallon sashin falonta maimakon layin
takwarorinta motoci, sannan ta sauko da gudu ta
dafa kafadar wasu jami'an tsaron gidan da suka
iso gare ta.
"A wanke min motar nan yanzu kada a bar
komai jikinta, sannan kada wani ya neme ni
yau, ina da bukatar kadaici"
Ta shige ba tare da ta jira amsar su ba. А
falonta ta yar da jaka ta soma tsalle na kaduwa
yayinda ta dauki wayarta ta falo ta latsa
lambobin Ibrahim.
"Hello honey kin isa gida?"
Matiyan Masoya
Ta fashe da kuka.
Rahma AbdulMajid
"Bally kai da Father zaku kashe ni, kuna jawo min bala`i"
Muryarsa da alamar rikici a-yayinda yake
tambayarta 'me ya faru Farida me nene kike kuka?"
"Balala na bige mutum da motata hankalina
baya wurin, watakila ya mutu watakila ya
musakance, hankalina na tare da matsalar ku kai
da Fathe.. Ibrahim.."
"Kwantar da hankalinki, a ina haka ta faru
zan dauki mataki?"
"Akan fly over na.....Balala ni na kashe
mutum kuma babu dama na tsaya...oh! God!"
"Kin kyauta da baki tsaya ba, zan aika ayi
abin da ya dace...amma in kika tsaya zasu iya
yi miki lahani kin san mutanen Africa yadda
suke tunani, yanzu kada ki fitar ke ce don tunda
baki tsaya ba zai iya shafar sunan gidanku don
haka..."
"kai gida ya dama kyale ni"
Ta yi jifa da wayar ta rike kai ta fada kujera.
Duka abinda ya ke kwantar mata da hankali na
wasu `yan dakiku shine cewar Ibrahim zai yi
wani abu.
*
Ya zauna kofar dakin yana murmushi
sannan ya soma karanta ta kamar haka:
25 Matiyan Masoya
Zuwa ga Farida.
Rahma AbdulMajid
9th/8/2010
Ni ba dan jarida bane kamar yadda kuka
zata ko kuma na ambata ba, sam! Ni wani talaka
ne mai kare hakkin talakawa yan uwansa da
duk iya karfinsa. A jiya talata goma ga watan
Agusta kika yi arangama da wani dattijon talaka
da ya kammala kalacinsa a tsakiyar titi saboda
rashin gata ya rage abin da ya ci don ya tsallaka
titin ya kai wa marainiyar 'yarsa da bata da gata
sai shi, kika dauke shi da motar ki kirar Infinity
mai ruwan silba lambar KJA 243. Wani abu da
ya fi jan hankalina shine rashin tsayawar ki da
nuna gata ga wannan rai da ba shi da gata sai
Allah, kika bar shi a nan kwance mutu kwakwai
rai kwakwai. To albishirin ki ko da baki so ji ba,
ina son in taubatar miki da cewa wannan bawa
ya rayu, amma ba dole ne rayuwar ta sake yi
masa amfani ba. Akwai yiwuwar zai rasa
kafarsa in har ya tashi, in fa har ya tashi
kenan, domin tashin ma babu tabbas,
kasancewar har yanzu da nake yi miki magana
baya ko uffan, kuma ba a sami hada kudin da za
ayi masa gwajin kwalkwalwa ba. yarsa wadda
bata ci bata sha sai ya rage máta tana nan
hannun titin Allah bata sami mai bata ci ba
ballantana taimakon arundugun kudin tayar da
kafadar mahaifinta. wannan lamari ya ja hankalin yan jarida musamman ma na The
Nation yayinda daya daga cikin jami'an su ya
raka mu har asibitin ya kamala duk wani bincike
2t Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
kan yayata mai wannan danyen aiki. Abin da
yayı musu cikas shine sanin kowane ne mе
wannan wulakanci ga talakan kasa, abinda ni
kadai kawai na sani, ni na san ke ce kika aikata
kuma ina da ingantattun bayanai da zan iya
bayar wa akan haka amma ban yi ba. Na san
zaki tambayi kanki dalilin da ya hana ni ko na
neman wani abu ne gurinki? Sam! Ba haka
bane, bana neman wani abu a wurin ki baya da
hakkin wannan bawan Allah. Ki kula da shi ki
dauki nauyinsa, amma idan kika ki yin haka, to
zan yi abin da ya dace, ina da hotunan wannan
lamari da kwafen wannan wasika tawa gare ki
zan kara bayani na aika ta shelkwatar 'yansanda
masu neman ki, da kuma kafafen yada labaru
domin matsa wa yansanda lamba.
Shi dai wannan bawan Allah yana nan
kwance a asibitin koyarwa na jihar Lagos.
Sunansa Gabriel Moses, ina zuwa duba shi har
tsayin awoyi arba'in da takwas in ga ko kin yi
wani motsi idan baki yi ba ni zan yi inshaAllahu
Da ga Farid Akil
08063800300
Ya rufe takardar ya tura a wani ambulan mai
kan sarkin gidan Jaridar Aminiya, sannan ya
kalmashe ta yana cikin fara'a. Bai san ya
karanta wannan wasika tasa da karfi ba sai da
ya ji tafi da shewa sannan ya daure fuska, bai
27 Maliyan Masoya Rahma AbdulMajid
juyo ba don ya san Mahdi ne sai da ya dawo gabansa sannan ya dube shi.
"kai kuma ta yadda kake rubuta wasikar
soyayyarka kenan?"
Ya sake ballewa da dariya yayinda Farid ya
ja tsaki ya mike.
"Wannan ce wasikar soyayya?. Ni wannan
wasikar ma ba ita na yi wa ba, babanta na yi wa
nayi amfani da sunanta ne kawai amma shi nake
so ya karanta don kamar ya fi ta hankali... kai
wai baka yarda da cewa gamon tsiya kawai nake
da yarinyar nan, amma ba wai ina binta bane, na
gaya maka abin da ya faru jiya ko baka yarda
bane?"
Dakata dakata. Kwantar da hakilonka...
yanzu gaya min manufar wannan wasika taka
da tasirinta"
Ya dawo gare shi.
"manufarta itace na gwada tawa iyawar ko
zan iya kwatar wa talaka hakkinsa ko kuwa a'a"
Mahdi ya kalle shi cikin nuna tausayi da
takaici.
"Farid ba sarka muka zo yi garin nan ba,
aiki muka zo nema in baka sani ba ka sani, in
har ba zan baka shawara ka ji ba to ka yarda
cewa in ka jawo bala'inka ba zan jira ka
ba...yanzu ka sami irin wadan nan manyan
mafiyoyi da 'ya'yansu ka ce zaka ja da su kai a
wa ko a me?"
Ya juya ya koma daki.
28 Motiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Idan bala'In ya samu ka rantse da Allah ba
ka san ni ba, domin ni fa ban tsayawa, jira ni a
nan
*
Balala ya sauko daga faffadar matattakalar
daga shi sai gajeren wando bulu yana kiran
Guddies. Wani mutum ya bayyana da sauri,
cikin shirin kwat baka da sauran kayan hadinta,
yace 'yes sir' Ibrahim ya dafa shi suka karasa
gaban kofar tangaran mai zuwa farandar falon.
"Guddies aikin taimako kai kadai zaka iya
yi min...Farida ta bige wani dattijo jiya bayan
rabuwar mu, hankalinta ya kasa kwanciya, ina
cikin damuwa..."
Yayi ajiyar zuciya.
"Na sami labarin an kwantar da shi a asibitin
koyarwa, ina so yanzu ka je ka nemo inda yake,
ka yi duk abin da a ka bukata na kudin da zai
ceci rayuwarsa ko nawa ne ka sanya min bill,
zan ba ka naka kason amma ka.."
"sir an kama ta ne a wurin?"
Ya kada kai cikin nishin nuna damuwa.
"Ba a kama ta ba, kuma shi ne abin da ya fi
min dadi, bata tsaya ba, babu wanda ya san ita
ce, amma ka san Farida, ji take tamkar tayi kisa,
don haka hankalinta ba zai kwanta ba...Sunan
gidansu bana so ya fito a lamarin nan ballanta
nata, don haka ka je ka ceci rayuwarsa da
aljihuna a matsayin sadaka"
Ya sake bude baki zai yi magana amma
Ibrahim ya nuna shi da yatsa.
29 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Mutumin nan kada ya mutu Guddie, idan
ya mutu hankalin Farida ba zai ta6a kwanciya
ba, kenan nawa hankalin zai tashi, idan kuwa
kai ka jawo wannan kuskure to hankalinka ya
bar kwanciya"
Ya nitsu yace yes sir sannan ya juya ya fita.
Ibrahim ya sake latsa lambobin Farida amma
kamar dazun bai samu ba ya ci gaba da shafa
kai fuskarsa a cakude yana fadin.
"yarinyar nan don Allah kada ki sanya kanki
a wani hali. Babu abin da zai faru"
A karshen layi Guddie zai karya da motar sa
zuwa kan babban titi amma sai ya ga tsayuwar
jeef skuardia wadda ya sani a gefensa ta yi masa
wuta sannan ta sauke gilas. Abdul Hadi ne da
kansa cikin irin shigar Guddie yayi masa
ishararsa da ya lakanta da hannu ya ko amsa
cikin kashe wutar motarsa ya fito ya shiga ta
mai gidansa.
Suka kalli juna sannan Guddie ya sunkuyar
da kai.
"Maimakon sakon da Ibrahim yayi maka ina
son tura ka Bahrain daren yau ka je ka sha iska
ba don kayi min komai ba, sannan ga sadakar
milyan biyu. Aikin da zaka yi min shine kawai
na tabbatar da aiken Ibrahim bai samu ba kuma
ba tare da ya san bai samun ba..."
"Amma chairman..."
"Kada ka ce min komai, ka san komai na
sani, gasar dake tsakani na da Na`ibi ba zallar ta
kasuwa bace ta rayuwa ce. Bana son `yarsa ta
32 Motiyan Masoya Rahmu AbdulMa jid
auri dana, ka ga watakila kasa taimakon ta bana
in yayi ya sanya ta kufula, bukata ta biyu itace
yadda jaridu suka fara buga labarin wannan
hatsarin watakila a kai ga tonon asirin cewa 'yar
Na'ibi ce ta aikata, kuma dole abin ya 6ata masa
suna, abin da kuma nako so kenan, don haka
idan biya min wannan bukata a milyan biyu zai
yi kadan to na kara ya zama uku"
"Na yarda Chairman amma..
"...Amma in baka yi yadda nace ba babu
kudi babu Bahrain watakila ma babu aikinka,
domin ni ne mai wuka da nama ba Ibrahim ba,
amma in ka yi ban da wannan garabasa zaka
shiga cikin makusanta da suka san sirrina"
Ya sunkuyar da kai cikin ruwan sanyi yayi
dan tunani sannan yace "Ok sir
Farid ya zaro mayafin rufarsa da niyar zai
kwanta ya fanshe gajiyarsa bisa katifa, amma ga
mamakinsa sai ya ji an bangaji kofar dakin an
shigo irin shigowar da ba ta abokinsa ba. Ya
zabura don ya duba sai ko ga karin abin
mamaki, su uku irinsu daya sanye da singileti
bakake da fararen wanduna da bakin tabarau,
kawunansu kulle da hankici. Wani wanda ya
saba da shigarsu amma bai saba da kamaninsu
ba shine na hudu wanda yana shigowa kawai
nuna Farid yayi yace 'ku kama shi".
Mai daukan wuya mai daukan kafa mai
danke hannuwa suka cafke shi yana kakarin
fadin me nayi.. ku su waye... ku sake ni, amma
31 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
babu wanda ya tanka shi sai a cikin wata
jibgegiyar mota mai rufaffen gilasi wadda ta ba
shi amsa da zurar sa a guje. Basa duka basa
tanka zantukansa amma suna rike da shi har ya
bada gari ya sallama cewa dan kwanjin nan
nasa ba shi da rana ban da daukan nauyi da
damben mutum daya ko biyu. A gaban wata
shirgegiyar farar lemozin suka yi faki suka
daidaita kofofin inda suka bubbude suka jefa
shi cikin waccan. Kwatsam sai ya gan shi gaban
wani mutum da ke zaune shi kadai a kujerar
alfarma amma kuma ba tare da yayi kama da
masu kudi ba. Siriri ne matuka, amma
maimakon ya sanya abin da zai sanya shi yayi
kauri sai ya sanya shet mai yankakken hannu
mai ratsin fari da baki da wando baki duk da
babu zanzaro sun nuna tsadarsu, fuskarta birkice
da kasumba da alamar dattijo ne da ya damu da
aikinsa baya kama da masu laifi kamar yadda
yake kama da masu gaskiya. Da alamar mai son
sanya hannu a aljihu ne domin ko daga zaune
hannunsa na aljihu. Ya dubi Farid fuskarsa da
sauki ba walwala babu dariya.
"Kai ne Farid?"
"Ni ne me zan yi maka?"
Ya tambaya cikin tsageranci, mutumin ya
dada karkata kai.
"Abin da zaka yi min shine ka fitar da kanka
daga harkar `yata kafin ka yi nadama. Takwarar
ka bata gaya min tayi wani hatsari da mota ba
sai a wasikarka na sani, na gode da wannan. Sai
3. Mofiyan Masoya Rahma Abdul Majid
dai ina so ka mai da hankali kan abin da ya shafi rayuwarka, idan ma zaka shiga ta wani to ban da
ta gida na domin kuwa bana yafe wa mai shiga
rayuwar gidana. Maganar wanda `yata ta buge
ta tabbatar min da faruwar hakan kuma na
tausaya, zan kuma yi wani abu a kai, amma ba
yadda ka tsara ba. Kawai dai ina son kada
kuruciya ta debe ka amma bana jiran ka ba ni
umarni ko shawara ka ji ko?"
Farid ya daure tsoro ya daure mamaki ya
kwakulo abin da zai iya cewa.
"Kamar ni kake domin ni ma ba na jiran a
ba ni umarnin abin da zan yi ranka ya dade, don
haka shawara daya, idan ba ka yi abin da ya
dace zuwa gobe da sha biyu ba ni ma zan yi
yadda ka iya."
Ya taba baki sannan ya gyada kai.
"To bari mu ga wa zai bata ko ya batar ni da
kai...Ku mayar da shi gidansa"
Kafin ka ce kwanbo tuni sun jefa shi cikin
motar da suka kawo shi ciki sun zura a guje
Suka bar waccan motar a kan titi.
Farida fara kal cikin jar T.shirt da gajeren
jan wando da suka yi mata kyau musamman da
ta hada da farin kambas na motsa jini ta dogara
da karfen da take motsa jinin a kai tana duba
jaridar, wadda tayi amfani da kalmomi na
tausayi da masu zafi kan lamarin bige mutumin
da gwamnati bata san da shi ba don talaka ne
kuma a ka gudu, kamar yadda jaridar ta dauko
33 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
rahotannin mutane masu yin tofin-Allah-tsine
kan masu irin wannan dabi'a ta wasa da ran
talakawa. Ta ciro kai ta dubi mahaifinta wanda
ya bata jaridar tsaye yana jiran ta, hannuwansa
sanye cikin aljihun da bai yi wa zanzaro ba duk
kuwa da yana sanye da farin tai kan bakar shet
din sa. Ta kada kai cikin matukar damuwa.
"Ba na kawo miki don ki damu bane na
kawo miki ne ki ga abin da kika yi kuma ki san
cewa akwai wanda ya san ke ce kika aikata har
ya turo min gargadi kuma na gargade shi..."
Ya juya mata baya yana dan taku a katon
falon.
"Ina so ki bar garin nan gobe ki tafi
Johannesburge can gida a South Africa ki zauna
har sai na kashe zancen nan... zan yi wani abu a
kai amma so nake ki tafi don ba na so a taba jin
sunan ki ko na gida na a ciki... kuma ga shi har
wani ya san ko aikin wane ne, ke nan ina, da
wasa ni da mai wannan aiki"
"Father!"
Ta ambata cikin mamaki da tsorata. Shi ma
ya juyo da yanayinta.
"In bar kasar saboda me? Don kawai kada a
ji sunanka? Koda mutumin nan zai mutu? Me
zai baci in na fito kafin wani ya fito na ce ni ce
kuma na bada hakuri, nawa ne abin da za a biya
ya ba shi lafiya? Babu abin da zaka ce sai na
gudu. Father rai muke magana, kana maganar
suna"
Ya dako tsawa.
34 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Yes ina maganar suna ne da rai, suna na ba
irin sunan kowa bane, ya fi rai a mafi yawan
lokuta, and... bana in kika ce za ki yi wasa da
suna na don son ran ki zan miki hukumci ba irin
na da da uba ba...Farida gobe da safe nake son
ki bar kasar nan, and rashin bin umar ni na zai
kwankwasa ki kin ji ko?"
Ya juya ya fita a fusace a yayinda ta bi shi
da kalio. Yana 6acewa ta jingina da bango cikin
wani dogon ajiyar zuciya da ya raka zamewarta
daga bangon zuwa kasa.
"Father! Why popsie why?"
Ta dubi gefenta inda wayarta ke soke kusa
da tawulin share gumi, kamar tana niyyar kiran
Ibrahim ne, amma daga baya ta ji wani tunani
ya doshi zuciyarta. Kamar fa ita ce ke haukar
son Ibrahim amma shi tuni ya ja da baya ya
sallama...Ibrahim baya son gaya mata ne amma
ya hakura da ita. Da a ce Ibrahim din da ne da
wannan lamarin da shi za a ci a side, amma
yanzu dubi yadda ya bar ta ita kadai, bayan shi
ta fara gaya wa a duniyar nan, kuma ya ci gaba
da yi mata karyar ya dauki mataki, amma har
yau shiru. Ta rike kai hannu bibbiyu. Karo na
farko kenan da ta ji tana son barin kasar kamar
yadda babanta ya sha yi mata tayi. Lallai akwai
bukatar ta yi nisa inda zata rage jin duriyar
Ibrahim, sai dai kafin ta yi hakan tana bukatar ta
ceci ran da ta sanya a uku sakamakon son
Ibrahim din tunda daga shi har babanta ba su
damu da lamarin ba. Amma kuwa idan da gaske
A
35 Maliyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ibrahim baya son ta yanzu ya cuce ta domin
bata san ta inda zata fara mantawa da shi ba.
Tayi jifa da hannayenta wadanda basu rabu da
jikinta ba ban da dokuwa da iska da suka yi, ta
so fashewa da kuka amma wani sashin dauriya a
zuciyarta yace mata sam. Kada ta yi kuka.
Gwada mantawa da Ibrahim kamar yadda ya
gwada mantawa da ke yayi nasara. Ta tashi
tsaye tamkar me maye tana tangadi ta bar falon
motsa jinin.
*
Farid na kwance a tsakiyar daya-dayan
dakin su, yau sa'arsa guda babu Mahdi wanda
yayi tafiya cikin zabarin neman aiki. Rashin
sa'ar gare shi shine tsoro dake masa tasiri wurin
hana shi daukan mataki. Yana tuna maganar
mutumin da ya kira kansa mahaifin Farida.
Koda yake bai bayar da wata cikakkiyar
gabatarwa wa kansa ba amma babu musu shine
mai mai`aikatar nan da ya je neman aiki. Tuna
shi da ma`aiktarsa da 'yarsa Farida abu ne da ke
bukatar lokaci musamman ma bayan sun yi
tozali ba a talabijin ko a rediyo ba, ido biyu
cikin mota daya kusa da juna, amma gargadinsa
gare shi ya fi dacewa da samun lokaci yanzu,
kamar haibarsa na sanya wa Farid ya ji kamar
ya bi umarni ya janye bakinsa daga wannan
zance, amma kuma yana jin mazakutarsa da
zuciyar kafiyar da aka san shi da ita da tunanin
taimakon wanda aka cuta suna ta yi masa
magiya kan ya bi abin da ya gindaya na cewa in
30 Matiyan Masoyo Rahma AbdulMa jid
ba a yi komai ba nan da sha biyun gobe to lallai
zai yi wani abu. Me zai yi ban da zuwa gidan
yansanda da na jarida ya sanar da cewa
yarinyar nan mai girman kai da rashin ladabi
shagwa6a6biyar da bata ganin mahaifanta da
gashi ita ce tayi wannan aiki. Da wannan
tunanin da na tsoron kada a far masa cikin dare
ya kwana ya tashi ya kuma jira ko zai ga wani
canji daga wurin Na'ibi Bici zuwa ga mara
lafiya yana mai yawo tsakanin gidansa zuwa
asibiti har karfe goma sha biyu da rabi sannan
ya mika wuya ga haramarsa ga fara lekawa
wurin `yansanda.
Ya tsaya cikin fargaba yana ta gyara kwalar
rigarsa a gaban kantar 'yansandan da suke tsaye
daya na rubutu daya na yi masa kallon raini da
wulakanci da tsoratarwa kwatankwacin abin da
fuskarsa ta saba nunawa.
"Uhum! muna jin ka kai ne cikon na biyar
da ya zo yace ya san wanda ya kade mr
Moses,kuma duka karya suke, idan kai ma wasa
ka zo yi ka sanar tun da wuri domin ba zan sake
daukan wasa kan maganar nan ba, 'yansanda
muke ba abin wasa ba"
Farid ya daure tsoro da alamomin kashe
gwiwa yay i ajiyar zuciya.
"Na san wadda ta bige mr Moses"
Dan sandan ya gyara tsayuwa cikin
murmushi.
"Au! Mace ce ma? To wacece ta bige
shi...?"
a
37 Mafiyan Masoya
"Ni ce na bige shi"
Rahma AbdulMajid
Muryar mai zaki da ban mamaki ta fi isa ga
Farid fiye da dansandan wanda dauke ido kawai
yayi daga kan Farid din zuwa ga wadda ta
bayyana a bayansa. Turancin ta babu alamar
turancin kasa sai kace sarauniyar ingila ke
magana. Koda muryar bata saba wa kamanninta
ba, Farid bai taba ji ba sai yau. Yarinyar da ta
bangaje shi ba tare da yayi mata komai ba, ta
bangaje wani mahaluki da mota da bai yi mata
komai ba shi ma. Yarinyar da ya fi jin haushi